0% found this document useful (0 votes)
1K views67 pages

Makarantar Matsafa

The document is a fictional love and horror story centered around a young woman named Nafisa, who aspires to become a teacher despite her family's wealth and societal expectations. Nafisa faces opposition from her uncle, who believes that her ambitions are inappropriate for a woman of her status, leading to emotional turmoil as she grapples with her identity and desires. The narrative explores themes of gender roles, familial pressure, and the quest for personal fulfillment amidst societal constraints.
Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as TXT, PDF, TXT or read online on Scribd
0% found this document useful (0 votes)
1K views67 pages

Makarantar Matsafa

The document is a fictional love and horror story centered around a young woman named Nafisa, who aspires to become a teacher despite her family's wealth and societal expectations. Nafisa faces opposition from her uncle, who believes that her ambitions are inappropriate for a woman of her status, leading to emotional turmoil as she grapples with her identity and desires. The narrative explores themes of gender roles, familial pressure, and the quest for personal fulfillment amidst societal constraints.
Copyright
© © All Rights Reserved
We take content rights seriously. If you suspect this is your content, claim it here.
Available Formats
Download as TXT, PDF, TXT or read online on Scribd
You are on page 1/ 67

[23/01 20:58] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️

```LoVe aNd HoRrOr story```👽

By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}

*SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta.

*FCWA*☀️

________________________

01

Ra'ayi riga in ji ƴan magana, wannan haka yake a lokacin da matasa sa'anina ke
sha'awar fita waje domin yin dogon karatu tare da burace-buracen ababen ƙyalƙyalin
duniya ni kuma shiga ƙauyuka ne ra'ayina domin koyar da yaran da ke cikin duhun
jahilci.Sunana Nafisa,matashiyar budurwa ƴar kimanin shekara ashirin da biyu a
duniya.Na fito gidan sarauta,a jinin masu izza da taƙamar dukiya sai dai ni sam ba
wannan ne a gabana ba.Duk da na sha wahalar shawo kan mahaifina kan ya bar ni na yi
karatun zama malamar makaranta amma kuma fafur ya hana ni fita aiki wanda hakan ba
ƙaramar barazana ba ce da cikar burin nawa.

Fuska shaɓe-shaɓe da hawaye na nufi ɗakinsa,shine kaɗai tilo da na san zai iya yin
magana mahaifina yayi amanna da ita ba tare da gardama ba.Ko sallama ban yi ba
ballantana neman izini kawai na tura ƙofar,kamar kullum yana zaune kan dadduma yana
jan casbi.A gabansa na zube kamar raƙumar da ke jin ƙishi,ya ɗago fararen idonsa ya
zube su a kaina kafin cikin tattausan furuci ya ce “Naf !”
Baki na turo gaba idona na sake zubo da wasu sabbin hawayen.
“ Yau kuma wa ya taɓa ki?” ya tambaye ni cikin nutsuwarsa wacce ke ƙara masa
ƙwarjini.

Cikin kuka na ce “Daddy ne wai ba zan yi aikin gwamnati ba”

Yayi murmushin da ya bayyana fararen haƙoransa waɗanda kullum suke shan gugar
asuwaki kafin ya ce “ki je zan yi masa magana” da sauri na girgiza masa kai na ce “
a'a Please uncle ka tashi mu tafi yanzu kafin masu hura wuta su ƙara masa ƙaimi” na
faɗi haka ne saboda ahalin gidanmu suna da ɗagawa sosai ta yadda suke ganin kamar
ƙasƙanci ne a ce jinin gidan ya je yana aikin gwamnati,aikin ma koyarwa.

Ya buɗe baki zai yi magana na yi saurin kamo tafin hannunsa wanda yake lutuf da
tsoka sai taushi kamar na mace,hannun nasa ya duba da sauri na sake shi saboda ba
tun yau ba ya yi min hani da hakan ba wai iya gare shi ba kawai a'a hatta ƙannaina
maza ya hana ni raɓar su ko kuma taɓawa a tsakaninmu.

Na sunne kai wasu hawayen na sake surnano min suna ɗiga kan farin hijabina.
“Nafisatu?” ya kira ni cikin wani salo,ba tare da na ɗago ba na ce “ na'am uncle”
“Me yasa ra'ayinki ya banbanta da sauran danginki? Me yasa kike son yin aiki
alhalin mahaifanki sun tanadar miki komai na rayuwa?”
Na ɗago na dube shi kafin na ce “ uncle kai ma ba ka son na yi wannan aikin jahadin
na shiga ƙauyuka ina wayar da kan al'umma? Saboda me uncle? Kawai don iyayena suna
masu arziki shi kenan sai na yi kwance na dogara da dukiyarsu? Me yasa ni ba zan yi
aiki ba?”

“ Saboda ke mace ce!” ya bani amsa yana kallon idona,ji na yi kamar ya watsa min
ruwa zafi kawai sai na tashi na fita a guje ina gwanjin kuka.Ina shiga babban
falonmu duk sai na tarar da ƴan uwana kuwa suna ta cece-kuce akan maganar,ɗakina na
wuce direct na haye gado na kwanta rub da ciki amma abin mamaki sai na ji tamkar
kan cinyar mutum ne kaina yake amma sam ban bai wa hakan muhimmancin ba na ci gaba
da rera kukana,har na fi jin haushin rashin goyon bayan Uncle Salem kan na
Daddyna.A hankali na soma jin ana shafar gashin kaina wanda ke luluɓe da
hijabina,ido na soma lumshewa ba tare da na shirya ba yayin da kuma na soma sauke
numfashi akai-akai.Ban sani ba ko na shiga duniyar mafarki ne ko kuwa zahiri ne
amma sai na tsinci muryar wata dattijuwa na yi min gatana haɗi da bani tarihin
ababen tsoro kamar yadda na fi ƙaunar kallon horror film.

★A can ɓangaren Uncle Salem kuwa Nafisa na fita da gudu yayi saurin tattare
littafansa kafin ya gyara zaman hiramin kansa ya fito.Direct ƙofar da za ta sada ka
da babban falon ya nufa bakinsa ɗauke da sallama,tsit duk falon ya ɗauka kafin duk
su yi ƙasa da idanunsu saboda yadda yake da matuƙar muhimmancin da kuma girma a
idonsu.Cike da girmamawa suka soma gaishe shi “ Barka da fitowa Daddy ƙarami“ domin
haka suke kiransa in ka fidda Nafisa da take ce masa Uncle ita ma ɗin shine da
kansa ya koyar mata da hakan.

“Fatan dai ba ƙara ta ba aka kai wurinka,a toh don na san ba kasafai za a gan ka a
nan ba” cewar Daddy yana ɗan murmushi yana kallon babban abokinsa,amininsa kuma ɗan
uwansa.Uncle Salem ya ce “tun da ma ka sani ai shi kenan sai a fara shirya mata
abubuwan da za ta buƙata in ta je can”

Daddy ya ɗan nisa yana kallon yaran wurin duk sai suka tashi suka kama gabansu,sai
a lokacin kuma Uncle Salem ya zauna suna fuskantar juna.

Duk shuru suka yi na wani ɗan lokaci kafin Daddy ya ce “ ba wai yadda kake tunani
ba ne aboki,ina da dalili na daban da yasa ban so Nafisa ta yi nisa da gida”
Uncle Salem ya murmusa ya ce “tun muna makaranta ake faɗar wannan kalmar akan kana
da dalilin ƙin yin wani abu amma har yanzu ba ka taɓa faɗa min mene ne dalilin
ba.Abdul Hameed ka sani cewa su yara da kake gani sun fi son bin zaɓinsu kan na
iyayensu,kuma kai ma in ba ka manta ba...” sai kuma yayi shuru.
Yanayin fuskar Daddy ta ɗan sauya kafin ya ce “babu damuwa zan bari ta je ɗin,
Allah ya bada sa'a ya kuma tsare ta akan abin da nake tsoron faruwar” da “amen“
kawai Uncle Salem ya amsa kafin ya miƙe tsammm ya nufi ɗakin Nafisa,ya tura ƙofa
tare da yin sallama sai kuma yayi tsaye cak yana buɗe ƙofofin hancinsa saboda kalar
wani ƙamshi da ya dake shi da bai taɓa jin irinsa a wannan duniyar ba....
[24/01 08:57] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️

```LoVe aNd HoRrOr story```👽

By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}

*SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta.


*FCWA*☀️

________________________

02

Tsaye yayi yana kallon yadda take bacci tana wani taɓe baki kamar mai kuka yayin da
goshinta ke fitar da gumi.Ya furzar da wani huci kafin ya ƙarasa ya zauna bakin bed
ɗin,a hankali ya cire mata hijabin nata wanda ya ɗan jiƙe saboda zufa.Sumar kanta
wacce take baƙar ƙirin ya soma shafawa yana tofe ta da addu'a,a hankali ta soma
sauke ajiyar zuciya tana wani motsa idonta kamar mai son buɗe su.

Kamar wanda ke wasa da maciji haka ya soma shafa farar fatar fuskarta wacce ta yi
ɗan ja saboda kukan da ta yi.Wata irin azababiyar ƙaunarta ce yake jin tana bijiro
masa,ji yake tamkar ya ɗauke ta ya haɗiye tsabar so.

Sam bai san abokin nasa ya shigo ba don ya lula sosai a duniyar tunanin muradun
ruhinsa,sai jin saukar muryarsa yayi “ sai yaushe ne za ka sanar da ita ɓoyayyen
sirrin da ka binne abinka?”

Uncle Salem yayi saurin ɗagowa ya dubi Daddy ya saki ɗan murmushin da ya zame masa
jiki kafin ya ce “ har yanzu Naf yarinya ce aboki,zan ƙara mata lokaci ” sai kuma
ya mayar da duban nasa ga fuskarta a iya kallon da yake jifar ta da shi ya isa ya
fallasa ma sirrin da ƙunshe a zuciyarsa.

“ Shekarunta ashirin har da biyu fa,lokaci na ƙurewa girma na sake zuwar ma amma
har yanzu ba ka ajiye iyali ba aboki” Daddy ya faɗa cikin rashin jin daɗi.

“ Shi aure ai ba sauri yake so ba,a'a fahimtar juna aboki.Ka yi tunanin yadda Naf
za ta ɗauki lamarin ne in ta ji cewa ni mijinta ne alhalin a uba ta ɗauke ni?”

Daddy yayi murmushi kafin ya ce “ to ai kun fi kusa,ban iya na sani”

Uncle Salem na shirin yin magana aka shigo haɗi da sallama,Ammy ce hannunta riƙe da
kofin ruwa.A mutumce ta gaishe da Uncle Salem wanda a girme ya girme mata sannan ta
dubi mijinta hasken idaniyarta ta ce “ ga maganinta yau ba ta sha ba sam” ya karɓa
ita kuma sai ta fita.

Kan dakalin gado Daddy ya ajiye maganin yana mai kallon Nafisar wacce har zuwa
yanzu take baccinta yayin da kuma hannun Uncle ɗinta ke kan sumarta.

“ Aboki me kake ɓoye min dangane da Naf?” yayi tambayar cike da kulawa.
A ɗan rikice Daddy ya ce “ no babu komai zan je na duba wasu takardu in ta tashi ka
bata maganin” yana gama faɗa ya fice,shi kuwa Uncle Salem kai ya girgiza tun suna
yara suke tare amma har izuwa yanzu bai san dalilin da yasa abokin nasa ke ɓoye
masa wani babban sirri da ke ɗawainiya da rayuwarsa.Tun da Nafisa ta soma tasowa
yake lura da yadda hankalinsa kocokwam ke kanta hatta makaranta in ta je ya dinga
kiran waya kenan yana tambayar labarinta,yana ɗaya daga cikin abin da yasa kuma ya
basa aurenta tun ba ta san kanta ba amma har yau ya ƙi sanar da shi mene ne sirrin.
Ganin kamar baccin nata irin wancan ne da ta saba yi ,sai Uncle Salem ya ɗauki
kofin maganin ya cika bakinsa da shi kafin ya taɓe bakinta yana ɗura mata shi kamar
yadda tantabaru ke ciyar da junansu,a hankali kuma take haɗiye ruwan maganin da shi
ne ya haɗa mata shi a haka har ta shanye shi tasss.Da ya kai ƙarshe sai da ya ɗan
lashe mata lips kafin ya miƙe ya fita,sashensa ya nufa ya rage kayan jikinsa yayi
wanka ya fito ya shafa turare kawai sai ya ɗauki system ɗinsa ya soma aiki yana
duba saƙonnin sojawan da shine ya tura su mission a daji.Reppot ne iri-iri wasu na
murna wasu na jimame,tuni kansa ya soma yin hayaƙi yana jin cewa da buƙatar ya je
can ɗin da bada wata sabuwar atisaye.

★ NAFISA

Ban san iya lokacin da na ɗauka ina bacci ba,ko da na tashi da ƙamshin turaren
Uncle Salem na soma cin karo wanda ya game ko ina na ɗakin.Na turo baki gaba kafin
na dubi hijabina wanda na san da shi ne ya cire min shi ko shakka babu.Wanka na
shiga,bayan na fito na yi sallar azahar don sallah na ɗaya daga cikin abin da na fi
so a kaf cikin abubuwan ibada ita da azumi wannan kuma horarwa Uncle Salem ce tun
ina ƴar shekara sha uku yake saka ni yin azumin Litinin da Alhamis,tun ina kukan
yunwa har na kai na saba.

Ina zaune kan dadduma Ammy ta shigo,“yawwa kin sha maganin ashe ” shi ne abin da ta
fara cewa.
Shiru na yi ina tunanin yaushe na sha magani amma ban tuna ba,amma tabbas da na
tashi na ji bakina na zaƙin zuma.Na sake turo baki don kuwa tuni kwanyata ta hasaso
min ina baccin ya bani magani.

“ Ammy ni yunwa nake ji” na faɗa kamar zan yi kuka,“ Sai ki je ki ci mana,ki taso
ki kaiwa Daddy ƙarami abincinsa” ta faɗa tare da ficewa .Ina kukan sangarta na fita
zuwa falo,cikin gunguni nake cewa Ammy “ duk ga ƴan aiki nan amma shine ba za su
kai masa ba sai ni ”

Ta dube ni da mamaki kafin ta ce “ au! Dama can ƴan aiki ke kai masa abinci?”
Ba tare da na ce komai ba na nufi dianing na ɗauki ƙaton tray ɗin da aka jera komai
nasa,na ɗauka tare da fita ina tafe ina turo baki har na isa sashen nasa dakyar na
lalubo sallama can ƙasan maƙoshi na yi.

Bai amsa ba sai ɗagowa da yayi yana kallona kafin kuma ya mayar da dubansa kan
system ɗinsa.Hakan yasa na ji haushi na ajiye tray kan table har na juya zan tafi
na ji ya ce “ Naf!” na tsaya cak ba tare da na juyo ba ina jiran abin da zai ce sai
kawai na ji tsayuwarsa a bayana.Da sauri na juyo muna fuskantar juna,idona tab
tsoro nake kallon nasa da nake hango tsantsar ɓacin rai a cikinsu.

“ Ka yi haƙuri!” na faɗa murya na ɗan rawa.Bai ce komai ba ya kamo hannuna ya zauna


da ni kan kujera,“ ki zuba abinci ki ci” shi ne abin da ya faɗa sam babu wasa a
maganar sai ya je ya zauna ya ci gaba da aikinsa.

Ni kuwa kallo na soma ƙarewa kyakkyawar fuskarsa mai cike da yalwatacen saje da ɗan
madaidaicin gemu,kan jajayen laɓansa na tsayar da ƙwayar idona waɗanda ke yin
furucin da babu sauti da alamu wani abu yake karantawa.

Tamkar wacce aka yi wa dole haka na ƙanƙance ido ina karanta bakin nasa,na waro ido
jin tamkar har da muryarsa ke yi min raɗa a kunne tana sanar da ni abin da yake
cewa ɗin.
“ Ba ki ji abin da na ce ba?” ya jefo min tambayar,da sauri na mayar da hankali kan
abincin haka na zuba na soma ci lokaci-lokaci ina satar kallonsa har na gama.

“ Kawo min wanda kika rage ɗin” ya faɗa ,sai na dubi plate ɗin yadda duk abincin ke
cakule saboda miya da na zuba dayawa don ina son haka.
“ Uncle bari na zuba ma wani” na faɗa tare da ɗaukar wani sabon plate ɗin.
Ya ce “ wanda kika rage nake so”
Na ɗan ɓata fuska cike da kunya na ɗauka na kai masa,ya amsa ya ajiye shi kan
system ɗin kafin ya soma ci hankali kwance .

“ Uncle wannan wane ne?” na tambaya ganin wani matashin soja baƙi an naɗe kansa da
bandeji.
“ Wani ne” ya bani amsa,da ido na ƙara kafe hoton don kuwa ni dai yayi min kyau
sosai har ban san lokacin da na ce “ yana da kyau sos...” yadda Uncle ya ƙware ya
shiga yin tari ya hana ni ƙarasa abin da nake son faɗa,da sauri na je na kawo masa
ruwa ya karɓa tare da rufe system ɗin ya soma sha kafin kuma ya miƙa min kofin ya
je ya kwanta kan kujera mai zaman mutum uku yana wani jan numfashi tuni na tsure
wuri guda ina kallonsa....
[24/01 10:58] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️

```LoVe aNd HoRrOr story```👽

By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}

*SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta.

*FCWA*☀️

________________________

03

Jikina na ɗan rawa na isa gare shi ina mai zube wa ƙasa daidai kusan kansa na ce “
Uncle?” shuru yayi min bai ce komai ba haka ya ƙi buɗe idonsa,hakan sam ba ƙaramar
barazana ba ce a gare ni don gani nake na yi masa laifi ne har ya sa shi ƙwarewa
amma ban san taƙamaimai mene ne ba.

“ Uncle?” na ƙara faɗa wannan karon ina mai kai hannu ina gwale fatar idonsa a dole
so nake ya buɗe su ya kalle ni,na kuwa ci nasara ya buɗe su sai dai yadda suka yi
ja sosai har sai da na ji tsoro na ɗan ja baya.

Murya a disashe kamar wanda ransa zai fita yana kokowa da numfashinsa ya ce “
Nafisa me na faɗa miki? Ban ce kar na saki ko da wasa kin ce wani namiji yana da
kyau ko kuma ki kalle shi ba?”

Na ɗan ja ajiyar zuciya tare da matsowa na ce “ ka yi haƙuri Uncle ba zan sake


ba,amma saboda me Uncle? Ka ga fa duk ƙawayena suna da samari ni amma ka hana ni
kuma...kuma kamar mai baƙin jini maza sun tsane ni ” shaaa hawaye suka zubo min
tuna yadda ko a makaranta ƴan ajinmu ba su shiga duk abin da ya shafe ni,kusan kuma
malamanmu maza ma haka ba kasafai suke saka ni yin wani abu ba,in an zo nan ta
wurin ƙannaina da kuma mazan da suka zo karatu a gidanmu su ma duk hakan ce ke
faruwa.
Ba tare da ya ce min komai ba ya tashi zaune haɗi da ɗan duƙewa ya dafe saitin
zuciyarsa,ina ganin haka sai na miƙe da sauri har ina tuntuɓe na nufi bedroom ɗinsa
na ɗauko masa maganinsa.Na cika kofi da ruwa tare da ɓallo ƙwaya biyu na miƙa masa
ya karɓa tare da sha,cikin ƙanƙanin lokaci ya soma yin wata ajiyar zuciya kafin ya
ce “ ki je ki haɗa kayanki,zuwa jibi sai na kai ki can ƙauyen da za ki koya”

Duk ƙuncin da ya cunkushe min zuciya ne ya tafi ban san lokacin da ƙawa zuci ya ja
ni ba kawai na rungume shi ina cewa “ na gode sosai my Uncle,kenan har ka yi magana
da Daddy ya amince wayyy!” na yi ihun murna ina jijiga bayan Uncle da na rungume
tsam a ƙirjina kafin kuma na sake shi da gudu na bar falon.

Ina shiga ɗaki na tarar da family na cin abinci,ɗakina na nufa na shiga sauko da
akwatina ko taimakon masu aiki ban nema ba na soma shirya kayana ina yi ina
murmushi ina jin daɗi na luluɓe min ruhi.Sai hoton kaina nake gani a cikin aji ina
koyar da darasi wa ɗalibaina,ban zauna ba sai na haɗa duk kayana na jiki da kuma
jaka da takalma.

Takardu da littafaina ma trolly daban na ware musu kafin na miƙe ina yawo cikin
ɗaki ina magana ni ɗaya kamar irin yadda malamai ke yi.A hankali na soma jin ciwon
kan da ya zame min aboki tun na ƙurciya na ziyartata,tun ina daurewa har na kai na
kasa jurewa na haye bed na kwanta.Mafarkin da na jima ban yi ba tun shekaru kusan
uku shine na soma yi kamar ana jirana.

Tsaye nake kan ƙafafuna na mage ina juya idona masu matuƙar haske da hange nesa
tamkar na Alhuduhudu. Manyan-manyan dabbobin daji ne a tsaye a gabana suna buɗe min
bakunansu masu manyan haƙora yayin da ni kuma ke ankare da kowanne daga cikinsu
kafin mu soma yin dambe ina jibgarsu duk na yi musu jina-jina da jini kafin wata
halitta mai siffar babban sauro ta caka min bakinta daidai cikina .Azabar da ta
ratsa ni ce yasa na saki wani razananen ihu,daidai nan na farka sai dai abin mamaki
daidai wurin da aka cake ni ɗin har a zahiri ciwo yake yi min.

“ Lafiya Nafi?” Ammy ta faɗa wacce ta shigo yanzu hankali tashe,ido na soma juyawa
amma na kasa faɗa mata don ko na ce zan faɗi abin da na gani a mafarki kamar abin
tsayi sam bakina ba zai iya furtawa ba.

Hawaye kawai nake yi,sai shi ma Daddy ya shigo yana tambayar lafiya.Kai kawai na
girgiza masa ,ya zo ya kamo hannuna ya ce “ kina ji na Nafisa faɗa min mafarkin me
kika yi?” da sauri na janye hannuna daga cikin nasa,na diro daga kan bed na nufi
ƙofa.
Sai kuma na yi tsaye ganin Uncle shi kuma zai shigowa gemunsa na ɗigar da ruwa da
alamu alwala ce yayi.
Haɓata ya tallabo ta yadda zai iya kallon fuskata da kyau ,tsakiyar idona ya dinga
duba yana wani motsa baki kafin ya ce “kin kuwa yi Azkhar yau?”

Idona na soma juyawa ina son kauce kallon nasa da ba ƙaramin takura min suke ba,sam
babu daɗi ji nake kamar yana zuƙo raina ne.
“ Kin yi Azkhar na ce?” ya sake tambayata.
Kai na girgiza alamun a'a,don kuwa ban yi saboda tun asubah na samu saƙon cewa
sunana ya fito a jerin waɗanda za su je bautar ƙasa wannan zumuɗin ya shagaltar da
ni yin Azkhar kamar yadda na saba.

Ya sake ni kafin ya ce “ biyo ni” sai ya juya,haka na take masa baya ina waiwayen
su Daddy muka fita zuwa can sashensa da yake waje.
Ɗakin Uncle Salem ciki biyu ne da falo,ɗakinsa guda na bacci guda kuma wanda yake
zuba kayan maganin aljanu na ruƙiya.Direct ɗayan ɗakin muka shiga,kaina ne ya juya
da na shaƙi warin magani iri-iri yayin da gefen cikina daidai inda aka soke ni ya
soma motsi har sai da na danne wurin.

“ Zauna a nan” Uncle ya nuna min wata doguwar kujera,babu muso sai na zauna
ɗin.Wata kwalba ya ɗauko tare da zuwa kusa da ni ya zauna kafin ya buɗe ta,tun
kafin ya ce min na sha na soma hawaye don ni kaɗai na san irin abin da nake ji a
duk lokacin da ya bani ire-iren maganin nan.

Bakina ya taɓe tare da ɗura min maganin,jikina ya ɗauki rawa kafin cikin fitar
hayyaci na soma basa labarin mafarkin da na yi tiryen-tiryen.Kwantar da ni yayi
yana mai jan doguwar rigar jikina sama,da sauri na rumtse ido lokacin da ya janye
hannuna ya ɗora nasa a daidai wurin da ake ta yi min motsi.

Teburin da ke ɗauke da tarkacen da shi kaɗai ya san na mene ne ya jawo,ina ji ina


gani da raina Uncle Salem ya soma tsatsaga fatata da reza.Banda wani zaɓi banda
hawaye don tuni maganin da ya bani ya kashe min dukkan jijiyoyin jiki sai kaina da
ke faman juyi tamkar an jefa ƙwarya a ruwa.

Wata kwalba ya ɗora daidai wurin ya soma tatsar jinina har ƙarar fitarsa kake
ji,kamar minti biyu kafin ya cire kwalbar ya ajiye ta kan teburi.Wani magani ya
shafa min a daidai ciwon mai bala'in zafi,har sai da raina ya kusa fita kafin da
sauri ya cika bakinsa da wasu ruwa ya zo ya fara shayar da ni su.Duk ɗigo ɗaya na
ruwan da zan sha to tamkar ana warware azabar da yake jikina ne , wannan yasa nake
shan maganin cike da zalamar da ta haifar min da soma shan yawunsa da kuma laɓansa.

Jikin Uncle Salem ne ya ɗauki wata irin rawa jin Naf ɗinsa na sumbatarsa kamar za
ta cinye leɓensa,duk wani tsohon feeling nasa da yake faman yin ƙasa da shi a
kowacce safiya ya soma taso masa.A daidai gaɓar da ya soma mayar mata da martani
kuma tuni bacci ya ɗauke ta,idonsa na fitar da wasu irin hawayen jaraba ya soma
sunsunar wuyanta yana jin tamkar ya mayar da ita cikakkiyar mace ko zai samu
salamar ruhi.

Dakyar ya rareashi kansa ya janye daga jikinta,daɓas ya zauna yana duban yadda take
baccin wahala . Ƙonannen jinin mai tattare da guba yayi baƙi ƙirin a cikin
kwalba,sai ya ɗauke shi ya je ya zubar toilet ya wanke kwalbar.

Sai da ya je ya sake wata alwala sannan ya nufi masjid,a can ya samu Daddy bayan
sun yi sallar sun fito ne Uncle Salem ya dubi abokin nasa ya ce “ Abdul Hameed ban
san me yasa ka zaɓi ka ɓoye min rufaffen sirrin Nafisa ba,amma hakan bai da wani
amfani don kusan na fahimci matsalar junun da ke jikinta ya samo asali ne daga can
tushe ba wai gamo ta yi da su ba”

Cak Daddy ya tsaya yana kallonsa, Uncle Salem ya jinjina masa kai ya ce “ tabbas ko
yau sun ziyarce ta,saboda sakacin addu'ar da ba ta yi ba”

Daddy ya ce “ mu je can gida zan yi ma bayani” haka suka wuce suka isa,a keɓaɓen
falon Daddy duk suka zauna tare da yin shuru Uncle Salem ya matsu ya ji labarin
yayin da shi kuma Daddy ya rasa ta ina zai soma.Can ya nisa tare da furzar da huci
kafin ya ce “ to da farko dai kamar yadda na faɗa ma ni ɗana ga sarauniya Ayodele
Ayush,kafin zuwan Musulunci a Victoria Falls suna bautar ababen bauta iri-iri ,yin
tsafi kuma sai ya zama adon garin.Sai dai sannu a hankali duk komai ya canza saboda
yadda mahaifina sarki Ameer ya taka muhimmiyar rawa ganin ya kawar da duk wani
fasadi sai dai kash zuwana duniya kuma aka tsiro da wasu sabbin canfi wai alamomi
sun nuna za a sake yin maimaici wato daga cikin tsatsona za a samu wacce za ta
jagoranci mulkin ƙasar.Amma tabbas ni ba magajin sarki ba ne,sosai na ji tsoro da
jin haka don tamkar karatu haka ake biya min maganar nan har na mallaki hankalin
kaina”

Uncle Salem yayi saurin katse shi da cewa “ haba aboki ta ya za ka yarda da wani
canfi?”

Daddy yayi murmushi wanda ya fi kuka ciwo kafin ya ce “ dole na yarda mana,duba da
tun ina ɗan shekara ashirin a duniya na ajiye iyali saboda yadda kullum nake kasa
bacci ina harin neman abokiyar rayuwa wacce zan jefar wa da ƙwan haihuwar shugabar
gobe ko zan samu sukuni ”
Uncle Salem ya ce “ kana nufin wai Naf?”

Daddy ya jinjina kai ya ce “aboki tun lokacin da na yi aure zan ce ma wannan


larurar da ka san ni da ita ta mugun feeling ta kau,shi ma tun a daren
farkonmu.Sannan kana dai ganin yadda lamarin aurena ya kasance a sirrance sai daga
baya iyayena suka sani,har bisa yanzu sarki fushi yake da ni saboda na ƙi yarda na
zauna a can Victoria Falls ni kuma ina gujewa Nafisa ƙalubalen da za ta fuskanta ne
in ta zama shugaba”

“To amma mene yake baka tabbacin cewa hakan za ta kasance?” Uncle Salem ya
tambaya .
Daddy ya ce “ saboda kama take da wata goggon Mamana ita ce mace ta biyu da ta
mulki Victoria,to yadda ka ga Nafisa ita ma haka take kai kace tsaga kara ne aka
yi.Hakan kuma babbar matsala ce domin zai iya kasancewa ita ta dawo duniyar nan a
gangar jikin Nafisa ”

“ Wai ko sarauniya Deborat?” Uncle Salem ya tambaya,don kuwa ita ɗin ba ɓoyayya ba
ce a duniyar nan duk kusan labarinta ya karaɗe ƙasashen duniya saboda shahararta
wurin iya yin tsafi,sai dai ko kafin Daddy ya ce wani abu tuni tv ɗin da ke manne
jikin bango ta soma yin wata tsaga “ƙiiiii!” kafin kuma ta faɗo ga ƙasa ,sai iska
kuma mai ƙarfi wacce ta haifar da fashewa ƙwan lantarki ji kake ɗuuu haskensa ya
ɗauke sai labulaye suka soma tashi sama suna wulwulwul....
[25/01 10:35] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️

```LoVe aNd HoRrOr story```👽

By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}

*SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta.

*FCWA*☀️

________________________

04

A cikin duhun ɗakin ne Daddy da Uncle Salem suka hango wata mace sanye da fararen
kaya wanda ko tantama babu likafani ne.A tsaye take jikin window sam ƙafafunta ba
su taɓa ƙasa ba sai wani lilo suke kamar wacce aka rataye,farin gashin kanta kuwa
sai yin sama yake iska na naɗa shi.

Cikin muryarta wacce kana ji ka san ba ta ɗan adam ba ce ta soma yin magana,“ ko
kai ko abokinka babu wanda ya isa ya dakatar da ni daga yunƙurin da nake,Yarima
Abdul Hameed ban sani ba ko ka san cewa sunan Deborat ya haramta ga duk wanda yayi
hijira ya bar gidansu domin guje abubuwan da allolinmu za su zartar,ka sani cewa
Nafisa jaruma ce ba mu zaɓe ta ba sai da sanin za ta iya.Sannan ka godewa Allah da
ya kasance aikin alkhairi ne za ta gudanar ba wai na cutar da al'umma ba,sannan kai
kuma da kake ta ƙoƙarin dakatar da mu ziyartar ta ka sani akwai lokacin da
maganinka ba zai yi aiki a jikinta ba don haka gara ka baiwa kanka lafiya ka bar
matarka ta yi aikinta yadda ya kamata.A tunaninka hatta auren naku ba mu sani ba?
Mun sani sarai saboda kai ne za ka yi jinyarta a lokacin da ta kammala aikinta na
farautar azzalumai ” tana gama faɗa kawai ta bi ta window ta fita yayin da kuma
komai ya dawo normal hatta hasken ƙwan lantarki rasss ya koma yana yi .

Daddy da Uncle Salem sai suka fara ƴar kallon-kallon ba tare da sun cewa juna komai
ba.
Can Daddy ya kasa yin shuru ya ce “ aboki ka yarda da fatalwa?”
“ Na yarda mana saboda ni ma ita ce ta raine ni” Uncle Salem ya basa amsa .

“ Ban gane ba”


“ Eh kamar yadda na faɗa ma ni kaina ban san iyayena ba domin a titi aka tsince ni
to Inna Delu ta raine ni ta bani dukkan tarbiyya da kuma kulawa ta uwa,sai bayan na
mallaki hankalin kaina ne ta sanar da ni ita wace ce saboda za ta koma makwancinta“

Daddy ya ce “ wai kana nufin dama Inna fatalwa ce?”

