Uwar Sadiku Complt by Sakina Yazid
Uwar Sadiku Complt by Sakina Yazid
WRITTEN BY
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
1
A kicin ya sameta tana wanke-wanke, motsin shigowarsa yasa ta juyo. Ta kare masa
kallo tana murmushi, shima kallonta yake yana murmushi. Yace
‘A’a! Gani nayi an ce Bichi za a je a gaida Baffa amma kuma naga an dau wanka kamar
za aje wajen bazawara.’
‘Au ashe fa ban gaya miki ba akwai wata budurwa ce ma da zan dan abinnan....'
‘Idan na dawo nace ki kwashe kayanki daga daki daya ai zaki gane.’
Ta kyalkyale da dariya.
Suna ta zolayar juna suka yi sallama tayi masa a dawo lafiya ya kama hanyar Bichi;
inda zai je ya gaida kakanninsa na wajen uba.
Haka suke rayuwarsu cikin walwala da kaunar juna tare da yaransu biyu Abdallah da
Farha masu shekaru hudu da kuma biyu.
…….
Wunin na yau baiyi mata dadi ba, gashi su Abdallah da zasu debe mata kewa suna
gidan yayan babansu Baba Sani. Babu abinda yake damunta amma dai bata jin walwala,
tunda sukayi sallama ya tafi Bichi take fargabar da bata san dalilinta ba. Haka har
akayi sallar la’asar.
Tana zaune a falo ta kunna TV tana kallo; duk da hankalinta baya wajen; taji ana
buga gate. Ta saka hijabinta ta nufi gate din, tana zuwa ta leka ta gefen gate din
ta hango Baba Sani a tsaye rike da mukullin mota. Ta karasa da sauri ta bude gate
din ta matsa don ya wuce
Ta fada tana kama hanyar cikin gidan da nufin ya biyota su karasa ciki. Ya ja ya
tsaya a bakin gate, ganin haka itama ta juyo ta tsaya tana dubansa. Kafin tace wani
abu yace
‘Ai ba ma sai na shiga ba, Umma ce dama tace na taho dake can gida yanzu.’
Gabanta ya fadi, dama tayi mamaki da ta ga Yaya shi kadai; musamman da yake su
Abdallah suna gidansa.
Ta kalleshi ta dafe kirji ta fara Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun a ranta. Fata
take Allah ya sa ba wani abu ne ya sami su Abdallah ba don watakila shi yasa
gabanta yake faduwa tun safe. Ta kasa magana kallonsa kawai takeyi tana kokarin
fassara damuwar dake kan fuskarsa, muryarsa ce ta katseta
‘Rufo gidan kawai ki zo muje, mu ake jira.’
Da kyar ta ja kafa ta koma cikin gidan zuciyarta na faman bugawa da karfi kuma da
gaggawa, dole ta sa hannunta ta dafe kirjinta.
Ta fada a fili.
Mukullin gidan kawai ta dauko sai wayarta ta jefe a jaka ta fito ta shiga bayan
motar Yaya Sani ya ja suka kama hanya ba tare da sunyi magana ba. Fata take Allah
ya sa ba yarantane wani abu ya samesu ba don wannan shine karo na farko da suka
taba zuwa gidan Baba Sani ba tare da ita ba kuma har aka barsu su kwana.
Suna shanyo kwanar gidan Umma ta hango mutane a tsaye cirko-cirko, ta dafe kirji
cikin matsananciyar fargaba; tabbas ta san Abdallah ne ko Farha wani ya mutu; Allah
ya sa ma ba su duka ne suka mutu ba.
Tuni hawaye ya wanke mata fuska yayinda ta balle murfin kofar motar ta fito ta nufi
cikin gidan da sauri tana ketare mutane.
Babu wanda ya tare ta har ta kai tsakar gidan, kafin ta karasa kofar falon ta
hango Umma a zaune a kan baranda ko shimfida babu. Mata ne a kewaye da Umman, duk
da bata da natsuwar da zata tantancesu amma ta san duk kuka sukeyi. Da sauri ta
karasa har tana cin tuntube, tan zuwa matan suka dan buda mata ta wuce har gaban
Umman. Tana zuwa gaban Umma ta zube, Umma ta goge hawayen dake fuskarta ta kama
hannunwanta duka biyun ta matse tana fadin
Tuni hawayen Aisha ya kara tsananta, ta kalli Bushra wadda take zaune a gefen Umma
tana share hawaye suna hada ido Bushra ta kara rushewa da kuka tana fadin
‘Yaya ya tafi Anti Aisha! Yaya Mustafa ya tafi mutuwa tayi mana yankan kauna.’
Take Aisha ta daskare, hawayenta ya bushe ta bude baki tana zare ido; idan ta kalli
Umma sai ta kalli Bushra. Ta bude bakinta cikin in-ina tace
‘Mustafa! Shi ai yana Bichi ko? Na zata Abdallah ne ko Farha, Abbansu ai yana gidan
Baffa ko?’
Babu wanda ya amsata sai kukansu da ya kara tsananta. Cikin rawar jiki ta fara
kokarin bude jakarta tana fadin
Anti Rakiya kanwar Umman ita ta dafe hannun Aisha wanda take kokawar bude jaka da
shi ta kalleta suka hada ido tace
‘Aisha hakuri zakiyi, Allah ya karbi rayuwar Abban Abdallah. Yana daf da shiga
garin Bichi yayi hatsari a motar sai gawarsa aka kaiwa su Baffa.’
Ta fasa bude jakar ta bude baki tabi Rakiya da kallo yayinda bugun zuciyarta ya
sake karuwa. Cikin rawar murya tace
‘Anti Rakiya duba jakarta ki dauko inhaler dinta, kada asthma dinta ya tashi.’
Nan da nan Rakiya ta zazzage jakar sai dai babu inhaler a ciki, daga waya sai
mukullin gida.
‘Babu fa inhaler a nan, babu ma komai a jakar daga waya sai key.’
Tayi waje da sauri tana share hawaye, kafin ta kai farfajiyar gidan wajen rumfar
motoci tuni numfashin Aisha ya fara sama. Tana dab da kaiwa gate Abba wanda shine
dan autan gidan ya taso ya sha gabanta
‘Subhanallah!’
Ya fice ya barta inda sauran ‘yan uwansu maza dake wajen har sun taso sun kewayeta
tana musu bayani.
Ko minti goma Abban baiyi da fita ba ya dawo, ya samesu a tsakar gidan nan a kan
baranda Aishan ta jingina da bango tana hawaye tana numfashi da kyar. Kafin ya
karasa Anti Rakiya ta mike ta karbi ledar hannunsa, nan da nan ta balle kwalin
inhaler din ta mikawa Bushra wadda ke kusa da Aishan. Haka aka dinga fesa mata
inhaler din har numfashinta ya dawo dai-dai.
Can wajen karfe shida saura Baffa Tijjani wanda kanin mahaifinsu Mustafa ne ya
shigo tsakar gidan ya sanar da su Umma zasu iya zuwa suga gawar Mustafa don an
kawota daga Bichi har sunyi masa Sallah da yake a can din an riga an wanke shi anyi
masa sutura.
Umma ta mike a hankali, itama Aisha ta mike yayinda su Bushra suka rufa musu baya.
Falon baki wanda yake da kofa a bakin gate nan aka shimfeda gawar Mustafa, tsaf an
yi masa sutura kuma da yake ba wani ciwo yaji ba fuskarsa tayi fes kamar ka kirawo
sunansa ya amsa.
Umma ce ta fara isa kan gawar ta tsuguna, ta bishi da kallo tana fitar da hawaye
yayinda Aisha ta zagaya ta daya bangaren ta tsuguna itama tana kallon fuskarsa
wadda tayi kama da ta me bacci kuma yana murmushi a lokaci guda.
Umma ta daga hannu sama tayi masa addu’a na tsawon lokaci sannan ta mike cikin
sauri ta fita daga falon tana share hawaye.
‘Mustafa.’
Babu amsa. Ta dan kara matsawa kusa tana shafa fuskarsa, kawai sai ta fada jikinsa
ta rungumeshi tana rusa kuka. Duk mutanen da suke wajen saida sukayi mata kuka;
tabbas mutuwa tayi musu gaggawa.
Shekaru biyar kacal da aurensu wanda aka yi shi cike da soyayya da kaunar juna
yanzu gashi mutuwa ta raba su; tabbas dole a tausaya musu.
Sai da aka yi musu magana za a dauki gawar don a kai kafin magriba sannan aka kamo
Aisha suka fito daga dakin; zuwa lokacin gaba daya gidan ya gama cika don har Maman
Aisha wato Hajiya da yayarta Zuwaira duk sun iso.
Haka aka fita da gawar Mustafa zuciyoyi suna begensa, musamman Aisha wadda ta kasa
gane yanda za ayi ta iya rayuwa a duniyarnan ba tare da Mustafa ba.
…….
Duk mutanen Bichi ma nan suka tare a gidan Umma ana zaman makoki; radadin mutuwar
Mustafa ya taso musu da na mutuwar mahaifinsa wanda shekarunsa shida kenan da
rasuwa.
Ranar da aka kwana uku ranar Baffa yace kowa ya tafi gida an gama zaman makoki,
washegari aka mayar da Aisha gidanta inda a nan ne zata karasa takabarta.
Anti Uwani kanwar Hajiya itace wadda ta dawo gidan Aisha don ta tayasu zama ita da
yaran zuwa lokacin da zata gama takaba; kullum sai an zo daga gidansu da kuma gidan
Umma don a duba su ga kuma ‘yan uwa da abokan arziki da suke ta zuwa gaisuwa
musamman da yake Mustafa mutum ne mai mutane ga kuma yawan kyauta.
_____
Satin da Aisha zata gama takaba aka raba gadon Mustafa. Gidan Umma suka hadu gaba
daya har Baffa da wasu ‘yan uwan nasu na Bichi.
Abubuwa da yawa da ya mallaka Aisha ma bata san da su ba, Yaya Sani haka ya dinga
lissafi yana cewa na Mustafa ne. Aka hada da gidajensa guda biyu ga motarsa ta hawa
da makudan kudade a accounts dinsa da filayensa guda uku, kuma ga gidan gona wanda
nasu ne su biyu shi da Yaya Sani.
Nan akayi lissafi aka fitarwa Umma nata sannan aka bawa Aisha nata da na yaranta;
tayi zaton ma zasu ce a bawa Yaya Sani kason yaran ya ajiye musu amma taji Baffa
yace duk a bata tunda ita din ma da iliminta kuma tana aikinta.
Aka bata zabi ko zata tafi da su Abdallah ko kuma a barsu wajen Yaya Sani, tace
zata tafi da su.
Baffa ya sake yi musu nasiha suka yiwa Mustafa addu’a suka yi mata sallama suka
tafi suka barsu ita da Hajiya da Zahida kanwarta da kuma da kuma Anti Uwani.
A ranar suka fara hada mata kayanta ita da yaran, gari yana wayewa suka tattara
suka koma gidan Hajiya gaba daya.
Gidajen guda biyu da suka fado kasonta ita da yara ta sa Yayanta Abubakar ya sa
mata ‘yan haya, ta ware kudi kuma ta bayar a samu wani waje da suke wahalar ruwa a
Bichi a yi musu borehole Allah ya kaiwa Mustafa ladan. Musamman Baffa ya kirawota
yayi mata godiya yayi ta saka mata albarka da Abba ya kai masa wannan labarin, haka
itama Umma har gidansu ta zo tayi mata godiya kuma ta duba su Abdallah.
Haka suka cigaba da rayuwa a gidan Hajiya; kullum da safe Baba Abba zai zo ya
daukesu ya kaisu makaranta idan an tashi kuma ya dawo da su.
……….
Yau satinsu biyu da komowa gidan Hajiya, bayan yara sun tafi makaranta Hajiya ta
sami Aisha a dakinta wanda aka gyara mata bayan sun dawo. A kwance take a gefen
gado bayan ta amsa sallamar Hajiya ta tashi ta zauna, Hajiya ta karasa ta zauna a
gefen gado ta dubeta cike da kulawa tace
‘Aisha.’
‘Yaushe zaki koma aiki? Kinga dai sati biyu kenan da fitarki daga takaba, ai ya
kamata ki koma ko?’
‘Hm! Wallahi Hajiya nima ban sani ba, aikin ma duk ya fice min daga rai wallahi.’
Ta share kwalla.
Ta kalli Hajiya da mamakin jin maganarta ta zare hannunta daga na Hajiyan ta share
kwalla, kafin tayi magana Hajiya ta cigaba
‘Tabbas mutuwar miji tana da ciwo tunda kafin naki mijin ya mutu nawa ya jima da
mutuwa ya barni daku gamu Allah ya raya mu. Ki godewa Allah Aisha, domin dama Allah
bai yi wa kowa alkawarin dauwama ba, mu din ma da muke raye lokaci muke jira. Ki
cire komai daga ranki ki cigaba da rayuwarki; ko babu komai yaranki suna bukatar ki
kuma walwalarki ce zata basu kwarin gwiwar cigaba da tasu rayuwar. Ki hakurkurtar
da zuciyarki ki cigaba da rayuwarki Allah zai kawo miki mafita in sha Allah, ki
cigaba da yiwa Mustafa addu’a Allah ya hadaku a Aljanna.’
‘Ina nan ina yi, kema kuma sai ki dage ki bawa kanki hakuri.’
Hajiya tayi murmushi ta dan kara bata hakuri sannan ta fita daga dakin ta barta
tana tuno lokacin da ya samo mata aikin lokacin saura baifi wata hudu ba ya rasu ma
ashe:
A kwance ya sameta a falo tana kallo, yaran duk sunyi bacci don har taran dare ta
gota. Bayan tayi masa sannu da zuwa ya wuce daki ita kuma ta tashi ta jera masa
abincin darensa a dining table. Ta bishi dakin suka fito tare, har ya zauna ya mike
ya koma dakin ya dauko takardar ya fito ya sameta a zaune ya mika mata takardar
sannan ya zauna ya fara cin abincin da ta zuba masa.
Karanta takardar takeyi tana murmushi, ta riga ta gaya masa bata son aiki amma shi
ya dage tunda ta karanci education to ya kamata a samar mata koyarwa; ko babu komai
ta sami abinda zata kula da kanta da shi. Ya kalleta bayan ya cinye lomar bakinsa
yace
‘Sai ki bani tukwici Malama Aishatu ga offer nan kin zama malamar gwamnati.’
Ta kalleshi tana dariya tace
‘Gashi nan na baka tuwo harda nama. Allah dai ya bani ikon yin aikin nan don ka san
ni da son jiki.’
‘Dagewa zakiyi fa, ki rike aikin nan kinga ko bayan raina kina da abinda zaki kula
da kanki da yara kuma ko ina rayen ma bamu san abinda gaba zata haifar ba don haka
aikin nan security ne a gare mu. Ki dage kawai Malama Shatun Musty.’
Wannan maganar tasa kwakwalwarta ta dinga maimaita mata tana share hawaye; gaban da
yake nufi kenan ashe. Ai dole ma ta koma aikin nan, kuma in sha Allah goben zata
koma.
UWAR SADIKU
WRITTEN BY
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
2
A hankali rayuwar Aisha ta fara dawowa dai-dai, sai dai kawai tana nan da tabon
rashin Mustafa a zuciyarta. Ga yaranta suna walwalarsu amma duk lokacin da ta
kallesu sai tayi kewar ubansu, musamman Abdallah da yake matukar kama da shi.
Gashi yanzu har an shekara da rasuwar Mustafa; duk abinda uba zai yiwa da ‘yan uwan
Mustafa basu taba fasawa ba, kuma suna yawan zuwa duba su ko kuma su zo su kwashesu
su yi musu kwana biyu.
Tuni an canza musu makaranta sun dawo kusa da gidan Hajiya amma Umma ta saka dole
kullum sai Abba ya zo ya kaisu, in ya so sai Aisha ta dauko su.
………..
Suna zaune a falon Hajiya ita da su Abdallah da kuma Afnan ‘yar wajen Zuwaira
sunata wasa, Afnan ce take bawa su Abdallah labari
‘Ni kullum Abbana ya dawo sai ya siyo min ayaba wataran ma harda apple.’
Farha tace
‘To muma dai kullum sai Mommy ta siyo mana duk abinda muke so, kuma Baba Abba yace
mu Abbanmu ya tafi can yana Aljannah don ya gina mana gida kafin muje.’
Tace
‘Mama.'
‘Abdallan Mama.’
‘Da ma Abba ya jiramu ko? Ai da sai mu tafi aljannar tare, amma shi yayi wani sauri
ya tafi.’
Ta bude baki zata sallameshi Hajiya ta fito daga daki inda take jiyosu tace
Hajiya ta karaso ta zauna a kan kujera kusa da Aisha, kafin ta zauna Aisha tace
‘Ba zai yi tafiyar tasa ba, tashi zakiyi kije. Babu wanda zai yi miki auren dole ai
sai an jira yardarki, idan kin saurari mutum ba shine yake nufin zaki aureshi ba.
Ki godewa Allah a hakan ma, kuma ki tashi kije ki ga mai kiran naki.’
Kallon da Hajiyan takeyi mata ya tabbatar mata ba zata saurareta ba don haka ta
mike ta shiga dakin ta sako hijabi ta zo ta wuce.
Hajiya ta bi bayanta da kallo tana jijjiga kai cike da tausayi; ta san dai Aisha so
take tace ba zata sake aure ba, ita kuwa bata yi mata wannan fatan. Har yanzu da
kuruciyarta domin shekarunta ashirin da biyar kachal, ba zai yiwu ba kuwa ace a
barta babu aure. Addu’ar Hajiya daya Allah ya bata miji nagari wanda ma zai so ta
fiye da yanda Mustafa yake sonta.
……..
‘Principal?’
Ta tambayi kanta.
Ta dan saita fuskarta daga murtukewar da tayi, ta nufi motar tana tafiya a hankali
tana tunani kala-kala; Allah ya sa dai ba wata matsala aka samu a wajen aikin ba da
principal zai taso da kansa har gidansu.
Tana tsayawa a kusa da motar ya bude kofar motar ya fito yana ta faman murmushi
kamar wanda yaga wata sabuwar amarya, dariya murmushin nasa ya bata amma sai ta
waske da murmushi tana fadin
‘Yallabai sannu da zuwa. Kai da kanka? Ai da kirawo nima kayi yallabai da ba sai ka
taso ba.’
‘Haba Malama Aisha, ai zancen mai mahimmancine shi yasa gara na taso dai na zo.’
Suka gaisa tana ta mamakin wannan zance da ya kawo shi. Suka yi shiru tana
sauraronsa, yayi dan gyaran murya yace
‘Um ai gara mu sami wajen zama ko? Ko nan cikin motar ma sai mu zauna kya fi
fahimtar abinda na zo da shi.’
Ta wuce gaba ya bita a baya suka shiga cikin gida; suna shigowa akwai gareji wajen
ajiye mota daya wanda motar mahaifinsu ake ajiyewa a da amma tunda ya rasu sai
wajen ya zama babu motar. Ta zaro kujerun roba guda biyu daga cikin kujerun da suke
ajiye a garejin ta gyara musu zama ta nuna masa daya tace
‘Bismillah.’
Ya zauna itama ta zauna a dayar. Suka sake yin shiru na dan lokaci, principal yayi
gyaran murya
‘Uhmm! Wato Malama Aisha na san dai kin yi mamakin ganina to amma kamar yanda na
gaya miki maganar mai mahimmanci ce sosai.’
‘Wato ina so ne ki bani dama na shiga cikin manemanki, tunda shi aure nufi ne na
Allah. Kuma na san dai duk wani bayani da zaki so ki ji a kaina kin riga kin san
shi, sai dai ina fatan ki yiwa zancen nawa kyakkyawar fahimta.’
Tuni murmushin fuskarta ya gushe, sai dai bata daure fuskar sosai ba. Ta kalleshi
suka hada ido ta kawar da nata idon yayinda shi kuma yake ta kara fadada murmushin
da yake fuskarsa. Ta gyara zama kadan tayi gyaran murya
‘Hmmm! Uhhm! Ban ki zancenka ba, amma dai ina bukatar karin lokaci don a yanzu bana
ma jin sha’awar sake wani auren. Don haka ina ga mu bar wannan maganar kawai
yallabai.’
‘Wannan babu wata damuwa, ni dinma ba sauri nake ba. Tunda dai kin san da zamana
babu wata damuwa Allah ya sa dai ni din ne mai rabo, kuma Allah ya ji kan babansu
Abdul din.’
‘Amin.’
Ta amsa a gajarce. Ta mike tsaye ta koma ta tsaya a bayan kujerar da ta tashi tana
wasa da kujerar tana fadin
‘Bari na shiga gida don dama kokarin dora abinci nake aka kirawoni.’
Shima ya mike.
‘Allah sarki, to ai babu damuwa. Akwai ‘yar tsaraba da na zowa da su Abdul ita a
mota bari na dauko sai ki shigar musu da ita.’
Kafin ta bashi amsa ya juya ya nufi gate. Tana nan tsaye ya shigo da leda a
hannunsa ya mika mata.
‘Yar alewa ce ta yara, kya shafa min kansu tunda naga kamar kina sauri balle nace
ki kirawosu mu gaisa.’
Sukayi sallama ya fice ita kuma ta nufi cikin gida tana mamaki da takaici a lokaci
guda. Gaba daya ma dariya abun yake bata; duk da dai principal mutumin kirkine amma
gaskiya ko zata yi aure ba zata aureshi ba balle ma da yake gaba daya auren ma
yanzu baya gabanta. Bayan Mustafa ba taga wani namiji a duniya da zata iya
sallamawa zuciyarta da jikinta gaba daya ba, ba zata iya ba gara tayi zamanta ta
kula da yaranta.
Tana shiga gidan ta wuce daki ta sami Hajiya a zaune a gefen gado, ta karasa ta
zauna tare da ajiye ledar a gabanta tana dariya.
Hajiya ta dubeta tana murmushi
Ta bita da harara
‘A’a Hajiya, nifa ban ce komai ba. Kawai dai ba zan aureshi ba kuma na gaya masa
don bana son ma na bata masa lokaci. Makarantar tasa ma na san zuwa sati mai zuwa
transfer dina zata fito don tun da na koma na nema a dawo dani nan Sabontiti don
tafi kusa. Yaje dai yaji da ‘yar matarsa nima naji da kaina.’
Hajiya tace
‘Amma dai kin san ba zamu zuba miki ido haka babu aure ba ko? Idan ma so kike kice
ba zaki sake aure ba to ki bari, ba ki kai shekarun da za a zuba miki ido babu aure
ba sai dai idan Allah bai fito da mijin ba.’
Ta sunkuyar da kai tana wasa da ledar da ta shigo da ita. Hajiya ta gyara zama ta
dafa hannunta
‘Hakuri zakiyi kinji Aisha, ki fawwalawa Allah lamarinki shi ya hadaki da Mustafa
kuma shi zai hadaki da wanda ya fi shi cikin bayinsa nagari. Ki cire komai daga
ranki ki sawa ranki idan Allah ya kawo miji zakiyi aure kin ji ko?’
‘Um.’
Ta amsa sannan ta yiwa Hajiya bayanin alewar ta tashi ta fice ta nufi dakinta.
Tana shiga ta turo kofar ta fada kan gado, hawayen da ta tare ya kwace; ba zata iya
auren wani mutum ba bayan Mustafa, ita din tashi ce shi kadai in sha Allah. Duk ma
rigimar da za ayi sai dai ayi amma babu wanda zata aura a duniya, sai dai su gaji
su barta.
……..
Tunda aka canza mata makaranta ta toshe duk wata hanyar da ta san principal zai
sameta, haka ya gaji da zuwa gidansu bata fita ya hakura.
Ta kula da yanda Hajiya take matukar so tayi aure, don haka duk wani wanda ya nuna
yana so ta da wuri take dakatar da shi kafin ma Hajiya ta ji zancen. A haka har aka
shekara uku da rasuwar Mustafa, lokacin Abdallah yana da shekaru bakwai Farha tana
da shekaru biyar.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
Ranar asabar ce yau, don haka gidan Yaya Zainab suka wuni ita da su Abdallah, sai
da sukayi sallar la’asar suka fito suka kamo hanya. Suna karyo kwanar gida ta hango
motar Yaya Abubakar, ta san yana gidan.
A dakin Hajiya suka sameshi yana zaune a kan dadduma Hajiya tana zaune a gefen gado
suna hira. Bayan sun gaisheshi su Abdallah suka fito falo da gudu suka barsu, itama
Aisha ta mike zata fita ta koma dakinta, Hajiya ta dakatar da ita
‘Dawo ki zauna ai maganarkice dama ta kawo Yayan naki, duk da na san babu wata
matsala.’
Ta koma ta zauna a gefen gado kusa da Hajiya cikin sanyin jiki don ko ba a gaya
mata ba ta san ba zai wuce maganar aure wadda kwana biyu da taga babu wanda yayi
zancen ta zata an hakura.
‘Yauwa to shine yayi min magana a kan yana so ya zo neman aurenki, idan kin
amince.’
Hajiya tace
Ta sunkuyar da kai don bata san me zata ce musu ba, kamar ma dai sun gama yin na’am
da maganar Musbahun.
Tana shiga daki ta jefa jakarta da hijabinta kan gado, ta dora hannu a ka; so take
ta rusa ihu amma ta san dole sai an jiyo ta. Ta karasa gaban mudubi ta tsaya tana
kallon fuskarta tana fitar da kwalla; kamar dai kowa ya manta da Mustafa ita kadai
ce bata manta da shi ba. Tana aikinta tana kula da kanta kuma yara iyayensu suna yi
musu komai amma an dameta da wani aure.
‘Musbahu.’
Ta fada a fili tana jijjiga kai, ta juyo daga mudubin ta zauna a gefen gado ta dafe
goshinta da hannuta.
Ya za ayi ta auri wani Musbahu, ta san shi sosai tunda abokin Yayan ne tun suna
yara kuma dama can ita Allah bai hada jininta da shi ba tana dai girmamashi saboda
abokin Yaya ne. Ta san matarsa daya da ‘yayansa, kuma ta san shi din dan kasuwa ne
don haka take ganin idan ta aureshi zata rasa damammaki da yawa kamar aiki da
takeyi da sauransu.
Haka ta karasa wunin nan a daki ita kadai, Hajiya tana kula da yanda yanayinta ya
canza saboda anyi maganar aure amma tayi burus da ita, don babu yanda za ayi a
kyaleta babu aure.
……..
Suna zaune a falo bayan sallar isha’i ta jiyo karar wayarta daga daki, kafin ta
motsa Farha ta zura da gudu ta dauko wayar. Bakuwar lambar ce don haka babu suna,
tayi sauri ta amsa kiran ta kara wayar a kunnenta kafin ta tsinke.
Tunda yayi sallama ta gane muryarsa, ta mike ta koma dakinta. Kafin yace wani abu
saida ya gabatar mata da kansa
‘Hm, ai na gane.’
Suka gaisa suka dan taba hira yana tambayarta yaranta. Daga baya ya sanar da ita
gobe zai zo bayan sallar isha’i, sukayi sallama suka ajiye wayar.
Ta janyo kujerar gaban mudubi ta zauna tare da ajiya wayar a kan mudubin, ta zuba
tagumi; gaskiya bata son mutumin nan, ba zata iya aurensa ba don kwata-kwata baya
cikin irin mazan da take jin zata iya rayuwa da su. Gashi taga Yaya da Hajiya duk
sunyi na’am da shi, ta san yanzu tana yin magana Hajiya zata ce bata son aure.
Ana yin sallar isha’i kuwa sai ga Musbahu, ba yaro ya turo ba da kansa ya shiga
bayan ya buga kofa an bude. Har falo ya shiga ya gaida Hajiya, tayi ta sa masa
albarka tana fatan Allah ya tabbatar da alkhairi. Bayan sun gama gaisawa ya koma
gareji don jiran Aisha wadda Hajiya tace masa yanzu za a turo ta.
Yana ficewa itama ta fito daga daki ta kama hanyar fita daga falon, sauri takeyi
don kada Hajiya tace wani abu don a halin yanzu haushin yanda Hajiyan ta dinga wage
masa baki take tana faman sa albarka kamar wadda yayiwa alfarma. Tana daf da isa
bakin kofa Hajiya tace
‘Haba Aisha, ai ko ruwa kya dauka ki bawa bakon naki ko, tunda dai bakonka
annabinka.’
Haka ta daure zuciyarta suka dan taba hira babu yabo babu fallasa, sai dai zuciyar
Aisha a cunkushe take bata jin zata iya bashi waje a cikinta. Haka dai har ya gaji
da surutu yayi mata sallama ya tafi.
Daga wannan lokacin ya zama duk juma’a sai Musbahu ya zo, duk da ya fuskanci bata
saki jiki dashi ba sai dai yana ganin kamar idan ya bata lokaci zata dawo ta saki
jiki.
Yanda Hajiya take kara sakankancewa da maganar Musbahu yasa ta kasa gaya mata bata
sonshi. Tayi kokarin gayawa Yaya Abubakar shima ta ga kamar ba zai fahimceta ba,
don haka ta hakura. Ta dai yiwa kanta alkawarin babu yanda za ayi ta aureshi.
___
Tunda mahaifinsu Aisha ya rasu duk ranar Juma’a sai Baffa Aminu ya zo gidan, shi ya
zama kamar ubansu. Yau din ma ana saukowa daga masallaci ya wuto gidan danuwansa.
Nan ya zauna a falon Hajiya, Aisha ta kawo masa abinci ya sa su Abdallah a gaba
suka ci tare. Sai da aka kusa la’asar ya fara shirin tafiya. Ya dubi Hajiya wadda
take zaune a kujerar zaman mutum uku yace
‘Ina Shatun ne, kirawota. Gara muyi zancen nan a gabanta mu ji yanda za ayi.’
‘Ku je ku cewa Mamanku tazo inji Baffa, sai ku zauna a can kuyi game a tab ko.’
Suka tashi da gudu suka tafi dakin Aishan. Basu dade da shiga dakin ba ta fito, ta
zauna a kan kafet daga gefen Hajiya tace
‘Baffa gani.’
‘Yauwa Shatu, da magana na zo. Akwai wani mutum; ni kaina ban san wa ya nuna masa
ni ba amma dai ya ce sunansa Yusuf Muhammad Bala, kuma darakta ne shi a ma’aikatar
ilimi ta jiha. Yana so na bashi izini ya zo neman aurenki. To kwanaki na san
Yayanki yace min akwai abokinsa, sai dai ban san ina zancen ya kwana ba don haka
nace ya bari na zo muyi magana da ke da mahaifiyarku tukunna.’
Ta gyara zama
‘Gaskiya ne Baffa, wancan din ne dai har yanzu yake zuwa kuma a yanda yake nunawa
yayannasu shi a shirye yake itace bata bashi dama ba.’
Ya dubi Aisha
‘Shatu hakane? Ko bai yi miki bane abokin Yayan?’
‘Babu wani yi mata da bai yi ba fa, ta dai sakawa ranta ba zata yi aure ba tunda
Allah ya kashe uban ‘yayanta.’
‘Subhanallah! Haba Shatu, rayuwar ai sai hakuri kinji, duk yanda Allah yayi da bawa
kuma dai-dai ne. Da kuruciyarki baki kai ki zauna babu aure ba tunda dai akwai
maneman, kiyi hakuri in sha Allah zaki dace kin ji Shatu. Kada ma na sake ji kince
ba zakiyi aure ba kin ji ko?’
‘Ai al’amuran sai hakuri Hajiya, kin san rabuwa da masoyi sai an yi jinyar zuciya
amma in sha Allah za a dace.’
‘To yanzu wannan din a dakatar dashi kenan koko shima a bashi dama yazo tunda
wancan din ma babu wata tsayayyiyar magana?’
Ta fada tana nuna Aishan, don haka Baffa ya mayar da hankalinsa kanta yace
‘Shatu ke nake sauraro, wannan din yazo ko kuwa kun daidaita da abokin Yayan?’
Ta sake sunkuyar da kai tana fakon idon Hajiya wadda ta dauke kai
Hajiya ta bita da kallo mai cike da tambayoyi yayinda shi kuma Baffa yace
‘To babu laifi in sha Allah. Ki kwantar da hankalinki ki duba a hankali; kin riga
kinyi aure kin san menene rayuwar aure don haka ba zamu yi miki auren dole ba. Idan
ya zo wannan din idan baku daidaita ba shima kada kiji komai sai a cigaba da
addu’a.’
‘Zo nan.’
Ta dawo ta zauna a inda ta tashi ta sunkuyar da kai, Hajiya ta harareta tace
‘Hajiya babu abinda yayi min, kawai dai bana sonshi ne.’
Hajiya ta bude baki tana mamaki, kafin tace wani abu Aishan ta cigaba
‘Kuma kinga daga maganganusa yana nuna min shi zai fi so na daina aiki sannan kuma
gida daya zamu zauna da matarsa, gaskiya ba zan ji dadin hakan ba shi yasa naga
gara mu hakura kada a bata goma daya bata gyaru ba.’
‘Ai shikenan, Allah ya sa hakane ya fi alkhairi. Bari Yayan naki yazo sai a dakatar
da shi ya daina zuwa yana batawa kansa lokaci.’
Hajiya ta bi bayanta da kallo tana mamaki yanda za ace namiji kamar Musbahu wai ba
a sonshi saboda dai fitna irin ta Aisha.
