KU DUBE MU Com
KU DUBE MU Com
*5/2/2019*
*Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah SWT da Ya bani damar fara rubuta wannan labari.
Ina addu’a Allah Yasa yadda na fara lafiya na gama lafiya kuma ni daku mu amfani da abinda ya
kunsa. Kuskuren da yake ciki kuma ALLAH Ya yafe min. Amin*
*HAKKIN MALLAKA*
©Batul Mamman
*Wannan labari da duka abinda ya kunsa mallakar BATUL MAMMAN ne. Ban yarda wani ko
wata ya juya min ko da shafi daya ne batare da izini ba. Sannan ban yarda a yada min wannan
labari ta kowace siga ba ta kafofin sa da zumunta, bugawa ko karantawa. Sabawa hakan zai janyo
daukar mataki akan duk wanda aka samu da laifin. Nagode.*
*FARKON FARI*
*1992*
Gidan Mal Ali Gidado babban gida ne a cikin karamar hukumar Sumaila dake Kano. Attajiri ne
wanda Allah Ya azurta da dabbobi masu tarin yawa. Garken shanu, tumaki da awakinsa bazasu
kirgu ba saboda yawansu. Wata katuwar gona ya samu a can bayan gari ya zubesu yana kula da
kayansa da taimakon mutane kalilan saboda bazai juri biyan da yawa ba. Bafillatani ne na usuli
dan siriri ba kiba ko kadan amma kallo daya zai tabbatar maka an zuba kyau zamanin kuruciya.
Mutan gari da iyalinsa suna kiransa Malamijo. Duk tarin arzikin Malamijo kusan kowa ya sanshi a
matsayin rikakken mai mako da bakar rowa. Kudinsa basa tabuwa indai ba aure ya tashi yi ba. To
a nan fa yarinya da iyayenta zasu ci su tada kai. Idan anyi auren ma amarya ita ce tauraruwa taci
mai kyau tasha mai kyau. Gidan gabadaya hannunta sai dawo har zuwa lokacin da Malamijo zai
gaji da ita ko tayi ciki. Daga nan fa ita da babu duk daya don gwani ne wurin wulakanta mata da
cin zarafinsu saboda shima ya sani kudinsa suke aure.
Malamijo ko suturar kirki baya sakawa saboda kada ya kashe kudinsa. Sau tari zaka ganshi cikin
kodaddun kaya yana yawo don bai taba yarda yayi dinki daidai jikinsa ba saboda gudun raini. A
halin yanzu ‘ya’yansa goma sha biyar amma shida ne kadai da iyayensu mata a cikin gidan.
Sauran taran basu da gata suna ga Allah suna ga Yadikko mata ta biyu a jerin aure auren Malamijo
wadda har yau ya kasa sakinta saboda mace ce da ta gagare shi juyawa. Bata taba haihuwa ba
kuma nata mahaifin ma da arzikinsa lokacin da akayi aurensu. Duk da haka dai auren nasu yana da
tsahon rai domin kuwa duka ‘ya’yan Malamijo akan idonta aka haifesu. Idan ya saki uwar yaran
tana kokari matuka wurin kulawa dasu sai dai rashin wadatasu da yake yi yasa itama abubuwan sai
a hankali. Yaran da suka ci sa’a suma sun taso da nasu iyayen a gidan to duk abinda aka kawo
wawaso ake dasawa mai uwa a gindin murhu ya tsira da abin arziki. Wanda babu tasa kuma ya
koma gefe yasha kallo.
Duk bakin hali na Malamijo yaransa sun tsira da abu daya wato ilimi na zamani da na arabiya.
Wannan ludufi da suka samu ya samo asali ne daga shawarar da abokinsa da suke kai dabbobi
kudu tare ya bashi na cewa idan sunyi karatu shine zai mora domin zasu sami aikin gwamnati
kuma a matsayinsa na mahaifinsu shine zaifi kowa jindadi da samun yaran. To dayake zuciyar ta
nema ce kawai ba musu ya amince. Shi kuwa abokin nasa Mal Kallamu yayi haka ne domin ya
taimakawa yaran da suke walagigi a cikin gari. Shawara dai irin ta abokai yana kokarin bashi
bakin gwargwado akan tsarin rayuwarsa amma yaki ji. Banda Mal Kallamun ma waye ya isa ya
fadawa Malamijo magana irin wannan kai tsaye batare da ya auna masa rashin mutumci ko da
rabin kwano bane ya kai masa har kofar gida.
Yau yake dawowa daga kudu inda ya kai motoci uku na dabbobi. Duk yadda aka san Fulani da son
dabbobinsu haka yake a wurinsa sai dai kudi ya fiye masa komai. Kuma gashi da nasibi don yana
samun alkhairi sosai kamar yau din da ya dawo.
‘Ya’ya da matansa haka suka yi ta fitowa ana masa barka da dawowa yana faman hura hanci kada
wata tayi gigin neman karbar jakarsa.
‘Yan mata biyu ne a daki daya tana kwance akan yamutsatsiyar katifa dayar kuma mai alamun ta
girmeta tana daga tsaye a kanta.
Yayarta ta da suke daga iyaye mata daban ta zauna a gefen katifar tana rage murya “Mairama
kinsan idan bamu je ba duk abinda yazo dashi su Inno karbewa zasuyi ko?”
Cikin bacin rai Mairama ta juyo “Adda Salame ban fa hanaki zuwa ba.”
Batare da kosawa ba sanin halin kanwarta ta sake murmushi “Mairama ki dena wasa da iyaye
babu kyau”
Tasowa tayi a harzuke sai dai ko kafin ta fara magana ta soma kukan abinda yake ci mata rai
“Adda har kin manta ranar da zai tafi yace mana mun cika masa gida kamar ‘ya’yan Allah bani,
wato irin wanda ba’a kaunarsu an dai haifemu bisa lalura. Gara ma ke kina zuwa wurin Innarki, ni
kuwa da kasa ta rufe idon tawa bani da wani gata”
Kuka Mairama take sosai Salame tana bata baki. Yarinya ce mai zuciya shiyasa abubuwan rashin
adalcin gidan nasu suke ci mata tuwo a kwarya. Ada da suke makarantar kwana idan suka tafi ko
marmarin hutu bata yi. Gashi yanzu sun gama harda watanni. Da yake sune manya Salame
mahaifiyarta ce uwargidansa ita kuma Mairama tata ita ce ta uku. Dukkaninsu babu wadda ta budi
ido da mahaifiyarta a gidan. Yayin da Salame take da mugun sanyin hali ita Mairama saurin fushi
gareta musamman akan yanayin gidan nasu.
Labulen dakin aka bankada Hajjo mai mulkin gidan a yanzu saboda ita ce amarya kuma yayinta
bai kare ba ta sakar musu harara.
“To tabbatattu isassu. Kuna kwance a daki Malamijo ya dawo bazaku je ku gaishe shi ba”
Da rawar jiki Salame ta mike tana tayar da Mairama “yanzu zamu fito”
Tsaki taja ta koma suka fito babu kowa a tsakar gidan sai kannensu maza da mata kusan kowa rike
da agwaluma daidai a hannu daga su har uwayensu. Hatta Yadikko rike take da guda tana
lailayawa a hannu don taji dadin sha. Kallonsu tayi idanun Mairama jajir.
“Me ya hanaku fitowa da wuri har ya gama rabon tsaraba?”
Salame taji babu dadi don ranta ya biya. Kayan kwalama irin wannan da wuya yake musu tsaraba
sai anyi matukar sa’a. Harara ta gallawa Mairama don ta tuna ya taba kawo musu agwalumar
kudun akwai zaki. Tare suka shiga rumfar Malamijo. Fankar kasa ce aka sakar masa a ka yana
shan iska kafin a hada ruwan wanka. Tabe baki yayi ya wani juyar da kai.
“Chege ‘yar kunama wai nan fushi kike yi saboda nashe zan dena ciyar daku kafin nayi tafiya?
Baffanku Kallamu ne ya fada min kuna gamawa zaku fara aikin gwamnati ku soma daukar albashi
kuna yaga min kawai kuma sai naji shiru.”
Da mamaki suke kallonsa. Ashe dalilin tijarar da yayi musu kenan a ranar harda kiransu kattin
banza ‘ya’yan Allah bani. Don kansa ya saki fuska yace yayi bincike an fada masa ashe sai sunyi
wata makarantar ta gaba da sakandire.
“Qur’anin Ubangiji ni kuma bazan sake biya muku komai ba. Ku fiddo mazajen aure na kawar
daku a sami sarari a gidan nan. Ga kannanku nan rida-rida dasu suma kullum cikin sasake ni suke.
Wannan adashin da babu alamun riba na kudin makaranta na soma gajiya”
“Yasin Malamijo yarana sai sun gama makaranta. Haka kawai wasu ma suka gama bare nawa
kuma maza”
Hularsa ya turo gaba yana kankance idanu “Ki shiga hankalinki dani Dije. Sai hegen labe kamar
kadangaruwa kullum kina manne da bango. Ina jiye miki kada watarana ki jiyowa kanki sallama”
Kwanakin da suka biyo baya gidan bai canja zani ta kowacce fuska ba sai ma tsananin da Salame
da Mairama suka kara shiga na rashin kawo mazajen aure. Malamijo har ikirarin hadasu da masu
yi masa aikin dabbobi yayi. Yaran nasa ne tubarakallah ga kyau amma fa babu farinjini….da
farinjinin dai tsayayye ne babu saboda babu mai kaunar hada iri da Malamijo saboda halinsa kaf
babu na zabe.
[7/25, 3:13 PM] Sameee💖💖: **********
B
Yawancinsu sanye suke da farar t-shirt da dogon wandon khakinsu, kadan ne da cikakkun kayan
suna bada umarni a bangarori daban daban.
Cikin jerin wadanda suke gudun da aka fi sani da 4-40 wasu matasa ne guda biyu suke magana
kasakasa don kada a ji me suke tattaunawa.
“zamu din kuwa in fara shiri tun wuri muna gama training”
Wanda yake yiwa maganar yayi gajeren murmushin gefen baki “ta fada min tana da kanwa kuwa”
Yana kallon yadda farinciki ya bayyana a kan fuskar abokin nasa ya fadada murmushinsa. Baya
bukatar wani abu da zai bata masa ranar ta yau domin burinsa bai wuce ya sami damar zuwa tadi
wurin sabuwar budurwarsa ba. Mantawa suka yi da wurin da suke suka cigaba da hirarsu sai da
suka ji tsawa daga wanda yake jagorantar training din nasu.
Daya daga cikin wakokinsu na sojoji da suka saba suka fara yi tare da sauran suna gudun har
lokacin da babban nasu ya dakatar dasu.
Su biyun ne dai masu surutu dazu suka fara dariya. Ba komai ke basu dariyar ba kuwa sai cewa da
suke idan aka kira su ladies wai sai su rinka hango kawunansu da sauran cikin kayan mata.
Captain Mustapha ya gaji da halinsu don basa ji kwata kwata gashi a karkashin platoon dinsa
suke. Sallamar sauran yayi dama duka a gajiye suke. Da yatsa ya yiwa samarin biyu alama da su
cigaba da gudun sai sun sake zagaye uku zasu tafi.
Wanda ya fi fitinar ya dube shi hankali a tashe sannan ya kame cikin daga murya yadda suka fi yin
magana da na gaba dasu ya roki alfarmar ya daga horon zuwa washegari.
Dayan Captain Mustapha ya yiwa kallon tambaya baiyi wata wata ba ya fadi uzurin abokin nasa,
wato zance da zaije wurin sabuwar budurwarsa. Murmushi yayi don ya sami damar horasu yadda
yake so.
“Zayyan Tureta”
Baki ya bude sai kuma yayi saurin rufe shi don kada ya sake yin laifi. Yana kallo aka sallami
abokin nasa don a bata masa rai tunda duka laifukan da suke aikatawa shine ja gaba. Hadir
Murtala ya faki idon Captain Mustapaha ya yi masa gwalo sannan ya bar wurin.
Ko da zai kare da rarrafe ya sani bin umarni dole ne.
Juyawa yayi a matukar gajiye zai cigaba da gudun Captain yace yaje gidansa ya jira shi. Idan ya
riga shi zuwa yana bukatar ya dawo ya ga a ina yake. Haka yake so yayi ta yi har sai ya iske shi a
gidan.
A guje ya kwasa sai bangaren gidajen sojojin yaje ya dawo Captain yana nan inda ya barshi kuma
yace ya sake tafiya. Sai da yayi haka sau hudu suna haduwa a kan hanya a wurare mabanbanta a
na karshen suka hadu a kofar gidan. Zuwa lokacin Zayyan da kyar yake motsa gabbansa amma a
haka ya kame a bayan Captain Mustapha.
Murmushi Captain din yayi masa. Yana kaunar yaron saboda kwazo da himma amma rashin jinsa
yayi yawa.
Mamaki ne ya bayyana a fuskarsa don ba haka ya zata ba. Tunaninsa kullum Captain Mustapha
shi yafi tsana duk cikin platoon dinsu. A waje ya jira shi ya fara shiga ya nemi iyalinsa su shirya
zai shigo da bako.
Wani yaro ne da zaiyi kimanin shekaru bakwai ya fito a guje yana dariya yazo gabansa ya tsaya.
“Kaine Tureta?”
“kaine kayi karyar rashin lafiya don kada kaje training? Daddy yace rannan ka sakawa wani
kunama a takalmi saboda ya shiga masallaci da takalminsa. Kuma wai ka iya karatu mai dadi
amma baka jin magana”
Baki Zayyan ya rike yana kallon yaron yana ta zuba da bashi labarin abubuwan da yake na rashin
ji tun zuwansa barrack din. Gyaran muryar Captain din suka ji yaron ya nutsu yana rike da hannun
Zayyan.
“Awwab?”
Sunkuyar da kai yaron yayi yana kara matse masa hannu suka yi murmushi tare. Bayan Captain ya
bi har cikin falon. Matarsa Hassana da ake kira Mami ta fito fuska a sake ta nuna masa wurin
zama da dan tebur a gaban kujerar wanda ta dora tray din abinci da abin sha. Wuri suka bashi yana
cin abinci Awwab na masa hira tamkar sun dade da sanin juna. Sai bayan rabin awa Captain ya
sake fitowa sanye da jallabiya irin mai gajeren hannu da fadin nan. Zayyan ya dan gyara zama ya
fusakance shi.
“Awwab ya dame ka da surutu ko? Halinku daya na fitina amma shi matsoraci ne”
Dariya Zayyan yayi yana kallon yaron da ya shiga ransa cikin kankanin lokaci. Basu dade suna
hira ba Captain ya sallame shi bayan dogon gargadi akan halayyarsa idan ba yana da burin a kore
shi tun kafin ya zama wani a cikin sojojin ba.
Har Hadir ya dawo Zayyan yana mamakin Captain Mustapha. Mutumin baya magana sosai idan ta
wuce karbar umarni da badawa. Kuma baya nuna damuwarsa akan kowa amma ace wai banda
sanin halinsa har labarinsa yake bawa iyalinsa. Hannun Hadir yaji akan kafadarsa yana jijjigawa.
“Zayyan lafiyarka kuwa? Inata magana kamar baka ji. Nace naje wurin Zainab mun daidaita
kanmu”
Cikin yanayin ko in kula yayi maganar hakan yasa Hadir taba wuyansa “zazzabi kake ko ciwon
kai? Zainab fa nace mun hada kanmu. Da naje babanta ya fito yana yi min tambayoyi karshe yace
in turo. Ina ta kokarin fahimtar dashi ba kai bane sai da ya tafi tace ta amince min itama. Nima
kuma na gani ina so….”
“Wai kasan yau a gidan Captain naci abinci har muka yi hira? Ashe haka yake da kirki mune bamu
fahimce shi ba. Kuma yana da da dan shekara bakwai abin mamaki yayi auren wuri inajin.”
Hadir ya kalli Zayyan ya tabbatar kalau yake sai ya rabu dashi. Washegari ne suka sake hirar
bayan kowa ya dawo hayyacinsa. Hadir da gaske ya nuna yana son Zainab kamar yadda ta amince
masa shi kuma Zayyan jin kansa yake ya kara girma saboda ya fahimci Captain baya kinsa. Kowa
da nasa farincikin a haka abokan suka cigaba da zaman barikin suna horowa akan matakan kariya
da tsaro. A gefe daya maganar su Hadir tayi nisa yana shirye shiryen idan sun sami hutu zaije
Kano ya sanar da iyayensa su zo su nema masa aurenta. Zayyan kuma wata nutsuwa ce take sauko
masa don ya burge Captain sannan ga shakuwa mai karfi tsakaninsa da Awwab da kannensa mata
biyu.
Kimanin watanni biyar sun shude kafin aka basu hutun sallah wanda ba wasu kwanaki bane na azo
a gani.
Duk da haka sun karba da godiya kowa yayi nasa wuri. Hadir mutumin Kano ne dan cikin gari
unguwar Madungurun. Shi kuma Zayyan dan wata karamar hukuma ne a cikin Sakkwato, wato
Tureta wadda ta zama inkiyarsa a barikin amma gidansu yana cikin garin Sakkwaton. Sun tafi gida
da murna da abinda suka samu a matsayin albashi kasancewarsu a mukami mafi karanta a cikin
sojojin Nigeria, Second Lieutenant. Su biyun da mafiya yawa daga cikinsu sun zabi shiga aikin
soja ne domin zama ababen alfahari ga kasar da basu da kamarta. Nigeria kasar da manya manyan
dattawa daga bangarori daban daban suka hadu suka hada karfi da karfe wurin kwato mata ‘yanci.
Wadannan matasan sojoji zukatansu sun tafi ga ganin sun zama kariya ga al’ummar kasarsu batare
da duba da bambancin yare, addini ko al’ada ba. Da wannan kyakkyawar manufa su Zayyan suka
baro jindadi da kwanciyar hankalin da suke samu a gaban iyayensu suka sadaukar da kuruciyarsu
don samarwa na baya kasar da zasuyi alfahari da ita.
**********
Tamkar ba soja ba tun da ya nufo gidansu yake jin faduwar gaba. Don ta shi a datse hutunsu
saboda babu abinda yake tsinta a gidan nasu da ya wuce bacin rai da bakincikin matar uba da
ya’yanta. Zayyan maraya ne ba uwa ba uba. Mahaifiyarsa mutuniyar Nijar ce ‘yar kabilar
Tamasheq a cikin Agadas, mahaifinsa ne Basakkwace. Sun hadu a yawon fataucinsa na dabino da
cukwi da yake zuwa sarowa. Soyayyar lokaci guda ce ta kamasu shi da Alheran bai kuma sha
wahala ba babanta Alh Ghousman Agali ya amince masa kasancewarsa kwastomansa da aminci ya
dade da wanzuwa a tsakaninsu. Mal Muhammadu Tureta a lokacin yana da matar aure guda daya
Jume da yara shida, maza uku mata uku kuma shima kasuwanci yana damawa dashi kafin daga
baya karayar arziki ta same shi. Wani mummunan zama akayi tsakanin Jume da Alheran. Da fari
Alheran ta kwantar da kai sosai tana bin Jume sau da kafa duk da irin wulakanci da cin kashin da
take yi mata ita da yaranta. Allah ma Ya taimaketa tana jin Hausa saboda cudanya da suke yi da
Hausawan kasar tasu.
Bayan wani lokaci tana hadiyar bacin rai ita kadai ga gorin haihuwa ta ajiye kawaicin a gefe suke
bugawa. Idan Jume ta shirya makircinta Alheran zata fidda kanta da kissar da wahala ta sanya ta
koya karfi da yaji. A shekara ta uku da aurensu Allah Ya bata ciki. Sunyi murna ba kadan ba ita da
maigidanta. Yadda yake matukar sonta haka yake son abinda yake cikin nata. Wata tara da
kwanaki kadan Allah Ya sauketa lafiya aka sami Zayyan. Kafin suyi arba’in Alh Ghousman ya
rasu. Alheran tasha kuka Mal Muhammadu ya dauketa suka tafi Nijar. A can ya barota bayan yayi
kwana goma sai da ta shefe watanni biyu domin bayan anyi ar’bain aka zo rabon gado kanin Alh
Ghousman yayi tsallan badake yace dukiyarsa ce kaf yayansa yake juyawa. Aka buga aka raya ya
dauko shaidun karya harda barazanar kai iyalan dan uwan nasa kara. Rigima gagaruma akayi
karshe suka hakura ya basu abinda yayi niyya cikin dukiyar mahaifinsu ya handame sauran. Da
wannan bakincikin ta dawo Sakkwato sai mijinta ne yake ta kokarin kwantar mata da hankali.
Zayyan na da shekara uku ta sake samun ciki. Wannan karon tana laulayi mai wahalarwa wasu
lokutan ko yatsa bata iya dagawa, amma duk da haka bata tsira daga kaidin Jume. A haka ta shiga
wata tara.
Wata asabar ta tashi da nakuda gashi Mal Muhammadu yayi sammakon fita ranar yaran duka su
ma basa nan. Tana cikin wannan yanayi ta rinka kiran Jume tana jinta tayi biris abinta. Cikin
tsananin azaba Alheran ta soma yunkurin haihuwa abinda ke cikinta kansa ne kawai ya leko Allah
Ya karbi ranta. Shima kuma wahala bata barshi ba bai jima ba ya koma. Jume ta ma manta da
cewa ta ji Alheran tana kiranta wanda tasan haihuwa ce tayi kwanciyarta tana bacci. A yashe a
kasa Mal Muhammadu ya dawo ya riski Alheran rai yayi halinsa. Yayi kukan rashinta ba kadan ba.
Jume tayi rantsuwa kwando kwando kan cewa bata ji ko da tari daga dakin Alheran ba. To dayake
abin da tayi ya dameta a rai shine ta dauki Zayyan ta rike. Riko ne dai irin na matar uba da bata
son dan kishiya amma dai duk tsiya tana kulawa dashi. A haka ya taso gatansa daya mahaifinsa.
Maikudi shine babban da namiji a gidan wanda ya kasance na uku a wurin Jume kuma tashin
hankalin gidan gabadaya.
Shekara biyu kenan da rasuwar Mal Muhammadu, Jume da iyalinta suka tattare duk wani abin
arziki suka boye. Dan wanda aka fitar shine aka raba musu tare harda Zayyan. Sauran Maikudi
yaki fito dasu tun ‘yan uwansa suna magana har sun ja bakinsu sun rufe.
Kafin ya iso gidan ya aika aka kirawo masa Zayyan suka hadu a gidan wani abokin Mal
Muhammadu wanda tare suka sansu a lokacin da suke zuwa fatauci Nijar din. Zayyan yayi murnar
ganinsa sosai saboda ba kasafai yake samun ganin dangin mahaifiyar tasa ba. A gaban abokin
Malam din Ghoumar ya dauko damin kudi ya mikawa Zayyan.
“Wannan shine kasonka na gadon Alheran. Sai da cutar ajali ta kama Baffanmu ya tuba ya dawo
mana da dukiyar mahaifinmu. A ciki an fitar da kason Alheran shine aka raba muku kai da Mal
Muhammadu bisa doron shari’a”
Kudin Zayyan ya shiga juyawa duk da bai kirga ba ya tabbatar suna da yawa. Ghoumar yayi
murmushi “kasan mahaifinmu yana da rakuma da dabbobi sosai. Sune aka sayar aka raba naku
saboda na sani babu abinda soja zaiyi da rakumi”
Dariya suka yi ya cigaba da yi musu bayanin cewa kason Mal Muhammadu da yake hannunsa
kuma zai kai gidan a lokacin za’a raba shi ne tsakanin Jume da su yaransa dukkansu. Abokin Mal
Muhammadu yace sun zabi bashi nasa a kebence ne saboda sanin halin Jume da Maikudi. Shawara
suka bashi ya tabbatar ya boye domin sun sani wannan kudi ba karamin gata zai masa ba. A nan
hannun aminin mahaifin nasa Mal Aminu ya bar kudin kafin yayi shawarar me zaiyi dasu. Daga
nan suka wuce gidansu tare.
Kamar yadda ya sanar da Zayyan haka Ghoumar ya sake yi musu bayani. Liman aka kira da wasu
malamai biyu suka kasafta kudin tsakanin Jume, ‘ya’yanta shida da Zayyan. Ana mikawa kowa
nasa Maikudi ya tashi yana kumfar baka.
“Yanzu kuke cewa Zayyanu akwai nasa kason a matsayinsa na danta. To kuma banda tsantsar
mugunta me zai sa rabon mahaifinmu a sake kasaftawa dashi?”
Ghoumar ya harare shi “rabon gado ba da ka ake yinsa ba malam. Abu ne da Allah Ya tsara da
kanShi. Zayyan yaci rabon kasancewarsa danta sannan yana da rabo a kason mahaifinsa”
Rigima ce ta kaure inda Jume da yaranta musamman Maikudi suka dage akan baza’a raba da
Zayyan ba. Da ya ga abin yaci tura yace ya yafe amma Ghoumar da Mal Aminu suka ce sam sai
ya karba.
Tsiya tsiya aka rabu babu dadi. Ghoumar rai a bace yace idan ya kuskura ya basu wani abu a
wancan kudin nasa na shi kadai bai yafe masa ba. Dariya ya bawa Zayyan ya dai yi masa nasiha
da kuma horonsa da rikon zumunci duk da yasan yanayin aikinsa abin zaiyi wuya.
Suna tafiya kuwa Jume ta kira shi dakinta suna zaune ita da Maikudi sai kumburi yake shi kadai.
“Zayyanu munyi magana da yayanka tunda kai a bariki kake rayuwa ka bashi kasonka ya cigaba
da juya maka”
Magana ce ta rainin hankali ya gode Allah da wayonsa sarai amma sai ya biye mata “to Jume
amma da na riga na barwa Kawun ne ya yi min kiwon a can Nijar”
Tsuke fuska tayi “kana nufin kai ba kudi aka baka ba?”
“Rakuma ne da dabbobi”
Maikudi ya tashi kamar zai buge shi don zuciyarsa na fada masa karya Zayyan din yake. Wani
kallo mai firgitarwa Zayyan ya watsa masa allurer soja ta motsa. Da kansa yayi lakwas ya koma
ya zauna yana kallon Jume.
“Kina kallo a gabanki yaron nan yake min kallon banza ko Jume?”
Bata kula shi ba ta sake kallon Zayyan fuska babu walwala “abinda za’ayi sai ka kawo wanda aka
baka a gabanmu ya hada ya juya muku din”
A ladabce yace “Gobe da safe in Allah Ya yarda zan je wurin Mal Aminu na karbosu.”
“Shi ka barwa don kana bakinciki da karuwata?” Maikudi yace yana kallonsa shekeke.
Bai tanka shi ba yana sauraron Jume tana fada masa gobe da sassafe yaje ya karbo kudin ya kawo
mata. Daren ranar har bacci ya kwashe shi yana mamakin wannan karfin hali da iko da aka ki dena
nuna masa duk da ya mallaki hankalinsa.
Washegari yaje wurin Mal Aminu ya fada masa yadda suka yi da shawarar da ya yanke game da
kudin. Goyon baya ya bashi suka yi sallama ya kwashi dukiyarsa sai Kano gidansu Hadir.
[7/25, 3:13 PM] Sameee💖💖: C
Washegari yaje wurin Mal Aminu ya fada masa yadda suka yi da shawarar da ya yanke game da
kudin. Goyon baya ya bashi suka yi sallama ya kwashi dukiyarsa sai Kano gidansu Hadir.
***********
“Ka koma ka fadawa wadda ta aiko ka na fada na kara ‘yata bazata tafi kwadayi gidan kowa ba.”
Cewar Malamijo yana karkada dan jikinsa duk don ya nuna da gaske fa yake.
Yaron wanda ya kasance kanin Salame da suka hada uwa ya tashi ya bar wurin Salame na zubar
hawaye. Wata tsawa Malamijo ya daka mata ta shi babu shiri jiki na bari.
“Kwalamammiya tashi ki bani wuri. Ku babu mijin babu wata sana’ar kawo dari da kwabo sai dai
aci a cika min shadda da bayan gari. Mtww Kallamu kwoi mugu, ya rinka rudata sai da na kaiku
bokon banza bokon hofi gashi ban ga komai a kasa ba”
Mairama da ke wanki a tsakar gidan ya nuna da bakinsa da yake turawa saitinta “ke kuma sai
bakin hali ba uhm ba uhmm uhmm kinbi kin tsaneni ina mahaifinki. Ko rokona abu ba kya yi. To
duk jarabar mutum dai ba’a sake uba. Nine nan dai uban naki don ko makaho ya shafaki ya
shafani yasan akwai jini. Da namiji kika fito ma sunana zan maida miki Yasin”
Wankinta ta cigaba tana yi hawaye na diga a cikin bokitin ta jiyo muryar Yadikko daga dakin girki.
“Ka dai ji kunya Malamijo, kana abu yana damunka shine ka rasa da wadda zaka rinka wannan
magana kamar wata sa’arka sai ‘yar cikinka. Rashin roko tayi min daidai. Masu yi din banda bakar
magana me kake tsinana musu bayan sun gama keta billensu”
Hularsa ya turo gaban goshi a karkace “mutum dai ya shiga taitayinsa dani don ni dadewa bazata
sa na kasa sallamar ‘yan hamayya ba”
Daidai nan Nene kanwarsa da ta kawo musu ziyara daga wani kauyen Gaya inda take aure ta idar
da sallah. Magana take da niyyar yi masa akan yadda yake yi da gidansa duk da dai ba yau farau
ba suka ji an banko kofar gidan.
Ta Madina ce babar Salame ta shigo ko sallama babu “gani nazo da kaina a bani ‘yata Malamijo
ko in nuna maka ba kai kadai aka haifa a watan tijara ba”
Tuni tsakar gidan ta kaure da ‘ya’ya da matansa an fito kallo. Salame jikinta har bari yake tana
kuka.
“Yanzu ke baki ji kunyar shigo min gida ba? Koda shike naji labarin yanzu ma zawarci kike kina
neman mafaka”
Daga murya tayi cikin fada ta nuna shi da yatsa “Ali ba tsoronka nake ji ba. A bani ‘yata biki
zamu na ‘ya’yan ‘yar uwata a Kano”
Wani karkataccen kallo ya bita da shi kafin ya kada baki yace “ke da kika lallabo cin arziki ina
ruwanki da iyalina bayan baki san zafin haihuwar ba?”