“ Eh sosai ! Bari na je na duba na ga ko Naf ta tashi” ya faɗa tare da miƙewa ya


fita ,hankalinsa da tunaninsa na kan fatalwar Deborat wacce kusan duk dare Inna
Delu na yi masa gatanarta.
Ko da ya shiga ɗaki ya tarar Nafisa na ta yin baccin gajiya ,ya dubi agogo ya ga
lokaci sai tafiya yake ga shi kuma ba ta yi sallah ba.Sam bai son ya tashe ta amma
sanin sallar asar ma nada ƙurarren lokaci yasa ya soma shafar fuskarta da tafin
hannunsa mai taushi da sanyi.

Cikin bacci na soma jin sanyi na ratsa min kumatu,ga taushi kamar auduga.A hankali
na ware idona na sauke su kan kyakkyawar fuskarsa,ban ida warkatsewa ba ya ce “
lokacin sallah Naf”

Jin ya ambaci sallah na yi saurin tashi hankali tashe don na tsani na makara,ya ɗan
ja da baya yana mai ci gaba da kallona kafin kuma ya fita.Ni ma fitowa na yi na
wuce can sashenmu sai da na fara gabatar da sallar sannan na yi wanka na saka riga
doguwa marar hannu na ɗaura kallabinta sannan na fita.

Yunwa nake ji hakan yasa direct kitchen na shiga,Ammy ce da A'i mai aiki ke ta
faman yin girki da dukkan alamu yau sarautar ta Daddy ta motsa shi yasa Ammy ke
aikin da kanta.
“Yunwa nake ji” na faɗa kamar zan yi kuka,A'i ta yi dariya ta ce “ oh shagwaɓarki
Nafisa ko auta albarka ”
Ammy ta ce “ bar ni da ita dai ta ci gaba da sakalcin in ta je can ƙauyen ai na ga
wacce za ta yi wa”

Kamar wacce suka yi wa allurar zaburar wa kuwa haka na wani kwanto jikin A'i mai
aiki wacce nake kira da Inna na ce “ ai tare da Innarmu zan tafi ita za ta dinga
kula da ni,kafin na dawo ta yi min girki mai daɗi” A'i ta washe baki don sosai take
jin daɗin yadda Nafisa ta ɗauke ta tamkar Kakarta sam ba ta nuna cewa ita ke ƙasa
gare ta,haka kuma ita ce ta raine ta tun tana cikin tsumman goyo ko aiki za ta yi
haka take goye ta in kuma ka ga sun rabu to Uncle Salem ne ke gidan.

“ Ki ma cire wannan a ranki don Inna A'i ba za ta bi ki ba” cewar Ammy tana mai
zuba min kunun gyaɗa a kofi.
Na ce “ wai Innarmu ba za ki je ba?”
A'i ta ce “ ke wasa take yi miki fa,tuni ai na haɗa komatsaina na ƙulle a buhu”
cike da jin daɗi na ɗauki kofin kunun gyaɗana na fito falo na zauna,tv na kunna na
saka horror film ina kallo ina sha sam ban jin tsoron abubuwan da ake nunawa wani
sa'in ma ji nake tamkar ƴan uwana ne.

Ƙamshin turarensa ne ya fara yi min maraba kafin shi ya shigo,na ɗaga kai ina
kallonsa .Sanye yake cikin kakin soja sun yi bala'in yi masa kyau sai dai ya aske
gemunsa da sajensa,da sauri na ajiye kofin hannuna ina turo baki ina kallonsa tuni
kuwa ya fahimci dalili don tun ina yarinya nake faɗa masa ina son saje,sannan Inna
A'i ta taɓa faɗa min ranar farko da na fara ganin Uncle Salem ya cire sage da gemu
haka na yi ta kuka ina ɓata fuska sannan kuma na ƙi yarda da shi .

Da sauri na miƙe zan bar wurin yayi saurin kamo tsintsiyar hannuna yana mai cewa “
oyaaa Naf ɗin Uncle kar ki yi fushi zo ki shanyen kununki ki zo mu je na yi miki
shopping ” jin ya ambaci shopping yasa na juyo don na san duk cikin shirye-shiryen
tafiyata ne.

Na sake turo baki a karo na biyu kafin na ce “amma shine ka aske ...” yayi wani
murmushi mai sauti yana cewa “ zai fito ai,kin ga kar ki yi fushi da Uncle ɗinki”
sai ya zaunar da ni tare da ɗaukar kofin ya ci gaba da bani kunun har na shanye
kafin ya ce “ je ki canza kaya ki zo mu wuce”

Da murna na koma ɗakina,sai dai ban canza kayan ba kawai dai na zumbulo dogon
hijabi har ƙasa.Ina fitowa Uncle Salem ya matso kusa da ni kafin ya ce “ ki canza
kaya Naf ” da mamaki na dube shi,ko ta ya aka yi ya gane ban canza ba.
Na marairaice fuska na ce “ Please mu tafi kar dare yayi” ya ɓata rai yana kallon
ƙirjina,sai na turo baki na koma ɗaki na je gaban madubi na yi tsaye ashe rabon a
yi ne ya kai ni don kuwa ina tsaka da tantance yadda saka hijabin bai ɓoye ainihin
shap ɗin jikina ba sai na hango wata farar mata tana saka min abubuwa a jaka,ta yi
zaune daram kan gadona.Na waiga da sauri sai na ga wayam,ina maida dubana kan
madubi daidai nan ta bi ta window ta fice.Da mugun sauri na je bakin windown sai na
gan ta a buɗe alhalin kullum a rufe take ban barinta a buɗe .

“ Naf wai har yanzu ba ki shirya ba?” na ji muryar Uncle Salem a bayana,na juyo da
sauri ina cewa “ yanzu zan shirya“ sai kuma na ga yana buɗe ƙofofin hancinsa ya ce
“ wannan wai ƙamshin mene ne kamar na Gawa?”

Da ido na tsure shi ina kallo jin ya ambaci gawa,a zuci na ce ‘ kenan dai da gaske
ne abin da idona ya gane min? Ko ɗaya daga cikin fatalen da ake cewa sun shigo
duniyarmu ne?’

“ Ki yi sauri ina jiran ki a mota” ya faɗa tare da fita.Kayan atamfa na saka kafin
na ɗora hijabi sama,sai da na je na shaidawa Ammy kafin na fita can tsakar gida
inda yake jirana.Bayan motar na shiga na zauna kusa da shi,waya na tarar yana yi
sai da ya bai wa direba umarni sannan ya soma tuƙa mu.

Sai da muka hau titi sosai kafin ya kashe wayar wacce duk rabinta turanci ne da
kuma sunayen makaman yaƙi.Na ɗaga kai na dube shi daidai shi ma ya dubo ni,sai muka
haɗa ido hannuna ya kamo yana murmushi ban san dalilin da yasa ni ya hana ni na
dinga riƙe hannunsa amma shi in ya yi niyya haka yake kamo ni.

“ Faɗa min me da me kike son saya?” ya tambaye ni yana ɗan matsa hannuna,ko kaɗan
ban jin wani abu na daban saboda a matsayin uba na ɗauke shi.Na langwaɓar da kai na
ce “ Chocolat da kuma teddy babba,sai turare da kuma ƙumbar kanti,da lipstick,da
uhmm yawwa da sabuwar waya Uncle Please ” na ƙarashe tare da ciro ƙafafuna na yo
sama da su tare da ɗora su kan nasa,ina jin lokacin da ya ja wani numfashi kafin ya
ce “zobe fa?” ya tambaye ni saboda yadda ya san ina son zobe sai dai duk in ya siya
min ban san ya ake yana ɓata ba.Na saki ɗan murmushi kafin na ce “ na hannunka nake
so” sai na soma ƙoƙarin zare wani zobensa mai shegen kyawu da sauri ya dakatar da
ni yana mai cewa “ zan saya miki wani dai”
Na turo baki na ce “ Uncle wannan zoben dai kamar a tare aka haife ku ko kuma wani
ɗanka sam ba ka son rabuwa da shi,ina ga ma ka fi sonsa fiye da Niii!” na ɗan ja
ƙarshen ban shirya ba saboda yadda ya kafe ne da rikatatun idonsa masu matuƙar
kaifi .

“ Shi zoben?” ya tambaye ni cikin wata irin murya,ban iya cewa komai ba sai kai da
na ɗaga masa alamar eh.A gabana ya cire zoben daga babban yatsansa na tsakiya sai
ya kamo hannuna na hagu ya zura min shi a yatsana na biyu,a hankali yayi ta shafar
zoben yana kallon tsakiyar idona har ya gama daidaita shi,sam tunanin ta ya aka yi
zoben da shi kansa a babban yatsa kawai ya tsaya masa amma ni kuma a yatsa na biyu?
Wannan tunanin sam bai shigo kwanyata ba sai na shiga yin murna har da wani rungume
shi, Uncle Salem ya ƙara jan ajiyar zuciya a karo na biyu.
Muna isa Mall ɗin ya ja ni izuwa ciki,ana ganinsa da kakin soja duk a soma basa
girmansa,ɗaya daga cikin ma'aikatan wurin aka haɗa ni da ita muka je tana nuna min
kaya masu kyau sam ban san Uncle yayi tafiyarsa ba sai da muka sauko ƙasa ina ta
baza ido amma ban gansa ba.Idona ya ciko da hawaye har zan tambayar mai kula da
shiga da fita sai ga shi ya shigo ,ya sakar min murmushi kafin ya ce “ zo ki zaɓi
wayar kafin a kira sallah” ya wani kama hannuna zuwa inda aka jera wayoyin manyan
masu tsada Iphone na ɗauka sai muka zo nan ya biya kuɗi muka wuce mota yayin da
kuma aka kawo min kayana har mota.

Tun a hanya aka soma kiran sallah ga shi wurin da ɗan nisa, Uncle ya ce “ Jabeeru
ɗan tsaya mu yi sallah kar jam'i ya wuce mu,dama da alwala ta” wuri direba ya samu
ya parker suka fita suka bar ni nan,ina duba sabuwar wayata na ji an ƙwanƙwasa
gilashin mota.Da sauri na dubi wurin sai na ga wata tsohuwa mai ƙusumbi a tsaye
tana kallona da manyan idonta da suka shige can ciki tsabar tsufa.
Banda ko dala a hannuna tun da ban fito da jaka ba,duk a tunanina almajira ce
wannan yasa na buɗe ƙatuwar ledar chocolat da sauran kayan maƙulashe na ɗauko mata
cake guda biyu da kuma jus,ina buɗe murfin motar sai ta ɗan matsa gefe na
fito .Fuskata ɗauke da murmushi na ce “ ga wannan Kaka banda kuɗi hannuna”

Cike da murna ta karɓa kafin ta ce min “ ki san yadda za ki yi ki hana mijinki


tafiya dajin nan rayuwarsa na cikin haɗari tarko ne aka yi masa”
Na yi dariya na ce “Kaka ai ni budurwa ce banda aure”

“Naf shiga mu tafi kin wani fito waje duk ana kallon ki“Uncle ya faɗa tare da buɗe
min ƙofa na shiga ina kallon tsohuwar wacce ke tsaye tana yi min murmushi amma abin
da ya bani mamaki yadda aka yi sam Uncle bai gaishe ta ba alhalin na san shi da
girmama tsofi don shine ya koya min yin sadaka musamman masu rauni irinsu.

Sai bayan na shiga motar ne na lura da ashe tun tuni shi Jabeeru ya zauna kan
mazauninsa.Har muka iso gida da tunanin tsohuwar nan danƙare a zuciyata amma sam
ban faɗa wa kowa ba sallah kawai na yi na fito na soma buɗe kayan ina nunawa Ammy
da kuma ƙannaina biyu Abdul da Mubarak,sai kuma sauran ƴan uwana waɗanda suke
cousin ɗina ne.Wayar iphone ɗin dai ce duk suka yi ta taya ni murnar mallakarta don
su duk sun jima da yinta in aka cire ƙannaina.Bayan an yi sallar isha'i Daddy da
Uncle suka shigo a tare nan ne na ji yana faɗar cewa gobe in Allah ya kai mu
Jabeeru direba zai kai mu can ƙauyen Ƙwargwam ni da Inna A'i saboda shi zai wuce
can mission.Sam kwata-kwata ban kawo zancen cewa akan Uncle Salem wannan tsohuwar
ke magana ba shi yasa kawai ban wani damu ba sai ma rigima da na ɗora masa na cewa
to dole da zarar ya sauko ya fara zuwa can inda nake kafin ya zo gida.

A cikin daren ma sai da na yi mafarkin tsohuwar nan ta sake ce min kar na bar
mijina ya tafi,amma na share batunta na soma shirin tafiya don tuni tun jiya ka
saka komai namu a cikin mota.

Ƙarfe tara tuni mun yi breakfast,sai duk muka fito.Uncle Salem motarsu ce ta wurin
aiki ta zo ta ɗauke shi yayin da ni kuma ta gidanmu ce.Duk lokaci guda motocin suka
tashi muka hau titi,ta windown mota muke kallon juna ni da Uncle muna sakarwa juna
murmushi har aka zo mararrabar hanya motocin namu suka rabu.Sai a lokacin na maido
dubana kan titi ina jin abu biyu,kewar Uncle da kuma murnar cikar muradina ba tare
na san abin da ke can yana jirana a ƙauyen Ƙwargwam.....
[25/01 20:21] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️

```LoVe aNd HoRrOr story```👽

By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}

*SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta.

*FCWA*☀️

________________________

05

Sosai Jabeeru ke sharara gudu kan titin da yake tsit babu kowa kamar an yi ruwa an
ɗauke.Kamar daga sama haka na ga tsohuwar nan mai ƙusumbi daga can nesa ta yi tsaye
tsakiyar kwalta amma duk nisan tazarar bai hana ni ganin ƙwayar idonta ba wacce ke
yi min magana kuma raɗam nake jin sautin muryarta kamar waccan lokacin.
“ Me kike jira da har yanzu ba ki sanar da Uncle ɗinki saƙona ba? In wani abu ya
samu ɗana sai na ɗanɗana miki azabar da ba ki taɓa tunani ba ballantana gani a
duniya” na shagala sosai da kallon ƙwayar idon nata sam ban san lokacin da Jabeeru
direba ya kawo dab da ita ba,cikin ƙaraji na ce “ Jabeeru ka taka burkiiii!” sai
dai ko kafin in rufe bakina tuni ya ratsa ta jikinta amma abin mamaki sam bai kaɗe
ta tamkar dai iska wannan mai kaɗawa haka gangar jikinta take.

Jabeeru ya tsayar da motar,ina haƙi ina ƙari na ɓalle murfin motar na fita na je na
yi tsaye na duba can gaba a zatona ko zan ganta sheme a ƙasa sai dai wayam ba
komai.Kamar wata mahaukaciya haka na ƙara yi a guje na duba bayan motar nan ma babu
kowa ko ɗigon jini babu.Da na leƙa ƙarƙashi ma babu komai,tuni sun fito suna
tambaya ta lafiya.Kai na dafe kafin na koma cikin mota na ɗauki wayata don na kira
Uncle Salem sai dai sam babu network.Zuwa wannan lokacin hankalina ya soma tashi ji
nake kamar dai gaske wani abu zai same shi.
“ Wai Nafisa lafiya duk kike wannan kai komon kamar mai saffa da marwa?” Inna A'i
ta tambaye ni.
Ba tare da na dube ta ba na ce “ network nake nema ina son kiran Uncle ne”
Jabeeru direba ya ce “ Hajiya fatan dai lafiya?”
“ Jabeeru ina son samun network don Allah,mu je ko cikin dajin nan ne mu duba ko
zan samu tsauni na hawa” na faɗa kamar zan yi kuka.

Inna A'i ta ce “ a'a gaskiya ba zan bari ki shiga daji ba,daga ganin wannan ciyayi
ba za su rasa maciji ba.Ki yi haƙuri mu ƙara gaba na san za a samu”
Jabeeru direba ya yi caraf ya karɓe zancen“ eh Hajiya wallahi sosai ake samun
macizai zo mu ƙara gaba ai mun kusa shiga inda ke da network tun da ga ƙarfen
falwaya can ina tsinkaye” jin yadda suke ta tsorata ni yasa na yarda muka koma ciki
sai dai juyin duniya motar ta ƙi tashi a dole kuma muka sake fitowa Jabeeru ya soma
dubawa.

Da wani irin gudu na ratsa cikin ciyayin saboda wasu manyan duwatsu da idona suka
hango min.Ina jin Inna A'i na kirana amma ko waigowa ban yi ba ballantana na amsa
mata,da isa ta na hau can ƙoli ai kuwa sai ga network ya shigo ko kafin na kira
Uncle text ne birjit irin waɗanda ake turowa in an so a kira mutum amma ba a same
shi ba.Hannu na rawa na rubuta lambar Uncle Salem wacce ke zaune raɗam a
kwanyata,sai na ji yana cikin kira amma ba a ɗauki lokaci ba ya ɗaga yana mai jan
ajiyar zuciya yayin da ni kuma na saka masa kuka tare da soma magana “ Uncle Please
kar ka tafi tarko suka haɗa maka duk ƙarya ce babu wani kashe sojojinku da aka yi,
Please ka koma gida”

“ Naf lafiya kike kuwa? Wane irin zance ne wannan? ” ya faɗa .Na ce “ ni ma ban
sani ba wata baƙar tsohuwa ce ke son haukata da farko ta ce mijina,yanzu kuma ta ce
kai”

“ Ya siffarta take?” ita ce tambayar da ya jefo min.


Na ce “ tana da ƙusumbi...” ko kafin na ida koro masa sauran bayanan ya ja wata
ajiyar zuciya kafin ya ce “ Ok to” yana faɗar haka aka shaida min kuɗina sun
ida,daidai nan kuma na ji muryar Inna A'i tana cewa “ Nafisa zo mu wuce motar ta
tashi” tuni na sauko na kama hannunta muka fito daga cikin ciyayin don sai da ta
biyo sawuna.

Muna shiga motar muka ci gaba da tafiya cikin gudun da ya saba,sai da muka yi wajen
awa uku kafin ya tsaya mu ci abinci da kuma fitsari sannan muka ɗora tafiya .Ba mu
kai ƙauyen Ƙwargwam ba sai wuraren sallar azahar lokacin rana ta zo tsakiya,muna
shiga garin gabana ya soma faɗuwa ina jin wani irin yanayi kamar wacce ta taɓa zuwa
dama har da wasu tsofin moments nake gani wanda na rasa daga ina suke ziyartar
kwanyata sam ban taɓa kawowa cewa suna ɗaya daga cikin ire-iren mafarkan da nake yi
ba tun ranar da na soma ganin period.

Kamar yadda tun kafin mun tawo Uncle ya bani duk wasu takardun sheda da ya karɓo
daga can makarantarmu haka muka samu wani yaro ya kai mu can gidan shugaban
makarantar wanda yake cikin ƙatuwar school ɗin wacce sosai na yi mamakin yadda aka
yi ma aka gina ta.

Da isar mu can sai muka taras da wasu malaman da alamu suma zuwansu kenan .Tarba
muka samu daga wajensa kafin ya nuna mana ɓangaren jerin flat/appartement ɗin da
aka tanada domin malaman ƙetare waɗanda ba ƴan ƙauyen ba.Kowane daga cikinmu ya
bamu key ɗin ɗakinsa kafin mu wuce ,Jabeeru ya tuƙa mota har zuwa ƙofar ɗaki mai
lamba uku wato nawa.Shi ne ya kai mana kayanmu ciki,ɗakin tsaf yake bai da datti
kamar an sa da zuwanmu.Ciki guda ne sai toilet da kuma ƴar ƙaramar kitchen,haka duk
muka jera komai wajensa Inna A'i ta cire zanen da muka tarar shimfiɗe kan ƴar
madaidaiciyar kafitar ta shimfiɗa wata,na shiga toilet bakina ɗauke da addu'a na yi
wanka tare da alwala sannan na fito sai na tarar tuni Jabeeru ya tafi ko sallama
bai yi min ba .Dadduma na shimfiɗa na gabatar da sallah yayin da ita kuma Inna A'i
ta shiga toilet ita ma don yin wanka.Ina zaune ina lazumi na ji ihunta haɗi da yin
ƙara,kafin kuma na ji tana magana da alamu akwai abin da take kora can kuma ta fito
kamar wacce aka jefo.

Cike da kulawa na ce “ Innarmu lafiya?”


Cikin masifa ta ce “tsakaka ce na gani kin san ban son ganinta“ ta bani amsa.
Na ce “ ai kuwa inda kashe ta kika yi da kin samu lada ”

Ba tare da ta ce komai ba ita ma ta zo ta yi sallar bayan ta gama ne muka soma taɓa


hira kafin kuma mu ji bugun ƙofa,ita ce ta je ta buɗe sai kuma ta dawo hannunta
riƙe da kwanon abinci tana mai cewa “ kin ga shugaban makaranta ya aiko mana da
abinci”

Na ce “ ban jin yunwa amma in kina ji kawai ki ci ki rage min”

Inna A'i ta ce “ ai kuwa ina ji tun da a mota abin turawa ne kawai kika bamu ” tana
nufin cake.Na yi dariya tare da ɗaukar wayata na soma saita app don jiya ban samu
na yi ba.Ita kuwa Inna A'i hankali kwance take cin shinkafa da miyar kajinta tana
santin cewa ashe ƴan ƙauye ma sun iya girki,ashe ba ta san guba ce take ciwa kanta
ba.

★ Uncle Salem

Tun jiya da ya rabu da zoben hannunsa yake jinsa wani iri tamkar gangar jiki babu
ruhi amma babu yadda ya iya haka ya haƙura ya bar wa Naf ɗinsa.Tun asali zoben Inna
Delu ce ta basa shi a ranar da ta sanar da shi za ta koma can maƙabarta
makwancinta,sam bai san amfanin zoben ba amma yau da Nafisa ta kira shi ta sanar da
shi cewa ta ga tsohuwa mai ƙusumbi kawai ya fahimci wato sirrin ganin Inna Delu da
yake a duk lokacin da wata matsala ta tunkaro shi ya ta'allaka ne da zoben.Suna
tsaka da gudu ya cewa direban da ke jansa yayi su koma gida,cike da mamaki direban
ya juyo ya dube shi sai dai babu damar tambaya don bai ma ga fuskar tambayar ba .
Suna tafe yana tunanin yadda Naf za ta ɗauki wannan lamari mai kama da wahayi don
gudu yake abin ya bata tsoro don ya fahimci har zuwa yanzu kamar ganin abin take a
mafarki.

Tunani ya soma ta yadda zai bi ya karɓe zobensa ba tare da ya ɓata mata rai ba,a
haka har suka isa Company.Ya fita cike da izzarsa wacce ba kullum yake bayyanar da
ita sai in yana cikin fushi ko kuma yana son gwada ƙarfin ikonsa akan wasu.Ofis
ɗinsa ya nufa tare da buɗe shi,yana shiga ya duƙufa yin bincike.

★Ƙwargwam

Sallah kawai ke raba ni da wayata wacce bayan na kira gida mun gaisa na shaida musu
mun sauka lafiya sai na soma chating da ƙawayena a whatsapp.Hira sosai muke a group
ɗinmu na ƴan makaranta har dare yayi,sam ba mu yi girki ba saboda akwai abinci shi
Inna A'i ta ƙara ci kafin ta kwanta ni kuma sam ban jin yunwa saboda dama haka nake
muddin ina maƙale da wayata.

Kiran Uncle Salem ya shigo a lokacin ne kuma na yi alwala na canza kaya ina shirin
yin shafa'i da witiri na kwanta.Na ɗauka tare da yin sallama na gaishe shi cike da
girmamawa sannan ya soma tambaya ta hanya ina basa amsa har muka yi hirar yadda
muka samu tarba mai kyau.

Ya ɗan jan numfashi kafin ya ce “ ina kewarki Naf”


Na yi ƴar dariya kafin na ce “ Uncle tun da ka fasa tafiya me zai hana ka zo nan
ɗin ka yi kwana biyu?”
Ya ce “ kika ce ɗaki ɗaya ne tal inda aka sauke ku”
Na ce “ eh amma ai ba za a rasa wurin da za ka kwanta ba ko da hotel ne”
Yayi ƴar dariya kafin ya ce “ to zan duba na gani,amma Please ki kula min da kanki
sosai banda magana da maza ko da kuwa shugaban makarantar ne ban so”
Na ce “ to Uncle in sha Allah,amma yaushe za ka zo?”
“ Sai zuwa wani satin Naf,yanzu akwai binciken da zan yi”

Kafin na basa amsa sai da na juya na dubi Inna A'i wacce ta zagaya toilet a karo na
uku tun lokacin da na soma waya,ina son tambayarta lafiya amma saukar numfashin
Uncle a kunnena yasa na ƙara mayar da hankali wurinsa.
“ To Uncle zan fara lissafin kwanaki tun yanzu”
“Faɗa min me za ki shirya min na special?” tambayar da yayi min kenan wacce na ji
wani banbarakwai don har wani salo na daban amon muryarsa ke fitarwa.Kamar zai yi
kuka na ji yana cewa “ Please Naf faɗa min mana kar ki ji kunyata ” hakan kuwa ya
ƙara ɗaure jijiyoyina na rasa amsar da zan basa,daga can toilet na soma jiyo saurin
nishin Inna A'i cikin azaba babu wani tunani na kashe kiran Uncle ɗin tare da nufar
toilet ɗin ina tambayar lafiya.Ba ta bani amsa ba sai ƙofar toilet ɗin da ta buɗe
ƙiiii da kanta,daga inda nake tsaye na hangi Inna A'i zaune kan wc tuni ta fita
hayyacinta don da alamu gudawa ce take ta yi.
Tsakaka na gani kan katanga tana saukowa kamar za ta faɗo bisa kanta da mugun sauri
na ɗauki takalme ina kiran sunan Allah na kashe tsakar,ta kuwa faɗo ƙasa bindinta
ya rabu da gangar jikinta da mugun sauri kuma ta bi ta ƙafafuna shuuu ta fice ta
bar guntun bindin wanda sai motsi yake.

Daidai nan Inna A'i ta soma kelaya amai kamar hanjinta za su faɗo,ba tare da
tsantsani ko ƙyanƙyaminta ba na taimaka mata ta yi wanka ,bayan nan na sa abin
kwashe shara na saka bindin tsakakar sannan na wanke toilet ɗin na rufe ƙofa.Ina
zuwa tuni Inna A'i ta yi bacci,ni ma sai na raɓa gefenta na kwanta.
Washegari bugun ƙofar ɗakinmu ne ya tashe mu,yadda ake jijiga ƙofar kamar za a
ɓallata yasa muka kalli juna kafin na miƙe na je na buɗe,da sauri na yi baya ina
kallon shugaban makarantar da mamakin abin da ya zo nema a yanzu ko ƙarfe shidda ba
ta yi ba.Yadda kuma yake yi min wani kallon tsaf yasa na sha jinin jikina......

Ga mai son shiga paid group 500 ne via


2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank

Sai ya turo min da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822


[26/01 13:14] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️

```LoVe aNd HoRrOr story```👽

By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}

*SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta.

*FCWA*☀️
________________________

6-7

Na haɗiye wasu yawu muƙut, Allah na gani ba na cikin mutane masu mugun tsoron nan
don za a iya kirana jaruma kai tsaye amma kallon idon headmaster kaɗai sai da suka
hautsana hanjin cikina.

“ Barka da warhaka shugaba!” na samu bakina dakyar ya furta.


Ya saki wani murmushi wanda kana gani ka san ba na jin daɗi ba ne kafin ya ce “
lafiya! Ina son duba toilet ne don ganin ko gyaran da aka yi yayi” ya faɗa cikin
wani irin amo.
Kamar na ce masa wane gyara kuma amma sai na basa wuri ya shigo,cike da girmamawa
ya gaishe da Inna A'i wacce ke zaune har yanzu a inda na bar ta kafin ya shiga
cikin toilet ɗin na take masa baya kuwa.Dube-dube na ga yana yi kamar mai neman
wani abu amma ban kawo komai ba don na yi tunanin ko gyaran ne a gaske yake
dubawa .

Fuskarsa duk ta nuna alamun ƙin jin daɗi har zai fito sai kuma ya tsaya cak yana
cewa “jinin mene ne can?”
Inda ya nuna na duba sai na ga daidai wurin da na kashe katsakakar jiya ne,amma ai
na wanke toilet ɗin sosai ta ya aka yi jinin bai fita ba.

Yadda ya watso min idonsa masu matuƙar dafi yasa na soma inda-inda,“ dama...dama
jiya ne da Innarmu ta shiga ta ga tsakaka...” da sauri ya katse ni “ kenan ita ce
ta buge mata bindi? ”
Tsuru-tsuru na yi don ina tsoron kar ya kore ni ya ce ba zan koya ba,ya ƙanƙance
ido ya ce “mu nan garin ba a kashe ƙwari ban san daga wane wajen kuka fito ba” sai
kuma ya fita ni ma na take masa baya,ina kallon yadda ya bi Inna A'i da wani mugun
kallo kafin ya fita.

Ɗakin na rufe bayan na gama kallon yadda har a wajen sai da yayi ta dube-dube.
Ko da na juyo sai na ga tuni ta shiga toilet,sai na jira ta fito sannan na shiga ni
ma na yi alwala na fito na yi sallah sannan na zauna na yi Azkhar ɗin safe.

“ Ina kwana Innarmu? Ya ƙarfin jikin naki?” na faɗa bayan na gama komai.
“ Alhamdullah ai na ma warware,ina ga kajin jiya ne suka buga min ciki don na yi
doguwar tafiya” ta bani amsa .
Na ce “ ai kuwa dai ,yanzu ki kwanta ki huta dai zuwa an jima sai ki yi mana girki”
Ta ce “ a'a na fa warke yanzu zan shiga kitchen“ tana gama faɗa ta miƙe kuwa,ni
kuma na ɗauki wayata nan na ci karo da miss call ɗin Uncle Salem ya fi goma duk
yayi su ne bayan na kashe kiransa na jiya.Ɓangaren saƙo na duba sai na ga text
ɗinsa yana bani haƙuri tare da alƙawarin ba zai sake ba.

Kiransa na yi sai dai sam lambar ba ta shiga,duk sai na ji babu daɗi haka na kunna
data na soma yin shat ban ajiye wayar ba sai da na ga ta kusa mutuwa sannan na saka
ta caji.Ina shirin shiga wanka na ji ana shelar ana son ganin dukkanin malaman da
suka zo a ɗakin meeting da ke cikin makaranta da misalin ƙarfe takwas da rabi .

★Uncle Salem

Cikin kaɗaicin son kasancewa da Nafisa ya soma bijiro mata da sabbin abubuwan da za
ta fahimci shi mijinta ne amma da dukkan alamu ya ga sam ita a iya uban kawai ta yi
masa matsuguni.Jin ta kashe masa waya yayi tunanin kunya da kuma fushi ne yasa ta
datse kiran,hakan yasa yayi ta jera mata su da ya ga ta ƙi ɗauka sai ya tura mata
text tare da kashe wayar ya rungume pilow.Zuwa yanzu haƙurinsa da juriyarsa sun yi
ƙasa sosai,yana matuƙar son kasancewa da ita a duk cikin sati ranar juma'a da
asabar kawai a bai yin azumi duk don kare mutumcinsa.Sau ɗaya tak ya taɓa neman
auren wata wacce dama ita ce take haukan sonsa,amma an zo yin auren aka fasa saboda
bai da wani asali.

Idonsa sun kaɗa sun yi jajur saboda abu biyu da suka haɗe masa, feeling da kuma
fushin Naf wanda a duniya in akwai abin da yake guje ma to bayansa yake shi yasa a
kowane lokaci yake yi mata abin da take so.Ko da kuwa iyayenta sun so nuna masa
illar gatan da yake yi mata sai ya ce musu har yanzu Naf yarinya ce.Sai dai a jiya
da Daddy ya ce masa ya ci a ce ta tare da kuma yadda ya ga surarta cikin doguwar
rigar da ta lafe jikinta duk ta fitar da shap ɗinta sai yake ji a ransa eh za ta
iya ɗaukar nauyin buƙatarsa.

Juyi yayi ta yi a daren,da ya ga dai sam baccin ba fa zai zo ba sai ya miƙe ya je


watso ruwa tare da zama kan dadduma yayi ta lazumi bayan raka'o'i biyu da yayi.Sai
daf da asubah ya samu bacci,amma duk da haka ana kiran sallah sai da ya je masjid
da ke nan cikin Company ya dawo ya ƙara komawa bacci.Bai farka ba sai wuraren ƙarfe
goma na safiya,wani wankan ya sake tare da shirya wa cikin wando tree quater na
sojawa da kuma rigarsa t-shirt ita ma ta kakin soja.Bai ɗora hulla ba ya dai saka
farin gilashi kafin ya ɗauki key ɗin motarsa ta aiki da kuma wayarsa.Sai da ya fito
a hanya ne ya kunna ta,bayan ya shiga mota ne ya ga saƙon cewa Nafisa ta so kiransa
amma ba ta same shi ba.Ya ɗan saki murmushi yana jin zuciyarsa ta yi sanyi ko ba
komai yana da tabbacin ta sauko daga fushin da take.Kiranta yayi har sau biyu,a na
uku ne Inna A'i ta ɗauka ta shaida masa ta fita.