Tana shiga dakin ta koro su Abdallah wajen Hajiya ta fada kan gado ta kwanta ranta
a bace; bata son aure amma ta rasa dalilin da yasa aure yake sonta. Ta fuskanci
lallai idan batayi da gaske ba za su fara samun matsala da Hajiya don babu wanda ya
kai Hajiya son ganin tayi aure, yanzu kuma ga Baffa. Wannan mutumin ma da Baffan
yace zai zo bata jin zasu daidaita, za dai ta saurareshi ne kawai saboda kada ace
taki kula mutane; amma gaskiya yanzu aure baya gabanta.
____
Ranar asabar da yamma sai ga kira daga Alhaji Yusuf M. B. Haka ta shirya ta fita ba
don ta so ba suka zauna a gareji.
Hirar tasu babu yabo babu fallasa; ya gabatar mata da kansa, kamar yanda Baffa ya
gaya mata shima ya tabbatar mata cewa shi ma’aikacin gwamnatin jiha ne kuma yana da
mata daya da yara biyar; daya namiji, hudu mata.
Duk da bai wani burgeta sosai ba amma dai ta san akwai yiwuwar su daidaita don
kamar shi din yana da saukin hali. Haka suka taba hira kafin suyi sallama ta koma
gida.
……..
A hankali Aisha ta fara sakewa da Alhaji Yusuf M B, ba wani tsananin so shi take ba
kuma zata fi so ace an barta da auren nan amma dai ta san a yanzu idan an tashi
zata iya aurensa. Sun gama maganar aiki ya gaya mata bashi da matsala da aikinta,
uwargidansa ma iya secondary school tayi shi yasa bata aiki amma duk da haka tana
business daga gida inda take sayar da atamfofi da duk wata sutura ta mata.
A tsarinsa yana so ya hadesu gida daya da uwargidan sai dai ita Aishan ta gaya masa
tafi so ya zama nata gidan ita kadai ko da cikin compound daya ne. Ya sanar da ita
gidansa bashi da filin da zai gina mata wani a ciki amma dai ya tabbatar mata ba
zai hadesu ba tunda bata [Link] haka ta saki jiki da shi sosai sunata soyayyarsu
tunda shi din gwanin soyayyar ne.
Duk da ta amince da Yusuf amma bata daina kewar Mustafa ba, wasu lokutan ma sai
taji kamar idan tayi aure taci amanar Mustafan. Idan taji haka sai dai tayi kukanta
ta share hawayenta don ko ta gayawa ‘yanuwanta ma basa fahimtarta, so kawai suke
tayi aure. Har gara ma Yaya Zuwaira da yake itace sakuwarta suna dan fahimtar juna,
amma Yaya Zainab cewa take “Da kece kika mutu da yanzu yayi aure yana morewa da
amaryarsa amma ke kina nan kina hana kanki bacci, addu’ar ma da kike masa ai ta isa
ba sai kin cigaba da kuntatawa kanki ba.” Don haka bata ma son yin zancen da ita.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
4
Tun kimanin shekaru shida da suka wuce ya so ya kara aure, don a lokacin har an je
gaisuwa gidansu budurwar da yake nema; sadaki kawai za a kai a saka rana sai kuma
aka wayi gari haka kawai maganar auren ta fita ransa. Yarinyar da yake nema bata yi
masa komai ba amma haka kawai yaji ya daina sonta. Da farko ta so ta takura masa,
amma sai Allah ya hadata da wani saurayi a daidai lokacin wanda ya fiye mata Yusuf
din.
Matarsa daya Hajiya Zahra’u da yaransu biyar; Sadik, Yusra, Rukayya, Khadija wadda
suke kira Dija sai Zulaiha mai shekaru uku wadda suke kira Ummi saboda sunan
mahaifiyar Zahra’un taci.
Hajiya Zahra’u mace ce mai matukar kirki ga kyauta, duk wani abu da zai farantawa
mijinta shi takeyi. Shima kuma ta samu yana da kulawa gashi yana mata yanda take
so; musamman ma yanzu da Allah ya kara buda masa ya fara tara abun duniya. ‘Yan
uwan Yusuf ma suna matukar kaunarta saboda yanda take musu kyauta kuma tana kulasu
tana kula da mahaifiyarsu Hajiya.
Tun Yusuf yana malamin makaranta ta aureshi, suna tare ya karo karatu ya sami
sauyin aiki ya koma ma’aikatar ilimi ta jiha; gashi yanzu har ya zama director.
Wannan ne ya saka Hajiya Zahra’u take ji cewa ita kadai ce ta dace ta zama matarsa,
don ita ta sha wahalarsa. Shi yasa ma wancan lokacin daya ya dauko maganar aure ta
san yanda tayi ta kifar da zancen.
Bata yin tsafi don tana da ilimin addini gwargwado saboda haka ta san abinda zai
rabata da imaninta, amma tana da malamanta irin na soro wadanda sukeyi mata aiki da
ayar Allah, wani lokacin ma har su bata ruwan rubutu ko tofi wanda zata yi amfani
da shi ko shi Yusuf din tayi masa amfani da shi.
Tunda taji anje gaisuwa wancan lokacin da ya fara maganar auren ta tashi ta tafi
har garin Gaya, wajen wani malami da aka hadata da shi Malam Hatimu mai ‘yan
makaranta. Tayi masa bayani so take kawai a sakashi ya manta da maganar auren nan
ya daina son yarinyar. A nan take kuwa ya zana hatimi ya nade mata laya ya bata
yace ta saka masa a karkashin katifarsa, idan dai ya kwana a kai ba zai sake
maganar auren wannan yarinyar ba. Haka kuwa akayi, wannan aure dole aka barshi.
Bayan fasa wancan auren ne abokinsa ya bashi shawara idan ya tashi sake aure kada
ya fada da wuri sai magana ta kankama, kuna shima sai ya dage da addu’a. Don haka
ma tunda ya fara neman auren Aisha babu wanda ya gayawa, don har abokan nasa ma
babu wanda sani.
Yayansa kawai ya gayawa wanda shine zai wuce masa gaba wajen neman auren kuma ya
gaya masa bai sanarwa kowa ba don haka shima kada ya bari zancen yake wajen mata.
____
A daki ta sami Hajiya tana zaune a kan dadduma inda ta idar da sallar la’asar, ta
shiga dakin da sallama ta karasa ta zauna a gaban Hajiyan bayan da ta amsa
sallamarta. Hajiya ta gyara zama tace
‘To wacce sura zan biya miki da kika sakani a gaba haka kamar mai daukar karatu.’
‘Kai Hajiya.’
‘To ya akayi?’
‘Kai ma sha Allahu, to ai hakan yayi. Bari Yayanki ya zo sai na sanar dashi in ya
so sai ki gayawa Yusuf din ya nemeshi suyi magana ko kuma ya nemi Baffa.’
‘To damuwar kuma da bacin ran na menene, ko shima Yusufan ba kya sonsa?’
Sukayi shiru na dan lokaci, Hajiya tana sauraronta don ta san zancen bai kare ba
yayinda ita kuma take tunanin kalmomin da zata yi amfani da su ko Allah zai sa
Hajiyan ta fahimceta. Jim kadan ta cigaba
‘Sai naga kamar idan nayi aure zan ci amanar Mustafa Hajiya, ban san ma dai me yake
damuna ba Hajiya. Ga su Abdallah kuma, bana son rabuwa da su sai na ga kamar abun
zai yi musu yawa; babu uba kuma ni dinma na zo na tafi wani gidan na barsu.’
Hajiya ta saka hannunta tana goge mata hawayen da yake bin kumatunta cike da
tausayawa
‘Na fahimceki Aisha, tabbas idan miji ya mutu yana tafiya da rabin zuciyar matar ne
kamar yanda mahaifinku yayi min. To amma hakuri shine siffar bayin Allah na gari.
Baki ci amanar kowa ba idan kikayi aure, ke dai kada ki taba fasa yiwa Mustafa
addu’a. Ki cire duk wata damuwa daga ranki Allah zai saka miki albarka a cikin
aurenki in sha Allah.’
Ta daga kai alamar to, ta kifa kanta kan cinyar Hajiya, ita kuma ta cigaba da shafa
mata kai yayinda take fadin
‘A’a, ba muyi wata magana ba. Shi sau nawa ma ya taba yi min maganar yara? Ai bai
fi sau a kirga ba. Kuma ni dama bani da niyyar tafiya da su gidan wani, a nan zan
bar miki su idan dai kin yarda tunda gashi Anti Uwani zata dawo nan kin ga ta
tayaki. In ya so ni sai na dinga zuwa ina dubaku tunda iyayensu suna yi musu komai
kuma na san ba zamu sami matsala da su ba.’
‘Ah ni kam ai dama zan fi so ki bar min su muyi zaman mu, amma idan kina son tafiya
da su ai sai kuyi maganar da shi ki ji me zai ce.’
‘A’a Hajiya, ba zan tafi da su ba fa, sai dai ko daga baya idan na ga da hali sai
su koma can din. Amma dai yanzu suyi zamansu.’
Suka dan taba hira sannan Aishan ta fito ta shiga kicin don dafa musu abincin dare.
Tabbas Yusuf baya yawan damuwa da yaranta, watakila shi din ba mai son yara bane.
Headmaster da Musbahu da suka fara zuwa wajenta a da kullum cikin yiwa yaranta
tsaraba suke amma shi babu abinda ya dameshi, duk abinda ya kawo to ita ya kawowa.
Har gara wancan hutun da za a koma first term ya kawo musu kyautar robobin ruwa da
jakunkuna na makaranta masu kyau da tsada, amma bayan wannan ba zata iya tuna wani
abu da ya hadshi da yara ba. Yana dai cewa ta gaishesu ko kuma idan ta fita da
Farha ya dinga janta da hira. Ita gaba daya ma idan tana tunanin su Abdallah ji
take kamar kar ta yi wani aure, bata son rabuwa da su kuma gani takeyi kamar bata
yi musu adalci ba.
Ta jijjiga kai ta kawar da wannan tunanin don ta tabbatar in dai zata cigaba da
irin wannan lissafin to tana dab da fasa wannan auren; ta san kuwa ba zasu daidaita
da Hajiya da Baffa ba idan haka ta faru.
Sati guda da yin wannan maganar waliyyan Yusuf suka kawo sadaki da kayan auren
Aisha. Gidan Baffa suka kai tunda shine ubanta, sadakinta naira dubu dari da kayan
lefe da duk wasu kaya da ake kaiwa na aure haka suka hada suka kai. Sun zo da sa
ranarsu suna so ayi biki sati shida, lokacin zai kama bayan karamar sallah da kwana
takwas kenan shi kuma Baffa yace ayi musu hakuri a barshi sati tara. Don haka aka
tashi daga taro a kan bayan sati tara za a daura auren Alhaji Yusuf Muhammad Bala
da Kuma Aisha Tukur Yawale.
Bayan sun sallami baki Baffa ya cewa Yaya Abubakar idan an yi sallar isha’i yazo ya
daukeshi suje su yiwa Hajiya bayanin kuma su kai mata kayan da kudin gaba daya.
……..
Tana zaune a falo tana kallon TV tare da su Abdallah wayarta tayi kara, tana dubawa
taga Yusuf ne don haka ta dauki wayar ta amsa ta kara a kunnenta ta mike
tanufi daki.
Tace
‘To ai yayi ko? Kin ga kafin nan na samu na dan gyara gidan tunda kince kin fi son
ki zauna gidanki da ban.’
‘Eh, gaskiya sai ya fi dadi tunda ma kace gidan jikin gidanka ne kaga ai duk muna
waje daya.’
‘Hakane, sai dai zan fi son ku a gida daya amma duk da haka na hakura yanda kika ce
haka za ayi. Gashi dai an ki sayar min da gidan amma sun bani haya, na ma biya na
shekara biyu.’
Tayi murmushi
Sai bayan sallar isha’i Yaya Abubakar da Baffa suka shigo gidan.
A falo Hajiya ta saukesu, bayan sun gaisa Baffa yace
‘To Alhamdulillah an kawo kudin ‘yata, kaya komai yayi Alhamdulillah kuma mun basu
sati tara zuwa lokacin an gama hidimar karamar Sallah.’
Ya zaro sababbin kudin daga aljihun Babbar rigarsa ta mikawa Hajiya yana cewa
‘Ga sadakinta don haka idan sun zo auren kawai za a daura, kaya kuma suna can
akwati shida gobe in sha Allah za a kawo.’
‘Amin ya Allah.’
‘To yaranta fa? Ina za a barsu? Don sai an san makomarsu kafin ayiwa uwarsu aure.’
Hajiya tace
‘Eh to, duk da dai bata ce min sunyi maganar yaran ba amma dai tace min bazata tafi
da su ba a nan zata bar min su.’
‘To babu laifi, Allah ya raya su yayi musu albarka. Allah ya sa albarka a cikin
auren. ‘Yan uwan ubansu ma suna kokari don haka ma yaran basu da wani maraici,
Allah ya saka musu da alkhairi.’
Hajiya ta amsa da Amin, sukayi sallama Baffa da Yaya Abubakar suka kama hanya.
Suna fita Hajiya ta mike ta leka dakin Aisha tana kwance a kan gado yayinda
Abdallah da Farha suke kwance a gefenta suna bacci, tace
Ta taso ta bi bayan Hajiyan suka shiga dakin kusan lokaci guda suka zauna a gefen
gadon Hajiya. Hajiya ta mika mata kudi tace
Duk lokacin da aka zo wata gaba a kan maganar auren nan sai taji kamar ta fasa,
amma ta san haka zata daure. Hajiya ta cigaba
‘Eh, ai na gaya miki a nan zan barsu, bamu dai yi maganarsu da shi ba amma a nan
zan bar miki su.’
Suka dan taba hira, Aishan ta tashi ta koma nata dakin zuciyarta cike da tunani
kala-kala.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
Suna gama waya da Aisha kuma sai hankalinsa ya dawo kan uwargidansa Zahra’u, duk da
dai itama Aishan ya ji ta kamar bata cikin yanayi na walwala amma dai kaf rigimar
Aisha zuwa yanzu ya haddace; kuma ya iya da ita.
Yanda za ayi ya gayawa Zahra’u zai yi aure shine matsalarsa; baya jin zata bashi
matsala tunda wancan lokacin ma da ya dauko auren bata bashi wata matsala; kawai
dai ya san tana da kishi kuma zuwa yanzu ta kara sakankancewa ba zai taba yi mata
kishiyaba tun da ya bar waccan maganar.
Tun yana office yake faman tunanin yanda zata kaya har ya dawo gidan bai samo amsa
ba, haka ya shiga gidan yara suka taso sukayi masa sannu da zuwa. Ya wuce daki
bayan ya amsa inda ya tarar da ita tana kwance a kan gado, bayan tayi masa sannu da
zuwa cikin kulawa ta fito ta hau jera abinci a dining table.
Har suka gama cin abincin da hirarrakinsu suka kwanta bacci bai iya gaya mata ba.
Don haka ma bayan an idar da sallar a asuba ya tsaya a masallaci yayi ta rakon
Allah alkhairin da yake cikin auren kuma ya roki Allah a kan ya basu hakurin zama
da juna. Saida ya dauki tsawon lokaci yana addu’a sannan ya fito ya koma gidan.
Ba wai tsoron Zahra’u yake ba amma dai yana son zaman lafiya da ita tunda itama
yana sonta sosai. Ya santa da kishi kuma shi baya so auren nan ya zama dalilin da
zai saka ta canza hali tunda ita din tana kulawa da shi sosai harma da danginsa.
Sai wajen karfe takwas da rabi na safe ya gama shirin tafiya office, ya fito a
shirye ya zauna a dining table inda take jiransa suci abinci.
Daga ita sai shi a gidan domin yara duka tuni driver ya kaisu makaranta. Suna cin
abincinsu suna hirarraki irin na miji da mata, duk da dai ta kula kamar wani abun
yana damunsa tun jiya; jira takeyi shi ya gaya mata kafin tayi masa magana.
Da murmushinta ta amsa
‘To Yallabai.’
Yana wucewa ta bi bayansa da kallo tana murmushi; ta san akwai magana a bakinsa
daman wannan lokacin take jira. Cikin sauri ta daga kofin shayinta ta kurbe ta
bishi dakin don haka kusan a lokaci guda suka shiga.
Kujerar mutum daya dake dakin ya zauna don haka ta zauna a gefen gado tana
fuskantarsa, ta kara fadada murmushinta tace
‘Gani Yallabai, me na samu? Ka san hausawa sunce idan ka ji kira samu ne.’
Yayi wani dan gajeran murmushi ya taso ya dawo kusa da ita, ya kama hannunta na
dama ya rike yana shafawa yana duban fuskarta. Suka shiru na dan lokaci sannan ya
dubeta yace
‘Kanwa kika samu Zahra, aure zanyi in sha Allahu shine nake so na sanar dake.’
Tuni ta bude baki tana binsa da kallo cike da mamaki. Ya sunkuyar da kansa a
hankali yayinda ta zare hannunta daga cikin nasa. Ta hadiye wani malolo da ya
tokare mata makogoro tana kokarin tokare kwallar da take neman kwace mata tace
‘Ai bazawara ce ma ko da yake mijin nata rasuwa yayi ya barta da yara biyu kanana.
Tana da hankali kuma sosai ga ilimi na san bazaku sami matsala ba in sha Allah.’
Da sauri ya amsa
‘Amin amin.’
Ya mike da sauri tunda dama so yake ya bar gidan kafin ta saka shi a gaba da
korafi. Ya matsa gaban mudubi ya dauki hularsa ya saka yanayi yana lekenta ta
mudubin, ya dauki mukullan motarsa ya juyo yana fadin
‘A dawo lafiya.’
Ta bi kofar dakin da kallo tana takaici da mamaki; ashe har yanzu bata wuce kishiya
a wajen Yusuf ba? Tayi zaton ma ba zai taba yi mata kishiya ba da taga shekaru
shida sun shude bai kuma kwaso maganar auren ba, tayi zaton da Mallam yace mata ya
dauke hankali sa daga kan maganar aure shike nan.
Hawayen da take tokarewa ya gangaro kan fuskarta, ta sa hannu ta goge. Ta cije lebe
data tuno kalamansa “tana da hankali sosai, ga ilimi” lallai namiji, wai yau ita
Yusuf yake gayawa zai auro mai hankali da ilimi.
Ta shiga dakinta ta turo kofa, ta jingina a jikin kofar, nan zuciyarta ta fara tuna
mata rayuwarsu a baya lokacin da Yusuf din bai yi kudi haka ba; lokacin da
albashinsa na wata da kyar yake kaisu kwana goma, a lokacin haka zata zauna da dadi
babu dadi amma duk ya manta.
Ta fara kaiwa da kawowa tana tunanin mafita don gaskiya bata son wannan auren nasa,
ta ina zata fara zama da kishiya?
Ta karasa ta zauna a gefen gado ta kafa tagumi, jimawa kadan ta mika hannu ta dauko
wayarta daga kan durowar gefen gado inda take ajiye. Har ta lalubo lambar yayarta
Yaya Murja zata kirawota sai kuma ta fasa ta rike wayar kawai; kamata yayi taje
gidan duk da ta san ba lallai Yaya Murja ta barta tayi yanda take so ba amma dai
tana son ganinta.
Matsalarta daya bata gayawa Abban Sadik zata fita ba don da ta gaya masa zaice Sale
direba ya dawo ya kaita.
Nan ta yanke shawara sauri zatayi taje ta dawo don idan ta gaya masa ya san me zata
je yi gara kawai ta tafi in ya so tayi sauri ta dawo kawai.
Nan da nan ta mike, ta saka hijabi ta dau jakarta da wayarta. Har ta zo falo ta
tsaya ta saka karamar jakarta a cikin hijabin ta mayar ta saki hijabinta. Ta rufo
kofar falon ta nufi gate, tana daf da fita Bala megadi ya fito daga bayan gidan
inda yake bawa fulawowi ruwa, yana ganinta ya karaso da gudu yana rage tsawo
‘Yauwa Malam Bala, na shiga nan gidan Umman Haidar duk wanda yazo nemana kace ayi
min waya sai na fito kawai.’
Saida tayi nisa da gidan sannan ta tsaya ta hau mota, dayake shata ta dauka kai
tsaye aka wuce da ita har gidan Yaya Murja.
Bayan sun gaisa da megadin da ya bude mata kofa ta wuce ta nufi cikin gidan.
Shafa’atu ce a falon wato abokiyar zaman Yaya Murja din wadda suke kira Anti Shafa;
tana zaune tana bawa Arif abinci. Bayan tayi mata sannu da zuwa suka gaisa, kafin
ma ta tambayeta tace
Nan da nan kuwa ta wuce saman inda nan ne wajen Yaya Murja din wadda itace
uwargida.
A falo ta sameta a kwance a kan doguwar kujera, ta kunna TV tashar Zee World
yayinda take ta faman dube dube a wayarta.
‘Ikon Allah, daga ina haka babu notice ko wani wajen kika zo kika biyo.’
Suka gaisa Yaya Murja ta tambayi lafiyar yaran. Ta dubi Zahra tace
Ta kawar da kai tana jijjiga kai, ta sake dubanta suka hada ido tace
‘Shine duk kika birkice haka? To ai naga ba yau ya fara maganar auren ba ko? Ai
kawai sai kice Allah ya bada sa’a tunda bake za kiyi masa auren ba, tsuntsun da
yaja ruwa ai shi ruwa zai doka.’
‘Yaya, shekararmu fa kusan ashirin da aure duk bai tashi kara auren ba sai yanzu?
Duk yanda nake tattalinsa amma shi ba zai raga min ba? Yana wani gaya min wai mai
hankali ce sosai mai ilimi, da yake ni bani da hankali.’
‘To meye bako a wajenki a cikin abinda yayi? Ai ki kwantar da hankalinki kawai kice
Allah ya bada sa’a domin idan kika ce zakiyi wata hayaniya ma kanki zaki dorawa
hawan jini. Ni ba gani ba, me ta rage min, rayuwarta takeyi ina tawa bani ma da
lokacinta. Kiyita addu’a kawai tunda ko bai yi yanzu ba ma nan gaba sai ya kara.’
Ta kau da kai, dama ta san haka Yaya Murja zata ce domin ita din hakurinta da ban
ne. Ta san ba zata sami mafita ba ta dai zo ne saboda kawai ta fada taji sanyi a
ranta tunda ita take gani kamar uwarta tun bayan rasuwar iyayensu.
Ta gyara zamanta tana kokarin kawar da damuwar, Yaya Murja ta katse mata tunani
‘Idan dai namiji ne babu yanda zakiyi dashi, idan kika ce ba zai yi miki kishiya ba
to kanki zaki dorawa damuwa sai yayi, ki roki Allah ya hadaki da ta gari wadda ba
zata cutar da ku ba gaba daya.’
‘Hakane Yaya.’
‘Yauwa Uwar Saddiku, ko ke fa. Bari na samo miki lemon ki kora, kina sallah kina
salati babu macen da zata baki tsoro.’
‘Ai barshi kawai Yaya, wallahi ko tambaya banyi ba na fito saboda takaici.’
Ta mike kafin Murja ta zauna suka nufi kasa tare, sukayi sallama tana sake bata
hakuri tare da yi mata alkawarin gobe da yamma zata zo gidan nata.
Haka ta koma gida zuciyarta a jagule; tabbas zatayi duk yanda zata yi taga an fasa
auren nan idan haka bai samu ba kuma to tafi so ta zama itace kan gida sai yanda ta
tsara.
Tana shiga gidan ta tarar da mai aikinta Jummai wadda dama zuwa take tana tafiya
idan ta gama aikinta, don haka tare suka shige cikin gidan Jummai ta kama aikinta
ita kuma Zahra’u ta haye dakinta wanda yake sama ta rufe kofa.
Tana shiga ta ajiye hijabin da jakarta a kan kujera, ta karasa ta zauna a gafen
gado ta kafa tagumi. Bata jima da zaman ba kuma ta mike ta lalubo wayarta a cikin
jakarta ta koma ta zauna akan gadon ta shiga laluben lambar wayar Amina; kawarta ce
ta aminci wadda zata iya cewa a yanzu bata da kawar da ta kaita.
Sau daya wayar tayi kara aka dauka, bayan sun gaisa Amina tace
‘Ba zaki gane ba kawata, wallahi ina cikin damuwa. Abban Sadik aure zai yi.’
Da mamaki ta amsata
‘Ikon Allah, namiji dan babansa. Yanzu ashe dama bayan waccan maganar mutumin nan
ba hakura yayi ba?’
‘Wallahi ko ni ma na zata ya hakura, amma yau da safen nan yake gaya min harda wani
ce min wai mai hankali ce kuma tana da ilimi.’
‘To ai ba wani abu bane kema kin san Abban Sadiku ba zai baki matsala ba, duk da
dai maza basu da tabbas. Sai ka gama shan wahalarsu da sun sami duniya su auro wata
suce da ita za a more.’
‘Kawata ni kawai na fi so yanda aka fasa wancan a fasa wannan ma gaskiya, na san
idan aka fasa wannan ba lallai ya kara dauko wata ba tunda kinga kullum girma yake
shima.’
‘Hakane kam, to ai sai ki kirawo Mallam kiji ko zai iya taimakawa tunda shi yayi
wancan aikin idan kuma ya gagareshi akwai wani malamin a garin Babura sai mu sa
rana muje.’
Tayi dan murmushi a karo na farko tun lokacin da Abban Sadiku yayi mata maganar
kara aure, sukayi sallama da Hajiya Amina.
Tana tsinke wayar kuma ta kirawo Malam Hatimu mai almajirai ta sanar da shi abinda
take so.
Bayan Mallam ya gama jin duk bayaninta yayi gyaran murya yace
‘To Hajiya za ayi aiki, kuma in sha Allah yanzu kam babban aiki za ayi. Sai ki yi
kokari zuwa gobe ki sanar damu lokacin da za a daura auren don mu san lokacin da
muke da shi kada mu bata lokaci.’
Sukayi sallama da alkawarin zata kirawo shi gobe ta sanar da shi lokacin da yayi
saura kafin auren.
Haka Hajiya Zahra’u Uwar Sadiku ta karasa wunin wannan ranar cikin damuwa.
……….
Tunda ya dawo gidan daga wajen aiki take tunanin ta yanda zata tambayeshi yaushe ne
auren nasa, ta kasa nutsuwa ta jeranta kalamanta yanda ba zai iya karanta damuwarta
ba. Har dare yayi bata sami wannan damar ba, ya gama cin abinci sa ya zauna a falon
sama yayi kallon TV daga baya kuma ya koma dakinsa.
Yana zaune a kan gadonsa ya mike kafa yana aiki a kwanfutarsa ta shiga dakin sanye
da kayan baccinta, bayan ya amsa sallamarta ta karasa ta kwanta a gefensa tace
Ya kauda idonsa daga kwamfutar ya dubeta alamar yana sauraronta, don haka ta cigaba
‘Da sauran lokaci gaskiya tunda kin ga bamu gama daidatawa ba tukunnu, ba zan iya
sanin lokacin ba yanzu.’
‘Uhmm!’
Taji dadin hakan don ta san hakan yana nufin tana da isasshen lokacin don karasa
nata shirye-shiryen.
Ya cigaba da aikinsa ita kuma tana kwance, jimawa kadan ta sake kiransa
‘Abban Sadik.’
‘Um.’
‘Don Allah me ya sa kake son kara aure? Idan akwai wani abu da kake bukata ai gara
kayi min magana na gyara ko?’
Ya ajiye kwamfutar a kan durowar gefen gado ya dan matsa kusa da ita ya fara wasa
da gashin kanta wanda babu kitso amma dai ta daureshi guri daya da ribbon, ya
dubeta suka hada ido sannan yace
‘Babu abinda nake bukata, kuma ke ma babu abinda kikayi min. Kawai dai mun hadu da
Aishan ne kuma tunda ida damar auren mace hudu ai babu laifin don nayi biyu ko?
Amma kada ki damu, babu abinda zai shafi son da nakeyi miki don ni din naki ne kuma
ke din tawa ce kin ji. Ki kwantar da hankalinki.’
‘Eh.’
‘Um.’
Ya cigaba da aikinsa yayinda ita kuma ta juya masa baya ta rufe ido da sunan bacci,
tunani kala-kala suna ta zarya a kwakwalwarta.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
6
Tunda Abban Sadik ya tabbatar mata ba a kusa aurensa ba ta dan sami natsuwar, domin
ta sanarwa Malam Hatimu shi kuma yayi mata alkawarin za ayi mata wani babban aiki
wanda daga shi maigidanta ba zai sake aure ba har karshen rayuwarsa. Don haka ta
saki ranta tana harkarta kamar bata da wata damuwa, kuma da bata ji yayi zancen
kayan auren ba sai ta kara sakankancewa aikin Malam ne yake aiki.
…….
Sai bayan da ya sanar da Zahra aurensa sannan yaje gidansu ya sanar da mutanen
gidan, mahaifiyarsu Hajiya Balaraba ta sawa abun albarka sosai duk da dai ta ja
masa kunne a kan kada ya kuskura ya bata da uwargidansa. Ita kuwa yayarsa Yaya
Saratu zancen bai yi mata dadi ba domin suna aminci sosai da Zahra’u; musamman da
yake ita din mai kwadayi ce sosai ita kuma Zahra’un mai kyauta ce sosai. Inda Allah
ya sawa abun ruwan sanyi don taga Yaya Bello shine gaba a wajen maganar, ta kuma
san idan ta fiya rawar kai zai ci mutuncinta. Don haka itama tayi Allah ya sanya
alkhairi kawai.
Yanda ya gayawa Zahra haka ya gaya musu, cewa ba a saka lokacin bikin ba, domin
Yaya Bello ne da abokinsa suka kai kayan kuma ya san babu wanda zai gayawa musamman
matarsa wadda suke shiri da Zahra. Itama Hajiya a haka suka barta.
Tunda taji labarin wannan auren Yaya Saratu ta kasa zaune ta kasa tsaye, a
tunaninta ko Zahra bata sani ba. Domin wancan karon da ya fara maganar auren Hajiya
ya fara gayawa kafin ya gayawa kowa don haka kafin shi ya gayawa Zahra Yaya Saratu
ce ta fara gaya mata. Hakan yana daya daga cikin abubuwan da suka kara harzuka
zuciyarta a lokacin, taga lallai idan ta bari akayi auren Yusuf ya rainata; don
haka ne ma ta san yanda tayi aka fasa.
Yanzu ma sauri Yaya Saratun takeyi domin ta fara kawowa Zahra labari, don haka
ranar da Yusuf ya sanar musu washegari ta shirya ta taho gidan Yusuf din.
Kamar yanda ta saba haka akayi mata tarba ta mutunci, kuma da yake da safe tazo
harda shayi da burodi aka ajiye mata. Saida taci ta koshi sannan Zahra ta kwashe
kwanukan ta zauna a kujerar zaman mutum daya wadda take kusa da wadda Yaya Saratun
ta zauna.
Ta gyara zama
‘Hajiya tana nan lafiya wallahi, hidimace tayi min yawa shi yasa kika ji ni shiru.’
‘Allah Sarki.’
Dama ta riga ta san zancen da ya kawota gidan kenan amma sai ta kauda kanta tana
murmushi tace
‘Kin san na zata mutumin nan ya fasa auren nan amma ashe ba zai hakura ba.’
‘To ya za ayi, ai babu laifi sai dai kawai muyita addu’a Allah ya bamu zaman lafiya
kawai.’
Wannan magana ta Zahra ta sage gwiwar Saratu, don haka cikin sanyin jiki tace
‘Uhm, ai maza sai a barsu, kedai Uwar Sadiku Allah ya kara miki hakuri don ko ta
shigo ma babu abinda zata tsinta a gidan nan. Ba zata iya gasa dake ba don ba duk
mutum ba wallahi.’
Suka cigaba da hira tana tambayarta labarin inda amaryar zata zauna inda tace mata
bata sani ba. Sai can wajen sha biyu na rana sannan tayi shirin tafiya; ai kuwa
Zahra ta hada mata goma ta arziki kamar yanda ta saba sannan ta kawo naira dubu
biyu ta bata kudin mota.
Sam batayi tunanin inda amaryar zata zauna ba sai yanzu da Yaya Saratu ta tuna
mata, duk da ma tana ji a jikinta ba za ayi wannan auren ba tunda Malam yace ba za
ayin ba. Amma dai zata so ta san tsarin da ya tanada don tayi shirin ko ta kwana.
Wancan lokacin dai da ya fara shirin auren akwai daki a falon kasa wanda yake a
kasan dakinsa, nan yace za a gyara amarya ta tare; tunda ba a kwana a ciki ajiya
kawai akeyi a ciki kamar store. Yanzun ma ta san bai wuce nan din ba, amma duk da
haka zata tambayeshi taji idan ya dawo daga wajen aiki.
Sai bayan la’asar Abban Sadik din ya kirawota ya sanar da ita yau ba zai dawo da
wuri ba, suna da meeting da mai girma gwamna kuma sai karfe takwas da rabi ma za a
fara meeting din don haka zai yi dare. Don haka ta cigaba da harkarta ta san sai
wajen sha daya na dare zai dawo kuma ba zai ci abincin dare ba.
Sai wajen goma da rabi ya dawo gidan, kusan tare suka shigo da Sadik wanda wanda
yake zauna a kofar gida yana hira da abokai sai da ya hango motar Abban sannan yayi
sauri ya shigo gidan da gudu.
Yana shiga falon tana saukowa daga bene wanda yake cikin falon, sanye take da
doguwar rigar bacci ta yafa mayafin abaya. Ta fadada murmushinta ta karasa saukowa
daga benen tana fadin
‘Sannu da zuwa Abba, ashe yau da wuri zaku gama meeting din ma.’