Shima sai yaji nasa jikin ya saki don kuwa yana ji da Iyalle ko a cikin dangi “ba haka nake nufi
ba. Ke Salame zo ki bi uwarki kuma sati guda na bada aka dara ban yafe ba”
Innar Salame tana tsaye tana karkada kafa daya tana jiranta ta fito. Mairama tana rakube a jikin
bango wurin da suke shanya tana jin inama ita ce zata je wurin dangin tata mahaifiyar. Sai dai ina
zata sami wannan damar. Mutanen da suke fulanin tashi basu nan basu can. Auren ma da Innarta
anyi ne kawai saboda sauke bashin da Malamijo yake bin babanta a lokacin. Hangota Innar
Salame tayi sai taji yarinyar ta bata tausayi.
“Mairama kema ko zaki bimu ne?”
Malamijo yayi wani tsalle sai gashi a gaban Mairama “wannan kuma kinyi tsararo Ta Madina,
babu inda zata je”
Iyalle da kanta tazo taja hannunta ta kaita dakinsu “hada kayanki ki bisu zanyi maganin abin”
A tsorace Mairama ta hada kayan saboda gudun kada ya hanata tafiya. Basu dade ba a dakin
Yadikko ta kwala musu kira suka tafi dakinta.
“Ni da Nene mun roka muku alfarma ya bari kuyi kwana goma. Idan kunje ku tabbatarwa da
kanku bazaku wuce lokacin da aka dibar muku ba”
Murna a wurin Mairama kai kace bikin na dangin tata mahaifiyar ne. Salame kuwa har ta gama
tsoro bai bata damar sakin jiki ba.
Da zasu tafi kashedi Malamijo ya rinka yanka musu kusan minti goma yana abu daya. Nene da
Yadikko sunyi masa shigar sauri sun kuma hade masa kai ba don haka ba Ta Madina bata isa ya
bata Salame harda karin Mairama ba.
**********
Kano ta Dabo tumbin giwa, birnin na Kano a yau yayi manyan baki daga garin Sumaila wato
Salame da Mairama. Wata unguwa da basu san sunanta ba suka wuce zuga guda ta ‘yan biki daga
Sumaila. Yadda Mairama ta saki jiki cikin mutanen sai ta baka mamaki da tausayi. Tun tasowarsu
ita dai bata taba zuwa wani wuri da zata ji dadi da sa’anninta ba sai makaranta. A can ma ba wani
sakin jiki gareta ba saboda tana ganin kowa yafi karfinsu. Gasu dai da uba mai kudi amma daga
kayan makaranta da akwati baya basu komai. Dan siyayyar nan ta provision sai dai su gani a
kwanar wasu. Shiyasa an rainasu sosai musamman Salame da sunanta ya dace da halinta.
Anyi Kamu a ranar da suka sauka da daddare inda amare aka kunshesu a daki tsakiyar ‘yan mata
kawayensu da ‘yan uwa, dangin angwayen su ka zo aka feshesu da turare.
Washegari kuwa lanchin (luncheon) za’ayi a filin wani katon gida mallakar kanin baban amaren
biyu.
Salame ta sami kaya kala biyar sababbi, biyu daga yayar innarta uwar amare sai uku daga Ta
Madinan. Guda ta cire a ciki ta baiwa Mairama tace ta saka kada ta fita daban tunda su dai ba
wasu suturun arziki na shiga taro garesu ba. Mairama sai murna da godiya ta sanya atampar da
akayi mata dinkin riga da zani buba anyiwa rigar cin baki da irin lace dinnan na adon kaya a wuya
da hannaye. Tayi kyau abinta gwanin sha’awa haka itama Salamen. Motoci bus bus ne aka haya
suka rinka kwasarsu aka kaisu wurin bikin.
Salame tana manne da kanwarta duk da cewa dai tana sakin jiki da ‘yan uwanta suna hira.
Teburinsu su bakwai ne da yake a zagaye yake suna fuskantar juna ana ta tsokanar wata cikinsu da
tayi saurayi daidai kofar shigarsu gidan. Karaf idanun Salame suka sauka akan Zayyan ya nisa
suna magana mai matukar mahimmanci da Hadir. Daya daga cikin angwayen dan uwa ne ga Hadir
din.
Iyayensu maza ciki daya suka fito. Shiyasa da Zayyan ya iso Kano aka sanya shi cikin abokan
ango. Cinikin fili suka gama kafin zuwansu nan a unguwar gandun albasa. Shi dai Zayyan ya ga
wurin babu gidaje sosai amma dillalin yana ta cika masa baki cewa nan gaba kadan unguwar zata
hade harma a rasa filin saidawa. Shima da yake ba mazauni ba sai ya amince ya biya kudi bisa
shawarar Hadir. Zancen gini kuma a hankali zasu yi tunda har yanzu ko rabin kudin da aka bashi
bai taba ba.
Takardun filin ne kwafi biyu da sa hannayensu ya mikawa Hadir daya yace gata nan ya ajiye masa
shi kuma zai aje daya a wurinsa. Sai da suka gama komai duk motsinsa akan idon Salame sannan
su ka koma cikin samari ‘yan uwansu. Ba karamin tafiya yayi da imanin Salame ba lokaci guda
taji sonsa ya game zuciyarta.
Mairama kuwa an sami sake hira tayi hira an kawo abinci kowa plate dinta shake da jallof din
shinkafa da yankan naman sa da aka soya sai salad, tumatir da albasa. Wayyo dadi jikinta har
tsuma yake kuma wai aka kirga su aka sake ajiye musu ledar tsire ga kuma lemon kwalba. Kar
kaso ka ga idanun Mairama hankalinta yayi kwano na Salame kuma yayi kan Zayyan da bai san
da zamanta a wurin ba.
Police band suna wakarsu amma kusan kowa abinci yake ci babu ‘yan rawa. Kwalbar fanta
chapman Mairama ta faki ido ta daga tana kwankwada asalin dadi da sanyi yana ratsata ta manta
da kunyar idanun jama’a. Bata samu ta sauke kwalbar mai 35cl ba sai da ta shanye shi tas. Daga
lokacin da ta soma waige ta tabbatar babu mai kallonta har zuwa sanda ta ajiye kwalbar Zayyan
yana gani. Baki ya rike yana kallon yadda ko da ta shanye sai da ta sake daga kwalbar ta
kwakkwafeta a bakinta. Kasa cin nasa abincin yayi komai tayi sai yaji ya burge shi shi kadai ya
rinka murmushi. Teburin kusa da nasu Mairama ne duka matan dama su uku ne su ka tashi a tare.
Mairama tana ji suna cewa sallama zasu yiwa amaren su tafi. Tana ganin sun bace cikin jama ’a ta
wayance ta tashi da kwalbar lemonta ta ajiye a wurin ta dauki wata mirinda da ko rabinta ba ’a sha
ba. Plate din nasu ma basu wani ci sosai ba ga nama sun bari. Kamar ta dauka shima sai dai ta
hakura lemon yafi mahimmaci a gareta.[7/25, 3:13 PM] Sameee💖💖: D
Banda wanda ta dauka sai da ta dan kurbi na kusa dashi sannan ta juya da sauri da taji ana kiran
sunanta.
Hadir ya tabo Zayyan da yake kyakyata dariya shi kadai da ya hango Mairama tana zaro idanu.
Matan da suka bar teburin ne suka dawo daya ta soma cigiyar lemon da ta bari. Mairama tayi tsit
don kuwa saura kadan ma ta shanye mirindar.
Idanu ya lumshe yana kallon kyakkyawar bafulatanar ta tsure karshe ta kuma rungume kwalbar ta
boye cikin lullubinta.
“Mata nayi”
Hadir ya tura kujera baya da sauri “nuna min ita muje mu tsarata wallahi”
Zayyan ya mike da sauri “naki din, kai fa satar budurwa kake yi”
Sauran mazan wurin suka sa dariya shi kuma ya kwashe lemuka uku da ba’a bude ba yayi gaba.
Salame tana ganin ya nufosu ta tattaro dukkan nutsuwarta tana murmushi don tun dazu suke hada
ido yana murmushi a zatonta ita yake yiwa yayin da hankalinsa kacokan yana kan Mairama ne.
Sallama yayi musu matan teburin gefen ana ta masifar rashin ganin lemo ya mika musu biyu sanna
ya dubi Mairama da tsoro ya hanata motsi ya mika mata chapman irin wadda ta fara sha. Dan
rausayo kai yayi ya duku wurin kanta.
“Kanwata ga wannan ki kara”
Sai lokacin ta dena jin mitar wadancan matan ta tsuke baki batare da ta juya ba
“Haka ma zaki ce? To ki shirya kuwa don zan tona” yace yana rage murya sosai daidai kunnenta.
A firgice ta waiga idanunta suka sauka cikin nashi. Ko ma me tayi niyar cewa makalewa yayi a
wuyanta ta sami kanta da manta a ina ma take na ‘yan dakiku. Lallausan murmushi ya sakar mata
wanda ya sake fito da kyaunsa da cikar sa.
“Muje can na fada miki me da me na gani” ya nuna can jikin katanga wurin wata katuwar bishiyar
darbejiya.
Ko dogon nazari bata tsaya yi ba ta bi bayansa kuwa don ta gama tsorata kaddai ace ya ga lokacin
da ta dauke musu lemon. Wani mugun daci ne ya taso ya tokare wuyan Salame har suka isa bakin
bishiyar tana binsu da kallo. Me yake shirin faruwa tsakanin kanwarta da mutumin da take jin bata
taba son wani abu makamancinsa ba a rayuwarta. Kallon da yake yiwa Mairama kadai ya isheta
amsa. Sauran ‘yan mata kuwa sai shewa itama zasu kwana suna tsokanarta kenan.
Suna isa wurin bishiyar yace “da farko dai sunana Zayyan, ni soja ne”
Idanunta suka yi kwalkwal da hawaye suna barazanar saukowa. Murya na rawa ta fito da kwalbar
da ta boye cikin mayafinta “me yayi zafi ni ‘yasu. Daga shan lemo sai dauko sojoji. Ni wallahi
nayi zaton sun tashi kenan. Don Allah kuyi hakuri kada ka kamani” tace tana kallon Hadir da ya
iso inda suke.
Maganarta dariya ta bashi ya mikawa abokinsa hannu da nufin gabatar dashi a gareta “Zayyan
Tureta…”
Wani kallo ta watsa masa tsoron yayi nasa wuri ta yatsina fuska za ta gwada musu tsiwarta “ya
tureni? To Bismillah dan halak ka fasa. Mutum ya tabani ba hakura zanyi ba”
Kasa cewa komai suka yi sai dariyar da suke yi mata tana karkada hannuwa. A ranta tana jin
tsoronsu zaratan samari irin haka amma kuma bata so ta basu damar cutar da ita.
“Kinga ‘yan mata sunansa Zayyan Muhammad Tureta ba tuureta na hankadewa ba, garinsu ne a
Sakkwato”
Kallonsa tayi na dan lokaci tana son yin nazari shin kamata zaiyi ko kuwa dai wani abin ne daban.
Yadda yayi maganar yana kasha mata ido ya sanya hankalinta ya kwanta itama harda dariya.
Kwatancen gidansu ya nema daga gareta da bayanin kansa sannan yace duk da karancin lokaci
yana son ganawa da mahifinta domin ya nemi aurenta. Kunya sosai ta lullube Mairama don itama
a ‘yar hirar tasu har ya shige zuciyarta. Ta fada masa gidan da suke yanzu da kuma kwatancen
gidansu yace zai zo da daddare su sake fahimtar juna.
Kusan da gudu-gudu ta koma teburinsu ‘yan matan suka soma zuba mata tambayoyi. Jiki na rawa
ta fada jikin Salame tana dariya.
Wani murmushin yake Salame tayi a ranta tana nadamar tahowarsu da Mairama. Ita kuwa dadi ya
cikata ta fada mata yadda suka yi.
Bata fahimta ba shiyasa tayi murmushi “gaskiya tawa ce, yace zai tambayi gidan da muke sai yazo
anjima. Ai tare zamu fito ki ganshi da kyau. Hmmm Hausarsa sai ta baki dariya, sakkwatanci
yake”
Maza uku ne a wurin. Zayyan, Hadir sai kuma wani abokin Hadir din tun kuruciya layin gidansu
ma daya Salisu. Tunda suka fito shi kuma ya kyallo Salame shima tasa zuciyar ta lula kogin
kauna.
Gaisawa suka yi a mutumce Hadir ya sake yi musu bayanin waye Zayyan da manufarsa akan
Mairama. Zuciyar Salame kamar ta fashe don bakinciki a ganinta cin fuska ne ma suke mata.
Bayan an gama bayanin Salisu yace shima fa yaga matar aure nan dai aka hau gabatar da kai.
Salame ko kadan bata yi farinciki ba. Salisu dan kasuwa ne a kantin kwari tun da kuruciya yake da
zafin nema bata sani ba yana da arziki sosai.
Mairama da Zayyan sun rabu akan cewa jibi kafin ya bar gari zai sake zuwa don a hada shi da mai
yi masa rakiya Sumaila wurin Malamijo. Idan ya tafi zai gabatar da maganar ga magabatansa don
bashi da burin a ja lokaci. Salisu ne dai bai wani sami hadin kan Salame ba hanlinta yana kan hirar
su Zayyan yace Mairama ta taya shi neman fada.
Bayan sun tafi a cikin gidan ana ta tsokanar Mairama ta kuwa biye musu tana yi tana sako yayarta
aciki. Salame kunci da bacin rai ya sanya ta fashe da kuka mai cin rai. Shiru kowa yayi Mairama
tayi juyin duniya taki cewa komai. Ta Madina aka sanarwa tazo itama tana tambayarta sai cewa
tayi wai gida take son komawa.
Ashar Ta Madina ta kunduma mata “ke har wani gida gareku a Sumailan kike son komawa?”
Fuskarta har ta soma kumbura tace “ni dai tafiya zanyi tsoro nake kada mu koma Malamijo yayi
fada don baiso muka zo ba”
Ba wani abu ke cinta ba face zallar kishi da kanwarta. A ganinta idan tasa su ka koma gida Zayyan
bazai san gidansu ba bare yabi Mairama shikenan kowa ya rasa.
Abu kamar wasa Salame ta tubure sosai. Ran Ta Madina a bace tace gobe da sassafe zata sakasu a
mota kuma ta kwana da sanin cewa bazata sake neman daukota ba, idan Malamijo zai cinyeta ne a
gidansa babu ruwanta. Dayake ido ya rufe maganar ta inda ta shiga ta nan ta fice.
Mairama a daren bata damu ba sai da ta tuna Zayyan yace zai zo hankalinta ya tashi. Har daki ta
kira Salamen ta roketa alfamar ta bari su sake kwana. Kallon da bata taba yi mata ba ta jefeta dashi
wanda ya haddasawa Mairama tuhumar kanta ko ta bata mata rai ne.
“Kinzo kin wani shige cikin danginmu sai wani cusa kai kike yi. Dadin abin dai duk tsiyar mutum
da danginsa na jini zaiyi tinkaho. Mu dai munyi sa’a muna da dangin uwa”
Mairama sai taji ranta ya baci itama “nima ba daga sama tawa uwar ta fado ba. Idan don nazo
bikin danginku ne Allah Ya baki hakuri bazan kara ba”
Kasa bata amsa tayi ranta a jagule ta karasa hada kayanta ta dauko wanda Salamen ta bata na taron
da akayi da rana ta saka ta mika mata. Bata damu ba ta karbe duk da a farko niyarta ta bar mata
kyauta ne.
Babu wanda ya aikesu bare yayi murnar dawowarsu gidan. Basu rufa awa guda ba ma Dije ta taso
Mairama tazo tayi mata aikin fura da take yi ta sayarwa saboda ciyar da yaranta. Tana tsaka da
aikin Inno ta kira Salame ita kuma aka bata surfen masara. Haka suka yi ta aikin babu mai yiwa
‘yar uwarta magana. Mairama ke satar kallon Salame cike da damuwa, ita kuma da sun hada ido
sai ta galla mata harara.
Washegari wuraren goma na safe aka aiko wani yaro wurin Malamijo. Dan aiken da ne ga wanda
yake taya shi aikin kula da dabbobinsa. Yaron yana haki don gudu yayi zuwa gidan ya sanar dashi
wani katon san sa yana neman kasawa ya bada izini a yanka shi. Tamkar an soki kahon zuciyarsa
ya zabura zai bi bayan yaron sai ya tuna babu takalmi a kafarsa ya koma ciki da sauri.
Lokacin da ake sanar dashi san ya kasa dan sa daya na wajen Inno mai suna Habibu yana ji ya
juya cikin gidan kafin ya ankara da tsayuwarsa. Inno tana gaban murhu za ta hada wutar girki yazo
yana haki.
“Inno yau kece a turaka?” ya tambaya babu alamun damuwa a fuskarsa sai ma farinciki. Yaran
gidan musamman masu uwaye sun san ranakun girkin iyayen nasu saboda abincinsu yana fin na
sauran ranakun auki.
“Idan bani bace uban me zanyi a nan da zafin ranar nan kwal a kaina”
Dariya ya saki har wawulunsa na gaba su ka bayyana “san Malamijo ne ya kasa Inno yau akwai
cin nama.”
Kamar wadda aka bawa kujerar hajji Inno ta saki dariyar farinciki ita ma. Su da nama sai dabba ta
kasa. Gashi ya fada girkinta sai yadda tayi kenan. Bakin dan nata ta toshe lokacin da yake cewa ta
cire musu manyan tsoka idan an soya irin na wancan karon.
Tsaf Malamijo ya gama jin me suke cewa ya shiga tafa hannuwa “ba amin ba, billahillazi baa min
ba. Kuji min ‘yan bakinciki masu fatan tsiya. Idan ba kun jawowa kowa wallahi mahauta zan
saidawa bazaku ci ba”
Yaron sai ya kama kuka nan da nan iyalan gidan su ka cika tsakar gidan. Don kada ayi biyu babu
Inno ta fada musu sa ne ya kasa kuma wai baza’a kawo musu kamar yadda aka saba ba. Iyaye
mata suka hau jimami yaransu harda masu dan wayo suna kuka. Kuka na gaske suke ana rokonsa
ya taimaka. Shi abin nasu tsoro ya bashi ma ya ja baya ya manne a jikin bango yan raba idanu.
“La-e-lafi qureshin wallahi idan ku mayu ne Allah Ya fiku” yace yana tottofe na kusa dashi “ko
ku matsa ko na dauko sarkin mayu yazo ya kama min ku kafin ku karasa ni. Haba ko da naji,
kullum zukewa nake jiki babu wata mamora kamar ba Ali mai garken dabbobi ba”
Magana yake yana kallon jikinsa yadda yake sai tsayi da uwar rama ya kula Mairama tayi
murmushi abinda bata saba ba. Tun haduwarta da Zayyan take jin zuciyarta fes babu wannan
mugun kuncin na gidansu. Mamaki sosai ta baiwa Malamijo don kullum ya tarasu yana irin
wannan hade rai take abinta bata kuka bata bada hakuri kuma. Sai yaji wani dan dadi a ransa haka
kawai.
Yadikko ce ta bashi amsar maganarsa “ta ina zaka yi kiba ka tara hakkin mutane sun fi talatin a
wuyanka”
“Ta, ta, ta uwar zance nasan sai kin tanka. Indai sa ne zaku ci amma yau akan idona za’ayi komai
har rabawar don bana so ake kwarar wasu. ‘Ya’ya dai duka nawa ne”
Gidan tuni ya kaure da ihun murna ya shige ya sako silifas zai tafi gonar kafin su ma wurin aikin
naman su kwashi rabonsu su boye.
Yana fitowa yayi kicibus da sojoji biyu a kofar gidan da wani yasha shadda sai kyalli take na
sabunta. Su kuwa sojojin ya ganesu ne saboda kayan jikinsu wanda suka yi matukar kyau a
cikinsu. Sai kuma dan Ta Madina wato kanin Salame da ta aiko rannan. Gaban Malamijo yayi
wata irin faduwa baki ya soma rawa.
Ko gaisuwar da suke masa bai iya amsawa ba ya koma ciki jikinsa na bari.
“Ashe ba banza ba dazu kike murmushi abinda baki saba ba, wato kunje Kano idon ku ya bude
shine kika kai karata wurin hakuma ko?”
Dago kai tayi da sauri Salame ma ta fito daga dakinsu don maganarsa ta hasko mata su waye.
Kenan batayi sa’ar rabasu ba.
Shi kuwa a harzuke yake matuka ya shiga nuna su da yatsa “nasan kece mai bakar zuciya ke ki ka
ingiza Salame ku ka kai karar, amma ku sani babu wanda zai kamani akanku, biki ne na barku
kunje kuma san nan nace za’a kawo muku ku ci me ya rage”
Kana ganinsa kasan a tsorace yake sauran matansa su ma duk sun tsure. Yadikko ce tayi karfin
halin riko hannun Mairama
Murmushi tayi tare da sunkuyar da kanta Yadikko ta kuma maimaita tambayar. Ganin ta ki
magana sai ta sake cewa “kodai surukai ne daga Kanon?”
A guje Mairama ta yi hanyar dakinsu cike da kunya. Yadikko ta fadada murmushinta tana yiwa
Malamijo da yayi saroro a wurin bayani. Sai gashi yana wani kasaitaccen murmushi yana kada
kai.
“O’oh kaga su Mairama Daso ‘yar Ma’aikin Allah. Ashe dai da farinjinin ta ban sani ba. Baku ga
sojojin ba fa gwanin ban sha’awa. Ganinsu kadai ya sani shauki na tono lokacin da muka fara
zuwa gwaji Jaji a can kasar Kaduna…”
Hajjo ta tuntsire da dariyar rainin wayo don tasan kawai sakin kwai zaiyi duk labaransa bata taba
ji yace yaje barikin sojoji ba.
Hankalinsa ya koma ga Salame yana tambayarta ko ita ma da bakonta. Ciwon da yake cin ranta
bai bari ita ta gwada kunyar ba kawai ta hade rai ta koma daki.
Mairama ya kwalawa kira ita ta bashi tabbacin akwai wanda yake son ‘yar uwar ta ta. Sai ga
Malamijo baki yaki rufowa “Ka ga Ummassalama abu yayi kyau. Allah dai Yasa mai shaddar ne
naki don bazaki iya da hakuma ba, wannan sai ‘yar kunama. Bari dai na koma wajen bakin”
Su na tsaye ya barsu da kokonta sai gashi ya dawo da fara’arsa har babbar riga ya doro akan kayan
jikinsa.
Tabarma aka shimfida musu a zure shi kuma yana daga kan wata kujerar karfe ya baza riga don
ya cika ido. Gaishe shi suka sake yi Hadir yayi masa bayanin komai game da zuwansu da bukatar
idan ‘yan matan sun amince ayi komai da wuri musamman saboda su basa samun damar fitowa
daga barikin suyi dogowar tafiya batare da dalili ba. Yawonsu baya wuce cikin gari kada a nemesu
sunyi nisa.
“Ku kwantar da hankalinku Kano dai ba bakuwata bace sannan a can birnin Shehun ma akwai
wanda na sani don na taba zuwa garin. Kunsan wani mai kilishi a hanyar Dange shuni? Yana nan
wani dan firit haka yace min asalinsa ma mutumin Zaria ne. Kila zai iya tuna ni don naji dadin
kilishinsa na sayi da yawa lokacin…”
Duk sun dauka wata alaka zai ce tsakaninsu ko karin bayani sai suka ji zancen yakare, Zayyan
sarkin dariya tunda yace mai kilishi dan firit ya daga kai ya kalli Malamijo sai kawai ya kunshe
dariyarsa kada ya jawowa kansa. Sun ji dadi ya ce ya basu yaran sai su fara shiri. Tashi yayi yace
su jira zai turo su ko gaisawa suyi tunda su Zayyan a ranar zasu koma Sakkwato.
Kusan a shirye Mairama take kira kawai take jira yayin da Salame ta nade akan katifa wai zazzabi
ke damunta. Mairama tayi mata sannu ta bi bayan kanwarta da ta sanar da ita Malamijo yace taje
wurin bakin.
Sai da tazo bakin kofar da zata sa da ta da zauren da suke, kunya ta hanata shiga. Da Hadir ya
hangota, ya fara zolayarta cewa ko sune bata son gani bari su basu wuri. Kai a kasa ta rufe fuska ta
shiga ta gaishesu. Salisu yana cigiyar gimbiya Salame ta sanar masa bata da lafiya. Yanayin
fuskarsa ya nuna baiji dadi ba.
“Ki dai taimaka min naga alama so take ta saka min ciwon zuciya”
Zayyan da Hadir ne suke kwantar masa da hankali har suka fita don a bar Zayyan suyi magana da
Mairama.
“Mairam tafiya ba sallama ko?”
“Nayi tunda zuwan nawa ya haifar da da mai ido gashi an bani ke”
Wata matsananciyar kunya ce ta shigeta ta sake dukar da kai. Shima yasan a hanya suke shiyasa
bai ja ta sosai ba yace zaiyi kokarin dawowa kafin magabantansa su zo. Yau a hanya suke suna
sauri. Wata leda ya mika mata, yayi yayi, taki karba sai ya tashi ya barta a wurin. Iyakarta bakin
kofa tayi musu sallama da kyakkyawar addu’ar tafiya.
[7/25, 3:13 PM] Sameee💖💖: E
*TUN RAN GINI…*
Tana shiga daki ta sami Salame a tsaye sai safa da marwa take saboda zulumi. Yanzu shikenan
abinda take so sai ta hakura dashi saboda Mairama. Gaskiya bazata iya ba domin son da take masa
ba kadan bane. Kuma ma dai ai ita ce ya kamata yaso tunda danginta ne, Mairama kara kawai
akayi mata. Ta nisa a cikin tunani taji Mairama tana mata magana.
Hade rai tayi ta koma ta zauna akan tabarma “ke yanzu banda rashin kamun kai me ya kaiki
dadewa wurin saurayi daga zuwansa na farko? Mutumin da ba wani saninsa ki ka yi ba don iya
zubar da aji.”
Kwarai Mairama tayi mamakin kalaman Salame don a iya sani da kuma shaidar da za’ayi mata a
gidan tafi kowa saukin kai da dadin mu’amala. To amma meye ya kawo wannan zantuka haka?
Kasa daurewa Mairama tayi ta koma bakin katifarsu ta zauna ita ma.
“Adda Salame wai me nayi miki ne haka don Allah? Kwana biyu kenan sai kiyi ta harara ta kina
fada min maganganu”
“Ji rainin wayo ki min kwace kizo kina min dadin baki” tace a ranta amma a zahiri sai ta daure
tayi mumushi “gani nayi daga yin saurayi kin haukace a kansa ko tunanin idan kin bar gidan nan
da wa zan zauna ba kya yi?”
Jikinta sai yayi sanyi ta sake matsowa kusa da Salamen “kai Adda me ya kaiki wannan tunanin?
Shine kike ta fushi…ohh ni wallahi duk kin tayar min da hankali na damu. Kema ga Salisu ba sai
mu bar gidan tare ba.”
Turo baki Salame tayi “dena min zancensa wallahi baiyi min ba, ke dai kinyi sa’ar Zayyan kawai
kina murna”
Rarrashinta Mairama ta soma yi a zatonta da gaske tunanin rabuwarsu a gaba ke damunta. Sauran
kannensu mata babu sa’anninsu, maza biyar ne su ke binsu. Koda Salisu ta shiga yi tare da bata
sakon gaisuwarsa ta yi tsaki da gaske dai bata son zancensa.
“To na bar zancen nasa Allah Ya kawo wanda ya fishi alkhairi. Shima yace na gaisheki da jiki
kuwa”
“Shi wa?” Salame ta fada cikin gatsali wanda Mairama duk ta sawa ranta duk a cikin rashin son
su rabu ne.
Tambayar kunya ta bata ta soma inda-inda ba ta san da me za ta kira shi ba. Sunansa dai da wahala
ta iya fada a yadda take matukar jin nauyinsa.
Zungurinta Salame tayi da kafa tana mata wani irin kallo mai tattare da kishin da ake kokarin
sakayawa.
“Zayyan kike nufi?”
Kai ta gyada ga mamakinta sai ta ga fuskar Salame ta washe sosai tana murmushi “ashe bai manta
ni ba. Me yace? Ina nufin da yaya ya baki sakon? Ki gaishe da Salame yace ko me?”
Dadi taji ganin sauyi a tare da yayarta ta kuwa biye mata tana fada mata yadda yace da zai bada
sakon gaisuwar. Har dare ranar Salame motsi kadan sai ta tuna wai Zayyan yace a gaisheta, sai taji
wani dadi yana ratsata.
**********
Matafiya sun sauka a cikin garin Sakkwato lafiya. Ba wata gajiya su ka yi ba don sun dade da fara
sabawa da wahala suna jure mata sosai. Gidansu Zayyan su ka wuce zai dauki kayansa da ya bari
sai su koma barrack dinsu.
Gidan yanzu dama daga Jume sai Maikudi, Rayyan da Badaru wadanda sune Zayyan yake bi
dukkansu babu mai aure. Matan kuwa Fiddausi, Mubaraka da Hafsatu duk suna dakunansu.
Kwasar tuwo Jume take yi Badaru yana zaune akan turmi da ya kifa sai Maikudi kwance a kofar
daki yana faman firfita su ka ji sallamar Zayyan din.
Babu wanda ya amsa masa cikinsu sai harara da suke binsa da ita. Dakinsa ya wuce kai tsaye ya
dauko jakar kayansa a ransa yana bakincikin halayyar ‘yan uwan nasa. Ba haka ya bar jakar ba
alamu sun nuna an bude an yamutsa masa kaya wurin neman abin da yake zaton kudi ne, sai dai
ko kwandala bai bari a ciki ba. Ratayo abarsa ya yi ya fito ya kulle dakin.
“Sai Allah Ya sake dawo damu ni zan wuce” yace daga tsaye yana dan rissinawa Jume.
Maikudi ya tashi zumbur yana kallonsa, ita ma Jume ta juyo da kujerar da take zaune a kai yadda
za ta fuskance shi da kyau.
“Zayyanu ni zaka wulakanta a gidan nan? In baka umarni saboda ba uwarka bace sai kasa kafa ka
take. Kwana nawa ina sawa a dubo ko gidan Aminun ka makale babu kai babu labari sai yau.
Shine har kake da bakin cewa zaka wuce.”
Baya son ya kai ga yi mata abinda zai zo yana nadama nan gaba ga darajarta na matsayin wadda ta
rike shi kuma matar babansa, da idan ya fada mata wata maganar ko hanyar da ya bi bazata so ta
sake bi ba.
Maikudi ya dawo kusa dashi ya miko hannu kamar wanda ya bawa ajiya “ina kudin da tace ka
karbo a wurin wancan tsohon munafukin?”
“Kaga kafin ka fara dogon surutu bani kudin ka wuce bana son rigima da al’murun nan” Jume ta
fada tana kara tamke fuska.