★ƘWARGWAM

Ko da na fito daga wanka tuni Inna A'i ta soya min dankali da kuma ƙwai,na yi zaune
na ci na ƙoshi kafin na jawo kayan kwalliyata na shafa mai da turare har da
hoda.Bayan nan na zaɓo doguwar riga ta tambaya ƴar côte d'ivoire,sosai ta amshe ni
sai na zaɓo hijabi da jaka da kalmi duk waɗanda za su hau da ita.

Ina shirin fita ita ma Inna A'i ta fito daga kitchen hannunta riƙe da kwanon miya
na jiya,ta ce “ ashe ba ki ci abincin nan ba dubi yadda duk yayi tsutsotsi ya
lalace”

Na dubi cikin kwanon na ga babu kyawun gani manyan tsutsotsi ne ke ta yawo suna
shige da fice cikin ragowar naman kajin.Da mamaki na ce “ amma kuma abincin har ya
isa lalacewa haka?”

“ Ni ma haka na ce,ko ƙila zafi” Inna A'i ta faɗa .


Na ce “ kawai ki zubar ki wanke kwanukan sai ki mayar musu ,ga key nan in za ki
fita ki rufe ɗakin na tafi sai na dawo”
“Allah ya tsare hanya”

Na ce Amen ina mai yin addu'ar fita daga gida.Kamar yadda ƴan magana ke cewa in ka
yi boko to ƙauyancinka ragage ne hakan yasa duk da ban san ko ina na makarantar ba
haka na dinga karanta duk wani allon sanarwa da na gani har na dace da ɗakin
meeting.
Da isa ta sai na tarar duk kamar ma kowa ya zo ni ake jira,sallama na yi tare da
samun wuri na zauna kusa da wata wacce na ga tana sanye da hijabi saɓanin sauran
matan da ke wurin duk sun ci uban ado an ɗora mayafi.
Babu jimawa kuwa manyan namu suka suka shigo,duk muka miƙe tsaye don nuna girmamawa
kafin mu zauna.

Ɗaya daga cikinsu ne ya soma yin magana ,su biyar ne huɗu maza sai mace ɗaya.
“Yawwa da farko muna yi wa baƙin malaman School Ƙwargwam Barka da zuwa,kamar yadda
kuka sani duk faɗin garin nan wannan ita ce kawai makarantar da ake koya karatun
boko da sauransu...” sai yayi wani murmushi wanda yake ɓoye wata manufa kafin ya ci
gaba da cewa “ Ƙauyen Ƙwargwam na zagaye da ƙauyukan maƙota guda huɗu,shine a
tsakiya sannan dukkan sauran ƙauyukan nan a wannan makaranta tamu mai farin jini
suke zuwa ɗaukar darasi.Kar dai na cika ku da surutu,ina son waɗanda za su koyawa
ƴan sakandari su koma layin nan duk su zauna” ya nuna wani layi,nan duk wasu daga
cikinmu suka ware kansu nan ne na fahimci wato ba iya primary ba ce kenan school
ɗin.

Kamar kuwa ya karanci tunanina sai ya ce “ makarantar ta kashi gida uku ne,da farko
Sakandari sai ya nuna layin malaman kafin ya ce wannan shi ne Principal ɗinku ku da
ɗalibanku,ƴan primary kuma ga naku shugaban headmaster sai ya nuna mutumen nan na
jiya da ya kawo min abinci shi kuwa har da yin wani murmushi.Ina so duk ku basu
girmansu,ni kuma mai yin magana ni vice headmaster,wannan kuma vice principal ya
nuna ɗayan namiji ,daga ƙarshe sai wannan kuma ita ce Grand Maa mai makarantar ce
ofishinta shine dogon nan mai jan penti in kuna da wata matsala ko wani abu da ya
shige muku duhu ita ce za ku je ku yi wa magana” bayan duk ya gama nasa jawaban su
ma ɗaya bayan ɗaya suka yi nasu kafin su faɗa mana fatansu da kuma tsarin
makarantar wanda tun da nake ban taɓa jin irinsu ba amma haka na ja bakina na yi
shuru.

Bayan an gama meeting sai wasu matasa suka shigo suka soma rabon coffe mai shegen
ƙamshi.Ana bani na karɓa ina kallon ruwan coffe ɗin waɗanda a tsakiya aka shatin
zuciya,na dubi na maƙwabciyata na ga ita ma nata haka yake.

Na yi shuru ina tunanin ko sai yaushe zan fara soyayya oho.


“Madam Nafisa ” Muryar headmaster ta katse min tunanin na ɗago muka haɗa ido,ya
sakar min murmushi kafin ya ɗaga kofin hannunsa kamar yadda Turawa ke yi mai nufin
Bismillah.
Na ɗan murmusa kafin na soma kurɓa ina ganin lokacin da ya saki murmushi ,a baki
coffe ɗin har ya fi daɗi kan kyawunsa a ido.

Bayan mun gama sha ne aka rabawa kowa ajin da zai koya ,sai kuma duk muka miƙe
Grand Maa sai ƙara jadadda mana take gobe tun ƙarfe bakwai na safe kowane malami ya
tsaya bakin ƙofar ajinsa.

Muna fitowa na cewa wacce muka zauna kusa da juna,“mene ne sunanki?”


“Adama,ke kuma fa?”
“Ni kuma Nafisa”na bata amsa nan muka so yin masayen lambobi sai dai ni na bar
wayata can gida tana caji a dole ni na bata tawa na ce sai ta ɗago min hannu.

Ina zuwa bakin ƙofar ɗakina sai na tarar da shi a rufe.Sai na zauna kan ƴar
matakalar da aka yi bakin ƙofa na tsaya jiran Inna A'i don babu tantama gidan
headmaster ta je.Ni kaɗai ce a wurin amma haka nake jin ana magana kusa da ni irin
sosai ɗin nan,da na waiga ko ina kuma babu wanda na gani.Shuru na yi ina tunanin ko
dai kunnuwana ne amma abin mamaki sai na ji ana dariya,da sauri na dubi inda sautin
ke fitowa wani ɗan rame na gani irin na gidan tururuwa tabbas a ciki nake jiyo
sautin amma sai aka yi tsit na wani lokaci.
Ni kuwa da son jin ƙwaƙwaf na duƙa tare da kai kunnena ƙasa ina saurara,ƙafafun
mutum na gani tsaye kusa da ni.Da sauri na tashi sai na ga headmaster ne,yayi min
kallon nan nasa kafin ya ce “me kike yi haka a waje?”
Na ƙaƙalo murmushin yaƙe na ce “na zo na tarar Innarmu ba ta nan ne shine na tsaya
jira har ta dawo”
“Kuma kin yarda za ta dawo ɗin?” ya jefo min tambayar wata iri,ni kuma da yake ba
wani damuwa na yi ba na ce masa “ eh za ta dawo ai ita ce za ta zauna da ni har mu
koma”
“Hum!” ya ja wani ƙyaci kafin yasa key ya buɗe min ɗaki,na yi masa godiya tare da
shigewa ciki.

Har zan shiga wanka na soma jin ƙaurin ƙonewar abinci,da sauri na shiga kitchen na
kashe gas ɗin .Bayan na yi wanka na fito na yi mamakin da ban ga Inna A'i ta dawo
ba,wayata na cire a caji na duba sai na ga Uncle ya kira ni sai na mayar masa ya
ɗauka.Muka fara gaisawa kafin na ce “ Uncle ina ne za ka je na ji kamar kana
driving?”
“Wurinki mana ko ba ki so?”
Cike da murna na ce “ wai Uncle da gaske?“
“ Na taɓa yi miki ƙarya? Ke dai kawai ki shirya tarbena don na kusa zuwa sai an na
iso” yana gama faɗa ya kashe,ni kuma cike da zumuɗi na miƙe na soma gyara ɗakin na
shiga kitchen na fara duba abubuwan da duk muka zo da su na haɗa masa lemun zoɓo na
jona ƴar ƙaramar frigine ɗin da ke nan a kitchen na saka.

Haka na zauna na yi ta yin abubuwan da na san yana so kafin isowarsa.Aikin da na


duƙufa shi ya mantar da ni wani cewa Inna A'i ta fita,haka na wuni ni ɗaya sai dab
magrib ne Uncle Salem ya kira ni ga shi ya iso ni na je na tarbo shi can fara isa
makaranta.Gidan gaba na shiga ya tuƙo motar yayi parking nata daidai ɗakina,nasa
sabon key ɗin da headmaster ya bani na buɗe sannan muka shiga .A gajiye yake wannan
yasa ya soma shiga wanka,ko da ya fito tuni an soma kiran sallah da sauri na ɗauke
idona ganin ya fito babu riga daga shi sai farin towel ya ɗaura a ƙugu.
A ɗan daburce na ce “ Uncle ga kayan buɗa bakinka”
Bai ce komai ba sai gefen katifa da ya zauna haka nan ya ƙi saka kayan,da kansa ya
zuba zoɓon don dai ni ba zan juri kallonsa a haka ba na shige toilet na ɗauro
alwala .

Da zan fito sai da na ɗan ziro kai don ganin ko ya saka riga sai dai karaf muka
haɗa ido da shi,yana nan kuma a inda na barsa.Ya sakar min murmushi yayin da ni
kuma na fito cike da kunya,kaina sunkuye na ɗauki dadduma na soma yin sallah ko
kafin na gama ya canza kaya ,a nan ɗaki shi ma yayi sallah gefena kan nasa
daddumar.

Hannuna ya kamo da nake ta yin Azkhar ɗin yamma da ban samu na yi bayan sallar asar
ba.Wani irin sanyi ne nake ji yana ratsa ni ga tuwon tafin hannunsa sai wani matse
min nawa yake .

“ An gama yi wa Uncle ɗin fushi?” ya tambaye ni yana murmushi mai sauti.


Na ce “ ni ban yi fushi ba”
“ Kalle ni” ya faɗa ,a hankali na dube shi ɗin idonmu ya sarƙe cikin na juna ina
son kawar da kai amma tamkar wacce ya yi wa dabaibayi na kasa.A hankali na soma
sauke ajiyar zuciya ,tsawon lokaci muna a haka kafin ya buƙaci in zuba abin da na
dafa mu ci.Jiki duk a sanyaye na zuba muna ci muna aukin kallon juna har muka
gama,ana kiran sallar isha'i na miƙe don gabatarwa amma ya katse ni “je ki yi
ɗahara ki sake alwala”

Ban musa masa ba don ba ya daga cikin halayena yin gardama a gare shi.Da mamakina
kuwa da na shiga toilet alwalata ta karye iya ɗan kusanci da muka samu kawai,amma
sam ban kawo shi wai don wannan niyyar yasa ya ce na je na sake alwala shi yasa ko
da na fito ban wani ji kunyarsa ba na haye dadduma,shi ma sai da ya sake yin wata
alwala kafin ya yi sallah.

Hira muka soma yana tambaya ta meeting ina basa amsa cike da sakewar fuska kafin na
soma jin cikina na yin ciwo,tun ina daurewa har na kasa.
“ Je ki kwanta” cewar Uncle ,ina cije leɓe na haye katifa tare da yin rairan ina
duban sama dafe da cikina.

Jakar da ya zo da ita ya buɗe sannan ya ɗauko wasu kwalabe yayi wani haɗi cikin
kofi ,kafin ya cika bakinsa da ruwan ya zo ya ɗora shi kan nawa.Na buɗe bakina na
dinga haɗiye ruwan maganin a hankali ina lumshe idona har na shanye duka,ina jin
yadda Uncle ya soma tsotsar lips ɗina amma banda wani ƙarfin hana shi dukkan jikina
ya saki kwanyata ma tamkar ta rabu biyu tunanina yana gushewa yana dawo wa kamar
wani network.

Wani irin zazzaɓi ne nake jin yana rufe ni a sunnu,na ware idona a hankali kamar na
jariri sabon haihuwa ina kallon Uncle da ya gama tsotse min baki.So nake na faɗa
masa ina jin sanyi amma babu bakin magana,tashi na ga yayi yasa key ya rufe ƙofar
sai a lokacin ne kuma Inna A'i ta faɗo min a rai.

Jakar kayana ya buɗe ya je ya ɗauko kayan baccina,irin rigar nan mai buɗewa ya saka
min bayan ya zare ta jikina sai rumtse ido nake don ko bra ban saka ba saboda
muddin ba fita zan yi ba takura min take.Shi ma irin rigar ya saka sai dai bai
ƙulle tashi ba,ina ganin ya kashe hasken ɗaki ya kunna wutar ƴar ƙaramar waya sai
ya ɗauko ƙaton blanket ya rufe ni kafin shi ma ya shigo ciki.Hannuna mai sanye da
zobe ya kamo ya riƙe kafin yayi min rumfa da ƙirjinsa mai cike da yalwa gashi ta
kwanta sai santsi take.

Wannan karon yana ɗora bakinsa kan nawa ji na yi kamar ya jona ni ga lantarki,tuni
na ji duk jijiyoyin jikina sun dawo aiki.Na ƙanƙame shi gam ina yin numfashi da
sauri-sauri,yayin da shi kuma ya ci gaba da shan yawuna kafin ya soma shayar da ni
nasa can kuma ya cire bakinsa ya mayar da shi daidai kunnena yana cewa “faɗa min wa
ya baku abinci jiya?”
Dukkan jikina rawa yake saboda sabon yanayin da na tsinki kaina,na tallabo bayansa
da kyau na ƙanƙame shi ina jin lokacin da igiyar rigata ta since ƙirjinmu ya mannu
da na juna sai na ji kamar raina zai fita tsabar shock.Murya na rawa na ce “
headmaster ne!” ina gama basa amsa ya ƙara lalubo bakina wannan karon har da
romance yana yawo da hannunsa a duk sassan jikina.Ni dai duk abin kamar a mafarki
nake jinsa ba zahiri ba saboda tunanina ba zaune yake daram ba,ban san lokacin da
na yi bacci ba bugun ƙofa ne ya tashe ni.Na ware idona a hankali sai na ga Uncle a
tsaye bakin ƙofa yana murza key,yana gama buɗe wa sai Inna A'i a tsaye kamar wacce
aka fiddo daga rame.......

My book is only 500 via

2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank

DM +22795045822

Zuwa page 10 zan gama free page in sha Allah,za ki iya yin payment ɗinki tun yanzu.
[26/01 17:59] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️

```LoVe aNd HoRrOr story```👽


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}

*SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta.

*FCWA*☀️

________________________

08

Da wani irin sauri na gyara rigar baccina wacce na tuna sosai Uncle ne ya saka min
ita .Na miƙe tsaye ina mai ci gaba da kallon Inna A'i wacce ta shigo ƙafafunta
fututu kamar wacce aka fiddo daga kabari.Tana shigowa Uncle ya maida ƙofa ya
rufe,sannan ya je ya zauna kan dadduma hannunsa riƙe da ƙaramar casbi.

“ Innarmu daga ina kike?” na samu kaina da tambaya.


Sai ta dubi Uncle Salem,ni ma sai na dubi bangaren da yake ina mai tambayar kaina
‘shi wannan a nan ɗakin ya kwana ko me?’ a nan take kuma kwanyata ta soma kawo min
gogagen kilishen abubuwan da suka faruwa sai dai ba su fita sosai ba dishi-dishi ne
ban ida tantance taƙamaimai abin da ya faru ba a tsakaninmu.

“ Bari har na yi wanka Nafisa, lokacin sallah ma ya gabato ” Inna A'i ta faɗa tare
da nufar toilet.
Yadda na ji idonsa na yawo a jikina yasa na kai dubana gare shi,sai na ga ashe
cinyoyina ne yake kallo bai ƙyaftawa.Duk sai na ji babu daɗi don dai bai saba yi
min haka ba,na je na ɗauki hijabina na saka na yi tsaye har sai da Inna A'i ta fito
daga wankan sannan na shiga saboda fitsarin da nake ji ya matse ni.

Wani irin tsoro ne ya kama ni ganin ina yin fitsari baƙi ƙirin da shi tamkar wani
Lipton .Wani kuka ne ya ƙwace min tare da tashi ina yarfa hannu,ban san ta ya aka
yi har Uncle ɗin ya ji kukan ba sai gani na yi ya shigo toilet ɗin sam kuma a
wannan matakin da nake cikin tsoro ban ga aibun shigowarsa ba .

Wani irin sihirtacen kallo yayi min a tsakiyar idona da suke tsiyayar da hawaye
kafin ya ce “ ki yi wankan tsarki ki fito, wannan dattin ciwon cikin da kika yi ne
jiya ko kin manta har magani na baki?” yayi maganar yana jan ruwa fitsarin ya
wuce,sai a lokacin na ji kunya tare da gyaɗa masa kai alamun na yarda.

Murmushi ya sakar min kafin ya fita,sai a lokacin na cire rigar baccin da


hijabi.Wankan tsarkin na yi kamar yadda ya umarce ni kuma sai na ga ya kyautatu ɗin
na yi shi.Bayan na fito sai na ga yana bai wa Inna A'i magani da murfin roba,ya fi
kala uku maganin kafin kuma ya miƙe ya fita.

★Uncle Salem

Jiya a lokacin da Inna A'i ta ɗauki wayar Nafisa ,a cikin muryarta kawai ya ji
hucin wani ruhi da ke jikinta.Bai kuma yi wani dogon tunani ba ya fahimci tabbas da
matsala,can gida ya koma ya tattaro duk maganin da ya san zai buƙata kafin ya ɗauki
hanyar garin Ƙwargwam.Abu guda ya sani shine ba zai iya rabo su daga ƙauyen can ba
tun da har Innarsa Delu ta yarda ta bar su suka wuce alhalin kuma ta fitowa Nafisa
a siffar ruhi.
Ko da ya zo kuma bai ga Inna A'i bai yi mamaki ba,ita kanta Naf ɗin ƙwayar idonta
kawai ya kalla ya hango yadda guba ke son game dukkan jikinta.Abu biyu ne yasa ya
bata maganin,na farko don ya ji wane ne ya ciyar da Inna A'i don samo mafita,na
biyu kuma don karye abin da aka baiwa Nafisar a cikin shayi ta sha.
A jiya ba don yana son ceto Inna A'i ba babu abin da zai hana shi ya mayar da
Nafisa cikakkiyar mace,sosai moment ɗin ya ja shi zuwa ƙarshen shauƙi.Ba tare kuma
da ya fita ba daga nan inda yake kwance da taimakon zoben hannunta ya lalabo Inna
A'i a can wani ƙasurgumin daji tana yi ta tafiya ita ɗaya kamar mahaukaciya saboda
tun bayan fitarta zuwa mayar da kwanukan gidan headmaster a nan bakin ƙofar ɗakinsu
ta ji kamar ta zurma cikin rame kafin kuma ta tsinci kanta wani wuri.Dukkan detail
ɗin nan Uncle Salem ya gansa daki-daki,wanda kuma ko ita Inna A'i aka tambaye ta ba
za ta kawo shi ba.

Yadda ta ji muryarsa kamar daga sama shi ya sa ta juyo baya ta fara dawowa gida
kuma,ko lokacin da ta buga ƙofa daga cikin ramen ta fito sai dai Uncle ya toshe duk
wata ƙofa da zai sa A'in ta fahimci wani abu.

Yanzu kuma da ya fito, tsugunawa yayi ya ɗiga wasu ruwa cikin ramen kafin ya rufe
kwalbarsa ya saka a aljihu.
Masjid ɗin makarantar ya nufa wanda ake ta kiran sallah,yana isa ya shiga sawun
gaba bayan yayi nafiloli sai ya zauna har lokacin sallar yayi .Tuni kuma masallacin
ya cika aka tayar bayan an gama ne Uncle Salem ya juyo yana kallon headmaster wanda
ya zauna kafaɗa da kafaɗa da shi.Ya saki wani murmushi kafin ya ci gaba da yin
Azkhar ɗinsa,har sai da ya gama kafin ya basa hannu ya ce “ Assalamu alaikum ”

Headmaster cikin mazgewa ya miƙawa Uncle hannu suka yi musabaha wacce yayi da na
sanin yin ta,don kuwa akwai kumfan magani a hannunsa na karye sihiri.
“Wa'aleykum Salam ! Fatan an sauka lafiya?” ya amsa tare da saurin janye hannunsa.

Uncle Salem ya ce “ lafiya lau alhamdullah ! Na zo duba wurin da matata ne za ta yi


aiki ita da Kakarta sai kuma na ga wuri yayi kyau”

Cike da takaici headmaster ke kallon Uncle ,don kuwa tun zuwansa jiya akan idonsa
na ɓoye ya sauka.Sannan sarai ya san da shi ne ya warware zare da abawar da ya
ƙullawa Inna A'i,amma saboda ya iya munafurci shine zai ce masa wuri yayi kyau.
Cike da iya tako shi ma headmaster ya ce “ ai kuwa dai school Ƙwargwam na kula da
malamanta har ma da ɗalibai”

Uncle wani murmushin ya sake yi kafin ya ce “ ni ne shaida,amma me yasa kuka bata


ɗaki mai lamba uku bayan ita sabuwar zuwa ce?”
“ Ɗakin nada matsala ne?”
“A'a kawai na tambaya ne”
“In ba ta sonsa ai sai a canza mata”
“ A'a na faɗa ma wuri ne mai kyau,kuma lamba ukun ai ita ce daidai da ita surukar
Inna Delu guda” Uncle ya faɗi haka ne ya na saka idonsa cikin na headmaster don yi
masa gargaɗi kan cewa kar ya sake cutar masa mata in kuma ya ƙara yin kuskuren haka
shi da shi shege ka fasa.Da sauri kuma ya miƙe ya barsa nan.


Bayan na gama sallah haka na tsure Inna A'i da tambayoyi sai ta faɗa min inda ta je
amma sai kwana-kwana take yi min daga ƙarshe ma ta shige kitchen tana cewa “bari na
haɗa mana breakfast ”
Na ce “ yau fa Litinin ko kin manta azumi muke ni da Uncle ”

“ A'a yau ba za ki yi ba,ki bari har Alhamis ” Uncle ya faɗa wanda ke shigowa.Na
dube shi da mamaki jin yau shine ke cewa na ajiye azumi,“ Uncle ina yi fa” na faɗa
kamar zan yi kuka ina kallonsa.Ya ɗauke kafin ya ce “a'a akwai maganin da za ki sha
yanzu kafin ki ci komai” sai yayi gaba ya ƙarasa gaban jakarsa ya fiddo wata
kwalbar zuma.

Ido tab hawaye nake dubansa,ya ɗago ya kalle ni kafin ya ce “za ki zo ki sha ko sai
na zo nan na ɗauko ki na matse miki baki tare da ɗura miki shi?”

Jin ya fito a Uncle Salem ɗinsa mai tsanani yasa na ƙarasa gabansa na yi zaune tare
da tanƙwashe ƙafafuna.Da wata ƴar ƙaramar cokali ya soma bani zumar har sai da na
sha bakwai da ita kafin kuma ya soma bani wasu sauran maganin,ɗaya kuma ya ce “
wannan kuma sai in kin ci abinci za ki sha” sai ya miƙo min na karɓa ina gunguni.

Yayi murmushi mai ɗan sauti kafin ya ce “ Naf sai yaushe za ki girma?”
Kamar suɓutar baki na ce “ ranar da ka yi min aure”

Shuru yayi bai ce komai ba,ni ma sai na rashin kunyata.Na ɗaga kai da niyyar satar
kallonsa sai na ga ashe ni ɗin ce yayi ƙuri kamar mai kallon tv.Zan yi ƙasa da kai
yayi saurin tallabo haɓata ya ce “ da gaske kin shirya zaman auren?”
Na lumshe ido ina dariya,ya ce “ faɗa min na ji saboda in na koma gida na yi wa
Daddynki magana a soma shirin biki”

Na ɗan cinno baki gaba na ce “ni da ko saurayi banda” kamar daga sama na ji bakinsa
kan laɓana, wannan karon dai kam cikin hankalina nake.Cike da razani na buɗe ido
kafin da sauri na tashi daga gabansa jikina na ɗan yin rawa,duk da ba yau ne ya
saba yi min kiss ba amma a goshi ne ko a kumatu ya saba min sannan an ɗauki lokaci
mai tsayi rabon da yayi.

“Nafisa?” na ji muryar Inna A'i,da sauri na nufi kitchen ɗin ina jin daɗin kiran
nawa da ta yi.Ina shiga ta yi min wani kallo sai na ji na tsargu na yi tunanin ma
ta gani ,a ɗan daburce na ce “ ni ma ban san me yasa Uncle yayi haka ba,shi ba giya
yake sha ba ballantana na ce bai cikin hayyacinsa ”

“Ungo ni ki je ki sha ya fi wannan surutun da kike yi min marar kan gado,duk


duniyar nan akwai mai sonki sama da shi Salem ɗin da har za ki yi tunanin zai yi
abin da zai cutar da ke” Inna A'i ta faɗa .
Na karɓi kofin kunun tare da komawa can gefe na soma sha sam na ƙi yarda na koma
can,ita ma ba ta matsa min amma ina shanyewa sai na fito don tuni gari yayi haske
sannan lokacin da za mu je bakin aji ƙarfe bakwai ne.

Ina fitowa na gansa a zaune ido rufe yana wani jan numfashi tare da ɗan game fuska
haɗi da yamutsa ta.Toilet na shiga na yi wanka,da na fito sai na tarar ba ya nan.A
gaggauce na shirya tsaf,na zuba takardun da zan yi amfani da su da abin rubutu.
Inna A'i ta fito tana min wani kallo kafin ta ɗauke kai,“ki je yana mota yana
jiranki ku yi sallama”

Jiki a sanyaye na fita ganin irin yadda ita Innarmu ta canza min fuska wacce nake
ɗauka uwa ta biyu.Hijabi na saka kafin na fita,gidan gaba na buɗe na zaune na sunne
kai tare da yin shuru ina wasa da zoben hannuna.Kujerar da nake zaune a kai ya ɗan
buɗe ta ja baya,da sauri na kalle shi yadda na ga idonsa sun kaɗa sun yi ja yayi
bala'in bani tsoro.Murya na ɗan rawa don duk a tunanina kuka ne yayi,na ce
“Uncl...” sauran maganar ce ta maƙale jin bakinsa kan nawa abin ma bai tsaya nan ba
ya soma shafar hijabina ta sama .Hawaye ne suka soma zubo min ,ba yau ne farkon jin
cewa uba yayi mu'amala da ƴarsa ba na sha jin ire-iren labarun nan a kafar BBC amma
ban taɓa tunanin akwai ranar da abin zai zo kaina ba don ban taɓa banbance Daddy da
Uncle ba.Duk abin da yake yi ko motsi ban yi ba da yatsana ballantana na yi
yunƙurin hana shi ,hawaye kawai nake yi don babu bakin kuka saboda Uncle ya mayar
da shi sweet ɗinsa.Sama da minti goma kafin ya janye daga gare ni amma ina jin
hucin saukar numfashinsa kusan fuskata da na rumtse idona.Shashekar kukansa da na
ji ta yi kuma bala'in tayar min da hankali fiye da abin da ya gama yi min,na buɗe
idona ina kallonsa shi ma hawayen yake fitarwa kafin ya kama hannuna dukkan biyun
ya ce “ don me Naf? Me yasa kike horar da ni da yawa? Me yasa ba ki ganin zazzafar
ƙaunar da nake yi miki? I love Naf! Ina sonki,ina buƙatar ki a kusa da ni haƙurina
ya ƙare”

Tamkar wacce aka bugawa guduma a kai haka na ji ,kalamansa kuwa kusan tarwatsa min
kwanya suka yi sam kasa fahimtar abin da yake nusar da ni na yi.“Wuce ki tafi ki
kula min da kanki”ko ida rufe bakinsa bai yi ba na ɓalle murfin motar na fito.....

My book is only 500 via

2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank

DM +22795045822
[28/01 15:33] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️

```LoVe aNd HoRrOr story```👽

By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}

*SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta.

*FCWA*☀️

________________________

09

Ƙafafuwana har harɗewa suke saboda kalaman da Uncle Salem ya fesar min,ruhina kuwa
yayi wani irin sanyi saboda zazzafan romance ɗin da yayi min wanda ya toni duk wani
sirrin zuciyarsa da muradinta na shekara da shekaru.Ta ya zan so Uncle soyayya ta
aure? Ta ina ma zan fara wannan cakwakiyar da sam ƙanƙanuwar kwanyata ba za ta iya
ɗaukar wannan rikicin ba.Ina shiga ɗaki na tarar da Inna A'i tana jera min takardun
da ni ce na fidda su a jaka,ta ɗago ta dube ni kafin kuma ta kawar da kai.So nake
na shaida mata kalamai da kuma abin da Uncle yayi min ko zan samu sukuni amma sam
ba ta bani fuska ba.Wannan yasa kai tsaye na shige toilet,ga mamakina duk jikina ya
ɓace saboda abubuwan da yayi min har sai da na canza pant na kuma wanke fuskata.Ina
tsaka da maida kwalliyar fuskata na ji ƙarar tashin motarsa,na ja ajiyar zuciya
tare da motsa laɓana kaɗan na ce “Allah ya sauke ka lafiya!” sai na ɗauki wani
sabon hijabi saboda wancan duk Uncle ya cukuikuye shi sannan hawayena sun jiƙa shi
ta gaba.
“Na tafi sai na dawo”na faɗa dakyar,ta ce “a dawo lafiya” jakata na ɗauka tare da
fita daga cikin gidan na nufi can ɓangaren makarantar.
Ina zuwa gaban ajin da zan koya na tarar tuni ɗaiɗaikun ɗalibai sun zo,haka suka
gaishe ni irin yadda ake yi.Wani sanyi ya ratsa ni duk sai na ji ƙuncin ya sauka
daga zuciyata har da murmushi,ina nan tsaye kamar sauran malamai bakin aji aka soma
kawo yaran sai a lokacin na dinga cewa su shiga aji su zauna.Ina nan tsaye wani ya
kawo ƴarsa sai kuka take,da sauri na kama hannunta ina mai rage tsayi na ce “yi
shuru mana babyna ko ba ki so na baki alawa?”
Cikin murya ƙurciya ta ce “ina so”
Na ce “yawwa to yi shuru sai na baki ,me sunanki?”
“Firdausi”ta bani amsa,na gyara mata zaman ɗan guntun hijabinta kafin in saɓe ta
kamar wata ƴata na ce “to yi wa Daddy bye bye sai mu je aji na nuna miki inda za ki
zauna” da murmushinta kuwa ta yi masa alama da hannu,ya ce “na gode Madam ”
Na ce “bai komai ai aikinmu ne” sai kuma na shiga aji na zaunar da ita a kujerar
gaba ta kusa da kujerar da aka ware domin zamana.

Bayan nan na ƙara komawa can bakin ƙofa,ban shigo ba har sai da ajin ya cika zuwa
lokacin tuni ƙarfe takwas ta buga.Ina shiga na yi zaune ina kallonsu ɗaya bayan
ɗaya ina jin wani sanyi na ratsa min zuciya,kafin kuma na tashi na bi ɗaya bayan
ɗaya ina tambayar kowa sunansa.Dukkansu yara ne da ba za su wuce shekara bakwai
ba,wasu ma ba su kai ba,ina cikin zagayen ajin sai ga headmaster ya shigo shi da
mataimakinsa.

Takarda mai sunan ɗalibai ya miƙo min da kuma alli wanda zan yi rubutu da
allo,liste ɗin na ɗauke da ɗalibi ɗari cicif.Bayan fitarsu ma sai da na sake kiran
sunayen yaran kafin na je na soma yin rubuta a jikin baƙin allon wanda yake goge
fesss,kwanan wata na rubutu da kuma ABCD sai na soma koya musu suna yi duk bayan na
faɗa.Haka muka ta yi har lokacin shan iska yayi,sai dai kamar yadda meeting ɗin
jiya ya sanar da mu dokokin makarantar hakan yasa ban fidda su waje ba.

Grand Maa ce ta shigo ita da wata budurwa ɗauke da wani basket,cike da girmamawa na
gaishe ta yayin da kuma budurwar nan ta soma raba wa yara abincin da za su ci.Bayan
ta gama a gaban idona Grand Maa ta miƙawa wani yaro biscuit kafin su fice.
Bayan an gama cin abinci duk suka je suka jefar da abin take away ɗin a shara nan
na ci gaba da yin cours ina aika kowane ɗalibi ya zo ya rubuta harafi ɗaya daga
cikin ABCD ɗin da na yi musu.Ƙarfe sha biyu na rana cif aka kaɗa ƙarar rawar
tashi ,nan aka zo fara ɗaukar yara ba ni na baro ajin ba sai da kowa ya watse .