‘Um ina jin ai yana bacci ko? Bari na duba yana dakinsu ai.’
Ta nufi dakin wanda yake can gefe guda a cikin falon, kafin ta karasa yace
Ta tsaya ta juyo zatayi magana, kafin ta bude baki Abban ya daga murya ya kwalawa
Sadik kira, ya bude baki zai yi masa kira na biyu Sadik din ya turo kofar dakin ya
fito. Ya karaso a hankali yana shafa kai yana kallon kasa kamar mara gaskiya. Kafin
ya karaso Abban yace
‘Eh Abba dama Sulaiman na bawa wayarsa da ya kawo aka saka masa chaji.’
Abban ya cigaba
‘Na hanaka wuce karfe tara a waje amma baka ji ko? So kake mu sa kafar wando daya
da kai ko Sadik?’
Da sauri yace
Ya jijjiga kai yayi kwafa ya wuce ta tsakanin Zahra da Sadik din ya haye sama ya
nufi dakinsa.
Sai da yayi wanka sannan ta kawo masa shayi, ya zauna a kan kujera yana kurbar
shayin yana duba wasu takardu yayinda ita kuma take kwance a kan gadon tana
kallonsa. Jimawa kadan ya dubeta yace
‘Ki kwanta kiyi barcinki tunda na dawo, kinga gobe da wuri ‘yan makaranta zasu
tashe ki.’
‘Abban Sadik.’
‘Dakin kasa za a gyarawa amaryar mu fara kwashe kayanmu ko kuwa wani dakin za ayi
mata.’
Tayi murmushin yake saboda yanda taga kamar maganar ta saka shi nishadi, ta juya
kai ta amsa
‘A’a! Wai saboda na fara kwashe shirgina daga dakin a hankali ba sai an tsaya a
kaina ba.’
‘To ki kwantar da hankalinki ki kara baje shirginki ba nan zata zauna ba, ina dai
duba wani gidan a nan kusa wanda zan saya sai ta zauna a can.’
‘Au! Amma dai ba wata matsala bace ta sa za kayi hakan ba ko? Tunda ka ga nan din
ma da zai ishemu kuma ni ka san bani da matsala da hakan.’
Ya ajiye kofin shayin a kan teburin gabansa bayan ya kurbe shayin sannan ya bata
amsa
‘Babu wata matsala, kawai dai ita din ta fi son haka ko kuma akalla ta sami
complete apartment nata wato daki, bandaki, falo da kitchen; kin ga kuma idan ta
zauna a nan daki kawai zata samu sauran duka hadaka ne.’
‘Um, lallai! Ai ko dai da ka hade mun ko babu komai kaji motsin mutum ma rahama ne.
Da nan zata zauna ai ko mu sai mun fi samun natsuwa tunda ko dai ba kwanana ba kana
cikin gida tare da iyalanka gaba daya.’
‘Wallahi, nima hakan naso amma dai ita bata son hakan sai dai ko zuwa nan gaba
kafin ayi auren mu gani.’
‘Um.’
Sukayi shiru yayinda Abban Sadik ya cigaba da duba wayarsa da take hannunsa, Zahra
ta gyara kwanciya ta rufe ido kamar mai bacci saboda bata son ya sake yi mata
magana don ya gama bata haushi; tun kafin ma yayi auren har ya fara sauraron
yarinyar da zai aura tana tsara masa yanda za ayi, yarinyar ma da yace bazawara ce
ba budurwa ba.
Ita bata son ya raba musu gida; in dai har dole sai ya kara aure to ta fi so ya
ajiye su gida daya da duk matar da zai aura. Gani takeyi kamar idan aka raba gida
cutarta za a dinga yi, a kaiwa amarya abinda ba a kawo mata ba. Ta fi so su zauna
tare ta dinga kula da motsin mijinta. Duk da ta san auren ba zai yiwu ba kamar
yanda Mallam ya gaya mata, amma dole ta shirya don idan auren ya yiwu gaskiya dole
ya hadesu don bazata sallamawa wata bazawara miji ba.
Haka har bacci ya kwasheta.
…….
Yau saura sati biyu daurin auren Aisha da Yusuf, tuni ake ta shirin biki ana
sayayya a gidan su Aishan. Sai dai a yawancin lokuta bata bada hadin kai, don haka
Zainab, Zuwaira da Hajiya sune suke ta shirinsu. Ta dai zabi gado mai matukar kyau
da yake Baffa ne ya turo hotunan yace ta zaba, amma daga wannan duk abinda aka
tambayeta sai dai kawai tace ayi; ta dauki ATM card dinta ta bawa Zainab ta gaya
mata password saboda sayayyar.
Haka su Zainab suka gama sayayyar gidan amarya ba tare da amarya ba.
Yau ma Yaya Zainab ce da Zuwaira suka tafi kasuwa domin sayo carpets, babu yanda
basuyi ba su tafi da ita amma taki. Tace sune suka siyo labule don haka su siyo
carpets din da yayi matching. Don haka suka tafi suka barta a gida inda daga baya
Zahida ta zo suka hadu sukayi zamansu.
A zaune suke a dakin Aisha, ita Aishan tana kashingide a kan gadonta yayinda Zahida
take zaune a gefen gadon suna hira. Ta dubi Aishan wadda take ta faman danna waya
tace
‘Yaya Aisha sai ana maganar aurenki sai kiyi ta basarwa, wai ko bakya son mutumin
nan ne.’
‘To wa ma ya sani ne? Amma fa he’s ok sosai ma, duk wani quality na miji yana da
shi. Gashi ba sai na gaya miki ba ke kanki kin san yana so na. Kawai dai ina jin
Mustafa ya tafi da rabin zuciyata shi ya sa nake ji kamar na bar muku garin
wallahi.’
Ta harareta tace
‘Umm! To in sha Allah sai mun kai ki, komai zai tafi daidai. Allah ya ji kan Abban
Abdallah amma babu yanda bawa zai yi da ikon Allah duk yanda kika ga Allah yayi da
bawa daidai ne.’
‘Hakane.’
Haka suka cigaba da hirarrakinsu Zahida tana cigaba da kwantarwa Aisha hankali game
da auren tunda duk wanda ya sansu da Yusuf ya san yana sonta kuma itama tana sonshi
sai dai kawai gaddama irin ta Aishan.
Sai can wajen shabiyu da rabi tayi musu sallama don zata dauko yaranta Nur da Hafsa
a makaranta sannan su wuce gida.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
Saura kwana goma auren Aisha da Yusuf aka buga kati, da kansa ya kawo mata katin
hade da na wuni wanda zatayi a nan gidan Umma sanna yaje ya kaiwa Baffa nasa kuma
ya kaiwa Yaya Abubakar ma.
Bai san yanda Zahra zata dauki maganar ba don ya ce mata da sauran lokaci, kuma
yayi sa’a Yaya Bello ya bashi hadin kai ko daya zancen bai fito ba. Tun saura sati
uku bikin ya kama hayar wani karamin gida wanda gida daya ne tsakanin sa da gidansa
da Zahra take, bashi ya kama gidan da kansa ba abokinsa Jafar ne ya kama shi yasa
ma ko masu gidan basu san wa aka bawa ba. Da fari ma so yayi ya saya sai suka ki
sayarwa sukace na marayu ne haya zasu bayar, don haka aka gama magana Jafar ya biya
kudin haya na shekara biyu. Nan da nan aka shiga aikin gayara; ko da wasa bai je
gidan ba, Jafar ne a kan komai don amininsa ne tun na yarinta.
Yau da wuri ya taso daga office, yana tuki yana tunanin yanda zasu kwashe da Zahra
idan taga katin nan. Baya jin zata bashi matsala tunda wancan karon ma bata bashi
matsala ba duk da ta san yana neman aure tunda suka hadu da yarinyar, har aka saka
rana bata yi masa wata fitna ba. Abinda bai gane ba har yanzu shine dalilin da yasa
ya fasa auren waccan yarinyar.
Har ya karaso gidan yana wannan tunanin da bai samo amsar ba, me gadi ya bude masa
gate ya shigar da motarsa ya ajiye a gareji sannan ya shiga gidan. Ita da yaran
duka suna zaune a falon kasa suna kallon TV, suka tashi gaba daya kowa yayi masa
sannu da zuwa bayan ya amsa ya haye dakinsa dake sama.
Sai da ta dauko ruwa daga kicin sannan tabi bayansa, bayan tayi masa sannu da zuwa
ta nemi waje ta zauna.
Ya saba zuwa gidan da envelop don haka ma bata damu ba da taga ya shigo da envelop,
kafin ta shigo dakin ya boye envelope din don haka da bata gani ba sai ta cigaba da
harkarta.
Saida yaci abinci ya huta, yana kashingide a falonsa na sama yana kallon tashar BBC
ita kuma tana zauna a gefensa suna hira ya mike yana fadin
‘Ina zuwa.’
Kafin ta amsa ya shige daki, jimawa kadan ya fito rike da katin daurin aure kamar
guda goma a hannunsa. Ya dawo inda ya tashi ya zauna ya jingina da doguwar kujera,
ya ajiye katin a gefensa ya dubeta yace
‘Dama so nake na cemiki kanwar taki fa nan da kwana tara za a daura auren.’
Dauke wuta tayi saboda yanda taji kamar ya buga mata guduma a ka, ta yi kokari ta
rike nutsuwarta tana yake
‘Ah, ba nace miki zan kara aure ba? To ita nake nufi.’
Ya dan diririce saboda bai sa ran zata tambaya ba kuma da yanda yaga kamar ta dan
shiga damuwa
‘Eh, daman babanta ne zai yi tafiya saboda bashi da lafiya zasu je Egypt ayi masa
aiki, shine yace idan na shirya sunaso a daura auren kafin ya tafi.’
Ta kau da kai
Sukayi shiru na dan lokaci kowa da abinda yake tunani, ya dauko katunan gayyatar da
ya ajiye ya mika mata
‘Ga wannan saboda mutanen gidanku, Yaya Muhammad ma dazu na kai masa office.’
Ta karba jiki a sanyaye, ta kalli sunan da kwanan watan ta yi lissafi nan da nan ta
gano saura ma kwana taran kamar yanda ya fada. Ta bude baki da kyar ta ce
Ta hadiye malolon da ya tokare mata makogoro saboda takaici; wato har ya mayar da
sunanta Uwargida ma kenan?
‘To kuma tarewa zatayi ko har sai Baban nata ya dawo zata tare?’
‘A’a, ranar da aka daura zata tare, ai wannan gidan na jikin gidan Bashir na kama
hayarsa ina jin ma har an gama gyarawa idan dai ba Jafar yayi min shiririta ba kin
san shi na dora a kan neman gidan.’
Wani abu ya tokare mata zuciya a dai dai lokacin da duk wata dama da take da ita ta
kwace mata.
A da har ta fara tunanin suna da lokaci Malam ya gama aikinsa ta yanda ko an daura
bazata tare ba amma yanzu da yace mata a ranar zata tare tana jin kamar za a sami
matsala saboda jiya Malam yace mata akwai aikin da za ayi amma wanda zai yi aikin
ya tafi umra sai sati mai zuwa zai dawo sannan ayi aikin.
Da sauri zuciyarta take harbawa; ya za ayi ta iya zama da kishiya bayan itace matar
Yusuf ta rufin asiri, sai yanzu da yayi kudi yake jin zai auro wata. Gaskiya sai
inda karfinta ya kare, gobe zata kirawo Malam idan babu hali ma zata nemi wani
malamin. Ba za a zo gidanta a mayar da ita kalar kwatance ba.
Muryar Abban Sadik ta katse mata tunani yana ta wannan murmushin nasa da take ganin
kamar da gayya yake yi.
Ta yi yake
‘To me zan ce? Wannan shirin aure da ba a saka da ni ba ai dole na koma cikin ‘yan
kallo.’
‘Ya zaki ce haka, ai na miki bayani ni kaina ba wai haka na shirya ba.’
‘Ban sami lokaci na siyo miki kayan fadar kanwa ba amma da safe zan tura miki kudi
naira dubu dari biyu sai ki sayi duk kayan da kike so da kuma sauran shirye-
shiryenki.’
So take tace bata so amma ba zata iya ba domin ta san idan ta barsa to zai je ya
karawa amaryar, don haka tace
Sukayi shiru suka cigaba da kallon TV din da take gabansu, kowa da tunanin da yake
ransa.
Ta wuce ta nufi dakinta wanda yake kusa da nashi dakin, yayinda shi kuma ya bi
bayanta da kallo yana mamakin abinda ya bata mata rai bayan wancan karon da zai yi
aure bata nuna haka ba. Ya dubi katin gayyatar da ya bata yanda ta barsu a nan,ya
kawar da kai. Allah yasa dai kada ta tayar masa da wata fitna kuma.
Ita kuwa Zahra tana shiga dakin ta turo kofa ta tsaya a bayan kofar, ta saki
hawayen da take makalewa ya gangaro kan kumatunta.
Wato dai ta tabbata Yusuf aure zai yi, lallai namiji kanin ajali! Menene bata yi
masa?
Ta tuno rayuwarsu lokacin yana malamin makarantar firamare; albashinsa baya isarsu,
haka take hakura da abubuwa da yawa sannan kuma ‘yan uwanta suna yawan taimaka
mata. Ko da ya sami sauyin aiki ya fara samun cigaba bata taba tsammanin zai yi
mata kishiya ba, ta samu ta barar da wancan yanzu kuma ya dauko wannan; kuma harda
munafurci don ta tabbatar zancen da ya gaya mata na dalilin da yasa aka matso da
ranar auren kusa karya ne.
Tayi kwafa, ta bar bayan kofar ta wuce bandakin ta turo kofar, ta karasa gaban
mudubin sink ta tsaya ta dafa sink din tana kallon fuskarta a mudubi.
Babu abinda take gani sai hawayen da ta kasa daina fitar dasu; idan ta tuna yiwuwar
Yusuf dinta zai kwana da wata matar har wani daci take ji a bakinta.
Haka ta dauki lokaci tana hawaye tana kallon mudubin ba tare da ta san me take
tunani ba, saida ta fara gajiya da tsaiwa sannan ta kunna fanfon sink din ta wanke
fuskarta. Tana fitowa daga bandakin ta sami waje a gefen gado ta zauna ta cigaba da
tunanin mafita.
Sai wajen sha daya da rabi na dare Abban Sadik ya gama abinda yake, har zai kwanta
sai kuma ya fasa. Ya fito daga dakinsa ya nufo dakin Zahra; don bata saba barinsa
ya kwana shi kadai ba ko da kuwa tana jego ko rashin lafiya. Duk da ya san yau din
ya dan motsa kishinta amma dai gara ya lallabota su shirya.
A hankali ya tura kofar dakin ya shiga; tana kwance a gefen gadon a takure da kayan
da ta wuni da su gashi ko fitila bata kashe ba. Ya kalleta yayi murmushi don ya san
tabbas bacci ne ya kwasheta.
‘Bacci ya kwasheki baki ko canza kaya ba? Ko a nan zamu kwana ne?’
‘Um, ban ma san nayi bacci ba wallahi. Bari dai yanzu zan shirya na taho gara dai
mu kwana a can din.’
Kwanciya kawai Zahra tayi amma duk yanda ta so tai bacci kasa daukanta yayi, sai
bayan asuba sannan ta samu baccin ya kwasheta. Inda Allah ya taimaka mata ranar
asabar ce yara babu makaranta don haka shima Abban Sadik da yaga tana bacci sai
kawai ya fito daga dakin ya rufe mata kofa, ya zauna a falonsa yana karance-
karancensa.
Sai wajen karfe goma sannan ta farka, nan da nan ta wanke fuska ta sako kaya ta
fito falo. Ta kalleshi tayi yake sannan tace
‘Sorry Yallabai, na barka da shan shayi ba bread. Wallahi bacci ne ya kwasheni kuma
ka ki tashi na.’
Yayi dariya
‘Bari nayi sauri na hada mana breakfast, 'yan gidan ma na san sun tashi don ga
muryarsu can a kasa.’
‘Mommy, tun dazu nake nemanki Yaya Yusra ta hanani zuwa dakin Abba na kirawoki,
muna tashi ta sauko da mu kasa ta hanamu komawa kuma ta hada mana shayi ba dadi. Ai
zaki bani wani shayin ko?’
Ta riko hannunta suka karasa saukowa ta zauna a kan kujerar zaman mutum uku kusa da
Rukayya da Khadija wadanda suke zaune suna kallon cartoon, ta dorata a cinyarta
tana murmushi tana bata amsa
‘Uwata ta kaina, Yaya Yusra bata kyauta ba bari mu ci abinci sai nayi mata fada.’
Daya bayan daya yaran suka gaida Mommy, bayan ta amsa ta dubi Yusra tace
‘Ina Yayanki?’
‘Bari nayi sauri na dafa mana indomie, yau bacci ya daukeni duk an ji yunwa har an
bawa Uwata shayi mara dadi.’
Ta harareta
Suka saka dariya gaba daya, ta mike ta nufi kicin Ummi tana biye da ita.
Nan da nan ta dafa musu indomie da kwai, ta jera a dining table sannan ta hau saman
ta kirawo Abban Sadiku wanda suka sauko tare. Kafin ta sauko duk yaran sun zauna a
table sai Sadiku wanda bai fito ba har wannan lokacin, ta wuce dakinsa ta tura
kofar. Ta sameshi yana kwance rub da ciki a kan gadonsa daga shi sai gajeran wando,
motsinta ya tasheshi ya juyo yana dubanta yana mutssike ido.
‘Da kaji shigowata ba, to ka fito ga abinci can indomie na dafa, idan ka bari tayi
sanyi ba zaka dafa wata ba haka zaka ci.’
Ta juya ta fice ta wuce ta zubawa kowa abincinsa sannan itama ta zuba nata ta zauna
suka fara ci; yara suna ta hira da Abbansu ita kuma tayu shiru kawai tana cin
abincin. Hankalinta yana kan maganar aurensa, ta kasa nutsuwa.
Kafin su gama cinye abincin ita ta cinye nata tunda dama kadan ta zuba, ta mike ta
dauki kwanonta ta shigar kicin ta ajiye. Tana fitowa ta wuce sama ta koma dakinta
ta turo kofa ta cigaba da tunanin mafita.
Saida suka kusa gama cin abincin Sadik ya fito daga dakinsa, bayan ya gaida Abban
ya zauna ya ja kwanonsa wanda Mommy ta riga ta zuba masa abinci. Haka ya hakura ya
ci indomie wadda ta riga tayi sanyi saboda Abba yana zaune, da ya san Abban bai
koma sama ba jira zaiyi sai ya tashi sannan ya fito ya dafa mai dumi; don ya san
Mommy ba zata iya hanashi ba fada kawai takeyi.
Bayan sun gama karyawa nan suka zauna a falon kasa suna kallonsu, jimawa kadan
wajen Sha biyu saura Jummai mai aikin Mommy tazo. Bayan sun gaisa da yaran ta kama
aikinta, Yusra ta haye sama don ta sanar da Mommy zuwanta.
A hankali ta tura kofar ta shiga da sallama, tana daga kwance a gefen gado ta amsa
sallamarta. Ta turo kofar ta karasa ta zauna a gefen gado kusa da kafar Mommy
yayinda ita kuma ta fara kokarin mikewa zaune.
‘Mommy Jummai ta zo, ta ma fara aikinta.’
‘To.’
‘Lafiya dai kike kare min kallo kamar yau kika fara ganina Yaya?’
‘Babu komai.’
Sukayi shiru na dan lokaci; to me ma zata boye musu? Ai gara ma ta gaya musu ubansu
zai yi aure su san zaman da zasuyi da shi. Ko babu komai Yusra dama ta zama
abokiyar shawararta tunda ta ga tunaninsu ya zo daya. Da dai Rukayya ce da sai ta
boye mata don wannan sak halin ubanta ta yiwo, ko kuma halin Yaya Murja; don wani
lokacin tabbas tunaninta irin na Yaya Murja ne.
Ta danyi gyaran murya wanda ya janyo hankalin Yusra ta dubeta, ta kawar da kai tace
‘Aure Mommy!’
‘Um, ya sami wata bazawara wai mai yara biyu shine zai aureta. Next week ma za a
daura auren.’
Ta kara zaro ido
‘Hmm! Munafurci mana irin na da namiji. Ko nima ban sani ba sai jiyan yake gaya min
wai asabar mai zuwa za a daura masa aure saboda tsabar wulakanci.’
‘Hmmmn! Amma gaskiya bazawarar na ta wanki kan Abba. Tab! To yanzu kuma ina yace
zai sakata tunda bai bamu notice ba ai ba lallai mu iya kwashe kayan dakin kasa
zuwa next week ba.’
‘Wai ya kama hayar wannan gidan na kusa da gidan su Mashkur, a nan zata zauna.’
‘Kan bala’i! Har ya kama hayar gida amma sai jiya kika sani. Lallai abun babba ne
Mommy.’
A daidai nan Sadik ya turo kofar ya shigo, ya tsaya a bayan kofar yana sauraron
karshen zancen Yusra. Ya dubi Mommy yace
Yusra tace
‘Kin san fa irin auren nasa, wancan karon haka ya tashi mutane a tsaye kuma ya zo
ya fasa. Ki sa masa ido kawai kiga gudun ruwansa.’
Mommy tace
‘Hmmm!’
‘Mommy jiya fa kince zaki bani dari biyar na saka data, ita na zo tuni.’
Shi kuwa Sadik ficewa yayi yana mamaki, duk da ya san auren ba wani tasiri zai yi
ba. Duk da haka yanzu kam ya san shi dai babu wata matar da zata zo tace zata bata
masa rai ko tayiwa Mommy ba daidai ba; tabbas zai saita yarinya komai girmanta.
Musamman da yake shi din dogo ne kuma yana da zati kamar mahaifinsa, don haka yake
jin kansa komai ma zai iya.
……
Haka ta wuni ranar ba tare da walwala ba, shi kansa Abban Sadik din ya gane halin
da take ciki. Sai dai da yake ya riga ya san tana da kishi kuma ya san yayi mata
laifi sai ya kau da kansa yana fatan nan da wani dan lokaci zata huce.
Wajen karfe uku na yamma yara suka tafi islamiyya, ana yin sallar la’asar kuma
Abbansu ya shirya zai fita don haka itama ta shirya tace ya sauketa a gidan
kanwarta Suwaiba.
Saida ta ci kukanta ta koshi Suwaiba na bata hakuri sannan ta zaro katin daga
jakarta ta mikawa Suwaiban tace
‘Tsabar wulakanci sai jiya na sani kuma bayan da fari ce min yayi basu ma gama
daidaitawa ba.’
‘Wallahi zan yi maganinsu da shi da ita bazawarar tasa, zan ga shegiyar da zata zo
gidana tace zata zauna da mijina lafiya.’
Haka suka dauki lokaci Suwaiba tana bata hakuri har ta dan sami natsuwa, ba jimawa
kuma ta mike tana fadin
‘Bari kiga na tafi kafin ya shanya ni har yara su dawo daga islamiyya, na san yanzu
haka wajenta ya tafi.’
‘Ah! Yaya Zahra, shikenan kuma babu inda zai je sai wajenta.’
Tayi kwafa kawai ta nufo kofa, Suwaiban tayi mata rakiya sukayi sallama ta kamo
hanyar gida. Sai da ta iso gida sannan ta kirawo shi tace masa ta koma gida ba sai
yaje daukanta ba.
Babu kowa a gidan sai Jummai da take karasa wanke wanke, ta bata abinda zata dora
mata na abincin dare ta haye sama.
Tana zama a daki ko mayafi bata cire ba ta kirawo Mallam ta sanar da shi aure ma
saura kwana bakwai, tayi masa bayanin uzurin da Yusuf din ya bata. Bayan ya gama
sauraronta yace
‘Ikon Allah, tabbas akwai wata a kasa don babu mamaki ba haka suka barshi ba. Yanzu
haka akwai aikin da suka yi masa don ayi gaggawar daura auren. Amman kada ki damu,
da kaina zan fara aikinki wanda mukayi magana yau din nan. Sannan kuma idan ban
samu na gama ba to akwai abinda zan baki ki daga carpet ki saka ta daidai inda zata
tsallaka idan an kawo miki ita, in dai ta tsallaka to da izinin Allah rana tana
fitowa zasu fito tare ta bar gidan kenan har abada.’
Sai da tayi ajiyar zuciya tana murmushi saboda jin dadin wannan bayanin na Malam
Hatimu mai almajirai, tace
‘Kada ki damu ai lakanin da nasaba zai zo, ita kadai zai yi aiki a kanta. Ke dai ki
turo min sunanta da na mahaifinta, idan da hali ma harda na kakanta kafin ranar
Alhamis an gama aiki. In ya so sai ki aiko ko kizo ranar Juma’a ki karba. Ai tunda
sun zo da fitna sai an tashi tsaye.’
‘Hakane Malam, in sha Allah zuwa gobe ma zan turo maka sunan nata. Sai kuma maganar
abun sadaka ko?’
‘Ai kwarai kuwa, Zaki turo kamar naira dubu sittin don sai an sayi rago ma an yanka
anyi sadaka da naman, idan aiki yayi sai ki cika dubu hamsin.’
Tana ajiyewa ta kirawo Hajiya Amina ta bata labarin halin da ake ciki, ta sanar da
ita akwai kudin da Abban yace zai bata idan ya bata zata rakata sayayya kuma ranar
Juma’a zata rakata Gaya wajen Malam Hatimu. Sukayi sallama suka ajiye wayar.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
A zaune suke a garejin gidan Hajiya inda dama nan suka saba zama in ya zo zance,
hirarsu suke cikin walwala. Ya dubeta sukayiwa juna murmushi, yace
‘Ni na ishi abokai da zancen zanyi aure amma ke ko ‘yar rawar kan nan da amare
sukeyi ba kya yi.’
Ta kyalkyale da dariya
Ya kama haba
‘Wai ke ina zaki kai son girma ne? Har yanzu fa ashirin da ake kirga shekarunki.’
Yayi dariya
Tayi sauri ta sunkuyar da kai saboda yanda yake kallonta. Suka yi shiru ba tare da
ta amsa ba, ya katse shirun
‘Sai fa kin bani amsa in ba haka ba sai dai muyi ta zama a nan.’
Murmushi kawai tayi ta sake sunkuyar da kai, don haka shima yayi shiru ya zuba mata
idanu. Ta dago suka hada ido ta kawar da kanta tana murmushi tana ta juya wayarta
wadda take hannunta.
‘Aisha.’
Ya sake zuba mata ido har tana jin motsin kwayar idonsa a kan fuskarta, kallon da
yake mata ya sa ta tabbatar sai ta amsa tambayar. Ta bude baki a hankali tana
murmushi tace
‘Um.’
‘Ban ji ba.’
‘Na shirya.’
Suka cigaba da hirar tasu duk da yawanci shiru sukeyi shi yayi ta kallonta ita kuma
tayi ta satar kallonsa suna yiwa juna murmushi.
Shi Yusuf ba mutum ne mai yawan hayaniya ba ita ma kuma Aisha bata da surutu kuma
ga miskilanci, don haka sai suyita kallon kallo suna musayar murmushi.
Jimawa kadan ya mike yace
Ya fara tafiya suka jera zuwa waje don tayi masa rakiya, suna cikin tafiya ya bude
wayarsa ya dubeta yace
‘Gaya min lambar account dinki mana na saka miki ko naira dari haka kya sayi
goggoro.’
Suna karasowa bakin motarsa taji wayarta tayi kara, tana dubawa ta bude baki tana
kallonsa saboda sakon da ta gani. Ya gyara zamansa a mota yayinda tace
‘Yallabai kudin nan ai yayi yawa sai kace goggoron gwal zan siya?’
Tayi dariya
Kafin ya tambayeta maganar abinda take bukata wajen biki ya riga ya ya ke ko nawa
ta nema iya dubu dari zai bata, amma sai ta ma ki yarda ayi zance. Shiyasa ya tura
mata da dubu dari biyu, ko babu komai ta cancanci hakan don yana sonta sosai.
Dabi’unta suna burgeshi gata da kunya, shi kuma a rayuwarsa yana son mace mai
kunya.
Yana tuki yana ta tunani har saida ya kusa zuwa gidan Suwaiba sannan ya tuna Zahra
tayi masa message cewa ta koma gida, yayi murmushi ya karkata kan motar ya dau
hanyar gida.
------
Haka aka cigaba da shirye shiryen biki; duk wani abu da ya kamata a yiwa amarya
‘yan uwanta sun tsaya a kanta anyi. Duk da yaron cikin da Zahida take dauke da shi
haka ta dinga rakata wajen gyaran jiki, suka je saloon aka rangada mata kitso a
dogon gashinta. Duk lokacin da tayi kamar zata shiga damuwa sai su taru suyita
lallabarta.
Su kuwa Abdallah da Farha murna ma sukeyi za ayi wa Mamansu biki, Abdallah ne kawai
ya kan dan nuna damuwa idan yaji ana Mamansa wani gidan zata koma. Shima a hankali
Hajiya ta dinga kwantar masa da hankali don haka kowa shirin biki kawai yakeyi a
gidan.
Zuwa ranar Alhamis amarya ta dau kyalli, ranar Alhamis din da safe kannen Hajiya
tare da matar Baffa suka hadu da su Zainab suka tafi kafi. Tsaf suka gyare gidan
amarya suka kunna turaren wuta, gida ya dumame da kamshi. Ko ina yayi fes, dakuna
uku da falo ga kitchen sannan kuma da fili inda za a iya ajiye mota daya.
Ba a ce dasu su shiga gidan Uwargida ba don haka ma da suka ji yunwa sai Zainab ta
fita ta siyo musu abinci, suka ci suka karasa aikinsu suka koma gida.
……..
Ya riga ya gayawa ‘yan uwansa ba za ayi taro ba don haka mata basu zo gidan ba sai
wadanda suke zuwa gidan Hajiyarsu Allah ya sanya alkhairi. Kannen Hajiya mutum biyu
da kuma kanwar mahaifinsa tare da matar Yayansa Bello sune zasu je daukan amarya
kuma ya riga ya sanar dasu idan sun daukota kai tsaye su wuce da ita gidanta, idan
ya zo da kansa zai kaita wajen Zahran.
Sai da ya gama duk wani shiri nasa na tarbar bakinsa 'yan daurin aure sannan ya
kama hanyar gida, lokacin dare yayi don har yara sunyi bacci.
Haka Zahra ta tare shi babu yabo babu fallasa don kawo yanzu ta kasa danne kishinta
wanda bakin ciki ne yake kara mata shi; musamman idan taga yanda yake ta rawar kai
a kan auren. Bayan ta ajiye masa abincin dare ta dubeshi tace
‘Bari naje na kwanta don gobe mu da hidima saboda baki duk da dai ba taro za ayi
ba.’
‘Hidimar me kuma? Ai ba wani taro don su Hajiya ma na gaya musu ba sai mata sun zo
ba daga baya sa zo.’
Ta dan faki idonsa ta gatsina baki wanda tayi saurin biyewa da murmushin yake
‘Eh ai nima ka gaya min, amma ai naga idan aka dauko amarya wajen uwargida ake fara
kaita ayi nasiha kafin a kaita dakin miji, shi yasa zamu gyara gidan kuma na tanaji
abun tukuici.’
‘Oh, wanna ai nace ba sai sun kawota ba daga baya na kawota kawai.’
Ta kalleshi yayinda ya cika baki da lomar abinci yana kallon wayar hannunsa.
Tanada nata tanadin da tayiwa wannan zuwan na amarya amma zai rusa mata aiki,
gaskiya ba zata yarda ba. Idan shi ya kawota ba lallai tayi abunta a sirri ba
sannan kuma ba lallai ya kawota a daren ba; ita kuwa a wannan juma’ar take so ayi
ta ta kare. Ta danyi gyaran murya tare da bata rai
‘Uhm! Ashe fa naku tsarin da ban ne. Naga dai abun karramawa ce da girmama uwargida
tunda iyayenta ne da iyayenka zasu kawota, idan basu kawota sun nuna mata mu zauna
lafiya ba ai dole tazo ta kalleni banza banza…'
Ta tabe baki itama ta katseshi a daidai lokacin da kwalla take fadowa daga idonta
‘Um um ai ba sai kace komai ba wanne bari kuma? Tun yanzu ka fara raba kan gidanka!
Ka ce ba zata shigo cikinmu ba ni da ‘yayanka, yanzu kuma kace ba za ma a kawota a
nuna mata girmana ba, ai shikenan ku yi zamanki ku biyu nima na koma cikin ‘yan
kallo.’
Ta juya da hanzari ta nufi hawa sama, ya mike tsaye yana kallonta da mamaki da
damuwa
‘Haba Zarah…'
Kafin ya karasa ta haye sama tana share hawaye, ya koma ya zauna a kan kujerar
kamar wanda aka tunkuda, ya bi hanyar da ta bi da kallo yana mamaki.
Tabbas Aisha ce ta nuna ta fi son gidanta ita kadai kuma da ya gayawa Zahra bata
nuna damuwa ba, amma yanzu shi da kansa yace ba sai an kawota ba saboda gudun ayi
wani abu da zai tada rigima. Ya ma riga ya gayawa Aishan da Yaya Zuwaira cewa idan
an daukota a kaita gidanta kai tasye.
Ya dafe kai yana mamakin Zahra, wai shi da kansa ya tarwatsa gidansa kuma anki a
girmamata. Ya ma za ayi tace haka bayan duk wannan kaffa-kaffan da yake yi dominta
ne?