Dago idanu yayi ya zube mata a kanta sai gashi jikinta ya yi lakwas. Rayyan da Badaru ma kowa
ya sha jinin jikinsa. Maikudi ne kawai hankalinsa bai kai wurin ba.
“Jume!”
“Kudi dai gadona ne ni kadai kamar yadda a gabana aka bawa kowa nasa...”
“Idan na fahinceka Zayyanu kudin ne ba za ka bani ba saboda ban isa in nemi abu a wurinka in
samu ba?”
Tausayi ta bashi yadda ta hakikance akan rashin gaskiyarta bata ko tunani sai son bukatarta ta
biya. Hannu ya zura cikin aljihun wandonsa ya zaro naira dari ‘yan ashirin guda biyar ya mika
mata.
“Ga wannan ku kara cefane” yace cike da nutsuwa, bai kuma jira cewarta ba ya fice waje inda
Hadir yake jiransa.
Yana fita Maikudi ya warce kudin a hannunta yana jaddada mata tasan yadda zata yi ta karbo
musu ragowar idan ba haka ba shine zaiyi ajalin Zayyanu sai ya ga ta inda zaiyi amfani da kudin.
“Banza shashasha to sai ka dawo, kafin kayi ajalin nasa shi zaiyi naka. Har mamaki kake bani
yadda kake manta zuciyar Zayyanu da kuma kasancewara soja. Yanzu idan yasa aka kamaka duk
duniya bana jin kana da wanda zai fito da kai. Nima kaina tsoronsa nake ji dan jakar uba, daurewa
kawai nake ina masa barazana. Amma muje zuwa sai na dawo dashi tafin hannuna. Uwarsa ma
mai suna kamar na tsuntsaye bata iya karawa dani ba”
**********
Sati uku da dawowarsu a tsukun lokacin iyayen Hadir sun zo daga Kano an daidaita maganar
aurensa da Zainab. Kullum ya dawo ya ishi Zayyan da labarin hirarsu ko maganar biki. Ranar da
ya bishi kuwa yadda ya kula suna son juna musamman Zainab da duniya bata ganin kowa da gashi
sai Hadir sai yaji muguwar kewar Mairama.
Ranar lahadi ya samu da babu training sosai ya fita yaje ya sanar da Mal Aminu da mutum biyu
cikin ‘yan uwan mahaifinsa game da auren da yake nema. Sunyi farinciki da alkawarin bayan ya
koma Kanon ya fadawa mahaifin yarinyar zasu je bayan sati daya da zuwan nasa. Godiya yayi
musu ya nemi matar Mal Aminu mai suna Gwaggo Ladi matar da ta maye masa gurbin uwa wurin
kulawa da bashi abinci da sauran abubuwa lokacin da kowa ya gane gashin kuman da Jume take yi
masa. Kudade ya bata da yake so a fara siyayyar kayan aure ta yadda idan zasu tafi zasu je ne a
shirye saboda nisa.
[7/25, 3:14 PM] Sameee💖💖: F
Sai da ya nemi izinin fita na kwana biyar, da kyar kuwa bukatarsa ta biya saboda ba kasafai ake
son suna yin nesa da barikin ba. Ranar da zai tafi sai da ya bi ya sallama da Captain Mustapha.
Yanzu alakarsu tamkar wa da kani ga kuma yaransa sun mayar da Zayyan uba na biyu. Shi
Captain Mustapha asalinsa da Katsina ne daga shi har matarsa don auren gida ma su ka yi.
Asubancin fita yayi ya shiga cikin gari gidajen dangin Mal Muhammadu. Daga can ya wuce tasha
sai Kano.
Yayi sa’a masu kilishi sun fito ya sayawa Malamijo. Shi dai a dan zamansu na farko bai hango
komai a tattare da shi ba sai barkwanci.
Kwanakin da suka gabata Salame ta dami Mairama wai me ya hana Zayyan dawowa saboda
Salisu ya matsa lamba kuma Malamijo ya riga ya bashi. Ganin akwai kudi yaron ya kara shiga
ransa. Salame so take ta tabbatar Zayyan bazai dawo ba sai ta amince masa ko babu komai zata
huta. A haka tana tsoron saurin amincewa ya dawo a bashi Mairama ita kuma ta rasa. Akwai ranar
da ta tambayi Mairaman ko ta fadawa Zayyan yanayin gidansu.
“Kinsan boye-boyen babu amfani gara yasan wa zai aura kada Malamijo ya nuna masa hali”
Bata rai Mairama tayi “yau da kanki Adda Salame kike cewa Malamijo zai nuna hali? Ni dai
soyayya bazata sa na kwashe sirrin gidanmu na kaiwa saurayi ba. Idan bai aureni ba shikenan ya
gama sanin komai nawa. Kuma ko yaya Malamijo yake ai babanmu ne dole mu so a mutunta shi”
Waskewa Salame tayi amma a ranta tana ganin ta sami hanyar rabasu “irin wannan sharhi ba wani
abu nake nufi ba, abar maganr dai”
Yau kamar daga sama sai ga dan aike wai ana sallama da Mairama inji Zayyan.
Wanka take yi lokacin ta gama aikin fura Salame ce taji sakon. Jikinta har bari yake tsabagen
murna ta fada dakinsu da sauri. Kaya ta sauya da sauri ta shafa hoda harda janbaki ta sako daya
daga cikin kayan da Ta Madina ta dinka mata. Komai da azama take kada Mairama ta fito ta
sameta. Tazo fita ta koma ta cire mukullin sif din kayansu bayan ta kwashe duk wani kayan sawa
ta saka a ciki ta jefa a karkashin sif din ta fita tana dariyar mugunta.
Bata yiwa kowa sallama ba don basa tsakar gidan ta fice zaure. Dama niyarta da an tambayeta ina
zuwa tace wurin Innarta zata je.
Kamshin turare wanda Salisu ya kawo mata zuwansa na karshe ya fara ji kafin ya ganta. Ta
gumbuda turaren sosai kuwa a ransa yaji dadi ba Mairamansa bace take wannan aika-aikan. Fuska
ya saki yana mata murmushi. Ta sunkuyar da kai tana ‘yar dariya don jin kanta take kamar yau
take sallah saboda ganin Zayyan.
Wani abu taji ya soki zuciyarta, wato ku sunanta bai rike ba. Bata nuna damuwar a fuska ba sai ma
wani kasha murya da ta tsiri yi “Salame dai ko, baka ma rike sunana ba saboda baka damu dani
ba”
Banbarakwai yaji zancen nata “Afuwan kada ki fadawa Mairama tace ta fasa na yiwa Addarta ko
ince Addarmu laifi”
“Ba wani abu ai, ita ma bata soma fada ba yadda ta matsu tayi auren nan. Allah Ya dube mu, masu
gudunmu saboda Malamijo zasu sha kunya”
Zayyan mutum ne mai saurin dago ina mutum ya dosa idan suna magana, yanzu ma tuni ya
fahimci akwai abinda Salame take son fada masa tun hirar bata tsawaita ba.
Hannu ta dora akan bakinta kamar gaske tana ware idanu “ba dai Mairama bata yi maka bayani
ba? Irin haka ai da wuri ake fada saboda toshe matsala don kada kaji a waje. Idan na koma zan
fada mata gara ta sanar da kai komai da wuri zai fi. Sai ka danyi hakuri ta gama aikin furar
sayarwa ne ta shiga wanka”
Wai shi za ta jawa rai, kawar da kai yayi abinsa yana kallon waje. Haka nan bata yi masa ba tun
haduwarsu ta farko a gidan Gwaggonta da akayi bikin yaranta. Sai tayi ta wani kifi-kifi da idanu
amma sau goma idan zai dago kai sai sun hada ido.
Yanzu da ta ji bashi da niyar tambaya sai ta sake salo. Jan hanci yaji tana yi alamun tana kuka.
Dawo da hankalinsa yayi gareta da sauri.
“Ya dai?”
Goge hawayen da ko digonsu babu tayi sannan ta dan tabe baki duk yana kallonta “gara kawai na
fada maka don abin zai yiwa Mairama nauyi”
Halin Malamijo kaf da yanayin zamantakewar gidansu ta kwashe masa. Hatta dangin mahaifiyar
Mairama sai da ta kwancewa zani. Jinjina kai kawai yake yi yana kara tausayin Mairama sosai.
Yanayin rayuwarta kusan daya da tashi wato dukkansu basa jindadi a gidan iyayensu.
Salame sai ta dauki sauyin yanayinsa a matsayin tarkonta ne ya fara kamu ta dan murmusa “nasan
rashin dangin uwa lokacin aure a kusa da ciwo…..” ta dan ciji labbanta “…uhmmm ni kaga
dangin Innata suna garin nan kuma bikin da muka hadu ma nasu ne, Mairama kara kawai aka yi
mata”
Yanzu ya gama gane manufar wannan dogon sharhin. Kaurara murya yayi ya hade rai
“Salame!....”
Bai karasa maganar ba sai ga Mairama ta fito da sassarfa sanye da kayan da tayi aikin furar ta
makale a bayan kyaure.
Zayyan ne ya amsa yana mai jindadin ganinta “Mairam yau a nan zamuyi tadin?”
Kai ta sunkuyar ta sake yafito Salame sai kawai tayi gaba abinta ta fice don tasan me take nema.
Kusan minti goma tun bayan fitowarta take ta neman mukullin sif din bata gani ba. Baki ta saki
ganin ta fice bayan tasan kiranta take. Duk sai taji ta muzanta saboda Zayyan ma ya gani kuma
baiyi mamaki ba duk da bai san me take bukata a wurinta ba.
“Nima in zo bayan kyauren ne?”
Hannu ya daga ya dakatar da ita “dawo abinki nima nan kayan jikina sun sha wahala da kurar
hanya amma na kasa hakuri ko masauki ban nema ba nayo nan”
Jikinta ta kalla musamman zanin taji babu dadi. Zayyan ya matsa mata akan ta fito ba zai dade ba
sai dare zai dawo. Busu-busu haka ta fito kayan jikinta masu saurin nuna datti ne dama saboda
haskensu.
Kanta ta sunkuyar tana kallon kasa ta gaisheshi ya amsa fuskarsa a sake. Lura yayi a takure take
sai ya mika mata ledar kilishin Malamijo yace ta shiga gida sai anjima zai dawo.
Yana tafiya a hanya amma zuciyarsa ta fada kogin tunanin kalaman Salame da kuma yanayin da
ya ga Mairama. Yana da yakinin Salame ko dai tana son sa ko kuma kawai bata son cigaban
kanwarta ne. Ko ma meye zaiyi kokarin sanin wacece Mairama Ali kafin ya koma bakin aikinsa.
A cikin gidan kuma Mairama sake komawa tayi neman mukulli har ta hada gumi amma ta rasa ina
ya fada.
Da ta gaji da nema ga rashin sanin ina Salame ta tafi sai kawai ta cire kayan jikinta taje ta
wankesu. Dije ce ta kasa hakuri tace mata me take yi da daurin kirji ta fada mata bata ga mukulli
bane.
“Ta fita”
“Taje gidan uban wa?” suka ji Malamijo ya daga murya yana fada.
Tsoro taji da tasan zai shigo gidan a lokacin bazata fada ba.
Da ya ga bata da niyyar amsawa saboda rashin sani da kuma kokarin rufa mata asiri sai ya mayar
da akalar tambayar ga Dije.
Hannuwa ta yarfe “ina dakina ina zan sani, dama tunda yaron nan mai kudi ya fara zuwa daga
birni naga take takenta so take tafi karfin kowa”
“Babu mai fin karfina a gidan nan, idan ta dawo a turo min ita inji da izinin wa ta fita”
Zai shiga dakinsa Mairama tayi saurin dauko masa kilishin “Malamijo gashi yace na baka”
Ledar ya karba da sauri yana lekawa. Ganin kilishi yayi gari guda ya soma dariya “soja yazo
kenan Mairama”
Kanta ta kawar gefe tana murmushi ya bantaro mai dan girma kamar tafin hannunsa ya mika mata
Sai da ta karba din tace masa nasa ne kawai. Dije tuni yawu ya tsinke tayi kasake tana jiran ya
bata amma sai ta ga bashi da niyya.
Harararta yayi yana kanne ido “iyayen kwadayi ungo kafin a tara min taragutsan nan su fara min
kallon nama”
Wani dan guntu ya bata ta jefa a baki a kan idon Hajjo. Fitowa tayi itama tana bata rai “ko a bani
ko na gayyato jama’ar gidan nan”
Bashi da zabi haka ya dangwara mata a tafin hannunta. Jefashi tayi duka a baki sannan ta daga
murya tace kowa ya fito Malamijo yana rabon kilishi.
Ai kan kace kwabo sun soma taruwa mutum kadan ne basa nan. Malamijo kamar ya hadiyi zuciya
haka ya rinka yafita musu yana badawa ba da zuciya daya ba.
Ana tsaka da kiran magariba Salame ta shigo gidan. Can wurin Ta Madina da taje bacin rai kawai
ta karo don sosai take fushi da ita har yanzu saboda abinda tayi mata a Kano. Sallama tayi a dakin
Mairama ta amsata ciki-ciki. Tsaki ta doka ta ajiye gyalenta ta fita yin alwala. Bayan tayi sallah ne
Mairama ta tambayeta ko ta ga mukullin sif din.
Zuciya ta soma cin Mairama saboda ta tabbatar dazu da gangan Salame ta fita duk da tasan kiranta
take yi. Wai ma me ya kaita wurin Zayyan din.
“Shikenan”
“Shikenan me?”
Maimakon amsar fatar baki sai gani tayi Mairama tasa iyakar karfinta tana jijjiga kofofin sif din
tana neman ballesu. Da saurinta ta mike don ta dakatar da ita.
“Meye hakan?”
“Dame yayi miki kama? Balleta zanyi tunda mukullin ya bata in nemi kayan sawa”
“Adda Salame idan wani abu nayi miki ki fito fili ki fada min amma ba ki zauna kullum kina jin
haushina kina min tsaki ba. Kin sani wallahi ba don ke Addata bace ….”
Wata fuzga ta kaiwa kofar sai gata ta bude ta dauko kayan da zata saka bata sake kula Salame ba.
Gefe ita ma ta koma tana ta hucin kishi ganin yadda Mairama ta zage tana kwalliya saboda
Zayyan.
“Aikin banza ki gama adon yace ya fasa tunda yanzu yasan daga wane irin gida ki ka fito.”
Salame sai ta tsame kafarta tayi waje. Tana zaune tana jira a raba tuwon gidan na al’ada a bata nata
Mairama ta fito bayan an fada mata dawowar Zayyan. Da tazo wucewa tana jin uban tsakin da
Salame taja har sai da Dije ta soma sababi ko da ita take.
Hira suka yi cikin nutsuwa rabi duk shi yake maganar saboda kunya irin ta Fulani. Tana son
tambayarsa game da abubuwan da take zargin Salame ta fada masa amma ta gaza. Kamar ya sani
kuwa da kansa ya shiga bata labarin asalinsa da rayuwarsa ta baya zuwa yanzu. Tausayinsa taji har
idanunta su ka ciko da kwalla.
“Bana so yanayin rayuwar gidanku ya sanya ki fara tunanin zan gujeki ko hakan zai shafi
zamantakewarmu. Gidajen da muka fito daban, sannan gidan da zamu samarwa kanmu da ‘ya’yan
da nake burin ki haifa min shima daban.”
Tamkar kasa ta zage ta hadiyeta taji saboda kunyar kalaminsa na karshe. Da dabara ya samu ya
rinka kwantar mata da hankali da kwadaita mata irin tanadin da yake mata idan ta zama
mallakinsa. Ba shi ya bar gidan ba sai tara da rabi na dare. Washegari ya sake zuwa kuma a ranar
ne ya sanar da Malamijo zuwan kawunnansa idan ya koma.
“Abin da nake so da kai shine ka fada musu su taho da sadakinsu ayi komai a kare. Yaran nan sun
zaunu babu dalilin ayi ta jan lokaci. Budurwa kamar Mairama ta bawa shekaru shatakwas baya
harda watanni ina kallonta tana kallona. Ga yayarta ita ma zan fadawa yaron nan Salisu sai ayi a
lokaci guda”
Dadi maganar ta Malamijo tayi masa yayi na’am da ita. Ana gobe zai koma yana jiran fitowar
Mairama sai ga Salame da ta shiga tashin hankali sakamakon gabatowar aurenta da Salisun da
bata so. Hanyar waje tayi a daidai inda yake zaune ta jefa masa takarda ta fita. Ba nisa tayi ba tana
layin bayan gidansu tana jiran ya karanta wasikar yazo ya sameta.
Layuka kadan ya karanta inda take sanar dashi son da take masa da kuma jiransa da take a bayan
layi idan ya amince yazo ya sameta. Mairama ce tayi sallama sai kawai ya yayyaga takardar ya
dunkuleta a hannunsa.
Sun jima suna hira yana fada mata haduwarsu ta gaba ta zama tasa tana dariya a hankali Salame
ta dawo kamar kububuwa. Ta kwashi awa guda da doriya tana jiransa bai zo ba. Yanzu da ta shigo
takardar hannunsa ya watsa a iska ko kallonta baiyi ba. Zuciyarta kamar za ta fashe saboda
bakinciki ta wuce ciki.
Bahaushe ma yasan babu wanda ya isa ya sauya kudurar Ubangiji ga bayinSa shiyasa mu kan ce
wai tun ran gini….Bayan duka wasu shirye shirye da hassada daga bangaren ‘yan bakinciki irin su
Jume da ‘ya’yanta da kuma Salame mai son maso wani, da azahar din wata asabar aka daura auren
Zayyan Muhammad Tureta da Mairama Ali Gidado. Sai kuma Salisu Lawan da Ummusalma Ali
Gidado. Kowacce cikinsu angonta yayi bajinta gwargwadon aljihunsa ya yi mata kayan lefe. Ko
ba’a fada ba kayan Salame sun kere na Mairamu duk da Zayyan din ma baiyi kasa a gwiwa ba,
amma a haka Salame ta dauko ido ta sakawa kayan Mairama a ganinta da ita su ka fi dacewa.
[7/25, 3:14 PM] Sameee💖💖: G
*….TUN RAN ZANE*
Hakan take domin kuwa yau ne za’a kai amaren dakunansu. Dakin Yadikko aka tarasu Malamijo
ya shigo zaiyi musu nasiha ta karshe safiyar lahadi.
Kallonsu yayi daya bayan daya sannan ya juya wurin Yadikko.
Hularsa ya turo gaba "abi miji sau da kafa shine shawarata gareku. Banda tsiwa ko rashin kunya
sannan ayi ta hakuri. Duk wadda ta kaso aurenta babu abinda ya shalleni ah to. Allah bada zaman
lafiya ku tashi ku tafi kada ayi dare Mairama tana da nisa. Birnin Shehu kwai dan karen tafiya
daga nan kamar za'a ya da shege"
Wannan magana ma sai da ta taba ran Salame. Babu wanda ya damu da cewa ita ke son Zayyan
har ake wani zancen nisan garin. Haka su ka fito suna ta kuka, kowacce da abinda take yiwa.
Salame kukan rabuwa da masoyi take yi don tasan an riga an cuceta an rabata da Zayyan.
Mairama kuwa kukanta bai wuce na rabuwa da 'yar uwarta da gidan nasu duk da ba dadinsa suke
ji ba, sai kuma fargabar sabuwar rayuwar da zata fara.
Akori kura biyu ke biye da motocin daukar amaren na kayan dakinsu da aka samu Malamijo yayi.
Gadaje daidai ne da saitin kujeru da kuma kayan kitchen. Gidan Salame aka fara tsayawa a Kofar
na'isa babban gida ne mai bangare uku na Salisu da 'yan uwansa. Yadikko da Hajjo su ne zasu
tsaya a nan ayi jere tare da 'yan uwan Ta Madina. Basuyi mamaki ba ganin har sunyi jeren katon
gado a daki daya da kwaba da madubi masu kyau daidai da zamani wanda Ta Madina da 'yan
uwanta suka yi. A falon ma sunyi mata kujeru manya da suka fi na wajen Malamijo an malale
kasan da leda mai ado da ta dace da labulen da suka yi mata. Kayan da suka zo dasu wani daki
guda aka nuna musu suka jera kujerun da gadon ya dauke su tsaf saboda ba wani yawa garesu ba.
Kannen Ta Madina suna aiki suna yabawa su Yadikko magana wai kudin Malamijo bai tsinana
musu komai ba. To su din ma basu tanka ba tunda idan anbi ta barawo abi ta mabi sawu.
Dije da Inno su ne jagora a tafiya kai Mairama nata gidan. Yamma likis suka isa Allah Yasa ba
wata gayya ce ba basu fi su biyar ba. Sanin cewa idan ya kaisu gidansu Jume sai ta saka shi jin
kunya ya nemi alfarmar kanin babansa zai saukesu a gidan kafin su yi jeren. Nan su ka kwana ana
ta tarairayarsu. Mami matar Captain Mustapha ita ma tayi abinci mai yawa suka je aka yi taro a
gidan. Jume ko zuwa bata yi ba amma 'ya'yanta mata sun je suna ta yada magana wai kalen dangi
ya guji nasa asalin. Haka nan 'yan uwan Mal.Muhammadu sun je da yawansu.
Da safe Hadir ne yaje daukosu aka kaisu gidan da aka bawa Zayyan a bangaren gidajen da suke
cikin barikin. Daki daya ne kato da bandaki a cikinsa sai falo madaidaici da kitchen karami. Bata
zo da komai ba sai iya kayan da Malamijo yayi mata. Anyi jere lafiya a daren aka kawo amarya
dakinta su kuma suka koma Sumaila washegari.
Zaman Zayyan da Mairama abin burgewa ne da sha'awa ga duk wanda ya sansu kuma yake
mu'amala dasu. Babu abinda ya rageta dashi ta fannin soyayya da kyautatawa. Ita ma a nata
bangaren tana binsa sau da kafa da biyayya da tattali. Yanayin gidansu yasa ta iya girki bashi da
matsala ta wannan fannin ma.
Satinsu biyar da aure Zainab ta tare matar Hadir. Mami dadi ya isheta ga hausawa 'yan uwanta a
kusa duk da nasu gidajen suna bangare daban. Sunfi girma da kyau. Su Mairama kuwa layinsu
daya da Zainab. Hade kai suka yi suna zaman gaskiya da bawa juna shawarwari. Mami ce babba
amma Zainab duk ta fisu wayewa. Mairama kuwa dama albarkacin boko ta san wasu abubuwan
amma kifin rijiya ce. Idan suna hira abin dariya, Mairama kana jin hausarta zaka gane bafillatana
ce, Zainab sakkwatanci ziryan ita kuma Mami Hausar Katsina.
Yau juma'a Mairama tana cikin girki kafin dawowar Zayyan taji sallamar Awwab. Kowa yasan
dan gidanta ne na gaban goshi. Zainab har ta gaji da mita ta kama kannensa Zahra da Fauziyya a
matsayin nata.
"So ka ke Anti Zainab ta shigo ta soma tsokanarka ko" tace tana murmushi.
"Mami tace in gaisheki kuma zata zo kiyi mata kalba anjima"
Fita yayi zai tafi ya ga ta biyo bayansa a guje ta shige bandaki tana kakarin amai. Awwab ya rasa
me zaiyi sai kuka yana mata sannu. Ita ke fama da matsananciyar tashin zuciya da amai kamar
zata fitar da kayan cikinta amma kuma ita ke bashi hakuri saboda yadda ya gigice mata.
Kallonta yayi tana dafa bango tana daga kafa da kyar. Hannunta ya rike har kan kujera yace "In
fadawa Mami ko Anti Zainab?"
Dariya ya bata ya kafeta da ido wai tayi dariya. Motsin mutane suka fara ji daga waje ya tashi da
sauri ya bude kofar. Zayyan ne da wani security soja sun kinkimo katon kwali ga wasu kwalayen
biyu kuma a kasa daga gefe. Yana ganin Awwab yace ya je ya fadawa Mairama ta koma daki zasu
shigo da kaya. Ta ji me yace kafin Awwab din ya dawo ta koma ciki ta kwanta.
Suna shigo da kayan ya fadawa Zayyan tana amai. Nan fa hankalinsa ya tashi ya bishi dakin bayan
sun gama shigo da kayan.
Sai da ta harari Awwab ta bashi amsa "ulcer ta ce ta tashi tun dazu da na sha coke kirjina ke suya"
"Shine baki taba fada min kina da ulcer ba suk sati nake ajiye miki crate din minerals? To anyi an
gama"
Bata da wata ulcer a iya saninta amma ta ki jinin asibiti. Kitchen din yaje ya zubo abinci.
Wani aman taji ya taho mata daga ganin abincin ta daure "Awwab baici ba ka bashi zan ci anjima"
"Nima bazan ci ba sai kinci" Awwab din yace yana marairaicewa.
Zayyan ya janyo hannunsa ya zauna a kusa dashi da kyar ya samu ya karba yana ci yana mata hira.
Mairam ta soma dariya da Awwab ya dage sai ya fada masa me yake nufi. Sai can yamma ya tafi
ya fadawa Maminsa bata da lafiya. Taso zuwa amma tunda Zayyan yana gida sai ta hakura sai
gobe.
Sai dare Zayyan ya bude kwalayen da suka zo dasu. Daya firinji ne madaidaici mai kofa daya
amma da freezer daga sama. Sai kuma TV da bidiyo duka sababbi. Mairama godiya harda kuka
don murna.
Bayan kwana biyu kullum tana fama da amai da jiri ya kaita asibiti aka basu tabbacin ciki ne da
ita. Tamkar ya hadiyeta don farinciki. Gani yake yanzu zai sami abinda zai kira nasa, jininsa sosai.
**********
Lokaci yana tafiya al'amura suna faruwa garesu. Captain Mustapha ya sami karin girma zuwa
mukamin Major bayan ya dawo daga wani aiki da aka tura shi Warri. Zayyan da Hadir kuma sun
zama Lieutenants.
Cikin Mairama yana da wata shida amma idan ka ganta sai ka rantse bazata kara kwana ba zata
haihu. Su Mami sun gama sadakarwa ‘yan biyu ne a cikin. Bata wani laulayi sosai sai cin abinci
akai akai tayi bulbul ta sake kyau da cikowa. Kwakkwaran motsi idan tayi Zayyan ya rinka cewa
yaya akayi. Zainab ma cikin gareta wata uku amma ita laulayi yake saka ta don bata iya komai
yanzu sai kwanciya duk ta rame abin tausayi. Mazajensu na fita suke tarewa a gidanta su taimaka
mata da aikin gida. Mami tayi ta kokarin hana Mairama amma bata ji, tafi ganewa motsa jikin
dama kuma haka ake so ga mai juna biyu.
Yau litinin suna tare a gidan Zainab su Awwab suka dawo daga makaranta. Tun da suka ga gidan a
rufe sun san inda Maminsu ta tafi sai suka bita. A falo suke zaune suna hira yau Zainab din jikinta
da kwari ba kamar kwanaki ba.
Kowa yana cin abinci an hadawa yaran a tray karami na silver iyayensu su ma sun hada tare.
Zainab ce ta kula da Awwab gabadaya idanunsa suna kan Mairama. Idan ta yamutsa fuska sai yayi
kamar zaiyi kuka.
“Awwabu ya aka yi ne kake ta kallon mamanka?”
Mami ta tuntsire da dariya “kai kuma baka son cikinta yayi irin na maman Ebere din ne?”
Ya gyada kai “saboda fashewa zaiyi watarana, haka Ebere tace na mamansu ya fashe a asibiti.”
Zahra ta kai masa bugu a kafada “Kai Hamma haihuwa zatayi fa mu sami baby” Hamma shine
sunan da Mairama tace su rinka kiransa dashi don da fari Awwab kawai suke cewa.
Maminsu ya kalla a tsorace “kinji tana rashin kunya Mami, ni dai ba ruwana”
Tsokanarsa Zainab ta shiga yi tana cewa Mairama danta yakware a wautar ‘yan fari. Da abun ya
ishe shi sai ga hawaye Zahra da Fauziyya aka sami na yi. Mairama ta janyo shi kusa da ita.
“Kyalesu baby zan dauko maka a asibiti idan nawa cikin ya fashe kai kadai zaka rinka dauka.”
Wata dariya ya saki da ta kara masa kyau da nuna kuruciyarsa yana murna, har da yiwa su
Fauziyya gwalo. A haka rayuwarsu take tafiya komai nasu cikin aminci tamkar ‘yan uwa na jini.
Ranar da nakuda ta kama Mairama Zayyan sun tafi gidan gwamnati shugaban kasa zai kawo
ziyara. Nauyi da kunya ya sanya ta kasa fada masa tun gabanin asuba da ta fara ciwon har ya fita.
Gashi abu yafi karfinta zamani ba na waya ba bare ta nemi taimako. Allah ne ya kawo mata
Awwab tana cikin wannan matsanancin halin ta daure tace yaje gida ya kira Mami kuma ya
tabbata ta taho yanzun nan. Ya kusa shekara tara a lokacin shiyasa duk da bata fada ba jikinsa ya
bashi ba lafiya ba.
A guje ya koma gida sai gasu cikin mintuna kalilan. Tana ganinta tace ya fita ta shiga daki ta
taimaka mata su fito kawai ta fara nishi. Mami ta san babu yadda zatayi tun da ta hango kai yana
neman fitowa a take Allah Ya sako mata karfin zuciya ta karbi haihuwar santaleliyar yarinyar da
Mairama ta haifa.
Tubarakallah yarinyar akwai girma da kiba taci ta koshi tun a ciki ga kyau. Kukan da ta chanyara
ne ya sanar da gidan da yake jikin nasu an sauka. Matar gidan bayerabiya ce suna kiranta Maman
Dolapo ta shigo da sallamarta domin su ma musulmai ne. Awwab aka tura ya kira Zainab itama
tazo suna ta murna aka dora musu ruwan wanka. Yarinya tana ta wutsil wutsil kakkarfa da ita.
Mami girman yana gareta ita ta yiwa Mairama wanka. Jaririya kuwa Maman Dolapo ta roki
alfarmar a barta tayi mata irin nasu na yarbawa. Babu wanda ya hana saboda zaman mutumci suke
yi da ita. Sun kuwa ga wanka ba irin wanda suka saba ba. Ta wanke yarinyar nan sosai ga
mamakinsu harda manja mai kyau ta dauko daga gidanta ta shefe jikin yarinyar ta mitstsiketa sosai
sannan aka fara wankan da kyau ana fitar da datti da maikon manjan. Ko da ta gama yarinya kana
tabata jikin nan subul ta kara wani haske kamar jini ya fito. Lallausan kayan sanyi aka sanya mata
lokaci na damuna sannan akace Mairama ta bata nono. Nan fa ake yinta kunyar jama’a ko karbarta
ta kasa. Zainab ta kamata ta maidata daki. Zata rufe mata kofa Awwab yayi kekam dole ta barshi
ya bi bayan mamansa ana musu dariya.