A gajiye na shiga gidan,Inna A'i ta yi min Barka da zuwa na amsa ina mai rage kaya
na shiga toilet.Bayan na yi wanka ta gabatar min da abinci,na saka plate ɗin gaba
tare da ɗaukar waya na kira Ammy bayan mun gaisa cike da alfahari nake bata labarin
yadda ranar farko ta kasance ,sai murmushi take kafin mu yi sallama ina gama cin
abinci na ɓingire bacci wanda tamkar jirana ake aka ƙara yi min maimaicin duk abin
da suka faru a yau ɗin tun daga lokacin da na je na yi tsaye gaban ajina har zuwa
lokacin shan iska na yara.Yaron nan da Grand Maa ta baiwa biscuit na ga yana ta
kuka yana kallona yana kiran “madam? Madam cikina ciwo! Madam mutuwa zan yi ,wayyo
cikina” amma sam wai na kasa tashi daga kujerar da nake zaune,a gaban idona jini ya
soma yi masa zuba ta ƙofofin hanci kafin kuma ya faɗi babu rai bayan yayi wata irin
ƙara wacce daga nan na tashi daga baccin.

Na yi miƙa tare da duba agogo sai na ga tuni lokacin sallah yayi,kawai na miƙe na
je na ɗauro alwala na gabatar da sallar.Sam ban wani bai wa mafarkin da na yi
muhimmanci ba sai ma takarda da na ɗauka na soma rubuta abubuwan da zan koyar da su
gobe,bayan nan kuma sai muka hau yin hira da Inna A'i lokaci lokaci kuma ina
chating abina.
Ana kiran sallar magrib na tura wa Uncle saƙo kamar haka “barka da shan ruwa!”
Sai ya maido min da amsa da “ azumin da kika yi sanadin karewarsa?”
“Kamar ya?”
“Eh mana Naf ɗanɗanon yawunki ma kaɗai ya isa ya karya min azumi,uwa uba kuma
tattausan ƙirjinki” da ya turo min saƙon nan na karanta shi ya fi sau goma,ina ta
juya kalaman cikin tunanina ina jin tabbas Uncle nada buƙatar ganin likita don kuwa
na sha jin ana cewa in mutum ya daɗe bai yi aure ba to hankalinsa na yin rauni .Da
wannan na yi masa uzuri na ce kawai bai da lafiya ne kuma na yi alƙawarin zan sanar
da Daddy a sama masa magani.

★Uncle Salem

Ikon Allah ne kawai ya kai shi gida lafiya,duk yadda azumin nasa ya zama gurgu
hakan bai sa shi ya ajiye shi ba.Wanka kawai yayi ya ci gaba da yin abinsa har aka
kira magrib ya ajiye shi,ya dawo daga sallah kenan ya tarar da saƙon Nafisa .Cikin
son nuna mata fa eh haƙurin nasa ya ƙare yasa duk ya cire nauyi ya soma yi mata
magana cikin wannan salon.Yayi jiran amsarta amma shuru,kawai sai ya kira Daddy ya
sanar da shi ya kamata a fara shirin yin bikinsu da Nafisa amma sai Daddy ya ce ya
je can gida su yi maganar ido da ido tun da tuni ya sanar da shi bai samu damar
zuwa dajin ba.

Sai bayan sallar isha'i ya tafi can,a babban falo suka zauna Ammy ta kawo musu
gasashen naman kaza da kuma shayi.Suna ci suna tuna baya, Uncle ne ya soma da cewa
“ Abdul Hameed ka tuna lokacin da muna yara kai ne ke son gashen nama irin haka? ”
Daddy yayi murmushi ya ce “a lokacin ai tantabaru ne muke gasawa,sannan muna samari
ne ba yara ba”
Uncle Salem yayi murmushi ya ce “ai kuwa dai ”
“Kamar sati nawa kake ganin ya kamata a sa ranar bikin?”

“Zuwa wata uku haka, lokacin an yi musu hutun makaranta a ranar da ta dawo sai a
saka ta lalle” Uncle ya faɗa yana hasko tuni ga lokacin nan ya zo.

“To babu damuwa ,amma ka samu ka sanar da Nafisar komai?” Daddy ya tambaya.
“A'a tukuna dai amma ...” sai kuma ya ji nauyin abin zai ce kawai sai yayi
shuru,shi ma Daddyn bai damu ba sai ma kiran Ammy da yayi ya sanar mata ,sosai ta
nuna farin cikinta kafin ta fita.Bayan sun gama tattaunawa Uncle ya fito ya nufi
flat ɗinsa,an gyara komai an share an goge.Wanka yayi ya shirya cikin bacci sannan
ya soma yin wuridin da ya saba a kullum kafin kuma ya ɗauki wayarsa ya soma kallon
hotunan Nafisa wanda a iya kallonsu kawai hankalinsa sai tashi yake yana jin
buƙatar kasancewa da ita.

★ ƘWARGWAM

Yau ma ban ci abinci da dare ba kawai cake na ci da chocolat,sai na saka wasu a


jakata wanda zan baiwa Firdausi kamar yadda na yi alƙawari.Ina yin kwance na ce
“Innarmu don Allah ki yi min gatana irin ta dogon ƙarni mai abin tsoro”

“A'a Allah ya tsare ni Nafisa ,kin ga bacci ma zan yi don gobe ina son yi mana
dambu tun da safe” ta faɗa tare da yin kwanciyarta gefe da ni.Na turo baki tare da
lumshe ido,hoton abubuwan da Uncle yayi min duk suka dawo min.Sai wani abu nake ji
yana bijiro min na shauƙi amma ban ma san taƙamaimai mene nake buƙata ba,amma sosai
nake jin daɗin tunanin don abin da nake ji yana bani shauƙi sosai.Sai laɓana nake
motsawa kamar wacce ke son Uncle ɗin ya ƙara shan su,a haka bacci ya ɗauke ni mai
haɗe da mafarkinsa muna having sex.Yadda duk jikina ya amsa kamar a gaske yasa na
buɗe idona dakyar da suka yi min nauyi,na duba lokaci a wayata sai na ga ƙarfe uku
da minti uku na yunƙura na tashi zaune daidai nan hasken ɗakinmu ya ɗauke don dama
ban iya bacci cikin duhu.Fitilar wayata na kunna sai dai tamkar wata wutar kyandir
haka ta soma yin rawa kafin kuma ta ɗauke ɗif.Ban wani damu ba na sake ɗaukar wayar
don sake kunnawa wannan karon cak screen ɗin ya ɗauka kafin kuma ta mutu da kanta.

Daga bakin ƙofa na hango wata mace mai fararen kaya a tsaye gashin kanta na tashi
cikin iska.
“Wace ce?” na tambaya.
“Deborat” ta bani amsa kai tsaye,kafin kuma ƙyaftawar ido tsundum na ganta kusa da
ni a zaune muna kallon juna.

Ido sune ƙofar hango ruhi, wannan yasa nake kallon ruhinta tun daga wajensa har
cikinsa.“Ke ce kike yi min gatana kullum” na furta bayan na gama lalubo dukkan
asalinta.Ba ta bani amsa ba sai jawo ni da ta yi ta kwantar ni kan cinyarta ta soma
shafar sumar kaina,na lumshe ido don kuwa shafar irin dai ta matar da nake ji ce
tana yi min haka duk dare.Sai dai wannan karon shafar ta babanta don tsintar kaina
na yi a wani wurin, dube-dube na soma yi har na ci karo da allon sanarwa inda aka
rubuta “DARASIN SANIN RUHANIYA” ina shiga ciki abun mamaki duk sai na tarar da kaf
malaman nan da muka yi meeting da su,ga kuma su headmaster da principal su ma duk
suna zaune yayin da Grand Maa ke koyar da karatu.Kamar wancan lokacin haka na zauna
kusan Adama,na mayar da dukkan hankalina ga Grand Maa inda take cewa “kamar yadda
vice headmaster ya faɗa muku lokacin meeting wannan school Ƙwargwam ta kasu kashi
uku primary,da Sakandari sai kuma kuma Ajin Ƙwargwam wanda iya malamai ne kawai
muke koyarwa” tana rufe bakinta na jefa mata tambaya,“Grand Maa me Ƙwargwam ke
nufi?”

“Matsafa!” ta bani amsa kai tsaye,sai na yi shuru ina tunanin zuci na ce ‘Ƙwargwam
school na nufin MAKARANTAR MATSAFA? to amma su wane ne matsafan?’

Tamkar Grand Maa ta shiga zuciyata kuwa sai ta bada amsa ta hanyar cewa “darasinmu
na farko shine chapter ruhi da gangar jiki,ta wannan hanyar ce ake gane matsafi”
tana gama faɗar haka sai ta yi wani abu da hannunta nan take sai ga wani table ya
bayyana a gabanmu,sannan a samansa wani yaro ne kwance babu kaya jikinsa da na dubi
yaron sai na ga ba kowa ne ba face ɗalibina wanda ta baiwa biscuit a ɗazu .....

My book is only 500 vi

2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank

DM +22795045822
[29/01 03:16] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️

```LoVe aNd HoRrOr story```👽

By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}

*SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta.

*FCWA*☀️

________________________
Last free page 10

Ganin Grand Maa ta ɗauki wuƙa za ta tsaga cikin yaron na yi saurin rumtse idona,ina
sautin kururuwarsa yadda yake kuka yana cewa “madam ki cece ni kar ki bari su cutar
da ni ” na buɗe idona da suka yi jawurrr na sake zuba su kan Grand Maa wacce ke
zuba jinin yaron nan a kofi ta hanyar saka ludayi tana wani kwaso shi.
Bayan ta gama sai ta kai kofin bakinta ta sha sannan ta miƙawa principal shi kuma
da ya sha ya bai wa headmaster daga nan sai vice principal da kuma vice
headmaster.Grand Maa ta ƙara karɓar kofin ta ce “lamba ɗaya sha ka bai wa lamba
biyu,haka za ku dinga yi har kowa ya sha” wanda aka kira da lamba ɗaya na duba,
kyakkyawan saurayi ne irin sosai ɗin nan kuma sai na ga yana kama da headmaster da
dukkan alamu ɗansa ne,bayan ya sha sai ya miƙawa lamba na biyu shi kuma ya miƙo min
na karɓi kofin ina kallon yadda jinin ɗalibina yake kwance a ciki mugayen matsafan
nan sun mayar da shi lemun sha .Na kai kofin kusan bakina na yi kamar na sha kafin
na miƙawa Adama wacce ita kuma ita ce lamba huɗu,so nake na ce mata kar ta sha amma
idon Grand Maa ƙurrr suke kanmu ina ji ina gani Adama ta sha jinin kafin ta ba na
kusa da ita a haka har kowa ya sha aka mayar da kofin.

Daga nan sai Grand Maa ta yi wani siddabarun sai ga yaron da aka feɗe cikinsa ya
tashi zaune daram da buɗaɗen ciki idonsa na shatatar da hawayen jini yana kallon
tsakiyar ido har yanzu kuma bai gushe da neman taimakona ba sai dai sam ban san ya
za a yi na taimake shi ɗin ba.

Wasu kwalabe ta jera saman table ɗin,ta yi wani alama da hannu a nan take duk suka
buɗe kansu.Bakinta na furta ɗalasiman tsafi ta dinga umartar ruwan da ke cikin
kowacce kwalba da su je su shiga buɗaɗen cikin yaron,nan ya soma yin wata irin
zabura kamar an jona shi da lantarki abin da na kasa jura kenan na ce “ōvovār̃ī”
hakan yana nufin komai ya tsaya wato wait/stop cak duk komai ya tsaya kuwa yayin da
dukkansu suka soma amayo jinin da suka sha suna wani waro ido kamar za su mutu.Sam
ban wani damu ba sai ma zuwa da na yi na ɗauki ɗalibina ,kamar yadda uwa ke gudun
matsala ta samu da ɗanta ko kuma in ta ga wani abu zai cutar da shi take ɗauke shi
tare da ɓoye shi haka na yi wa ɗalibina na ƙanƙame shi gam a ƙirjina ina kallon
Grand Maa wacce ke yin ƙarfin hali tana cewa “lamba uku ki ajiye shi kar lokacin
kaddamar wa ya wuce duk ki ɓata mana shiri ki maido mu baya”

Na girgiza mata kai na ce “ba zan bayar da ɗalibina ba”

“Lamba ɗaya je ka ƙwato min abin farauta” Grand Maa ta basa umarni ai kuwa sai ya
miƙe tsaye ya tunkaro ni,muna kallon juna cikin ido sai na ga tamkar na san shi
yana dab da kawowa wurina kuma sai na tuna a inda na san idon,wato tsakakar ranar
nan ce da bugewa bindi.Na dubi ƙafarsa sai na ga yana yin ɗingishi,“kār̃bās!” na
furta nan take kuma ya ɓangwale ya faɗi yana ihu,nan kuwa na ga hankalin headmaster
ya tashi ya nufo shi duk da kuwa ƙoƙarin tsayar da shi da Grand Maa ta yi don ba a
so kowa ya gusa daga wurinsa sai da umarni.

Ta yo kaina za ta ƙwace shi da ƙarfi ni kuma da mugun sauri na bi ta rufin ɗakin na


tashi sama cikin iska muka bar wurin.Ban san inda na ɓoye yaron ba amma tabbas na
kuɓutar da shi kuma na basa tsaro,daidai nan kuma na tashi daga baccin saboda kiran
sallar asubah da aka yi.

Dukkan cinyoyina na ji suna yi min ciwo kamar wacce ta yi wasar tsere,dukkan


abubuwan da suka faru da ni kuma sai na manta da su .Wanka na yi tare da alwala na
zo na yi sallah,bayan na gama na soma yin Azkhar ina lumshe ido alamun bacci ne
yake son ƙara yin gaba da ni amma kiran Uncle Salem ya shigo wayata na je na ɗauka
tare da yin kwance na kara wayar a kunne.
Yau shine ma ya gaishe ni da farko,na amsa cikin mayen bacci ina jin yana cewa “
mafarkin me kika yi Naf ?”
Baccin da nake ji ne ya sake ni a nan take tuna na yi mafarkinsa mun haɗa shimfiɗa
da shi muna mu'amalar aure ,amma me yasa yake yi min tambayar nan shine abin dubawa
.Cike da gyatse na ce “kai wane iri ka yi?”
Sai da ya saki murmushi kafin ya ce “mafarki na yi ga shi nan an kawo min ke
gidana,muna kwance kan bed duk babu sutura a jikinmu ina yi miki zazzafan romance
ke ma kina maido min da kuma na fara kusantarki sai kika fara yi min kuka kina
kiran sunana Uncle Sal zafi ka bari ban so.Amma sai na soma rarrashinki har kika yi
shuru kika bar kuka,Naf na ji daɗin mafarkin nan sosai kin ga yanzu ma da zan yi
sallah sai da na yi wanka”

Tun da ya soma magana na rumtse ido,wato shi ko kunya bai ji yayi mafarkin suna sex
da ƴarsa sannan har wani labari yake bani.Ina ƙoƙarin kashe kiran ya tsayar da ni,“
Please Naf kar ki kashe min kira faɗa min yau ma kin yi mafarkin tsoro?”

Jin ya canza akalar zancen yasa na yi shuru,sosai na tuna na yi mafarkin ban tsoro
amma na kasa tuna abubuwan da suka faru
[30/01 07:40] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️

```LoVe aNd HoRrOr story```👽

By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}

*SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta.

*FCWA*☀️

________________________

Last free page 10

Ganin Grand Maa ta ɗauki wuƙa za ta tsaga cikin yaron na yi saurin rumtse idona,ina
jin sautin kururuwarsa yadda yake kuka yana cewa “madam ki cece ni kar ki bari su
cutar da ni ” na buɗe idona da suka yi jawurrr na sake zuba su kan Grand Maa wacce
ke zuba jinin yaron nan a kofi ta hanyar saka ludayi tana wani kwaso shi.
Bayan ta gama sai ta kai kofin bakinta ta sha sannan ta miƙawa principal shi kuma
da ya sha ya bai wa headmaster daga nan sai vice principal da kuma vice
headmaster.Grand Maa ta ƙara karɓar kofin ta ce “lamba ɗaya sha ka bai wa lamba
biyu,haka za ku dinga yi har kowa ya sha” wanda aka kira da lamba ɗaya na duba,
kyakkyawan saurayi ne irin sosai ɗin nan kuma sai na ga yana kama da headmaster da
dukkan alamu ɗansa ne,bayan ya sha sai ya miƙawa lamba na biyu shi kuma ya miƙo min
na karɓi kofin ina kallon yadda jinin ɗalibina yake kwance a ciki mugayen matsafan
nan sun mayar da shi lemun sha .Na kai kofin kusan bakina na yi kamar na sha kafin
na miƙawa Adama wacce ita kuma ita ce lamba huɗu,so nake na ce mata kar ta sha amma
idon Grand Maa ƙurrr suke kanmu ina ji ina gani Adama ta sha jinin kafin ta ba na
kusa da ita a haka har kowa ya sha aka mayar da kofin.

Daga nan sai Grand Maa ta yi wani siddabarun sai ga yaron da aka feɗe cikinsa ya
tashi zaune daram da buɗaɗen ciki idonsa na shatatar da hawayen jini yana kallon
tsakiyar idona har yanzu kuma bai gushe da neman taimakona ba sai dai sam ban san
ya za a yi na taimake shi ɗin ba.

Wasu kwalabe ta jera saman table ɗin,ta yi wani alama da hannu a nan take duk suka
buɗe kansu.Bakinta na furta ɗalasiman tsafi ta dinga umartar ruwan da ke cikin
kowacce kwalba da su je su shiga buɗaɗen cikin yaron,nan ya soma yin wata irin
zabura kamar an jona shi da lantarki abin da na kasa jura kenan na ce “ōvovār̃ī”
hakan yana nufin komai ya tsaya wato stop cak duk komai ya tsaya kuwa yayin da
dukkansu suka soma amayo jinin da suka sha suna wani waro ido kamar za su mutu.Sam
ban wani damu ba sai ma zuwa da na yi na ɗauki ɗalibina ,kamar yadda uwa ke gudun
matsala ta samu ga ɗanta ko kuma in ta ga wani abu zai cutar da shi take ɗauke shi
tare da ɓoye shi haka na yi wa ɗalibina na ƙanƙame shi gam a ƙirjina ina kallon
Grand Maa wacce ke yin ƙarfin hali tana cewa “lamba uku ki ajiye shi kar lokacin
kaddamarwa ya wuce duk ki ɓata mana shiri ki maido mu baya”

Na girgiza mata kai na ce “ba zan bayar da ɗalibina ba”

“Lamba ɗaya je ka ƙwato min abin farauta” Grand Maa ta basa umarni ai kuwa sai ya
miƙe tsaye ya tunkaro ni,muna kallon juna cikin ido sai na ga tamkar na san shi
yana dab da kawowa wurina kuma sai na tuna a inda na san idon,wato tsakakar ranar
nan ce da na bugewa bindi.Na dubi ƙafarsa sai na ga yana yin ɗingishi,“kār̃bās!” na
furta nan take kuma ya ɓangwale ya faɗi yana ihu,nan kuwa na ga hankalin headmaster
ya tashi ya nufo shi duk da kuwa ƙoƙarin tsayar da shi da Grand Maa ta yi don ba a
so kowa ya gusa daga wurinsa sai da umarni.

Ta yo kaina za ta ƙwace shi da ƙarfi ni kuma da mugun sauri na bi ta rufin ɗakin na


tashi sama cikin iska muka bar wurin.Ban san inda na ɓoye yaron ba amma tabbas na
kuɓutar da shi kuma na basa tsaro,daidai nan kuma na tashi daga baccin saboda kiran
sallar asubah da aka yi.

Dukkan cinyoyina na ji suna yi min ciwo kamar wacce ta yi wasar tsere,dukkan


abubuwan da suka faru da ni kuma sai na manta da su .Wanka na yi tare da alwala na
zo na yi sallah,bayan na gama na soma yin Azkhar ina lumshe ido alamun bacci ne
yake son ƙara yin gaba da ni amma kiran Uncle Salem ya shigo wayata na je na ɗauka
tare da yin kwance na kara wayar a kunne.
Yau shine ma ya gaishe ni da farko,na amsa cikin mayen bacci ina jin yana cewa “
mafarkin me kika yi Naf ?”
Baccin da nake ji ne ya sake ni a nan take tuna na yi mafarkinsa mun haɗa shimfiɗa
da shi muna mu'amalar aure ,amma me yasa yake yi min tambayar nan shine abin dubawa
.Cike da gyatse na ce “kai wane iri ka yi?”
Sai da ya saki murmushi kafin ya ce “mafarki na yi ga shi nan an kawo min ke
gidana,muna kwance kan bed duk babu sutura a jikinmu ina yi miki zazzafan romance
ke ma kina maido min da kuma na fara kusantarki sai kika fara yi min kuka kina
kiran sunana Uncle Sal zafi ka bari ban so.Amma sai na soma rarrashinki har kika yi
shuru kika bar kuka,Naf na ji daɗin mafarkin nan sosai kin ga yanzu ma da zan yi
sallah sai da na yi wanka”

Tun da ya soma magana na rumtse ido,wato shi ko kunya bai ji yayi mafarkin suna sex
da ƴarsa sannan har wani labari yake bani.Ina ƙoƙarin kashe kiran ya tsayar da ni,“
Please Naf kar ki kashe min kira faɗa min yau ma kin yi mafarkin tsoro?”

Jin ya canza akalar zancen yasa na yi shuru,sosai na tuna na yi mafarkin ban tsoro
amma na kasa tuna abubuwan da suka faru.
“Faɗa min me kika gani?” ya sake faɗa .
Na ce “ni na manta komai”
“Kin sha maganinki kuwa kafin ki kwanta?” ya jefo min tambaya,ni sam na ma manta da
ya bani magani.Na ce “eh a'a...”
“Baby ina ga ke ma kina son na zo kusa da ke shi yasa kike wasa da shan magani,amma
babu damuwa duk weekend zan dinga zuwar miki” da sauri na ce “a'a ban so ka yi
zamanka ”
“Saboda me? Naf me yasa kike son hana cikar burinmu ne ? Haƙurina ya ƙare fa ina
buƙatar kulawa kin san abin da nake ji duk dare? Da zazzafan feeling ɗinki nake
bacci ina tuna surar jikinki na matsu na ji komai na jikinki a hannuna yana sarrafa
shi ...” kuka na saka masa ina roƙonsa don Allah ya bari ban son irin wannan zancen
daga ƙarshe na ƙara da cewa “uncle ka je asibiti don Allah likita ya duba ka”
“Ke ce likitata domin ke kaɗai kike da maganin ciwona,kin ga yanzu ma duk kin tayar
min da hankali ji nake...” ban bari ya ida ba na kashe kiran ina mai ci gaba da yin
kuka.

Inna A'i wacce ta fito daga toilet ta ce “in kin gama kukan sai ki tashi ki yi
sallah”
Na ɗaga kai na dube ta ina mamakin yadda aka yi ta canza min,na turo baki gaba na
ce “Innarmu kin bar sona ” na faɗa ,ba ta kula ni ba ta haye dadduma.Ni ma tashi na
yi na shiga toilet na yi wanka sannan na ɗauro alwala na zo na gabatar da
sallah,ina Azkhar ina tuna mafarkin da na yi da Uncle Salem nan take kuma na soma
jin jikina na saki har wani sanyi-sanyi nake ji yana rufe ni.Na je na ƙara haye
katifa tare da jan bargo na rufa ina lumshe ido,karon farko da na ji ina muradin
yin saurayi mu yi soyayya sannan aure ya biyo baya sai yayi min duk abin da Uncle
ɗina yayi min cikin bacci.Da wannan tunanin bacci ya sake yin awon gaba da ni sai
kuma na ci gaba da mafarkina daga inda na tsaya wato cikin wani daji na tsinci
kaina.A gabana kuma wani ɗaki ne na kara,a bakin ƙofa wata tsohuwa ce zaune tana
hura wuta amma ban ganin fuskarta.

Na matsa kusa da ita na ce “Kaka jiya na yi ajiya a wannan ɗakin cikin dare” ko
kafin ta ɗago idona ya sauka kan ƙusumbinta.

Ta ɗago tana kallona,ganin mun san juna sai na sakar mata murmushi na ce “Kaka dama
ke ce? Nan ne gidanki?” na faɗa ina nuna ɗakin.
Ta jinjina kai kafin ta ce “ki shiga ciki yana nan yana bacci amma kar ki tashe ”

Na shiga ɗakin sai na tarar da ɗalibina kwance bisan kunnuwan ganye yana
bacci,fuskarsa kawai ake gani saboda yadda aka yi masa rufa da wata fatar dabba.

“Ya samu rauni sosai Allah yayi sa'a ma kin kawo shi nan kan lokaci da saura ƙiris
ya rasa ransa” Kaka ta faɗa wacce ta shigo hannunta riƙe da ƙwayar sai tururi ke
tashi.

Zama ta yi kusa da shi kafin ta yaye fatar,da sauri na kawar da kai ganin yadda
ciwon nasa yake buɗe har yanzu.
“Ki matso ki soma ɗinke masa cikin ” ta faɗa .
Na juyo da sauri na ce “ni kuma?“
“Eh kin zata wa zai yi miki aikin?” ta faɗa tare da miƙo min wani mashi mai kamar
wuƙa da kuma baƙin zare.
Jikina ne ya soma rawa haka na zauna ina kallon yadda ta ƙara wanke cikin nasa tare
kuma da zuba wani magani,hannu na kyarma na soma ɗinki yayin da ita kuma take faɗar
wasu surkullen da ita kaɗai ta san ma'anarsu a haka har na ida.

Na yi baya ina mayar da numfashi,ta tashi ta je can gaban wani babban teburi ta
ɗauko min zuma ta bani na karɓa ina washe baki saboda ina son zuma kullum sai Uncle
Salem ya bani ita tun ina ƴar yarinya.
Zumar na soma sha muna kallon juna ni da Kaka kafin ta ce “ban san dalilin Deborat
ba da ta zaɓi ta ɓoye miki baiwarki,amma na so a ce kin zama tamkar Kakarki Ayodele
ciwon idon Mayu...” sai kuma ta yi shuru yayin da ni kuma na tsaya da shan zumar na
ce “wai Granny Mamar Daddyna?”

Ta jinjina min kai kafin ta ce “eh sosai ita fa! Kin san ita ma ba ta da tsoro
kamar ke take,sai dai ita dukkan aikin da alloli da magabata suka saka ta yi tana
sane da komai ba kamar ke ba da yake zuwar miki siffar mafarki”

“Yanzu mafarki ne nake yi kenan?”


“Kusan haka ne! Sai dai wannan muna kiransa da balaguron ruhi,wasu suna yinsa cikin
bacci yayin da wasu kuma ke yinsa ido farke ”

“Ita Kakata Ayodele ya take yi?” na tambaye ta,sai da ta saki wani murmushi kafin
ta ce “in na tsaya baki labari ai ɓanar lokaci ne kuma ba za ki fahimta ba,amma MRS
SADAUKI ta fi kowa iya bada labarinta shi yasa ta fitar da littafi na musamman
dominta ungo” ta faɗa tare da miƙo min wani littafi ban kai ga duba sunansa ba na
ji muryar Inna A'i na ce “Nafisa ki tashi ki shirya ƙarfe bakwai fa har ta wuce” da
sauri na ware idona tare da yaye abin rufa.

“Littafin mene ne wannan babu kyawun gani?” Inna A'i ta faɗa tana yamutsa fuska.

Sai a yanzu na farga da littafin da ke riƙe a hannuna,an yi masa cover da hoton


matattu har da fatalwa na motsa bakina dakyar “MUTUWARE(Duk mai son jin labarin
Ayodele sai ya tuntuɓe ni)”

“Ki bar kirawo min mutuwa don Allah ” Inna A'i ta faɗa ,na yi dariya ina saboda na
daɗe da sanin babu abin da take tsoro a duniya kamar mutuwa da kuma fatalwa,haka
duk kusancinta da mutum ba za ta iya kwana da gawarsa ba.

Sai da na yi dariya mai isata kafin na saka littafin cikin jakata sai na shiga
toilet,ruwa na sauka a jikina mafarkin da na yi na yanzu ya faɗo min a rai abin da
ya fi bani mamaki ta ya aka yi littafin ya bayyana gare ni alhalin cikin bacci aka
bani shi? A nan take wani tsoro ya kama ni wanda zan iya cewa wannan ne karon farko
da na taɓa jin tsoro game da ire-iren abubuwan nan.

A gaggauce na yi wanka na fito na shirya, breakfast ɗina ma cikin kwano mai murfi
Inna A'i ta saka min shi kafin na wuce can makaranta.
Tuni kuwa dalibai sun soma zuwa,sai da na je na ajiye jakata a cikin aji kafin na
fito na yi tsaye.

Abun mamaki duk malamin da muka haɗa ido da shi sai ya harare ni,ciki kuwa har da
Adama wacce ajinmu ke manne da na juna.Ina son yi mata magana amma sam ba ta bani
fuska ba sai wani cijewa take.

A haka har lokacin shiga aji yayi,na shiga ina mai yin tsaye tare da fiddo takardar
liste ɗin ɗalibai na soma kiran sunayensu bayan na gama na ce “ akwai wanda bai ji
sunansa ba?”

“Madam ni ” na ji wata murya wacce ta min kama da wacce na sani,na juya inda na ji
sautin sai idona ya sauka kan ɗalibina na jiya da dare amma fa sam ban gane wai shi
ne ba saboda mafarkin da na yi na manta shi.

“Mene sunanka?” na tambaye shi.


“Abdul” ya bani amsa,hakan na nufin sunansa na cikin jerin farko na masu A .“Abdul
wa me sunan mahaifinka?” nan ya faɗa min amma abin mamaki sam babu sunansa a liste
ɗin.
Na ce “kuma jiya da na yi kiran sunan ɗalibai ka ji naka?”
“Eh Madam ” ya bani amsa.
Ban ƙara cewa komai ba sai na fita zuwa ofis ɗin Grand Maa kamar yadda aka ce in
wata matsala ta samu can za mu je.Tun daga bakin ƙofa na ji jinin jikina ya daskare
yayin da kuma numfashina ya canza salon tafiya,dakyar na danna belt na neman izini
ta bani izinin shigowa.
Ina buɗe ƙofa na ci karo da lamba ɗaya ɗan headmaster shi kuma zai fita,yayi min
wani mugun kallo kafin ya fice ni kuma na ƙarasa na gaishe da Grand Maa.Ciki-ciki
ta amsa kafin ta ce “ me kika zo yi kuma?” tambayarta ta ce ta yi min wani iri amma
na watsar da ita kafin na ce “ an manta ba a rubuta sunan ɗaya daga cikin ɗalibaina
ba bisa liste ” sai na faɗi cikakken sunansa .

Wani irin kallo Grand Maa ta yi min na kar ki raina min hankali kafin ta ce “ ai ba
mantawa aka yi ba,ki duba liste ɗin da kyau” yanzu ma furucinta sai ya yi min wani
iri,amma sai na yi kamar yadda ta ce ɗin na nutsu da kyau na duba liste ɗin sai na
ga liste ɗin ta fara da lissafin lamba biyu,sannan a can sama ga sawun rubutu nan
mai ɗauke da lamba ɗaya sai dai sam ya goge ba ka ma ganin abin da aka rubuta.

“Me haka ke nufi?” na tambaye ta ina mai ɗaga kai ina kallon ta .

“Kin ga Malama fitar min daga ofis ki bar yin kamar ba ki san komai ba,ni ba za a
yi comedy da ni ba” ta faɗa cikin ɗaga murya tare da nuna min ƙofar fita,ganin
yadda tuwon fuskarta ya kumbura har yana motsi ga idonta da suka rikiɗe suka zama
kamar na Zombie yasa da sauri har ina tuntuɓe na baro ofis ɗin.

Ina shiga aji sai na ɗauki biro na rubuta sunan yaron daga sama,sai na soma yi masu
darasi har lokacin shan iska yayi.Kamar yadda aka sanar da mu cewa iya ranar Monday
kawai a ba za mu fitar da yara aji ba a nan za su ci abincin da makaranta ta dafa
musu,to yau suna da damar fita wannan yasa na ce su je su sayi abin da suke so amma
da zarar sun ji ƙarar rawa su dawo.

Kowa ya fita daga aji amma banda Firdausi,na dube ta tare da cewa “ke me yasa ba za
ki fita ba?”
“Babana ya ce bai da kuɗi” ta bani amsa.Abincina na buɗe muka ci tare bayan mun
gama na bata chocolat tare da cewa “kullum zan dinga kawo mana abinci mu ci kin ji
ko?” kai ta gyaɗa min alamun to.Haka ta yi ta mini surutu har lokacin dawowar
ɗalibai yayi.