Ya ture kwanon abincin ya mike ya bi bayanta.
Kamar yanda ya zata a dakinta ya sameta, tana zaune a gefen gado tana tunani tare
da fitar da hawaye; ta riga ta karbo layar da Malam ya bata ta sa a wajen da amarya
zata tsallaka kuma a ranar Malam yace tayi don da gari ya waye amarya ta bar mata
gidanta, idan ba a kawo mata amaryar ba ya za ayi ta samu wannan damar?
Da yake bata hade kofar dakin ba har ya shiga bata sani ba saboda nisan da
tunaninta yayi, sai da yayi gyaran murya sannan ta dawo hayyacinta.
Ta yi sauri ta share hawayenta ta mike tsaye tana kokarin shigewa bandakinta, yayi
sauri ya kara taku biyu ya riketa.
Bai bata amsa ba ya riketa ya zaunar da ita a gefen gadon ya zauna a kusa da ita
sannan yace
‘Kiyi hakuri ki fahimceni, da kai a nace kada a kawota saboda kin san halin mata
ban sa da su wa za a taho ba daga can gidan nasu. Amma idan dai wannan ne ya bata
miki rai to ki daina damuwa za a kawo miki ita nan, tunda dama su Goggo Habiba ne
zasu daukota. Shikenan?’.
‘Ni bani da wata damuwa kuje kuyi yanda kuka tsara kawai.’
‘Ku cigaba da shirin tarbar amarya, za a kawo miki ita idan kuka gama sai su kaita
nata gidan. Shine tsarina.’
‘Uhhm!’
‘In akwai wani abu da kike bukata sai kiyi min magana.’
Tayi shiru na dan lokaci, har zai tashi tayi gyaran murya tace
‘Dama akwai kudi da zan bawa amaryar kyauta kuma sababbi ake bayarwa, to na bada
naira dubu goma a samo min sabbinsu har yanzu ba a kawo ba, ban sani ba ko zan samu
a wajenka.’
‘To babu damuwa, idan kika shigo sai na baki akwai wasu da na canza.’
Ya mike ya fice ya ja mata kofa. Ta bi kofar da harara da murguda baki kamar yana
wajen tace
Duk a gidan suka kwana ana ta hira da kuma shirin biki. Gari yana wayewa Aisha ta
kara firgicewa, hawayen da take makalewa ma yau kyaleshu tayi. Tana hawaye tana
yake duk a lokaci guda saboda yanda zuciyarta ta jagule.
A falo suke zaune kusan duk dangi ne a kewaye da ita anata raha da kokarin kwantar
mata da hankali.
Ta sha kwalliya cikin wani shudin leshi mai ado da fulawowi ruwan gwal ta yafa
karamin mayafin nan da ake kira Chantilly a kanta. Hannuwanta da kafufunta sun
dauki kunshi ga fatarta sai sheki takeyi. Kunshin yayi matukar kyau a kan fatar
tata duk da ita din ba fara bace, fuskarta babu yabo babu fallasa domin ta ki bari
ayi mata kwalliya; sai dai hakan bai hanata yin kyau ba.
Tana zaune a tsakiyar danginta amma kamar ace kyat! ta ruga da gudu.
‘Mama Baba Abba ya zo, da Anti Bushra da Anti Rakiya harda ma Sultan da Hajiya
karama. Bari ma naje na shigo da su na manta.’
Kafin a bata amsa ta mike ta sake fita da gudu cikin murna da farin ciki tana ta
tsalle-tsalle.
Take jikin Aisha ya kara sanyi, ta dubi Zahida wadda take gefenta suka hada ido
Zahidan tana kokarin kara mata kwarin gwiwa da idonta; nan da nan hawaye ya kwace
mata ta mike da gudu tayi dakinta. Kafin ayi magana Zahida ta mike ta bi bayanta
Anti Uwani tana fadin
Ko saurarenta bata yi ba ta rufa mata baya suka turo kofar. Ta kusa kaiwa bandaki
Zahida tace
‘Ya Aisha.’
Ta juyo ta tsaya, yayinda Zahidan ta kara matsowa. Ta fada jikin Zahida suka
rungume juna; duka su biyun kowacce tana fitar da hawaye, sai da suka dauki lokaci
a haka sannan Zahida tayi kokari ta banbare Zainab daga jikinta saboda yanda take
ji yaron dake cikinta ya fara takura yana zullo. Suka rike hannun juna suna kallon
juna suna hawaye, Zahida ta jasu suka karasa suka zauna a bakin gado. Aisha ta
matse hannun Zahida ta bude baki cikin rawar murya tace
‘Hida zan iya kuwa? Hida Mustafa ya tafi da rabin zauciyata, ya za ayi na iya
sallamawa wani mutumin ruhi na?’
Ta kifa kai a cinyar Zahida ta cigaba da kuka Zahida tana shafa kanta tana share
nata hawayen. Da kyar ta lalubo bakinta tace
‘Ki yi hakuri Yaya Aisha, ki cigaba da yi masa addu’a. You will be fine in sha
Allah kuma wannan auren da zakuyi shine zai tabbatar da cewa kin karbi hukuncin
Allah a kanki, ki cigaba da addu’a.’
Motsin bude kofa ya sa Zahidan ta waigo yayinda Aishan ta dago kanta fuskarta duk
hawaye. Bushra ce ta turo kofar a hankali ta shigo da sallama ta mayar ta rufe
kofar.
‘Anti Bushra.’
Ta karasa ta tsuguna a gaban gwiwoyin Aisha ta dafata tana dariya
Zahida tace
‘Kiyi hakuri Anti Aisha kin ji, wannan shine hukuncin Allah. Allah ya sa miki
albarka a rayuwarki. Hajiya tana gaisheki, kuma don karta sakaki kuka ne taki zuwa
amma duk da haka sai da kikayi kukan.’
‘Anti Hida kin barta zata latse mana hancin yaro saboda kukan amarci.’
Sukayi dariya gaba daya, Aishan ta mike tana dariya ta shige bandaki tana fadin
Sai da tayi da gaske sannan ta iya tsayar da hawayenta ta fito ta gyara fuska, suka
fito aka cigaba da bikin wanda dama amaryar da kanta tace bata son kida.
Ana saukowa daga sallar Juma’a aka daura auren Yusuf da Aisha.
Kafin ayi sallar magriba matar Yaya Abubakar ta tattara yaranta ta hada da Abdallah
da Farha da kuma yaran Zahida suka wuce gidanta; haka Hajiya ta sakata saboda yanda
take ganin idan an zo daukar amarya zasu sata kuka.
Ana idar da sallar magriba Anti Uwani ta leka dakin Aisha tacewa Zahida su shirya
‘yan daukar amarya sun taho. Nan take hawaye ya sake ballewa a idon Aisha, haka
Zahida da Zainab suka sakanta a gaba suka tayata shiryawa.
Atamfa ta saka dinkin riga da siket, rigar fitted ce shi kuma siket din dogo ne mai
tattara a baya. Ta nade jikinta da farar laffaya wadda Sajida ‘yar kanwar Hajiya ta
aiko mata ita daga Switzerland; inda take zaune da mijinta. Kana ganin laffayar nan
ka san an kashe kudi, fara ce kal da zanen shudayen fulawowi a kasanta ga duwatsu
sai kyalli take. Tunda aka ware laffayar kamshi ya cika dakin saboda yanda Zahida
ta dauki lokaci tana yiwa laffayar nan turaren wuta.
Tayi matukar kyau musamman da yake an samu ta daina kukan, sai kwalla kawai wadda
da zarar ta fito take gogewa da tissue din da yake hannunta.
Wajen karfe takwas na dare masu daukan amarya sukayi sallama a gidan, ba tare da
wani bata lokaci ba aka basu amarya. Anti Uwani da kuma Inna wato kanwar mahaifinsu
tare da su Zahida sune suka tafi rakiya.
Sai bayan sun kama hanya sannan Yaya Bello ya kirawo Yaya Saratu ya sanar da ita
idan sun dauko amaryar su fara kaita gidan Zahra sannan su kaita dakinta. Shi kuma
Yusuf Zahida ya kirawo ya sanar da ita domin da sun gama maganar gidanta za a
kaita.
Ba tare da wata damuwa ba suka kama hanyar unguwar Sokoto road inda nan ne za a kai
amarya.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
9
An riga an bawa ango hutun aiki na ‘yan kwanaki don haka ranar Juma’a ma sai wajen
sha daya ya tashi daga bacci. Bayan ya gama karin kumallo ya shirya abokinsa Alhaji
Safiyanu yazo suka fice, sai da suka karbi kayan da ango zai sa daga wajen guga
sannan suka wuce guest house din Alhaji Safiyanu inda daga nan zasu shirya su wuce
daurin auren.
Yana fita itama Zahra ta hau shiri, nan da nan aka gyare gida aka sa turare ya
dauki kamshi. Zuwa azahar aminiyarta wato Hajiya Amina ta karaso da abincin da baki
zasu ci domin ita aka bawa kwangilar, bayan sun kule a daki suna zaune a gefen
gadon Zahra Amina ta dubeta tace
‘Baki da matsala kawata, sai wani sheki kikeyi kamar ba wadda za ayiwa kishiya ba.’
‘To me yafi raina kawata, auren dare daya ai ba zai daga min hankali ba.’
‘Hakane.’
Suka gama shirya yanda za ayi sannan suka sauko falon aka cigaba da hidima inda
‘yan uwan Zahra suka zo aka hadu.
Daga baya wajen la’asar kuma Hajiya Karima matar Yaya Bello ta iso tare da Maimuna
matar Musa kanin Yusuf din da yaransu.
……..
Ana cikin kiran sallar magriba Hajiya Amina ta mike ta yiwo alwala a dakin baki da
yake kasa, ta tsaya a falon ta dubi Karima tace
‘Yaya Karima kuyi alwala sai ayi Sallah a dakin don a samu a share falon a gyara
tunda ance da anyi sallar magriba za a kawo amaryar.'
Nan da nan kuwa aka mike, aka fara alwala ana Sallah.
Kana shigowa falon kujerar zaman mutum uku ce ta bawa kofar baya, don haka idan
mutum ya shigo akwai waje tsakanin kujerar zaman mutum uku da Kuma ta mutum daya
inda ta nan ne mutum zai karasa tsakiyar falon ga zauna. Duk wanda ya shigo ta nan
wajen yake wucewa don haka Zahra da Amina suka yanke shawarar a nan za a ajiye ‘yar
layar da Malam ya ce a saka inda amarya zata tsallaka.
Da fari Amina ta so a saka a kasan dan carpet din da yake bakin kofa amma Zahra ta
sanar da ita shi ana yawan dagashi saboda yawan wucewa, idan aka saka a nan akwai
yiwuwar wani ya gani. Wannan babban center carpet din kuwa tunda kafar doguwar
kujera a kansa suke ba a dagashi, gara su saka a nan tunda dole ta nan za a wuce da
ita.
Ana gama shara Hajiya Amina ta faki ido ta daga carpet din ta ajiye layar ba tare
da kowa ya kula ba, daga baya suka idar da sallah suka fito aka zauna aka cigaba da
hirarraki. Daga baya makota suma suka shisshigo aka hadu ga yara sunata guje-guje
don haka aka cika falon.
Tunda ‘yan kawo amarya suka daukota suka kamo hanya Yaya Saratu ta kirawo Zahra ta
sanar da ita sun taho kamar yanda ta nema; a cewarta don su kintsa. Karfe takwas da
kwata motocin amarya suka tsaya a kofar gidan Zahra.
Sai da kowa ya fita daga mota sannan aka bude motar amarya, Inna ce ta fara fita
sannan amaryar ta fito yayinda Goggon Yusuf din ta fita ta daya gefen suka saka
amarya a tsakiya Goggo na rike da hannunta. Duk matan da suka fito daga motocin su
suka wuce gaba don haka amarya ce a karshe da su Goggo, sai Anti Karima matar Yaya
Bello wadda itace a karshe ta dafe musu baya.
Suna shiga falon aka fara zabga guda, nan da nan wasu daga cikin matan dake falon
suka mike.
An shigo da amarya sai kuma aka dan sami tsaiko mutane sun dan yi yawa ana ta
magana su gafara a karasa a zaunar da amarya. Kafin su gama budawa Anti Karima ta
tabo Goggo ta nuna musu daya gefen tace
‘Goggo ku zaga ta nan mana, yara sun cushe nan din yanzu sai na fitar da su.’
Don haka Goggo ta ja amarya suka kewaye kujerar mutum biyu suka shigo ta daya gefen
tsakanin kujera da TV, nan amarya ta kwabe takalminta fuskarta lullube da mayafi
aka karasa da ita aka zaunar da ita kusa da Zahra bayan an tashi matar da take
zaune a wajen.
Nan take zuciyar Zahra ta cushe, suka kalli juna ita da Amina dake gefenta Amina
tayi mata alama ta nutsu don haka ta hadiye takaicin da ya taso mata ta waske.
Nan su Goggo suka saka su a gaba da nasiha a kan su zauna lafiya, bayan sun gama
akayi addu’a. Duk yanda Amina taso ta canzawa layar nan waje bai yiwu ba domin
yarane ma a daidai wajen a tsattsaye suna kallon amarya suna surutunsu.
Bayan an Shafa addu’a Amina ta mikawa Zahra canjinta naira dubu goma ta dorawa
amarya a cinyarta tana fadin
Zahida ta sa hannu ta dauke suka yi godiya amarya ta mike, daidai lokacin Amina ta
mike ta wuce musu gaba tana kokarin su bi ta daya gefen inda ta saka layar dai-dai
lokacin Inna tabi ta daya gefen tana fadin
Don haka suka bi ta inda suka shigo ana ta zabga guda, suka fice amarya ta bar
falon yana kamshinta.
Makotan Zahra duka sukayi mata sallama suka wuce don suna son su ga gidan amarya,
nan da nan zugar yara suka bisu harda ‘yan uwan Zahra ma don babu wanda yaga gidan
sai yanzu kowa yake so yaje ya gani.
Aka barsu daga ita sai Amina da Yaya Murja sai Yusra wadda itama take taya uwarta
kishi.
Suna ficewa Yusra ta shige dakinsu ta turo kofa, Yaya Murja ta dubi Zahra da Amina
tace
‘Kowa ya tafi ganin gidan amarya, to Allah ya baku zaman lafiya. Bari na dauko
wayata a dakinki Zahra can na sa chaji.’
Tana hayewa sama Zahra ta dubi Amina rai a bace harda kwalla a idonta
‘Kin gani ko Aminoni, kin gani ko! Na gaya miki Karima bata kaunata tun tuni, tunda
aka fara maganar auren nan ita da mijinta suke rawar kai da shisshigi. Ita ta hana
ayi mata kishiya amma don iskanci duk wadda za ayiwa itace a gaba wai ita nan matar
Babba a dangi. Wallahi sai na gyarawa matar man zama ko da wa take yawo.’
‘Ki bar wannan maganar, yanzu zan dauke miki layar tunda na san gobe da safe zai
kawo miki ita in ya so sai kiyi amfani da wannan damar kinga daga ku sai ku.’
‘Aminoni ban so matar nan ta wuce gobe a gidan nan ba, amma bari Allah ya kai mu
goben zan yi maganinta.’
Motsin saukowar Yaya Murja ne ya dakatar da ita, take kuma ta sauya zancen
‘Ai hakuri ne naki, kece babba idan baki bada wata kafa ba babu abinda zai faru.’
‘Gara dai ki gaya mata, ki rike girmanki babu matar da zata fiki a wajen miji. Kuma
gashi ma ke danginsa duk suna sonki ai ke idan tace zata ja dake ma sune zasuyi
miki fadan.’
A hankali mutane suka fara dawowa gidan kuma suna yi mata sallama domin wucewa
gidajensu. Daga baya Aminan ma tayi mata sallama bayan ta bata ‘yar karamar layar
wadda ta saka a aljihun doguwar rigar da take jikinta, ta rakata kofar falon sukayi
sallama ta fice.
……..
Sai wajen sha daya na dare saura sannan Alhaji Safiyanu ya kawo ango gida da
ledojinsa guda biyu; daya na Zahra, daya kuma na Aisha.
Gidan Zahra ya fara shiga, lokacin duk yara sunyi barci don haka babu kowa a falo.
Kai tsaye ya wuce sama.
Dakinsa ya wuce kai tsaye, kamar yanda yayi tsammani Zahra bata ciki. Don haka ya
ajiye kayansa ya dauki ledar da ya shigo da ita ya wuce dakinta.
Tana kwance a kan gado sanye da kayan bacci an kashe fitila da alama bacci takeyi,
ya kunna fitlar tare da yin gyaran murya ya karasa ciki da sallama. Ta juyo ta
dubeshi sannan ta tashi zaune a tsakiyar gadon, yayinda shi kuma ya zauna a gefen
gadon.
‘Sannu da zuwa.’
Da murmushi ya amsa
Yanayinta da kuma yanda take bashi amsa ya fahimci bata da walwala kuma idan yaja
hirar zasuyi rigima, don haka ya ajiye ledar a kan durowar gefen gadonta yana fadin
‘Ga wannan ke da yara, sai dai naga duk kunyi bacci sai ki saka a fridge kwayi
breakfast da shi.’
‘Mungode.’
Suka dan taba hira tana ta faman cijewa saboda kada tayi kuka a gabansa, shi din ma
da yake yana sauri ya tafi wajen amarya kafin Zahran ta fara wata fitnar sai kawai
yayi mata sallama yace ta rufe musu gidan.
Ta biyoshi a baya har suka zo bakin kofa sannan ta rufe musu kofar shi kuma ya
wuce, ya dauki ledarsa a mota ya nufi gidan amarya.
……….
Kamshin da ya cika gidan shi ya fara yi masa maraba, ya riga ya san ita kadai ce a
gidan don haka yana shiga ya mayar da kofar ya kulle. Ya karasa ya ajiye ledar
hannusa a kan dining table, ya juyo ya karewa falon kallo yana murmushi.
Ya shige dakin yana rike da Babbar rigarsa, tun kafin ya karasa ciki ya hangota a
kan gadon nade da laffayarta ta kashingide daga zaune a gefen gadon. Ya karasa ciki
da sallama wadda ta farko da ita daga gyangyadin da takeyi, ta gyara zama tana amsa
sallamar.
Ya karasa ya zauna a kusa da ita yana kallon fuskarta yana murmushi yayinda ta
mayar masa da murmushinsa tana kokarin boye kwallar da take makale a idonta. Ya
kama hannunta na hagu yana kallon lallenta, ta bi hannunsa da kallo yanda ya rike
hannunta. A take hawayen da take boyewa ya kwace; Mustafa; ta kasa cire shi daga
kwakwalwarta tunda aka ce an daura mata aure.
Sai da ya dauki lokaci yana lallashinta sannan ta iya samu ta tsayar da hawayenta.
Ya tayata ta warware laffayarta suka ci abinci sannan sukayi alwala sukayi Sallah.
Sai da yayi da gaske da ita sannan ta iya canza kayanta ta saka kayan bacci, yana
ta yi mata dariya kamar wata budurwa saboda kunyar da take ji. Bayan sun gama ya
kashe musu fitila suka kwanta, rungumeta kawai yayi saboda ya kula da yanda take
cikin damuwa kuma ga bacci da take ji. Ya danne duk wata bukata tasa ya kyaleta
zuwa gobe, kafin nan ta kara sakewa ta sami nutsuwa.
……
Kusan lokaci guda suka tashi da asuba, nan da nan sukayi wanka suka yi Sallah. Yayi
zaton zata koma bacci don haka ya fice daga dakin ya komo falo ya fara kokarin hada
TV. Bai jima da fitowa ba itama ta fito, suka zauna yana hada TV din suna hira, har
ya gama suka zauna suna kallo.
‘Nifa yunwa nake ji, bari na duba ko ruwan shayi na sama mana.’
Ta mike ta nufi kicin, yayinda shima ya nufi dining table inda ya ajiye ledar da ya
shigo da ita jiya. Ya zazzage kayan shayin da burodin da ya siyo ya kwasa ya kai
mata kicin din.
Yayi tunanin Zahra zata basu breakfast amma baya so yayi maganar don bai san yanda
za su dauki abun ba. Nan da nan Aisha ta hada musu shayi da burodi ta dumama
ragowar naman jiya suka zauna suna kallon TV suna cci
____
Tana zaune a falonsa ita kadai tana shan shayi, shayin kawai zata iya sha a halin
yanzu domin kanta ciwo yake yi saboda yanda bata samu tayi bacci ba ko daya. Kwana
tayi tana tunanin yanda za ayi Yusuf, nata ita kadai, yaje ya kwana da wata mace.
Kuma haka ta tashi tana ta wannan tunanin tana tsaki.
Tun sassafe Jummai ta zo don haka ta barta da yaran a kasa ta dawo sama ta zauna.
Koda Jumman ta shigo saida ta tambayeta ko za a yiwa amarya abinci amma tace a’a.
Ta san ya kamata tayi amma bazata yi ba, domin da ana so ta bata abincin ai da a
nan cikin gidan za a saka amaryar su zauna tare.
Karar wayarta ce ta katse tunaninta, ta daga wayar ta duba, Abban Sadik ne.
‘Alhamdulillah. Gamu nan shigowa yanzu zan kawo miki kanwar taki.’
A take ta tuno abinda ya kamata ta fara yi, inda ta tashi da hanzari ta koma
dakinta. Ta san dai inda suka boye layar nan jiya tabbas Abban Sadiku ta nan zai
shigo falon don haka gara ta nemo layar taje ta mayar ayi ta ta kare kawai.
Tana shiga dakin ta nufi wardrobe inda ta rataye rigar da ta saka jiya a saman
wardrobe din, ta zura hannunta a hankali cikin aljihun rigar ta laluba taji babu
komai. Ta koma ta daya gefen ta zura hannunta a dayan aljihun ta laluba a hankali
bata ji komai. Mamaki ya bayyana a fuskarta, ta fizge rigar daga saman wardrobe din
ta karasa ta bajeta a kan gado ta sake lalube aljihun duka biyun bata ji komai ba.
Ta daga rigar ta zazzage babu a binda ya fado, ta zauna a kan gado tana kallon
rigar tana mamakin inda layar ta shiga.
Tabbas ba mantuwa tayi ba, a hannunta Amina ta bata layar kuma tabbas a aljihun
rigar ta saka. Bata cire ba ta barta a kan da safe ta dauke; to a ina layar zata
fadi?. Gashi tsaf aka share gidan jiya kuma yau ma Jummai har tayi shara.
Ta mike ta koma gaban wardrobe din ta sake dubawa ko a kasa layar ta fado, bata
sami komai ba. Ta dawo ta zauna a gefen gadon tana tunani; to ina layar zata shiga?
‘Ikon Allah!’
Ta fada a fili.
Motsin taba kofar ne ya dawo da ita hayyacinta, Yusra ce ta shigo da sallama tace
Taja tsaki
‘Mtsewwww! Kice masa ina wanka.’
Ta fada bandaki ita kuma Yusra ta juyo ta [Link] jin lokacin da Abban ya shigo
dakin ya fita. Har ta gama wankan nan bata gano inda layar nan tayi ba don haka ta
hakura tunda Aishan ta riga ta shigo ta zauna a falon. Haka ta fito ta zabo leshi
mai kyau ta shirya tsaf ta fesa turarukanta masu kamshi sannan ta sauko.
Tun kan ta karasa saukowa ta hangosu; Aishan tana zaune a kan kujerar zaman mutum
daya shi kuma Abban yana kan kujerar zaman mutum uku. Sadik da Yusra tunda suka
gaisheta suka bar wajen, don Yusra ma tunda ta gaisheta ta haye sama bata sauko ba.
Rukayya ce a zaune a kusa da Aishan sai Ummi da take ta faman yi mata surutu.
Ta karaso da sallama, ta wuce kai tsaye ta zauna a kusa da Abban Sadik. Tana
murmushi ta dubeshi
Yaji dadin yanda ya ganta da fara’arta don haka shima tashi fara’ar ta karu
Suka gaisa cikin walwala, Zahra ta umarci Jummai ta kawo muta ruwa da lemo, ta dubi
Abban Sadika tace
‘Ka san kasa tashi nayi saboda gajiya shi ya sa ban samu na dafa muku abincin safe
ba, ko a kawo muku yanzu ku karya.’
Tace
‘A’a na koshi.’
‘To Zahra ga kanwarki nan, naga ma kun riga kun saba kuma ban ga alamar matsala ba.
Allah ya hada min kanku. Na gaya mata duk abinda take bukata ta nemeki, yara kuma
yanzu sun zama masu gida biyu, duk inda suka shiga daya ne.’
Zahra tace
‘Hakane, Allah ya bada zaman lafiya. Ai ga uwata sarkin kaudi har ta makale mata.’
Yana wucewa Zahra ta sha kunu ta bata rai, suna hada ido da Aisha ta dauke nata
kana saboda yanda taga sauyin yanayin.
‘Ku kuma kowa ya bace kuna zaune kuna biya bakin mutane, tashi ki bani waje.’
Nan da nan suka fice daga falon ya zama daga Zahra sai Aishan, tana ta faman bata
rai ita kuwa Aishan ta ma kasa hada ido da ita tunda ta kula da yanda yanayinta ya
canza.
Jimawa kadan ta tashi ta kashe talabijin din dake kunne a falon ta haye sama ya
zama Aishace ita kadai a falon.
Ta cika da mamakin yanda kiri-kiri Zahra tayi mata fuska biyu a cikin abinda bai fi
minti ahsirin ba .
Sai da aka yi wajen minti talatin sannan taji motsin saukowarsu, yana tafe Zahra
tana biye da shi rike da jakarsa ta computer da litattafansa. Sai wani faman
murmushi take suka jero suka shigo falon, ta dubi Aisha da fara’a tace
‘A’a, ina ‘yayan naki sukayi Anti Aisha shine suka barki ke kadai?’
‘Uhm.’
Ta mika mata 'yar karamar leda dauke da turaren wuta da wata karamar burner tace
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
10
Saida amarya ta kwana biyu sannan su Yaya Zuwaira suka kawo mata ziyara tare da
Abdallah da Farha. Nan suka wuni ana ta hira, sai bayan la’asar sannan suka tafi,
suka barta da kewarsu.
Haka Yusuf ya cigaba da kwantar mata da hankali har ta samu ta dan kara sakewa.
Ranar Talata ne ya kama kwana uku, don haka ranar ne zai koma kwanan Zahra. Ya riga
yayi musu bayani da daddare zai dinga canza waje kwana don haka wadda zai kwana a
wajenta ita zatayi masa abincin dare.
Bayan ya dawo daga sallar magriba ya sameta a falo tana kallon TV, bayan ya amsa
sannu da zuwanta ya zauna a kusa da ita suna fuskantar juna, yace
‘Yanzu zan wuce wajen yayarki, amma gaskiya bana son barinki ke kadai. Kinga da a
can kike da bani da wata damuwa.’
‘To ai ni ban ce maka ina jin tsoro ba, tunda idan ma wani abun ya taso zan iya
kiranka ko na kirawo Mommy ko?’
‘Hakane, amma dai bari naje gidan sai na kawo miki Yusra ta zo ta taya ki kwana.’
Sai da yayi da gaske sannan ya Kanye jikinsa ya tashi yayi mata sallama ya fice a
kan yanzu zai dawo ya kawo mata Yusra.
…
A falo ya samesu gaba daya banda Sadik, bayan Mommy ta amsa sallamarsa duka sukayi
masa sannu da zuwa. Ya karasa ya zauna a kan kujerar zaman mutum uku kusa da Mommy,
ya dubeta yace
‘To ai kaga dalilin da yasa nace a hademu kace tace bata so, ai na zata zata iya
kwana ita kadai.’
‘To ai gasu nan duk wanda ka daukar mata, sai dai Yusra itace take tayani kula da
kannenta idan suna bacci.’
‘Abba bari na shirya muje, amma fa ban yi homework dina ba, ga hadda ma ina so Yaya
Yusra ta biya min.’
‘Kada ki damu itama Antin zata biya miki, kwaso kayanki kafin na sauko daga sama
sai na raka ki.’
‘Ke wai wacce irin yarinya ce Rukayya, kin ji kowa ya ce ba zai je ba sai ke uwar
sakarci ko? Idan ya kuma zuwa yace wa zai je kika amsa sai na ci mutuncinki
wallahi, kin ji na gaya miki.’
Tayi tsuru-tsuru tana mamakin yanda kawai don tace zata kwana gidan amarya abun ya
bata ran Mommy haka. Yusra ta harareta tace
Tare suka sauko ita da Abban tayiwa Mommy sai da safe suka wuce, yana kula da yanda
yanayinta ya canza don haka ya tabbatar fada Mommy tayi mata.
Bayan ya rakata ya tabbatar Aisha ta kulle kofa sannan yayi musu sallama ya dawo.
Dakin baki Aisha ta nuna mata ta ajiye kayanta, sai a hankali Rukayya ta sake
sukayi homework din kuma ta biya mata haddarta, suka dan taba hira suna kallo
sannan wajen karfe goma na dare aka dauke wuta.
Aisha ta shiryo suka kwanta tare da Rukayya a dakin baki.
……
Saida ya gama duk abinda yakeyi, ya zauna a falon sama yana kallon TV. Bayan yara
sun kwanta itama ta zo ta zauna a kusa da shi, jimawa kadan ya dubeta yace
‘Zahra.’
‘Yallabai.’
‘Ban ji dadin abinda kikayi ba, don Allah ki bar yaran nan su yiwa Aisha duk abinda
take so wanda bai sabawa addini ba. Ina laifi idan yara sun tayata kwana, amma nayi
magana kince ai ita ta zabi haka. Kuma Rukayyan ma saida kikayi mata fada saboda
kawai na sakata aiki tayi.’
‘To ni me nace, shikenan ba zan fadi ra’ayi na ba saboda matarka. Yara kuma ai naka
ne, ni babu wanda na hana idan ma Rukayya ce ta gaya maka nayi mata fada to karya
takeyi.’
‘Ni dai don Allah kiyi min alfarma ki bari a zauna lafiya, don Allah.’
‘Uhm.’
Sukayi shiru na dan lokaci, daga baya kuma ta tashi ta wuce dakinsa ta kwanta tana
matse kwalla. Wato daga ya dana dadin amarya kwana uku kacal har ya fara nema yayi
mata fada a kan matarsa, lallai zata gyara musu zama. Haka ta kwana zuciyarta babu
dadi.
Daga wannan lokacin ya zama kullum idan zai kwana gidan Zahra to Rukayya ce take
taya Aisha kwana, tun tana dagewa har ta hakura. Kuma sai ya zama jininsu ya hadu
da na Aishan suka zama kamar wasu kawaye duk da dai Rukayyan tana shan gori a wajen
Mommy da Yusra.
-----
Ranar Alhamis da magriba bayan ya gama shirinsa zai koma wajen Aisha Mommy take
gaya masa ita da yara zasu je wajen Hajiya gobe Juma’a don sun kwana biyu basu je
ba. Har ya fita ya dawo yace mata zai gayawa Aisha don haka idan sun shirya suyi
mata magana sai su tafi gaba daya tunda driver ne zai kaisu. Yayi mata sallama ya
wuce.
----
Itama Aishan yana shiga ya sanar da ita gobe da yamma zasu je gidan Hajiya da su
Zahra, don haka da gari ya waye yana fita office ta kama hidimarta don tayi sauri
ta gama. Ya riga ya gaya mata sai bayan masallaci amma duk da haka tana gama
aikinta wajen sha biyu ta sa hijabi ta nufi gidan Zahran.
Babu kowa a gidan sai ita kadai da Jummai wadda take share tsakar gida, tun a nan
suka gaisa da Jummai ta wuce ciki.
Tana zaune a falo tana ta faman latsa waya tayi sallama ta shiga bayan ta amsa
mata. Da fara’arta ta karasa ciki ta zauna a kujerar mutum daya.
‘Lafiya kalau.’
Sukayi shiru na dan lokaci, ita Zahra ta cigaba da duba wayarta kamar babu mutum a
wajen yayinda ita kuma Aisha take mamakin wannan tsare gidan da muzuran da ake
mata. Ta yi dan gyaran murya tace
‘Uhm, Abban Sadik yace zamuje gidan Hajiya da yamma shine na leko mu gaisa. Idan
kun shirya ko yara suyi min magana sai mu tafi.’
‘To.’
Ta mike tsaye tayi mata sallama ta fice, ita kuma tabi bayanta da harara harda
kwafa saboda kishi.
Ta tsani ganin matar nan, gashi dai an ce bazawara ce amma kamar budurwa. Kuma ta
zata Malam Sule direbanta ne ita kadai amma za ace su wani hada fita.
Sai wajen karfe hudu saura sannan Zahra ta shirya, ita da yaranta gaba daya banda
Sadik, domin shi yace ba zai je ba. Suka fito gaba daya suka shiga mota, har Yusra
zata shiga gaban mota Mommy tace ta dawo baya. Don haka suka shiga bayan motar gaba
daya, ita da Yusra, Rukayya, Nana da kuma Ummi duk da wajen zaman Ummi bai kai na
mutum daya ba.
‘Malam Sule ka tsaya a kofar gidan matar Abba da ita zamu tafi.’
Suna fitowa yayi parking a gate din Aisha ya latsa honk, ya juyo yacewa Yusra
Mommy tace
‘Kayi mata honk din zata fito ko kuma ka buga mata gate.’