Babu abinda makota basu yiwa Mairama ba. Daki ta shiga tayi kukan rashin dangin uwa da basu
damu da ita ba. Da kanta ta nemi Zayyan akan bata son zuwa gida wanka saboda ta sani ba wata
kulawa da zata samu. Bayan auren nasu sunje sau daya bata ji dadin gidan ba ko kadan. Wani kallo
na kyashi ake watsa mata, Yadikko ce kadai mai janta a jiki. Malamijo kuwa zubar da girma yayi
gaban Zayyan yana fada masa yadda yake cikin mawuyacin halin kula da iyali. Allah Yasa sunyo
musu tsaraba irin ta Sakkwato amma duk da haka sai da ya bashi kudi. Kurewar lokaci yasa basu
tsaya a gidan Salame ba. Abin da bata sani ba da gangan Zayyan yayi haka don ko kadan baya
kaunar yadda Salamen take yiwa matarsa ita kuma bata gani.
Ba su suka dawo gida ba sai daya saura na dare. Lokacin kowa ya watse hatta Mami ta tafi saboda
yara sun fara bacci. Mairama da jaririyarta ma baccin suke jiki ya gaji ga wankan da suka sha. Ko
ina a gyare tsaf gidan ya bude kofar dakin a hankali don kada ya tasheta ko fitila bai kunna ba.
Kayansa ya cire yaje yayi wanka ya fito yana komai a nutse don baya son damunta. Duhun dakin
yasa garin neman robar mai ya tunkudu wani abu daga kan madubin ya fado da karfi. Karar ce ta
tashi baby din yaji ana inya inyaa.
Hanyar kofa ya nufa da fari ya ajiye sojancin na wucin gadi, sai yaji muryar Mairama tana cewa
shhhh. Da mugun sauri ya kunna fitila idanunsa a kan gadon. Kyakkyawan gamo yayi.
Masoyiyarsa abar kaunarsa ya gani tare da baby kunshe cikin shawul fari tas.
Zuciyarsa ce tayi wani irin nauyi ya tako gaban gadon a hankali ya zauna a gefenta. Murmushi ta
sakar masa kafin ta dora masa jaririyar a kan hannuwan da ya miko mata. Rungumesu yayi tare
yana fidda numfashi da sauri. Mairama sai ta soma hawayen farinciki ta kara shiga jikinsa yana
yiwa baby addu’a. Sun dauki lokaci a haka kafin ya bude fuskarta tana tandar baki.
Karbarta tayi ta juya masa baya zata shayar da ita ya hawo gadon ya zagaya gabanta “kada ki
cuceni da kunya”
Ba yadda ta iya yana ta kallonsu cike da sha’awa kamar wani zai ce ba nasa bane. Bai iya tashi ba
har ta gama ya ga babyn tayi bacci ita ma idanu sun fara rufewa.
Kwanciya ya gyara musu ya dauko darduma ya shimfida yana nafilar godiyarsa ga Allah. Duk
gajiyar da ya kwaso ranar babu wani bacci da ya iya yi sai gadinsu har asuba tayi. A masallaci
Major Mustapha da Hadir su ka yi masa barka tare da sauran abokan aikinsu ana taya shi murna.
Papa Dolapo ya tsokane shi wai Allah Yasa dai ba mai kiriniya bane kamarsa akayi dariya.
Aikinsu bai kare ba zasu koma gidan gwamna. Kafin su tafi Major Mustapha da Hadir su ka je
gidan ganin baby da kuma yi mata addu’a. Zayyan ya dan taba Hadir yana yi masa magana da ido.
Ya san zancen shiyasa ya dubi Major din.
“Sir kaine zaka rada mata suna fa, kayi mata huduba”
Wani iri yaji yadda yaran nan suke matukar girmama shi tamkar yayansu na jini “wane sunan zan
saka mata?”
Shiru Zayyan yayi sai ya koma ciki da sauri wurin Mairama a daki.
“Mairam bamu tsayar da shawarar suna ba ga Major can yana jira”
“Don Allah Sojana sunanta Alheran, idan na sake haihuwa sai a saka sunan Innar”
Muhawara suke yi sosai ya gaji ya karbi nata “baki da wani suna da kike son a saka mata? Suna
biyu nake son a saka”
Sarai ta fahimce shi, a dole yana son bata dama ita ma ta sanyawa yarinyar suna. Sai dai duk
yadda take son saka sunan innarta tana ganin shi yafi dacewa da ya fara sakawa. Bata yi dogon
tunani ba tace “Radhiya”.
Murmushi kawai yayi ya fita ya sanar da Major sunan ‘yarsa Alheran Radhiya Zayyan
Muhammad Tureta. Hadir yace “mutumina wannan sunaye haka”
“ ‘Yar soja ce, ya kamata a komai ta fita daban” ya bashi amsa yana magana a hankali kada a ji.
Major Mustapha ya gama yi mata huduba sannan yace ya maidata ciki suyi shirin tafiya bakwai ta
kusa.
Kwanaki hudu da haihuwa duk wanda ya kamata ya sami labarin haihuwa daga danginsu ya sani.
Tasha Zayyan yaje ya bada sakon wasika zuwa ga Kawunsa Ghoumar domin a sanar da sauran
dangi abinda aka samu. Sai wasikar ta isa akan gaba suna shirin zuwa saboda aurensa da yazo da
gaggawa basu sami damar halarta ba.
[7/25, 3:14 PM] Sameee💖💖: H
**********
“Kasan Allah Malamijo idan naje Sakkwato haka zikau Allah shi tsinan”
Fuskarsa a murtuke kamar zai kai mata duka ya tashi daga kwanciyar da yayi “ wai ni dake waye
ya haifi yarinyar nan ne eyyee?”
Yadikko ta galla masa harara “kaine ubanta wanda na sani da ana sakewa wallahi bana jin ko
tsinken ashanar gidan nan zai so a alakanta shi da kai. Me kake yiwa yaran bayan haihuwarsu?
Nan haka muka kaita gidan miji abin kunya babu wani kayan arziki wai kuma ‘yarka ce, kai da
garin nan kowa ya shaida arziki gareka”
“Sa ido, sa ido…kowa zaiyi ya bari tunda ba da uban mutum muke kiwon ba”
“Ba sai ka zageni ba, gaskiya ce dai dole na fada maka. Mairama baka fitar da ita kunya da biki ba
dole kayi bajinta ita ta fara kawo maka jika a gidan nan. Ka kuma hada da gara tunda ba’ayi musu
komai ba da bikin. Salame ba don mahaifiyarta tana kusa ba itama da haka za ta tare ba garar”
Malamijo ya mike yana kada hannuwa yana kumfar baka saboda an bukaci kudi “garo ba gara ba,
idan sai na bada kudi kunyi mata gara zaku je don Allah kuyi zamanku na yafe. Yo dangin uwarta
ma suka bace bat a doron kasa basa waiwayarta tunda ta rasu balle ku”
“Laifin waye to idan bana ka ba? Kowace mace ka gani kana so saboda zalama. Kuma ba dole su
bace ba. Kayi auren biyan bashi tana haihuwa kace ka saketa kuma sai sun biya rabin kudin. Tsoro
yasa sun gudu bakinciki kuma ya kashe yarinya karama ta bar marainiya”
Yadikko kin hakura tayi sai da kyar da sudin goshi Malamijo ya bata dubu uku da kuma tinkiya
guda daya “gashi nan a tafi a kaiwa ‘yar kunama kafin na fara ganinki cikin bacci na. Ke dai da
mayya ce da tuni na dade a tukunya”
Warce kudin tayi a hannunsa “fadi ka kara, aradu da ina maita da tuni an dade da raba gadon ka”
Hanjin cikin Malamijo ne ya kada da gaske furucinta ya bashi tsoro. Ko dai mayyar ce ne? shiyasa
kullum baya gaba sai dai baya kamar kudin guzuri.
**********
Kwance take akan doguwar kujera a falonta lokaci lokaci ta dago kai ta tsartar da miyau a duk
inda ta ga dama tana faman yatsina fuska. Salisu ne ya shigo da langa cike da gurasa da tsire irin
wanda take so.
Kamar bazata zuba ba sai kuma ta tofa ya mayar ya ajiye jiki na rawa ya miko mata langar ta
amshe ta soma ci don yunwa take ji dama. Ta dauko yanka na biyu ya saki fuska yana dariya “yau
da albishir na dawo, me zaki bani tukwici?”
Baiyi fushi ba don ya saba da halinta. Bata boye masa kiyayya har yanzu da take dauke da ciki na
wata biyu. Tsiyarta take tsulawa a gidan tana cin karenta babu babbaka kawai don tasan Salisu
yana masifar son ta.
Naman da take shirin hadiya ne ya makale mata a makoshi ta soma tari. Ruwa ya bata ko kalla
bata yi ba bare ta karba.
“Me kace?”
“Mairama….”
Zuciyarta ce take tafasa da bakin kishi. Yanzu Mairama har ciki Zayyan yayi mata ta haihu.
Saboda shi tafi wata uku Salisu bai sami kanta ba sai da ya hada da fin karfi. Rigima sosai suka
kwasa kamar auren bariki tana ta yi masa Allah Ya isa. Ganin babu sarki sai Allah daga baya ta
hakura ba don tana son sa din ba sai don kawai ba ta hango mafita daga kaddararren aurensa ba.
Da ciki ya bullo kamar ta zare don bata kaunar komai tsakaninsu lokacin da za ta kasha auren ta
nemi hanyar shiga gidan Zayyan. Indai soyayya na saka hauka, kan Salame ya dade da kwancewa
akan mijin kanwarta. Kuka ne ya kwace mata mai cin rai da zuciya. Mairama ta rigata samun
abinda take muradi. Salisu ya tsaya kallon ikon Allah yadda take kuka haikan.
“Yanzu meye abin kuka bayan kema kina da cikin nan” a tunaninsa ko don ta riga ta haihuwa ne.
“Allah Ya sauwake nayi kuka don ta rigani haihuwa” tace cike da tsiwa.
Gabanta ne ya fadi ta soma inda-inda “banda abin Mairama da kwarewa a rashin kunya daga
auren sai ta bashi kanta. Wannan ai zubar da mutumci ne. A lissafina sai nan da kwana hudu ma
zamu cika wata tara da aure amma gashi ita ta haihu. Anya ma kuwa cikin nan….”
“Ke Salame! Shiga taitayinki. Kanwar ta ki kike neman jifa da kazafi saboda wani shirmenku na
banza da hofi. Na dade da kula ko sunanta na ambata ko agidan ku aka ambaceta sai fuskarki ta
sauya. Idan ma wani abin ne ya hadaku ki shirya jibi zamu wuce Sakkwaton sai ku sasanta”
Kallon wulakanci ta jefa masa duk da taji tsoron tsawar da yayi mata “ba zani ba idan ka matsu da
ganinsu kaje kai kadai”
Ransa ne ya soma baci shima “na fasa a gobe ma zamu tafi, haba yarinya mai nutsuwa da kunya
baki da aiki sai na kusheta da jifanta da bakaken kalamai”
“Da kasan tana da halayen kirki me ya hana ka nemi aurenta ka barni na auri wanda nake….”
Tasss taji saukar mari a kumatunta sai da ta ga haske, rai a matukar bace Salisu ya nunata da yatsa
“bar ganin ina lallabaki wallahi sai nayi miki shegen duka a gidan nan. Ke wace irin mutum ce
ne? Kina ta abubuwa ina kawar da kai to amma tura ta kai bango tunda har jininki baki raga musu
ba. Ki shirya gobe zamu tafi sannan ki tashi ki hada ruwan omo da dettol ki bi duka gidan nan ki
goge min. Su bayan kofofi da kujeru duka ki tsaftace min gida ko ina warin yawu ya isheni. Idan
na sake kamaki kina tofa yawu nan ba a wancan abin ba wallahi jikinki ne zai gaya miki. Tashi ki
bani wuri ni”
Ba karamin tsorata tayi ba ta kai mai hakuri bango. Tsoro ne da ita tun da can, soyayyar Zayyan da
ta bari a zuciyarta da kyashin kanwarta su ne suka maidata haka. Jiki na rawa ta tashi yace ta dawo
sai ta gama cin abincinta tukunna.
[7/25, 3:14 PM] Sameee💖💖: I
*KANA NAKA…*
Shirye shiryen tarbar bakin da zasu zo suna ya kankama. Zayyan ya dage a gidan mahaifinsa
za’ayi taron duk da cewa kawunansa da Mal Aminu sun ce gara ya yi a nasu saboda gudun bacin
rai da ga Jume ko ‘ya’yanta. Ya riga ya gama tsara yadda zai bi da su domin gujewa hakan. Gidan
yaje har daki ya same ta ta hakimce tana taunar goro.
Tabe baki tayi tana kallonsa ya zauna a kan yagaggiyar ledar dakin “kawarsu dai wadanda aka
haifawa. Ni a su wa kuma?”
Basarwa yayi ya tankwashe kafafu “dama alfarma nazo nema, ina son ayi taron sunan a gidan nan
ne”
“Dama jiranka nake naga iya gudun ruwanka tun da aka fara shigowa da bokatan fenti dazu. Ita
matar taka basu da dangi ne da bazata koma gidansu ba? Naga haihuwar fari ce, ya dace ace tana
gaban iyayenta. Tsabagen rashin ta ido ka barta a gidanka kuna kwana daki guda.”
“Cikin masu zuwa sunan akwai matar babanta da zata zauna har ayi arba’in tare da ita. Ni zan
koma wani gidan a cikin barikin kafin su gama”
Maikudi ne ya shigo fakam fakam ya sami guri ya tsaya ayi zancen dashi. Zayyan ya sake fada
mata yana son sauke baki da ga Nijar da kuma mutanen Sumaila a gidan nasu tunda babba ne.
“Ince ko ka ga nayi kama da baiwar gidanku da zan zauna tarbar baki. Kaga Zayyanu tun wuri ka
san me kake ciki da bakinka”
Murmushi ta ga yayi maimakon ya tashi ma sai ya gyara zama “to babu matsala zan yiwa su
Kawu magana. Sai abu na biyu nace idan an kawo kudin rakuman wace sana’a Maikudi zai fara?”
A tare su ka taso masa kamar zasu zaune sh. Maikudi ya zauna a gefensa yana fara ’a kamar gonar
auduga, hakansa zai cimma ruwa. Jume ma sai ta saki fuska kamar ba ita ba.
Sai ga Maikudi ya tashi jiki na rawa “Bari na kira yayyenka malalatan banza su zo a fara gyara
gidan nan, mu gidanmu da yake da wadatar dakuna kamar ramin bera, Jume yaushe zaki ce sai ya
nemi su Kawu don iya tonawa kai asiri”
Matsowa tayi kusa da Zayyan tana dariya “shima yasan wasa nake yi masa. Ka nemi masu fentin
su zo ayi a gama da wuri sai a share dakunan ayi shimfida.”
Mayar da kansa wawa yayi suna ta bidirinsu yana biye musu. Maikudi da son banza harda cewa an
hutar dasu yin fenti tunda su ma baifi wata uku ya rage dukkansu su ukun zasuyi aure ba.
**********
Cikin ikon Allah baki sun iso an kaisu masauki, washegari za’ayi taron suna. Zayyan ya wadata
iyalinsa da duk abin da ya dace. Wani hadin kai da ga bangaren sojojin su ma sun hada masa
gudunmawa sannan matayensu sun zage dasu ake komai kamar yadda su ka saba idan dayarsu ta
haihu ko wani taro ya tashi. Salame da Nene Marka kanwar Malamijo a gidan zasu kwana sauran
kuma duka suna gidansu Zayyan.
Su Nene sun riga isowa ga yamma jama’ar gidan sun watse sai ita da Mairama da Zainab. Mami ta
wuce gida Fauziyya tana fama da zazzabi. Salisu na tsayar da mota a harabar gidajen da suke jere
a wurin ta fito da sauri gabanta yana faduwa ta barshi yana yiwa security din da yayi musu rakiya
zuwa gidan godiya.
Ciki ta shige tana fatan yin tozali da Zayyan. Sai dai idanunta akan na Mairama su ka sauka tana
shayar da jaririyarta. Wani kululun bakinciki ya taso ya tsaya mata a wuya. Mairama tayi wani
mugun kyau ta ciko ko ta ina. Kallo daya zaka yi mata kasan cewa hankalinta a kwance yake. Da
sauri ta cire yarinyar da ga bakin abincinta ta tashi ta fada jikin Salame tana murna da tsalle sai da
Yadikko tace tayi a hankali saboda yanayin jikin haihuwa.
“Wayyo Adda Salame nayi kewarki sosai ashe kina hanya. Ina yayan namu?”
Da kyar ta amsa “yana waje, ki tura mijinki ya bashi masauki”
Tsabar murna duk ta rude ma tayi hanyar daki neman mayafi sai ta jiyo muryar Zayyan din suna
magana da Salisu. Salame cikin zakuwa ta juya “bari naje mu gaisa da angon karni”
Nene ce ta dakatar da ita “wa yake ta angon karni baki ga ‘yar taki ba, dawo kiyi zamanki nasan
zasu shigo”
Ba haka taso ba amma dolente ta zauna. Mairama ta gabatar da Zainab wadda ta tashi tana tayata
hadowa su Salame abinci da sha.
Daga nan Zainab din tayi sallama ta tafi Yadikko kuma ta shiga wanka. Baby tana kwance akan
wani bargon yara mai kyau Mairama ta sake komawa kitchen ta soma kuka. Har wannan lokacin
Salame dama bata yi karar cewa a bata ita ba bare ta dauketa saboda bata ma son ganinta har ranta.
Kukan ya tsananta Mairama tana ji ta kasa cewa ta dauketa tunda ai ba kurma bace sannan tana jin
nauyin ta fito ta dauketa a ga tayi rashin kunya.
Nene tana da ga bandaki kukan ya isheta tana tunanin me ya sami yarinyar. Harara Salame ta jefa
mata sannan tasa hannu tana dan taba gefen jikinta wai rarrashi. Daga sama ta bayan kujerar ta ga
an zuro hannuwa an dauketa.
Waigawa tayi da sauri idanunta su ka gane mata Zayyan Tureta. Sanye yake da khakinsa ya zura
hularsa cikin wani abu da aka yiwa maballi daga kafadar rigar. Yayi matukar kyau da haske aure
ya sake gyara shi. A kafada ya dora ‘yarsa yana shafa mata baya.
“Zayyan ina wuni?” Salame tace cikin sanyin jiki. Bata san zai shigo ba da ko don ta burge shi ta
dauki ‘yar.
Tamkar bai ga mutum ba ya shareta ya shiga kwalawa Mairama kira. Tana tsaye dama daga kofar
kitchen din duk abinda Salame tayi ta gani tunda kujerar ta bata baya ne. Mamakin wannan
mummunan canjin daga ‘yar uwarta take yi. Ashe ko me ya hadasu tun kafin suyi aure bai kare ba
har yana son shafar ‘ya’ya. Hawaye taji ya soma sauko mata tana kallon bayan Salame a inda take
zaune kamar gunki saboda yadda taji kunyar abinda ta yiwa jaririyar a gaban babanta.
Hawayen nata Zayyan ya gani ya matsa gareta da dayan hannun da yake shafa babyn ya janyota
jikinsa da karfi ya rungume da hannu daya.
“Kada na sake ganin kin bar min yarinya ita kadai a falo. Idan babu kowa ki goyata ki shiga
kitchen din…kinji”
“Kayi hakuri baza’a kuma ba, na ga Adda tana wurin ne” tace tana karbarta daga hannunsa.
Salame ta juyo kamar mai ciwon wuya tana neman kalaman wanke kanta.
Kamar bai ji ba sai cewa yayi “Taimaka ki hada min abinci da zan tafi dashi inda zamu kwana da
Salisu. Zan kaishi yayi sallah da wanka na dawo na dauka. Amma ki fara cikawa wannan sojar
ciki”
Hannunta daya ta dora a gefen ido tayi masa salute “Yes Sir”
Matsowa yayi yana neman sumbatarta ta goce tana dariya. Mutuwar zaune Salame tayi. Shi kuwa
Zayyan da biyu yake yi don ji yayi ya kara tsanarta. Ba don ta hada jini da Mairamansa ba da sai
ya saka ta a guardroom ko na sa’a daya ne ya huce kukan ‘yarsa.
Da ya fita Mairama ta kawo mata sauran kayan abincin batare da ta sake yi mata magana ba ta
zauna bawa ‘yar nono.
“Ki kwashe ba ci zanyi ba don yanzu ba komai ke zauna min a ciki ba”
Wai nan so take ta sanar da ita itama tana da cikin. Sai Mairama ta gwada mata halin matar soja da
ta fara koyon yadda yake juya zance musamman idan ya fuskanci abu kake son sanar dashi da
dabara don ka bashi haushi.
"Adda yaya hanya? Ya zaman Kano?"
Sai da Salame ta kara kallonta irin baki ji me nace dinnan ba sannan ta chanja zancen tace lafiya.
Zaman kurame su ka koma har Nene ta fito tana tambayar me ya sami baby dazu take kuka. Babu
wadda ta amsa mata a cikinsu duk sun daure fuska sai ta kyale su ta sa tv a gaba tana kallon tashar
NTA.
Zaman ne ya ishi Salame ta tashi ta shiga daki wai zata yi wanka. Mairama ta bi bayanta taji ko
akwai abin da zata bukata. A tsaye ta sameta tana karewa dakin kallo tana tabe baki.
"Af...ke fa gadon da Malamijo yayi mana dashi aka kawoki ko? Amma naga labulayen kamar
sababbi ga TV ma a falon da firij. Kin fara sana'a ne ko Zayyan din kike tatikewa?"
"Yo Allah na tuba Adda mace da mijinta har sai kinji yaya ake kudi ke fita har a gyara mata gida?
Dadin zama ne kawai da iya tafiyar da miji"
Ta fadi haka ne saboda gorin da Salamen ke shirin yi mata. Ita kuma Salame sai ta dauka cin fuska
ne ko ta gane ta son sa.
"Ki dai bi a hankali maza basu da tabbas. Canja mace a wurinsu ba wata tsiya bace"
Zaro idanu Mairama tayi da mamaki. Har fatan aurenta ya mutu kuma Salame take yi? Indai haka
ne dole ta kama kanta don bata ga me ta tsare mata ba da take nuna mata hassada irin haka. Kowa
ya shaida mijinta yana da kudi ta rasa gane bakincikin na meye.
Karfe goma na safe a gidansu Zayyan tayi musu. Anyi taron suna na kayatarwa don Zayyan ya
sakar musu yadda zasu fita kunya. 'Yan uwansa mutan Agadas sunyi masa halacci duk da rashin
mahaifiyarsa sun zo da yawansu tare da gudunmawa mai yawa. A cewarsu basu sami bikinsa ba
dole a fanshe yanzu. Gashi jaririya ta gaji sunan 'yar uwarsu.
Mutan Sumaila ma sun sha kallo ganin irin suturar da Zayyan ya wadata Mairama da su na fitar
suna. Abin nasu ya burge sosai musamman da wata kanwar innar Zayyan ta kawo kayansu na
gargajiya na kabilarsu ta Tamasheq ta bawa Mairama.
" 'Yata ga wannan ku saka ke da maigidanki da jikarmu ayi hoto. Dashi nake son tafiya saboda
wadanda basu zo ba su ganku."
Mairama sai godiya take su Zainab suna tayata. Riga ce fara kamar buba ta zarta gwiwa da kadan
gaban ta sha aiki da shudin zare sai zani shudi. Ga kuma sarkoki da yari duka irin nasu da
abubuwan sakawa a ka. Mami ce ta karbi Radhiya yayin da wasu 'yan mata biyu kusan sa'annin
Mairama su ka ja ta dakin da su ka kwana. Da taimakonsu ta shirya komai su suka yi mata. Abin
hannu da na wuya da kunne harda hanci kowanne yayi mata cif. Na gashin kuwa sai da daya ta yi
mata kalba kananu guda uku-uku a gefe da gefen kunnenta ta zubo mata dogon gashin irin nasu
sannan aka dora mata shi ya zauna daga gaba kai kace wata sarauniya ce. Hatta fuskarta
kwalliyarsu aka yi mata leben nan ya sha fenti yayi baki. Da yake fara ce ba karamin kyau tayi ba
ta saje dasu. Wata guda ta soma ji daga tsakar gidan aka dora mata shudin yadi irin na zanin wani
irin yafawa yadda suke yi sannan su ka rike mata hannuwa aka fito da ita.
Turus tayi ga wata irin kunya kamar sabon aure da su ka hada idanu da Zayyan. Yayi kyau har bata
san yadda za ta kwatanta ba. Shima kayan gargajiyar ne a jikinsa na ciki farare babbar rigar da
kuma rawani duka shudi.
Kanta a kasa shi kuwa ya zuba mata idanu, manya cikin 'yan uwan nasu suna ta guda. Da shirinsu
suka zo da sunan yi masa nasu bikin. Taro ya kayatar da jama'a ba kadan ba duk da iyakarsu cikin
gidan. Salame tamkar ta bude ido ta ganta a matsayin Mairama. Ganinsa cikin wannan kaya ba
karamin sake fama mata ciwon son sa da yake nukurkusarta yayi ba.
Mai hoto aka kira yazo akayi ta dauka. Gwaggon Zayyan tace suyi su uku zata kai hoton gida.
Days suka dauka a tsakar gidan a tsaye tana rike da Radhiya shi kuma a gefenta. Dayan kuwa
dakin Innarsa yace su shiga a kan tsohon gadonta ya zauna da 'yarsa a hannu ita kuma a kusa
dashi. Daga nan ta kira danta Awwab ta dora masa kanwarsa tana tallabe da kanta daga bayansa ta
dan duka aka yi musu sannan Zayyan ma ya shiga.
Ranar idan ka gansu dole su baka sha'awa. Mutan Agadas har irin abincinsu sun dafa duk na bikin
dansu Zayyan da murnar haihuwar Alheran Radhiya.
A gidan maijego ta kwana ranar tare da danginsa ana ta bata labarin 'yan uwansu da irin yawan
danginsu. Gwaggon Zayyan tace mata cikin gurbatacciyar hausarta da ace Zayyan ba soja bane
gida Nijar suka so komawa dashi bayan rasuwar Mal Muhammadu.
"Idan ya sami saukin aiki ku kawo mana ziyara kinji Mairama. Zayyan dan gata ne saboda yana
zagaye da dangi masu kaunarsa saboda maraicin uwa. Da mahaifinsa ya amince min naso tun
rasuwar Alheran na dauke shi."
Hawaye ta ga dattijuwar tana gogewa shiyasa taji zuciyarta ta karye "In sha Allahu zamu zo"
Mairamu a ranar tayi kwanan farinciki da bakinciki duka lokaci guda. Soyayyar da ta samu daga
wurin dangin mijinta ta tsaya mata a rai tayi matukar farinciki. Sai kuma tunanin dangin Innarta da
babu wanda zata iya nunawa tace nata ne ta wannan bangaren. Sun manta da ita da shafin
rayuwarta saboda rashin uwa da tsanar da suka yiwa Malamijo akan rikon sakainar kashin da ya
yiwa 'yar uwarsu a gidansa.
Asubar fari aka fara tashi saboda masu shirin komawa. 'Yan Sumaila ne farkon tafiya aka bar Nene
zata zauna wanka idan sunyi arba'in su tafi Sumailan tare. Mutan Agadas ma kaf sun gama shiri
wai basa son dorawa Zayyan nauyi idan suka cigaba da kwanaki. Kawunnansa biyu ne a cikin
tawagar Ghoumar da Sidi. Shatara ta arziki suka yi masa kyautar kudi da irin abin amfani nasu na
can. Kamar kada su tafi haka Mairama taji har kofar gidan inda bus guda biyu zasu daukesu tayi
musu rakiya.
Daga nan gidanta ta koma tare da Yadikko da Salame su ma a ranar zasu wuce.
Manya akwai kaifin tunani da hangen nesa. Cikin kankanin lokaci Nene ta gane manufar Salame
akan Zayyan. Tasha mamaki ba kadan ba saboda a da tana yi mata kallon wadda zata iya sadaukar
da komai domin farantawa kanwarta. Ashe abin ba haka yake ba. Ta ciki na ciki ne. Jan bakinta
tayi ta tsuke bata tona ba sai dai ta jasu su biyun tayi musu fada akan sabon yanayin alakarsu.
Kallon Salame Nene tayi ta dauke fuska tare da janyo jakar kayanta tana shan kunu.
Nene tace "Salame idan ma da sabani na kula kece kike jansa. Tun zuwanki ina lura dake ko da
wasa wallahi baki dauki Radhiya ba."
Saurin kallon Mairama tayi don kuwa hakan ne. Mairama tuni ta gane shiru kawai tayi.
"Nene bana jindadi tunda nazo garin nan shiyasa. Mairama Allah Ya baki hakuri...shikenan ko"
tace a kagauce tana son fita daga dakin.
"Juna biyun shine zai sa ki kasa daukar 'yarki? Ki dai yiwa kanki fada don rayuwa bata da tabbas"
Mairama bata ma tanka ba ganin za ta rana musu wayo. Da zasu tafi Salisu ya kawo kudi ya bayar
a sayawa Radhiya kaya harda cewa inji mamanta Salame. Godiya suka yi masa sun san kuma kara
ce kawai yayi amma babu wani inji Salame.
Sun shiga gidan Nene ta goya Radhiya ta shige daki wai garin akwai sanyi. Ga gida mai daki daya
tana rufo kofar Zayyan ya rungume Mairama harda ajiyar zuciya.
"Taron jama'a ko?" Tace tana kokarin kwace jikinta kada Yadikko ta fito.