Bayan sun shigo waƙa na soma koya musu sai na ga sun fi mayar ma da hankali a
kanta,yadda duk suka shiga nishaɗi sai abun yayi min daɗi.
Lokacin tashi ya gabato sai na yi zaune tare da fiddo liste ɗin sunaye,abun mamaki
sunan Abdul da ni ce na rubuta shi ya goge babu shi.Shuru na yi ina sauraren bugun
zuciyata da yake wani harbawa fiye da ƙa'ida,dakyar na aro jarumtar sake rubuta
sunan nasa sai kuma na soma kira ɗaya bayan ɗaya har na gama duk sai aka zo fara
ɗaukarsu har kowa ya watse.

Ina fitowa muka yi kiciɓis da Adama na ce “madam Adama Barka da warhaka fatan kina
lafiya?”
“Bayan kin kusa kashe ni shine kike tambayar ina lafiya ? To nan sani ba” ta bani
amsa tare da yin gaba fuuu.Na yi tsaye cak ina kallon ta kafin dakyar na ɗaga
ƙafata na wuce zuwa gida,sai na tarar da Jabeeru direba muka gaisa a mutumce nan
Inna A'i ce ke faɗa min Ammy ta aiko shi ya kawo mana abubuwan buƙata har ƙatuwar
frigine wacce aka cika da kaji zuƙu-zuƙu.

Bayan ya tafi ne na shiga na yi wanka na fito,ina zaunawa Inna A'i ta miƙo min kofi
cike da madara tana cewa “ungo ki shanye ƴar autata ” ganin yadda ta yi min abin
cike da soyayya yasa na karɓa na sha ba tare da na tambayi na mene ne ba.
[30/01 08:07] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️
```LoVe aNd HoRrOr story```👽

By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}

*SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta.

*FCWA*☀️

________________________

Last free page 10

Ganin Grand Maa ta ɗauki wuƙa za ta tsaga cikin yaron na yi saurin rumtse idona,ina
jin sautin kururuwarsa yadda yake kuka yana cewa “madam ki cece ni kar ki bari su
cutar da ni ” na buɗe idona da suka yi jawurrr na sake zuba su kan Grand Maa wacce
ke zuba jinin yaron nan a kofi ta hanyar saka ludayi tana wani kwaso shi.
Bayan ta gama sai ta kai kofin bakinta ta sha sannan ta miƙawa principal shi kuma
da ya sha ya bai wa headmaster daga nan sai vice principal da kuma vice
headmaster.Grand Maa ta ƙara karɓar kofin ta ce “lamba ɗaya sha ka bai wa lamba
biyu,haka za ku dinga yi har kowa ya sha” wanda aka kira da lamba ɗaya na duba,
kyakkyawan saurayi ne irin sosai ɗin nan kuma sai na ga yana kama da headmaster da
dukkan alamu ɗansa ne,bayan ya sha sai ya miƙawa lamba na biyu shi kuma ya miƙo min
na karɓi kofin ina kallon yadda jinin ɗalibina yake kwance a ciki mugayen matsafan
nan sun mayar da shi lemun sha .Na kai kofin kusan bakina na yi kamar na sha kafin
na miƙawa Adama wacce ita kuma ita ce lamba huɗu,so nake na ce mata kar ta sha amma
idon Grand Maa ƙurrr suke kanmu ina ji ina gani Adama ta sha jinin kafin ta ba na
kusa da ita a haka har kowa ya sha aka mayar da kofin.

Daga nan sai Grand Maa ta yi wani siddabarun sai ga yaron da aka feɗe cikinsa ya
tashi zaune daram da buɗaɗen ciki idonsa na shatatar da hawayen jini yana kallon
tsakiyar idona har yanzu kuma bai gushe da neman taimakona ba sai dai sam ban san
ya za a yi na taimake shi ɗin ba.

Wasu kwalabe ta jera saman table ɗin,ta yi wani alama da hannu a nan take duk suka
buɗe kansu.Bakinta na furta ɗalasiman tsafi ta dinga umartar ruwan da ke cikin
kowacce kwalba da su je su shiga buɗaɗen cikin yaron,nan ya soma yin wata irin
zabura kamar an jona shi da lantarki abin da na kasa jura kenan na ce “ōvovār̃ī”
hakan yana nufin komai ya tsaya wato stop cak duk komai ya tsaya kuwa yayin da
dukkansu suka soma amayo jinin da suka sha suna wani waro ido kamar za su mutu.Sam
ban wani damu ba sai ma zuwa da na yi na ɗauki ɗalibina ,kamar yadda uwa ke gudun
matsala ta samu ga ɗanta ko kuma in ta ga wani abu zai cutar da shi take ɗauke shi
tare da ɓoye shi haka na yi wa ɗalibina na ƙanƙame shi gam a ƙirjina ina kallon
Grand Maa wacce ke yin ƙarfin hali tana cewa “lamba uku ki ajiye shi kar lokacin
kaddamarwa ya wuce duk ki ɓata mana shiri ki maido mu baya”

Na girgiza mata kai na ce “ba zan bayar da ɗalibina ba”

“Lamba ɗaya je ka ƙwato min abin farauta” Grand Maa ta basa umarni ai kuwa sai ya
miƙe tsaye ya tunkaro ni,muna kallon juna cikin ido sai na ga tamkar na san shi
yana dab da kawowa wurina kuma sai na tuna a inda na san idon,wato tsakakar ranar
nan ce da na bugewa bindi.Na dubi ƙafarsa sai na ga yana yin ɗingishi,“kār̃bās!” na
furta nan take kuma ya ɓangwale ya faɗi yana ihu,nan kuwa na ga hankalin headmaster
ya tashi ya nufo shi duk da kuwa ƙoƙarin tsayar da shi da Grand Maa ta yi don ba a
so kowa ya gusa daga wurinsa sai da umarni.

Ta yo kaina za ta ƙwace shi da ƙarfi ni kuma da mugun sauri na bi ta rufin ɗakin na


tashi sama cikin iska muka bar wurin.Ban san inda na ɓoye yaron ba amma tabbas na
kuɓutar da shi kuma na basa tsaro,daidai nan kuma na tashi daga baccin saboda kiran
sallar asubah da aka yi.

Dukkan cinyoyina na ji suna yi min ciwo kamar wacce ta yi wasar tsere,dukkan


abubuwan da suka faru da ni kuma sai na manta da su .Wanka na yi tare da alwala na
zo na yi sallah,bayan na gama na soma yin Azkhar ina lumshe ido alamun bacci ne
yake son ƙara yin gaba da ni amma kiran Uncle Salem ya shigo wayata na je na ɗauka
tare da yin kwance na kara wayar a kunne.
Yau shine ma ya gaishe ni da farko,na amsa cikin mayen bacci ina jin yana cewa “
mafarkin me kika yi Naf ?”
Baccin da nake ji ne ya sake ni a nan take tuna na yi mafarkinsa mun haɗa shimfiɗa
da shi muna mu'amalar aure ,amma me yasa yake yi min tambayar nan shine abin dubawa
.Cike da gyatse na ce “kai wane iri ka yi?”
Sai da ya saki murmushi kafin ya ce “mafarki na yi ga shi nan an kawo min ke
gidana,muna kwance kan bed duk babu sutura a jikinmu ina yi miki zazzafan romance
ke ma kina maido min da kuma na fara kusantarki sai kika fara yi min kuka kina
kiran sunana Uncle Sal zafi ka bari ban so.Amma sai na soma rarrashinki har kika yi
shuru kika bar kuka,Naf na ji daɗin mafarkin nan sosai kin ga yanzu ma da zan yi
sallah sai da na yi wanka”

Tun da ya soma magana na rumtse ido,wato shi ko kunya bai ji yayi mafarkin suna sex
da ƴarsa sannan har wani labari yake bani.Ina ƙoƙarin kashe kiran ya tsayar da ni,“
Please Naf kar ki kashe min kira faɗa min yau ma kin yi mafarkin tsoro?”

Jin ya canza akalar zancen yasa na yi shuru,sosai na tuna na yi mafarkin ban tsoro
amma na kasa tuna abubuwan da suka faru.
“Faɗa min me kika gani?” ya sake faɗa .
Na ce “ni na manta komai”
“Kin sha maganinki kuwa kafin ki kwanta?” ya jefo min tambaya,ni sam na ma manta da
ya bani magani.Na ce “eh a'a...”
“Baby ina ga ke ma kina son na zo kusa da ke shi yasa kike wasa da shan magani,amma
babu damuwa duk weekend zan dinga zuwar miki” da sauri na ce “a'a ban so ka yi
zamanka ”
“Saboda me? Naf me yasa kike son hana cikar burinmu ne ? Haƙurina ya ƙare fa ina
buƙatar kulawa kin san abin da nake ji duk dare? Da zazzafan feeling ɗinki nake
bacci ina tuna surar jikinki na matsu na ji komai na jikinki a hannuna yana sarrafa
shi ...” kuka na saka masa ina roƙonsa don Allah ya bari ban son irin wannan zancen
daga ƙarshe na ƙara da cewa “uncle ka je asibiti don Allah likita ya duba ka”
“Ke ce likitata domin ke kaɗai kike da maganin ciwona,kin ga yanzu ma duk kin tayar
min da hankali ji nake...” ban bari ya ida ba na kashe kiran ina mai ci gaba da yin
kuka.

Inna A'i wacce ta fito daga toilet ta ce “in kin gama kukan sai ki tashi ki yi
sallah”
Na ɗaga kai na dube ta ina mamakin yadda aka yi ta canza min,na turo baki gaba na
ce “Innarmu kin bar sona ” na faɗa ,ba ta kula ni ba ta haye dadduma.Ni ma tashi na
yi na shiga toilet na yi wanka sannan na ɗauro alwala na zo na gabatar da
sallah,ina Azkhar ina tuna mafarkin da na yi da Uncle Salem nan take kuma na soma
jin jikina na saki har wani sanyi-sanyi nake ji yana rufe ni.Na je na ƙara haye
katifa tare da jan bargo na rufa ina lumshe ido,karon farko da na ji ina muradin
yin saurayi mu yi soyayya sannan aure ya biyo baya sai yayi min duk abin da Uncle
ɗina yayi min cikin bacci.Da wannan tunanin bacci ya sake yin awon gaba da ni sai
kuma na ci gaba da mafarkina daga inda na tsaya wato cikin wani daji na tsinci
kaina.A gabana kuma wani ɗaki ne na kara,a bakin ƙofa wata tsohuwa ce zaune tana
hura wuta amma ban ganin fuskarta.

Na matsa kusa da ita na ce “Kaka jiya na yi ajiya a wannan ɗakin cikin dare” ko
kafin ta ɗago idona ya sauka kan ƙusumbinta.

Ta ɗago tana kallona,ganin mun san juna sai na sakar mata murmushi na ce “Kaka dama
ke ce? Nan ne gidanki?” na faɗa ina nuna ɗakin.
Ta jinjina kai kafin ta ce “ki shiga ciki yana nan yana bacci amma kar ki tashe ”

Na shiga ɗakin sai na tarar da ɗalibina kwance bisan kunnuwan ganye yana
bacci,fuskarsa kawai ake gani saboda yadda aka yi masa rufa da wata fatar dabba.

“Ya samu rauni sosai Allah yayi sa'a ma kin kawo shi nan kan lokaci da saura ƙiris
ya rasa ransa” Kaka ta faɗa wacce ta shigo hannunta riƙe da ƙwayar sai tururi ke
tashi.

Zama ta yi kusa da shi kafin ta yaye fatar,da sauri na kawar da kai ganin yadda
ciwon nasa yake buɗe har yanzu.
“Ki matso ki soma ɗinke masa cikin ” ta faɗa .
Na juyo da sauri na ce “ni kuma?“
“Eh kin zata wa zai yi miki aikin?” ta faɗa tare da miƙo min wani mashi mai kamar
wuƙa da kuma baƙin zare.
Jikina ne ya soma rawa haka na zauna ina kallon yadda ta ƙara wanke cikin nasa tare
kuma da zuba wani magani,hannu na kyarma na soma ɗinki yayin da ita kuma take faɗar
wasu surkullen da ita kaɗai ta san ma'anarsu a haka har na ida.

Na yi baya ina mayar da numfashi,ta tashi ta je can gaban wani babban teburi ta
ɗauko min zuma ta bani na karɓa ina washe baki saboda ina son zuma kullum sai Uncle
Salem ya bani ita tun ina ƴar yarinya.

Zumar na soma sha muna kallon juna ni da Kaka kafin ta ce “ban san dalilin Deborat
ba da ta zaɓi ta ɓoye miki baiwarki,amma na so a ce kin zama tamkar Kakarki Ayodele
ciwon idon Mayu...” sai kuma ta yi shuru yayin da ni kuma na tsaya da shan zumar na
ce “wai Granny Mamar Daddyna?”

Ta jinjina min kai kafin ta ce “eh sosai ita fa! Kin san ita ma ba ta da tsoro
kamar ke take,sai dai ita dukkan aikin da alloli da magabata suka saka ta yi tana
sane da komai ba kamar ke ba da yake zuwar miki siffar mafarki”

“Yanzu mafarki ne nake yi kenan?”


“Kusan haka ne! Sai dai wannan muna kiransa da balaguron ruhi,wasu suna yinsa cikin
bacci yayin da wasu kuma ke yinsa ido farke ”

“Ita Kakata Ayodele ya take yi?” na tambaye ta,sai da ta saki wani murmushi kafin
ta ce “in na tsaya baki labari ai ɓanar lokaci ne kuma ba za ki fahimta ba,amma MRS
SADAUKI ta fi kowa iya bada labarinta shi yasa ta fitar da littafi na musamman
dominta ungo” ta faɗa tare da miƙo min wani littafi ban kai ga duba sunansa ba na
ji muryar Inna A'i na ce “Nafisa ki tashi ki shirya ƙarfe bakwai fa har ta wuce” da
sauri na ware idona tare da yaye abin rufa.
“Littafin mene ne wannan babu kyawun gani?” Inna A'i ta faɗa tana yamutsa fuska.

Sai a yanzu na farga da littafin da ke riƙe a hannuna,an yi masa cover da hoton


matattu har da fatalwa na motsa bakina dakyar “MUTUWARE(Duk mai son jin labarin
Ayodele sai ya tuntuɓe ni)”

“Ki bar kirawo min mutuwa don Allah ” Inna A'i ta faɗa ,na yi dariya ina saboda na
daɗe da sanin babu abin da take tsoro a duniya kamar mutuwa da kuma fatalwa,haka
duk kusancinta da mutum ba za ta iya kwana da gawarsa ba.

Sai da na yi dariya mai isata kafin na saka littafin cikin jakata sai na shiga
toilet,ruwa na sauka a jikina mafarkin da na yi na yanzu ya faɗo min a rai abin da
ya fi bani mamaki ta ya aka yi littafin ya bayyana gare ni alhalin cikin bacci aka
bani shi? A nan take wani tsoro ya kama ni wanda zan iya cewa wannan ne karon farko
da na taɓa jin tsoro game da ire-iren abubuwan nan.

A gaggauce na yi wanka na fito na shirya, breakfast ɗina ma cikin kwano mai murfi
Inna A'i ta saka min shi kafin na wuce can makaranta.
Tuni kuwa dalibai sun soma zuwa,sai da na je na ajiye jakata a cikin aji kafin na
fito na yi tsaye.

Abun mamaki duk malamin da muka haɗa ido da shi sai ya harare ni,ciki kuwa har da
Adama wacce ajinmu ke manne da na juna.Ina son yi mata magana amma sam ba ta bani
fuska ba sai wani cijewa take.

A haka har lokacin shiga aji yayi,na shiga ina mai yin tsaye tare da fiddo takardar
liste ɗin ɗalibai na soma kiran sunayensu bayan na gama na ce “ akwai wanda bai ji
sunansa ba?”

“Madam ni ” na ji wata murya wacce ta min kama da wacce na sani,na juya inda na ji
sautin sai idona ya sauka kan ɗalibina na jiya da dare amma fa sam ban gane wai shi
ne ba saboda mafarkin da na yi na manta shi.

“Mene sunanka?” na tambaye shi.


“Abdul” ya bani amsa,hakan na nufin sunansa na cikin jerin farko na masu A .“Abdul
wa me sunan mahaifinka?” nan ya faɗa min amma abin mamaki sam babu sunansa a liste
ɗin.

Na ce “kuma jiya da na yi kiran sunan ɗalibai ka ji naka?”


“Eh Madam ” ya bani amsa.
Ban ƙara cewa komai ba sai na fita zuwa ofis ɗin Grand Maa kamar yadda aka ce in
wata matsala ta samu can za mu je.Tun daga bakin ƙofa na ji jinin jikina ya daskare
yayin da kuma numfashina ya canza salon tafiya,dakyar na danna belt na neman izini
ta bani izinin shigowa.
Ina buɗe ƙofa na ci karo da lamba ɗaya ɗan headmaster shi kuma zai fita,yayi min
wani mugun kallo kafin ya fice ni kuma na ƙarasa na gaishe da Grand Maa.Ciki-ciki
ta amsa kafin ta ce “ me kika zo yi kuma?” tambayarta ta ce ta yi min wani iri amma
na watsar da ita kafin na ce “ an manta ba a rubuta sunan ɗaya daga cikin ɗalibaina
ba bisa liste ” sai na faɗi cikakken sunansa .

Wani irin kallo Grand Maa ta yi min na kar ki raina min hankali kafin ta ce “ ai ba
mantawa aka yi ba,ki duba liste ɗin da kyau” yanzu ma furucinta sai ya yi min wani
iri,amma sai na yi kamar yadda ta ce ɗin na nutsu da kyau na duba liste ɗin sai na
ga liste ɗin ta fara da lissafin lamba biyu,sannan a can sama ga sawun rubutu nan
mai ɗauke da lamba ɗaya sai dai sam ya goge ba ka ma ganin abin da aka rubuta.

“Me haka ke nufi?” na tambaye ta ina mai ɗaga kai ina kallon ta .

“Kin ga Malama fitar min daga ofis ki bar yin kamar ba ki san komai ba,ni ba za a
yi comedy da ni ba” ta faɗa cikin ɗaga murya tare da nuna min ƙofar fita,ganin
yadda tuwon fuskarta ya kumbura har yana motsi ga idonta da suka rikiɗe suka zama
kamar na Zombie yasa da sauri har ina tuntuɓe na baro ofis ɗin.

Ina shiga aji sai na ɗauki biro na rubuta sunan yaron daga sama,sai na soma yi masu
darasi har lokacin shan iska yayi.Kamar yadda aka sanar da mu cewa iya ranar Monday
kawai a ba za mu fitar da yara aji ba a nan za su ci abincin da makaranta ta dafa
musu,to yau suna da damar fita wannan yasa na ce su je su sayi abin da suke so amma
da zarar sun ji ƙarar rawa su dawo.

Kowa ya fita daga aji amma banda Firdausi,na dube ta tare da cewa “ke me yasa ba za
ki fita ba?”
“Babana ya ce bai da kuɗi” ta bani amsa.Abincina na buɗe muka ci tare bayan mun
gama na bata chocolat tare da cewa “kullum zan dinga kawo mana abinci mu ci kin ji
ko?” kai ta gyaɗa min alamun to.Haka ta yi ta mini surutu har lokacin dawowar
ɗalibai yayi.

Bayan sun shigo waƙa na soma koya musu sai na ga sun fi mayar ma da hankali a
kanta,yadda duk suka shiga nishaɗi sai abun yayi min daɗi.
Lokacin tashi ya gabato sai na yi zaune tare da fiddo liste ɗin sunaye,abun mamaki
sunan Abdul da ni ce na rubuta shi ya goge babu shi.Shuru na yi ina sauraren bugun
zuciyata da yake wani harbawa fiye da ƙa'ida,dakyar na aro jarumtar sake rubuta
sunan nasa sai kuma na soma kira ɗaya bayan ɗaya har na gama duk sai aka zo fara
ɗaukarsu har kowa ya watse.

Ina fitowa muka yi kiciɓis da Adama na ce “madam Adama Barka da warhaka fatan kina
lafiya?”
“Bayan kin kusa kashe ni shine kike tambayar ina lafiya ? To nan sani ba” ta bani
amsa tare da yin gaba fuuu.Na yi tsaye cak ina kallon ta kafin dakyar na ɗaga
ƙafata na wuce zuwa gida,sai na tarar da Jabeeru direba muka gaisa a mutumce nan
Inna A'i ce ke faɗa min Ammy ta aiko shi ya kawo mana abubuwan buƙata har ƙatuwar
frigine wacce aka cika da kaji zuƙu-zuƙu.

Bayan ya tafi ne na shiga na yi wanka na fito,ina zaunawa Inna A'i ta miƙo min kofi
cike da madara tana cewa “ungo ki shanye ƴar autata ” ganin yadda ta yi min abin
cike da soyayya yasa na karɓa na sha ba tare da na tambayi na mene ne ba.

Sosai na yi ƙoƙari wurin watsar da duk abin da ya faru da ni a makaranta muka sha
hira da Inna A'i kafin ta kawo min naman kaza wanda ta yi wa wani romo na musamman
dama tun da na dawo ban ci komai ba sai na zauna na soma ci sai na ji tamkar
ɗanɗanon magani amma ban yi magana ba na ci na ƙoshi.

Inna A'i ta ce “zan fita na je kasuwa akwai abubuwan da zan sayo ”


Na ce “kin san kasuwar ne?”
“Taxi zan shiga,ba zan jima zan dawo”
“To a dawo lafiya” na faɗa nan ta fice ni kuma saboda kaɗaici yasa na jawo wayata
sai dai sam babu network a dole na ajiye ta na ɗauki littafin MUTUWARE ,tun a page
ɗin farko na soma jin kaina na juyawa yayin da nake ganin kamar abin da ya faru ya
taɓa faruwa da ni,da na tsananta tunani ne kawai idona suka hasko min abin da ya
faru da ɗalibina Abdul a daren jiya.Na dafe saitin goshina da ya soma tsira min,ba
tare da na shirya ba na kwanta baccin dole wanda ban yi niyya ba.

Cikin wata kasuwa na tsinci kaina,sai tafiya nake ina waige-waige kamar mai neman
wani abu.Yayin da hankulan ƴan cikin kasuwan duk ya dawo kaina kamar sun ga sabuwar
halitta,har tambayar kaina nake mene ne suke kallo a jikina.Ban ɗauki dogon lokaci
ba kuma na samo amsar,wato dogayen fuka-fuka ne a bayana sai motsa kansu suke.Ban
kuma ɗauki lokaci ba na tashi sama ina baza idona ta ko ina ,can na hango Inna A'i
tana ta sauri yayin da wata matsafiya ke take mata baya tana naɗe inuwar Inna A'i
tamkar wata tabarma.Shuuu na dira a tsakiya cak matsafiyar ta tsaya tana
kallona,“bani abin da ke hannunki ” na faɗa saboda kusan rabin kurwar Inna A'i na
hannunta.
Da sauri ta saka abin cikin kwagiri (wata jaka ce da tsofi ke ɗaurawa a ƙugu don
zuba kuɗi)

Ihun Inna A'i yasa da sauri na juya ta ɓangarenta,sai na ga ta faɗi na je da guduna


ina kiran sunanta na tallabo ta.Ko da na waiga sai na ga babu matsafiyar babu
alamunta,daidai nan na tashi daga baccin saboda kakarin mutuwa da na ji ana yi kusa
da ni.

Na buɗe idona a hankali da suka yi min nauyi,sai na ga Inna A'i ce kwance tana
kakarin mutuwa jini na fita ta hancinta.Hankali tashe na ce “me ke damunki
Innarmu?”

Numfashinta kamar zai fita take min jawabi “a kasuwa ne wata mata ta bani ƙananun
kifi na ci shine kawai na soma jin jiri,jikina kuma kamar ana cire min wani abu”

Fatarta na kalla na ga ta yi wani mugun ja ga wasu sawun halittu tamkar dai


kifin.Tsam na miƙe tare da saka takalmi,idona har wani rufe wa suke saboda ɓacin
rai,ni kaina ban san wa nuna min kasuwar ba haka dai na samu kaina da tunkarar wata
hanya har na isa.Allon sanarwar na duba inda aka rubuta ƘWARGWAM MARKET wato
kasuwar matsafa,ƙafata na ɗora da niyyar shiga sai dai tamkar akwai wani abu da ke
jana a baya wanda ya hana ni shiga ciki.Na gwada hakan ya fi shuren masaki amma na
kasa,a ƙarshe ma dai sai zube wa na yi ƙasa a gajiye numfashina na shirin tsinkewa.

Nan na kawo ƙarshen free page duk mai son ci gaba zai biya 500 via

2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank

Sai ya turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822

NB: Yanzu nake rubuta shi ,so don Allah kar ki zo kina ce min ke complet kike so Ni
kaina banda shi.
In kuma ya kammala 1k ne kuɗinsa.

30 Janairu 2025
[30/01 08:49] MRS SADAUKI: *SURUKATA*🪽🪽🪽

Na
*Chamsiya Laouali Rabo*
```{MRS SADAUKI}```✍️

*FCWA* ☀️

*SADAUKARWA Ga:*. Shamsiyya Manga, My Namecy 😊

___________________________________

01

A duniya akwai wata babbar illa wacce ba kowa ke fahimtar illa ba ce sai wanda abin
ya faru da shi kamar dai ni da duniya ta yi juyin waina da ni.
Farinci;kalma ce da ban san me take nufi ba ballantana na more ta,na taso cikin
matsin rayuwa mai cike da ƙalubale da rikitacen al'amari wanda da ace ba a kaina
hakan ta faru ba da ko shakka babu ba zan taɓa yarda kan cewa Uwa na iya cutar da
Ƴar da ta tsugunnai ta haifa ba.

Sunana Janiki,ƴar asalin ƙasar Yuganda ce a wani ƙauye da ake kira da Norobi,ƙauyen
ya shahara wurin bai wa al'ada haƙinta.Ni ce ta farko wurin iyayena,sai ƙannaina
uku Ayo mai shekara goma sha bakwai,sai Sarah mai 13years sai kuma ƴar autarmu
Natasha mai shekara goma.Dukkansu baƙaƙe ne sai ni ɗaya tal ke fara sol kamar
zabaya,da wannan jama'ar ƙauyen suke tsokanata da ƴar fara mayya.Tun ina da
ƙanannun shekaru ake kirana da haka har zuwa yanzu da nake cikin shekara ta ashirin
da biyar.

A hankali nake wanke kwanukan da zan zuba abincin rana,ina rera waƙoƙin da ake koya
mana a Coci.Saukar dundu na ji a bayana kafin ashar ta biyo,“ to daƙunanna haihuwar
asara,kin kama kwanuka kina shafa kamar mai yi wa jariri wanka sai sun sauko daga
makaranta ba ki gama ba ko?” muryar Mama ce wacce a kullum nake fargabar jin ta.

Jikina na kyarma na ce “ na kusa ida wa Mam...” ko rufe baki ban yi ba ta gwaɓe


mini haɓa tare da shure ni da ƙafa tana mai cewa “ don ubanki kar ma ki gama zauna
nan ki yi ta shafar kwanukan in ƙannan ubanki ne” ban ce komai ba sai sauri da na
ƙara ina mai ci gaba da tsiyayar da hawaye,ina gama wanke wa daidai ƙannaina na
shigowa su duka ukun a tare kowacce riƙe da jakar makarantarta.

Kamar wasu jarirai haka Mama ta soma tarairayar su tana tambayar su makaranta, sai
washe baki take tana fara'a kamar ba ita ce ta gama haɗe mini fuska tana zagina
haɗi da dukana ba.

“Shegiya mayya ta wani zubo mamu shegun ƙattin idonta tana kallo,ba za ki je ki
fidda abincin ba sai na kare miki ƙafa?” Mama ta faɗa a lokacin da na shagala ina
kallonsu,sumi-sumi na wuce zuwa mafada.Kamar yadda na san kowa shi ɗaya yake cin
abinci haka na ɗauki kwanuka ina zuba abinci har na fidda shi duka,haka na jera
kwanukan kan ƙaton faranti na kai gaban Mama.

Nan kowacce ta ɗauki nata ni ma na ja nawa tare da komawa gefe na fara ci kenan sai
ga Sallamar Hajiyar Lubabatu ƙawar Mama wacce a duniya in akwai wacce ta tsane ni
bayan Mama to ita ce ta biyu.

Ina ƙoƙarin sunne kai don gudun mugun kallon da za ta watso mini,amma sai ta
shammace ni ta sakar min murmushi har da tsarabar furuci mai daɗi.

“ Ah ƴata Jakini abinci ake ciki?” ta faɗa .

Da sauri na gaishe ta “ ina wuni Tanti?”

“Lafiya lau alhamdullah” ta amsa kafin su soma taɓawa ita da Mama,can kuma suka
miƙe suka shiga ɗaki.Da wannan damar yasa na matsa kusa da ƙannan nawa ina mai cewa
“ yawwa ku koya min karatun”

Ayo mai mugun hali ta miƙe ta shige ɗaki,sai Sarah ce ta fara koya min duk da ba a
rubuce ne ba amma ina fahimta sosai.

“Janiki ashe har yanzu kina ta ƙoƙarin koyon karatu?” Hajiya Lubabatu ta faɗa bayan
ta fito na tsawon lokaci da suka ɗauka ita da Mama a ɗaki.Na ɗan saki murmushi tare
da jinjina kai,ta ƙara yin ƙasa da murya ta ce “ yawwa ki daure ki koya kin ji ai
ana son mace ta waye ta fannin karatu,in kina so ma zan turo malami na Musamman don
koy...” maganar ce ta yanke saboda fitowar Mama.

“Kin ga fa Ayo ce da rigimar da ta saba ashe ta ji hirar da muka yi” Mama ta faɗa
tana murmushi kafin ta janye Hajiya su nufi ƙofar fita da alamu rakiya za ta yi
mata.

Ina nan zaune sai ga Ayo ta fito tana hararena,wanda kuma ban san dalilin haka ba
sai da Mama ta dawo.

“To Janiki sai a fara shiri lokacin aurenki yayi,yanzu nan Hajiya Luba ta zo min da
shawarar arziki kuma na yi amanna da ita” sai kuma ta yi shiru tana kallona kamar
yadda ni ma ita nake kallo.

“Ai kin san babban ɗanta Aliyu ko?” Mama ta tambaye ni,na jinjina kai tare da sunne
kai ina jin zuciyata na mugun bugawa da sauri.

“To da shi muka yanke shawarar haɗa ki aure,tun da dama ba wani karatu kike yi ba
sannan ba saurayi ne da ke ba” Mama ta ƙara faɗa .Idona ne suka kawo ruwa,na ɗaga
kai dakyar na ce “ Amma Mama tsoho ne fa,ya kai shekara arba'in duka-duka nawa
nake?”

“Yanzu na haifo ki Janiki!” ta faɗa cikin ƙaraji kafin ta ci gaba da yi min masifa
“ wato kin samu zai rufa miki asiri ya aure ki shine za ki wani tsiro min da wani
iya yi,a'a ba tsoho ne ba shine tuwo tashi ki bani wuri” ta yi min wata uwar tsawa
tare da kai min duka.

Da mugun sauri na tashi na shige ɗaki,kan katifa na haye na ci kuka sosai har na
gode ma Allah.A haka na samu bacci ya ɗauke ni,haniyar mutane ce ta tashe ni da
bushe-bushe.

“Me kuma ake yi a gidan?” na tambayi kaina,shigowar da Abba yayi ce ta bani amsar
tambayar hannunsa riƙe da alawa da goro.Bakinsa kamar gonar auduga tsabar
murna,miƙo min yayi kafin ya ce “ kuɗin an gani ana so ne aka kawo miki Janiki,ina
taya ki murna ke ma za ki je ɗakinki?”

“Duk yaushe aka tsara wannan ban sani ba? Yanzu fa na kwanta bacci” na yi furicin
ina duba tsohuwar agogon ɗakinmu sai na ga ƙarfe wajen biyar har da rabi na maraice
alhalin lokacin da na kwanta duka-duka ƙarfe ɗaya ne.