Yanayin da tayi maganar ya sa babu damar musu don haka kawai sai ya fita ya buga
gate din, bugu daya ta bude. Cikin girmamawa ta gaisheshi tace
Jimawa kadan ta fito ta mayar da gate din ta rufe ta karaso jikin motar ta bude ta
gefen da Yusra take zaune tare da sallama tana fadin
‘Yaya Yusra dan matsa na zauna, ko Nana ce zata koma gaba sai mu zauna a bayan.’
Dukansu suka kara babbakewa Yusra ta banka mata harara yayinda Rukayya ta sunkuyar
da kanta, Mommy tace
Mommy tace
‘Gurin ba zai isa ba ai baki gani bane, ki zauna a gaban mana ke.’
‘Ina ga ai ko Ummin Abban aka miko nan ai wajen zai isa Hajiya.’
‘Malam Sule, ka san dai Yallabai baya barin yara zaman gaban mota ko? Ta shiga
gaban kawai muje in ba haka ba ka kaimu sai ka dawo ka kaita.’
A tunzure tayi maganar don haka Malam Sule yayi shiru.
Aisha ta dan ja baya, nan da nan Yusra ta ja kofar motar ta rufe yayinda Mommy tace
‘Mu tafi.’
Ta juya zata koma gidan sai kuma tayi wani tunani; yanda taga yanayin matar nan
bata jin zata bar Malam Sule ya dawo kuma idan taje bata san me zata fada a can ba
idan kuma ya dawo bata je ba bata san irin sharrin da za tayi mata a wajen maigidan
ba. Ta riga ta san gidan don yayi mata kwatance kuma a bakin titi ne, don haka ta
juya ta nufi titi, nan da nan ta sami motar haya ta bisu.
Zuciyarta har tafasa takeyi saboda takaici, ya za ayi ta shiga gaban mota da direba
bayan ga yara. Ko da ma yaran ba zasu shiga gaban motar ba idan suka mammatsa bayan
motar ma zai ishesu har ita. Amma saboda an shirya sharri da wulakanci ace ta shiga
gaban mota, kuma a ja mota a tafi a barta.
Nan da nan ta isa gidan, kafin ma tayi tambaya ta gane domin ta hango motar Malam
Sule a kofar gidan, ta sallami mainmota tana juyowa Malam Sule ya fito daga motar
yana rage tsawo
‘Ranki ya dade tahowa kika yi? Don Allah kiyi hakuri, Hajiya ce tace na jirasu idan
na mayar da su sai na taho dake.’
‘Babu komai.’
Tuni Mommy ta riga ta yi musu bayani cewa Aishan ce tace bazata biyo su ba sai dai
a kaisu a dawo a kaita don ba zata hada tafiya da su ba. Take Hajiya tace a gayawa
Malam Sule kada ya koma wanda dama Mommy ta riga ta gaya masa. Zancen suke mayarwa
ta shigo, Hajiyan ce ta amsa sallamar ta, ta karasa ciki jikinta babu kwari saboda
kallon da akeyi mata.
Ta wuce ta zauna daga gefen Hajiya inda yake da dan sarari, cikin sanyin murya ta
gaida Hajiya wadda ta amsa mata kamar a fusace.
Jikinta ya kara sanyi sosai, don haka ta gyara zama ta sunkuyar da kai tayi shiru
tana wasa da yatsunta.
Suka cigaba da hirarrakinsu kamar babu ita a wajen, don Anisa ma ko gaisheta bata
yi ba. Nawal da Ummi ne kawai suke kulata da yake ta dan ja su da wasa.
Ba ta dade da zama ba Hajiya ta tashi ta shige daki, tana shigewa Mommy ta fice ta
koma tsakar gida inda Hindu mai aikin Hajiya take zaune a tabarma ta zauna. Kafin
wani lokaci duk sun fice sun barta ita da Rukayya.
Ita kanta Rukayyan so take tayi mata magana amma ta kasa, bata jin dadin yanda ake
mata amma ba zata iya yin komai a kai ba.
Jimawa kadan Mommy ta cewa Hindu ta yiwa Hajiya magana zasu tafi. Ba jimawa ta fito
ta wuce Aisha da Rukayya a falo ba tare da tace komai ba ta karaso tsakar gidan.
Suka taso gaba daya sukayi sallama da Hajiya, nan take Rukayya ta fito Aisha na
biye da ita itama tayiwa Hajiya sallama.
Sai da Hajiya ta bata rai sannan ta amsa, ta kauda kai. Yara suka wuce Mommy na
biye da su tare da Anisa don ta yi musu rakiya. Aisha ta bisu a baya tana shafa
jakarta, kudi ne dubu goma a ciki ta kawowa Hajiya amma bata ga fuskar bayarwa ba
don haka kawai ta bisu suka fice.
Suna fitowa Yusra ta shige gaban mota Mommy da sauran yaran suna kokarin shigewa
baya Aisha ta wucesu ta karasa bakin titi. Suka bita da kallo, Malam Sule ya
yunkura zai bita Mommy tace
Tana tsayawa kuwa ta sami mota don haka kafin ma su juyo ta shige mota direba ya
ja.
Mommy ta dubi Anisa wadda take tsaye rike da hannun Nawal tace
‘Kin gani ko? Ko kallo bamu isheta ba saboda ta raina ni. Ai shike nan.’
Aisha tana zama a bayan tasi din da ta shiga kwalla ta fado mata. Wannan wane irin
sharri ne, kallon da ake mata a gidan Hajiya ta tabbatar wani sharrin Zahra tayi
mata. Ta kula da yanda bayan sun fito Yusra ta zauna a gaban mota wato ta zo su
tafi, ita kuma tunda ita ta kawo kanta to ita zata mayar da kanta shi yasa ma ta
wuce su.
Har taje gida zuciyarta tana tafasa saboda takaici, da yake tana shiga gidan akayi
magariba sai kawai ta yi Sallah sannan ta zauna tana tunani; ita kuma wannan nata
salon kishin kenan? To haka zasuyi ta zama kenan? Lallai akwai aiki.
-----
A al’adarsa kusan kullum idan ya taso daga aiki sai ya biya gidan Hajiya ya
gaisheta, haka zai zauna suyi ta hira har sai dare yayi sannan ya wuce gida. Duk da
yau bai taso da wuri ba haka ya wuce gidan Hajiyan don ya san gobe asabar da jibi
ba lallai ya samu yaje ba tunda suna da meeting da gwamna kuma ya san sai dare.
Bayan sallar isha’i ya shiga gidan, bayan sun gaisa da Hajiya da mutan gidan, ya
zauna suna hira. Wajen karfe tara da kwata ya duba agogo yace
‘Hakane.’
‘To na zata Sule direbanka ne kuma kai kace ya kawosu tare da Zahra?’
Ta tabe baki
‘Sun zo mana. Amma yarinyar nan don rashin mutunci wai ba zata biyo Zahra su taho a
mota daya ba sai dai Sule ya koma ya daukota ya kawota da ban.’
Mamakinsa ya karu
‘To haka dai sukayi, sai da Sulen ya kawosu ni kuma nace kada ya koma shine ta biyo
motar haya ta zo ita kadai kuma ta shigo tana yiwa mutane gani-gani. Da zasu tafi
ma kuma haka, Anisa ma tana kallo yarinyar nan ta wuce Zahra da yaran a mota ta hau
motar haya.’
‘Ikon Allah!’
‘Ki zo ki tarar da mace da mijinta kice ba kya son mu’amala da ita? Dama shi yasa
tace ka raba musu gidan?’
‘To gaskiya dai ya kamata ka taka mata burki, idan tana sonka to ta soka da
iyalanka.’
Suka dan kara hira Hajiya tana jaddada masa lallai ya dau mataki, daga baya yayi
mata sallama ya tafi.
……
Ranshi yayi matukar baci, wannan wane irin wulakanci ne Aishan tayi kuma ta rasa ma
a inda zatayi sai gaban Hajiya. Idan ta san ba zata hada tafiya da Zahra ba me yasa
ba zata gaya masa ba; to don me ma zata ce ba zata hada tafiya da iyalansa ba? Ya
kasa gane meye dabarar hakan da ta aikata, don kuwa ya san Hajiya ba zata yi mata
karya ba.
Kafin ya isa gida dare ya yi don haka sai ya fara tsayawa gidan Zahra tunda ba nan
zai kwana ba idan yayi musu sallama sai ya koma gidan Aishan inda zai kwana.
Ruwa kawai ya sha da yake yaran ma duk sun yi barci, ya zauna a falon kasa itama ta
zauna. Bayan ta sake yi masa sannu da zuwa ya dubeta yace
‘Na me fa?’
Ta gatsina baki
‘Uhm, to mun dai fita mun tsaya a mota Malam Sule ya buga mata kofa ta fito ina
zaune a bayan mota taki shiga tace wai ya kaimu sai ya dawo ya kaita, bata fadi
wani dalili ba don ni ko gaisheni ma batayi ba. Haka dai muka gaji da tsayuwar nace
mu tafi tunda yamma tana yi, da muka je kuma Hajiya tace Malam Sule ba zai dawo ya
dauketa ba, can kuma sai muka ganta ta zo a motar haya. Da muka fito dawowa ma kuma
haka, bata ko kallemu ba ta wuce ta hau tasi don haka muma muka taho.’
Yayi shiru yana takaici, ta riga ta san zugarta tayi aiki don haka ta gyara zama
tayi shiru. Jimawa kadan yayi mata sallama ya tashi ya nufi gidan Aisha.
……..
A zaune ya sameta a falo tana kallon TV, yana shiga falon ta mike da fara’arta tana
yi masa sannu da zuwa. Babu walwala a fuskarsa ya amsa, ya wuceta ya ajiye ledar
burodi a kan dining table ya shige daki.
Ta kula da yanda yake a fusace don haka bata bishi ba, ta tsaya ta gyara abincin da
ta ajiye masa a kan dining table sannan ta bishi dakin.
Tana shiga shi kuma ya gama shiryawa, ya wuce ta gefenta ba tare da ya kalleta ba.
Ta tsaya a nan ta sunkuyar da kai; tabbas ta san an gaya masa karya da gaskiya shi
yasa zai shigo yana cin magani. Ta share kwalla ta bi bayansa.
A dining table ta sameshi yana cin abinci, sai ta wuce ta zauna a gaban TV ta
cigaba da kallonta. Bai dade ba ya gama cin abincin don bata jin ma ya koshi ya
taso ya dawo inda take, ko kallonsa bata yi ba har ya zauna.
‘Aisha.’
‘Me ya sa baki bi su Zahra kun tafi gidan Hajiya ba kika tafi a motar haya?’
‘Sun shiga bayan mota ita da Yara, nace su matsa na zauna tace wajen ba zai ishemu
ba, nace to Nana ta koma gaba sai na zauna ni a bayan. Tace yaranta baza su shiga
gaban mota ba sai dai ni na shiga, ni kuma naga da aurena, ina matarka kuma na
shiga gaban mota da direbanka ai ba daraja. Shine tace ya kaisu ya dawo ya kaini,
ni kuma kafin ma ya dawo na hau tasi na tafi.’
‘Ni ba haka aka gaya min ba, kuma bana jin Zahra zatayi haka tunda yaran ko
makaranta Sule zai kaisu suna shiga gaba. Kuma a dawowa me yasa baki biyosu ba
tunda a lokacin Anisa tace Yusra gaba ta zauna.’
Ta riga ta fuskanci inda zancen ya dosa don haka cikin halin ko in kula tace
‘Saboda ban san irin shirin da suke dashi ba a dawowar shi yasa kawai na dawo ta
hanyar da na tafi.’
‘Aisha! Bana son fitna irin wannan, saboda na raba muku gida ba zai yiwu kice ba
zaki hada mu’amala da Zahra da yarana ba. Shekaru wajen sha bakwai nake zaune da
ita ban taba samun matsala da ita ba, gaskiya ba zan dauki irin wannan ba.’
Ya katseta
‘Ni dai na gaya miki gaskiya ba zan dau wannan ba, yanzu Hajiya sai fada takeyi
saboda abun da kuka yi.’
‘Mtsewww! Ni dai na gaya miki don kin sa na raba miki gida da iyalina ba wai yana
nufin ba zakiyi mu’amala da su ba, kuma kece karama dole kiyi hakuri ki bita idan
wata sabga ta hadaku. Wannan din ma kuma zan bincika kuma zan dauki matakin a kan
mai laifi.’
Ta riga ta gama shirin kwanciya bacci domin kayan bacci ne ma a jikinta, don haka
itama ta mike ta kashe wutar falon ta wuce dakinta ta kwanta.
Ba zata iya binsa dakinsa ba don bata son zama da mutum idan yana jin haushinta; ko
waye shi, kuma bata ga laifin da ta yi masa ba balle ta bashi hakuri. Ta kashe
fitila ta kwanta bayan tayi adduointa.
Sai da ta kwanta sannan hawaye ya kwace mata; fadan da yazo yana yi mata ya fi bata
mata rai a kan abinda Zahra tayi mata don ita za a iya cewa kishi ne. Amma shi ya
zo yana gaya mata dole ta kula iyalansa; kenan ma har yanzu ita bata zama iyalinsa
ba kenan? A haka har bacci ya kwasheta.
Tana jinsa ya fita masallaci da asuba, itama ta tashi tayi sallah ta sake komawa,
sai wajen karfe bakwai sannan ta fito ta shiga kicin. Nan da nan ta soya doya da
kwai ta zuba ta dora a dining table ta koma daki ta yiwo wanka ta shirya, har ta
fito bai fito ba.
Don haka ta zuba nata abincin ta zauna ta kunna TV tana ci tana kallo.
Yana gama cin abincin ya tashi ya fice ba tare da yace mata wani abu ba, duk da dai
ta san gidansa ya tafi.
Yana zuwa bakin gate din gidan Malam Sule yana sauka daga acaba, ya karasa da sauri
ya kwashi gaisuwa.
‘Yauwa Malam Sale, dama Ina nemanka. Ni jiya wai ya akayi kuka tafi gidan Hajiya ba
tare da Aisha ba?’
Ya shafa kai
‘Ranka ya dade ai mata sai hakuri, rashin fahimta ce aka samu ni kuma na rasa yanda
zanyi da su ranka ya dade. A dai bata hakuri.’
‘So nake ka gaya min tsakanin da Allah Malam Sule don Allah kada ka boye min, me ya
faru? Ya akayi baku tafi da Aisha ba?’
A hanakli malam Sule ya koro bayani, yayi masa bayanin abinda ya faru har zuwa
lokacin da suka dawo. Ya dora da
‘To kaga yallabai babu yanda zanyi, kuma ai bai kyautu Ina tuki ace ta zauna a
gaban mota ba, ai ko Yusra ta girma kamar haka ai ta shiga baya na tuka ta balle
matarka ta aure ranka ya dade. Amma a dai yi maslaha yallabai lamari ne na kishi.’
Kansa ya kulle gaba daya; yanzu ya za ayi Zahra tayi haka, kuma sannan jiya ta
zauna ta tsara masa zance yaje yanata yiwa Aisha fada. Ya tuno yanda take kallonsa
lokacin da ya hakikance yana fada.
A zatonsa ya san Zahra shi yasa ya kama zancenta don bai zata zata yi masa karya
ba, ashe ma bai santa ba. Ranshi yayi matukar baci; babban damuwarsa yanda ta dora
Hajiya a kan karya har take jin haushin Aishan, ya san kawo yanzu kaf danginsa sun
ji zancen nan.
Ya karasa cikin gidan ya shiga da sallama.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
11
Ranar asabar ce don haka yana shiga ya samesu a falo ita da Yusra, Nana da Ummi
domin ragowar basu tashi ba. Da gudu Ummin ta rungumeshi tana masa oyoyo, gaba daya
suka gaisheshi. Itama Mommy tayi masa sannu da zuwa ya amsa ba yabo babu fallasa,
ta san dai akwai matsala daga yanayin yanda ya amsa ba tare da bata lokaci ba ya
haye sama. Nan take ta tashi ta haye tabi bayansa.
A zaune ta sameshi a dakinsa a kan kujera, ta wuce ta zauna a gefen gado tace
‘Alhamdulillah.’
‘Eh, kika ce min Zahra kin binku tayi ku tafi gidan Hajiya bayan cewa kikayi ta
shiga gaban mota?’
‘To motar ta cika, gaban motar ne kawai da waje aka ce ta zauna kuma taki.’
‘Amma kin san gaban mota ba wajen zamanta bane tana matar aure, don me Yusra ko
Nana bazasu shiga gaban motar ba?’
Ta sha kunu ta kauda kai, sukayi shiru na dan lokaci yana kallonta yana sauraron
amsarta. Tace
‘To yanzu kafi kishin matar da ka auro kwanannan a kan yaranka, naga dai suma sun
balaga ko?’
Mamakinsa ya karu
‘Oh! Da baki san sun balaga ba kike barinsu suna shiga gaban motar idan zaku fita
ko kuma idan za a kaisu makaranta? Ko kuwa sai jiyan suka balaga?’
Ta murgude baki ta kawar da kai
‘Gaskiya bana so, kada ki sake yi min irin wannan. Ba zan dauka ba, yara su shiga
gaban mota ku ku shiga baya idan ba haka ba wallahi zan dau mataki a kai kuma
matakin ba zai yi miki dadi ba.’
‘Uhm, yanzu dai zugo ka tayi dani da Hajiya kazo kace mu makaryata ne kenan.’
‘Karyar dai da kika biyawa Hajiya, ai Hajiya bata san me ya faru ba sai abinda kika
gaya mata. Kada ki sake yi min irin wannan na gaya miki.’
Kafin tace wani abu ya fice daga dakin yana saukowa ya fice daga gidan ya nufi
gidan Aisha.
……..
Yana shiga ya sameta a kicin tana wanke-wanke, yanda bai yi mata sallama ba bata sa
rai zai ce mata ya dawo ba. Ga mamakinta sai ya karaso kichin din yace
‘Na dawo.’
‘Sannu da zuwa.’
Har yayi wanka ya fito tana kicin din, tana hada kayan abincin rana saboda idan
ranar tayi sai kawai ta dora. Ya leko kicin din tana tsaye tana yanka kabeji, yace
Ta juyo tace
Ya koma falo ya zauna ya kunna TV, yana kallo amma hankalinsa baya wajen, yana ta
tunanin yanda zai yi da Aisha don ya kula fushi takeyi da shi. Yana sane da cewa
jiya bata kwana a dakinsa ba amma shima a jiyan fushi yayi saboda abinda aka ce
masa tayi, saida ya ji daga bakin Malam Sule da kuma yanda Zahran tayi masa da yayi
mata magana sannan ya san bai kyautawa Aisha ba.
Yana nan zaune ta zo ta wuce daki, yayi zaton zataje ta dauko wani abun ne yaji
shiru bata fito ba har wajen minti talatin. Don haka ya tashi ya bi bayanta;
dakinsa ya fara dubawa bata ciki sai dai kawai ta gyara dakin don haka ya wuce
dakinta.
Tana zaune a kan gadonta ta mike kafa da novel a hannunta tana karantawa, bayan ta
amsa sallamarsa ya karasa ya zauna a gefen gadon. Ta gyara zama ta dan matsa don ya
sami wajen zama sosai.
Yayi gyaran murya yana ta wani murmushi da yake bata mamaki tunda a saninta fushi
yake da ita don ko da zai fita bai ko kalleta ba.
Yace
‘Um, ya kika zauna a nan? Yau ba kallon Zee World don ne?’
Suka yi shiru na dan lokaci yana kallonta, yaga dai bazata kulashi ba, ya kirawo
sunanta
‘Aisha’
‘Na’am.’
Ta mika hannu ta dauki littafinta a kan cinyarsa tana kokarin budo shafin da take,
ya sake zare littafin daga hannunta yana fadin
‘To ki taso muje falo inda muka saba zama, ai naga ko a can ma kina yin karatun
ko.’
Ta gyara ta sauko daga kan gadon, ta dauki littafin nata a kan cinyarsa ta nufi
falon. Yayi murmushi kawai ya biyota a baya; tabbas ya san Aisha tana da miskilanci
amma bai yi zaton zata iya yi masa fushi haka ba. Suka dawo falon ta sami waje
kujerar zaman mutum daya ta zauna ta cigaba da karatunta shi kuma yana kallon TV.
Duk yanda yaso ya jata da hira ta ki bashi hadin kai, gajerun amsoshi take bashi da
basu wuce e ko a’a ba, ko kuma tace Um. Har ya gaji ya koma ya sa mata ido yana
mamakin wannan dogon fushin.
Suna nan zaune har sha biyun rana tayi, ta tashi ta shige kicin ta dora abincin
rana. Ta kusan gama abincin ya ce mata zai je masallaci ya dawo.
Yana ficewa ta ajiye masa abincin rana a table tayi sauri ta cinye nata, ta wuce
dakinta ta kwanta. Tana jin shigowarsa tayi kamar bacci takeyi, don haka ya kyaleta
ya zauna yaci abincinsa shi kadai.
………
Inda Abban Sadik ya fita ya bar Zahra nan ta zauna tana takaici; wato Yusuf har ya
auro matar da zata sa yace mata makaryaciya. Dole ne ta dauki matakin don bazata
zauna da wannan yarinyar ba, shima Malam Sule kuma dole ya bar mata gidan don ta
san karshenta shi ya fadawa Abban Sadik yanda akayi; dama tana sane da yanda yake
kokarin kin bin umarninta.
Ta ji dan danshi a kwarmin idonta, ta kai yatsanta ta taba wajen ta kalla; hawaye
ne. Ta jijjiga kai cike da takaici; tabbas yanda ta fitar da wannan kwallar sai ta
fitar da Aisha daga rayuwar Yusuf ko da kuwa Aishan tsafi takeyi. Tabbas yanzu ta
kara gasgata maganar Malam da yace ba haka suka barshi ba.
Kamar an mintsineta ta tuna bata ma yi magana da Malam ba tunda ta nemi layar nan
ta rasa, don haka ta mike ta nufi dakinta. Tana shiga ta saka mukulli ta kulle
kofar saboda kar yara su dameta. Ta zauna a gefen gado ta dauki wayarta ta kirawo
Malam Hatimu.
Bayan ta gama yi masa bayanin batan layar yayi ‘yar dariya yace
‘Allah sarki, masu ita sun dauke kenan Hajiya, ai kunyi sakaci. Sannan kuma
yarinyar ta zo da sa’a watakila kuma da nata hatsabibancin, amma ba zata iya damu
ba duk taurin kanta.'
‘Eh, kada ki damu akwai aiki wanda za ayi kuma aikin nan zai rabata da mijinki har
abada, ke ko bayan ranki bazasu sake hada inuwa daya ba. Ammafa gaskiya aikin yana
da tsada sosai, yauwa.’
‘Kada ka damu Mallam, ko nawa ne zan biya ayi wannan aikin indai zai yi yanda
kace.’
‘Ai Hajiya aiki kamar yankan wuka, sai dai kudin aiki naira dubu dari uku da
tamanin zai kama komai da komai.’
Ta dan dauke wuta saboda jin yawan kudin; to a ina ma za a ta sami wadannan kudin,
ta danyi gyaran murya ta cigaba
‘Gaskiya Hajiya a hakan ma anyi miki ragi, don kinga aiki biyu za ayi. A mallaka
miki ruhin maigidan ta yanda sai yanda kikayi da shi ita kuma a nesanta ruhinta da
nashi ba zasu sake sha’awar kasancewa da juna ba.’
Ta jijjiga kai, tabbas tana son wannan aikin amma bata da kudi a yanzu
‘To shikenan Malam, zan yi kokari na hada kudin nan da wani lokaci in sha Allah zan
nemeka.’
Sukayi sallama tana tunanin inda zata sami wadannan kudin don gaskiya a halin yanzu
bata da kudi. Jarinta na business dinma da takeyi ta dan yi musu gibi so take ta
sami dama ta tambayi Abban Sadik. Bata da wata kadara sai sarka da dankunnen gwal
nata da na yara kuma gaskiya ba zata iya sayarwa ba. Amma ko a jikin Abban Sadik
din zata san yanda zatayi ta sami kudi.
Haka ta wuni tunani har dare yayi, tana ta lissafin yanda zata sami wadannan
kudaden. Zuwa dare dabara ta fado mata, don haka nan da nan ta nemo Hajja mai kayan
mata. Gaba daya ma ta manta da matar nan don kafin ma Aisha ta tare ya kamata ta
nemeta ta hada mata masu zafi amma da yake ta sa ran auren ba zai dade ba sai ta
manta.
Nan suka gama magana da Hajja a kan a hada mata masu zafi kamar na naira dubu
hamsin don so take gaba daya ta mantar da Abban Sadik kowacce mace. Aka yi mata
lissafin dubu saba’in da alkawarin in dai ta tura kudin a lokacin to gobe da azahar
za a kawo mata sakonta.
Bata da kudi amma saboda akwai abinda ta shirya haka ta kwashe kudin nan a account
dinta na business ta turawa Hajja, ya zama saura abinda baifi dubu ashirin ba a
account din. Tana tunanin da ta fara aiki da kayan nan sai ya biya kudinsu.
………
Haka suka wuni Aisha taki kula Abban Sadik, tace masa ba fushi take ba amma kuma
taki ta saurareshi idan tayi murmushi to ita da waya ne. Haka har dare yayi.
Tana yin sallar isha’i ta kwanta a dakinta tsaf da niyyar bacci, don haka shi kadai
ya zauna a falo yana kallon TV.
Bayan karfe tara ya fita ya dubo wajen Zahra sannan ya dawo, ya shirya ya wuce
dakinta.
Duk yanda ta so ya kyaleta a daren nan saida ta sallama masa, haka ya dinga tsara
mata kalamai na lallashi a kunnenta har ya samu ta huce.
Sai da safe ya gaya mata zasu shirya asabar mai zuwa ya kaita ta sake gaida Hajiya
kuma su bata hakuri.
_
Kamar yanda sukayi alkawarin da Hajja washe gari sai gata ta zo da kanta. Ta yi
sa’a lokacin da ta zo yara suna islamiyya don haka babu kowa a gidan sai ita, duk
da haka dai a dakin baki ta sauketa suka zauna suka turo kofa.
Nan Hajja ta baje kaya tana bayani; kayan da ta hado mata sun kai rabin ledar bagco
ga kuma tsumi a galan. Ta zauna tayi mata bayani dalla-dalla tana rubutawa; bayan
sun gama Hajja tace
‘Hajiya Zahra ai idan akayi maka kishiya baka zama haka, gyara zakiyi na musamman
idan ba haka ba sai ki ga wankin hula ya kaiki dare. Yaran nan na yanzu masu ido a
tsakar ka, wallahi kada ki saurara mata.’
‘Hmm! Ni da na gani Hajja, yarinyar daga zuwanta har ya canza min, jiyan nan dana
kirawo ki nan ya kare min tijara saboda ta tsaro masa zance. Ai dole sai na tashi
tsaye.’
Ta zura hannu a jakarta ta zaro wani dan kulli a farar Leda, ta cigaba
‘Kin gan shi nan ba ma bawa masu kishiya ma saboda idan kikayi amfani da shi ba zai
sake jin dadin wata mace ba sai ke, gashi dubu goma ne amma ki bada biyar saboda
wannan cinikin da kika yi min.’
‘Allah Hajja?’
‘Allah Hajiya. Ai idan baka iya kama barawo ba sai barawo ya kama ka. Idan ma kina
bukatar wani taimakon akwai aikin da mukeyi sai yanda kika yi da maigidan, idan ma
sakinta kike so yayi zai yi.’
‘Allah Hajja? Kin san nifa bana son aikin nan da akeyi da aljanu.’
‘Kema kin san aikina Hajiya, wannan din ma da zan kawo miki ayoyi ne da kanki ma
zaki gani. Naira dubu ashirin kawai zaki bayar shikenan an gama.’
Nan take suka kulla ciniki, suka rabu a kan idan ta sami kudin zata nemo Hajja. Ita
kuma Hajjan ta sake tabbatar mata da idan dai tayi aiki da wadannan kayan da ta
kawo mata ko naira dubu dari ta nema sai ya bata.
……..
Ta riga ta san da fushi ya fita daga gidan gashi yau din dai a wajenta zai kwana. A
sanin da ta yi masa ta san da fushinsa zai shigo don haka ta yi duk wani shiri na
tarbarsa.
Duk da yanzu din itama ta so tayi masa fushin amma dole ta hakura saboda abubuwan
da ta shirya; duk da daman ta riga ta saba bata son fushinsa, ko da shine yayi mata
laifi da zarar yayi fushi zata fara bashi hakuri.
Tunda Hajja ta tafi tasamu ta sha tsumin nan ta koshi, ta bi sauran kayan duk tayi
amfani da su, don haka kafin ma yazo ta fitni kanta.
Yana son shinkafa da salad don haka ta shirya fried rice da kaza ga lafiyayyen
salad, ta jera a table.
Sai wajen tara da rabi ya shigo gidan, Yusra ce kawai a falo da Rukayya suna
homework. Yana shigowa Rukayya ta shirya, suka fice ya rakata don ta taya Aisha
kwana sannan ya dawo ya rufe kofa.
‘Yallabai.’
‘Menene?’
‘Ka san dai fushinka baya min dadi, don Allah kayi hakuri in dai nice ba zan sake
ba.’
Ya juyo gaba daya ya tsaya yana kallonta, har ya bude baki zai yi magana sai kuma
ya fasa. Yadan matso kusa da ita sannan yace
Ya mayar mata da murmushin da take ta yi masa sannan ya juya ya wuce gaban wardrobe
ya debo kayan baccinsa ya fara canzawa.
Tace
Bayan sun gama cin abinci suka zauna a falonsa suka dan taba hira, da ta kula ya
fara jin bacci ta tashi ta shige dakinta ta sake shiryowa ta sa rigar bacci ta fito
ta shige dakinsa.
A dabi’arsa baya neman matarsa sai yayi bacci kai daya, lokacin dare ya raba sosai
kuma dukansu sun rage baccin. Ga mamakinsa yau yana kwanciya ta fara lalubensa, bai
kawo wani abu don wannan ba bakon abu bane tunda matarsa ce; kawai dai ya san ta
saba jira sai sun rage baccin musamman da yake mafi yawa cin lokuta kafin ya kwanta
ita din bacci ya dauketa.
Haka sukayita fama; yana yi yana mamakin yanda yau gaba daya take kamar a gigice
tunda ya riga ya saba shi yake sarrafata kuma a hankali yanda yake so. Bai yi
mamaki sosai ba don ya san akwai abubuwan da mata suke Sha musamman don wannan
harkar, don haka yake tunanin itama wani abun ta sha.
Suna gamawa kamar yanda ya saba ya zare jikinsa yaje yayi wanka, bayan ya fito ya
tabata yace mata taje tayi wanka ko kuma tayi alwala idan ba yanzu zata yi wankan
ba. Haka ta tashi taje ta wanko jikinta tayi alwala ta fito ta sake kwanciya.
Can cikin dare baccinsa yayi nauyi ta sake lalubarsa, kamar a mafarki ya farka. Ya
gyara kwanciya yace
‘Um.’
Suka cigaba. Baya son ya rasa sallar asuba a masallaci don haka suna gamawa ya
tashi yayi wanka, itama ta tashi tayi nata wankan lokacin wajen karfe uku da rabi
na dare. Suka koma suka sake kwanciya.
Ko da yaje masallaci ya dawo yaci burin biyan bashin baccin da ya ci, saida yayiwa
sakatarensa message yace masa zai dan makara don ya samu yayi bacci sannan ya koma
ya kwanta.
Tana idar da sallah itama ta dawo ta kwanta, yayi zaton bacci zasuyi kamar yanda
suka saba don wani lokacin sai wajen karfe shida take tashi ta shiga kicin don
shirya ‘yan makaranta.
Tana kwanciya ta laluboshi, duk yadda ya so ya kyaleta kasawa yayi; ba wai saboda
yana bukatarta a wannan lokacin ba sai don yana ganin matarsa ce ba zai iya kyaleta
ba musamman da wannan bukatar. Suna gamawa lokacin har shida ta gota don haka a
gurguje ta mayar da kayanta ta wuce kasa don shirya ‘yan makaranta. Ta fuskanci
gajiyawarsa wanda dama haka takeso; so take ta sauke masa duk wata sha’awa da yake
da ita saboda idan yaje kwanan Aisha sai ya kwanta yayi ta baccin a can ba tare da
ya kusanceta ba.
Tana fita daga dakin ya tashi ya shiga wanka, bayan ya fito daga wankan ya zauna a
kujerar gaban mudubi ya kafa tagumi; me ya sami matar nan ne? Ko ma me ta sha
gaskiya yau ta jigata shi. Bacci yake so ya koma amma ya hakura saboda yana tunanin
idan ta sameshi a kwance bayan yara sun tafi makaranta to lallai zata sake nemansa
shi kuwa ya san ba zai iya ba. Don haka nan da nan ya shirya ya sauko dai-dai
lokacin yara sun fice.
Ta saka mishi abincinsa wanda yana gama ci yayi mata sallama ya fice, gidan Aisha
ya shiga don ya dubata inda ta sanar da shi sati mai zuwa zata koma aiki. Yayi mata
sallama ya fice bayan ya sanar da ita zasu dinga fita da yara idan Malam Sule ya
ajiyeta sai ya wuce da su.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
12
Kwanakin nan biyu haka Abban Sadik yayisu babu baccin kirki saboda yanda suke kwana
hidima, har Allah-Allah ya dinga yi kwanan Zahra ya kare ya koma wajen Aisha.
Ranar da zai koma wajen Aisha kuwa da wuri ya dawo daga wajen aiki, ana cikin kiran
sallar isha’i .