Murmushi tayi ta sunkuyar da kai ya dago habarta "dadina da mutum kunya. Yaci ace mun wuce
wannan matakin fa, ga 'yar soja can kina gani"
"Ni dai kazo ka tafi kada ta fito ta sameka"
"Na yarda"
Rungumeta ya sake yi sosai "Ina sonki Mairam, shigowarki rayuwata ya sanyani farinciki mara
misaltuwa. Karo na farko naga da dangin Innata su ka zo da yawa haka saboda ni. Kuma duk a
dalilinki ne da kyautar Alheran da kika yi min. Nagode"
"Ina fatan Allah Ya bani ikon cigaba da kyatata maka Sojana. Kayi min komai a rayuwata. Ka
rabani da kunci da bacin rai. Ka zame min miji, aboki kuma dan uwa"
Kashe mata ido yayi "ina ma daga ni sai ke a gidan nan kike wannan kalaman"
Ta gano manufarsa ta shiga dariya a hankali. Kofar dakin aka taba ya tashi a guje ya fice ita kuma
ta dake fuska kada Yadikko tace me suke yi.[7/25, 3:16 PM] Sameee💖💖: ***********
Kyakkyawar kulawa da gyara Mairama take samu daga wurin Nene Marka. Ita da Zainab da
Mami shakuwarsu sai gaba take kara yi. Idan kaga Awwab baya gidan to makaranta ce ta tsare shi
ko dare ya tafi yayi bacci. Amma kullum yana wurin Mairama da kanwarsa Radhiya. Zahra da
Fauziyya suna shan gori yayi ta cewa su Antinsu bata kawo baby ba har yanzu. Idan ya fadi haka
Zahra sai tace ai nata cikin ya kusa fashewa ne su ma bazasu bari ya taba musu baby ba.
Zayyan ba karamin kewar matarsa yake ba. Ko yaya Nene ta dan bada wuri sai ya faki ido ya
rungumeta yana fada mata yadda yake kewarta da matsuwa ayi arba'in dinnan kowa ya huta.
Jaririyarsu Radhiya ta kara yin bulbul gwanin sha'awa. Idan kayi mata kallo daya sai ka rasa wa ta
debo cikin iyayen. Bafillatanar mahaifiyarta ko sojan babanta da yake surki tsakanin mutanen
Agadas da na Tureta. Yarinya ce mai matukar shiga rai musamman idan tayi murmushi gefen
kumatunta na dama ya lotsa. Awwab har yatsa yake sakawa a wurin don kawai tayi masa
murmushi.
Ranar da su ka cika wata biyu Zayyan ya kwashesu a motar haya sai Sumaila. Mairama bata taba
tunanin zata yi kewar gidansu ba sai yanzu. Sun isa yamma likis 'yan uwa ana ta tururuwar
ganinsu.
Malamijo yana jin isowarsu daga gona ya zari takalmansa ya yo gida. Fadi yake 'yarsa mai auren
soja ce ta iso tare da jikarsa. Abin arziki kaza guda ya bayar irin 'yar sati goman nan aka yanka
Yadikko ce da girki tayi musu shinkafa da miya.
Daki aka gyarawa Zayyan ya kwana. Da safe abin mamaki sai ga Salame wai bazata iya jiran su
iso gidanta ba tana kewar Radhiya. Mairama taji dadi balle da ta ga yadda take haba haba da
Radhiyan harda su goyo duk da ana hanata saboda nata cikin ya fara fitowa.
Zayyan dauke kai yayi saboda shige masa da take yi tana ta so ko magana yayi mata. Allah sai Ya
dauke hankalin Mairama daga garesu bata kula ba.
Kwanansu biyu sannan su ka wuce Balan a karkashin karamar hukumar Gaya inda gidan Nene
yake. Tana da kishiya guda daya mai yara shida. Maigidansu manomi ne babu wani kudi sai rufin
asiri. Irin kyautar da Zayyan yayi mata Mairama kanta tayi mamaki. Nene Marka harda kuka tana
masa godiya.
"Nene mune da godiya, Allah Ya saka da alkhairi. Idan ta sake haihuwa ke zaki dawo ko?"
Mairama ta tashi daga wurin da sauri saboda kunya. Nene tayi masa dakuwa tana murmushi "kuji
min dan kaniya, wato a gaban nawa kake rashin kunya ko Zayyanu"
"Fada nayi fa saboda kada ace wata daban ce za ta zo." Tare su ka yi dariya don ta saba da
barkwancin surikin nata.
Kofar dakin ta kalla ta tabbatar Mairama tana wurin kishiyarta sannan ta dan matso fuskarta babu
alamun wasa "Zayyanu nasan kana sane da son da Salame take yi maka"
Gabansa ne ya fadi ya dago kai yana kallonta da kallon kofa "Nene ki bar zancen nan, yau ko
Mairam zata fadi ta mutu bazan auri Salame ba. Matar da aure bai hanata nunawa mijin kanwarta
soyayya ba"
"Kafin muyi aure...don Allah bana son kowa yaji. Ni dai babu abinda ya taba hadani da ita"
Hankalinta taji ya kwanta "nagode Zayyanu. Ka rike min amanar Mairama. Ga maraici ga rashin
dangin uwa har yau mun rasa a wace rugar ma suke zaune. Duk tsiyar Malamijo yana ta kokarin
nemansu domin ya faranta mata. Salame kuma ka barni da 'yar banza. Idan ta nemi tada muku
hankali da kaina zan gyara mata zama don ba gagararmu tayi ba"
Kafin azahar sun koma Sumaila inda ta sake kwana biyu suka bar garin bayan ihsani mai tsoka da
ya yiwa Malamijo da matan gidan. Mairama har mamakin ina ya sami kudi haka takeyi saboda ita
tasan duka duka albashin nasu babu wata tsokar kirki.
Sun baro Sumaila tana sa ran za su wuce Sakkwato sai gani tayi sun shiga cikin Kano zuwa wata
unguwa yana yiwa dreba kwatance. Gaban wani gida zubin zamani a wancan lokacin mai kyau da
tsari tun a waje aka ajiye su. Mukulli ya dauko da ga aljihunsa ya bata yana dauke da Radhiya.
Kallon tuhuma take masa yayi murmushi da ka yayi mata alamar ta bude. Ba musu ta bude yana
cewa ta shiga da Bismillah. Farfajiyar gidan tana da dan girma daidai mota guda daya. Sai kuma
ainihin ginin wanda flat ne gidan. Yana gaba tana biye dashi zuciyarta da tarin tambayoyi har ciki.
Wani korido su ka fara bi a karshensa kofa take inda suka tarar da katon falo ga kofofi a ciki. Daya
bayan daya suke shiga yana mata bayanin. Kitchen, dakuna hudu, store da kuma bandakuna ko ina
da fenti amma babu kaya. Daki daya ne aka shimfide da leda ga katifa sabuwa da filo biyu sai
zanin gado a cikin ledarsa ko budewa ba'ayi ba.
"Gidanka ne nan?"
Zaunar da ita yayi ya mata bayanin kudin gadonsa da ya narkar a wannan gini domin inganta
rayuwar iyalinsa. Ya zabi zuwa Kano saboda gujewa fitina daga bangaren su Jume. Dama yanzu
matsanancin fushi suke yi dashi saboda an gama taron suna basu ga komai ba. Da Jume da tado
zance yace gida dai shima na mahaifinsa ne, idan basa son ya rabesu a raba gado ko dakin
mahaifiyarsa a bashi. Sunyi rigima ba kadan ba ya fito musu gar da gar dinsa a soja mara daukar
raini ko kadan. Suna ji suna gani dole suka hakura da haram din da suka kwallafawa rai.
Addu'a ta rinka jerowa yana amsawa daga nan yace to fa ta shirya jiya da ya taho cikin Kano
siyayya yayi musu yana so ko sati suyi a gidan kafin ya koma aiki.
Kitchen ta leka ya siyo karamin risho, tukwane biyu da yan kayan bukata. Wani sabon shafin
amarci su ka bude a gidan ga diyarsu a gefe tana samun kulawa. Wasa-wasa kwanansu goma sha
biyu sannan su ka fara shirin komawa Birnin Shehu. Duk yadda taso kuwa yaki kaita gidan
Salame don baya kaunar duk wani dalili da zai sa su hadu.
**********
Watansu biyu da komawa Zainab ta haihu. Sai dai ita a gidan iyayenta ta zauna su Mairama da
Mami ke zuwa kullum har akayi suna. Jariri yaci sunan kanin baban Hadir da ya rasu gabanin
haihuwarsa Ibrahim.
Rayuwar wadannan bayin Allah haka ta cigaba da tafiya cikin so, yarda da aminci. A kowane
mataki su na kokari wurin ganin sun tsayawa juna cikin dadi ko akasinsa. Da Salame ta haihu ya
barta taje ta kwana hudu a Kano inda ta rinka fuskantar Gadara da wulakanci daga wurin yayarta
ta. Da yake ta fara sabawa da wannan bakon hali sai ta daure zuciyarta don kada ayi batacciya.
[7/25, 3:17 PM] Sameee💖💖: ....ALLAH NA NASA
"Ummin Awwab me yake damunki ne kwanakin nan sai wata rama kike yi kamar wadda za'a yiwa
kishiya"
Dago kai Mairama tayi jiki a sanyaye "Mami ni kaina na rasa gane dalilin wannan rama. Kuma ke
shaida ce ina cin abinci sosai"
"Kinbi kin dashe kinyi fayau. Jiya ina ji baban Radhiya yana fadawa Hadir wai kinki bari ku je
asibiti. Baki ga yadda ya damu ba fa"
Mairama tayi shiru ita kanta ramar da take yi tana damunta. Dadinta ma dai Radhiya kullum kara
habbaka take. Suna wannan hirar Fauziyya ta shigo da Radhiya tana nishi anyi daukan rungumarni
mu fadi.
Kafin su shigo kukan Radhiyan ne ya isar da zuwansu. Mairama ta girgiza kai tana takaicin
wannan kukan banza na Radhiya. Tana jaririya babu ruwanta amma yanzu rigima da kuka ga fada
duk ta iya. Idan ta raina girman mutum ya dauketa sai yakushi tana doke doke duka wataninta tara
a lokacin. Zayyan dariya yake yace 'yar Soja bata daukar raini. Wasu lokutan kuma sunanta na
gaskiya yake kira idan yana jin nishadi. Har ta gane indai taji Alheran tasan babanta ne.
A cinyar Mairama ta ajiyeta ta kalli uwar tasa dariya. Zainab tace "kunji min mara kunya ko? Mu
da take gani kullum yanzu dariyar ma sai mun roka. Dadinta dai har Awwab bata yiwa"
Homework yake yi a gefe yana jin tsokanar da ake masa ya taso ya kinkimeta yana cewa "Ummi
wallahi tayi nauyi da yawa ki dena bata abinci"
Me zasu yi banda dariya kuwa. " to sarkin wauta, an taba hana mutum abinci saboda kiba ne?"
Cewar Mami
Shi dai bai ga aibun maganarsa ba ya dauketa gashi siriri sai tsayi da yake faman yi ya tafi dakinsu
Zahra. Kayan wasa ya baje mata yana cewa sai tace Ummi da Daddy. Gajiya tayi da wasan ta
soma rigima sai ya dauketa. Duk da haka kukan take masa ya sabata yana haki "gaskiya kin fiye
kuka Alheran dinnan"
Kamar taji me yace kuwa ta kai masa duka a fuska harda yakushi. Zafin da yaji a gefen idonsa na
hagu yasa shi sakinta tim a kasa ta fasa wata gigitacciyar kara. Zainab da Mami ke rige rigen shiga
dakin ya dafe gefen idonsa da yake jini ko ta kanta bai bi ba a kasan. Zainab tayi saurin daukarta
yayin da Mami babu tambayar ba'asi ta dauke Awwab da mari.
Shima kukan yake sosai Mairama ta taho ta rike shi murya na rawa ya nuna mata wurin "yakushi
na tayi fa"
"Sai kayi mata me?" Mami ta kuma tahowa kamar za ta doke shi.
Da karamar murya ya amsa "Faduwa tayi daga hannuna"
Takaici ne ya kamata kuma wai Mairama tana kare masa. "Bari Daddynku ya dawo sai na fada
masa" ta koma ga Mairama rai a bace "ke kuma kin karbi yarinyar nan kin rarrasheta ko kuwa"
Mairama tace to yau abin harda ita. Karbarta tayi ba shiri an tabo Mami yau ta fara shayar da ita
amai ya taso mata da gudu tayi bandaki. Abu kamar wasa sai gata ko tashi da kafafunta ta kasa.
Mazajen nasu ba ma sa cikin barrack din an turasu wani training cikin jeji sai sunyi kwanaki.
Dalilin ma da suke tarewa gidan Mamin kenan.
Abu na taron mata tare su ukun da yaransu suka tafi asibiti. Ciki aka gano a jikin Mairama har
wata uku. Kuka ta saka ganin Radhiya duka duka nawa take. Kuma ga kunyar ace yarinya bata
shekara ba ta sake ciki. Su Zainab kuwa sai murna. Mami tace mata ya kamata kafin su Zayyan su
dawo ta yaye Radhiya saboda cikin yana wahalar da ita ga tsotso. Da yake akwai kawaici a daren
ta tafi ta barwa Mami ita sai kayanta da ta turo Awwab dasu.
Yadda Mami ke bawa Radhiya kulawa ya kara tabbatar musu da cewa zaman mutumci da amana
ba sai da jini ba. Da ita da yaranta duk sun tare a jikin Radhiya an bar Mairama da uban laulayi sai
Zainab dake sintirin zuwa wurinta.
A kwana na biyar su Zayyan su ka dawo. Sun sha wahala sosai sai dai kuma aiki ne na sabo. Da
murnarsa ya shigo yana kiran 'yar soja Mairama tace masa tana gidan Major ta tafi yaye.
Hannunsa ta kama suka zauna ta dora kanta a kafadarsa "Sojana bani da lafiya ne"
Ya dago kan ta "na sani kuma asibiti zan kaiki, amma meyasa baki bari na dawo ba sai yaye?"
"Me?"
Sungumarta Zayyan yayi yana murna "Mairam kice Tureta ya tureki a karo na biyu"
Salati ta hau yi tana mai jin kunyarsa shi kuwa ko a jikinsa. Dama ta samu sai sabon amarci don
ma laulayin yana hana sakewa. Sai da Radhiya ta cika kwana goma sannan Mami ta dawo da ita
da kaya da tarkacen wasa.
******
Bayan wata guda da yaye Radhiya wata litinin Mairama tana gyaran wake za ta yi alala da rana
Zayyan ya shigo ba lokacin dawowarsa ba. Hannunta ta dauraye ta fito wurinsa.
Mikewa yayi akan doguwar kujera yana riko hannunta ta zauna a wurin da ya matsa mata.
"Alala zanyi"
Hancin nasa ta riko tana dariya "nasan ba ka ci, banyi tsammanin dawowarka yanzu ba ne. Sai na
canja abincin, waken...."
Kofar falon da taji ana bugawa da karfi kuma kamar muryar Zainab yasa bata gama fadin me tayi
niyar fada ba. Da sauri ta bude kofar tayi baya a tsorace ganin Zainab tana rusa kuka kamar ranta
zai fita ga Hadir a bayanta dauke da Ibrahim.
Hanya ta basu su ka wuce cikin falon Zayyan ya hada ido da Hadir yayi murmushin dole jikinsa a
sanyaye yace "ka fada mata ne?"
Zainab kuka take har lokacin Mairama ta rude sai tambayarta take me ya faru. Hadir take kallo
tana jiran bayani daga baya tace "ko dai aure za ka kara?"
"Wallahi dama auren ne Ummin Awwab da ya fiye min da wannan tashin hankalin"
Dif Mairama tayi sakon yana sauka a kwakwalwarta. Liberian da babu wanda yake cikin barikin
da bai san tashin hankalin da suke ciki ba. Nigeria ta shiga cikin lamarin tana basu gudunmawar
sojoji domin a kwantar da tarzoma. Dibansu akeyi lokaci lokaci ana turawa. Rawa taji jikinta yana
yi ta kasa tsayuwa da kyau sai da Zayyan ya riketa ya zaunar da ita a kusa dashi.
Abinda ya dawo dashi gida da wuri kenan ya kasa fada mata. Kai ya gyada kawai ta kalli yadda
Zainab ke kuka itama ta soma hawaye. Duk wata kalmar rarrashi da ban baki abokan sun lalubo
domin kwantarwa matansu da hankali. Zainab ta fi gigicewa itama tana son Hadir fiye da zato da
tsammani. Da kyar ya samu ta tashi su ka koma gidansu aka bar Zayyan da Mairama.
Ranar bata iya yin girkin ba jikinta yayi mugun sanyi. Abincin Radhiya ma sai shi yake bata. Ita
kwanciya tayi a daki kawai tana zubar da hawaye. Bai ce mata komai ba sai cikin dare ya kwantar
da ita a jikinsa yana rarrashi
"Mairam nayi zaton zaki bani goyon baya sosai har naje na dawo mu koma Kano"
Tsokanarta ya fara yi don ta sake "tafiyar wata uku ce fa, zan dawo kafin ki haihu in Allah Ya
yarda"
Sake shigewa jikinsa tayi yana jin cikinta da ya fara tasawa ya dora hannu a kai "Ashe haka ki ke
so na ban sani ba?"
Shiru tayi ya cigaba da maganarsa shi kadai "a iya zamana dake Mairam bani da wani abu da zan
fada akanki sai alkhairi. Duk abubuwan da na rasa a baya zuwanki ya wanke min kuncinsu.
Shiyasa nake matukar son ki. Wannan tafiya da ina da yadda zanyi ko dai na tafi daku ko kuma na
hakura ne. Ina rokonki da ki karfafa min gwiwa naji dadin bautawa kasata."
Wani irin abu take ji yana mata yawo a jikinta. Idan a da tana tunanin tana son mijinta to a yau
sonsa yana neman ranta ne. Gani take kamar bazata iya jurar rashinsa a tare da ita ko da na kwana
daya bane. Ashe baka sanin mahimmancin abun da ka ke dashi sai yayi nisa da kai. Bata san
lokacin da bacci ya dauketa ba sai ajiyar zuciya da take ta saukewa.
Sai da ya tabbatar tayi bacci ya tashi ya dauro alwala. Yasan yaudarar kansa zaiyi idan yace zaiyi
bacci a wannan daren. Nan da kwana biyar zasu bar kasar, zai bar iyalinsa wanda basu dogara da
kowa ba sai Allah sai kuma shi da nauyinsu yake wuyansa. Yayi nafila raka'a goma tare da witri
sannan ya zauna yana jero addu'o'i. Motsin Radhiya yaji yayi saurin fita da ita daga dakin don
kada ta tashi Mairam yaje ya hada mata tea a feeder ta shanye. Yana jiran ta koma bacci yarinya
ido ya soye ta fara kiriniya. Bata tafiya sai rarrafe da mikewa. Biye mata yayi suna wasan. Sai
gabanin asuba ta bingire a jikinsa tayi bacci. Kan ta ya rinka shafawa baiyi zato ba sai hawaye ya
ziraro masa ya goge da sauri yana baiwa zuciyarsa hakurin cewa wata uku a wurin Allah kamar
kiftawar ido zasu zo su wuce.
**********
Gidan Hadir ma basuyi bacci ba don Zainab kwana tayi kuka. Mami da sauki tunda ba zuwan
Major na farko wurin rikici ko yaki kenan ba. Sai dai itanma kukan tayi don ba'a sabo da rabuwa.
Washegari harabar gidajen nasu kaf babu wata hayaniyar kirki. Sojoji ashirin ne zasu tafi a cikin
magidantan da suke wurin. Kowa yana gida tare da iyalinsa.
Bayan la'asar Zayyan ya dauki Mairam su ka je gidansu da gidan kawunansa da Mal Aminu ya
fada musu zaiyi tafiya. Kowa yayi masa addua da fatan alkhairi ban da Jume da bata dena jin zafin
rashin basu kudi ba. Duk da haka ya yi musu kyauta ita da su Maikudi tunda sunyi aure. Matan ma
a ranar sai da ya kai musu ziyara.
Sukuku su Mairam su ka koma babu walwala a tare dasu ita da Zainab. Mami ce tayi musu fada
akan idan sun cigaba da haka a wane yanayi suke so mazajensu su tafi. Sun ji maganarta don
kowacce sai da tayi kokarin gyarawa. Mairam dambun nama ta yiwa Zayyan gari guda sai da ya
dibarwa Hadir da Major. Ta kuma saki jiki tana bashi kulawa fiye da yadda ta saba.
Sauran kwana biyu su tafi tana goge masa khakinsa Radhiya ta fito daga daki da kafafunta a
hankali saboda rashin kwarin tafiyar. Murna ta kama Zayyan ya sunkuceta yana sumbatar
kumatunta.
" 'Yar soja ta girma, yau yawo zamu je tunda anyi kafa"
Kamar taji me yace ta rinka bangala dariya. Ajiyeta yayi zai chanja kaya su fita tasa masa kuka
"Daaadaa" yaji tace tana dago masa hannuwa.
A nutse ya juyo ya tabbatar shi take kira. Har yanzu hannuwanta take miko masa "Daaadaa". Ya
kalli Mairam ita ma mamakin yarinyar ya kamata. Awwab bashi da aiki sai koya mata Ummi da
Daddy wai dole sai tayi magana. Yau gashi ta kira mahaifinta dadi yasa yaji idonsa na alamun
zafin kwalla. Daukanta yayi ya shiga dakin su ka bar Mairam tana guga tana diga masa hawaye a
kayansa.
Ranar ashirin da daya ga watan Mayu na 1993 ne Giginya Barrack dake cikin garin Sakkwato ta
kwashi sojojinta za'a kaisu Lagos washegari su tashi zuwa Liberia ta ruwa.
Daren ranar ya kasance dare na soyayya, jaddada alkawura da kuma sabunta matsayi a zukatan su
Zayyan da iyalansu. Daga shi har Mairam babu wanda ya runtsa kuma hakan take a wurin Hadir
da Zainab da Major kansa da Mami.
Komai Mairam ce ta yiwa Zayyan hatta abinci a baki take bashi. Tayi ta daurewa kada tayi kuka
zuciyarta ta kasa daukan wannan lamari. Ko kadan baya son nuna mata damuwar da yake ciki
shiyasa ya fake da yiwa Radhiya wasa.
Jiniya mai sanar da su fito ce tayi kara sai da cikin Mairama ya murda kawai ta fashe da kuka iya
karfinta.
"Zayyan"
Tashi yayi ya rungumeta tsam a jikinsa "ashe kin iya fadin suna na"
"I love you Maryam Ali Gidado. Ki rike wannan a zuciyarki har na dawo. Nayi miki ajiya a kan
mudubi idan na tafi ki duba"
Hade bakinsu yayi tamkar ranar su ka fara haduwa yana jin karar jiniyar a karo na biyu ya saketa
ya dauki Radhiya.
"Daaadaa" tace tana washe hakoranta biyu dimple dinta ya lotsa ciki sosai.
Ita ma ya sumbaci kuncinta hagu da dama kafin Mairam ta farga ya fice daga gidan.
[7/25, 3:17 PM] Sameee💖💖: Daga tashar jirgin ruwa ta Apapa da ke dake Lagos su Zayyan zasu
tashi a jirgin ruwa zuwa babban birnin Liberia wato Monrovia. Akan tekun Atlantika jirgin nasu
ya dau hanya sai da suka wuce Benin republic wadda mu ka fi sani da Cotounou, sai Togo, Ghana,
Cote d'voire sannan Allah Ya saukesu a kasar da rikici na cikin gida ya kaurewa tun shekarar 1989.
Motocin yaki aka turo domin daukarsu. Zayyan da Hadir zuwansu sansanin yaki irin wannan na
farko kenan. Major Mustapha yazo ne a matsayin babban soja don ba wuri daya zasu zauna ba.
Shi Computer Engineer ne saboda haka aikinsa yafi karfi ne daga bayan fage musamman da a
wannan lokacin babu masu karatu irin nasa da yawa saboda karancin kayan aiki.
Cikin garuruwa ko kauyuka da rikicin yafi shafa ake watsa sojojin. Sune suke kwantar da tarzoma
da fitina idan ta taso a tsakanin mazauna garin da kuma 'yan tawaye.
Ranar farko su Zayyan da sauran da su ka zo tare da yawansu basu iya rintsawa ba. Daki ne kato
kowa da yalolowar katifarsa akan gadon karfe mai hawa biyu. Wasu kuma a kasa katifunsu suke
saboda rashin wadatar gadajen. Zayyan da Hadir a kusa da juna suka shimfida katifun da aka basu.
Shi dai tunanin Mairama da Radhiya yake yi. Ko me sukeyi a wannan lokaci? Tafiyar Radhiya ta
kara kwari a kwanakin da suka shafe a kan ruwa? Idan ya koma zata yi masa kyuya? Gajeren tsaki
yayi da wannan tunanin. Burinsa ace kowane mataki na rayuwar 'yarsa ya faru a kan idanunsa.
"Yadda ka san nayi tsuntsuwa naje na gansu na dawo" yayi maganar cike da kewa.
Muskutawa Hadir yayi ya gyara kwanciyarsa. Shi kuma Zayyan yayi rub da ciki ya rike fuskarsa a
tafukan hannunsa da ya tokare kansa dasu.
"Bansan yaya Zainab take yi da Ibrahim ba yanzu. Kusan wata guda yaron nan ba ya iya bacci sai
akan kirjina"
Dariya Zayyan yayi "kace akwai daru, don ma bai kai Alheran rigima ba abin zai zo da sauki."
Wani cikin wadanda suka tarar a sansanin yana daga gefe yana jin hirarsu ya soma dariya "kusan
kowa ranar farko sai yayi hirar gida"
Gwangwani ya dauka a kusa da shi ya bubbuga da hancin katuwar bindigarsa. Sai ga sojoji suna
tashi zaune wasu akan gado wasu a katifa. Kalilan ne masu bacci. Mutumin yace "kunga yau anyi
baki ku tashi mu san juna." Ya kalli bangaren da yawancin bakin nasu suke "babu wani abin debe
kewa a wurin nan sai hira da muke samun yi da juna cikin dare"
Na kan gado na dirowa na kasa na matsawa sai gasu sunyi da'ira sun zagaye katifar wanda yayi
maganar. Da gani zai girmi da yawansu. Kallonsa ya ga suna yi ya kada kafada.
Ihu wasu suka fara su Zayyan dai abin duka sabo ya zame musu. Duk wata hayaniya sun saba da
ita a irin training da suke zuwa. Amma wannan karon fa a filin yaki suke tare da sojojin wasu
barracks din da basu taba haduwa ba. Muryar mutumin yaji ya soma magana.
"Nine shugabanku a harkar abinci" sai sowa da tafi yayi murmushi "Chief cook kuke gani. Suna
na Captain Ogbonna Odili. Ina da mata Mabel da yara hudu a Enugu. Ogechi, Uloma, Nneka da
Kachiku muna kiransa Kachi. Kamar kowa a nan ina matukar son family dina. Musamman ma
Uloma saboda tana da kokari sosai a school. Yanzu zaka rubuta mata abu indai ta karance shi daga
farko zuwa karshe to ya gama zama. Da kuke ganina kudi nake nema domin na kaita wata babbar
makaranta a garinmu ta gifted children. Uloma is born to be a great doctor"
"So shall it beeeee" wasu suka amsa da ihunsu na sojoji. Capt. Ogbonna yana ta dariya ya cigaba
da hirar iyalinsa ana tayashi murna.
Bayan shi sai aka ce mutum daya cikin newcomers ya gabatar da kansa. Papa Dolapo ne ya fara
shima yana bayani ana dariya da kuma nuna tausayi musamman da yace ya baro matarsa da
tsohon ciki suna jinjina masa.
Zayyan sai ya tuna cikin jikin tasa matar ya daga hannu "I am next please, please"
Dariya suka sa ana tsokanarsa ya dake yana basu labarin Mairama da Radhiya "babban farincikina
kafin na taho Alheran ta iya kiran suna na"
"Fada mana ya take cewa" wani yace sauran na goya masa baya.
"Daaadaa"
"Kuma nima matata tana da ciki amma sai mun koma zata haihu In sha Allah. Sorry Papa Dolapo
kaine za'ayi ba kai"
Hadir yayi dariya yana cewa Zayyan yayi masa wayo "muna komawa da wata tara zaka ji Zainab
ta haihu"
Tafawa suka yi wani mutumin Adamawa Austin Bakari dan kabilar Chamba ya fara bada labarin
iyayensa tsofaffi wanda sun dora duk wani buri nasu akan cigabansa. Labarin iyayen nasa akwai
ban tausayi domin dukkansu guragu ne da basu da mataimaki sai shi kadai. Dan albashin nasa
shine cinsu shine shansu. Ya sanya sauran cikin yanayi na jimami kowa na fadin albarkacin
bakinsa sai su ka ji wata muguwar kara mai razanarwa.
Basu gama da wannan firgicin da ya sanyasu daukan bindigoginsu cikin sauri ba kuma sai ga daya
daga cikin masu patrol na wannan daren ya shigo bindigarsa tana kan saiti ya fada musu 'yan
tawayen da su ka addabi wannan sansanin nasu sun kawo musu hari.
Idan da suna jin wai-wai, yau ga su zahiri a filin daga. Harbi ne yake tashi ko ta ina suka firfito
kan kace meye wannan wurin ya kaure. Anyi musayar harsashi sosai duk da duhun dare sun sami
damar fatattakar mutanen har da nasarar cafke mutum daya.
Wani bacci dama babu shi a lissafi maza suna filin daga. Kwana ukun farko sunyi su ne cikin
rudani da tashin hankali. Da gasken gaske 'yan tawayen suke son korar sojojin Nigeria daga wurin.
Akwai wuraren da suke tsammanin samun nasara su janyo mutanen garin domin a hadu a ture
gwamnatin shugaba mai ci a lokacin. Rigima ta cikin gida a ganinsu mai zai kawo wasu baki da
abin bai shafa ba a matsayin peacekeepers.
Kafin wani lokaci su Zayyan sun kara gogewa da halin da suka tsinci kansu yanzu. Shine ya koma
yi musu limanci bayan tafiyar Abdulwahid Gbenga wanda ya kasance da shine limamin. Duk
daren da babu gajiya sosai a tare dasu suna zaman hira a daki ko a waje. Su kunna wuta su zagaye
wurin suna jin dumi saboda shigowar sanyi gadan gadan. Da safe kuma masu manyan mukami su
ke jagorantar training dinsu don ba zama.
Watansu daya da kwanaki annobar cholera ta shigo kauyen da yafi kusa da inda suke. Garin kai
taimako wurin fitar da marasa lafiyan zuwa asibiti a cikin gari wasunsu suka dauko ciwon suka
kawo musu.
Cikin kwanaki bakwai mutum tara sun kamu. Amai suke yi sosai da gudawa. Suna ta kokarin
neman agajin babban sansanin domin a kawo musu magunguna sannan a dauke marasa lafiyan
cikinsu zuwa asibiti amma abu yaci tura. Ba wai sakon bai isa garesu bane, yaje amma su ma suna
jiran command daga babbar headquarter saboda komai na soja bisa doka da oda ake yi.