Abba bai wani damu da tashin hankalin da na shiga ba ballantana ya bani amsar
tambayar da na jefo,kawai ya ajiye goro da alawar ya fice.Ban iya fita ba saboda
har yanzu ina jin hayaniyar mutane da saura ba su watse ba,sai bayan gari yayi duhu
ne gidan yayi tsit sai a halinsa kawai.Dakyar na je na yi wanka na sauya kaya na
zauna tare da rabka uban tagumi ina tunanin zuciya ‘ yanzu dai gaske Umar za su
aura min? Mutumin da kullum fuskarsa a haɗe take bai fara'a ? To shi ya ce yana
sona ko shi ma dole za a yi masa?’ maganar Mama ce ta katse min tunani “ ki tashi
kin yi baƙi” gabana ne ya bada rasss.....
[11/12 à 02:37] MRS SADAUKI: *SURUKATA*🪽🪽🪽

Na
*Chamsiya Laouali Rabo*
```{MRS SADAUKI}```✍️
*FCWA* ☀️

*SADAUKARWA Ga:*. Shamsiyya Manga, My Namecy 😊

___________________________________

02

“Ba.baaa...ƙi kuma Mama?” na jefo mata tambayar muryata na ɗan rawa ,ƙwanda ta kai
min ga kai tana cewa “ munafuka kamar ba ta son auren ,tashi don ubanki ki je suna
jiran ki”

Wani kallabi na jawo na ɗora a kaina kafin na fita,a cikin rumfa na gan su a zaune
kan kujera sun tsurawa ƙofar ɗakinmu ido.

Dakyar na aro nutsuwa na gaishe su“ ina wuninku?”


“Lafiya lau amaryarmu” suka amsa su duka biyun lokaci guda,a fakaice na ƙare musu
kallo suna sanye cikin dogayen kaya amma babu wanda ya ɗora hulla duk da ƙwan
fitilarmu bai da wani haske sosai amma hakan bai ɓoye min ganin kamanninsu da Aliyu
ba.

“To mu za mu wuce dama mun zo gaishe ki ne,kasancewar ɗazu dandazon mutane yayi
yawa ba mu samu muka gan ki ba ” ɗaya ya faɗa ,kafin su miƙe dukkan su.
“To na gode” shine abin da na faɗa ina mai shigewa ɗaki ba tare da jiran sai sun
tafi ba ko kuma tunanin yi musu rakiya.

“Har sun tafi?” Mama ta jefo min tambaya,na gyaɗa mata kai ta ce “ mene ne suka
kawo miki?”
“Babu komai Mama ” na faɗa a sanyayye.Ta ja tsuki kafin ta ce “ wannan shegen
sanyin halin ki bar shi tun yanzu,don gidan yawa za ki je sannan mijinki babban
mutum ne wanda kullum cikin yin baƙi yake dole ki yi tunanin zama da shi.Yanzu su
baƙin kin basu ruwa ma?”

Cikin na dube ta na ce “ Mama ruwan me za su sha su da ba wani abinci suka ci ba?”


ludayin miya ta jefo min aka yi rashin sa'a kuwa ya same ne ga ƙwandar ƙafa,na saki
ƙara tare da soma yin hawaye.Nan Mama ta rufe ni da balbalin bala'i da masifa sai
da ta yi mai isarta sannan ta yi shiru.

Haka na rakuɓe can jikin gini ina shafar hawaye,ƙafar kuma tuni ta ɗan kumbura tana
min zugi. Tausayin kaina ne ya kama ni,ina daga gefe ina kallon ƙannaina suna
lesson tare da yin hira jefi-jefi a tsakanin su amma ni tamkar wata mujiya sun
maida ni gefe.

‘ Allah ke da magani,da wannan masifar ta Mama ai gara na yi auren na bar mata


gidanta ’ na faɗa a zuci kafin na kwanta kan tsohuwar ledar ɗakin sai baccin
wahala.

Washegari kamar yadda Mama ta sunnanta mini a kowacce safiya zan miƙe na haɗa wa
ƴan makaranta abincin safe haka na tashi tun da sauran duhu na fita zuwa
madafa.Dakyar na samu wutar ta kama,na ƙara wanke tukunyar kafin na ɗora kan murhu
na zuba ruwa.

Garin ɗan wake na ɗauko na zuba kayan haɗi na kwaɓa,kafin na je na share tsakar
gida tasss.Ko da na gama tuni tukunyata ta tafasa,sai da na wanke hannuna sosai
kafin na jefa ɗan waken sai kuma na shiga yanka albasa da sauran abubuwan da zan
soya mai da shi.

Ba ni na ida aikin ba sai ƙarfe bakwai da wasu mintina,sai na hau kuma wanke
kwanuka.Ina nan a zaune ƴaƴan takarda suka fito duk kowacce ta yi wanka ta shirya.

“Janikiii?” Mama ta ƙwala min kira,jiki na ɓari na tafi a guje don amsa kiran hakan
ya tuna min da ciwon ƙafata sai na tsangale ƙafar ina mai raba ta da ƙasa.“ Mama ga
ni ?” na faɗa ina yamutsa fuska saboda zugin da ƙafar ke yi min,“ daga nan bakin
ƙofa za ki tsaya ?” ina jin haka na san da akwai matsala amma na daure na ida
shiga,kamar jira take ta kai min duka tana mai cewa “ da kika girka abinci ubanki
ya kawo shi da za ki ce ba za ki zuba musu ba? Har da wani zaginta kina yi mata
gorin cewa kin kusa bar musu gidansu”

Ina jin haka sai na ɗaga kai na dubi Ayo don kuwa na tabbata ita ce ta ja min
sharri,ina hawaye na fito na shiga madafa na zuba musu abin karyawa na kai musu.

Wanke-wanken da na ƙare cikin kuka kenan,da za su tafi don tsokana har da ce min ta
yi “ ƴar aiki mun tafi makaranta” ban kula ta ba sai Sarah ce ta shigar min ta
hanyar bangazar ita Ayon.

Bokiti na cika da ruwa na je na yi wanka,ko da na fito sai na tarar da robar da na


ajiye ɗan wake a tsakar gida alamu ya ƙare.
” Mama ina nawa?” ita ce tambayar da na yi ko da na shiga ɗaki don yunwa nake ji
jiya ban ci komai ba na kwanta,duk da ba mu yi girki ba amma su sun ci wanda aka
tarbi baƙi da shi.

“ Ba ki ci ba ne? To ya ida ” ta bani amsa tana mai ci gaba da cin nata wanda ta
baɗe da yaji sosai har sai da yawuna suka tsinke.Ban ƙara cewa komai ba na je na
buɗe jakar kayana na ɗauko mai na shafa kafin kuma na fita zuwa ƙofar gida.Kan
dakali na zauna ina magana ni ɗaya “ Yesu kana dai ganin halin da nake ciki amma ka
yi shiru,sai yaushe ne zaka amsa kokena?” sai kuma hawaye suka zubo min,na duƙe kai
ina mai ci gaba da kukan haɗi da ɗaukar wata tsumagiya na soma wasa da ita ina yin
zane.

Inuwa na gani kai gare ni,da wani mugun sauri na ɗago kai sai muka yi ido huɗu da
wani kyakkyawan saurayi.Ya sakar min murmushi kafin ya miƙo min hankici,ban karɓa
ba sai farin hannunsa da ƙure da ido ina kallon yadda jijiyoyin hannunsa suka fito
sharrr da su tsabar hasken fatarsa.

Kan fuskata ya jefo min hankicin ya kuwa rufe ta ruf,da mugun sauri na lumshe ido
tare da buɗe ƙofofin hancina ina shaƙar ƙamshin turaren da ke kan kyakkyawan farin
ƙyallen. Can kuma na sa hannu na cire shi daga kan fuskata,sai dai wayam ban ga
saurayin ba.Waige-waige na soma ko Allah yasa na gansa sai dai tsit layin yake babu
kowa ,na miƙe tsaye ina mai cewa “ to ina kuma ya tafi? Amma ai bai kai ace har
yayi nisa ba” sai kuma na maida dubana ga ƙasa inda sawun takalminsa ya fito raɗam
har da wasu harufa,kamar wata zarariya haka na soma bin sawun takun takalmin ina
tafe ina mamaki har na zo hanyar fita gari.Sai kuma na yi tsaye ba tare da na ƙara
taku ɗaya ba,na ce “ cab! Ashe ba ɗan ƙauyen nan ba ne ai wannan da gani ma sai a
babban birni” sai kuma na juya zan koma,abin mamaki sai na ga nisan komawa can gida
ba kamar tafiyar ba.Sai ma a lokacin na yi da na sanin abin da na yi don da wuya
har zuwa wannan lokaci ace Mama ba ta neme ni ba.Na kwashe sama da minti talatin
ina tafiya kafin na isa gida,sai na tarar Mama ba ta nan sosai na ji daɗin haka
kawai na shige ɗaki tare da kwantawa saboda muguwar gajiyar da na ji ta saukar min.

A firgice na farka jin sautin muryar Mama tana zagina tare da jefo min tambayar da
ta hantsila hanjin cikina “ ina abincin da na ce ki yi kafin na dawo?”
Ido na shiga zarowa saboda ni na kasa tuna lokacin da muka yi da ita na yi
girki,ga ƴan makaranta kuma sun yi tsaye sun zubo min ido da alamu sun kwaso yunwa.
“ Don ubanki ba magana nake yi miki ba? Ina dambun da na ce ki yi?” Mama ta faɗa
tana zuba min dundu a baya,cikin azaba na ce “ yana madafa cikin tukunya” a yadda
na yi maganar cikin haƙiƙanin gaskiya ƙila shi ya saka Mama fita,ni kuwa da na san
ban yi komai ba sai na ƙara tsurewa na zauna zaman jiran ta dawo na karɓi hukunci.

“ Ke Ayo kika ce ba ta girka komai ba,je ki madafa ki zuba kan babban kwano a ci
gaba ɗaya” Mama ta faɗa bayan ta dawo ɗakin.Sam ban yarda da abin da ta ce ba sai
da Ayo ta shigo da dambu yana ƙamshi,duk suka kewaya suka soma ci suna santin yayi
daɗi.Ni kuwa ido na tsura musu tare da yin saƙo ina ta son tuna lokacin da na yi
dambun,“ Janiki ina kika samu kifi?” tambayar Mama ta katse min tunani,murya na ɗan
rawa na ce “ Abba ne ya aiko da shi”

Cike da masifa ta ce “ don baƙin hali irin naki shine kuma kika saka shi a miyar
dambu?”

“Na rage saura yana madafa” na sake sharo wata ƙarya ba tare da na san dalili ba,da
wani irin sauri Ayo ta miƙe ta je ta ɗauko Kifin nan kuma suka shiga ci ban sani ba
daɗin kifin ne ya shagaltar da su suka kasa ganewa kifi ƙwaya ɗaya sai ci suke ya
ƙi ƙare wa ko yaya.
Amma ni kam na lura da hakan,sai ya zamana tsakanin ƙaryar da nake yi tana zama
gaskiya da kuma wannan abin al'ajabi wanne ya kamata na fi jin tsoro......
[13/12 à 08:05] MRS SADAUKI: *SURUKATA*🪽🪽🪽

Na
*Chamsiya Laouali Rabo*
```{MRS SADAUKI}```✍️

*FCWA* ☀️

*SADAUKARWA Ga:*. Shamsiyya Manga, My Namecy 😊

___________________________________

03

Abu dai kamar a mafarki ya tabbata gaskiya ne duk abubuwan nan da ke faruwa.Bayan
sun ci sun ƙoshi suka ture Kifin wanda har yanzu kamar yadda Ayo ta ɗauko shi yake
ko kaɗan bai ragu ba,“ ga shi nan ki ci ba don halinki ba” cewar Mama tana watso
min mugun kallo.

Dakyar na iya ɗaga ƙafa na je na ɗauki kwanon da kifin yake ciki na fita can tsakar
gida,kasa ci na yi sai aukin tunani da na fara.

‘ To duk wannan wa ya ajiye shi? Ko dai saurayin ɗazu? To in haka ne wane ne shi?
Ko aljani?’ sai kuma na waro ido a take kuma na ji wani tsoro ya mamaye ni.
Ƙugin da cikina yayi shi ya fargar da ni da yunwar da ke ƙumshe da shi tun safe ban
ci komai ba.Haka kawai na ji ban iya cin abin da ban san waye ya ajiye shi ba.Can
madafa na kai na ajiye shi sannan na fita zuwa maƙwabta gun ƙawata Rahila,na kuwa
yi sa'a ummarta ba ta gidan don sosai ta tsani ƙawancen namu duba da yadda na zama
mujiya a cikin ƙauyen babu mai ƙaunar ya raɓe ni.

“ Laaa! Wai ke ce? Yanzu kuwa nake shirin zuwa gidanku na kai miki ɗan malele da na
yi” Rahila ta faɗa cikin fara'a.Na saki murmushi na ce “ kamar kuwa kin san tun
safe ban ci komai ba”

Nan take yanayin fuskarta ya canza ta ce “ ba ku yi abincin ba ne ko kuwa yau ma


hana miki suka yi?”

Na ce “ bani da na ci na ƙoshi na baki labari” ba ta musa ba haka miƙo min shi


cikin kwanon mai murfi,na buɗe tare da zauna wa na soma ci .

“Akwai sauran yajin ne ki ƙara min?” na tambaya,ta je ta kawo min kafin ta ce “


wane labari ne za ki bani?” ban ɓoye mata ba na labarta mata batun ɗan waken da
Mama ta hana min har zuwa aljanin saurayin yau da kuma abubuwan mamakin da suka
faru.

Rahila ta ce “ ki ce gamo kika yi da aljani na ƙwarai,kin san da cewa ita ma Asabe


ta taɓa ganin wani ɗan albarka har ya taimake ta ?”

Na waro ido na ce “ wai kuma aljani da gaske?”


Maimakon ta bani amsa sai ta canza zancen da “ jiya wai bushe-bushen mene ne aka ta
yi gidanku? Na so na leƙa amma Umma ta hana”

Nan take na ji abincin ya fita raina,na fidda hannuna tare da sunne kai.“ Mene ne
wai?” Rahila ta tambaya da sauri.
Dakyar na bata amsa da “ aure za su yi min da ɗan hajiya Luba aminiyar Mama”

“Wai Luba ƴar bori ?”


Na gyaɗa mata kai kawai,Rahila ta wani ƙara gyara zama ta ce “ cab! Wane daga ciki
to? Ai na ga duk suna da aure”

“Aliyu” na bata amsa .


“Innalillahi wa'inna ileyhi raji'un!” ta furta tare da yin shiru,sanin wannan
furicin musulmi ba su yinsa ne sai in wani mummunan abu ya faru na yi saurin ɗago
kaina na dube ta.Hawaye na gani tanƙam a idonta,hankalina sai ya ƙara tashi na
shiga tambayar ta “ Rahila lafiya?”

“Janiki har ƙiyayyar da Mama ke yi miki ta kai haka da har ta yarda ta aura miki
mahaukaci?” ta yi furicin hawaye na silalo mata.
Na daki ƙirji na ce “ mahaukaci kuma?”
Ta jinjina kai ta ce “ wane ne bai san Aliyu nada taɓin hankali ba? Tun bayan
dawowarsa daga mission ya haukace an ce wai ƙarar alburushi ce ta taɓa masa
kwanya,amma wai a hakan Mama ke son haɗa ki da shi?”

Jikina ne ya hau rawa kamar wacce aka zubawa ruwan ƙanƙara har sai da Rahila ta
riƙe ni gam,“ na shiga uku Janikiii?” ta furta cike da tashin hankali.Da sauri kuma
na ture ta tare da miƙewa tsaye ko hannu ban wanke ba na fita a guje zuwa gidanmu .

Cak na tsaya ganin Hajiya Luba zaune dirshen kan tabarma ita da Mama suna tsara
yadda bikin zai tafi har da zanen kayan katakai.
“Ke lafiya don ubanki kika wani shigo a firgice kamar mai figar ruwa?” Mama ce da
wannan furicin ,hakan ya bai wa Hajiya Luba damar ɗagowa ta dube ni.
“ Ƴata Janiki ƙaraso ki duba da kanki ki zaɓi kalar gadon da za a yi miki ” shine
abin da ta ce ,kamar mahaukaciya haka na ƙara kwasa a guje na fita a tsiyace.Gudu
nake ban tsaya ba sai da na kai bayan gari sannan na samu wuri na zauna na haɗe kai
da gwiwa na soma kuka kamar raina zai fita.

Tsawon lokaci ina a haka kafin na ji tsayuwar mutum a kaina,ban wani damu ba na ci
gaba da kukana.

“ Ke ba ki gajiya da kuka?” na tsinkayo sautin muryarsa,da wani mugun sauri na ɗago


na dube shi .Saurayin ɗazu da safe ne,yayi wanka ya sauya kaya sai baza ƙamshi
yake.

Ruwa ya miƙo min a gora ya ce “ ungo wanke fuskarki sai ki goge ta da wannan ” ya
haɗo min har da sabon hankici.Kamar wacce ya yi wa asiri haka na karɓa na buɗe
murfin gorar,ina soma wanke fuskata sai na ji duk wata damuwata ta gushe.Na lumshe
ido ina mai ci gaba da watsa ruwan da nake jin su tamkar ruwan tsarki da father na
Coci ke bamu labari.

Ina buɗe ido yanzu ma wayam ban gansa ba,“ to ko dai aljanin ne kamar yadda Rahila
ta ce?” na tambayi kaina a fili kafin na miƙe na kama hanyar gida.

Kiciɓis muka yi da Hajiya Luba a ƙofar gida,ta dubi fuskata kafin kuma ta maida
idonta ƙurrr kan hankicin hannuna.Yadda ta ƙure shi da kallo yasa ni ma na kai
dubana,sai na ga a tsakiyarsa an zana masa wani hatimin masarauta.

Da sauri na jimƙe shi ina mai cewa “ har za ki tafi?” ta sakar min murmushi ta ce “
eh ai mun gama zaɓen komai” sai kuma ta raɓa gefena ta wuce .Na bi ta da kallon
mamaki,sai na ga ta waigo muka haɗa ido da sauri na shige cikin gida.

“ Tun da kin dawo daga yawon gantalin sai ki zo ki fidda masara a ruwa ki je ki kai
niƙa,yau tuwon laushi za a yi” Mama ta faɗa tana mai ci gaba da ƙirga kuɗin
hannunta,na kuma yi imanin cewa Hajiya Luba ce ta bata.

Sai da na je can ɗaki na adana hankicina biyu har da na ɗazu kafin na zo na soma
aikin da aka sani.Bayan na fidda masarar na je na kai niƙa na dawo sannan na hura
wuta,na ɗora tukunyata sannan na soma tankaɗe garin.
Haka na yi aikin ni ɗaya ko ijin wuta babu wanda yayi min har na gama,na je na yi
wanka .

Ana kiran sallar magrib Abba ya shigo a gajiye ,ni ɗaya kawai na gaishe shi ya amsa
kafin ya ce “ ki kai min ruwan wanka”
“Toh Abba” na faɗa tare da fita na kai masa,kayan da ya cire kuma na ɗauko na fito
da su don na wanke Mama ta tsayar da ni.

“ Me za ki yi musu?”

“Wankewa zan yi” na bata amsa.


“Kin manta gobe Lahadi? To ki ajiye su zuwa gobe da safe sai ki haɗa da na yaran
duk ki wanke”

“Amma Mama gobe akwai zuwa Coci” na faɗa murya na ɗan rawa don ban son yin abun da
za ta hana ni zuwa wurin bautar Ubangiji.

“Gara da kika tuna min Kirista ta ƙwarai ai ni kin san bani sallah sai ke”
Da sauri na sunne kai saboda a duniya ina tsoron mugun kallon Mama,na gwammaci ta
dake ni a kansa.Haka ina ji ina gani na mayar da kayan,da kowa ya fara cin abinci
ni kasa ci na yi saboda tunani biyu na
[30/01 08:49] MRS SADAUKI: Sati guda currr Mama ta ɗauka tana azabtar da ni da
yunwa,ba wai ba ta bani abincin ba ne a'a sau ɗaya tal nake da damar cin abinci a
wuni a maimakon sau uku.Kuma wanda ake bani ɗin ba wani ba ne,ƙarin haushi kuma ni
ce ke girka musu abincin wani sa'in ma ita Mamar sai na yi mata nata daban saboda
juna biyun da ya bayyana gare ta mai kwaɗayi.

Yau ta kama asabar,gobe kuma ranar zuwa coci in na tuna da goben zan kai wa abin
bautar tamu kokena a ɗakinsa har wani sanyi nake ji yana ratsa ni.
Tun wuri na yi dukkan ayyukana har da wankin kayan ƴan gidan,sannan na yi musu
girki.Ina zaune gefe ina kallon su suna cin girkin rana,shinkafa da miya ce na yi
musu sai ƙamshin kifi take.

“ Ko a zuba miki tun yanzu?” Mama ta jefo min tambayar,na jinjina kai alamun eh.Sai
ta ɗauri wani ƙaramin faranti ta zuba min tare da turo shi gabana tana zagina “ don
ubanki gobe ma ki sake yi min laifi,azabar da zan yi miki sai ta fi wannan.Kuma ki
bar kallona da shegun idanun naki masu kama da na aljanun ruwa ”

Ban ce mata komai ba na ɗauki abincin na fara hannu baka hannu akushi,ko minti biyu
cikkake ban ɗauka ba na cinye kuma ban ƙoshi ba.Sai na soma kallon su Ayo da har
yanzu suke cin abinci suna hira hankali kwance,ni kuma yatsuna na soma siɗewa ina
jin hanji cikina na yin ƙugi alamun dai abincin bai ishe su ba.

Mama ta tashi ta ɗauki buta ta shiga banɗaki,da sauri Sarah ta cika hannu ta zuba
min a farantina har sau biyu.Jikina har rawa yake wurin soma ci.

“Tukunyata kika buɗa kenan?” Mama ta faɗa cike da masifa,na girgiza mata kai.Uwar
masu mugun hali ta ce“ cikin namu ta damtsa ta ƙarawa kanta”

Mama ta sa hannu ta buge farantin abincin ya juye ga ƙasa,ta dungure min kai ta ce
“ ke da baki jin kunya abincin ƙannan naki za ki ci?”

Sarah ta ce “ Mama ni fa na zuba mata na ga ba ta ƙoshi ba”

Da sauri Ayo ta ce “ ƙarya ce Mama Janiki ce ta ɗeba da kanta kin ga sawun ƙaton
hannunta ma”
Da harara Mama ta bi ni kamar idon za su faɗo kafin ta shige ɗaki,ni kuma da sauri
na kwashe abincin na je wurin pampo na wanke shinkafar.Yunwa ce ta saka ni na ci
haka nan,sai kuma na sha ruwa na fita na zauna kan dakali.

Tunanin abubuwan da Mama ke yi min na soma,hawaye suka zubo min na ce “ ban san me
zan yi don na faranta ranki ba Mama da tabbas sai na yi shi” sai kuma na goge
hawayen kafin na ci gaba da cewa “ duk kai ne ka ja min da ace ba ka kusance ta ba
da tabbas ba za a samu cikina ba,na tsane ka! Ban sonka!” na furta kamar ina gaban
shi mahaifin nawa.

Idona na ji an rufe min ta baya,na saki ɗan murmushi na ce “ Rahila ce” da sauri ta
buɗe min idon tare da dawowa gabana ta yi tsaye.
“ Kukan mene kike?”
“Babu komai daga ina kike da tsakar rana?”
“Umma ta aike ni na karɓo ɗinkunanmu,bari na nuna miki ” Rahila ta faɗa tare da
ajiye ƙatuwar ledar kan dakali ta buɗe ta soma nuna min ɗinkunansu kala uku ita da
Mamarta duk zanuwan iri ɗaya ne gwanin sha'awa.

Ban san lokacin da na ce “ kin ji daɗinki Rahila ke Umma na son ki”

Ta ce “ haba Janiki wace irin magana ce wannan? Ke ma ai Mama na son ki kawai dai
don kuna da yawa ne shi yasa kike ganin kamar tana nuna banbanci ni kuma kin ga ni
ɗaya ce kawai mace ga Umma”

Na girgiza kai na ce “ wannan bai isa yasa Mama ta ƙi ni ba,kullum tana hantara
ta.Kin ga mu bar hira nan zuciyata na ƙara ciwo”

“Ya maganar aurenki?”


Na taɓe baki na ce “ har yanzu dai Hajiya ba ta sake zuwa ba”
“Shi Aliyun ya zo?”
“A'a fa,Rahila ga Umma can ta leƙo ki je kar ta yi miki faɗa ” na faɗa ,da sauri
kuwa Rahilar ta tafi saboda in ka ga Umma na yi mata faɗa to a kaina ne kawai
kwata-kwata ba ta so ta gan mu tare.

Ni ma tashi na yi na koma gida,masarar tuwo na fidda a ruwa kafin na je ɗaki don


karɓo kuɗin niƙa.Mama tana kwance na kira sunanta,shiru ba ta amsa ba sai a na
biyun ta tashi da ta yi min wata uwar tsawa har sai da na firgita.

“Na ce mene?”
“Kuɗin niƙa” na bata amsa.
“Saboda kuɗin niƙa sai ki tashe ni ina bacci? ”
“Ki yi haƙuri ban san bacci kike ba” na faɗa tare da fita waje,Ayo wacce suke
exercices ita da sauran ta tuntsire da dariya kafin ta yi min gwalo sai ta miƙe ta
shiga ɗaki.

Babu jimawa ta fito tare da cillo min kuɗin niƙan,na duƙa na ɗauka tare da zuwa na
ɗauki robar masarar na fice.Ina isa mashin na tarar da layi,na ajiye nawa kafin na
koma can nesa da mutane na zaune.Idona suka ciko da hawaye,tunanin shan maganin
ɓera ya zo min a kwanya na mutu kowa ya huta.

“In kin gama kukan ungo ki ci” na ji muryarsa kamar daga sama,na ɗaga na dube shi
kafin na dubi abin da yake miƙo min.A take yawuna ya tsinke,hannu na rawa na karɓa
ba tare da jira ba na soma ci.
Ya ja ajiyar zuciya tare da zama kusa da ni,bai ce min komai ba har sai da na ci
rabin abin da ya kawo min wanda ban san taƙamaimai mene ne ba amma a tsakiyar akwai
niƙaƙen nama.
Gorar ruwa ya miƙo min na karɓa na sha,na yi ajiyar zuciya tare da dubansa cikin
ido.

“ Shikenan sai kika gudu kika bar ni?” ya faɗa .


Na sunne kai kafin na ce “ da gaske wannan shi ne tarihina?”
Ya saki murmushi mai sauti ya ce “ eh sosai”
“Amma kai ya aka yi ka sani?”
“Saboda ba ki san ni ba shi yasa har kika yi wannan tambayar,amma ni da nake yarima
mai jiran gado jinin masarauta ai wannan ba abin mamaki ba ne?”

“Kenan tsafi kake?” na samu kaina da tambaya.Bai ce komai ba ya miƙe tsaye,“ ina za
ka je ?”
“Zan koma gida mana” kafin na kai ga cewa komai mai yin niƙa ya kira sunana na
waigawa don na amsa masa kawai ban farga ba Prince Mahadi ya ɓace.
Niƙana na je na ɗauka tare da biya sannan na wuce gida,ragowar abincin da ya bani
sai na kaiwa Natasha ta karɓa cike da murna ta shiga ɗaki.

Ina tsaka da hura wuta Mama ta shigo madafar ta yi tsaye kaina,“ gidan uban wa kika
samu gurasa da nama?”
Gabana ne ya bada wani rasss ,na dubi Mama kawai ina zarar ido ga kuma Natasha
gefenta tana cin abincin.

“Da ke nake!” ta ƙara faɗa a dake tana haɗe rai.


Murya na ɗan rawa na ce “ bani aka yi ”
“Na sani ai,uban wa ya baki shi nake son sani?”
Idona ya kawo ruwa na ce “ sadaka aka ban” ban rufe baki ba ta shure ni da ƙafa
tana cewa “ almajira ce ke ballantana a baki sadaka? Wato daga jin za a yi miki
aure shine kika fara biyar maza? ” nan ta rufe ni da duka kafin ta ce “ taso ki
biyo ni don ubanki sai na duba ki” haka na tashi ina kuka na bi bayanta har
banɗaki.

“ Ki cire pant ɗinki na duba ki” ta faɗa ,jikina ne ya ƙara ɗaukar mazari yayin da
kukan da nake ya ƙaru na buɗe baki da niyyar yi mata rantsuwa amma marin da ta
sauke min yasa na yi yadda ta ce.Na rumtse ido gam,ina jin kamar zuciyata za ta
fashe tsabar baƙin ciki yadda Mama ke duba ni har da gwada saka min yatsa ta yi
kafin ta fita ta bar ni nan cikin banɗaki ina marayan kuka.

Sai da na yi mai isata kafin na miƙe na fito,Ayo ta bi ni da kallon tausayi kafin


ta je kusa da Mama tana cewa “ Mama kin san halin Janiki ba za ta taɓa aikata abin
da kike zargi ba,kuma sam hakan da kika yi gaskiya bai dace ba”

“Ki rufe min baki ko na ci mutuncinki,so kike na zuba mata ido ta je ta lalace?”
Mama ta faɗa .

Madafa na shige ban ƙara jin abin da suka tattauna ba,haka na yi musu girkin duk
raina a dagule.Bayan na gama na ɗumama ruwa na je na yi wanka,amma duk da haka
zazzaɓin da nake guje ma sai da ya saukar min.Haka na je na shige ɗakinmu na kwanta
kan katifata na duƙunƙune na soma rawar sanyi,har aka kira sallar isha'i ban fito
ba.Ina jin muryar Natasha na cewa ga lemu da ayaba da Abba ya kawo amma ban iya
ɗaga kai na dube ta ba ballantana na karɓa,tana fita kuma Ayo ta shigo tana
tambayata.

“ Janiki ba ki sha ne?” dakyar na buɗe fuskata na ce “ banda lafiya ” sai ta matso
kusa da ni ta zo ta ɗora hannunta kan wuyana kafin ta fita.Babu jimawa shi ma Abba
ya shigo kafin ya ce na tashi ya bani magani.Haka ya ɗebo ruwa a kofi ya bani na
sha cike da tausaya wa ,sai dai kamar ma an ƙara wutar ciwon sai abin ya ƙara
ƙamari.Da gudu na fita na soma kelaya amai kamar raina zai fita,na zube nan cikin
rumfa ina jan numfashi.

Ina jin Mama na masifar ita dai ba da kuɗinta za a kai ni asibiti ba,amma a haka
Abba ya fito yasa na wanke baki ya kai ni asibiti.Ina tsoron allura hakan yasa sai
da ya riƙe ni sannan aka yi min,bayan mun dawo ne na samu na ci ayabar sai na
kwanta na lumshe ido babu jimawa bacci ya ɗauke ni.

Washegari na yi ranar tashi,ko da na farka har sun share ɗakuna da kuma tsakar
gida.Girkin ma sun ɗora,haka na je na gaishe da Mama da Abba shi kaɗai ya amsa ita
kuma banda saƙon mugun kallo babu abin da ta yi min.

“ Munafuka yanzu da aka gama aikin gida ai ga shi can ta fito,kuma wallahi ba za ki
je coci ba gida za ki zauna” na tsinkayo furicin Mama ina ƙoƙarin shiga
banɗaki.Daga nan ina jin yadda Abba ke cewa “ daga yau ba ta yi aikin ba shikenan
ta zama munafuka? To nan gaba ayyukan gidan raba su za a yi ita da sauran danginta
su rinƙa yi a tare,wankin kaya kuma kowa ya wanke nasa”
Ina jin Ayo na cewa “ Abba mu da muke zuwa makaranta”
“Ai ba ku yin ta maraice sabka guda kuke yi,don haka in ta yi aikin safe ku sai ku
yi na maraice ke da Sarah.Ita ma da zarar an bani kuɗina zan mayar da ita
makarantar ta ci gaba da karatunta”

“Auren fa?” wannan karon Mama ce ta yi maganar.


“Aure ai bai hana karatu”
“Amma dai ka san yanzu ta kusa shekara goma da barin makaranta ko? To wane aji za a
saka ta?”
“Daga inda ta tsaya za ta ci gaba,ai shi karatu bai da girma ko ke yanzu kika ce
kina son komawa sai na mayar da ke” Abba ya faɗa cikin tsokana.

Daidai nan na fito daga banɗaki sai na ga Mama na murmushi muna haɗa ido kuma ta
gimtse fuska tare da kawar da kai.Ni kuwa ji na yi kamar na je na rungume Abba
tsabar farin ciki,dama can mugun hali na Mama yasa na bar zuwa makaranta kawai don
na kula da su Ayo ita kuma ta fice wajen kasuwancinta wanda a ƙarshe jarin ya karye
ta zauna gida.

Abincin kari muka ci,yau na ci na ƙoshi saboda a gaban Abba ne.Bayan haka aka soma
shirin zuwa Coci ni ma na shirya kuwa sai dai yau ba kaya iri ɗaya muka saka ba
saboda banda irinsu su da Mama sai suka yi anko.
Da muka fito fuskar Abba ta nuna bai ji daɗin yadda aka ware ni ba,amma sai bai ce
komai ba muka fita waje har muka shiga taxi Mama ba ta yi ƙorafin don me na biyo su
ba.
Da muka je can coci sai na hangi Momy,gudun fitina yasa na zauna a nan gaba yayin
da su kuma suka je can wurin ta.Da lokacin yin sallah da addu'a yayi haka na lumshe
ido na ta kai kokena wurin Yesu cike da yaƙini.Bayan nan aka soma gwajin
fasaha ,tambayoyi ne akan rayuwar Yesu duk wanda ya sani sai ya ɗaga hannu ya bada
amsa,yau ma kamar waccan satin na fi kowa bada amsa wanda a ƙarshe har Father ya
buƙaci na je can kan dandamali.
Lasifika ya bani tare da cewa na bada tarihin Yesu,ai kuwa haka na soma zayyanowa
har ina haɗawa da wasu baitoci.Liƙen kuɗi aka soma yi min kamar ba gobe,Sarah ta zo
tana tattare min har na kammala shi ma Father sai da ya bani kyauta ta musamman
tare kuma da yin selfie da ni.