Wajen Zahra ya wuce kai tsaye, bayan sun masa sannu da zuwa ita da yaran ya amsa ya
dubeta yace
‘Bari na wuce don yau a gajiye nake wallahi, don Allah da zarar karfe tara tayi ki
rufe gidan nan kar a sake budewa sai da safe.’
Ta bi bayansa da kallo tana murmushin jin dadi, domin aikin da tayi ta san yau din
nan idan banda bacci babu abinda zai iya.
Hakan kuwa aka yi; ita Aisha bata kawo komai domin bata da matsala da hakan, suka
kwana suna baccinsu har asuba. Ko da gari ya waye haka suka gama hirarrakinsu ya
shirya yayi tafiyarsa aiki.
Har saida aka sake kwana bayan ya dawo daga masallaci sannanne wani abu ya shiga
tsakanin sa da Aisha, a nutse yanda ya saba kuma yanda yake so suka farantawa juna.
Da dare yayi kuma ya koma kwanan Zahra.
Yana fargaba da addu’ar Allah ya sa yau bata sha abinda ta sha wancan karon ba don
gaskiya ya fi so yaji dadi yana cikin hayyacinsa.
Yanda akayi wancan karon din kuwa haka aka sakeyi, babu yanda ya iya haka ya dinga
hakura da baccinsa. Saida ya koma wajen Aisha sannan ya maimaita mata yanda yayi.
Haka suka cigaba da yi duk da ita Aisha bata dauki abun a matsala ba, sau dayan nan
ya isheta musamman da yake yana daukan lokaci ya tabbatar bukatarta ta biya. Haka
rayuwa ta cigaba.
Zahra bata taba shiga gidan Aisha ba kuma bata turo yaranta, tunda tana amarya dai
data tura Yusra da waya ta dauko mata hoton falon bata sake tura su ba. Rukayya ce
kawai take zuwa tayata kwana, itama don babu yanda Zahran zata yi ne. Sai kuma
Allah ya sa Aishan da Rukayya jininsu ya hadu sosai, don haka Rukayyan take jin
dadi zuwa kwana; duk da dai idan gari ya waye ta fito daga gidan Mommy hanata
komawa takeyi har sai wani daren.
_
Yanda ya saba duk karamar sallah kaya kala uku yake yiwa kowa, tsakanin Zahra da
yaranta. Idan kuma babbar sallah ta zo to kaya kala daya yake musu, sannan kuma ya
kawo sa da rago wanda za a yanka na layya.
Ranar asabar ce don haka yana gida da yamma, suna zaune shida Zahra a falonsa suna
hira; da yake yaran duk sun tafi islamiyya. Ya dubeta yace
‘Yanda aka saba mana, ka san dai a wajena ake siya ko business din nawa ya dan samu
cigaba.’
‘Hakane, to zan tura miki dubu dari da hamsin, yara kowa dubu ashirin ke kuma
hamsin. In ya so sai ki kawo muku abinda kike so, ita kuma kanwarki itama sai na
tura mata hamsin din.’
Ta langabe kai
‘Haba yallabai, to ita ba zata yi min cinikin ba? Ka turo har natan mana na dai san
ba zai wuce leshi ba. Za a kawo su kala-kala in ya so sai tazo ta zaba.’
‘Kwarai kuwa. Amma gaskiya da zaka karawa yara ko da dubu biyar-biyar ce ka san fa
kayan yanzu sun dan kara kudi.’
‘A’a hakan ma zai isa. Kin san fa Babbar Sallah ce dole sai na tanadi abun layya.
Ni ban ma sani ba na siyo sa kamar yanda na saba ko kuma na siyo muku raguna dai-
dai ke da kanwarki yara kuma a basu biyu.’
‘Haba dai, ai sa ya fi auki. Idan ka siyo mana sa daya da rago ya ishemu gaba daya
idan muka hadu muka soya sai a raba. Sai dai idan ita Aishan ta fi son rago sai a
bata nata.’
‘A’a na san bata da matsala, bari dai naje kasuwar naji farashin dabbobin tukunna
sai ayi wanda ya samu.’
Suka gama hirarrakinsu daga baya ta barshi a nan ta shiga kicin dora abincin dare.
……..
Sallah saura sati biyu Aisha ta tashi da wani zazzabi, da kanshi ya kaita asibiti.
Aka yi mata duk wasu gwaje-gwaje da suka dace, aka tabbatar bata dauke da juna
biyu, sai dai malaria don haka aka rubuta mata magunguna suka kamo hanya.
Har suka zo gida yana tsokanarta a kan shi ya fara murna har ya gama shawara idan
mace ta haifa Aisha zai mayar idan kuma namiji ne Muhammad. Haka suka tsaya a
chemist aka yi mata allurai sannan suka dawo gidan.
Kwana biyu ta fara warwarewa, da daddare suna zaune a falo ya mike kafafunsa ta
tada kai da cinyoyinsa ta kwanta suna hira kuma suna kallon TV.
Yace
‘Wai Sallah ta kusa ke ko labarin kayan Sallah ba kya yi balle na abun layya.’
‘Wai da yake ba ni zanyi ba, kuma na san mai yi yana sane da lokacin.’
‘Lallai ne baki da matsala. To akwai leshina a wajen yayarki, gobe sai ki shiga ki
zabi daya. Kin san tana sayar da kayan sawa shi yasa kawai nake sayen kayan sallar
a wajenta.’
Ranta ya sosu, Yaya za ayi yace matarsa ce zata saya mata kayan Sallah ko an gaya
masa ita babu masu sayar da kayan a danginta. Bata son ta ja maganar yaga kamar ta
damu; kuma da yake tana da ragowar kaya a akwatin lefenta sai abun bai dameta ba
sannan kuma akwai leshi da suka siya ita da ‘yan gidansu wanda daga Switzerland
suka tura kudi aka siyo musu don nata ma yana wajen tele inda Zahida ta kai musu
dinki, don haka tace
‘Ka gani ni dai ina fama da kaina gobe ban san yanda zan tashi ba, idan ka je kawai
ka zabo min wanda ya burgeka.’
‘Ah bari ma kawai na kirawota ta turo min hotunansu sai ki zaba ko?’
Kafin ta amsa ya daga waya ya kirawo Zahra, wadda a take ta turo masa hotunan
leshin ta Whatsapp.
Irin leshin nan ne mai hade da mayafinsa, ta san kudinsu basu wuce dubu ashirin da
biyar ba. Bata raina ba, sai dai kuma leshin baya burgeta kwata kwata. Tabbas da
anyi shawara da ita ba za a saya mata wannan leshin ba domin ita da a bata wannan
gara a bata leshi marar mayafi ko ma atamfa. Ta duba su gaba daya ma kalolin ba
wani kyau sukayi ba amma dai ta zabi wani kalar ruwan toka mai fulawoyi ruwan goro.
Ana kawo leshin ta kaiwa Hajiya tace a bawa Zahida ta kai mata dinki zasuyi waya.
Sai ana i gobe Sallah ya sanar da ita sa zai yanka da rago, kuma zuwa zatayi su
soya tare a gidan Mommy in an gama soyawa sai a raba a dibarwa kowa nasa. Tsarin
bai yi mata ba domin tun bayan zuwansu gidan Hajiya bata son shiga harkar Zahra,
sai dai bata son tayi masa musu kada yaga kamar kullum itace take fara bashi
matsala. Don haka tace babu komai hakan yayi.
Ta san Zahran ce ta shirya masa hakan kuma ta san don a cuceta ne, amma zata tsaya
taga gudun ruwansu tukunna.
Kudin kayan sallar da ya turo mata a ciki ta samu ta fidda dubu ashirin kudin aikin
da Hajja tace zata yi mata; domin ko leshin da ta bawa Aisha ma dubu ashirin da
biyar take sayar da shi amma a kan dubu hamsin ta bawa Abban.
Nan da nan ta kirawo Hajjan ta sanar da ita kudi sun samu, tayi mata alkawarin zata
kawo mata aikin ana saura kwana uku Sallah.
Ranar asabar kuwa sai ga Hajja, bayan sun gaisa ta zaro farar kwalba irin ta fiya-
fiya. Tarkace ne kawai a cikin kwalbar sai wani guntun tsoka da aka sokawa allura
ga kuma takarda wadda ke dauke da rubutun larabci a jiki wadda aka nannade aka
sakata a tsaye. Ta mikawa Zahra kwalabar tare da wata mitsitsiyar kwalbar baka tace
‘Kin gansu nan; wannan babbar ki sami singiletinsa wadda ya saka yayi gumi a
jikinta ki gutsiri dan mitsitsi ki saka a ciki. Idan kika saka sai ki juye man da
yake cikin wannan kwalbar ki mayar ki rufe. Ki samu waje mai duhu ki boye
kwalbarki; idan kikayi haka to zaki sha mamaki don ya daina musa maganarki kuma duk
abinda zai bata ranki ba zai yi shi ba.'
‘Allah Hajja.’
‘Ai sai dai idan bakiyi yanda nace ba, amma tabbas idan kinyi yanda nace to baki da
matsala.’
Sukayi sallama tana ta jin dadi.
Ranar a wajenta ya kwana don haka singiletin da ya cire ita ta samu ta yanka ta
hada kamar yanda aka umarceta. Ta samu waje a dakinta bayan wardrobe ta boye
kwalbar. Ta kwana tana walwala da farin ciki.
Ranar Sallah ba a wajen Aisha yake ba, amma dai ya sanar da ita da safe zasu tafi
da tuwon Sallah don su kaiwa Hajiya idan an sauko idi don haka itama ta zuba nata.
Tun dare Rukayya ta tayata ta gama miyar taushenta sannan ta hada zobonta mai dadi.
Asuba nayi ta dora tuwo, da yake ba yawa ne da shi ba nan da nan ta gama. Suka
gyara gidan tare da Rukayya suka yi wanka. Atamfa ta saka sabuwa kar dinkin doguwar
rigar mai matukar kyau, tayi kwalliyarta sannan suka budade gidan da turaren wuta.
Zuwa karfe bakwai da rabi sun gama komai don haka Rukayya tayi mata sallama a kan
zata je gida don kayanta suna can.
Bata dade da fita ba ya shigo tare da Sadik; tunda aka kawota yaune rana ta farko
da Sadik ya shigo gidan kuma yaune rana ta biyu data taba ganinsa, don ko a unguwar
bata hangoshi. Bata son yanda yake mata wani kallo mai cike da raini, amma dai
haka ya gaisheta ta amsa.
Basu dade da shiga ba suka fito, ta basu abincin gidan Hajiya a flask da kuma zobo
a kula suka kama hanya.
………
Ya riga ya sanar da ita tsarin yanda suyar naman Sallah zata kasance, ya gaya mata
ranar Sallah ake farawa a karasa washegari don haka idan an yanka za a zo ayi mata
magana.
Sai wajen sha daya aka turo Rukayya ta kirawota, nan take ta canza kaya suka tafi
tare da Rukayyan.
Masu aiki ne su biyu Uwar biyu da kuma Hansatu, sai Jummai, sannan kuma ga Asiya
wadda itace ‘yar autar su Zahran wadda ta koma hannu Yayansu Muhammad tun bayan
rasuwar mahaifiyarsu. Ana ta aikace-aikace, su Hansatu suna kokarin hura wuta, ta
karasa suka gaisa da Mommy babu yabo babu fallasa. Su Jummai ma duk suka
gaggaisheta, amma tana kallon Yusra bata gaisheta ba kuma babu wanda yace wani abu.
Ta zauna ta kamawa Jummai nama suka cigaba da yankawa.
Murahu biyar aka dora don haka aikin nasu ya fara da sauri. Gaba daya naman san
gida aka shigo musu da shi, sai raguna guda uku. Ya raba rago daya da rabi aka
bayar sadaka a waje, aka sake shigo musu da rago daya da cinyoyin na biyun.
A take Mommy ta ware naman da za ayiwo musu dambun nama ta bayar aka tafi kaiwa.
Ragowar kuma ana soyawa ana kulle wani ana kai mata freezer.
Duk kaskon da aka sauke za a watso naman a faranti ace kowa ya taba, haka har
magriba suna aiki. Babu laifi an soya da yawa don haka ana yin Sallah Mommy tace a
barshi haka gobe a karasa.
A gajiye Aisha ta dauki ‘yar jakarta da ta shigo da ita tayi musu sallama ta koma
gida.
Ta gaji, bata taba yin aikin sa ba don ita kullum raguna ake yanka musu. Ta so ace
an bata nata naman tayi yanda take so da shi amma da yake wannan ne karon fari ta
hakura; amma tabbas bazata sake wannan aikin hadakar ba. Danyen naman da taga ana
sakawa a freezer tayi zaton za ace ga nata amma bataji an ce ba, tana jira taga
goben tukunna.
Ranar ma ba a wajenta zai kwana ba don haka ita da Rukayya suka kwana. Tun bakwai
na safe yayiwo mata waya yace su taho an fara aiki; da kyar ta tashi suka shirya
suka fice. Tana sane taki cin abinci suka fice. Suna zuwa suka dan taba aikin ta
fuskanci tayi kamar awa daya tana aiki ta cewa Mommy zatazo gidan tayi breakfast
yanzu zata dawo. Ta fice ta barsu a ranta ta san ba zata koma ba don ta gaji.
Tsit gidan kamar babu kowa, don haka ya wuce daki. Tayi dai-dai a kan gado tana
baccinta don ko motsinsa bata ji ba, saida yayi gyaran murya ya zauna a gefen gadon
sannan ta farka.
‘Lafiya dai ko, anata aiki ashe kina nan kina bacci.’
‘Jiri naji yana kwasata ga kaina yana ciwo shi yasa na zo na kwanta, ka san
zazzabin nan ba wai ya gama sakina bane.’
‘Eh hakane.’
Yana shiga ya wuce falo, don haka mommy ta bishi. Yana kokarin kunna TV tace
‘Uh, bata jin dadi ne. Jiri take da ciwon kai kin san bata gama warwarewa ba tayi
zazzabi kwanan na.’
Suka dan taba hira sannan ta tashi ta wuce dakinta, tana shiga ta zauna a gefen
gado cike da damuwa; tabbas cikine da Aisha don jiyan ma tana kula da yanda take
abubuwa jikinta babu kwari. Tab, ya za ayi ta bari a haihu da mijinta, gashi ta
cika gida da yara mata yanzu idan Aishan ta haifi maza uku ko mutuwa yayi sai ta
fita gadon arzikin da aka tara da ita. Gaskiya ba zata yarda ba.
Ta shafa hannunta inda aka saka mata inplant na family planning; tabbas da an koma
aiki zata je a cire mata wannan abun don ya zama ko da bata sami hanyar lalata
cikin Aisha ba to sai dai suyi haihuwar tare. Ba zata sha wahalar talaucin Yusuf ba
kuma ya tara dukiya a fi ta gado. Haka ta zauna tayi ta tunani har saida Nana ta
shigo kiranta ta sanar da ita an sauke wani ta zo ta nuna wanda za dora sannan ta
taso ta fito.
Zuwa la’asar sun gama soya duk naman da za a soya, sai su Jummai da suke ta faman
gyara wajen. Danyen naman kuma duk an lode a babbar freezer.
A falon kasa ta zauna ta dibarwa Hajiya nata naman cikin wata babbar roba mai
murfi! Duk da Hajiyan ma ya yanka mata rago a gidanta amma haka suka saba sai an
kai mata. Ta sami ‘yan bakaken ledodi ta zubawa su Jummai nasu tunda dukansu ta
basu danye da yawa sun kai gida sannan kuma biyansu zata yi kudin aikinsu.
Ta dauko kwanon samira mai kamar girman langa tuwo da miya ta zuba naman har ta
cika sannan ta rufe sannan ta dauko roba irin ta take away din nan ta zuba kayan
ciki ta rufe.
Tace
‘Anti Aisha?’
A falo ta sami Aishan tana zaune tana kallon TV tana shan zobo da cake. Bayan ta
sake gaisheta ta mika mata kwanukan tace
Bata zata nama bane a tunaninta ko abinci ne don haka tace da Rukayyan ta ajiye a
kan dining table. Bayan ta ajiye ta kuma ce mata
‘Ki debo zobo a fridge ki sha, ga cake nan a kan dining table ki dauka.’
Ta shiga ta debo zobon ta fito ta dauki cake din ta wuce ta zauna a kujerar zaman
mutum daya. Ta kurbi zobon sannan tace
‘Kada ki damu in dai cake ne next time in zaki tayani kwana sai mu bi dare mu yi
miki na zuwa a school ko? Sai dai fa ina tsoronki a kicin kin yi kankanta fa.
Shekarunki sha daya fa, bar ganin kinyi tsawo.’
‘Kai Anti, Allah zan iya. Ai dai kema kin ce ina da natsuwa don haka kin san ba zan
yi barna ba ko?’
‘Tabbas kina da natsuwa Rukayya, in sha Allah za muyi cake mai dadin gaske kuwa.’
Saida ta shanye zobon nan suna hira sannan ta tuna da gargadin da akayi mata ta
tashi ta fice ta koma gidan.
Bata dade da fita ba Aisha ta tashi ta bude kwanukan, ta bude baki tana mamaki;
kada dai ace duk naman nan da aka soya wannan ne rabonta, ko kuwa dai daga makota
aka aiko da wannan din.
‘Ikon Allah.’
Ta fada a fili tana mamaki da dariya. A yanka sa guda kato da rago amma a sammata
wannan, ai ko su Jummai ta san sun cancanci kason da yafi wannan. Amma dai zata
jira tunda yau maigidan a nan zai kwana taji bayani.
Ta mayar da kwanukan ta rufe ta barsu a wajen.
……..
Sai bayan sallar isha’i ya shigo gidan, kamar yanda ya tsira ‘yan kwanakin nan haka
ya mike a kan kujerar zaman mutum uku ya fara gyangyadi. Har ta gama jera masa
abincin dare ta zo ta tsaya a kusa dashi bai ji motsinta ba; ta rasa gane wannan
yawan gyangyadi da baccin da yake mata ‘yan kwanakin nan, sai kace wanda yake
kokawa da zaki a office din. Tabbas da ace shine matar da zata ce ciki ne da shi.
Tayi gyaran murya ta zauna a hannun kujerar tace
‘Sai dai idan mafarkinki nakeyi kika bani abincin a mafarki, ba dama mutum ya
kashingida sai kice yana gyangyadi.’
Tayi dariya
Saida suka gama cin abinci suna hira sannan yace mata
‘Dan debo min naman nan mana, Zahra tace ta raba an kawo miki naki ko?’
‘To ni dai shi aka bani. Shiyasa nima na zata daga makota aka kawo. Wannan nama ai
ko su Jummai kason su ai ya kamata yafi wannan balle ni, duk da ban san yanda
tsarin yake ba.’
Yayi shiru yana mamakin wannan rabo na Zahra, domin ko yanzu da zai fito ya ga nama
zai kai fanteka biyar a falon sama kuma ya san akwai wani ma a kicin.
Sai wajen goman dare sannan ya tafi wajen Zahra don yayi musu sai da safe. Babu
kowa a falon sai Sadik yana kallon TV yana cin nama da burodi. Bayan yayiwa Abban
sannu da zuwa ya amsa ya wuce sama.
A dakinta ya sameta tana kwance a kan gado sai dai ba bacci takeyi ba, bayan ya
amsa sannu da zuwanta ya karasa ya zauna a gefen gadon yayinda ta nade kafarta don
ya sami wajen zama.
Yace
Da mamaki ta amsa
‘Bana jin, na dai ga naman ne a ‘yar Samira don ko kafin na fito ma na cinye
rabinsa. Duk wannan naman ya za ayi kuma ace wannan ne rabonta, ko ba ke kika zuba
bane.’
Ta bata rai
‘Ikon Allah, na kula kai dai idan dai a kan Aisha ne ba zan taba burgeka ba. Gani
nayi ita kadai ce a gidan nata, idan ta cinye wannan ba sai ta turo a kara mata ba?
Kai kuma ai ga naka can na ajiye maka a dakinka kamar yanda muka saba. Nan fa mu
shida ne ni da yara ga masu aiki, baki da danginka duk nan suke shigowa kuma a nan
zasu ci ga makota ma duk a nan zan dibar musu. Naman Sallah kuma dama ina yaga wani
auki da mutum zai zata zai samu da yawa?’
Binta kawai yake da kallo yana mamaki, so yake yayi mata fada amma ya rasa me ya
hanashi.
‘Kayi hakuri idan rabon da nayi bai yi maka ba, ka kwashi naman gashi can a falo ka
kai mata ta raba in ya so ta aiko mana da kason mu.’
‘Wannan duk ba abun kuka bane, shikenan a barshi haka. Allah ya maimaita mana. Ni
na tafi sai da safe.’
Kafin ta amsa ya tashi ya fice daga dakin, ta bi bayansa da kallo tana mamaki don
ta zata fada zai yi kuma sai taga ya fice. Tayi murmushi da ta tuno da aikin da
Hajja tayi mata; tabbas aikin ne ya fara ci da ta san baran-baran zasuyi don ba
zata bashi naman ba.
Dama tana sane tace a nan za su soya naman don kawai Aishan tayi mata aiki ne don
bata isa taci kamar rabonta ba.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
13
Tunda ya shigo gidan ta gane bashi da nutsuwa, bai yi mata maganar naman ba don
haka itama sai kawai ta kyaleshi. A nan kan dining table a nan kwanukan da aka kawo
naman suka kwana, har ta saka musu abincin safe suna nan bata dauke ba.
Kwai kawai ta soya suka hada da shayi da burodi suke karyawa, suna yi suna hirarsu
cikin walwala. Ya dubi kwanon yace
‘Naman nan inaga in na fita zan bawa Malam Sule danyen nama ya kawo miki, sai ki
soya ki barshi a nan kya yi amfani da shi tunda ko babu komai naman sallah ai ka
bawa baki.’
Da mamaki ta dubeshi
‘To duk sun rabe wancan naman, akwai dai danyen nama a babbar freezer a can idan
zaki yi miya ki dinga turawa a karbo miki. Wanda za a kawo din kuma sai ki soya.’
‘Hakan ma yayi, amma ba sai an kawo wani danyen nama ba. Kasan na gaya maka nayi
layya a gidan Umma ko? To wallahi ta ajiye min nama danye da soyayye, don nice ma
nace su barshi a can idan naje na taho da shi da tuni an kawo shi.’
‘Ba haka bane, ka san fa raguna hudu aka yankawa Umma naman ma ai ya yi mata yawa;
ga na Yaya Abubakar, ga nawa ga kuma na mijin Zahida sannan daga gidan Baffa ma
cinyar sa aka kawo.’
Sai bayan azahar ta shirya sukaje tare ya ajiyeta a gidan Umman, nan yara suka hadu
akayi ta murna. Tayi matukar kewarsu don haka ta sanar da Umma duk ranar Juma’a
zata dinga daukarsu daga makaranta su dinga yin weekend a wajenta, in ya so ranar
Lahadi da yamma sai ta dawo da su.
_
Kamar yanda ta daukarwa kanta alkawarin ana sallacewa taje aka cire mata abun
family planning din da ta saka, don haka ko al’ada batayi ba bayan an cire ta sami
ciki. Shi kanshi Abban Sadik din bata sanar da shi da cikin ba ta bari sai ya kai
kamar wata hudu; saboda bata so ta gaya masa ya gayawa Aisha kada ta cutar mata da
ciki.
Duk wata tambaya da zata yiwa Rukayya a kan alamun ciki a tattare da Aishan
Rukayyan ta tabbatar mata ba haka bane. Sai dai bata yarda da hakan ba; gani takeyi
kamar Rukayyan ce bata gane ba. Don haka har saida cikin nan yayi wata uku sannan
ta sanar da Abban Sadik wanda daman ya riga ya gane kyaleta kawai yayi.
Tunda ta san ta sanar da shi cikin nan kuma bata ji ya ce Aisha ma tana da ciki ba
sai ta tsiri fitna; kullum akwai abinda zatace ya sa Aishan ta dafa mata daga
karshe kuma idan an dafa bata ci sai ta san abinda tace bai yi mata ba. Da kanshi
ya gane hakan ya daina biye mata.
Namiji take so ta haifa don haka sosai ta dage da addu’a Allah ya sa namiji ne a
cikinta, sai da cikin ya kai wata biyar sannan taje aka yi mata hoto wato scanning
inda aka tabbatar mata namijin ne.
--------
Kwanci tashi cikin Zahra har ya kai wata bakwai, ya riga ya fito sosai gashi da
alama yaron da yake cikin nata yana da nauyi sosai. Dole yasa take hakura da
kusantar Abban Sadik kamar yanda take so, ya zama sau daya a mafi yawancin dare
wasu lokutan ma kuma idan yaga yanayinta haka yake lallabata suyi bacci ba ayi
komai ba.
Babu abinda yake bata mata rai a rayuwarta kamar ta tuna cewa Yusuf yana da wata
matar da zai iya biyan wannan bukatar da ita. Ta fiso ace ita kadai Yusuf zai iya
kusanta, idan kuma ta kama dole sai an hada da wata to ta zama itace a sama.
Yanzu da bata iya yi masa yanda take so tabbas ta san ranar kwanan Zahra kwana
sukeyi suna faranta ran juna, watakila ma shi yasa a mafi yawancin kwanta yake
lallabata suyi ta bacci kawai; duk da tayi masa bayani sau babu iyaka cewa zata iya
don babu inda yake mata ciwo amma ya ki ya saurareta.
……..
Ita da Jummai ne kawai a gidan saboda yara duk sun tafi makaranta, maigidan kuma
daman ba a wajenta yake ba. Jummai tana kasa tana ayyukanta yayinda ita kuma take
zaune a falon sama tana kallon TV.
Jummai ce ta kwankwasa mata kofa ta sanar da ita zuwan Hajiya Amina, nan da nan ta
bayar da umarni ta hawo sama. A nan fridge din saman ta samar mata ruwa da lemo
suka zauna sun hirarrakinsu.
‘To ke kuwa ya za ayi a zo gidana kuma a fini iyawa? Ai ba zai ma yiwu ba. Kin san
cikin ma da na dauka tana da shi ashe babu komai in gaya miki.’
‘Ke kawata?’
‘Allah kuwa, kuma kin san nayi scanning an tabbatar min namiji ne a ciki na.’
‘Kada ki damu dayan ma yana tafe in sha Allah. Yanzu kawai damuwata na san a ranar
kwananta kashe dare suke suna harka tunda in ya zo nan sai yayi ta wani faman nuna
min tausayi na yake ji wallahi duk jarabata haka nake kyale mutumin nan saboda
takaici. Ko da yake na san dama haka yake idan ina da ciki da ya fara girma yake
rage wannan bukatar, to amma yanzu kin ga ai ba kamar da ba da nake ni kadai.’
‘Kai kawata, kina faman motsi da kyar ki dinga tausayin kanki mana. Ki barshi kawai
wallahi damarsu ce, amma da kin haihu ki nemi Hajja ta hadaki da kyau sai ki koma
aiki.’
Haka suka cigaba da hirarrakinsu har wajen azahar sannan Aminan tayi mata sallama
ta tafi.
Ta kula Amina ba zata taimaka mata wajen karkato Abban Sadik ya rage kusantar Aisha
ba don haka ta barta da zancen, amma bata fasa tunanin mafita ba don tayi lissafi
ta ga daga yanzu zuwa tayi arba’in akwai wajen wata biyar kenan da zai je yayi ta
kusantar Aisha tana nan tana kallo.
Gashi ba gidansu daya ba balle ta gane me yake faruwa idan ya shiga dakin Aishan.
‘Yan kwankin nan idan yayi mata sallama ya tafi haka take kasa bacci saboda
takaici. Da haka ta yanke shawarar zata nemi Hajja ko da akwai abinda zata iya bata
tunda dai ta san tana da abubuwan da idan aka sakawa mutum a abinci za a tayar masa
da sha’awa don haka ta san na kashe sha’awar ma ba zai gagara ba.
‘Hajiya kenan, Uwar Saddiku baki da wasa. Kada ki damu akwai abinda zan taho miki
da shi kawai ki tanadi dubu goma da kuma kudin montana shikenan.’
Yamma tana yi kuwa sai ga Hajja. Nan suka zauna a falonta, bayan sun gaisa tace
‘Hajja, kin san me nake so? Wallahi so nake idan kina da wani abu wanda kika san
baya cutarwa amma dai ya zama ko da ya je wajen matarsa ba zai iya komai ba, a
kalla zuwa lokacin da zan haihu na dawo normal sai mu cigaba da karawa.’
‘Uwar Sadiku kenan, kin san kan tsiya. To akwai abinda zan baki, shayi kawai zaki
dafa dashi ko zobo idan dai ya sha babu abinda zai iya komai kokarinta sai bayan
akalla awa goma Sha biyu. Ke wasu ma har awa ashirin da hudu. Kedai aikin da zakiyi
kawai shine ki san yanda zakiyi duk ranar kwanta ya sha wannan hadin musamman bayan
magriba.’
‘Babu wata illa, da zarar ya dauki lokaci zai fita daga jikinsa ya cigaba da
harkarsa normal.’
Cikin walwala ta karasa wunin ranar; ko babu komai ta san abinda yake hanata bacci
ya kau don haka yau akwai bacci harda minshari.
…….
Yaran su kadai ya samu a falon kasa don haka bayan sun yi masa sannu da zuwa ya
basu ledojin da suke hannunsa wadanda kazar Yahuza suya ce a ciki.
Nana ce ta dauke ledojin yayinda Abban yace
‘A kaiwa Mommy ta dauki nata tukunna, kafin kurar gidan taga menene a ledar.’
‘Abbaaa!’
‘Na’am, ni ai ban kama suna ba ko?’
Sukayi dariya gaba daya suka nufi saman, shima Abban ya bisu a baya.
Tana zaune a falonsa a kan kafet ta mike kafafun ta dorasu a kan filo saboda yanda
suke dan kumbura. Daga gefen damanta jug ne cike da zobo yana gumi saboda sanyi
yayinda take rike da karamin kofi mai dauke da zobon da alamu sha takeyi.
Suna shiga suka zube a gabanta suna yi mata bayanin naman da Abba ya siyo yayinda
Abban ya wuce ya zauna a kan kujerar bayanta. Ta bude ledojin ta dauki nata, ta
mikawa Yusra sauran tana fadin
‘Gashi nan kowa ya dau daya sai a sakawa Ummi nata a fridge tunda tayi bacci.’
Ta sake yiwa Abban sannu da zuwa, bayan ya amsa ya dubi kofin hannunta yace
‘Zobo kam ai na mu duka ne, suma yaran duk sun sha da rana. Bari na dauko kofi na
difara maka don ma kada na cika maka ciki ka kasa cin abincin amarya.’
Ta kurbe ragowar wanda yake kofin hannunta tana kokarin mikewa, ya dafe kafadarta
yana fadin
‘Ba sai kin dauko wani ba, zuba min a wannan tunda kin shanye. Kadan zan sha na
wuce sai ki cigaba da jin dadin ki.’
Ta zuba masa zobon a kofin da ta shanye, ya dauka yana zuka a hankali suna hira.
Sai da shanye kofi guda ya kara rabi sannan yayi mata sallama ya fice.
Tabi bayansa da kallo tana murmushin mugunta; ta san duk daren da ya siyo kaji irin
wanna to hirar dare yake so ayi, yanda ya sha zobon nan kuwa ta san wannan hirar ta
yau babu abinda zai iya.
-------
Tun da yamma ya sanar da ita kada tayi abincin dare don zai siyo abinci. Shayi
kawai ta dafa mai kayan kamshi suka baje a falo suka gama ciye-ciyensu suna
hirarrakinsu.
Sai da suka gama komai suka kwanta a nan labarin ya canza, duk yanda ya kai ga
sha’awarta da son ya kusanceta abun bai yiwu ba. Yayi iya kokarinsa itama tana
taimaka masa amma abu yaki, daga karshe itace ta koma tana bashi baki saboda yanda
ya shiga tsananin damuwa. A tunaninsa bashi da lafiya, amma kuma babu wani rashin
jin dadi da yake ji, haka ya kwana cikin damuwa da tashin hankali.
Da asuba bayan ya dawo masallaci ya sake kokarin gwadawa amma shiru, nan ma haka ta
dinga nuna masa ita bata damu ba yayi kokari kawai ya je asibiti a duba shi.
Da gari ya waye ya shirya ya fice office da niyyar idan ya rage aiki zai nemi
likitanshi ya ji yanda za ayi. Yanayin aiki da kuma kasancewar babu wani abu da
yake masa ciwo sai ya manta, sai da yamma bayan ya tashi daga aiki sannan ya tuna.
Yana tunanin yanda za ayi da yammannan ya sami likita sai kuma ya tuna kwanan Zahra
ne yau ita kuma dama ba cikakkiyar lafiyace da ita ba, don haka ko bai kulata ba ma
babu damuwa.
Haka ya koma gidan.
Kamar kullum bayan ya gama hidimarsa ya kwanta, tana lalubensa yana gocewa saboda
baya son abinda ya faru jiya da Aisha ya sake faruwa. Amma kuma a hankali sai yaji
kamar zai iya, nan da nan kuwa suka shiga hidima yana jin dadi. Don haka sai yayi
tunanin matsalar ta jiya ce kawai abun ya wuce.
Haka yayi kwana biyun nan a wajen Zahra lafiya kalau don haka cikin walwala ya koma
wajen Aisha.
Ga mamakinsa duk yanda ya kai ga dagewa tsakaninshi da Aisha sai kallo, haka yayi
kwana biyun nan yana mamaki. Ita kuma sai dai ta dinga kwantar masa da hankali tana
nuna masa ba komai bane, musamman da yake ya gaya mata zai je yaga likita.