Major Mustapha da ya ankara cewa sansanin su Zayyan ne ya matsa lamba sosai ranar da za'a kai
musu maganin bayan kwanaki shadaya da fara cutar yabi bayan ma'aikatan lafiyan cikinsu. Su ma
din sojoji ne amma hannuwan rigarsu daga dantse akwai wani farin abu da yake nuni da alamun
cewa su likitoci ne.
Major Mustapha har yanzu bashi da magana sosai amma ya damu kwarai da kannen nasa Zayyan
da Hadir. Motarsu ta iso sansanin a daidai lokacin da Zayyan yake limancin sallatar gawar Papa
Dolapo wanda yayi ta fama da cutar ta amai da gudawa na kwana uku kafin rai yayi halinsa. Jikin
Major yayi sanyi haka na likiticin da suke tare dasu. Zagaye sansanin nasu akayi da wasu irin
wayoyi masu kaifi aka rubuta musu QUARANTINE da manyan harufa. Ma'ana an kebesu daga
shiga ko fita har sai an sami kyakkyawan tabbacin cutar babu sauranta a tare dasu. Ana gudun su
sanyawa wasu sojijin ko kuma su sakawa mutanen wani kauyen garin kai taimako.
Likitocin kadai aka bari suka shiga suma sun rufe jiki sosai da wasu kaya hatta fuskokinsu ba'a
gani. Sunyiwa kowa allura sannan aka shiga bawa marasa lafiyan taimakon da ya dace. Ta bayan
wayar suke magana da Major yana tambayarsu halin da suke ciki. Nuna masa suke yi babu wani
abu lafiya kalau suke.
Ta'aziyar Papa Dolapo yayi musu wanda aka saka gawarsa a cikin motar da zasu koma da ita nasu
sansanin. Idan sunyi sa'a za'a bari gawar ta koma Nigeria. Idan basuyi ba kuma to a nan za'a binne
shi iyalinsa su dau hakuri.
"Shekaranjiya da aka toro wani troop din wannan wasikar tazo. Ta Lt Badmus ce"
Wasikar ya dago musu kowa jiki a sanyaye domin Papa Dolapo ne Lt Badmus.
Major Mustapha ya kara da cewa "duk da ban bude ba amma an fada min matarsa ce ta haihu.
Zayyan makotanku ne ko?"
Kai ya gyada ya kasa cewa komai ya juya ya bar wurin zuciya tayi nauyi.
Sai da ya ga sun shiga cikin wurin da yake mazaunin dakinsu ya koma motar da ta kawusu suka
bar wurin.
**********
Rayuwar matan da mazajensu basa nan a barikin babu dadi. Ci da sha bai yanke ba tunda ana basu
albashinsu to amma fa kowacce kullum kwanan duniya da fargaba take kwana matsawar ba
mijinta ta gani ya dawo ba.
Mairama, Mami da Zainab dauriya suke yi kowacce tana son nuna ita ma jarumar kanta ce mai
hakuri da juriya. A gefe daya basu fasa yiwa mazajensu addu'a da fatan alkhairi ba.
Awwab kusan ya dawo gidan Mairama da zama. A nan yake kwana idan ya dawo daga makaranta
ya lalace wurin wasa da Radhiya. Sunyi shakuwar da har Mairama tana tabawa kyuya musamman
idan zai fita. Kyalesu take yi tana fama da cikinta don ma laulayin yayi sauki yanzu.
Awwab ya fita da Radhiya sun tafi wurin Mami sai Mairama ita kadai a cikin gida. Hayaniya ta
soma ji daga waje ta yafa mayafi ta leka. Can ta hango Zainab da wasu matan da suke tare sun
zagaye wata. Fitowa tayi cikin sauri jin kamar ana kuka.
"Innolillahi wa inno ilaihi raji'oon....Oko mi tikú" kuka Maman Dolapo take tana tumani a kasa ga
danyen jego.
Mairama ta tsorata da yanayin da ta ganta, ta taba wadda ta fi kusa da ita "what is wrong with her"
Ita ce amsar da ta doki kunnenta taji gabanta ya yanke ya fadi. Zainab ta matso kusa da ita tana
fada mata wai yanzu aka sanar dasu rasuwar tasa. Cholera ce ta kashe shi Zayyan ne ma ya sallace
shi, sannan anyi masa sutura a can kasar.
Kuka su ka taya Mama Dolapo aka kaita cikin gidanta. Bayan kwana biyu sai ga 'yan uwanta da
yayan mijin suka zo daukansu ita da yaranta guda hudu zasu koma Akure. Ranar ma wani sabon
kukan ne ya barke a tsakaninsu domin da yawa sun sani da wahala su sake sanya juna a ido har
abada. Maman Dolapo ta tafi ta barsu da kewa da kuma fargabar labarin wa zasu sake samu kuma.
**********
Jaruman kasarmu suna can suna aiki tukuru bisa umarnin da kasa ta basu na wanzar da zaman
lafiya a daya daga cikin kasashen gamayyar ECOWAS.
A yayin da magidanta suke tashi da safe su je ofishoshinsu yamma na yi su koma gida ga iyalansu,
su ci, su sha mai kyau, su kalli matansu da 'ya'yansu su ji dadi wadannan sojoji suna cikin dokar
daji suna fama da cizon sauro da wasu nau'in kwarin, rashin abinci mai gina jiki, karancin
tsaftataccen ruwa balle ayi maganar wanka kullum da sauransu. Masu aure a cikinsu suna kewar
matansu amma babu halin kasancewa dasu.
Yau da gobe kunnuwa sun saba da jin harbi da karar tashin bomb. Da idanunsu suke ganin 'yan
uwansu, abokansu harsashi ya huda wani sassa na jikinsu sun mutu a take. Ko kuma bomb ya tashi
dasu kana kallon mutumin da kuke tafiya kuna hira dashi ya tarwatse gabobin jikinsa sun watsu ko
ta ina.
Jaruman nan sun yarda sun aminci su sadaukar da rayukansu a duk lokacin da kasa ta bukata
domin zaman lafiya da kwanciyar hankanlin al'ummar kasarsu. Babu ruwansu da addini, kabila ko
wata al'ada. Sun hadu akan abu daya ne wato TSARO na rayuka da dukiya.
A yayin da wahala tayi wahala, anga jiya anga yau a fanin rashin makusanta ko a kama mutum a
sansanin abokan gaba a gana masa azaba domin ya fadi wani sirri da za'a iya cutar da nasa 'yan
uwan sai ka ga zukatansu sun bushe ana yi musu kallon mutane marasa tausayi da imani. Sai dai
abubuwan da idanunsu suka gani da wanda kunne yaji wani fa har ya bar duniya bazai taba
kusantar abu makamancin wannan ba.
Jarumanmu ababen alfaharinmu, sadaukanmu da babu albashin da kasa zata basu da zai wanke
ciwuka na zahiri da badini da suke dawowa dasu daga filin daga. Ga kuma iyalansu a yashe
madogaran nasu, bangon jinginar nasu basa nan.
Wata hudu da tafiyarsu Zayyan sun fara jiyo kamshin komawa gida wata rana da yamma gari ya
hade yayi bakikkirin ruwa zai iya saukowa a kowane lokaci wani mutum yazo wurin gaje gaje
dashi da shiga irin ta mutanen wani kauye a kusa dasu. Jikinsa duk raunuka yace 'yan tawaye sun
yiwa garinsu kawanya suna harbi kan mai uwa da wabi.
Sun riga sun san mutanen suna yin haka shiyasa su ka shiga motarsu ta yaki su ka durfafi kauyen
da hanzari. A bakin wurin da yake kamar gate dinsu ne su ka hadu da motar su Major Mustapha.
Ya fake da aiki ya taho ganin kannensa.
Duk da bambancin matsayi bai hana Zayyan zuwa ya rungume shi ba. Major yayi turus yana
cewa.
"Stand at attention Lady"
Zayyan ya kara gyara fuska sai dai dole dariya ta kwace masa. Karar bomb suka ji mutumin da ya
kawo rahoton yace ‘yan tawayen sun kai mota shida. Su Major Mustapha sai kawai su ka bisu.
Sai da suka yi rabin tafiya kawai babu zato babu tsammani sai tashin bomb suka ji a gabansu ga
ruwa ya fara sauka. Mutane ne suka fara bullowa ta tsakanin bishiyu da yawa ba na wasa ba sun
zagayesu. Babu wata mafita sai fitowa suka yi suna musayar harsashi ga wuta motarsu ta kama
saboda tankin mai da aka harba.
Bayan wani lokaci a cikin wannan yanayi ruwa mai karfi ya soma sauka kamar da bakin kwarya a
cikin jejin gari yayi duhu baka ganin komai sai tashin kura, hayaki da wutar da ruwan bai gama
kashewa ba. A gefe guda kuma Zayyan da Hadir ne suke gudun ceton rayukansu sakamakon
bomaboman da suka tashi a wurin har uku ga harbin bindiga da bazasu iya tantance takamaimai
daga ina yake fitowa ba.
A motocin yaki uku suka fito banda babbar range rover da suka ciko ta su Major Mustapha. A
lissafe sun kai mutum ashirin da takwas amma su biyun suka rage wanda kusan da taimakon
Zayyan ne Hadir bai mutu ba. Duk inda ka juya gawarwaki ne kwance cikin ruwa da jini. Kallo
daya zaka yiwa wurin zuciya ta tsinke kaji inama dai mafarki ne. Duk mai imani bazai so koda
makiyinsa ya tsinci kansa a wurin ba. Suna cikin wannan jeji dumu-dumu a tsakanin abokan gaba.
Hankulansu a tashe kunnuwansu basa jin komai sun dode saboda karar bomb ya yi musu karfi.
Zayyan ne ya hango Major Mustapha wanda a bisa la'akari da matsayi shine shugabansu a wannan
fitar. Mutumin da yake tsananin mutuntawa kwance yana daga hannu. Baya yayi da sauri Hadir
yayi masa kallon mamaki don bai iya ganin komai shi saboda karfin ruwan "kada kace min
komawa zakayi? Kazo mu bar wurin nan don Allah"
Kallon Hadir yayi ya sake kallon Major din ya koma gareshi a guje. Dago shi yayi da zafin nama
sautin harsashi yasa shi komawa ya kifa a kansa suka fadi tare. Wata siririyar kara Major
Mustapha ya saki mai cike da tsananin azaba wadda ta saka shi kai duba gareshi. Wani
mummunan firgici ne ya saukar masa ganin kafar Major din ta dama a gutsire bomb ya tarwatsata.
Zuciyarsa ce tayi nauyi ya soma kokarin daga shi domin su gudu.
Wata damka yaji ya kai masa ruwa yana wanke musu fuskoki "Lieutenant get out of here"
Bai saurare shi ba ya ciccibe shi duk da cewa ya fishi girma sosai ya saba shi a baya. Ture shi yaji
yana yi yana dan dake muryarsa "this is my final command to you Tureta. Go!"
Sojoji sun horo da tsananin biyayya ga na gaba amma wannan karon bazai bi ba. Gudu ya soma yi
dashi suka nufi inda Hadir yake tsaye hannunsa na zubar jini sakamakon harbinsa da akayi suka
soma yankar daji.
Cak ya tsaya ya dena tafiya har Hadir yana cewa "muje mana"
Gabansa ke lugude ya kalli kafarsa ya dago a razane "Karbe shi ku bar wurin nan"
Wata ajiyar zuciya ya sauke kafin Hadir ya karbi goyon duk da shima yana da raunuka. Matsawa
yace suyi nesa dashi sannan ya dago idanunsa da suka jike da hawaye sosai. Kamar mai rada yake
musu bayani.
"Bomb ne"
Su biyun duka suka kalle shi a gigice. Bai nuna damuwa ba ya cigaba da magana hawayensa suna
tona asirin firgicinsa. Motsi kadan zaiyi bomb din wanda aka binne cikin kasa ya tarwatsa shi.
Daya bayan daya yake kallonsu
Abinda Major ya dade baiyi ba ya soma shima sai kuka duka su ukun babu mai rarrashin dan
uwansa.
Kafarsa ce ta danyi rawa cikin karaji yace su bar wurin. Ba yadda suka iya dole suka bar wurin a
guje zukatansu suna kuka idanu na hawaye. Basuyi nisa sosai ba suka jiyo muryarsa mai dadin
sauraro idan yana yi musu limanci.
Kuka ya fashe dashi sosai a hankali ya soma karanto kalmar shahada yana ji a ransa wannan ma
dama ce da Allah Ya bashi.
Sunyi gudun rabin kilometer suka ji wata gigitacciyar kara wadda tasa su biyun faduwa su ka
gangara kasan wani katon rami. Kafin su kai kasansa daga Major Mustapha har Hadir tunaninsu
yana ga Zayyan Muhammad Tureta. Zayyan sarkin barkwanci, mutum mai tsananin so da kaunar
iyalinsa da basu da wani wanda zasu jingina dashi suji dadi idan ba shi ba ya mutu a bakin aiki
bayan yayi matukar kokari wurin tseratar da rayukansu.[7/25, 3:18 PM] Sameee💖💖: BAYAN AWA
TALATIN DA BIYU
Mutumin da ya kai rahoton karya ga rundunar su Zayyan shine durkushe a babban sansanin da su
Major Mustapha suke. Kuka yake kamar karamin yaro ga sojoji sun tsare shi babu wasa a
idanunsu.
Mutumin ya daga idanunsa jajir ya sake maimaita musu cewa yan tawaye ne suka kamashi. Sunyi
masa mugun duka sannan aka umarce shi da yaje ya san yadda yayi ya kawo sojojin Nigeria
wannan wurin. Idan baiyi ba garinsu gabadaya zasu tasa. Tsoro ya sanya shi cika umarni. Amma
suna zuwa da ya ga me ake yi ya gudu. Shine yazo nema musu agaji duk da yasan da wahala a
samu mai rai cikinsu.
Yana rufe baki wani zuciya ta debe shi ya buga masa kasan bindiga a keya ya fadi sannan ya bishi
ya rinka duka da kafcecen takalminsa. Da kyar aka rike shi kowa ya sani akwai kaninsa uwa daya
uba daya a cikin wannan sansanin.
Motocinsu suka cika da makamai suka tafi tare da wannan mutumin. Daga nesa suke hango sauran
hayaki ga kauri ya karade wurin. Dirgowa suka shiga yi daga motocin suna gudu har suka je
wurin. Su din sojoji ne fa jaruman maza amma hankulansu sunyi mumminan tashi da ganin
wannan kisan gilla da aka yiwa mutanensu. Binsu suka rinka yi daya bayan daya wadanda jikinsu
yayi alamun harbi ne kawai likitocin cikinsu suna dubawa ko akwai masu rai. Basu yi dacen
samun ko daya ba. Duk da haka shugaban tawagar yace su bazu cikin dajin babu mai tafiya sai sun
tabbatar ba'a bar kowa ba.
Mutum biyu ne suka bi hanyar da su Zayyan suka wuce cikin sa'a sai gasu a bakin kwazazzabon
da Major Mustapha da Lieutenant Hadir suka fada. Suna hangosu daya ya dira ciki dayan kuma
yana daga waje ya fara kiran ga wasu gawarwarkin a nan. Sai dai me, yana juya Major Mustapha
yaji yayi wani irin gurnani na azabar ciwo. Ya zubar da jini ba kadan ba wurin da kafar ta cire ya
kumbura suntum ta soma yin kore. Ihu yasa yana kiran suyi sauri wannan yana da rai don bai ma
gane shi ba.
Ya koma ya juya Hadir. Mamaki karo na biyu, shima da ransa saboda bugun zuciyarsa da yake a
raunane amma baya motsa komai na jikinsa. Sauran sun zo an taru an fitar dasu cikin sauri suka
isa sansanin inda aka wuce dasu bangaren kula da lafiya. Daki ne madaidaici da 'yan kayayyakin
taimakon gaggawa da abinda ba'a rasa ba.
Komai cikin sauri ake gabatar dashi domin alamu sun nuna su biyun sun galabaita fiye da zato da
tsammani. Anyi nasarar cirewa Hadir bullet a hannunsa sai dai buguwar da yayi wanda suke
tsammani a kansa ne har yanzu bai motsa ko da yatsa ba. Babu kayan gwaje-gwaje sosai da zasu
iya gano ainihin matsalarsa.
Major Mustapha shima an gyara wurin da kafarsa ta cire. Bayan allurai da ruwa da ake kara masa
babban likitan Major Dalhatu ya tafi ofishin ogansu gaba daya a wurin. Izinin shiga ya nema ya
tsaya a kame a gaban Colonel Fredrick Madueke.
"I am trying to reach the HQ at Monrovia Captain . We need to fly them back to Lagos"
Captain Dalhatu ya juya ya fita bayan ya sara masa. Yasan Lt Col Madueke akwai tsantseni.
Bazaiyi saken da rayuwar wadanda suka tsira zata salwanta ba a nashi bangaren.
Kwana daya, biyu, uku, hudu....shiru headquarter bata turo helicopter da suka roka domin a kai su
Major airport din Monrovia ba. Lt Col Madueke kullum yana magana da headquarter sun ce suna
jiran feedback daga Nigeria. Abu yaci tura suka debesu da kansu a motoci ga gargada da komai
zuwa Monrovia din. Nan ma a basu dama ko izinin fitar dasu ya zama aiki. A haka sai da suka
kwashe sati uku ana abu daya. Hadir yana nan jiya-e-yau. Major Mustapha kuwa ya farka amma
azabar ciwon kafarsa tasa ya koma yana sumbatu. Dole yayi sambatu wurin ciwon nasa ya soma
fitar da ruwa mai wari saboda kwayoyin cuta da suka shiga ga rashin kayan aiki. Anyi rigima
harda nunawa juna bindiga tsakanin Capt Dalhatu da wani soja a headquarter din saboda rashin
daukar patients dinsa da akayi. A haka sai manya masu mukami ko wanda yasan wani shine abin
dubawa. Mu kasarmu har kullum wa ka sani wa ya sanka ce.
A rana ta ashirin da bakwai Allah Yayi aka dauki Major Mustapha da Lt Hadir zuwa Lagos.
Yanayin da suke ciki suna bukatar taimako na gaggawa sosai. Kai tsaye aka wuce dasu 68
Nigerian Army Reference Hospital dake Yaba a Lagos.
An yiwa Hadir gwaje gwaje karshe dai likitoci sunce kawai a jira ko dai ya tashi ko kuma rai yayi
halinsa. Idan da hali ana bukatar 'yan uwansa domin jinya da kuma fara biyan kudaden asibiti idan
ana son su cigaba da aiki a kansa. Buguwar da yayi a kansa sai ya farfado zasu san ainihin iya
damejin da tayi masa.
Major Mustapha kuwa aiki gagarumi yake bukata a rubabbiyar kafarsa. Ciwo wata guda ya ga
izaya ra'ayil aini har yanzu bai san waye a kansa ba duk da ya farka. Dungulmin kafar ke fitar da
tsutsa saboda rashin gatance musu da kasa tayi a lokacin da suke da bukata. Gasu da rauni ga
rashin kayan aiki a inda suke. Anzo kasar tasu kuma asibiti na bukatar makudan kudade domin su
yi masa aiki a yanke abinda yayi saura na kafar. Sojoji da basu kirguwa sun tafi da lafiya sun dawo
gidajensu da nakasa ta har abada. Shima dai an bukaci a nemo nasa iyalin domin kulawa dashi da
kuma kudin asibiti wanda gwamnati bazata iya daukar nauyi ba duk kuwa da cewa a kokarin bin
umarninta suka riski kawunansu a wannan hali.
BOYAYYUN JARUMAI (NA SARAWA MATAN SOJOJI)
Jiniya ce irin wadda aka kunna ranar tafiyarsu yau ma aka saki. Motoci manya na sojoji suka rinka
shigowa barrack din a guje zuwa bangaren ofisoshin manyansu. A can aka bada cikakken rahoto
game da mutuwar gabadaya sojoji da aka dauka a ranar tafiyarsu Zayyan daga Giginya Barrack da
kuma halin da Hadir da Major suke ciki.
Wuri ba sai ya kaure da hayaniya ba, manyan sojoji ana ta shige da fice suna samun cikakkun
bayanai. Tattaunawa ce tsakaninsu akan yadda ya kamata su bullowa lamarin. Masu aure cikin
wadanda suka tafin wurin tara ne sauran duk samari. Wasu ma basu dade da zuwa barikin ba.
Matan wadanda suke asibiti dai babu yadda za'ayi a boye musu. Bisa wannan dalilin aka buga
takarda mai dauke da bayanin halin da kowanne yake ciki za'a bawa matarsa.
***********
Mairama tana gidan Zainab taje kitso suna zaune daga bayan gidan wanda katanga ta karesu babu
mai ganinsu. Sannan an dan zarta bangon gidajen ta barin hagu da dama domin ya zama kariya
tsakaninsu da gidajen kusa dasu. Sai dai ba'a hade ginin ba zasu iya wucewa. Yawanci matan ke
amfani da wannan wurin domin ayyukan da suka fi karfin cikin gidan kamar suya da babbar
sallah.
Zainab tana yi mata kitson gefe Radhiya ce da Ibrahim an baza musu tarkacen wasa suna ta ihunsu
irin na yara da duniya ta yiwa dadi.
"Ai kallonki nake duk sati kitso, ni nan ina jiran muji kishin kishin din zasu dawo ne naje ayi min
famin (perming ko saka relaxer). Ya tafi ya barni da kitson ya dawo ya tarar dashi. Hum'uhm"
Dariya Mairama tayi "nima da kika ga na nacewa kitson bana son haihuwa da kai a tsefe ne.
Lokacin wannan yarinyar kan na kusa cizgewa don azaba"
Tafawa suka yi suna kyakyata dariya kowacce tana tuna nakuda da haihuwarta.
"Kin gansu tafiya daga wata uku an shiga na biyar ga ki haihuwa ko yau ko gobe" cewar Zainab
da 'yar damuwa a fuskarta.
Wannan dadewar tasu ta dami matansu sosai. Kowacce dai tana kokarin daurewa ne don kada su
rinka tadawa juna hankali. Amma a zahiri babu wadda bata kukan dare idan kewar mijinta da
rashin sanin halin da suke ciki ya dameta.
Radhiya baki ya bude ba laifi don akwai surutu. Zaman da take yi dasu Zahra shi yake kara bude
bakin. Ta dai fi likewa Awwab saboda yawo. Sai ya dauketa suyi ta karade barikin nan.
Yanzu ma 'yan takalmanta masu madauri aka sanya mata bayan an gama kitson tasa kuka ganin
sun doshi gida "Ummi, Amma wawo" nufinta a kaita wurin Hamma su tafi yawo.
"Hajiyar gantali ni dai na gaji. Kiyi fatan daga islamiyya ya biyo sai ya kaiki wurin Mami"
Tana jin sunan Mami kuma kukan ya karkata tana kiranta. Tana ta bata baki yarinya taki shiru. Ba
yadda ta iya dole ta kaita gidan. Mami tana cewa ta zauna tace gida zata tafi jikinta babu dadi.
Radhiya harda yi mata bye bye tace idan Awwab ya dawo yazo ya karbar mata kaya don tasan yau
ma ita kadai zata kwana Mami bazata bari a dawo da Radhiya ba.
Cikin dare bacci ya gagareta kamar yadda take ta fama 'yan kwanakin nan. Kullum cikin mafarkin
Zayyan take, watarana ta tashi da kuka wani lokacin kuma idan mafarkin yayi dadi ta tashi da
farinciki. Sai dai a can kasan zuciyarta tana fama da wani irin firgici wanda ta kasa gane dalilinsa.
Envelop din da ya bar mata ranar tafiyarsa ta dauko ta shafa amma har yau taki budewa. Tsoron
me ya rubuta take yi, karshe ma dai ta fadawa kanta idan ya dawo ya karanta mata da kansa.
Haka ta cinye daren a tunani baccin da kyar ya dauketa. Bayan tayi asuba ma komawa tayi abinta
ta kwanta. Wurin tara na safe ta ji bugu kamar za'a balle mata kofa. Haka ta taso da hijab a baibai
saboda sauri ta bude tayi karo da Christie. Itama makociyarsu ce tare da mijinta akayi tafiyar.
"Mama Radhiya e bi like say your sister don die ooo. She just knack her head for ground after one
officer wey I no know come give her letter"
Mata ta ga sun zagaye Zainab ga Ibrahim yana ta tsala ihu. Ashe a kansa ma ta fada bayan ta
karanta takardar Allah Yasa akwai mata a wajen suka dauke shi.
Da kyar Mairama ta durkusa a gabanta tana rike mata hannu "Zainab menene?"
Takardar ta iya mika mata kawai. Mairama tana karantawa itan ma sai kuka da tausayin Hadir.
Christie ta cewa ta shiga da Zainab gida tana zuwa. Hankali a tashe tana baza sauri ta tafi gidan
Mami don ta fada mata. A can ta tarar da wani mummunan tashin hankalin.
Mami ke kuka sosai tana ta hada kaya ta jibge akwatuna biyu a falon tana ta watsa kayanta da na
su Fauziyya a ciki.
Gabadaya yaran suna gefe kowa yayi tsit harda Radhiya da ta ga babu mai kula ta. Awwab bai san
me ya faru ba amma ganin mahaifiyarsa na hawaye shima yake tayata.
Mami na ganin Mairama taje ta rungumeta ta sake fashewa da kuka "Ummin Awwab na shiga uku,
ina zan sanya kaina"
Duk ta gama tsorata ta daure tace "addu'a zakiyi Mami ba kuka ba, komai yayi zafi maganinsa
Allah. Me ya faru?"
Hawaye ne ya cigaba da zuba a fuskokinsu Mami tace "Katsina zan tafi yanzu. Sai naje na ajiye
yaran in sanar dasu sai mu wuce Legas din"
Suna haka Zainab ta shigo ta goya Ibrahim da har yanzu yake kukan faduwarsu ta dazu tana jijjiga
goyon tana kuka. Mairama ce tayi mata bayanin me ya sami Major kuma. Su uku suka hada kai
suna ta kuka abin tausayi.
Kusan a tare Mami da Zainab su ka fuskanci Mairama "Zayyan fa?"
Dammm taji gabanta ya yanke ya fadi ta juya a guje ga nauyin ciki ga kafarta da take yawan
rikewa ta nufi gidanta. Tsoronta daya kada itama anzo sanar da ita halin da Zayyan yake ciki ba'a
sameta ba. Bata tarar da kowa ba ta tsaya tana ta haki tana jin kamar za ta amayar da abinda yake
cikinta a lokacin. Da jan kafa ta koma gidan Mami sun gama shiri ita da yaran.
"Zainab, Mairama...Allah kadai yasan ranar sake haduwarmu. Komai nawa ya danganta da samun
saukin Daddy"
"Amin" suka amsa sannan Zainab ta kara da cewa itama zata je ta sanar da nata iyayen ne domin a
aika Kano gidansu Hadir. Sannan a san yadda za'ayi a dawo dashi gida.
Ji suke kamar daga ranar sun rabu kenan suka yi ta kuka sosai. Radhiya da kyar aka rabata da
Awwab ta makale masa wuya tana ta ihun Amma.
***********
Gidan iyayenta Zainab ta wuce cikin kasa da awa guda ta isa. Bayan ta yiwa mahafinta bayani a
take ya taso babban wan ta ya bashi kudin mota yace ya wuce Kano gidansu Hadir ya sanar dasu.
"Zainab kinfi kowa sanin halin da nake ciki. Kudin da na bawa yayanki wallahi harda na cefanmu
na yau da gobe ne. Kasuwar babu kudi yanzu sai nayi huluna biyar ba'a sayi ko daya ba"
Shiru tayi wani hawayen yana sauko mata. Ita ta sani kuma bata boyewa iyayenta talakawa ne
fitik. A Kano ma iyayen Hadir ba wasu masu karfi bane. Sai dai sun fi nata sosai. Albashin Hadir
shine yake turawa gida kuma a haka yake yiwa iyayenta ihsani lokaci zuwa lokaci. Zuciyarta ta
gama tsinkewa da wannan bakon lamari a gefe guda kukan Ibrahim yaki tsagaitawa.
Mahaifiyarta ta karbe shi tana ta juya shi da shafa jikinsa ashe ya sami gocewar kashi ne a hannu
sakamakon faduwar da Zainab tayi a kansa. Babanta ya karbe shi ya tabbatar hakan ne yace ta
tashi su tafi gidan dori.
"Zainab kamar baki da ilimin Tauhidi? Ki fawwalawa Allah ki yawaita addu'a. Daga gidan dorin
zan wuce wurin kawunki ko Allah zai sa yana da abinda zai ranta min ko ni kadai ne sai na wuce
Ikkon. Kinsan babu yadda za'ayi na barki kije ke kadai baki san ko ina ba ga yaro babu lafiya"
Kai ta gyada kawai suka tafi gidan dorin aka gyara masa hannun. Ibrahim ya zama abin tausayi
don ya jigata ba kadan ba. Suna dawowa sai zazzabi da amai ya sarke shi ko hannu baya iya
motsawa da kyau. Zainab tayi kuka har taji babu dadi.A rana daya rayuwar wannan baiwar Allah
ta juye gabadaya. Miji yana asibiti a wata uwa duniya, amma babu kudin zuwa gareshi. Babanta
yace su jira yayanta da yaje Kano ya dawo. Idan iyayensa sun dauko shi sai ta tafi can ko da yaya
zai samu ya biya mata kudin mota. Yini kuka, kwana kuka haka ranar ta kasance mata.
***********
Gidansu Mami unguwa daya ne da na su Major Mustapha. Iyayensu maza su biyar ne a gidansu.
Baban Major ne na biyu nata kuma auta. Da suka tashi aure sai suka zauna a gidajen da katanga
kadai ke raba su.
Daga tasha bus ta hau zuwa unguwar tasu. Tana shiga layin ta hango babban wan iyayen nasu da
suke kira Alh Baba. Yayi shigar mutumci da babbar riga da farin rawaninsa irin na malamai.
Motarsa kirar Pigeout (pijo) zai shiga daya daga cikin yaransa zai kaishi unguwa ya hangota.
Dakatawa yayi don ya tabbatar da wace ce saboda ita da Usainarta sai kayi musu farin sani kake
iya tantance su.
Tana matsowa ya saki murmushi saboda daga yaranta ya ganeta masu kama da mahaifinsu
"Mutanen Shehu saukar kenan?"
Daga ita har yaran sun durkusa da niyar gaishe shi kawai ta fashe da kuka. Yaran ya kalla yasan
duk yadda akayi wani abu ya faru "Kai Muhammadu wuce ciki da kannenka" ya fadawa Awwab.
"Ke kuma muje" ya nuna mata hanyar gidansu Major.