Bayan an tashi dukkan kuɗin da na samu sai na miƙawa Abba ,ina ganin Mama kamar ta
fashe da alamu ta ji haushin haka.Da muka isa gida kuwa Abba ya sake jaddada
alƙawarinsa na mayar da ni makaranta,a ranar ya sayo min uniform da kuma Books da
duk abin da zan buƙata.

Washegari sai da na yi aikin da na saba yi kafin na yi wanka na shirya.Mama dai sai


cika take tana batsewa amma wannan bai hana Abba kai ni makaranta ba,duk da ina da
shekaru dayawa hakan bai dame ni ba musamman da na ga akwai wanda suka kai ni da
girman jiki.Ina da ilimina dama,hakan yasa sosai nake fahimtar abin da ake koyawa
wasu kuma dama tuni Sarah ta koya min su.Kamar a mafarki nake jin kaina haka na yi
shawagi a filin makarantar da muka fito shan iska,abinci ma kasa ci na yi saboda
shauƙi har muka taso na nufo gida.

Ina shigowa Mama ta ce “ sai ki ɗauki cefane ki ɗora girki tun da baƙin ciki ya
rufe miki ido sai da kika koma makarantar” ban ce mata komai ba na ɗauki cefanen
sai da na cire uniform na je na hura wuta ,babu jimawa na haɗa jalob ɗin taliya.Na
sauke tukunya na shiga wanka,bayan na fito na ɗauki kasona wanda Mama ta zuba min
na ci na wanke hannu ba don na ƙoshi ba.Amma na share tare da ɗauko kayan makaranta
na soma dubawa,sallamar Hajiya Luba ta saka gabana faɗuwa.Kamar yadda na yi tunanin
kuwa zancen auren ne ya ƙara kawo ta inda take shaidawa Mama ranar juma'a za kawo
lefe kenan sai ta sanar da dangi waɗanda za su tarbi kaya.Tun kafin ta fita kuwa
Mama ta soma kiran wayar na kusa da ita tana sanar da su za a kawo lefen Janiki,har
wani murmushi take tana nuna tsantsar farin ciki wanda ni kuma tuni zuciyata ta
aminta Mama ba za ta taɓa yin farin cikin akan abin da zan amfani da shi ba sai dai
in wanda zai cutar da Ni ne.....
[19/12 à 04:41] MRS SADAUKI: *SURUKATA*🪽🪽🪽