A hankali ya zama kullum idan dai ya shigo yiwa Zahra sallama zai tafi wajen Aisha
zai tarar ta ajiye zobo, shayi ko kuma kunun zaki, shi kuma da ta yi masa tayi sai
ya sha sannan zai tafi.
………..
Haka rayuwarsu ta cigaba, yaki yaje asibiti musamman da yake yana samun biyan
bukata a wajen Zahra. Sai dai yana mamakin yanda akayi ranar da yake wajen Zahra
lafiya amma da yazo wajen Aisha sai ya kasa komai.
A cikin tattaunawarsu da Aisha ya sanar da ita idan yaje wajen Zahra baya samun
wannan matsalar. A tunaninta asiri ne Zahran tayi amma ta kasa gaya masa, sai dai
ta dage da neman maganin karya sihiri.
Musamman ta sami ruwan zamzam take yi addu’ar karya sihiri tana sha tana wanka, shi
kuma duk wani ruwa da zai sha a gidan nan sai ta yi masa addua’ar a ciki amma babu
wani cigaba. Yanzu ma an kai matsayin da ta daina bari ya jagwalgwala ta, shima
kuma ya daina rawar kai a kanta. Sai dai kullum cikin bata hakuri yake yana yi mata
alkawarin zai je asibiti a duba shi amma dai ya kasa zuwa, ita kuma bata bashi
kwarin gwiwar yaje asibitin ba saboda ta riga ta yarda sihiri ne, don haka dai ta
dage da addu’a.
__
Ranar Alhamis Zahra ta tashi da ciwon nakuda sai dai da yake ciwon bai zo mata gaba
daya ba ta cigaba da aiyukanta tana yi tana hutawa. Ba kwananta bane amma dai ta
riga ta sanar da shi tana nakuda don haka ranar gaba daya a cikin sauraron kiranta
yake.
Tun wajen karfe biyar na yamma ya dawo daga aiki, wajen Zahran ya fara shiga bayan
ya dubota sai ya koma wajen Aishan tunda yana nan da ta ji wani ciwo sai tayi masa
waya.
Sai bayan sallar magriba sannan ta kirawosa, a gurguje ya shirya yayi sallama da
Aisha bayan ya sanar da ita idan akwai abinda yaran suke bukata zai ce su karba a
wajenta.
Tun wajen karfe bakwai suka shiga asibitin aka shigar da ita labour room, sai wajen
karfe taran dare sannan ta haihu.
Dakin da ta haihu ita kadai ce a ciki sai ma’aikatan lafiya da likita, likitan yana
tsaye a daidai kanta yayinda matron da kuma nurses uku suke daidai kafafunta suna
dubawa suna taimaka mata. Tara da minti biyar tayi yunkuri ta haifi yarinyarta
santaleliya, a take matron ta yanke cibiya ta dauki yarinyar ta mikowa likita. Ya
karba ya dubi Zahra da take kwance yace
‘Sannu Hajiya.’
Ta amsa tana murmushi.
‘Mace?’
Likita yace
Nan da nan ma’aikatan lafiya suka shiga kokarin wanke mai jego da abinda ta haifa,
daga baya aka fito aka sanarwa Abban.
Bayan likitan ya fito yayi masa duk wani bayani kuma ya sanar da shi zasu riketa ta
kwana in ya so zuwa gobe da yamma za a sallameta.
A hanyarsa ta komawa gidan ya dauko kanwarta wadda zata tayata kwana a asibitin
suka wuce gidan. Nan da nan ta zabo mata kaya ta hado mata dan abinda zata ci. Babu
yanda bai yi da su Yusra su tafi gidan Aisha su kwana ba suka ki, kananunma sun
riga sun fara bacci don haka tace zasu iya kwana. Haka ya hakura ya sa Sadik ya
rufe musu gidan suka koma asibiti.
Ko da suka koma asibitin saida ya siyo musu duk abubuwan bukata ya kawo kudi ya
bata sannan ya kamo hanyar gidan.
Wajen Aisha ya fara shiga inda dama a nan ya kamata ya kwana, yana shiga yayi mata
sallama ya sanar da ita zai kawo mata Rukayya sai ya kwana da sauran yara.
Tace
‘Dare yayi wallahi, don Allah ka barta tayi baccinta sai da safe kawai. Idan kuna
bukata wani abu kawai ka sanar da ni.’
Tunda aka canza mata daki aka gyara Baby aka kwantar da ita a kusa da ita take
mamaki, tayi scanning an gaya mata namiji zata haifa yanzu kuma ta haifi mace.
Ta dubi Rahma; wadda kanwace a wajenta wato ‘yar kanwar babarsu, mijinta ne ya rasu
tun yaronta yana karamin kuma bata sake aure ba shi yasa duk irin wadannan abubuwan
ita ake kira.
Tace
‘Rahama kin san kuwa nayi scanning an ce min namiji zan haifa, amma kinga ikon
Allah mace na haifa.’
‘Um, ai wallahi Anti abun fa na Allah ne dama likitocin ma lalube suke a duhu
abinda Allah ya boye ai mutum ba zai iya gani ba.’
‘Hhhh! Kin san da ace ba ni kadai ce a dakin haihuwar nan ba Allah cewa zanyi canza
min suka yi.’
Ta kyalkyale da dariya
‘Lallai Anti, kuma kinga gata nan kamar ‘yayanki don wannan sak yanda kika san
Sadiku yana jariri.’
‘Hmmm!’
Ta yarda mace ta haifa kuma tana kaunar yarinyar amma dai tabbas ta saka ran
haihuwar namiji, don haka ne ma ya saka komai kayan yara maza ta siya.
Haka dai ta yi ta wasi-wasi har bacci ya kwasheta.
……..
Da wuri Aisha ta tashi tunda ta san Zahra bata nan, ta soya doya da kwai yanda zai
ishesu gaba daya sannan ta dafa ruwan zafi ta zuba a babban flask, ta dafa shinkafa
da miya. Bayan ta gama wajen karfe bakwai saura ta kirawoshi a waya tace ya turo
yara su dauki abinci.
Ta san watakila zasu dau lokaci kafin su karaso kuma ta san idan da shi suka taho
yana da mukulli don haka tayi sauri ta shiga wanka tunda itama zata je aiki.
Ta fito daga wankan daure da karamin tawul dinta ta ji shigowarsu falon yana mata
sallama. Nan da nan ta dauki jilbab dinta ta zura ta fito falon tana amsa sallamar;
shi da Nana ne da Rukayya.
Bayan sun gaisheta ta amsa ta nuna musu kwanukan suka fara dauka, ya dubeta yace
Ta bashi amsa da
‘Eh.’
‘Rukayya tunda kowa ya shirya sai ku ci abinci kawai kowa Yaya ta zuba masa na
makaranta na san yanzu Malam Sule zaizo sai ku tafi. Kafin ku dawo Mommy ta dawo
mana da babinmu.’
Aisha ta tambayeshi kwanan masu jego ya sanar da ita basuyi waya ba sai daga baya
idan gari ya kara wayewa.
‘Bari nayi serving abincin kawai da na sako kaya sai mu ci kada yara su zo suna
jirana.’
Ta juyo ta kama hanyar kichin yayinda shi kuma ya juyo da kujerar dining table daya
ya zauna don ya jira ta. Har ta shiga kicin din kuma sai ta dawo ta tube jilbab din
jikinta ta jefa kan kujerar zaman mutum uku, ta cigaba da kaiwa da kawowa tana
kwaso abinci daga kicin tana ajiyewa.
Idonsa yana kanta har ta gama, sauri takeyi don haka bata ma kula da yanda yake
kallonta ba.
Bayan ta gama ajiye abincin ta bi ta gabansa ta wuce da niyyar shigewa daki. Bata
kula da lokacin da ya mike tsaye ba sai ji kawai tayi ya kama hannunta ya dawo da
ita ta fada jikinsa. Duk yanda ta so ta kwace kasawa tayi, don ya riketa sosai kuma
dama ya gama sanin lagonta.
Wajen wata uku kenan rabonsa da ita, yau din kuma ji yake kamar zai iya biya mata
bukata. Ko ma dai menene ba zai iya hana kansa ita din ba a yanzu, ya san abinda
take tsoro kuma ya ji a jikinsa babu wannan matsalar don ko daga yanda ya riketa
itama ta ji alamun hakan. Da kyar ta lalubo muryarta tace
‘Malam Sule yau Antinsu ba zata aiki ba ku wuce ka kai yara kawai sai ka wuce
office ka jira ni.’
Nan da nan ya kife wayar ya jefata kan kujerar zaman mutum uku.
Ko ba a gaya mata ba ta tabbatar yau lafiyarsa ta dawo, sai wajen takwas saura
sannan ya kyaleta.
‘La ilaha illallahu, yau ka makarar dani zaka sa principal tayi ta yi min mita.’
Haka tayi sauri ta shiga wanka, Koda ta fito ya riga ya saka kayansa yana falo yana
jiranta.
Da taga dai karfe tara ta kusan yi haka ta hakura tayi waya makarantar ta sanar da
su ba zata sami zuwa ba.
Daga baya ya shirya ya wuce asibiti ya barta a gidan yana mata dariya.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
14
Har Abban Sadik yaje asibiti yana mamakin yanda akayi yau lafiyarsa ta dawo a wajen
Aisha, duk wani lissafi yayi shi amma ya kasa samo amsar. Abu daya ya iya yankewa
duk da ya kasa tuna tabbas din abinda ya faru kuma baya son ya zargi Zahra. Yana
zargin kamar duk ranar da ya sha zobo ko shayi a wajenta to idan kwanan Aisha ne
baya iya komai, domin a iya lissafinsa wannan zobon ne kawai bai sha ba tunda a
asibiti ta kwana, shi yasa bai sami matsala ba. Ya yanke shawarar zai sa ido ya
gani kuma ba zai sake yarda ya sha zobon nan ba sai dai idan ranar kwananta ne ita
Zahran.
Yana isa asibitin aka sallamosu, don haka ba tare da bata lokaci ba ya dauko su ya
dawo da su gida. Nan da nan aka shiga hidima da mai jego.
A ranar ya kamata ya dawo kwananta amma ta san a bisa al’ada kamata yayi ta barwa
Aisha kwanan sai tayi arba’in.
Bata da matsala da hakan don tuni ta kirawo Hajja don ta karo mata maganin da ta
bata don ta cigaba da dafa masa zobo; tayiwa kanta alkawarin yanda tayi jegon nan
shima haka zai yi.
Tunda yamma ta sanar da shi ta barwa Aisha kwanata har sai tayi arba’in, yaji dadi
sosai kuma ta kara daraja a idonsa.
Saida ya gama duk abinda yakeyi a cikin gidan sannan ya shiga dakinta yi mata
sallama. Ita kadai ce a dakin tana zaune a kan gado domin baby tana bayan Rahma
kuma suna falon kasa.
Ya zauna a dai-dai kafarta yace
Ta jijjiga kai
‘To ni zan wuce, Sadiku zai rufe muku kofa sai ya kawo miki mukullan.’
Ta dubi flask din da yake kan durowar gefen gado tana gyara zama tace
Ya jijjiga kai
‘Ai yau bazan sha shayin nan ba don a koshe nake, ki ajiye flask dinki kiyi ta
tsiyaya kina sha a hankali.’
‘Ki daina tempting dina, yau a koshe nake kin san daga wajen liman nake a nan muka
zauna aka bankare mana kaji da gurasa muka ci. Abincin daren ma da kyar zai sami
shiga yau.’
Duk wayonta haka ta hakura ya fita ba tare da ya ko kalli flask din shayin nan ba,
yayi mata sallama ya wuce wajen Aisha.
Yana fita ta fara nadama, ta san ba zai iya gane ta saka wani abu a shayin ba to
amma me yasa ya ki sha? Gashi sai da ya bari ta barwa Aisha kwananta sannan ya wani
ki shan shayin. Saida tayi kwalla saboda takaici; tayiwa kanta alkawarin zasu hadu
gobe.
…………..
Da mukullinsa ya bude gidan kamar yanda ya saba ya shiga, tana falo tana karatun
littafi da shayi kofi daya a gabanta tana sha. Bayan tayi masa sannu da zuwa sun
gaisa ya dubeta yace
‘A’a, jegon har ya fara tabaka ne? Yau fa kwanan Mommy ne ko ka manta ne?’
‘Babu wani jego ai haka akeyi, tunda tana jego ai ke zaki karbi kwanan zuwa tayi
arba’in don kema idan kika haihu haka zata yi. Don haka ki shirya ina nan har
arba’in.’
Tayi dariya
‘Gaskiya dai ka koma, ni ban karbi wannan kwanan ba. Kawai saboda ta haihu sai kuma
ka barsu ita kadai da Baby, ina laifi idan ka kwana a can din. Nifa idan na haihu
babu wani arba’in duk da babu abinda za ayi amma ba zan yafe kwanan ba, ka kwana a
nan din dai like just be there ba wai ka tafi ka barni da baby ba wai kai ka gama
aikinka, tab!’
‘Abinci zan baka kaci ka koshi ka koma can in an kwana biyu ka dawo.’
Duk yanda ya so ya tsara Aisha ta karbi kwanan nan ki tayi, haka ta dafa masa
taliya ya ci ya koshi ya sha shayi sannan tayi masa sallama ta rufe kofarta ya koma
wajen Zahra.
…….
Ko da taji shigowarsa luf tayi kamar mai bacci domin tazata wani abun ya dawo
dauka.
Sai da ya shiga dakinsa ya shirya sannan ya kirawota a waya domin da baiga Rahma ba
yayi tunanin ko a dakinta zasu kwana. Ta zata ya riga ya fita don haka ta dauka
tana mamaki.
‘Ina nan fa, a nan zan kwana.’
Nan yayi mata bayani kamar yanda Aishan tayi masa, suka ajiye waya tunda dama
kiranta kawai yayi don ta san a gidan zai kwana.
Har bacci ya kwasheta tana tunanin wauta irin ta Aisha, ya za ayi abata miji kwana
arba’in tace a barshi? Ko yanzu ma da akayi haka ta san idan dai Aishan ta haihu ko
da tsiya-tsiya sai an bata kwana arba’in din nan tunda ita haka taga ana yi.
……….
Kwanansu daya da fitowa daga asibiti Aisha taje barka da kayan barkarta da ta
tanada cikin leda; kayan baby ne masu kyau da tsada. Sai da ta tabbatar yana gidan
ta shiga domin tuni ta sha jinin jikinta da matar nan.
Bayan la’asar ne suna zaune ita da shi a falonsa da Baby a hannunsa Rukayya ta
shiga falon da sallama ta sanar da Mommy zuwan Anti Aishan. Har ta mike zata tashi
ya cewa Rukayyan ta hawo da Antin nan mana. Kafin tace wani abu Rukayyan ta fice,
bata dade ba suka dawo tana dauke da ledar yayinda Aisha take biye da ita.
Babu laifi suka gaisa da Zahran da yake a gabansa me, aka mika mata Baby ta dauka
ta sa albarka. Suka dan taba hira gaba daya har Abban Sadik din, ta turawa Zahra
ledar tace
‘Ga wannan babu yawa, Allah ya rayata ya kara lafiya.’
Tayi musu sallama ta sauko ta koma gida, zuciyarta fari fes saboda yanda tayi
barkarta a gabansa tunda ta san Zahran bata yi mata komai a gabansa.
……..
Saida aka kwana biyar sannan ya sanar da su sunan yarinya, ya saka mata Sumayya. Da
kyar Aisha ta daure ta sanar da ‘yan uwanta sunan inda ta nemi Yaya Zuwaira da Yaya
Zainab su zo amma kada su taho da yara don bata son fitna.
An ci burin wannan sunan kuma an shirya taro inda aka gayyato mutane da yawa,
dangin Abban Sadik din ma haka suka zo da yawansu saboda Yaya Saratu aka bawa
goronsu na gayyatar ta tabbatar ta hado kansu sannan suka taho.
Aisha ta riga ta tambaya ko akwai aikin da zata tayasu amma Zahra tace mata babu
domin komai bayarwa za ayi a yiwo daga waje, don haka ranar sunan ba tayi shirin
tafiya gidan da wuri ba. A tunaninta ma ‘yanuwan Abban zasuyi ta shigowa gidan nata
amma har shadaya babu wanda ya shigo. Batayi mamaki ba domin dama ta san babu wanda
yake kaunarta a danginsa, tun lokacin da suka je da Zahra gaba daya suka ki sakewa
da ita. Duk da sun je ita da Abban sun bawa Hajiyan hakuri amma har kawo yanzu basu
saki jiki da ita ba.
Sai wajen sha biyu saura sannan Zuwaira da Zainab suka iso, ba tare da bata lokaci
ba suka shirya tare da Aishan suka wuce gidan sunan.
Tun daga bakin gate Rukayya ta hangosu, da gudu ta karasa ta kama hannun Aishan
tana yi mata sannu da zuwa, ta gaida su Yaya Zuwaira sannan ta wuce gaba suka bita
a baya.
Tun daga falon duk ‘yan uwan da Rukayya ta san basu taba haduwa da Aishan ba sai
tace musu
Haka har suka wuce falon sama inda Mommy take, su Yaya Saratu ma duk suna wajen
anata hira.
Suka karasa kusa da Mommy Aisha ta zauna kusa da ita su Yaya Zainab din ma suka
zauna.
Gaisheta sukeyi suna mata barka amma da kyar take amsawa tana wani dauke kai.
Suka juya wajen Yaya Saratu wadda itama da kyar take amsa gaisuwar.
Yaya Murja ce kawai ta sauraresu da girmamawa, ragowar mutanen da suke wajen suka
cigaba da hirarrakinsu babu wanda yake bi ta kansu. Don haka suma suka gyara zama
suka fara kus-kus dinsu su kadai.
Basu dade da zama ba wata dattijuwar mata ta shigo, tun daga kafar bene take zabga
kirari tana guda
‘Uwar gida Uwar Saddiku, kinyi taki kinyi ta raggo. Uwargidan Yusuf maki gani ido
ya makance. Yanda duk kika dama haka za a sha Uwargida ta Uban Sadiku ko mahassada
sun ki. Haihuwa kyautar Allah, ba rawar kai bace ba iyawa bace, ke Allah ya zaba
uwar SADIKU matar Yusufa….’
Yaya Saratu ce ta fara mikewa ta lika mata naira dubu tana fadin
‘Kin min daidai, babu karya a cikin zancenki uwar Sadiki taci dubu sai ceto.’
Abun nata ya fara yawa kuma duk wanda ya san Aisha kishiyarta ce ya san da ita
akeyi. Yaya Murja ce ta mike ta dauki kudi a jakarta ta ja matar sukayi kasa ta
sallameta.
Bata dade da fita ba su Aisha suka mike Yaya Zuwaira ta karasa kusa da Zahra ta
ajiye mata kudi naira dubu goma tace a siyawa Baby sabulu. Sukayi musu sallama suka
fito.
A gidan Aishan suka karasa wuninsu suna jajanta mata zama da wannan matar don ko su
kansu sun kula da yanda ita da ‘yan uwan Yusuf din basa ko kaunar Aisha.
Tun tuni Aisha ta san dangin Yusuf basa sonta amma sai yau ta kara tabbatarwa, don
zata iya cewa a ‘yan uwansa matar Yaya Bello ce kawai ta saurareta sai kuma Innani
wadda ita din ‘yar uwar Hajiya ce.
Haka aka gama taro aka watse, abincin sunan nan kuwa Aisha ko kalarsa bata gani ba
domin lokacin da suka fito daga gidan ba a fara rabo ba kuma da aka fara babu
wanda ma ya tuna da ita duk da an kaiwa makota abincin gida-gida.
…...
Wajen sati biyu da gama taron suna sai Yusra ta tsiri shiga gidan Aisha, haka kawai
da rana ko da daddare musamman idan Abbansu yana gidan sai Yusra ta shigo. Wata
rana ita kadai take shiga wata rana kuma ita da kannenta. Hatta Rukayya saida tayi
mamaki saboda Yusra bata taba shiga gidanba amma sai gashi yanzu kusan duk ranar da
Abbansu yake gidan sai ta shiga.
Amma da zarar Abban ya zauna an kawo abinci aka ce ta zo ta ci sai taki, tace ita
ta koshi. Sai dai kawai su zauna a falo suna kallon TV.
Yau shinkafa da miya Aisha ta dafa ta hada salad ga kuma zobo. Tare suka zauna da
Abban suka fara cin abincin, sai dai da kyar ta hadiye lomar farko saboda dandanon
miyar bai yi ba. Ta ajiye cokalin tana jira taji mai zai ce.
Tace
Kamshin miyar ya canza gaba daya, gashi yana wani santsi da dandanon mara dadi.
Dole ta dauke wannan miyar ta kawo musu mai da yaji suka ci abincin nan domin bata
ma da wasu kayan miyan gashi abincin dare ne.
Haka suka kwana tana mamakin abinda ya bata mata miya, har gari ya waye bata gane
ba don haka ta cigaba da harkokinta.
Bayan an kwana biyu kuma ranar asabar tayi tuwon shinkafa da miyar gyada da rana
shima ga mamakinsa yanda waccan miyar tayi wannan ma haka tayi.
Dandanon babu dadi ga shi kuma har wani bashi miyar takeyi, dole ta tashi tayi
sauri ta kada musu miyar kuka suka ci tuwon.
Sanda ta ajiye abincin dare tana kula da Abban Sadik sai da ya dandana kadan sannan
ya saki jiki yaci.
Daga baya kuma suna zaune a falo suna hira da daddare yake tambayarta
‘Wai kuwa kin gane abinda yake bata miki miya, ko kayan kamshi da kike sakawa ne?’
‘Wallahi ban gane ba, bana jin kuma kayan kamshin ne amma dai zan cigaba da
dubawa.’
‘Ya kamata dai ki kula sosai, idan ma wani abune yake shiga abincin sai ki mayar da
hankali ki gyara.’
Ta kula da yanda yake kokarin ya zargi ko tana saka masa wani abun a abinci wanda
hakan ya sosa mata rai, sai dai itama ta rasa abinda yake faruwa da miyar tata.
A ‘yan kwanakin nan saida abincinta yayi irin haka wajen sau biyar, domin har dafa
duka tayi wadda ta dinga yi musu kanshi da kumfa kamar sabulu.
Gaba daya ta shiga damuwa, amma ta kasa gane inda matsalar take. Gashi Abban Sadik
ya fara hakura da abincinta sai yaje waken Zahra yaci. Don haka ta mayar da hankali
take ta rokon Allah ya yaye mata kuma ya nuna mata abinda yake faruwa kada taje ta
cutar da su ita da Abban Sadik din.
……
Ranar Alhamis ce, kamar yanda suka saba a kwanakin nan Yusra ce da Nana a zaune a
falon Aisha bayan sallar la’asar. Kallon TV sukeyi ta tashi ta shiga kicin ta dora
abincin dare; tuwon miyar kuka ta dora wanda bayan ta sa komai a wuta ta fito daga
kicin din ta shige daki.
Tana shigewa Yusra ta dubi Nana tace
Da gaggawa ta karasa kusa da cooker, ta kai hannu ta dauki murfin tukunyar miya ta
ajiye a gefe. Ta zaro 'yar farar ledar da ta ke daure a jikin siket dinta ta bude,
da sauri ta debi abinda yake cikin ledar ta barbada a miyar ta juya ta kulle ledar
ta rike a daya hannunta. Ta dauki murfin tukunyar wanda murfin glass ne tana
kokarin rufe tukunyar, bata san yanda aka yi ba murfin ya subuce ya tarwatse a
kasa. Karar faduwar murfin ya sa Aisha ta karaso kichin din da gudu wadda dama tana
hanyar dawowa kicin din, itama Nana da sauri ta karasa kicin din.
Yanda Yusran take kallonta tana rawar jiki ya sa ta san bata da gaskiya, ta karasa
a hankali tace
Tana karasawa ta kula da ledar da take hannun Yusra, ita kuma tana ganin hankalinta
ya kai kan ledar tayi sauri ta fara kokarin boyewa.
Da sauri Aishan ta cafke hannunta ta dauki ledar tana budewa da mamaki tana fadin
Tayi tsuru-tsuru tana kallonta tas tana wani murguda mata baki tace
‘ba komai.’
Ta fara kokarin juyawa ta fita daga kicin din Aishan ta daka mata tsawa, take ta
tsaya.
Ta kwance ledar ta duba sosai tana yi tana shanshanawa; idan dai ba kuskure tayi ba
to sabulu ne sai dai an gurza shi kamar da abun gurza kubewa. Ta gyada kai; tabbas
sabulu ake saka mata a abinci ‘yan kwanakin nan da abincinta yake baci. Ta dubi
Yusra tace
‘Hhhh! Ba ni kike cuta ba Yusra, ubanki kike cuta saboda dai sabulu ba abinci ba
kuma tabbas zai iya illata lafiyar mutum musamman mutum mai shekaru kamar Abbanki.
Ni ubana ya mutu na san menene maraici, ba abune mai dadi ba amma ke naki uban kike
so ki dinga bawa sabulu saboda ki illata shi. Na san Mommy ce ta turoki, don haka
idan kin je ki gaya mata nace tsohonki kike zubawa sabulun yana ci, idan kuwa ya
mutu ku ya macewa ku da ita domin kune kaf danginku babu wanda ya kaishi kudi balle
ku sa rai wani zai kula daku kamar yanda yake yi. Garin zalunci zaku cutar da kanku
a banza.’
‘Gashi nan idan kin je kice mata nace abinda tayi min Allah yayi mata kuma kema
haka.’
Ta murguda baki ta ja tsaki sannan ta fizge hannunta ta fice daga gidan tana huci,
Nana tana biye da ita.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
15
A fusace suka shiga gidan, Anti Rahma ce a zaune a falo da Baby a hannunta. Ta bisu
da kallo bayan da suka nufi hawa sama tace
‘Ke Yusra meye zaku shigo gida babu sallama ko baki ga mutum a falon bane?’
Tana zaune a falon Abban tana kallon TV tana shan romon kaza, suna shiga suka zube
a gabanta Yusra ta kifa kai a cinyarta ta fashe da kuka. Ta dafa kanta da mamaki ta
dubi Nana tace
Da mamaki ta tambaya
‘Anti Rahma?’
‘Tace zamu kashe ubanmu kuma kowa a danginmu ba masu kudi bane sai shi, harda cewa
ita babanta ya mutu.’
Yusra ta bude tafin hannunta ta turawa Mommy ledar garin sabulun wadda dama ita ta
bata ita, nan da nan ta dauke ta zura a bayanta. Yusra tace
‘Mommy garin na rufe tukunyar ne to dama non stick ce mai murfin glass shine murfin
ya fadi ya fashe tazo tana ta maganganu.’
Suna cikin wannan maganar Anti Rahma ta hawo sama ta zauna a kan kujera tace
‘Ita da matar ubanta ne, kawai saboda ta fasa murfin tukunya shine za a zageta a
gaya mata maganganun banza har ana cewa ta zo ta gaya min saboda raini.’
Rahma ta taya su jimami da mamakin yanda murfin tukunyar zai sa ayi haka, tace
‘To ai murfin tukunyar bai fi karfin uban Yusra ba da za a zageta a kai kwanukan
nan da kai da kanka ma kake fasawa shine harda zagi. Kai wasu matan dai sun kwashe
kayansu daga gaban ma’aiki.’
Sukayi shiru na dan lokacin, jim kadan Mommy ta zabura ta mike ta tsallake su ta
wuce daki, jimawa kadan ta fito da mayafi ta dubi su Yusra tace
Sadik ne ya shigo yana rike da hannun Ummi yana karasa shigowa yace
‘Mommy kowa yana cikin gida wannan yarinyar tana baya tana ta faman wasan kasa,
kalli jikinta fa.’
Rahma ta sha gaban Mommy tana mika mata Sumayya tana fadin
‘Haba Yaya, ai bata isa kije ba saboda wannan maganar. Riketa muje sai na ji
uzirinta, ai idan kika je raini sai ya shiga tsakani.’
Ta karbi Sumayya ranta a bace; bata so Rahma ta hanata ba don da sai ta tafi da
yaran ta sa Sadik ya mammari Aishan.
Tunda Abbansu ya daina shan zobonta a kan kullum sai yace cikinsa yana bashi
matsala ta shiga damuwa saboda ta san yana samun biyan bukatarsa a can. Don haka ta
fito da wannan dabarar domin ta san idan ranshi ya baci wajen abincin dare to daren
ba zai yi dadi ba. Da farko gishiri tayi tunanin a dinga karawa sai kuma taga ai
idan gishiri ne da an ci za a gane ta fi son abinda idan ya ci zai zargi ko wani
abun ne na asiri aka zuba masa; don haka ta sami sabulu.
‘Muje Yaya.’
Mommy ta dubi Sadik wanda Nana ta gama yiwa bayanin abinda ya faru tace
‘Ka bisu kaima saboda naga matar nan saitin ta yana gocewa.’
Rahma tace
Haka Rahma ta wuce Yusra, Nana da Sadik suka bita a baya suka nufi gidan Aishan.
……..
Su Yusra suna fita Aisha ta zubar da miyar, ta gyara wajen. Har zata dora sabuwar
miya sai kuma taji hankalinta bai kwanta da tuwon ba ma don haka sai ta sauke ta
sheka masa ruwa tunda daman rude kawai tayi.
Ta fito daga kicin din ta zauna a falo da niyyar idan tayi sallar magriba ta dafa
musu jollof kawai.
TV a kunne take amma bata gane me ake fada a TV din tunani kawai take tana mamakin
me ta tsarewa Zahra.
Tana nan zaune aka buga kofa don haka ta tashi ta bude, batayi mamaki ba da ta
gansu don ta san sai wani abun ya biyo baya.
Babu yabo babu fallasa Rahma tayi mata sallama don haka ta wuce ciki bayan ta cewa
Rahman Bismillah. Suka karasa falo suka zauna, ita Yusra sai faman muzurai takeyi
tana murgude baki shi kuwa Sadik ko zaman ma bai samu yayi ba, tsayawa yayi a
kansu yana muzurai kamar wani soja. Ta bi su da kallo, har zata cewa Sadik din ya
zauna sai kuma ta fasa don ba ita ta hanashi zaman ba. Bata son kallon da yake
mata; tunda take a rayuwarta bata taba kallon idon mutum taga zallar kiyayya ba
kamar yanda take gani a idon Sadiku.
Rahma ta katse mata tunanin tana gaisheta, babu izgilanci ko alamar fushi a maganar
Rahman don haka itama ta dan saki jiki suka gaisa ba yabo ba fallasa.
Rahman tace
‘Yar taki ce tace ta fasa murfin tukunya kuma sai tazo da maganganu marasa dadi,
shine nazo na ji wai me ya faru ne?’
Kamar ba zata yi magana ba, ta dan kauda kai tana murmushi sannan tace
‘Haba dai murfin tukunyar me? Abinda kaima a hannunka yana fashewa.’
Nan ta mayar mata da abinda ya faru da kuma sabulun da ta kama Yusran da shi, tace
‘Murfin tukunyar bai dameni ba kwata-kwata amma ace yarinya kamar Yusra ta san
yanda zata bi ta cutar dani saboda ina auren babanta ai kinga dole na zata aikota
aka yi.’
Mamaki ya cika Rahma, ta juya ta kalli Yusra. Yanda yarinyar tayi tsamo-tsamo ya
tabbatar mata lallai ta aikata. Ta mayar da dubanta ga Aisha tace
‘Ikon Allah! To don Allah kiyi hakuri, wallahi abune na yarinta don na tabbatar
babu yanda za ayi Mommy ta turota tayi wannan aika-aika. Kuma na tabbatar da taje
bata gaya wa Mommy din abinda tayi ba, ta dai ce ta fasa miki murfin tukunya kinata
fada. Zan yiwa Mommy din bayani in naje, yara ne sai hakuri in Sha Allah na san
haka bazata sake faruwa ba.’
‘Bari mu koma.’
Gaba daya yaran haushin Rahma suke ji saboda su zuwa sukayi ayiwa Aisha rashin
mutunci amma ta zauna tana bada hakuri.
Koda suka koma wajen Mommy din haka Rahma ta zauna tayi mata bayanin abinda Yusran
ta aikata; sai dai daga yanda Mommy din take bata amsa ta san bata gamsu ba. Domin
daga karshe ma cewa Rahman tayi sharri ne Aishan takewa Yusra, itama bata san
sharrin Aishan bane shi yasa ta kama zancen.
Haka ta taso jiki babu kwari ta sauko daga falon saman tana jiyo hayaniyarsu.
Tabbas daga wannan dan bayani da suka mayar ta gamsu ko da ba Mommy ce ta sa Yusra
wannan aika-aika ba to da saninta aka aikata; haka ta zauna tana mamakin yaushe
Zahra ta zama haka, ta watsar da tarbiyyar yaranta saboda kishi.
………
Ko da ma su Rahma basu zo ba dama Aisha bata yi niyyar gayawa Abban Sadik abinda ya
faru ba, ba ayi abun a gabansa ba kuma zuwa yanzu ta fahimci Zahra mace ce da ta
iya juya zance don haka ta barwa ranta abun. Amma idan suka gaya masa wani abu to
tabbas da shi da su bazasu ji dadinta ba.
Sai dai itama Mommy din ta gane idan ta kai masa wannan maganar abun zai zama kamar
ta kai karar kanta ne, don haka itama sai tayi shiru. Suma yaran ta gargadesu kada
su gayawa Abbansu kuma kada su gayawa Rukayya wadda lokacin da akayi abun tana daki
tana hadda.