Awwab kamar ya bita ganin tun a gida suke ta kuka amma tarbiyarsu tasa ya bi umarnin kakan
nasu. Ciki suka shiga matan gidan suna ta murna ana tambayarsu mamansu suka ce tana wurin Alh
Baba.
Basu sami baban Major ba sai Iya mahaifiyarsa. Alh Baba ya tura aka kira ragowar kannensa
sannan suka bukaci jin dalilin zuwanta tana kuka. Duk sun sani cewa ya tafi Liberia tunda yazo
yayi musu sallama. Tana kuka ta sanar dasu abinda takardar da aka bata ta kunsa. Gidan sai kuka
tamkar ance ya riga ya rasu.
Bayan dawowar mahaifin Major iyayen su kayi zaman shawara. An daidaita magana akan cewa
Alh Karami baban Mami da kuma yayan Major Mustapha da suke uwa daya uwa daya su ne zasu
tafi.
Mami ta kasa daurewa tana kuka, Alh Baba ya dubeta "kiyi hakuri Hassana. Su dinmu dauko shi
zasuyi a dawo dashi gida yayi jinyar a kusa. Legas tayi mana nisa. Idan munje da yawa bamu san
ina zamu kwana ba"
Ba haka taso ba ko kadan amma bata da yadda zata yi. Tana ji tana gani asubar fari suka kama
hanya a motar Alh Baba.
**********
Kwanaki biyar kenan da samun sakon da ya tada hankula a Giginya army barrack. Mairama ta
rame sosai a 'yan kwanakin. Radhiya ma bata samun kulawa yadda ya kamata saboda tun ranar da
suka tafi fargaba tasa ta fara nakuda a tsattsaye tana daurewa.
Rayuwa take yi mara dadi. Babu miji kuma babu wadanda suka zame mata tamkar 'yan uwa na
jini. Tarin fargaba ne ya cika zuciyarta da kokonto. Ta damu tasan halin da su Hadir suke ciki ga
kuma rashin sanin komai game da Zayyan ya sanya take jin kamar zata yi hauka.
A kwana na shida ciwo yaci karfinta ta daure taje ta buga kofar gidan Christie. Ita dinma duk
zulumi da fargaba sun cinyeta tana ta ramewa. Tana ganin Mairama a haka tasan nakuda ce. Gida
ta koma ta dauko zani ta saba Radhiya a baya sannan ta taimaka mata suka tafi asibitin sojojin
inda take awo.
Ta kwashe kusan awa shida tana fama banda wanda tayi a cikin gidanta kafin Allah Yasa ta sauka
lafiya ta haifi danta tamkar Zayyan yayi khaki don yafi Radhiya kama dashi sosai.
Likitocin sun bata kulawa yadda ya dace sannan aka kaita dakin da zata huta saboda wahalar da
tasha. Christie tace mata zata je gida tayi girki ta kawo mata don taji kwari. Matar akwai kirki
sosai ita ma. Radhiya ta sake dauka dama da tana ciki wurin haihuwa ta siyo mata fanke a 'yar
kasuwar gefen asibitin taci ta koshi ta debo ruwa a famfon waje ta bata.
Suna fita ta sake daukan jaririn sai kawai tasa kuka. Yaron da tayi fatan zuwansa duniya
mahaifinsa ya karbeshi yayi masa addu'a. Sai gashi ta haihu din a lokacin da bata da masaniyar
halin da yake ciki. Karin kukanta yau ta haihu babu kowa nata sai Christie da ta tsaya mata tamkar
'yar uwa. Mami da Zainab suna can lalurar mazajensu ta saka su a gaba. Yanzu ita wa take dashi
da zata tura a sanar da gidansu da gidan iyayen Zayyan. Tun tafiyarsa babu wanda ya tako ganinta
cikin 'yan uwansa ko da wasa. Me ya ja mata nesanta da 'yan uwanta da na mijinta da rashin zama
cikin mutanen da tasan sunyi tarayya a yare, addini da al'ada? Auren Soja ta bawa kanta amsa.
Sojan ma Zayyan wanda idan za'a sake bata zabi tayi rantsuwa har ranta shi din a sojansa zata sake
aure. Tana sonsa kuma tana alfahari da aikinsa kamar yadda yake yi shima.
Tunani ta zurfafa tana yi akan rashin sanin yaya zata yi labarin haihuwarta ya iske danginsu.
Lokacin Radhiya shi yayi komai abinsa. Yanzu kuwa komai ya dawo gareta.
Kan jaririn ta shafa tana hawaye "Daadaa yaci burin ganin zuwanka duniya ko suna bai yarda mun
zaba ba saboda yace yana son yayi yiwa jaririnsa huduba da kansa"
Yaro yana baccinsa cikin kwanciyar hankali ta kwantar dashi a gefenta daga jikin bango tana shafa
shi a hankali.
"Sojana ka bar min amana mai nauyi. Baka fada min yaya zanyi ba idan baka dawo da wuri ba"
Kuka ta shiga rerawa a hankali tana jin wani matsanancin ciwon kai. Kwanciya ta gyara a gefen
dan ta lumshe idanunta ta baiwa kofa baya.
Tana ji likitoci biyu suka shigo dukkansu sojoji da nos guda daya. Wanda ya karbi haihuwarta ya
yiwa dayan bayanin cewa ta zubar da jini kuma jininta ya hau kada a sallameta sai gobe.
"Na fahimta Dr. Ina file din nata?" Ya tambayi Nos ta mika masa.
"Matar Lt. Zayyan Tureta ce? Sune last week akace gabadaya unit dinsu...."
Wanda ya karbi haihuwar yayi saurin sa hannu akan lebensa yana magana a hankali harda juya
harshe zuwa turanci a zatonsu bacci take, kuma kana yi mata kallo daya ka ga bafillatana wadda
ake musu kallon basu da wani ilimin boko sai kiwon shanu.
Mairama taji gabanta ya fadi wani abu yana mata yawo a jiki tun daga kai har tafin kafa, sai ta
daure ko motsi bata yi ba. Nos din ta kalli bayanta da tausayawa a hankali tace.
Basu san daga ina ba sai ganin Mairama suka yi rike da kafadun Nos din idanunta a rufe cikin
karaji take tambayarta "what happened to my husband?"
Kallon kallo suke yi sai taji gabadaya duniyar tana son kife mata. Durkushewa tayi gwiwoyi a
kasa tana kallonsu tamkar wadda ta sami tabin kwakwalwa.
Tashinta yazo musu a bazata haka fahimtar turancinta shiyasa suka kasa bata amsa kai tsaye.
Shirunsu kadai ya isheta amsar da take nema da yanayin da taga sun shiga na tausayinta da tsoron
fada mata gaskiya.
"Kinga ki kwantar da hankalinki idan kinji sauki za'a fada miki komai"
Murmushi tayi mai sauti tana ja da baya da baya har ta kai jikin bango ga hawaye tana zubarwa
kamar ruwan famfo "da hankalina fa, nasan abinda nake tunani hakane. Innalillahi wa inna ilaihi
raji'un. Ya Allah....ahhhh. ....kirjina..wayyo Allah.. Ka jikanka Sojana"
Likitan da yazo zai canji wancan aiki ya dan matso kadan "kizo ki zauna...uhmm"
Jaririnta kawai ta dauka ta saka shi a kafada tana cigaba da kukanta tana cewa "tun yaushe ya
rasu?"
Basu iya cewa komai ba tayi hanyar kofa suna kiranta taki tsayawa. Sai dai kafin ta fita jikinta ya
soma rawa likitan da yafi kusa da ita yayi saurin karbe jaririn ta fara neman faduwa tana wata irin
jijjiga ga jini ya balle mata.
Nos da daya likitan ne suka kamata aka dora akan gado suna neman ceto rayuwarta.
[7/25, 3:19 PM] Sameee💖💖: Kwana biyu da rabin wuni Mairama tayi kafin ta gane inda take da
babbar jarabawar da ta tunkaro rayuwarta. Ta farfado da misalin uku na rana washegarin ranar da
ta haihu. Idanunta a rufe suke amma tana iya jiyo maganganu kamar ana fada. A hankali ta fara
fuskantar me ake cewa wanda yayi sanadin fitowar hawaye daga idanunta, kuma har lokacin a rufe
suke.
"Ni dai na fada miki gobe zan tura Rayyanu yaje garinsu ya sanar da iyayenta su zo su dauketa
don bazan iya jigila ba."
"Haba Maikudi kai kuwa baka ganin ga danyen jego ga rashin lafiya. A barta ta huta mana"
Gwaggo Ladi da tayi maganar ya kalla darajar mijinta Mal Aminu ya kasa bata amsar da yayi
niyya. Wani dan tunani yayi ya kara tabbatarwa gara yabi komai a hankali don samun biyan
bukata.
"To naji sai ta zauna har sai ta gama takaba an raba gado. Ince ko hakan yayi" ya mayar da
kallonsa ga Mal.Aminu da ya dauke kansa saboda takaicin halin Maikudi. Yaron ya fita zakka
tamkar ba jinin Mal Muhammadu ba.
Mal Aminu da ya gama tofe jariri da addu'a ya dago kansa "bana son hauka Maikudi. Takaba dai
tana haihuwa ta fita. Sannan tun muna shaida juna kada inji kada in gani, kaf abinda Zayyanu ya
bari na matarsa ne da 'ya'yansa tunda yana da da namiji."
"Inji ubanka"
Mamaki kamar ya kashe shi saboda Jume ce ta bashi wannan amsar. Akan tabarma take tana bawa
Radhiya abinci. Daga jiya zuwa yau tayi wuri-wuri da ita. Rasuwar Zayyan ta tabata fiye da zato
da tsammaninta. Duk wata mugunta da ta taba yiwa mahaifiyarsa dashi kansa sune suka yi mata
dabaibayi. Cikinsu babu wanda ya taba nufinta da sharri gashi sun bar mata duniyar tayi yadda
take so. Nadama ce ta gaske take nukurkusar zuciyarta. Ga Maikudu don abin kunya daga jiya
zuwa yau banda rashin mutumci babu abinda yake zubawa a dakin. Daure fuska ta sake yi
"Kina ji fa aka ce yayi wata guda harda dorin kwanaki, duk dacin mutuwa ai yaci ace tayi sauki an
fara fuskantar gaba"
Mairamu ta kasa boye kukan zucin ta koma yi a fili. Ashe har yafi wata da rasuwa bata da
masaniya. Shine take ci tasha har tayi wasa da dariya? Ashe Sojanta ya koma ga Allah take ta
tunanin dawowarsa. Yanzu shikenan nata mijin saboda soja ne ko kabarinsa babu wani danginsa
da zai sani? Anyi masa wankan gawa? An sallace shi? Wace irin mutuwa yayi duk basu sani ba.
Kukanta ya tsananta Gwaggo Ladi ta tashi ta matsa kusa da ita ta tsaya a gefen gadon.
Maikudi yayi qiqam kamar sanda sai da Jume tace ya fita, yayi waje yana surutai.
Yaron ta karba wanda rabonta dashi tun jiya. Yaji yunwa kuwa sai ruwa aka rinka bashi da tana
kwance.
Gwaggo Ladi tace Malam yayi masa huduba da Muhammad Zayyan. Ina fata hakan yayi miki"
Hawayen Mairama har fuskar jaririn tayi murmushi "Sojana Allah Ya raya min kai."
**********
"Wai Zayyanu dai Zayyanu soja mijin 'yata Mairama kake nufi?" Malamijo yayi maganar kamar
zaiyi kuka.
"Shi nake nufi. Allah Yayi masa rasuwa a kasar da suka je" Rayyanu ya bashi amsa. Shi da Badaru
da 'yan uwansu mata kaf mutuwar Zayyan ta shigesu sosai. Mutum mai barkwanci da saurin
manta bacin rai. Duk yadda su ke bata masa bai hana shi kyakyawan zumunci dasu ba ko da su
bazasu yi masa kallon arziki ba.
Malamijo ya daga hannu ya dora a ka "Laaaaahhhh ha'ila ha ilallahu, kaico Mairama, 'yar
marainiyata ta rasa miji kuma"
Lokaci kankani a tsakani zance ya bazu ko ina mijin Mairama ya rasu a filin daga. Mutane suka
fara zuwa yiwa Malamiji ta'aziyya yana cewa nan da kwana biyu zai wuce Sakkwato.
A cikin gidan ma jikinsu duk yayi sanyi. Ba wani haduwa suke yi sosai ba saboda nisan
garuruwansu amma duk da haka a iya lokutan da su ka ganshi anyi masa shaidar arziki. Malamijo
yasa a dafa abincin sadaka ya saki bakin aljihu abinda basu saba gani ba. Cikin yaransa maza ya
tura babban mai bin Mairama a shekaru yaje Balan ya sanar da Nene Marka. Idan zata bisu
ta'aziyya ta taho washegari su wuce jibi. Sannan ya tura mai bi masa Kano gidan Salame.
Suna zaune shi da 'yan gaisuwa wani yake tambayar yaya Zayyan din ya rasu don shi ma akwai
dan uwansa soja a kudu, yana tsoron a tura shi yaki. Malamijo bai tashi bada amsa ba sai da yaga
Rayyanu ya tashi zai zaga ya soma jawabi.
"Hmm ai ba'a cewa komai Haladu. Yaron nan harbi, harbi dai da kake ji da gani a finafinan su
Amita Bachan sai da aka sakar masa harsashi kusan goma amma a haka ya rinka kutsa kai cikin
abokan gaba yana gamawa dasu. Bawan Allah ya tafi ya barwa Mairama da yaranta komai nasa.
Ko sati batayi da haihuwa ba. Shine ma zanje domin na tattaro dukiyar na kawo nan sai na juya
mata da kaina saboda duk yadda ka kai da yarda da wani ba kamar naka ba. Nakan ma mahaifi"
[7/25, 3:20 PM] Sameee💖💖: Dattijuwa ce goye da yaro tana gurfane a gaban gadon Salame wadda
take hakimce tana bata umarnin ayyukan da zata yi a cikin gidan. Banda kudi sune masu gida rana
yaushe wannan mata da a shekaru zata girmi Ta Madina ace ita ce Salame 'yar cikin cikinta take
yiwa rashin kunya son rai tana kada kafafu tayi daurin Mayam Babangida.
"Kada ki sake na fito baki gama aikin nan ba Kande" ta kare cikin fada.
"Sha Allahu ma zan gama da wuri." Sai ta dan kwantar da kai "nace ko na kwantar miki da Halifa
tunda ya riga yayi bacci? Aikin nawa zai fi sauri"
Wata uwar harara da Salame ta galla mata ya sanya ta tashi da sauri ta fita daga dakin. Tana fitowa
ta sami wani matashi yana sallama. Kallo daya tayi masa ta gane ya hada jini da matar gidan
shiyasa tace ya zauna. Ruwa ta kawo masa sannan ta sanar da Salame tayi bako.
Sai da ta gama bata lokaci sannan ta fito tana takaicin hanata hutu da akayi. Tun aurenta da Salisu
bazata ce ga wata rana da take cikin farinciki sosai ba. Haka dai take rayuwa daga fada sai masifa
sai kuma muguwar hassadar Mairama da tayi sake ta kama zuciyarta sosai.
Dago labulen dakinta tayi ta fito. A wulakance take kallon kanin nata "ah'a Bature kai ne dama"
Zamowa yayi daga kan kujerar ya gaisheta. Bai manta zuwansu da sallah ba inda ta karesu musu
tas wai sun haye kujeru abinda ba'a saba ba. Da suka koma gida kowa yana korafi suna cewa da
Adda Mairama ce bazata musu haka ba banda shi don ransa ya baci. Ya dai ci alwashin idan ba
aike ba babu abinda zai sake kaishi gidanta. Gaisuwar kuwa albarkacin mai aikinta da ya gani ne
kada ace basu da hadin kai. Kusan halinsu daya da Mairama shiyasa Malamijo ya aiko shi don
sauran babu mai yarda yazo.
"Wani abin ne ya faru kazo ko kuwa?"
Shigowar Salisu kenan yaji yadda take yiwa kaninta magana. Shi ya rasa dalilinta na kin 'yan
uwanta yanzu kaf bata son mu'amala ta hadasu. Nashi dangin ma bata raga musu amma yana daf
da magance matsalar nan.
Bature ya gaishe shi ya amsa a mutumce sannan yace ta biyo shi daki. Bakin nan a gaba ta bi
bayansa.
"Me yake damunki ne? Yaro ya taho tun daga Sumaila babu wata tarba me kyau sai me ya faru?
Yanzu ke da 'yan uwanki babu wanda zai zo don sada zumunci wurinki sai da wani dalili?" Ya jero
mata tambayoyin cikin bacin rai.
Bata saurare shi ba ta fice don sallamar Bature ya koma inda ya fito. Salisu ashe yana bayanta sai
ganinsa tayi ya zauna yana tambayarsa mutanen gida.
"Ki kyale Kande aiki na ga tana yi. Kuma shi Halifa ba'a kwantar dashi ne? Kusan a bayan matar
nan yake wuni ita bata huta ba shi ba'a barshi ya sake yayi wasa ba"
"Idan ta sauke shi damuna zaiyi. Kuma dai tunda biyanta akeyi meye a ciki?"
"Salame kin..." kasa karasa magana yayi ganin ta tafi luuu kamar zata fadi ta saki kara iya karfinta.
Maimakon Salisu ya tarota sai mamaki ya kama shi har ya kasa motsi. Salame ce fa da yasan bata
kaunar kanwarta. Me zai sa ta shiga wannan yanayi kamar ance mata shi da kansa ne ya mutu ko
mahaifinta.
Bature ma abin ya daure masa kai "Adda cewa nayi mijin Adda Mairama fa ba Malamijo ba"
Zama kawai tayi dabas akan kujera tana kuka sosai. Shikenan Zayyan ashe bata da rabon zama
dashi. Salisu ya kawar da kai daga gareta.
Bakin gate ya raka Bature ta bashi kudin mota sannan ya koma ciki. Tana nan tana rusa kuka
Kande na bata hakuri. Yana zuwa ya finciko hannunta sai da Kande ta tsorata. Dakinsa ya kaita ya
jefata kan gado iya karfinsa. Fuskarsa a daure babu wasa ko kadan ya jefa mata tambayar da ta
kada mata hanji.
"Tun farkon haduwarmu dama Zayyan kike so?"
"Kin cuceni, ban dade da aurenki ba zuciyata ta bani cewa ban yiwa kaina adalci wurin zabar
matar aure ba. A tunanina na auro mace mara son zumunci ne kawai da raina na kasa da ita. Ashe
kin wuce haka. Salame mijin kanwarki kike so kuma har kike kishi da ita alhalin kina gidan naki
mijin"
Har yanzu ta kasa magana sai kuka. Shi din ma nasa idon da hawaye saboda bai taba kawo hakan
a matsayin dalilin da yasa take yiwa Mairama haka ba.
"Bazaki je Sakkwato gaisuwa ba" kallonsa tayi da sauri ya sake hade rai "ke daga yau sai abu yayi
tsanani sosai zanyi miki izinin fita kina ji na. Idan kika karya min doka wallahi, wallahi sai na
shayar dake mamaki"
**********
Ranar da aka sallami Mairama a ranar Mal Aminu da Jume su ka amince da a kwashe kayanta ta
koma gidansu Zayyan. Idan iyayenta sun zo sai su tafi da ita gida.
"Ku wuce da ita su Mubaraka sai su zo a kwashe kayan gobe tunda zaman barikin babu amfani"
Mairama tana jin haka ta ajiye kunyarta a gefe "Kawu ina son zuwa don akwai abubuwan da nake
son hadawa da kaina"
Caraf a kunnen Maikudi "ko ma meye muma din jinin Zayyanu ne. Kije ki huta ni da kaina zan
jagoranci zuwa a debo kayan saboda kada wani abu ya salwanta"
Soye idanu tayi don bazata yarda a hanata zuwa ba. Ta nuna musu akwai makota da take son yiwa
sallama irinsu Christie wadda bata kara gani ba tun lokacin da tace zata je yi mata girki.
Mal Aminu yace "Ka barta taje Maikudi. Daga nan ma sai mu bincika muji ko akwai wani abu da
zasu bawa iyalin mamatan. Mu bari jikinta ya kara kwari ko nan da kwana biyu ne"
Ransa baya so saboda ya kula tunda ta dage sai taje akwai dukiya dankare a gidan da bai taba
zuwa ko kofarsa ba.
"Ina mukullin a bani na rike saboda 'yan barka da gaisuwa kada wata ta dafe"
"Maikudi kenan, ko ma wacece ba sai dai muce Allah Ya bada sa'a ba. Sata a gidan soja, gidan
sojan ma a cikin bariki kamar mutum ya tashi da burin karar kwana" Gwaggo Ladi ta gwaba masa
magana.
Bai sake magana ba su ka tafi gida. Jume tasa matan su Badaru gyarawa Mairama dakin Innar
Zayyan. Tana shiga ta tuna ranar sunan Radhiya da hotunan da suka yi da Zayyan da Awwab a
ciki. Idanunta da basa rabo da hawaye suka fara abinda ya zame musu jiki yanzu.
Jume da kanta tazo tace mata ta shirya ta fito zata yi mata wankan jego. Jariri kuma Gwaggo Ladi
ta dauka tayi masa wanka irin wanda bai samu ba tun ranar haihuwarsa saboda kasancewarsu a
asibiti.
**********
"Ya muke ta bin lungu ne yaro? Nayi zaton a irin unguwannin nan da suke malale da titi gidan
yake"
Rayyanu ya kalli Malamijo ya sake daure zuciyarsa a karo na barkatai ya bashi amsa akan irin
wadannan tambayoyin da yake ta yi masa.
Su hudu ne a ayarin tafiyar banda Rayyanu suka biyo motar haya. Nene Marka, Malamijo, Hajjo
da kuma Salisu. Gidan yanzu Yadikko da Hajjo ne kawai a gidan, ya saki Dije da Inno yana shirin
karo wata. Tun a tashar Kano ana cewa a kawo kudin mota Malamijo ya shiga tarin karya, daga
baya ma sai yayi gaba yana dukan kirji sai da ya hango Salisu ya biya musu kudin motar su duka
sannan ya dawo yana cewa kwarewa yayi.
"Sai ji nayi wani abu siririt ya wuce min ta makoshi. Kwarewa babu dadi, ammm nawa ne kudin
motar ne?"
Nene tasan dalilin tafiyar tasa sai kawai ta dauke kai. Hajjo ce ta fada an biya yayi wata barazanar
zura hannu a aljihu zai dauko kudin ya bawa shi. Sal da Salisu yace ya bari duk daga ne.
Iyaye da dangi duk lalacewarsu sunfi ace baka da kowa. Sallamar Malamijo kawai Mairama taji ta
sa kuka sosai. Kuka ne na ganin babban gatan da ya rage mata duk fadin duniyar nan. Shine bango
abin jingina a gareta wanda take sa ran idan tayi kukan rashin miji zai rarrasheta yace ta barwa
Allah komai. Idan tayi kukan rayuwar marayunta zai yi mata alkawarin matsawar yana numfashi
'ya'yanta bazasu tagayyara ba.
Jikin Nene Marka ta zube suna kuka tare. Malamijo ya tausayawa Mairama sosai ya mika hannu
ya dauki Radhiya. Zayyan wanda duka gidan an rasa mai kiran sunansa har Maikudi kuwa saboda
tuna musu da marigayi da yake yi matar Badaru ta kwanto daga bayanta ta mikawa Hajjo.
"Iko sai mai shi, Malamijo dubi yaron nan don Ma'aiki."
Radhiya tana gefensa ya karbi jaririn yana kare masa kallo. Salisu yazo ya karbe shi shima ya ga
kama sosai da mahaifinsa.
"
Mazan sun koma waje inda ake zuwa yi musu ta'aziyya matan kuma suna daga ciki. Sai dare ne
Mal Aminu ya sanar da Malamijo za'a kwaso kayan Mairama sai su tafi da ita.
"A'a a bar yarinya a gidan mijinta. Idan akwai wata dukiya da bazata iya juyawa ba ni sai na tafi
da ita ba wani abu."
Maikudi yayi saurin cewa "dukiyar marayu zata fi dadi a hannun dangin uba. Saboda haka gobe
zamuje ayi duk yadda za'ayi ne. Gida kuma ba nasu bane na bariki ne. Tunda ya rasu dole ne su
tashi komai dadewa"
A hankali zantukan nasu suka fara neman komawa rigima. Maikudi da Malamijo kowa ya nuna
zalamarsa a fili. Shiyasa kowa cikinsu yake ganin dole ya tsaya akan dukiyar da basu da tabbacin
akwaita.
Shabiyun rana kuwa washegari suka isa kofar gidan da ya kasance na Mairama da Zayyan
kwanaki kadan da suka wuce. Ta kalli gidan Zainab a rufe har yanzu. Tana son sanin halin da suke
ciki da mazansu amma yanzu babu hali sai komai ya daidaita a nata bangaren. Gidan Christie ma a
rufe yake. Bayan ta bude nata gidan sun shiga da yayyen Zayyan mata da kuma Hajjo sai ga wasu
cikin abokan zamansu na kusa. Gaisuwar mijinta suka yi mata da barkar Zayyan karami. Ta
tambayi ina Christie wata ta bata amsa da cewa ranar da ta haihu Christie tazo tayi mata girki
kuma ta farfadawa makota haihuwar. Ta koma daidai lokacin da Mairama ta suma. A nan take jin
duka sojojin sun rasu ciki kuwa harda mijinta. Bata iya shiga ba ta koma gida bayan ta sauke musu
Radhiya. Shine aka sami wani da ya san gidansu Zayyan aka fada musu. Ita kuma Christie ta tafi
garinsu ta fadi mutuwar har yanzu bata dawo ba.
Duka matan abin tausayi musamman wadanda mazansu suka tafi a bayan su Zayyan. Suna cike da
tsoro da fargabar me zai je ya dawo.
Wasunsu sun saka hannu wurin tattare kayan kitchen da na falon Mairama ana hade komai wuri
guda ana fitarwa. Cikin dakin ta shiga zuciyarta tayi matukar rauni. Shikenan daga yau duk wasu
memories da suka gina da Zayyan a gidan nan cikin wannan dakin sai dai zu dawo mata a tunani.
Kukanta Hajjo ta jiyo ta shiga dakin da sauri.
"Haba Mairama ashe bazaki sakawa zuciyarki salama ba? Ni ko kadan ban so aka ce wai azo
kwasar kaya da wuri kamar ana korarki ba. Su dakata ki sami nutsuwar zuciya sun ki"
Mairama ta bude wani akwai ta dauko envelop din da Zayyan ya bata hannu na rawa ta saka a
jakar hannunta sannan aka fara hada kayan gidan.
Malamijo yana waje yaki shiga ba don kunya ba sai don bakinciki. Shi kadai a ransa yake nanata
an yaudareshi aka ce masa Zayyan soja ne. To yaji sojan ne amma ba wani mai mukami bane ashe.
Ji dai wannan akurki da ya ajiye masa 'yarsa ya raya a zuciyarsa. Kuma ashe ma ba nasa bane. To
duka kudaden da yake masa alheri dasu a ina yake samowa? Faduwar gaba yaji da ya tuna indai fa
babu wani abin kirki da ya bari komai na Mairama da 'ya'yan wuyansa zai dawo. Hodijan inji
mutanensa, aradun Allah bazai iya karawa kansa nauyi ba. Yanzu fa yara goma sha bakwai
gareshi. Salame ce kadai a gidan miji tunda dai Zayyan ya rasu. Gata ta tunda tayi aure ta ari rigar
rashin mutumci ta saka.Tsaki yaja sai hankalinsa ya koma ciki inda yake jiyo muryar Maikudi.
"Kai wannan takadirin yaro da gani zaiyi mugunta. Me kuma yake nema a cikin mata?"
Shiga yayi da Salisu ya sami Maikudi yana fada "ki fito min da duk wani kudi ko takardun
abubuwa masu mahimmanci na Zayyan. Dukiyar magada sai da saka ido. Ba wai da ka zaki dauke
komai ki rike ba"
Salisu ya riko hannunsa "kaga Mal Maikudi duk abin nan ba na rigima bane. Mairama ba jahila
bace da zata ci dukiyar mamaci. Sai dai fa ina so ka sani duk danginku babu mai gadon Zayyan sai
Mairama da 'ya'yanta"
Kamar zai kaiwa Salisu duka ya soma fada "ni nasan ba banza ba kuka taho kwanku da
kwarkwata. Ashe da manufarku. To babu wanda ya isa yayi sama da fadi da dukiyar magada
muddin ina raye"
Mairama dai sai kuka. Malamijo ya zakalkale yana ta zubar musu da daraja a gaban 'yan uwan
Zayyan. Idan Maikudi yayi shi za'a ce da sauran kuruciya. Shi kuwa yana mahaifinta ga jikoki har
uku amma har yau bai fasa halinsa ba.
Mal Aminu da kawunsu Zayyan sun shigo sun same su ana ta mayar da magana. Sam Mal Aminu
baiji dadi ba. Ga Mairama sai ajiyar zuciya kawai take yi.
"Daga can ofishin nasu nake an kaini har wurin wani babba cikinsu a nan munyi magana. A
takaice dai muna da yawa da muka rasa 'yan uwa a wurin nan. Amma yace muyi hakuri ba'a turo
komai daga gwamnatin tarayya ba da zasu sallami iyalan sojojin ko kuma masu rauni"
"Ikon Allah, yanzu ace mutum ya rasa rayuwarsa a bakin aikinku amma babu sallama ga iyalansa
da maraici ya kama su?" Cewar Salisu
"Don ma baka je wurin bane. Mutanen da yawa wallahi. Sun ce kuma sojojin da aka rasa suna da
yawa ba wai na nan bane kadai. Kuma wai gwamnati bata da kudi amma zasu neme mu idan an
sami wani abin"
"Wannan ai zancen banza ne, bata da kudin take kashe mana 'yan uwa? Ni bazan hakura ba.
Wannan magana kuma bazan bari ta mutu a nan ba." Maikudi yace yana tashi tsaye "idan ma an
fada ne don a sa jikina yayi sanyi kada na tsayawa marayun nan wallahi sai naje" ya zubawa Mal
Aminu idanu.
Murmushi yayi kawai yace motar daukan kayan tazo. Kawunsu ne ma ya rinka yi masa fadan baya
son rashin kunya. To amma da yake duka talakawa ne maganarsu bata wani tasiri a wurinsa.
Abu kamar wasa Mairama da tazo barikin nan a matsayin amarya kasa da shekara biyu wai har
anyi zaman an gama. Mijinta abin kaunarta ya tafi ya barta a hannun wadanda basu damu da halin
da take ciki ba, kawunansu kawai suka sani.