Na
*Chamsiya Laouali Rabo*
```{MRS SADAUKI}```✍️

*FCWA* ☀️

*SADAUKARWA Ga:*. Shamsiyya Manga, My Namecy 😊

___________________________________

06

Shirye-shiryen kawo lefena bai sa na ƙi zuwa makaranta ba,sai dai sam na kasa
nutsuwa na yi karatun yadda ya kamata.Tsorona guda shine kar bayan auren mijin da
za a aura min ya hana ni karatu, wannan na samu Abba na kai masa kokena ya kuma
alƙarwanta min abu ne da ba zai taɓa faruwa ba.

Ranar juma'a ce suka tsayar don kawo lefe,yau ta kama Alhamis tuni kuwa dangin Mama
sun cika gidan sai gyaran kayan da za a yi miya da su gobe suke.Abin da ya fi ban
mamaki kuwa bai fi yadda na ga ana jiƙon ruwan lalle ba,wanda a al'adar garinmu
ranar da aka ɗaura aure kawai ake yi wa amarya wanka da su.Amma sai na yi shiru na
ja bakina,ina rakuɓe na kasa cin komai sai ga Rahila ta shigo.Kusa da ni ta
zauna,kamar yadda ba na farin ciki da wannan auren ita ma haka.

“ Ashe har da ɗaurin duk za a yi a goben?” Rahila ta faɗa ,sai na yi rau-rau da ido
amma na kasa cewa komai yayin da ita kuma ta ci gaba da cewa “ an ce gobe bayan
sallar juma'a za a ɗaura a masallaci,irin na shari'ar Muslunci za a yi tun da wai
mahaifinki ma musulmi ne” sai a lokacin na lumshe ido kafin na maimaita kalmar “
musulmi?” cikin wata irin murya Rahila ta ce “ eh wai! Kenan Abba ba shi ya haife
ki ba?” na buɗe idona hawaye na masu surnano min na dubi Rahila da kyau na ce “ ni
ma ban sani ba,ƙila hakan ne.Amma ke wa ya faɗa miki?”

“Umma na ji suna yin hirar ita da ƙanwar Hajiya Luba ” ta bani amsa,sai na sunne
kai ina wani irin huci.“Mahaifinki Balarabe ne wai,kuma fari ne tasss kamar ke,sai
yanzu ni ma nace ai sai larabawa irin wannan gashi naki tubarkallah ”

“ Kaina yana ciwo Rahila ki taimaka min da magani” na furta tare da yin kwanciya.
“To bari na je na siyo” tana fita na je na buɗe jakar kayana na ɗauko hankicin da
Prince Mahadi ya bani na soma goge hawaye da shi ina shaƙar ƙamshinsa.Ba ta wani
jima ba ta dawo ta kawo min maganin,na karɓa na sha sai kuma duk muka yi shiru.

Mama ta shigo ta dube ni kafin ta ce “ Rahila ko kuna da buƙatar yin wani ɗan
shagali ne?”

“A'a Mama” ta bata amsa.


“To ki yi mata ko dilka ne kafin gobe a yi mata lalle,kitso dai kam sai dai ta
zauna da gashinta don babu ƴar wahalar da za ta kitse mata wannan tulin gashin”
Mama ta faɗa tare da jefo wata baƙar leda.Rahila ta ɗauka tare da buɗewa sai ta
kalle ni kafin ta ce “ kayan gyaran jiki ne,bari na haɗa sai ki shafa a dukkan
jikinki” kanzil ban ce mata ba har ta ɗauko wani ƙaramin kwano ta haɗa kayan sai da
suka yi kamar minti goma kafin ta matsa min na tashi na shafa.

Wani tsohon zanena na ɗaura zuwa ƙirji kafin Rahila ta soma shafa min dilkan a kaf
jikina.Sai da na yi kusan awa ɗaya kafin ta je ta kai min ruwan wanka,dakyar na iya
fita saboda idon mutane.Bayan na fito daga wanka haka suka ta yaba yadda na ƙara
kyau,ita kanta Rahila haka ta yi tsaye tana kallona kafin ta taɓe baki ta ce “
wannan ɗan tsamin ran ko an yi dilkan ma ai ga banza”

“In ma dai iya tsamin ran ne kawai da sauƙi,in ɗayar maganar ba ta tabbata ba” na
faɗa kamar zan yi kuka.Rahila ta ja numfashi kafin ta ce “ to da yake an ce iya
ƙarar alburushi ne ya taɓa masa ƙwaƙwalwa,ƙila haukan ba yadda muke tunani ne ba”

“Sani dai sai Allah ” na faɗa kafin mu soma yin hira jefi-jefi.Da Rahila ta tafi
gida sai na ji kaɗaici ya ƙaru amma haka na daure,sai wuraren magrib su Ayo suka
shigo gidan ashe wurin kitso da lalle suka je .Abin da na fahimta hatta su sun san
gobe ake ɗaura min aure amma ni banda darajar da za a sanar da ni.

Natasha ta zo ta faɗa jikina tana nuna min kitson da aka yi mata har da
duwatsu,yadda take murna da nishaɗi sai na ji sanyi a raina.

“Hum! Sai wani murmushi take kamar wani auren ƙwarai” Ayo ta faɗa wacce ita ma ta
yi kitson da lalle,na ɗaga kai na dube ta kawai ban ce mata komai ba.Sai ta ja
tsuki ta fita,Sarah ta matso tana cewa “ ki bar kula ta,so take ta ɓata miki daren
aurenki ki kwana da baƙin ciki”

“Mu ga kitson naki ke” na faɗa na yi kamar ban ji me ta ce ba,ta cire hullar kanta
na gani.Da na ga kitson sai na ji ina sha'awar ganin gashina a kitse sai dai kuma
na yi saurin cire hakan a raina sanin abu ne da ba zai yiyu ba,rabona da kitso tun
ina ƙarama shi ma dunƙule biyu ne Mama ke yi min sai ta yi ƴan tsoraye a sama.
Ina nan zaune aka kawo min abinci har da ruwan da zan sha,na tsurawa abincin ido
ina kallo yau ce rana ta farko da aka taɓa yi min wannan gatan sai na saki ɗan
murmushi tare da jawo kwanon na soma ci .Ina tuna gobe ne fa aurena sai na ji ya
fita raina ba don ban jin yunwa ba sai don fargaba.Ƙawayen Mama da da danginta na
ta ci gaba da yin hidima kafin ɗaya daga ciki ta kawo min wani tsimi ya fi kalar
biyar,ban san na mene ne ba amma dai na yi biyayya na sha sauran kuma ta miƙa min
ta ce na dinga sha har ya ƙare sai kuma wasu ƙullinka gari da kwalin madara su ma
ta faɗa min yadda zan sha,ɗaya ne ta ware daga cikinsu ta ce “ wannan dole sai
bayan sallar magrib za ki sha” kai kawai na gyaɗa tare da amsa.
Bayan fitarta ne na jawo sabuwar ƴar ƙaramar trollyn da na ajiiye domin saka
abubuwana,na zube duk magungunan sannan na kwanta ina ta ci gaba da wahalar da
kwanyata da tunani iri-iri.Duk gari yayi tsit ba ka jin sautin komai sai na
karnuka,tuni kowa ya samu wuri ya kwanta amma ni sam bacci ya ƙauracewa idona.Haka
na yi ta juyi ina jin kamar na tashi na fita amma sai na haƙura na ci gaba da
bulaye a tunani a haka ban san lokacin da bacci ya ɗauke ni ba.
Washegari hayaniyar mutane ce ta tashe ni tun asubah,kasancewar akwai waɗanda suka
kwana gidanmu akwai kuma musulmi daga cikinsu.Daga inda nake kwance nake kallon
yadda wata ke yin sallah cike da nutsuwa tana karanto wasu abubuwa da ban san na
mene ne ba,har ta kammala ina kallon ta .Na ja ajiyar zuciya,ina sha'awar musulunci
suna burge ni musamman in sun yi shigarsu ko ina a rufe.

“Ki tashi ki yi wanka,ki shafa dilka sannan kuma ki turare jikinki da wannan kafin
mai lalle ta zo” Mama ta faɗa cike da sanyin murya,na dube ta sai na ga duk ta yi
wani iri amma ban tambaye ta dalili ba na tashi na yi yadda ta ce .

Ko da na yi wanka na biyu tuni wacce za ta yi min lalle ta zo,doguwar riga na saka


na zo na zauna kan tabarma kafin a soma sai da aka bani kunu mai zafi na sha.

Kusan awa huɗu ana yi min lallen kafin a ida, jefi-jefi muna taɓa hira da mai
lallen har muka yi ɗan sabo.
Wuraren ƙarfe ɗaya na rana Abba da abokansa tuni sun taru da kuma dangi Mama
maza.Tun a lokacin na soma jin gabana na faɗuwa,ina jin ƙarar cirawar motoci na
sunne kai ina jin kamar zuciyata za ta fasa allon ƙirjina ta faɗo.Kamar minti
talatin haka sai kuma ga su sun dawo ,wani maroƙi kuwa ya soma shela “ An ɗaura
aure ya ɗaru,Aliyu Jafar ya zama mijin Janiki Al Haris ”

Duk da ina cikin tashin hankali bai hana ni maimaita sunan ‘ Al Haris ’ a zuciyata
ba,wato sunan mahaifina kenan,don dai shi Abba sunansa ba haka yake ba .

Mata biyu ne suka ja ni zuwa banɗaki,kan wata kujerar katako na zauna bayan na cire
doguwar rigar jikina kamar yadda suka ce.Haka suka yi min wanka da ruwan lalle,sai
a lokacin kuma aka wanke min sumar kaina tasss har da saka min turare.Sai waƙe-waƙe
suke har aka gama,sabbin kaya aka saka min haka ma takalmi sannan aka luluɓa min
wata dara sabuwa dal aka fito da ni sai guɗa ake ta ko ina.

Ɗakin Mama aka kai ni har kan gadonta,wanda yau ne kawai zan ce na zauna shi.Banda
kuka babu abin da nake yi,yayin da ƴan uwanta ke yi min nasiha gefe guda kuma Mama
ce hakimce cikin shigar sabbin k
[30/01 08:49] MRS SADAUKI: Free 08

Wani irin abu ne na soma ji yana ratsa ruhina yana shiga,tamkar wacce aka juye wa
tunani na wani ɗan lokaci haka na jin kwanyata ta yi wani lummm tare kuma da yin
wani sauti kamar an buga ƙwai ga dutse.

Na ware idona a hankali kan SURUKATA wacce take yi min gizo kamar mutum kamar wata
halitta.

“ Ƴata Janiki ?” ta kira sunana cikin wani sauti tamkar mai yin raɗa.

Sam ban motsa bakina ba,amma tabbas na ji a jikina na amsa da “ da na'am Mama” sai
dai sam wannan ba furicin bakina ba ne,ƙila ruhina!

“Tashi ki je ki kwanta na san kin gaji,Aliyu yi mata rakiya zuwa ɗaki” ta faɗa tana
wani murmushi .

Ya amsa da “ to Hajiya Mama” kafin ya miƙe ya ɗauke ni cak ya ɗora kan kafaɗa,sai
ya zamana kaina ya sunne ƙasa yana reto.Idona ne suka soma nuna min wasu abubuwan
da ke luluɓe a ɓoye a ƙarƙashin jan capet ɗin falon cin abinci,sai dai na kasa
tantance na mene ne abu ɗaya na riƙe shine an ƙawata da wurin da jini.

A hankali Aliyu ya kwantar da ni kan bed ɗin,tamkar wata jaririya sabuwar haihuwa
haka nake lumshe ido ina kuma ɗan buɗe su da zumar tantance wacce duniya nake sai
dai sam na kasa .
Wani bacci mai kamar ido biyu ne na soma yi,gani nan ina gudu cikin daji yayin da
wasu mutane masu rabi mutum rabi doki na take min baya a tsiyaci.Sosai nake gudu
ina waiwayen su,suna dab da damƙo ni Prince Mahadi yayi min iyaka da su ta hanyar
diro wa daga sama kamar wani aljani.A nan take kuma suka yi baya suka gudu,yayin da
shi kuma ya jawo ni ya haɗe ni da ƙirjinsa.

Numfashi na yi ta saukewa saboda gudun fanfalaƙin da na yi,ya hura iska kan fuskata
kafin ya matso da tasa fuskar dab da tawa kamar zai sumbace ni sai ya min raɗa a
kunne “ ki tsaya ki lura da kyau,sannan ki kula da kanki” yana gama faɗa min haka
na farka ina haƙi.Abun mamaki har zuwa yanzu ina jin wannan yanayin in mutum yayi
gudu,maƙoshina ya bushe ƙamas .Na diro daga gadon,ina fitowa falo na yi kiciɓis da
Hajiya Luba.

“Har kin tashi ? Ga ruwa na kawo miki ” ta faɗa cike da kulawa,hannuna har rawa
yake na karɓi kofin na shanye ruwan tass ta ƙara tsiyaya min wasu na shanye,sai da
na yi kofi huɗu kawai ƙishin ya gushe.

“ Halan kin kwanta da ƙishi ne? Ko kuma mafarkin shan ruwa kika yi?” Hajiya Luba ta
yi min tambayar tana wani kafe ni da ido.
Mafarkin da na yi tsaf ya dawo min a kai,amma sai na zaɓi na ɓoye mata na ce “
dama...dama ina da yawan shan ruwa ne”

“Ok to ki kula sosai ba kowane ruwa ne ke maganin ƙishi ba”

“Me kike nufi Hajiya?”

“Babu komai,je ki yi wanka ki fito ki ɗora girkin rana” ta faɗa tare da ficewa.

Can ciki na koma na shiga toilet,bokiti na ajiye tare da buɗe ƙaramin pampo sai na
ɗauki soson wanka na zuba sabulu na soma cuɗa jikina.Ina saɓa fuskata da sabulu sai
na ji tamkar wani na kallona,da sauri na sa ruwa na wanke fuskar ina gwalar
ido.Babu kowa kawai tunanina ne ya bani hakan.A gaggauce na ida na fito,cikin
sabbin kayana na lefe na zaɓi doguwar rigar atamfa na saka.Tunani na soma a kan
abin da ya rage a ɗakin nan amma sam na kasa tunawa,trollyn da aka zuba min kayan
kwalliya na buɗe na shafa mai da turare kafin na fita can kitchen.

Tsaye na yi ina kallon uwar garar da ke cike da store ,ina mamakin duk me ake yi da
su har haka kamar mai wani gidan marayu.Ban san me zan dafa ba,kawai sai na yanke
shawarar bari na je na tambayi Hajiya .

Yin sallama ba ta cikin tabi'ata,wannan yasa yanzu ma ina isa ɗakinta kawai na
kutsa kai.Kusan daskarewa na yi saboda tarar da Hajiya da na yi zaune kan wani
tsumma ,kan kafaɗarta kuwa wani tsuntsu ne manyan ido jajaye .

Na ɗan ja da baya da nufin fita,amma sai na ga tsuntsun ya buɗe baki yana magana
amma muryar Hajiya Luba ce ke fita.

“Ƴata Janiki,matso mana ki zauna a gefena” ta faɗa .

Jikina ya ɗau kyarma,na ce “ dama abin da za a dafa na zo nem...” ban ida kai
ƙarshen maganar ba wannan tsuntsu ya tashi sama bai dira ko ina ba sai tsakiyar
kaina.Daga nan kuma ban ƙara sanin abin da ya faru ba sai tashi na yi na gan ni
kwance kan gadano,duk yadda na so tuna abubuwan da suka faru kuma na kasa.Abu guda
na riƙe na je kitchen zan yi girki amma kuma ban yi ba.

Aka buɗo labule,Aliyu ne ya shigo fuskarsa kamar kullum a murtuƙe.Kakin sojansa ya


soma cirewa ni kuma na zuba masa ido ina kallo.A siffa ga namiji har iya namiji sai
dai raggo ne a shimfiɗa,ga kuma fitsarin kwance.
Na shagala sosai a kallonsa sam ban ga lokacin da ya zo gabana yayi tsaye ba,sai
saukar muryasa da na ji “ ke ba ki san ki gaida mutane ba ?”

“Ka yi haƙuri” na faɗa da sauri,ya ja tsuki kafin ya shiga toilet.Bayan ya fito ne


yake cewa “ Hajiya Mama ta ce bayan fitata kin zame jiki kin faɗi a kitchen,shin
dama kina da cutar farfaɗiya ne?”

Shiru na yi ina tunanin ‘ to yaushe hakan ya faru ban sani ba? ’

“Ta ya kuwa za ki sani tun da hankalinki ya gushe” ya bani amsar tambayar da na yi


wa kaina a zuci,cike da mamaki na ce “ ni fa ban yi magana ba” cikin ido ya kalle
ni kafin kuma ya juya ya soma kimtsa wa .

Na dafe kai ina jin can ƙasan zuciyata kamar akwai abin da ba normal ba,amma sam an
ƙi bani damar yin tunani ballantana ma na san gaskiyar abin da ke faru.

Daga can bakin ƙofa Binta ta yi sallama,da sauri na tashi na fita.Ta saki ɗan
murmushi kafin ta ce “ ku fito lokacin cin abincin dare yayi”

“To ga mu nan” na faɗa tare kuma da zancen ‘ kenan har dare yayi?’

“Mu je” na ji muryarsa tare da wani jan hannuna kamar wata ƙaramar yarinya.
Muna fitowa sai na ga duhun magrib ne kawai ya keto amma kamar wasu kaji wai
abincin dare za a ci.
Har muka shiga falon cin abinci bai saki hannuna ba,wannan karon kusa da Hajiya
Luba ya zaunar da ni shi kuma ya zauna gefena sai ya zamana sun saka ni tsakiya.

Da ido kawai Hajiya Luba ta dube ni amma abun mamaki sai na ji sautin muryarta
tamkar da baki ne ta yi maganar.
“Ki buɗe kwanon abincin ki bai wa kowa umarnin ci” shine abin da idon nata suka
faɗa min.

A hankali na kai hannuna tare da buɗe ƙaton murfin,nan tururi da ƙamshin naman kaji
ya cika wurin da kuma na wainar shinkafa.Na aro murmushi na yaɓawa fuskata mai cike
da mamaki na ce “ kowa ya ci ya ji dadaɗan girkin da na yi mana,fatan za ku ji
daɗinsa sosai”

Duk suka yi murmushi kuwa kafin a soma ci,ni ma cike da zumuɗi na soma ci saboda
yunwa da na kwaso.Bayan mun gama ci Hajiya Luba ta ƙara bani wani umarnin na kawo
jus,haka na miƙe na fita zuwa ɗakinta.

Da na shiga ɗakin duhu ne da shi ɗif,sai dai abun mamaki duhun bai hana ni ganin
komai na ciki ba tamkar safiya.Ban wani damu ba tun da ni dai burina shine na ɗauko
abin da aka aiko ni don shi,wannan yasa jus ɗin kawai na ɗauka na koma can haka na
rarraba wa kowa kafin na koma wurina na zauna na sha.

Muna gama sha aka kira sallah,sai duk suka fita wannan karon har da Aliyu.Ni kuwa
tamkar wacce aka riƙewa mazaunai haka nake ji sam ban yi ƙoƙarin tashi ba ma.

“Ungo ki sha” Hajiya Luba ta faɗa tana miƙo min kofin nan na ɗazu,na karɓa na
shanye tass kamar jira kuwa ake sai na soma jin duk abubuwan da ni ɗazu sai dai na
yanzu na ga wani banbanci shine yadda kawai na kwanta shanɗam kam capet.

Ba bacci nake ba,haka kuma ba zan ce idona biyu ba .A takaice dai ina tsakanin
duniyoyin biyu,ina kallon lokacin da Hajiya Luba ta miƙe tsaye ta soma zagaye ni
tana faɗar wasu ɗalasimai kafin kamar almara ta soma yi wa ruhina magana.

“Fito zuwa gare ni,zo ka yi min hidima ,lokaci yayi da nake ta faman jira” ta faɗa
tare nuna tsakiyar ƙirjina,tamkar yadda ƙasa ke tsagewa haka na soma ganin gangar
jikina na buɗewa kafin wani abu mai kama da inuwa ya fito,wanda ba komai ne shi ba
sai ruhina.....

Littafina na kuɗi ne,ki ɗaure ki biya 500 Hajiya via


2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank

DM +22795045822
[24/12 à 08:16] MRS SADAUKI: My book is only 500 via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank

DM +22795045822

Free 09

Tamkar a mafarki dai ruhina ya fita daga gangar jikina ya je gaban SURUKATA ya
zube,yatsan hannunta ta tsaga nan jini ya soma tsirta haka ta soma shayar da ruhina
shi na wani lokaci kafin kuma ta basa umarnin ya je ya koma inda ya fito.
Yadda in mutum ya suma in an zuba masa ruwa yake zabura haɗi da jan numfashi da
ƙarfi,to ni ma hakan ce ta faru da ni bayan ruhina ya dawo cikin gangar jikina.

“Ƴata Janiki kin tashi?” Hajiya Luba ta faɗa ,wacce a yanzu na gan ta zaune kusa da
ni.Kai na gyaɗa mata ba tare da na ce komai ba,don ji na yi kamar na rasa tunanina.

Ta saki murmushi ta ce “ tashi ki je ɗakinki zan aiko miki da magani domin magance
ciwonki” ba tare da na san wane ciwo take nufi ba na tashi na fita zuwa ɗakina.

A falo na tarar da Aliyu yana waya da dukkan alamu kuma da Ogansa ne duba da yadda
yake magana cikin ladabi.Har zan wuce bedroom amma yayi min alama da hannu a kan na
je.Sam jikina bai da wani ƙwari tamkar zan faɗi haka na je na tsaya a gabansa,ya
jawo ni tare da ɗora ni kan cinyarsa.Yana waya yana yawo da hannunsa a jikina can
ya ajiye kafin ya maido hankalinsa gare ni,wani irin kallo yake min kamar mai son
ya isar min da wani saƙo.Ina ganin ya matso fuskarsa gare ni na yi saurin lumshe
ido,ai kuwa abin da na yi tsammani ne.Sumbata na yayi ta yi haɗi da romance ,ba
tare da neman izini ba kwatsam aka shigo ɗakin.Da sauri na zabura na tashi ina raba
ido,ita kuwa Hajiya Luba kicin-kicin ta yi da rai tana wani kallonmu kamar ta ritsa
kwarto.

“Hajiya Mama ko da abin da kike buƙata?” Aliyu ya faɗa a kunyace ba tare da ya


tashi ba.
“Sai in ina buƙatar wani abu zan shigo ɗakinka Aliyu? Tun yaushe ka yi min iyaka da
shigowa ba tare da na sani ba?” Hajiya Luba ta faɗa ,amon muryarta na fitar da
hucin baƙin ciki.

“Ki yi haƙuri Hajiya ba haka nake nufi ba,dama ai ko ba ki shigo ba yanzu zan je na
sanar da ke zan je mission jibi ” Aliyu ya faɗa .

“Ai ban ga alamun za ka je ba ɗin,ke kuma uwar me kike jira da kika yi min tsaye ko
banda ikon yin magana da ɗana sai a gabanki?” wannan karon sosai fushinta ya
fito,jikina na rawa na nufi bedroom ba tare da na ce mata komai ba.

Kan gado na zauna ina haƙi kamar wacce ta yi gudu,wani abu nake ji tamkar zan
faɗi.Dukkan jikina ya ɗauki rawa,murya na ɗan rawa na ce “ Aliyuuu!” da ƙarfi na yi
maganar ta yadda zai ji.

Ai kuwa ya shigo a guje yana cewa “ me aka yi?”

“Zan faɗi jiri nake ji” na faɗa tare da tashi tsaye ,yayi saurin tallabo
ni .Hajiya Luba ta shigo tana cewa “ dama maganinta na zo kawo mata ungo ka bata
ta sha” ta faɗa tare da miƙa masa wata kwalba,Aliyu ya zaunar ni sannan ya dangwalo
maganin da yatsansa ya saka a bakina kamar ƙyaftawar ido haka na ji komai ya dawo
normal.Na ja wata ajiyar zuciya,cike da tausaya wa Hajiya Luba ta matso kusa da ni
tana mai cewa “ ki kwanta ki huta Ƴata Janiki, Allah ya baki lafiya.Ki riƙe maganin
nan wurinki duk lokacin da kika ji wannan yanayi to ki dangwale shi da yatsa ki sha
za ki samu sauƙi”

“ Na gode sosai Mama ” na furta cike da jin daɗi.


“Aliyu ina ga ya kamata a ɗaukar wa da Janiki ƴar aiki wacce za ta kula da ita da
kuma yi mata hidima,ciwon nan nata bai son yawan motsi da zirga-zirga ”

“To Hajiya Mama ” ya furta kafin ya miƙa min kwalbar maganin.A tare suka fita shi
da ita,ni kuma na kwanta kan gadona tare da rungume kwalbar a ƙirji.

Na saki wani murmushi na ce “ wai Janiki ce za a ɗaukar wa ƴar aiki, na gode abun
bauta da ka nuna min ranar da zan yi farin ciki” sai kuma na yi shiru na koma
zancen zuci ‘ to yanzu a haka zan zauna da Aliyu ba tare da mun mori rayuwar
aurenmu ba? Ko ya san bai da lafiya? Ƙila kuma shi wannan saurin inzalin bai ɗauke
shi matsala ba don ban ga ya nuna alamun damuwa ba’ sai kuma na ji tausayin kaina.

Ina nan kwance ya shigo, trolly ya jawo ya soma zuba kayansa yana yi yana waiwayena
har ya gama ya zo yayi tsaye kai gare ni ya tsura min ido.Duk sai na ji na
tsargu,ga kuma wani tsoronsa da ya dirar min lokaci guda.

“Ki tashi ki yi wanka ki canza kayan nan zuwa na bacci ” ya faɗa yana furzar da
huci.Ba tare da na ce masa komai ba na sauko,har zan wuce amma sai ya riƙe min
tsintsiyar hannu.Wani irin kallo ya soma aiko min kafin kuma ya sakar min hannun,da
sauri na shige toilet ina mamakinsa ko me ya shiga kansa yau.
Bokiti na tara a pampo kafin na soma yin wankan,ana buɗe ƙofa na san da shi ne.Ko
juyawa ban yi ba haka na ci gaba da yin wankan a takure ina jin idonsa gare ni.Na
jawo towel zan ɗaura yayi saurin fizge shi daga hannuna,daidai kunnena ya min raɗa
“ ina so mu yi wanka tare” ban kai ga yin magana ba ya buɗe shower ruwan suka zuba
gare mu.Na ja wani numfashi saboda sanyin ruwan ina shirin guduwa ya riƙe ni gam
tare da juyo ni muna facing juna,“ mene ne?” yayi min tambayar a dake .Idona suka
kawo ruwa na ce “ ban so na jiƙa gashina” sai ya sa hannu ya cire hullata wacce ko
bacci bai raba ni da ita yayi cilli da ita.

Gashina da na laulaye na yi masa naɗin tayar mota ya warware tare da cire ribob
ɗin,ido ya waro ganin sumar kaina.Kamar wani sakarai ya soma shafa ta yana jan ta
cike da mamaki,yana tallabo fuskata na lumshe ido.

Wanka muka yi cike da salon romantic,yadda Aliyu ya tafi da ni cikin shauƙi da


tausasawa kamar ba shine na jiya ba da yayi ta yi min tsawa.Yadda ya manne ni a
ƙirjinsa yana sauke min huci a kunne shi ya fi ɗaga min hankali,kamar wata ƴar baby
haka yayi min wanka.Karon farko da na ga soyayya gun ɗa namiji don ban taɓa yin
saurayi ba,bayan ya gama yi mana wankan muka ɗaura towel har zan taka da ƙafata
amma sai ya ɗauke ni.A zuci na ce ‘ ka ga wani sabon salo’ kan bed ya shimfiɗe
ni,yana shirin warware min towel na ce “ ka rufo ƙofa”

“Na ru..fe ta ca..cccan falo ” ya faɗa muryarsa na rawa,haka kawai na ji tausayinsa


saboda tsantsar buƙatuwa da na hango cikin ƙwayar idonsa amma na san ba za a je ko
ina ba saboda bai da wani ƙarfin.

Ido kawai na lumshe tare da yin shiru ina karɓa saƙonsa,ko ta ina yake min sumba
jikinsa na yin rawa.Ɗumin hawayensa ne suka sa na buɗe idona,da dukkan alamu ya ji
takaicin yadda yanzu ma da ya so kusantata kawai komai ya tsaya cak babu biyan
buƙata.Fuskarsa na tsure ina kallo ,kyakkyawa ne shi duk da yana baƙi hakan bai
ɓoye kyawun nasa ba.Ya koma gefe tare da kai hannu ya kashe ƙwan lantarki,ɗakin sai
yayi duhu.

“Zahra!” yayi furicin ,ban amsa ba don ba haka ne sunana ba.Ya jawo ni ya maido ni
kan ƙirjinsa tare da cewa “ shine kika yi shiru?”
“Ni sunana Janiki” na faɗa .
“Ban sonsa ne shi yasa na zaɓa miki sunan Zahra shi ya fi yi miki kyau,tun da kin
ga kai tauraruwa ce”

“ Zahra na nufin tauraro?” na tambaye shi.


Ya ce “ eh mai mugun haske ma kuwa”

“Kenan ni tauraruwa ce?” na sake jefa masa tambayar.Shiru yayi kafin can ya ja
numfashi ya ce “ eh ”
“Saboda me?”

“Me yasa kika aure ni?” shi ma ya jefo mini tambayarsa.Sai na kasa cewa
komai,hasken ɗakin ya kunna kafin ya ƙara maimaita min tambayar yana kallon cikin
idona a dole na amsa masa da “ Mama ce ta ce na aure ka”

“Hajiya Mama?”
Na girgiza kai na ce “ a'a Mamana”
“Kafin su aura miki ni sun yi miki bayani kaina ba?”
“Wane bayani?”
“ Komai!” ya faɗa tare sake kashe hasken,ina jin yadda bugun zuciyarsa ke tafiya da
sauri-sauri.

A hankali na ɗan janye daga jikinsa kafin na juya masa baya,amma kamar wani ƙaramin
yaro haka ya zo ya ɗora min ƙafarsa ɗaya tare da zagaye cikina a dole dai ya mayar
da ni cikin ƙirjinsa.A haka muka yi bacci kafin lemar fitsarinsa ta tashe ni,na
janye jikina da sauri tare da kunna hasken ɗakin shi ma ya farka sai muka fara ƴar
kallon-kallon kafin kuma ya sauka ya je ya shiga toilet.Ni kuwa tsaye na yi ina
kallon gadon da yayi shaɓe-shaɓe da fitsarin,a yau maimakon takaici sai na ji
tausayinsa....
My book is only 500 via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank

DM +22795045822
[26/12 à 09:10] MRS SADAUKI: My book is only 500 via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank

DM +22795045822

Last free page 10

Zanen gadon na cire ,sai na dubi ƙofar toilet da nake ta jin ƙarar zubar ruwan
shower da alamu wanka ne yake don dole sai wankan tun da uban fitsarin nan da ya
shashaɓa min.Ganin ba zan iya jiransa har sai ya fito ba kawai na yi niyya fita
waje na ciko bokiti da ruwa na goge ledar da ke kan katifa.Ba tare da wani tunani
ba na suturta jikina kafin na je na buɗe ƙofa na fita tsakar gida.Wani irin mugun
haske ne na jar wutar mai kamar ta murhu ya min maraba,kaf tsakar gidan ya ɗauki
kalar ja yayin da sararin samaniya yayi baƙi ƙirin kamar bayan tukunya sai giza-
gizai ke gudu .

A tsorace nake kallon giza-gizan masu kamar zanen fuskokin mutane,na toshe
kunnuwana saboda wata gurɓataciyar murya da ke rera waƙa cikin wani kiɗa marar
daɗin sauti kamar ana kiɗa goge.

Baya-baya na soma da na ƙasa na darewa tana tsagewa kamar yadda in an yi girgizar


ƙasa za ka ga wuri na ɓaɓarewa.Ihu nake son yi amma tamkar wacce aka riƙewa murya
na kasa,hatta motsa ƙafafun haka na kasa gusawa saboda yadda nake jin tamkar an
ɗinke fatata da kuma ƙasa.

Wani haske ne ya tawo daga sama kamar tauraro ya hankaɗa ni na yi baya tare tashi
sama ban dira ko ina ba sai cikin ɗakina,yayin da kuma ƙofar ɗakin ta bada ƙiiii
tare da rufe kanta.

Na dafe saitin zuciyata ina jan numfashi kafin na tashi dakyar na koma bedroom,sai
na tarar tuni Aliyu ya fito daga wankan yana tsaye kan dardduma yana Sallah.Toilet
ɗin na shiga na ciko bokiti da ruwa na goge ledar tare da saka wacce ta ɓace cikin
bokitin,tun a cikin daren na wanke ta sannan na yi wanka na fito.Har yanzu yana kan
dardduma ,kayan jikina na saka sannan na shimfiɗa wani zanen gadon.Can ƙarshen gado
na hau na kwanta ,abubuwan da suka faru yanzu da na fita suka faɗo min a rai.

‘ To wannan ɗin duk na mene ne? Ko dai gamo na yi?’ sai kuma na watsar da tunanin
don banda wanda zai ban amsa.Ina nan kwance shi ma ya zo ya kwanta tare da kashe
hasken ɗakin.A tsorace na tashi na ce “ Please ka kunna haske tsoro nake ji”

“ Zo nan ” ya faɗa tare da jawo ni cikin ƙirjinsa,ido na rufe ruf ina jin zuciyata
na bugawa da ƙarfi.“ Me ya tsorata ki?” ya tambaye ni.

“Babu komai kawai ban son duhu ne” na basa amsa.


“To ko ma mene ne ba zai taɓa zuwa nan ba don cutar da ke muddin kina kusa da ni”
ya faɗa tamkar ya shiga raina ya ga abin da nake tsoro.
Lamo kawai na yi ina sauraren bugun zuciyarsa,a hankali yake dadaɓa ni alamun na yi
bacci.Na yi murmushi ina tuna can gidanmu yadda nake bacci ni ɗaya,ga shi kuma
yanzu na samu abokin kwana duk da auren ba mai moruwa ba ne amma da ɗan sassauci
kan rayuwata ta gida.

Kalamansa ne suka katse min tunani inda yake cewa,“ Zahra na san ba ki sona an aura
miki ni ne bisa dole,sannan kuma yanzu da aka kawo ki sai kika ƙara tsanata saboda
larurar da kike tarar ina da ita.Ki yi haƙuri da sannu za ki saba za ki ga kamar ma
yana ɗaya daga cikin aikin da kika fi so na wankin kayan fitsarina,abu guda na sani
kina da lada don ni mijinki ne sannan aure dukkansa bauta ce.Allah ne ya ɗora min
babu yadda na iya,ba wai zaɓina ba ne duk da farko abin ya addabi ruhina har ya
taɓa aikin da nake saboda ina tsoron yin bacci a cikin abokai na yi fitsarin
kwance.Shawarar Mama ce da nake bi nake ganin canji,ita ce ta ce min kar na damu da
duk halin da zan samu kaina Allah bai ɗorawa bawa abin da ba zai iya ɗauka
ba,sannan in na je can mission inda zan yi bacci cikin mutane na saka a raina ba
zan yi fitsarin ba,kuma kin san abun mamaki hakan take faruwa fa sosai nake jin
daɗi” ya ƙarashe maganar yana sakin murmushi mai sauti yayin da kuma yake shafa
gadon bayana.

“Amma kuma sai in ka zo nan gida ne kawai fitsarin yake dawowa?” na samu kaina da
tambayar shi.

Ya bani amsa da “ eh! Amma ko a gidan ba kullum ba ne nake yi”

“Ita kuma ɗayar matsalar fa?” na tambaya a kunyace,shiru yayi bai bani amsa ba sai
da aka ɗauki lokaci kafin ya ce “ wace matsala kenan?”

“A'a ko ɗaya ,zan yi bacci” na faɗa jin yana son raina min hankali wato fitsarin
kwance kawai ya ɗauka a matsayin matsala shi rashin kusantata da ya kasa yi ba
matsala ba.

“Zahra don Allah kar ki guje ni kin ji?” ya faɗa yana wani ranƙwafowa kamar mai
leƙen fuskata.Na turo baki gaba kafin na ce “ kar ka damu Janiki ba ta taɓa yin
farin ciki ba dama,ina tabbacin cewa sanin zan iya zama da kai suka haɗa aurenmu”
na yi furicin hawaye na surnano min.

Hasken ɗaki ya kunna tare da yin zauna ,sosai nake jin idonsa a kaina duk da na
juya masa baya.
“Ki bani labarinki” ya faɗa .
“Aliyu ba ka jin bacci ne halan?” na faɗa
[30/01 08:49] MRS SADAUKI: MAFIYA*☠️

01

‘ Lokacin da muna yara,da zarar an ce MAFIYA kawai abu guda kwanyata ke bani
ƙungiyar shan jini ce mai sa a yi kuɗi.Amma yanzu da na girma,na kuma tsinci kaina
a ciki sai na fahimci cewa MAFIYA na nufin cikar muradi.
Sunana HAROON matashi ne ni ɗan kimanin shekara talatin da takwas a duniya,maraya
na uba ,shalelen mahaifiyata.Na taso cikin matsin rayuwa ta talauci kafin kuma na
tsinci kaina cikin daula...... '

“Haroon sakatariyarka ta ce yau ba za ka fita ba ko zan san dalili?” muryar Ammy ta


katse mini ɗan taƙaitaccen tunanin zucina wanda kusan lokuta da dama nake zama haka
kawai ina bai wa kaina labarin kaina.
Na saki murmushi ina kallon sanyin idaniyata abar alfaharina,“ ban jin daɗi ne Ammy
shi yasa,amma kar ki damu ciwon kai ne kawai”

“Kamar ya kar na damu ? Ciwon kan ne kake faɗa ƙaramin abu? Jira ni ina zuwa” ta
faɗa tare da yin gaba.

Na bi ta da kallon ƙauna,Ammyna kenan uwa ta gari wacce a idonta sam ba na girma


kullum tamkar ƙaramin yaro haka take ɗauka ta.Ina nan zaune ta dawo hannunta riƙe
da wata tasa da kuma ƙaramin towel,na lumshe ido lokacin da ta soma tsoma towel ɗin
a ruwa tana matse shi sai kuma ta dinga dadanna shi a kaina.Cikin ikon Allah na ji
ciwon kan yayi sauƙi,“Ammy ya isa haka je ki huta mana ban san yaushe za ki daina
ɗawainiya da ni ba,kamar wani ƙaramin yaro dai sai ririta ni kike” na faɗa ina mai
riƙe hannunta mai ɗauke da towel ɗin.

Ta dungure mini goshi cikin faɗanta da ta saba yi min ta ce “ sai ranar da ka kawo
matar aurenka a gidan nan.Wai HAROON yaushe za ka yi aure ?”

Da sauri na miƙe ina mai cewa “ aure! Aure dai kullum shine zancenki Ammy,duka nawa
nake?”

“Yanzu na haife ka” ta bani amsar da ta saka ni dariya,sai kuma na ce “ kar ki damu
zan nemo miki suruka kafin ƙarshen shekarar nan in sha Allah!” na furta ina mamakin
furucina na ƙarshe da na ambaci sunan maƙagina,wanda a ƙalla zan kai shekaru biyar
da muka yi hannun riga ni da umarninsa.Yanzu haka ambaton sunansa sai da na ji
maƙogorona yayi min wani zafi,halshena kuwa tamkar an saka reza ne an tsaga shi.

“Allah ya nuna mini wannan babbar rana, Ubangiji yasa ina da rai albarkacin Manzon
Rahama Ya Rabb ka dubi Harunana ka basa mata ƴar aljanna mai haska duk wani duhun
gidansa” ita ce addu'ar Ammy gare ni,ban ko amsa ba na yi gaba abina.

Ina fitowa harabar tsakar gida direbana yayi saurin tashi tare da nufar motar da a
yau ita ce zan shiga.Da kansa ya buɗe mini gidan baya na zauna,sannan ya ja motar.
Hanyar babban ofis ɗina ya ɗauka amma na yi saurin dakatar da shi.“ Ka ga kai ni
wurin da zan ɗan shaƙi iska yau ban ra'ayin aiki ko kaɗan ” na faɗa don haka kawai
nake jin yau raina a dagule babu daɗi ga wani irin bugawa da zuciyata take.

Gudu yake da ni amma hankalina ba ya ga hanya na lula sosai cikin tunani,ƙiiiii ya


ja wani uban burki sai a lokacin na dubi gabana.Wata kyakkyawar budurwa na hango
tana tsallakar da yara ƴan makaranta,yayin da duk ababen hawa suka tsaya suna jiran
sai yaran sun gama wucewa.

“Yi haƙuri yalaɓai bari na canza hanya” cewar direba ,da sauri na ce “no ! Jira”
ido kawai na tsura mata yadda take ta zulumniya cikin ƙaton hijabinta ,yayin da
hannunta kuma wanda ya sha jan lalle ke faman kamo na yara.

Ido na lumshe sa'ilin da ta game dukkan hannuwanta alamun godiya ,ban san mun bar
wurin ba sai da na ji direba yana cewa “ba don Malam Zainab ba ce da ƙila mutanen
nan ba su tsaya ba sai an samu waɗanda za su ce sai sun wuce”

“Ka san ta ne dama?” na samu kaina da tambayarsa.


Yayi ƴar dariya ya ce “to wane ne zai ce bai san Malama Zainab ba,yarinyar da duk
shekara ita ce ke cin gasar musabaƙa ta duniya.Makarantar can ma gwamnati ne ya
buɗa mata ita da sunanta,yalaɓai in ka ji yadda ɗalibanta ke yin larabci kai kace
ƙyanƙyasar Saudiya ce uwa uba ita in tana yi.Zaƙin muryar.....”

“Ya isa haka juya ka mayar da ni gida” na yi saurin katse shi saboda bugun zuciyata
da na ji sai ƙara hauhawa yake.Muna isa gida ko wani burki mai kyau bai yi ba na yi
saurin fita daga motar ba tare da na jira ya buɗe min ba.

Ammy na falo ta ga na shigo a hargitse,ta yo kaina tana tambayar lafiya amma ban
bata amsa ba na haye step ina taka shi bibiyu yayin da ita kuma ta mara min baya
tana faman kiran sunana.Ina isa ɗaki kuma na rufe shi gam da key,ga ƙofar na
jingina ina sauke numfashi kafin dakyar na ƙarasa na je na zauna kan kujera ina
kallon kaina cikin baƙin madubin da shine silar canza rayuwata daga jiya zuwa yau.A
zahiri ni mutum ne complet,amma a cikin madubi ba komai ne ba face ƙwarangwal ba
tsoka saboda da kaina na sayar da ruhina ga MAFIYA.........
[26/12 à 09:33] MRS SADAUKI: *MAFIYA*

02

Karon farko kenan da na yi da na sanin shiga MAFIYA,a tsawon shekarun da na yi a


ciki na yi su ne cikin farin ciki.Hawayen takaici nake yi yayin da ƙwarangwal ɗin
da ke cikin madubi ke ƙyartata dariya,ita ƙwarangwal ɗin nan ba kowa ba ne face
Ni,inuwata ce ko kuma na ce ruɓaɓen ruhina.Daga can bakin ƙofa ina jin Ammy na buga
wa tare da kiran sunana amma na kasa tashi ,zuciyata ta yi rauni ba zan iya tsayuwa
gabanta ba na shaida mata alƙawarin da na yi mata na samo matar aure ne ya cika sai
dai kuma baƙin ruhina da farin ruhin kyakkyawar budurwar nan sam ba za su iya zama
a inuwa ɗaya ba saboda rayuwar da ta rage min ƙalilan ce.

Wayata ce ta ɗauki ruri,ina dubawa na ga sunan Oga.A dole na ɗaga,“ ka zo muna da


meeting ɗin gaggawa” shine abin da ya faɗa kafin ya kashe.

Jiki babu ƙwari na miƙe na shiga toilet na wanke fuskata na goge ta da towel sannan
na fito.A bakin ƙofa na ga Ammy idonta sun yi jawur,na sakar mata murmushi na ce “
kar fa ki damu kan ki zan nemo wata tun da wannan ɗin ta fi ƙarfina”

“Wa kenan?”

“Budurwar da na gani yanzu da muka fita,kin ga Ammy kar ki damu zan cika miki
alƙawarin da na ɗauka” ina gama faɗa na soma tafiya,ta biyo bayana har muka sauko
ƙasa sannan ta ce “ ƴar wace ce ita da har ta fi ƙarfin ka?”

“Ba kowa ba ce kawai malamar makaranta ce” na bata amsa,“ mi sunanta?”

Na juyo muna facing juna sannan na bata amsa da “ zan fita yanzu in na dawo za mu
yi maganar”

“Allah tsare ka ya maido mini kai lafiya”

Dakyar na amsa da “Amen ” .Ina fita na karɓi key ɗin mota,don in magana ta shafi
Oga ban bari a yi draving ɗina.Tuƙi nake amma idona ita suke hasko min,dakyar na
samu na kai kaina can inda muka saba meeting ɗin.

Tuni mutane sun fara taruwa,na samu wuri na zauna muka ɗan soma cacabke wa da
sauran members.Sai da kowa ya hallara sannan wurin yayi tsit,Oganmu sai a lokacin
ya miƙe ya soma jawabi.“ Kamar yadda kuka sani wannan Association ɗin namu yana da
tsari,ba a shiga kudin sirrin kowa hakan ne yasa wasu informations ɗin ba mu
samunsu kai tsaye ta yadda za mu fahimci daga ina suka fito.Sai dai sosai dakarun
bayar da kariya suke iya ƙoƙarinsu wurin ganin babu wata ƙungiya ko baƙin haure da
za su kawo mana hari.To yau ma ɗin mun samu labarin cewa wani mummunan al'amari na
tunkaro ƙungiyarmu ,kune ƴaƴanta kune kuka san yadda kuke gudanar da rayuwarku don
haka ku nutsu ku yi nazari a cikinku babu wanda ya tsokano faɗa ko kuma yayi wani
kuskure wanda bai dace da tsarin ƙungiya ba?” Oga na kawowa nan da zancensa sai duk
ya soma bin mu da ido ɗaya bayan ɗaya.

Ko kaɗan ban kawo a raina cewa malam Zainab da na soma jin ƙaunarta ita ce matsalar
da Oga ke magana a kai ba wannan yasa sam ban ma nuna damuwa ba.Har aka gama
meeting babu wanda ya ce ga wata matsala sai Oga ya sallami kowa.Har zan fita ya
tsayar da ni,sai da ya kalli tsakiyar idona kafin ya ce “ HAROON ka shekara biyar a
cikinmu”

“Ai na sani Oga” na faɗa don ban ga amfanin sanar da ni ɗin ba.

“Eh tuni ne na yi ma don kar ka shagala” ya faɗa yana ƙara yi min kallon nan da ke
sa mutum ya tsargu,shiru kawai na yi masa.Can ya ce “ kana iya tafiya” na jinjina
kai.

Bayan na fito daga can direct wani gidan shaƙatawa na tsaya Park,wuri ne da iyaye
suke kawo yaransu don shan iska da kuma buɗe ido.Karon farko da na ji sha'awar
ajiye yara,yadda suke wasa gwanin ban sha'awa sai ya sake tuna min da Malama
Zainab.Hoton fuskarta nake gani a kan fuskar duk iyayen da ke wurin,sai nake ganin
tamkar ma a nan ita ce ke kula da su.Na ɓata lokaci sosai kafin na bar wurin,ina
draving ina tunaninta har na isa gida.Cak na tsaya bakin ƙofa ganin Malama Zainab
ɗin tare da Ammy a zaune.Na girgiza kai tare da dariyar kaina a zuci na ce ‘ HAROON
ka haukace tun da har a cikin gidanku Malama Zainab kake gani ’ sai na yi gaba har
na hau step ɗin farko sai na tsinkayo muryar Ammy na cewa “ HAROON zo ku gaisa da
malamar da za ta dinga koyar da ni karatu”

Da sauri na juyo sai muka haɗa ido da ita amma ta yi saurin kawar da kai,tamkar
wani gumki haka na tsaya ina kallon ta .Sanye take cikin pink ɗin hijabi,tafin
hannunwata a waje suke ta riƙe litattafai da su.Kamar wani sakarai haka jan lallen
yatsunta ya ja ra'ayina har ban san lokacin da na taka can inda suke a zaune kan
salon ba,“ mu ga littafin da za ku soma” na faɗa tare da kai hannuna zan karɓa amma
wani azababen suraci da ban san na mene ne ba ya daki hannuna da bala'in sauri na
yi baya har ina shirin faɗuwa.

“Yi sannu mana,Malama miƙo min na basa” cewar Ammy ta karɓo littafan ta miƙo min
sai dai sam na kasa amsa saboda wani irin haske da nake ganin yayi min katanga da
littafafan.Na girgiza kai na ce “ a'a Ammy ba sai na gani ba” sai kuma na nufi step
da mugun sauri na haye can sama,ina shiga ɗaki na ƙargame shi da key ina jin wani
tsohon ilimina na baya na dawo min.A nan take a inda nake na fahimci wani abu,ina
cikin fushin Allah mai tsanani ta yadda har har littafai masu kalmomin saninsa suka
yi min tawaye suka haramta gare ni........

MRS SADAUKI ce ✍️
[26/12 à 09:33] MRS SADAUKI: *MAFIYA*☠️
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️

*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo


(MRS SADAUKI✍️)

*Lambar waya:* +22795045822

*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*


Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
_____________________

03

Duk yadda na so nuna wa zuciyata ruwa ba a sa'an kwando ba ne amma sam sai ta yi
min bore ta ƙi aminta akan muradinta.Soyayyar Malama Zainab ɗin dai ta zaɓa ,duk da
tunanina ya ƙi bata haɗin kai wannan bai canza zane ba.Dakyar na cira ƙafafuna zuwa
toilet,kayana na cire kafin na shiga ƙarƙashin shower na buɗe pampon duka.Ruwa suka
soma jiƙa ni,sanyinsu na rantsa sumar kaina ina jin wata ƴar nutsuwa na sauko
min.Rabon da na ji yanayin buƙatar mace har na manta,zan iya kai wata biyu haka ban
yi lalata da ƴar kowa ba amma yau soyayyar Malama Zainab ta motso mini da tsimin.

Pampon na kashe ba tare da na yi wankan sabulu ba,towel na ɗaura a ƙugu kafin na


fito ina tsane gashina da ɗan ƙarami.Bayan na gama na saka ƙananun kaya na fashe
jikina da turare kafin na sauko ƙasa ,sai na tarar tuni ta tafi sai Ammy kaɗai
zaune a falo tana duba littafi.

Na ƙaƙalo murmushin dole na ce “ Barka da yamma uwa ta gari”

Ta ɗago ta ɗan dube ni na wani lokaci kafin ta ce,“ meke damunka HAROON ? Ina ce
ganin Malama Zainab zai sa ka nutsu amma sai na ga saɓanin haka”

Kusa da ita na zauna kafin na ce “ wai aka yi kika nemo ta? Ko dama kin san ta ne?”

“To wane ne bai san Malama Zainab ba duk Yamai? Na san ta mana har gidan marayun da
take kula da shi ina zuwa duk ƙarshen wata”

Na ɗan saki murmushi,taimakon al'umma yana ɗaya daga cikin halin kirki na Ammy.Duk
wata ƙungiya mai kula da marayu sun san ta sannan ba wata ɓoyayya ba ce a garin
Yamai don kusan duk wani abu da ya shafi Islam sai an kawo mata takardar gayyata
irin taron ci gaban addini da sauransu,amma ko kaɗan ban yi tunanin ta san Malama
Zainab ɗin ba.

“Bayan fitarka ne na tambayi direba sai yake sanar da ni,shine fa muka je har can
inda take na nemi alfarmar ta dinga zuwa tana min karatu a gida ” Ammy ta faɗa
murmushi kan fuskarta.

Ita ɗin tana da son Addini sai dai ba tada yawan karatu,kuma samun ilimi na ɗaya
daga cikin burinta sai dai ta karaya ne tana ganin ai shekarunta sun ja.

“To Ammy sai ku yi ta karatun,yaushe da yaushe za ta zo?”

“Duk bayan sallar magrib in sha Allah,zan dinga aika direba ya ɗauko ta in kuma ta
gama sai ya mayar da ita”
“Amma iyayenta sun bari?”

“Eh sosai,ai a gabansu na nemi alfarmar shi fa mahaifinta gani yayi ma kamar zunubi
ne ƙin yarda da abin da na roƙe su ɗin.Iyayenta ƴan mutumci ne kamar dai ita” ta
ƙarashe zancen fuskarta na canzawa,da sauri na kamo hannunta ina mai cewa “ mene ne
kuma Ammy? Don Allah kar ki tuna shi,kar fa ki manta kin yi mini alƙawarin haka”

Kai ta jinjina mini kafin ta ce “ zan shiga ciki sallar magrib ta gabato zan yi
wanka” sai kuma ta miƙe,na bi bayanta da kallo kawai.Ina nan zaune mai aiki ta kawo
min abubuwan motsa baki,ko kallon ta ban yi ba na soma ci ina tunanin abar ƙauna.Na
kurɓi lemun zoɓo kafin na miƙe na fita harabar gidan,mota na shiga na ƙara ficewa.

Ban yi nisa ba kuwa aka soma kiran sallah,amma ban wani damu ba na ci gaba da
tuƙina har na isa inda nake tunanin zan samu macen da za ta sama min nutsuwa.

Daidai wurin bada hannu na tsaya,almajiran suka fara miƙo min robobinsu duk da kuwa
gilashin motata a rufe yake ruf.Dayawansu ba za su wuce shekara ashirin zuwa da uku
ba,ganin ban buɗe ba yasa duk suka tafi sai ɗaya ce ƴar jaraba ta tsaya .Sai a
lokacin kuma na yi ƙasa da madubin motar,cikin daƙiƙa biyar na ƙare mata kallo fara
ce ita amma dauɗa ta saka ya disashe sannan irin kamar Fulanin nan na daji.

“Alhaji ka taimaka mini ina son kai Mamana asibiti ne” ta faɗa cikin marairaice
murya.

“Nawa ne farashinki? ” na samu kaina da furta wa,ido kawai ta zuba min da alamu ita
sabuwar zuwa ce ba ta san tabi'ar nan ta ban manda na baka gishiri ba.
“Za ki bi ni mu je in kina son na baki kuɗi” na faɗa a karo na biyu,sai na ga tsoro
ya bayyana a fuskarta.A hankali na soma mayar da madubin motar amma ta yi saurin
dakatar da ni ta hanyar saka hannunta daga sama ,sai na ƙara yin ƙasa da shi.
“In mun je da gaske za ka bani kuɗin?” ta jefo mini tambayar cike da yarinta.
Kai kawai na jinjina mata,sai na ga fuskarta ta faɗaɗa da murmushi.Gaban mota na
buɗe mata kafin na yi mata key,tuni gari ya ɗauki duhu sai hasken fitilun kan
hanya.Gudu nake sosai ta yadda ta soma yi min magana cikin tsoro “ don Allah Alhaji
ka yi haƙuri kar ka sayar da ni ”

Na ja tsuki ban tanka ta ba,sai dai na rage gudun motar sai ta saki ajiyar
zuciya.Gidana na kai ta wanda babu kowa a cikinsa hatta mai gadi ban sa ba,a waje
na yi parking duk muka fito.Na buɗe gidan na shiga sai na ga ita ta tsaya bakin
ƙofa,“ki shigo”

“A'a ba sai na shiga ba ka ɗauko kuɗin ka bani” tsabar takaici ban san lokacin da
na wani jawo hannunta da ƙarfi ba na shigo da ita ciki tare da rufe gidan.

“In kika ce ihu ko kuka za ki yi min zan sayar da ke ɗin tun da haka kike so” na
faɗa tare da yin gaba,a dole ta take min baya har cikin falo.Na kunna wutar ko ina
sannan na haɗe rai tare da nuna mata toilet na ce “ ki shiga ki yi wanka” jikinta
na kyarma ta shiga ɗin,sama da minti goma amma ta ƙi fitowa sai na mara mata baya
ina shiga na ja wani uban burki zuciyata ta soma bugawa fat! Fat! Fat! Sakamakon
ganin Oga cikin shigar kayan yarinyar da na ɗauko a mota.
Waige-waige na fara sai dai babu ita sai shi ɗin dai,kamar ƙyaftawar ido yarinyar
ta dawo normal ta soma magana amma muryar oga ce ke fita.

“ Tun da na soma meeting ɗin yau hankalina yake kanka,wato a fuskar kowa na lura da
damuwa saɓanin kai.HAROON ka fara soyayya faɗa mini wace ce ita?” yana gama faɗa
sai ya ɗauki siffarsa ta namijin kayan yarinyar nan suka zube a ƙasa sai nasa kayan
jajaye masu kamar jini.
Kasa furta komai na yi,don in na ce in yi magana ƙarya ce zan faɗa kuma tsaf zai
gane.To mene ne ma abin yi wa mutumen da yake da ƙarfin power ɗaukar siffar mace?
Shirun dai ne ya fi alkhairi a gare ni.
Kafaɗata ya dafa sai na ji wani zuuut,sai muka ɓace daga cikin toilet zuwa daularsa
wacce kusan a can muke taro masu muhimmancin sosai ko kuma in wani sabon members ya
shigo.Ban fita daga wannan mamakin ba na ji na yi sama cikin iska kafin kuma in ji
ni gammm,bayana ya bugu da bango yayin da hannuwana kuma aka banƙare su tare da
ɗaure su da kacar tsafi.

“Babu soyayya a tsarin ƙungiyarmu,amma kai ka karya doka! Zaɓi biyu zan baka ko dai
ka sadaukar da budurwar da kake so,ko kuma na aika ka ɓoyayyar duniya yanzu nan tun
kafin wa'adin shekarunka su cika”

Ido na rumtse gam,a cikin zaɓin biyu babu mai sauƙi a gare ni.Shekara biyar ta rage
mini a doron duniya kamar yadda muka yi yarjejeniya a ranar da zan sayar da
ruhina,an bani shekaru goma na rayuwa a wannan duniya kafin na isa ɗayar,a cikin
goman kuma na yi biyar saura biyar suka rage mini.‘Wane zaɓi zan ɗauka?’ na tambayi
kaina a zuci.......
[26/12 à 09:33] MRS SADAUKI: *MAFIYA*☠️

LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️

*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo


(MRS SADAUKI✍️)

*Lambar waya:* +22795045822

*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*


Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
_____________________

04

“Wato soyayyar da kake yi mata har ta kai ka kasa sadaukar da ita kai tsaye shi ne
ka tsaya shawara? Hahaha! Ōgāfōr̃!” Oga yayi lafazin ƙarshe cikin Yaren matsafa a
nan take kuma na ga tile ɗin ɗakin na darewa wata jar turɓaya na bayyana kuma sai
girrrr kake shi tamkar ƙatuwar tirelar ɗan danƙarau mai yin gina.

A inda nake can sama ɗaure a jikin bango nake kallon duk abin da ke faru,gidan ƙasa
ne ya bayyana sai a lokacin kuma kacocin hannuna suka kwance kansu yayin da na soma
yawo cikin iska ina kaɗawa kamar wata leda.

Wasu ɗalasiman tsafi Oga ya soma kafin ya ce “ je ka ɓoyayyar duniya ka yi ziyara


na tsawon kwana uku,in ka fito daga ciki sai ka bani zaɓin ka” rufe bakinsa ke da
wuya na soma ji na ina yin ƙasa har na shiga dogon ramen mai ɗauke da wata daular .

Ina shiga ciki komai ya soma komawa normal ya ɗinke,sai da na ja wani numfashi
sa'ilin da na ji ƙafafuna sun dogane da ƙasa.

Baƙar ƙofar na kalla ta gabana wacce nake da tabbacin ita ce za ta sada ni da


ainahin abin da ake kira da ɓoyayyar duniyar.Na shagala sosai ina kallon ƙofar tare
da tunanin da na san ba zai fishe ni dare ba,kawai sai na ji ƙiiiiii ƙofar ta buɗe
da kanta.
Ido na tsura ina jiran ganin wanda zai fito,amma sai na ji wata murya na cewa “
Barka da zuwa duniyar Ruhaniya ” ban amsa ba haka ban gusa daga inda nake ba .

Sai na ji an kamo dukkan hannuwana biyu ana jana amma ban ganin masu jan nawa,a
dole na soma taka ƙafata har muka bi ta ƙofar nan a take kuma ta rufe ji kake
gammm.Duhu ne ya turniƙe wurin,sai a lokacin kuma na ga inuwar masu jaye da ni
saboda wani jan haske da goshinsu ke fitar wa kamar wuta.

Ci gaba suka yi da ja na izuwa ciki,matakala muka soma takawa muna daɗa yin can
ƙasa.Har muka ainahin duniyar,nan ɗin ko ina da haske tamkar goshin azahar haka.

Duk masu bi suna wuce wa na soma duba,dayansu siffar mutane ce da su yayin da


sauran kuma suke ɗauke da sifofin dabbobi iri-iri.

Irin inuwar nan gani ta waɗanda suka yi min iso,a zuci na ce ‘ ko su waye su?’

“Dōr̃ānī! Masu kula da shige da ficen duk al'ummar nahiyar nan.Ko da wasa wani ya
tsaya hutawa dangane da aikin da yake yi za su hukunta shi ne” na ji muryar ɗazu ta
faɗa wacce ta tarbo ni tun a bakin ƙofa.

Saitin inda murya ta fito na duba,sai na ga yanzu ana ganinsa da kyau sai dai
muninsa ma ba zai bari ka ci gaba da kallonsa ba.

“Amma kuma ƴan Adam ne?” na tambaya.

“Duk faɗin nan babu mai ruhin bil'adama sai kai ,duk waɗanda ka gani da irin
siffarka to mutum ne da rigar aljan.Bima'ana gangar jikin ce ta mutum amma ruhin
aljani ne a ciki”

“To ya ake hakan tana faruwa?” na sake jefo masa tambayar.

“Mutanen da suka sayar da ruhinsu ga MAFIYA ,bayan wa'adin shekarun da aka ɗibar
musu ya cika za a aiko da su izuwa nan.Ruhikansu za su dinga yin bauta ,yayin da
gangar jikinsu kuma aljanai za su ɗauke ta su dinga amfani da ita.” yana kawo wa
nan sai yayi shiru yayin da ɗaya abokin aikin nasa ya ɗora da cewa “ dayawan jinnu
na son ganin kansu a duniyar bil'adama sai dai babu damar yin haka don ba za su iya
bayyana da siffarsu ba,wannan ya sa suka ƙulla yarjejeniya da manyan masu
ƙungiyoyin asiri da su dinga sayar musa da gangar jiki”

“To mi za su yi da ita?” na yi tambayar cikin zaƙuwa zuciyata na bugawa jin ni ma

You might also like