A daren Malamijo yace su shirya da wuri zasu wuce gobe. Mairama ta roke shi alfarmar zata je
gidansu Zainab kafin su tafi. Jume tana zaune tare da Mairama bayan ta yiwa Zayyan karami
wankan yamma tace mata "yanzu Mairama daga yau shikenan ko? Nasan da wuya ku rinka zuwa
tunda kin san ba ni bace na haifi Zayyanu. Ga bakin kishi yasa ni ban san ta yadda za'ayi na sami
dangin mahaifiyarsa ba balle su san halin da ake ciki ma "
"In sha Allahu zan rinka zuwa Jume. Idan basu zo ba wa zasu nuna a matsayin dangin uba?"
"To nagode Mairama. Sai kin daura dammarar hakuri da juriya. Yanzu sabuwar rayuwa ce zata
bijiro miki da baki taba zato da tsammani ba." Hawaye ya zubo mata da ta tuna rasuwar Mal
Muhammadu.
Washegari da wuri Mairama ta tafi gidansu Zainab. Allah Ya taimaketa bata mance hanyar ba.
Mahaifiyar Zainab din ta samu wadda ta fada mata kwana hudu da suka wuce babanta ya kaita
Kano gidansu Hadir. Duk da bata san kan garin Kanon sosai ta nemi tayi mata kwatance amma
anyi rashin sa'a ko sunan unguwar bazata iya tunawa ba don wahala yake mata. Mairama tana
kuka tace ta fada mata tazo itama zata koma garinsu.
"Kema mijin naki yaji rauni ne?"
"Rasuwa yayi."
Idanu ta zaro "idan Hadir yaji ban yaya zai ji ba. Allah Ya zama gatanku Mairama"
Sallama tayi mata ta koma gidan domin su karasa shirin tafiya. A daren jiya ta bude envelop din da
Zayyan ya bar mata. Ashe gabadaya sauran kudin gadonsa ne ya bar mata da takardun gidansa na
Kano. Dasu ta fita a jakarta idan ta koma zata fito dasu ta nunawa iyayen. Dama suna rayuwa ne
bayan tafiyar mazan akan albashinsu da ake bawa matan. Kudi ne da bai wani taka kara ya karya
ba. Wasikarta kuwa zuciyarta ta kasa bata kwarin gwiwar karantawa har lokacin.
**********[7/25, 3:21 PM] Sameee💖💖: Maikudi ne tsaye a ofishin da aka tura shi cikin barikin
su Zayyan akan maganar kudi ne dai.
"Jiya Babanku yazo akan zancen nan mun fada masa bamu da komai. Ya bada adireshinsa duk
lokacin da kudi yazo zamu nemeku" officer din ya bashi amsa bayan ya gama jero tambayoyi.
Yana hargaginsa na rashin mutumci yace "Ashe cewa yayi shine babanmu don ya ci kudin gado.
To wallahi karya yake. Babu wata alaka ta jini tsakaninmu"
Wani sojan ne ya shigo yana tambayar wancan me yake faruwa cikin harshen turanci. Sai da ya
sara masa ya bashi amsa da gani ya fishi mukami.
Maikudi yana jin ana bayani duk da bai iya gane duka maganar amma ya dan fahimci me akeyi ya
katse wancan "You understant Zayyan Muhammad Tureta is die? Me. Biggggggggg broza. Is me
faza dinmu daya ai" ya nuna kansa yana murmushi yana so su fahimci shine babban wan Zayyan.
Mutumin ya hade rai yace a kore shi kuma idan ya kuskura ya sake zuwa ba'a neme shi ba a kulle
shi saboda yana mudu hayaniya. Dayan yana soma fassara masa bai tsaya jin karshen ba ya fice
yana ta Allah Ya isa an kashe masa kani. A hanyarsa ta komawa ne ya rinka tunanin dole fa akwai
abinda Zayyan ya barwa matarsa. Idan ba haka ba da me suke rayuwa duk tsahon lokacin nan?
Yafi karfin ita da kwadayayyen babanta suyi masa wayau akan hakkinsa.
Yana zuwa dakin da Malamijo yayi masauki ya shiga. A shirye suke suna jiran dawowar
Mairama.
"Dama nazo akan yaran nan ne Radhiya da Zayyan. Nace ko zaka yiwa Mairama magana idan ta
yaye shi zan zo na dawo dasu gabanmu saboda gatansu dai bai wuce wurin dangin mahaifinsu.
Idan kun tafi yanzu kai ma nauyi ne kawai zai kara hawa kanka. Sannan bazan zuba ido bane tayi
aure 'ya'yana su koma agolanci a gidan wani"
Malamijo an tabo inda yake masa kaikayi kuwa. Ina zai kai karin bakuna uku a gidansa. Gara
Mairama yana son abarsa, amma yaran nan da aka ha'ince shi yayi ta yiwa babansu kallon kitse
ashe rogo ne "indai wannan ne babu damuwa. Zanyi magana da ita kuma dole ta amince don nima
bazan so suyi rayuwar agolanci ba azo ana wulakantasu"
Maikudi ya fita da wani mugun murmushi. Soro ya koma ya zauna jiranta. Ilai kuwa babu jimawa
sai gata tana ta sauri kada a gaji da jiranta. Dukawa ta danyi ta gaishe shi ya yafito ta da hannu.
Kanta a kasa ya fada mata yadda ya fadawa Malamijo. Ai tuni ta saka kuka iya karfinta tana
rokansa ya rufa mata asiri ita bata da niyar sake aure.
Gabanta ne ya fadi. Ta san halin Malamijo kuma tas zai bada yaran nata.
"Naji, amma bazaki bar garin nan ba sai kin fito da dukiyar kanina. Dole ne a raba gadonsa saboda
a sauke masa nauyi"
Hannunta yana rawa ta zaro envelop dinnan daga jakarta ya warce gabadaya. Sakar masa tayi
kafin ya hada da hannunta.
"Daren jiya na gansu shine nace dama yanzu zan fito dasu ayi abinda ya kamata"
Kankance idanu yayi yana kallonta bayan ya zaro takardun gidan da kuma damin kudi da aka
nannade da kyauro "ashe ke mutuniyar banza ce ban sani ba? Wato da guduwa zakiyi da komai
saboda tsabar mugunta da bakin hali kamar na tsohonki"
Wasikarta ta hango ta fadi ta mika hannu ya taketa da sauri da kafa "meye a ciki?"
Hankalinta yayi matukar tashi "wallahi Allah wasika ce ya bar min. Ba takardar komai bace"
Sai ta ga yayi murmushi saboda ya fuskanci yadda ta rude "soyayya manya" yatsansa ya kada
mata "kalli nan, zan cire takardun gidan saboda dama ina binsa bashi da bai biya ba. Ina jin gidan
ma bazai isa ya biyani ba amma dai su kadai zan dauka. Muje ciki idan munafukan dattijan nan
sun zo ki basu kudin a rabawa wanda aka ga damar bawa. Ni kuma nayi miki alkawarin babu
wanda ya isa ya rabaki da 'ya'yanki kuma zaki koma Kano da wasikar masoyinki"
Mairama kallon mugunta irin ta Maikudi ta tsaya yi ta rasa shawarar yankewa. A zatonta zaa raba
gado a barwa yaranta gidan sai su zauna a ciki. Ita kuma a cikin kudin ta nemi abinyi domin kula
dasu. Wani hawaye ke bin kuncinta tana jin zafinsu har zuciyarta "hakan yayi maka?"
Ya dage gira "yayi...ki sani idan kina tunanin juya magana ko Jume tayi kadan tasa na bar miki
yaran nan balle kuma wancan tsohon Mal. Aminu. Mahaifinki kuma a yadda na fahimta ko
sadakarki na nema zai iya hada min"
Share idanunta tayi tabi bayansa. Kowa yayi zaton kukan tafiya ne take yi da mutuwar mijinta. Su
Mal.Aminu sun zo ta dauko kudi ta mika masa. A take aka kira wani malami ya kasafta da aukinsu
kuwa aka bata nata aka ware na yaran yace batun bashi fa Mairama tace ya tabbatar mata babu msi
binsa komai kafin ya tafi. Maikudi ko tari baiyi ba ganin babu mai gadon nashi sai su kadai. Jume
har dadi taji yayi hankali.
Nasiha da ban hakuri aka sake yiwa juna sannan Mal.Aminu ya roki alfarmar kada ta tafi ta yanke
zumunci dasu albarkarcin 'ya'ya "mu kuma nan babban kalubale ne a garemu mu da gwamnati.
Mu dubi marayun yaran nan da mahaifiyarsu kafin mu ga me Allah Ya tsara musu. Haka ma
gwamnatin ta dubi rayuwar sojojin da take takama da sadaukarwarsu. A dubi masu ran wanda suke
a bakin aiki, a dubi masu rauni da nakasa sannan a dubi iyalan mamatan domin a gaskiya akwai
nakasu mai girma a rayuwar iyalan bayin Allahn nan"
Sun fara fitowa mata ana ta kuka Maikudi ya samu ya tarar da Malamijo shi kadai iska tana ta
kada yalolon yadin jikinsa yana manne masa ramar tana kara nunawa. Takardun gidan ya nuna
masa yana murmushin samun nasara.
"Naga ka kawo idanu ka dora akan dukiyar da baka da alaka da taruwarta shine nace bari dai na
nuna maka waye Maikudi."
"Na gidan Zayyan ne wanda yanzu ya zama nawa. Kana iya kaini kotu don a kwatarwa 'yarka da
jikoki hakkinsu amma ka sani kana yin hakan zan rabata da yaran nan ni kuma. Ta fada min akan
ta baka dukiyarta gara kowa ya rasa don baka ragawa kowa akan kudi"
Kallon Mairama yayi zuciyarsa tana tafarfasa. Wato Zayyan yana da gida shine ta dauka ta bawa
wan mijinta tana tunanin zata dawo masa gida ta jabe ya ciyar dasu. Lallai Mairama bata gama
saninsa bane shiyasa har taje tana tona masa asiri. Har shi zata ha'inta yana mahaifinta. Kwafa
yayi yana jiran su kebe don bashi da bukatar magana a gaban mutanen da ya kula bakinsu duka
daya.
Maikudi kuwa dariya yayi bayan ya tafi. Alamun Malamijo da ya gani ne yasa shi wannan magana
sai gashi tazo daidai da halin nasa. Mairama da Zayyan ma ta kasa tonawa mahaifinta asiri a
gabansa me zai kaita fada a gaban Maikudi?
Radhiya ta dauka Hajjo ta goya Zayyan suka tafi tashar da zasu sami motar Kano. Sai da suka dau
hanya don Salisu ya biya su kadai ne a ciki Mairama tana hawayenta Nene Marka na bata baki
kawai Malamijo ya soma fada akan bayar da takardun gida da tayi. Kai, ita kam da me zata ji ne a
rayuwarta. Tana kuka tayi musu bayanin yadda abin ya kasance.
"Ko dai mu koma ne a karbo takardun? Duk tsiyarsa baifi karfin hukuma ba fa Mairama" Salisu
yace nasa ran a bace.
Tsorata tayi "don Allah ku kyale shi. Yaran nan zai karbe, babansu ma baiji dadin zama dashi ba"
Nene tace "Duk da haka Mairama mu zamu tsaya miki. Gidan a ina yake?"
Salisu ya tabo dreban "Malam don Allah kayi hakuri ko zamu koma"
"Babu inda zamu je. Idan kuma sai kun koma to ni a ajiyeni a nan."
Rufe idanu yayi yana ta fada don sosai yaji haushin maganar Maikudi da rasa gidan da yayi. Ace
'yarsa da yafi so da tausayi a cikin 'ya'yansa ita ce tayi masa haka.
"Ina nan kan baka na bazan koma ba sannan kuma ki shirya tunda dangin miji sunfi uba ni bazan
dauki nauyin kowa ba. Gida dai gaki gashi kuje a baku daki. Sai yanzu na raina waye Zayyanun
ma. Har me yayi miki wanda ni ban miki dubunsa ba. Ji gidan da ya ajiyeki...."
Ta daure matuka amma bata jin zata taba jurewa wani ko da kuwa Malamijo ne ya zagi Zayyan.
Ko bata aure shi ba yanzu ta san daraja da kimar soja....wallahi yafi karfin raini.
"Yayi min komai Malamijo" tace cikin kuka tana rungume Nene iya karfinta har Radhiya sai da ta
tsorata "ko a kango muka zauna dashi har abada bani da tamkarsa. Wayyo ni ashe haka mutuwa
take da daci da tona asiri? Lokacin da nayi maraicin uwa bansan ciwon rashi ba saboda bamu saba
ba. Allah Ka jikan Zayyan ko Ka dauki raina nima na huta"
Zubar hawayenta ya taba Malamijo bare da ya ga ta rike kirjinta da yake mata mugun zafi. Dreban
yace wa su juya ta dago rinannun jajayen idanunta.
"Allah Ya kaimu masu gidan su girma zasu karbi abinsu da izinin Allah. Amma a yanzu tunda
yace yaji ya gani zai ci haram bazan shiga tsakaninsu ba"
Duk rashin halin Hajjo sai da tayi kukan tausayin Mairama. A haka suka tafi Kano Salisu yana ta
mamakin halin Malamijo. Ashe Salame gado tayi na munin hali ba taka haye ba.
Tare suka sauka a tasha ya ja Mairama gefe ya fito da kudi masu tsoka ya damka mata sannan suka
nemi motar Sumaila shi kuma ya shiga hayis zuwa gidansa. Dama ya riga ya gama shawararsa tun
a hanya shiyasa yana ganin yadda Salame ta fito muzumuzu ita a dole tana cikin alhinin mutuwar
masoyi ko sannu bata yi masa ba ya dakatar da ita zata tashi ta bar falon saboda ta ganshi.
Kiris...sauran kiris irin mai riss dinnan zawo ya tsinke mata. Tunda take bata taba jin fargaba da
tsoro kamar wannan lokacin ba. Ya saketa ta tafi ina? Sumaila? Allah Ya kiyaye. A iya zurfin
tunaninta Salisu yana mata son da zai iya hadiye kowane abu tazo dashi. Shiyasa take yadda taga
dama iyaka yayi fada anjima ya dawo yana bibiyarta. To ko dai kunnenta baiji da kyau bane.
"Ni ka saka?"
"Halifa da muka haifa da ana komawa baya Salame bazan so hada jini dake da mahaifinki ba. 'Yar
cikinsa tana cikin magagin rashin miji amma dukiya yake nema duk arzikinsa. Wallahi bazan iya
ba. Kije Allah Ya baki daidai dake."
Kande ya kwalawa kira tazo ya cire naira goma yace ta wuce ta kaiwa mamansa Halifa yana tafe.
Dayake daga can gidansu aka kawota ta riga tasan gidan.
Salame tana kame ta kasa motsawa ya wuceta ya shiga daki. Sai da abin ya sami wurin zama a
kwanyarta ta shiga ta fara masa ihun masifa.
"Wato akan Mairama ka sakeni saboda Malamijo ya bata mata rai. Bazaka burgeni ba sai naga ta
tare a gidan nan ranar asabar"
Duk inda zata cusa masa haushi ta rinka nema ko a jikinsa tunda ya rabu da kwallon mangwaro ya
huta da kuda.
Gidansu ta koma ko ta kan Halifa bata bi ba. Awa uku tsakanin saukar su Malamijo da dawowarta
gidan.
Yadikko ta tareta ganinta da akwati niki niki "ke kuma daga ina?"
Ashar Malamijo ya lailayo ya saki yana kara tunzura da yadda take magana ko a jikinta "wai
nufinku duk kun dawo min gida kenan?"
"Ya son ranka? Ca nake mata biyu ka saki a dan tsukin lokaci guda, ai gara ka dana" Hajjo ta fada
masa sannan ta saki labulen dakinta.
"To Al-Qur'an daga ke har Mairaman kowa taji da kanta bazan iya ba. Yara masu bakin hali kun
fita a talauce kun dawo a tsiyace"
Dakinsu na da ta shige abinta ta barshi tsaye. Nan taci karo da Mairama da kyawawan 'ya'yanta.
Kamar ta shareta sai ta fasa tace mata ya hakuri.
"Mungode Allah"
"Amin"
Daga haka babu wadda ta sake kula 'yar uwarta har suka yi shirin kwanciya. Ganin Mairama da
yaranta ya tuna mata da Halifa sai taji wani iri gashi bata yaye shi ba dama.
Kyandir Mairama ta kunna a gefen katifar da suke kwance ta kwanto wasikar Zayyan ta soma
karantawa.
_(Na rubuta wannan takardar tun ranar da sunana ya fito a cikin masu tafiya Liberia. Sai nake
ganin kamar jiya muka yi aure har zan tafi na barki. Mairam ban sani ba ko zan dawo ko shikenan
tafiyar. Don Allah alfarma daya nake roko kada bakinki ya taba gajiyawa da sanyani a addu'a. Idan
kewa ta isheki kinyi kukan rashina ki sani cewa nima ko a ina nake idan na tunoki sai na zubar da
hawaye. Ina sonki Fillo Allah Ya sani amma ina son ki saka a ranki mijinki yayi alkawarin
bautawa kasarsa ne. Zanfi kowa son son ace ina tare da iyalina kamar kowane magidanci. Sai
gashi aikina yayi min tsakani da hakan. Lokaci zuwa lokaci zan rinka tafiyar da babu lallai na
dawo. Duk da haka ina alfahari da aikina kema ki tayani kinji. Idan kin haihu kafin na dawo ki
zabawa abinda muka samu suna. Ki kular min da 'Yar Soja Alheran innar Daadaa. Sauran kalaman
da suka rage a kirjina sai na dawo gareki zaki ji su. Idan ban dawo ba na baki amanar kanki da ta
'ya'yana. Allah Yayi muku albarka. Lt Zayyan Muhammad Tureta)_
**********
Abokin fadan nata wani sangamemen yaro ne don shima akwai kuruciya sai girman jiki.
"An fada din" yace sannan ya cigaba da wakar da ta hadasu fada "Malamijo Malamijo tsolon rake.
Ga kwadayi ga rowa yaki yin gaba"
Wani kukan kura Radhiya tayi ta dire a gabansa ta nuna kasa "in ba tsoro ba dangwali" ta nuna
masa kasar wurin. Dabi'arsu kenan 'yan makarantar wadda ta kasance firamare ta gwamnati idan
ka yarda zaku dambace to kowa ya dangwali kasa. Daga nan sai a kaure karfinka ya kwace ka.
Dukawa yayi zai dangwala ga tsirarun abokansu da basu bar makarantar da wuri ba sun tsaya
kallo. Sai da ta daidaici yayi kasa da fuskar nan kawai ta dauke shi da mari ta ranta a na kare. Kai
tsaye staffroom ta wuce inda malamai suke wurin Umminta.
Tana shiga ta cukwikuye jikin Mairama tana kuka wai su Danmama ne suka dake ta. Tahowa suka
yi Danmama ne a gaba kayansa duk kura saboda faduwar da yayi garin bin Radhiya. Kofar
staffroom din taje ta saka su kneeldown har Radhiya sannan ta nemi jin ba'asi. Sai aka rasa me
fada mata. Duk fitsarar Danmama yasan da kunya dai ya maimaita wakar a gabanta. Radhiya
dama ko me zata yi mata bazata fada ba don kada ranta ya baci.
Daga bayanta taji wani malami yace "Anti barni dasu kiyi tafiyarki gida. Idan na gama zanesu zan
taho da wannan mai kunnen kashin"
Mairama ta gyara zaman farin gilashinta tayi dan murmushinta da ta saba yanzu da wuya kake
ganin bacin ranta ta koma ta dauko 'yan tarkacenta tayi hanyar fita daga makarantar don dama an
riga an tashi. Daga karkashin wata katuwar bishiyar marke take hango yara suna 'yan wasanninsu.
Idanunta suka sauka akan Emzee yana zaune yayi shiru yadda ya saba yana jiranta.
"Karami zo mu tafi" tace da dan karfi don ta kula bai ganta ba sai gashi ya taso da saurinsa.
Kayan hannunta zai karba tace ya barsu su tafi "Ummi ina Adda?"
Sunyi gaba wasu 'yan ajinsu suka rinka kwalo masa kira suna Emzee sai an dawo hutu. Wannan
suna da Mairama ta hakura da yakar sa dole shine sunan da yabi Muhammad Zayyan har gida.
Mutane kalilan ke kiransa Zayyan ko Karami kamar yadda take fada. Yace wani malami da suka yi
a firamare two ne yake kiransa MZ Tureta. Shikenan abu na yara ya koma Emzee.
A makaranta kuma gurfane gaban Uncle Idris su Radhiya ne da Danmama. Sai da Mairama ta tafi
Radhiya ta fada masa sunan da suke kiran kakanta dashi. Uncle Idris ya tabbatar zasu aikata yayi
musu bulala biyar biyar mai zafi da dorinarsa ita kuma biyu ladan biye musu. A waje ta jira shi
shima ya dauko kayansa tunda yau take ranar hutu suka tafi yana mata nasihar fada da maza.
A cikin shekarun da suka gabata rayuwar Mairama sai dai godiyar Allah. Zamanta a gidan
Malamijo tamkar zaman gidan haya ne. Iyakar gaskiyarsa shi nauyi ya masa yawa fitar da kudi
kamar ana mintsininsa ne. Ya kara kudin cefane da kyar da sudin goshi amma daga nan fa ko me
mutum ke bukata mace ko namiji cikin iyalinsa sai dai su nemawa kansu.
Abu na farko da Mairama ta fara yi shine adana kudaden gadonsu a ranta tana tanadinsu ne domin
karatun yaran a gaba. Sai da ta fuskanci sabulun wanka wannan idan bazata saya ba sai dai su
watsa ruwa kawai ta fara taba kudin. A hankali kudi suka fara samun gibi dole ta fara neman
sana'a. Tashin farko ta saro zobo tunda ta tsira da firig dinta ta soma yin zobo da lamurje na
saidawa. TV da bidiyo da duka kayan gadonta banda katifar da ta ajiye kusu suke kwana da yaran
duka suma saidawa tayi don ta kara jari. Allah Ya dubi halin da suke ciki ya buda mata kasuwa
tana ciniki sosai.
Salame tana gefe kullum tana yawo tsakanin nan gidan nasu da wurin Ta Madina wadda da fari ta
dauki fushi mai tsanani da ita sakamakon mutuwar aurenta. Har gida suka tura aka nemo Salisu ko
zai maidata yace idan ta sami miji tayi aure shima auren zaiyi.
Zaman gaba, bakinciki da hassada ta dauka tana yi da Mairama. Kayan dakinta Ta Madina ta sayar
ne ana bin malamai domin karkato hankalin Salisu. Shiya janyo ita bata da komai gashi jiki ya
saba da jindadi an manta wanki, shara da wanke-wanke.
Wahalar gidansu a yanzu har tafi ta da tsanani ko don zawarci suke oho. Hankalin Mairama yana
kan inganta rayuwar 'ya'yanta, na Salame yana kan me zata yi ta kere Mairama ko ta hanata
cigaba. 'Ya'yanta musamman Radhiya sun tsole mata ido. Abu kadan ne zata yi ta kai mata hannu
da duka amma Mairama bata taba tankawa ba. Lokuta da dama wurin Yadikko suke zama ko Hajjo
idan 'yan mutumcin suna kusa.
Wata rana ta gama zobonta da lamurje ta kukkulle a leda santana suna cikin wani katon baho a nan
bakin famfon tsakar gidan inda take aikinta ta tashi ta tafi jawo ruwa a rijiya zata wanke wurin.
Salame tana ta fakonta don dama ta gane yanayin aikin nata. Idan ta gama kullewa sai ta janyo
ruwa ta wanke wurin sannan ta dauka ta kai firig dinta ta jera. Su kan wuni da wuta amma da
wuya ta kwana.
Tafasasshen ruwan zafi Salame ta taho dashi a bokiti tayi daurin kirji kamar mai niyar shiga
wanka sai da tazo daidai bakin bahon da kayan Mairama suke ta sheka musu ruwan nan. Ledojin
dole suka yi laushi sunyi tsamo tsamo babu dadin tabawa. Salati ta soma yi wai wucewa zata yi ta
sirka ruwan wankanta don ta ga kamar famfon wurin yana diga an kawo ruwa. Mairama ci gaba
tayi da diban ruwanta sai da ta ciko bokiti tana zuwa ta ajiye shi sannan ta cira hannu ta kwashe
Salame da mari mai gigitarwa don tana kallon yadda komai ya faru.
Ihu ta kurma gidan da suke neman abin gani kuwa aka fara fitowa bawa ido abinci.
"Ni kika mara Mairama?"
"Gaki ga kumatun Adda Salame. Na gaji da wannan abubuwan da kika tsira tun kafin muyi aure
har yanzu ana abu daya. Kece dukan min yara, yada min habaici da bakaken maganganu duk akan
me? Me na tsare miki?"
"Dole kice haka mana tunda kin rabani da wanda nake so"
Yadikko na jin haka ta kora yaran gabadaya tace su shiga dakinta. Hajjo ba kunya ta bisu don jin
ba'asi. Salame kasa karasa bayanin tayi don tasan ita ce da jin kunya. Tabarmar kunya ta nade da
hauka wai Mairama tana yi mata gani gani saboda ta fara rike kudi.
Da daddare da Malamijo ya dawo Yadikko ta bashi shawarar ya raba musu daki mana.
"Babu wadda ta bani ko asi domin ginin gidan saboda haka idan zasu cinye kawunansu ne ma su
cinye bai dameni ba. Wadda taji haushi ta kawo miji tayi aure"
"Idan bazaka rabasu ba ka taimaka ka zame musu uba na kwarai ka kawo karshen wannan rashin
jituwa da yake tsakaninsu. Kafi kowa sanin cewa da ba haka suke ba"
Shu'umar dariya yayi kafin ya turo hularsa gaba ya bata amsa "ki kan bani mamaki wani lokacin
kamar baki san zafin zawarci ba. Kodayake baki taba danawa bane amma cuta ce mai zaman
kanta. Shiyasa kika ga suna harin junansu. Babu mai tayar min hankali ni dai"
Babu yadda ta iya haka ta tashi ta bar dakin nasa tana kara godewa Allah da bai bata haihuwa da
Malamijo ba.
Mairama ta gama yiwa Karami shirin bacci ta goya shi tana jiran kanwarta ta kawo Radhiya da
take wasa a wurinsu Salame ta shigo ta dawo daga zance da dan gayun saurayinta. Matashi ne ko
auren fari baiyi ba. Baje ledar da ya bata ta tsire tayi a gefen katifarta da burin cusawa Mairama
haushi. Abin dariya yadda take ci tana shuu da baki.
Tana ganin Radhiya ta sake bude ledar da kyau. Yarinya tace "Ummi nama"
Mairama ta dauko wata leda babba ta mikawa Na'ima kanwarta tace suje su raba sannan ta dauko
wata 'yar madaidaiciya ta bude ta janyo hannun Radhiya ta bata cinyar gasasshiyar kaza. Sai yanzu
take gode Allah da haka nan ta bawa Bature kudi ya siyo kajin nan guda uku. Ta dauki daya ta
basu biyu su raba.
Ai kuwa Salame ta shaka har wuya ta shiga fadin maganganu wai gara su suna kwance ake basu.
Wahalallu kuwa sai sunyi da karfin jikinsu kafin su dandani zakin nama.
Shiru ma magana ce. Mairama bata ce mata komai ba haushi ya kamata tsiren ya fice mata a rai.
"Dazu nace kin rabani da masoyina baki tambayi ko waye ba bare ki bani hakuri"
"Indai Salisu ne nayi imanin bazai sakeki saboda ni ba. Allah kadai Yasan dalilin mutuwar aurenki
sai kuma ku kanku"
Kallon cikin ido ta yiwa kanwar tata "Mairama, na rigaki ganin Zayyan kuma na rigaki fara...."
A harzuke Mairama ta tashi duk wani kulli na kanta yana kwancewa. Yanzun ta gama gano duk
abubuwan da Salame tayi mata sunfi kama da kishi. Duk da mijin nata baya raye amma tana
tsananin kishinsa itama.
"Ya isheni ba sai kin karasa ba, na fahimci da aurenki kike son nawa mijin. Idan abinda Salisu ya
gano ya sakeki kenan sai ince Allah Ya dada karawa."
Daga haka bata koma cewa komai ba sai da ta tabbatar Salame tayi bacci ta sha kuka ta godewa
Allah. Ta tabbatar Zayyan ya sani shiyasa shima baya son Salame saboda kada yaci amanarta.
Sabuwar kewarsa ke ratsa duk wani sassa na jikinta tana inama yana nan tare da ita.
***********
Shekararsu biyu a gida Salame tayi aure. Kafin auren Mairama ta tuna cewa Salisu abokin Hadir
ne a lokacin ta kwantar da kai wurin sau uku tana tambayar Salame kwatancen gidansu Salisu. Ita
kuma ganin ta matsu tasan ko meye yana da mahimmanci shiyasa taki fada. Gashi baya zuwa
garin don idan za'a kawo mata Halifa aiko drebansa yake likkafa ta kara ci gaba.
Bayan auren Salame ne Idris dan gidan Mal Kallamu abokin Malamijo ya sami aikin koyarwa a
makarantar firamare ta gwamnati ta cikin Sumaila. Da yake suna shiri da Mairama kamar wasa ya
gabatarwa Headmaster da ita akan ko 'yan aji daya ne ta samu ta rinka koyarwa. Shine ya amince
aka yi mata cuku cuku sai gashi ta sami aikin a karkashin L.E.A. Kwalin karatun nata iyakarsa
sakandire shiyasa bata wuce aji daya ba a koyarwar. Ita dai ko yaya ne hakan yayi mata don
albashinta yana mata rana ga cinikin zobo da lamurje.
Haihuwar Salame daya aurenta ya sake mutuwa. Wannan karon lalaci da rainawa miji ya janyo
mijin ya saketa. Duk abinda zai kawo mata sai ta karba a wulakance tace ba haka baban Halifa
yake yi ba. Sai da ta kaishi makurar da yayi mata duka ya sakota.
To yanzu ma an sake dawowa gidan jiya. Dan da ta sake haifa shima babansa ya kaiwa yarsa. Ta
dawo gida an sake komawa zaman zawarci ga rashin abinyi. Bakincikinta ya karu da yadda
Mairama da yaranta suke rayuwa ta rufin asiri. Duka suna karatu a inda take koyarwa.
Ta soma saka gilashi ne a lokacin da ta fara fama da matsanancin kaikayin ido da gani dishi-dishi.
Ta sha wahalar idon sosai ta kuma kashe k