……….
Wajen fiye da sati biyu kenan rabon da ya sha zobo a wajen Mommy, musamman da
daddare. Don haka yanzu normal yake harkarsa, duk yanda yake so yana samu a wajen
Aisha tunda ita Zahra tana jego. Baya son ya zargeta da zuba masa abun da zai taba
lafiyarsa amma dai yana so ya tabbatar ko don ya gane abunda ya haifar masa da
wannan matsalar.
Tun kafin ya karaso unguwar ya yiwo mata waya yace ta ajiye masa shayi in ya zo zai
sha kafin ya wuce tunda kwanan Aisha ne.
Da murna ta tashi da kanta ta shiga kicin don dama tunda ta haihu ko zobon zata
hada masa bata bari Rahma tayi kuma ko ya sha ko bai sha ba da kanta take zubar da
sauran ba tare da mutan gidan sun sani ba.
Nan da nan ta dafa shayin ta juye a flask ta hada da kofuna biyu ta kai dakinta
tunda yanzu mafi yawancin lokuta idan ya dawo tana dakinta.
A dakin kuwa ya sameta, tun kafin ma yace ina shayin ta zuba masa. Ya zauna a kan
dadduma ya jingina da gadonta yayinda ita kuma take kan gadon. Yana shan shayin
suna hira; a zuciyarsa yana fatan abinda yake zargi kada ya tabbata. Yana ji a
jikinsa cewa Zahra ba zata iya cutar dashi ba ko da kuwa don kishi ne.
Sai wajen tara da rabi sannan yayi mata sallama ya tafi; yana ta mamakin yanda yau
din take ta walwala fiye da ‘yan kwanakin baya, tana ta faman kakalo hira har ya
shanye shayin.
A wannan daren duk yanda yake bukatar Aisha kasa yin komai yayi, sai jagwalgwala ta
kawai da yayi. Sosai ta firgita saboda da ta fara murna cewa matsalarsu ta kare,
don haka saida ya dauki lokaci yana kwantar mata da hankali yana bata tabbacin ya
riga ya sami magani don haka daga wannan daren ba za a sake samun irin wannan
matsalar ba.
Haka suka kwana tana fatan Allah ya sa da gaske yake ya sami maganin yayinda shi
kuma yake matsanancin mamaki na yanda za ayi ace Zahra tana zuba masa wani abu a
shayin don ya kasa kusantar Aisha.
Wayewar garin ranar ya kama kwananta ne ita Zahran, har dare yayi ya shiga wajen
nata. Yayi niyyar ya tunkareta da maganar abinda take zuba masa a zobo amma kuma
har suka kwanta bacci yana wasi-wasi.
Duk saukin kanta da halayenta masu kyau da yake so amma fa bata taba karbar
laifinta; haka zata saka shi a gaba suyi ta musu a kan lallai sai ya fahimci ba
itace mai laifi ba sai dai idan wani ne mai laifin. Don irin wannan ma ya san ba
zata taba yarda tace ta saka masa abu a zobo ba, idan taga dama ma haka zata sa
kuka ta juya zancen a kan cewa shine zai zargeta tayi ta rigima har sai ya bata
hakuri.
Haka har gari ya waye sai dai kawai kallonta da yake yana mamaki; sau biyu tana
tambayarta me yasa yake kallonta shi kuma sai yace mata babu komai.
Haka ya kare wannan kwana biyun ba tare da yace mata komai ba.
Kuma duk cikin kwana biyun nan batayi zobo ko lemon tsamiya ba, shayi ma kuma da
bai nema ba bata bashi ba. Sai na safe kawai wanda yace a daina saka komai a ciki a
dinga bashi ruwa kawai zai hada shayinsa da kansa.
Ranar da zai koma kwanan Aisha ranar ne tayi zobo, lafiyayye sai kamshi ne yake
tashi ga sanyi har gumi jug din yakeyi. Duk yanda yake son zobon nan haka ya
hakura, har ta cika masa kofi ya dubeta yace
‘Kai ba zan sha zobon nan ba, bana jin dadin cikina sai dai ko wani lokacin.’
Suka cigaba da hirarsu a dining table, shi yana cin abinci ita kuma tana taya shi
hira da yake lokacin wajen karfe biyar ne don haka ita ta riga taci abincinta na
rana. Ya dubeta ya tura mata kofin zobon yace
‘Ni kam na sha nawa, wannan ai naka ne. Sai dai idan baka sha ba na ajiye da
daddare na sha.’
Ya cigaba da cin abincinsa; dama bai yi zaton zata sha ba tunda ta san ta saka wani
abun a ciki don tabbas ya san da babu wani abun a ciki da tuni ta shanye zobon nan.
Ya kusa gama cin abincin Sadik ya shigo daga makaranta, ya riga ya shiga SS 2 don
haka idan aka tashi daga makarantar yana tsayawa lesson sai biyar suke tashi. Bayan
yayi musu sannu da gida ya dubi jug din zobon nan yana gumi yace
‘Abba in dauko kofi in sha zobonka, wallahi zafi nake ji yau an yi rana.’
Abban ya bashi amsa yana nuna wanda Mommy ta riga ta zuba masa a kofi.
Da sauri Sadik ya karaso da niyyar daukan kofin, kafin ya karasa ta balla masa
harara tana kokarin buge masa hannu
Abba ya fada yana kokarin daukar kofin ya mika masa, tayi wuf ta rigashi daukewa
tana fadin
Sadik ya jefa jakarsa kan kujerar falon ya shige kichin yana gunguni, ta mayar da
kofin ta ajiye tana ta wani kumbura.
‘Zahra.’
‘Na’am.’
Ya kalleta suka hada ido, ta kau da nata idon saboda yanda yake kallonta kamar yana
kokarin karanto wani abu a zuciyarta.
Yace
‘Ko dai akwai wani abu a zobo nan ne wanda ba Sadiku aka zubawa ba ni aka zubawa.’
‘Ban gane ba? Kamar me kenan? Bayan ga irin zobon nan Sadiku ya debo daga kicin
kuma ya sha.’
‘To me yasa ba zai sha wannan ba kema kuma ba zaki sha ba?’
‘Gani nayi ai ba tarbiyya bace na zubawa ubansa abinci shi kuma ya dauka ya sha, a
kofin ma da na zuba maka. Amma idan kana so lallai ya sha zaka iya kiransa ka
bashi, ni dai ba zan sha ba tunda na gaya maka bana bukata. Me zan zuba maka a
zobon? Shekaru goma sha kana shan zobona ban taba zuba maka komai ba sai yanzu?
Saboda dai ni babu abinda zanyi na burgeka. Ai shikenan!’
Ta tura kujerar ta mike ta bar masa waje ta nufi dakinta, ya bi bayanta da kallo
yana mamaki.
Dama ya san haka zatayi domin hakan ne dabi’arta a duk lokacin da bata da gaskiya,
ya karasa cin abincinsa ya tashi ya shige dakinsa.
Ya saba bata hakuri idan sukayi irin haka sai dai yau ya ci alwashin ba zai bata
hakuri ba don shima ta bashi haushi da mamaki. Bayan sallar isha’i ya gama shirinsa
ya sameta a daki yayi mata sallama ya nufi wajen Aisha.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
16
Tun daga lokacin da Aisha ta kama Yusra tana zuba mata sabulu a abinci sai kuma ta
samu saukin fitnar Zahra, sai dai ita Aishan ta kasa sakewa da yaran gaba daya har
Rukayya. Ko da Rukayyan ta zo tayata kwana sai tayi ta kula da ita tana kula da
motsinta musamman a kitchen.
Tun wannan lokacin kuma sai fitnar Zahra tayiwa Aishan sauki, duk da bata fasa
aniyar raba Aisha da Yusuf ba ta dai bari ne kawai tana jira ta tara kudin da zata
iya bawa Malam Hatimu yayi mata aiki. Sannan kuma tunda Hajja ta bata maganin nan
ta boye a bayan wardrobe ta sami natsuwa tunda duk abinda take so yayi mata yana
yi, sannan kuma ko fada zai mata a kan wani abu da zarar ta bata rai sai ya fasa.
-------
Kwanci tashi har shekara ta zagayo an fara lissafin azumi, tunda aka ce azumi saura
sati hudu Abban Sadik ya fara maganar kayan Sallah.
Saida ya gama magana da Zahra tayi masa total gaba daya har na Aisha, ya tabbatar
mata da anyi albashi zai saka mata kudin.
Yana zaune a falon Aisha ta tada kai da cinyarsa suna hira, ya mika hannu ya dauki
wayarsa yace
‘Au, bari na turawa yayarki kudin kayan sallarku don na huta, sai kuma a shiga
hidimar azumi.’
‘Wai Mommy?’
‘Don Allah ni dai kada ka tura da nawa, ka turo min kudin zamu saya tare da su
Zahida kaga waccan babbar sallar ma haka sukayi anko babu ni.’
Tana gaya masa kuwa nan take ya tura mata dubu dari kudin kayan sallarta, sannan ya
tura wa Mommy nata da na yaranta.
Bayan ya je gidan ne take tambayarsa taga kudi amma basu cika ba; yayi mata bayani
cewa Aisha ta karbi nata zasu saya da ‘yan uwanta. Babu yanda ta iya haka ta hakura
da shirin tsiyar da tayiwa Aisha domin duk mitar ta yace mata shi ya riga ya gama
wannan maganar.
……..
Cikin azumi ya sanar da Mommy yana shirin zai je aikin Hajji kuma da ita zai je, a
take ta fara murna. Tayi masa godiya sosai sannan tace
‘Amma wallahi da ma Umrar azumi ka biya min, ka ga zuwana Hajji biyu fa zan so zuwa
Umra, musamman ta azumi. Kuma ka ga ma yanzu Sumayya bata isa yayeba.’
‘Hakane, to babu damuwa. Sai muje Hajin da Yaya Bello in ya so kafin karshen
shekarar sai na biya miki Umrar ko ba zan je ba sai kuje da Sadiku. Ita kuma
kanwarki badi sai muje Hajin da ita.’
Nan take ta sake cika da murna tunda taji yace zai biya mata suje ita da Sadik,
tana ganin kamar ma idan ta saka shi a gaba da naci ya hada harda Yusra in ya so su
tafi ita da yaranta. In ya so Hajin da yace zai je da Aisha kuma ta san yanda tayi
a ka bar zancen don tana ji a jikinta kafin shekara war haka ma ta samu an yi mata
aikin nan an kada mata Aishan.
……..
Saura kamar sati hudu tafiyar alhazai Aisha ta fara laulayi, amai da jiri babu
sassauci. Suna zuwa asibiti aka tabbatar ciki ne da ita sati hudu, aka rubuta mata
magunguna aka sallamesu.
Tun a hanya yake tsokanarta domin da ya fidda rai da yaga aurensu har ya haura
shekara ko batan wata bata taba yi ba. Yana kaunar Aisha sosai don haka yake so ta
haifa masa yara ko guda biyu ne, sannan ne zai tabbatar jininsa da tsokarsa ta
gaurayu da ta Aisha.
Don haka suka dawo gida suka cigaba da rainon cikinsu; duk da bayan ta fara shan
magungunan da aka bata laulayin yayi mata sauki tunda tana zuwa aiki kuma tana
harkokinta sosai.
Sati biyu da zuwansu asibiti ya kama ranar da jirgin su Abba zai tashi.
Tsaf Abba ya gama shirinsa yayinda Malam Sule da Yaya Bello suke jiransa a mota, ya
sa Rukayya a gaba ta hada kayanta, ya kaita gidan Aisha yace ta zauna a nan har sai
ya dawo daga Saudiya sai ta koma wajen Mommy. Ya sanar da Mommy din kuma ta dinga
duba masa Aisha don tana dauke da juna biyu. Yayi mata sallama ya fice suka kama
hanya.
Yana fita ta mike ta fara zarya a falon, wato don ma raini ita yake gayawa yayiwa
amaryarsa ciki ta kular masa kafin ya dawo? Tayi kwafa, in sha Allah wannan cikin
sai ya bare kafin ya dawo.
A take ta dauki wayarta, har ta lalubo lambar Hajja zata kirawo sai kuma ta fasa,
ta kirawo Malam Hatimu mai almajirai.
Bayan ta sanar da shi cewa wancan aikin fa tana nan tana hada kudinsa sannan ta
dora da bayani
‘Malam yanzu ciki ne da ita amma gaskiya ina so ne a lalata cikin, kwata-kwata bana
so ta haihu na fi so yanda ta shigo ita kadai ta fita ita kadai kawai.’
‘Wannan karamin aiki ne, yara ma zasu iya yinsa. Akwai laya da za ayi aiki a ciki a
baki ki samu ta tsuguna a kan layar nan, idan dai ta tsuguna to kafin awa daya
cikin ya rabu da jikinta.’
‘To Malam yanda za ayi ta tsuguna din shine matsalar don ka ga ma ba gidan mu daya
ba.’
‘Kada ki damu, ko yara ki bawa su jefa mata a masai. Na san masanku na tangaran ne
layar kuma mai sulbi ce ana jefawa ko ba a kora ba zata wuce, idan dai ta tsuguna a
kan wannan masan cikin nan sai ya fita daga jikinta.’
Tayi murmushin farin ciki, yayi mata bayanin kudi Naira dubu goma sha biyar. Nan
take tana ajiye waya ta tura masa kudin da alkawarin washegari zai taso yaro ya
kawo mata har gida ita kuma zata sallami yaron.
Cikin walwala ta karasa wunin ranar domin dama babban abinda yake firgita ta shine
Aisha ta tarawa Yusuf wasu yaran. Ta ci alwashin ko sau nawa yarinyar nan zatayi
ciki sai ta barar da shi muddin Malam Hatimu yana raye.
---------
Tunda Abban ya kaimata Rukayya Rukayyan take ta magiya don Allah suyi cake tunda
gobe da akwai makaranta kuma yanzu ta dawo na ta huta da dafa abincin makaranta.
Haka Aisha ta tashi ta hada kayan cake, da yake ta koyawa Rukayyan ma kusan duk ita
tayi aikin da yake ba Mai yawa bane. Ta gama ta zuba cake din a oven tanayi tana
wanke wanke, kafin magriba ta gama.
Ana idar da sallar magriba ta sa Rukayyan ta dafa musu indomie da kwai suka juye a
tray suna ci suna hira. Sun kusan cinyewa aka buga kofa, Aisha ta tsame hannunta
tana fadin
‘Waye.’
‘Mune.’
Ko bata ga mai maganar ba ta san Yusra ce don haka ta bude kofar tana Lahaula a
zuciyarta saboda sharrin yaran ya fara bata tsoro.
Suna shigowa falon Rukayya ta mike tsaye da kwanon abincin nasu a hannunta zata kai
kicin tana tande baki saboda indomie din da yaji. Suna karasawa ciki Sadik yace
‘Kizo in ji Mommy.’
Ta kalleshi da mamaki
‘Yanzu?’
‘A’a gobe?’
‘Ce miki akayi fa Mommy na kiranki kike tambaya Rukayya, kai kwanon kicin ki sha
ruwa ki zo kuje in ya so kya dawo.’
Ta wuce kicin din ta ajiye kwanon ta fito, ta dauki hijabinta wanda tayi sallar
magriba da shi a falon ta saka tace
Ta riga ta san wannan kiran ba na Allah bane don haka ta mayar da kofarta ta rufe
don ta san ba za a bar Rukayya ta dawo ba.
Haka kuwa akayi, tana shiga gidan Mommy tace an gama kwanan ba zata sake taya
wannan matar kwana ba. Tayi maganar kayanta aka ce yayyenta zasu kwaso mata gobe
amma ita kam ma idan aka sake ganinta a kofar gidan sai an karya kafarta. Haka ta
kwana tana matse kwalla saboda takaici; ga cake dinta a gidan wanda ta san bata isa
tayi maganarsa ba don ko an karbo ba za a bari ta ci ba.
……….
Haka da gari ya waye Aisha ta tashi ta gama shirin zuwa aiki, a al’ada bakwai da
kwata Malam Sule yake buga mata kofa su tafi, idan ya jiyeta sai ya wuce da yaran
tunda makarantar da take koyarwa ta fi kusa.
A shirye ta zauna a kan kujerar dining table tana jiransu, da taga da dan sauran
lokaci ta kirawo Yaya Zainab a waya ta sanar da ita zata zo in an tashesu daga
makaranta ta dauki Amira;’yar wajen Zainab din ce wadda shekarunta sun kai sha uku.
Ta sanar da ita Abba ya tafi Hajji kuma Zahra ta hana ‘yar tayin kwanan tata, in ya
so daga nan sai ta dinga kaita makaranta da safe suna dawowa tare tunda saura sati
biyu a bayar da hutun Sallah kuma tana sa rai kafin a koma Abban ya dawo.
Suka gama waya ta ajiye ta cigaba da kallon agogo. Har karfe bakwai da rabi ta gota
bata ji bugun Malam Sule ba, don haka ta kirawoshi a waya. Kafin ma tace wani abu
ya fara magana cikin girmamawa
‘Afuwan Hajiya, wallahi Hajiya Babbace tace yara suna makara don haka na wuce na
kaisu idan na ajiyesu na dawo na daukeki. Kin ganmu a hanya dana kaisu yanzu zan
juyo in Sha Allah Hajiya ayi hakuri da ni.’
Tace
‘Babu komai Malam Sule, ba ma sai ka dawo ba yanzu zan wuce babu komai.’
Kafin yace wani abu ta ajiye wayar tana murmushin takaici; batayi mamakin hakan ba
domin idan wannan munafukar matar ce mai fuska biyu abinda yafi haka ma zata iya yi
tunda wanda take kunya baya nan. Haka ta mike ta fita ta hau motar haya ta kama
hanyar makaranta.
Tana tashi daga makarantar kuwa ta wuce gidan Yaya Zainab, can ta wuni sai bayan
la’asar suka taho tare da Amira.
……….
Nan da nan ta sa aka shigo da shi bakin kofar falo, ko gaisawa basuyi ba ta karbi
sakon wanda yake a nannade a bakar leda ta bashi naira dubu uku tace ya hau mota.
Tun lokacin take tunanin yanda za ayi ta aika Yusra ta jefa wannan abun a toilet.
Tun lokacin da ta fasa mata murfin tukunya Yusran ta daina shiga gidan, gashi jiya
batayi tunani ba ta aika suka taho da Rukayya. Da ta sani ma da ta bari in ya so
yau din sai su yi amfani da wannan damar a jefa maganin kuma a taho da Rukayya.
Rukayyan ta riga ta bawa Mommy tabbacin a dakin baki suke kwana don haka a nan ne
take so a jefe layar tunda ta san shiga dakin Aishan zai yi wahala. Amma in dai
tana kwana a dakin bakin to tabbas ko cikin dare sai ta shiga bandakin.
Suna zaune a falo suna kallon TV bayan magriba Rukayya ta dubi Mommy cikin sanyin
murya tace
‘Mommy, kayana fa suna gidan Anti kuma harda books dina ina son naje na dauko don
gobe da su zanje school.’
Bude baki tayi zata yi mata tsawa sai kuma ta tuna dama tana neman damar da zata yi
aike gidan, ta dubeta tace
‘Ina zuwa.’
Sai da ta hau sama sannan ta kwalawa Yusra kira, tana zuwa ta jata daki.
Layar ta bata a hannunta tayi mata bayani yanda zata yi mata da ita, bayan ta gama
bayanin tace
‘Ki kula fa kada wanda ya gani, idan ta wuce ko bakiyi flushing ba babu matsala
amma idan kinga bata wuce ba to ki kora.’
Ta amsa
‘To.’
Ta harareta tace
Falon kasa ta dawo ta zauna bayan ta nade layar a siket dinta, ta cigaba da
harkarta kamar yanda Mommy din ta tsara mata. Jimawa kadan Mommy din ta sauko, tana
zama ta dubesu tace
‘Kuje ku debo.’
Nan take ta tashi ta wuce, Rukayya na tsaye a gaban wardrobe tana fito da kayanta
wadanda dama ba yawa ne da su ba yayinda Amira take jingine a jikin mudubi wanda
yake kusa da kofar bandaki. Amira tana shiga ta wuce ta zauna a gefen gado, ta kula
da yanda Yusra take mata kallon raini don haka itama ta tsare gida.
Bayan ta gama fito da kayan daga wardrobe din ta dauki jakarta ta makaranta ta bude
kamar tana neman wani abu. Ta dubi Yusra tace
‘Yaya Yusra dan zuba min kayan a ledar gata nan kusa dake, bari na tambayi Anti
books din da nayi homework naga bata sa min a nan ba.’
Kafin Yusran ta amsa ta fice tana dauke da jakar.
Tana fita Yusran taja tsaki
Tayi wuf da shige bandakin ta turo kofar, tana shiga ta jefa layar a toilet tayi
maza ta kora. Ta tsaya a gaban sink ta wanke hannunta ta danyi jinkiri sannan ta
fito.
A dai-dai lokacin Rukayyan ta shigo tana rufe jakarta wadda cake dinta ne taje ta
juyo tana fatan Mommy ba zata gani ba in ya so gobe in taje makaranta sai su cinye
ita da kawayenta.
Tana shigowa suka karasa hada kayan suka kwasa suka fice.
Suna fitowa falo Rukayyan ta yiwa Aisha sai da safe, har sun kusan fita daga falon
Aisha tace
‘Rukayya idan kin je ki kunno min ruwa idan tankin ya cika zan bugo waya sai a
kashe.’
Gida daya ne tsakanin gidan Zahra da na Aisha don haka bai sake hada ruwa ba a
gidan Aisha. Sai dai kawai aka hada tankin gidan Aisha da injin jan ruwa a can
gidan. Kafin ya tafi Hajji kullum da suba yake kunna ruwan tankunan su cika ya
kashe daga can ko kuma da daddare idan ba a can ya kwana ba. Tun ana i gobe zai
tafi ya manta bai kunna ba, ranar dazai tafi ma haka ya sake mantawa har ya tafi.
Ya gayawa Sadik ya dinga kunnawa kullum, sai dai yana tafiya Sadik din ya murder
wata waya ta yanda in ya kunna injin iya tankin gidansu kawai zai cika. Don haka ko
da suka shiga gidan Rukayya ta kunna injin tankin gidansu ne kawai ya sake cika aka
kashe.
-------
Sai wajen tara da rabi lokacin ma Amira ta fara gyangyadi a falon, suka wuce daki
suka kwanta. Bayan sun shiga dakin saida ta duba ko ina ta daga katifa ta daga
kafet don ta tabbatar Yusra bata binne mata wani abu ba sannan suka kwanta.
Can wajen Sha biyu da Rabi na dare fitsari ya matseta, tana tashi ta shiga bandakin
da yake nan dakin tayi fitsarin ta dawo ta kwanta. Minti goma Sha biyar da
kwanciyarta taji kamar ana karta wani abu a mararta, ta tashi zaune ta dafe mara ta
takure a waje guda tana fitar da numfashi da kyar.
A firgice Amira ta farka, bata gani sosai saboda duhu haka ta lalubota ta tabata
tana fadin
Da kyar ta amsa.
Take Amira ta tashi ta lalubi fitila ta kunna, ta karaso kusa da Aishan da gudu ta
dafata ta rasa me zata ce mata don haka ta fara kwalla. Ta kama hannunta tace
Sun kai wajen minti talatin a haka Aishan tana ta addu’a , a hankali ciwon ya fara
lafa mata. Har bacci ya fara kwasarta mararta ta kara katawa.
Ta yunkura saboda aman da ya taso mata, sai kuma taji ta jike. Ta ture Amira ta
mike tana fadin
A kasa ta tsuguna tana ji jini yana bin jikinta, ta taba yin bari kafin ta haifi
Abdallah don haka yanzun ma ta san abinda yake faruwa da ita. Ta kai kamar minti
goma Sha biyar tana murkususu a bandakin nan, Amira tana bakin kofa tana jiranta
cike da tsananin tashin hankali. Daga nan bakin kofar Amira tace
‘Anti na kirawo Mami a wayarki?’
Ta yunkura ta mike da kyar ta karasa gaban toilet din, ta sabule dogon wandon kayan
baccinta ta nade jinin da ta fitar a ciki sannan ta hau toilet din ta zauna.
Mararta tana kara murdawa tana matsawa jini yana sake fita, a haka har abun ya fara
lafa mata.
A hankali ta fara dawowa dai-dai, ta kirawo Amira wadda dama tana bakin kofa tace
taje bandakinta ta dauko mata pad. Ta janyo abun tsarki don ta wanke jikinta tana
murdawa taji babu ruwa.
Tabbas ta san Zahra ta hana a kunna mata ruwan kenan, dama taga ya ja baya shi yasa
tace Rukayya ta kunna. Tunda tazo gidan nan bata taba murda fanfo ta ji babu ruwa
ba sai yau, tana cikin wannan halin da take bukatar ruwa.
Amira ce ta katse mata tunanin ta kwankwasa kofar ta tura mata pad din. Ta dauke
pad din ta yiwa Amira bayani akwai ruwa a bokitin fenti a bandakinta da kuma wani a
kicin tace ta dauko mata su, in ba zata iya saukowa ba ta sami roba a kicin ta
dinga debowa. Haka Amira ta kawo mata ruwan nan ta samu ta wanke jikinta ta kora
toilet din ta goge sannan ta saka pad din ta dauro zanin da Amiran ta mika mata ta
fito ta kwanta a jigace.
Ta bude ruwan robar da ta dauko ta mika mata ta, karba ta sha kadan ta mayar mata.
‘Ki barsu Amira, da anyi asuba sai mu kirawosu. Yanzu tayar musu da hankali kawai
zamuyi ba zasu iya zuwa ba kinga biyun dare ce zata yi.’
UWAR SADDIKU
17
Saida gari ya gama wayewa sannan Aisha ta kirawo Yaya Zainab, direbanta yana dawowa
daga kai yara makaranta ta kamo hanyar gidan Aisha. Kafin ta zo Amira ta dafa musu
shayi sun sha sun canza kayansu duk da basu sami ruwan wanka ba. Yaya Zainab tana
zuwa suka wuce asibiti.
A can likita ya dubata aka ce cikin ya zube gaba daya don haka sai aka yi mata
allura aka rubuta mata magunguna suka dawo gidan.
Suna zuwa gida Yaya Zuwaira ta karaso suka hadu.
Zainab tace
‘Ko makota ai sai mu shiga a samo ko na dora miki ruwan wanka ne kafin a sami me
ruwan.’
‘Kada ku shiga, ba lallai su baku ba. Bari na kirawo Umman Janan zata sa a kawo
mana mai ga-ruwa.’
Aka bata wayarta ta kirawo Umman Janan wadda a bayan layinsu take gidanta da dan
nisa, nan take tace zata sa mai gadinta ya taho musu da dan ga ruwa.
Sai a lokacin Aisha take gayawa su Zainab ai duk makotansu nan kusa basa kulata,
duk kokarin da tayi ta shiga harkarsu sai sun tureta saboda dukansu kawayen Zahra
ne. Gaba daya gidajen da suke layinsu da masu kallonsu basa shiga harkarta, itama
hakan sai ya fi mata sauki saboda ta gane idan suna tare da ita za ayi amfani da su
a cuceta.
Kafin wani lokaci dan ga ruwa ya kawo, sai dai kuma babu inda za a juye. Nan take
Yaya Zuwaira ta tsayar da shi suka fita da direban Zainab suka siyo drums guda uku
sannan aka juye ruwan. Saida aka karawa dan garuwan kudi saboda zaman jiransu da
yayi, aka sallameshi a kan da yamma ya dawo ya sake kawo musu ruwan.
Nan da nan aka sa mata ruwan wanka, kafin ta fito an ajiye mata abinci ta ci ta sha
magunguna ta kwanta.
Nan su Yaya Zainab suka wuni, sai da yamma tayi Zahida ta karaso da Anti Uwani tare
da yara. Ana yin magriba suka tafi suka bar mata Amira da Anti Uwani.
Sai da ta huta bayan Magriba suna waya da Abban sannan ta sanar da shi bata da
lafiya, tayi bari. Sosai hankalinsa ya tashi don ya sa rai da wannan haihuwar, haka
ya hakura ya cigaba da yi mata addu’a a harami.
Tun daga wannan ranar sukayi alkawarin da mai ga ruwa kullum karfe bakwai ya zo ya
kawo mata kura guda, don bata san me yasa ruwan baya zuwa ba idan kuma matsala ce
ba aikinta bane ta kawo mai gyara.
Sati daya Anti Uwani tayi mata, ta murmure ta sami lafiya ta koma aiki sannan ta
koma gidan Hajiya. A wannan zaman ne dangin Aisha suka fuskanci kadan daga cikin
abubuwan da suke faruwa a gidan Aishan.
………
Kafin ya tafi aikin Hajji yayi musu bayani cewa za a kawo sa da rago, kuma ya yiwa
Zahra bayani sosai a kan idan an yanka sa a bawa Aisha cinya a hada mata da cinyar
rago kuma da kayan ciki.
Wajen karfe goma na safe mahauta suka zo da dabbobin, Malam Sule yana nan tunda
dama shi Abban ya sa ya tsaya masa ya tabbatar mahautan sunyi aikinsu sannan ya
sallamesu.
A nan a tsakar gida Zahra ta kafa kujera a gareji ta zauna, a kan idonta aka fede
dabbobin nan. Mutanen da suka saba karbar na sadaka suna bakin gate Malam Sule ya
ware naman sadaka da yawa ya fitar ya rabar. Ya dawo ya ware cinyar sa da kuma
cinyar rago tunda zuwa lokacin Zahra ta sa an dauke bahon da aka zuba kayan ciki
gaba daya an kai bayan gida inda ake wankewa kuma ba zai iya ce mata ta kawo a
debarwa Aisha ba.
Ta taso daga kujerar da take zaune ta karaso inda ake fidar, ta tsaya a kusa da
Malam Sule ta dubeshi shekeke tace
‘E Hajiya dama wanda Yallabai yace a kaiwa Hajiya Karama ne, shine zan mika mata.’
Ya sunkuyar da kai
Ba tare da ta bashi amsa ba ta kwalawa Hansatu kira. Nan da nan ta sheko da gudu
daga bayan gida ta tsuguna
‘Hajiya gani.’
‘Kwashi wanna naman ki kirawo Sadik ya zo ya dauki wannan a kai baya zan zo nayi
bayanin yanda za a gyara.’
Nan da nan kuwa ta dauki cinyar rago tayi bayan gida, kafin wani lokaci Sadik ya
zagayo ya dauki cinyar san ya zagaya da ita. Ta koma ta zauna ta bar Malam Sule
yana tsaye da baki a bude.
Sai da aka gama gyara naman nan tsaf ta tabbatar duk wanda ba a bayar sadaka ba an
zagaya da shi bayan gida sannan ta tashi daga wajen. Malam Sule da Mai gadi suka
hadu suka wanke wajen.
Tana zagayawa bayan gidan tace a hade naman gaba daya a saka mata a freezer tayi
miya da shi.
………..
Tunda ya sanar da ita a gidan Zahra za a yanka sa a kawo mata nama ta san ba lallai
ta samu ba. Da fari ta so tace ya bata rago a yanka mata a gidanta to amma bata so
ta nuna rashin amincewa da matarsa don tana kula da tsananin yardar dake tsakaninsa
da Zahran. Ya kawo mata itace da mai da duk wasu abubuwa da zata bukata na suyar.
Tunda gari ya waye ranar Sallah ita da Amira suka wanke kayan suyar suka ajiye
yanda da an kawo sai su fara aiki. Abu kamar wasa har la’asar ba a kawo komai ba.
Haka abun ya dinga bata dariya; wai naman sallar shi akewa wannan rowar da mugun
halin.
Ta riga tayi layya a gidan Hajiya kamar yanda ta saba duk shekara, kuma dama naman
yawanci ajiye mata akeyi. Don haka waya kawai tayi tace idan an soya a ajiye mata
wani a danye gobe sai a kawo mata.
Cinyar sa aka kawo daga gidan ‘yanuwan babansu Abdallah don haka kawai sai Umma
tace a soyawa Aisha ragonta gaba daya sai kuma a ajiye mata cinyar sa din a danye
tayi miya.
Haka kuwa akayi, washegarin Sallah da yamma aka kawo naman nan a gyare aka shigar
mata babu wanda ya gani.
......
Ranar kwana uku ga Sallah Nafisa; wadda ‘yar wa da kani suke da Abban Sadik; suka
kawo musu ziyara ita da yaranta. Gidanta babu nisa da nan gidan nasu shi yasa duk
shekara take kawo musu irin wannan ziyara.
Kamar yanda ta saba kai tsaye a gidan Zahra ta sauka, tun basu dade da zama ba
Rukayya ta kwashi yaranta su uku suka tafi gidan Aisha, a can suka ci abinci suka
ci nama da cake suka dawo. Suna shiga Bashar dan wajen Nafisan ya fada jikinta yana
surutu
‘Ummu munci nama da yawa, Anti ta bamu abinci kuma ta bamu cake da zobo baki ji
dadi ba.’
‘Um.’
Da yayi wannan maganar Zahra ta zata irin wanda ake kawowa daga makota ne, amma dai
sai ta bincika don ta san ko Abba ya munafunceta.
‘Zamu tafi Mommy, idan na fita na shiga gidan Anti Aisha mu gaisa sai mu wuce.’
‘To kuje mana idan kun fito sai ku dawo nan kafin nan na hada muku kayan yara.’
Don haka suka fice suka nufi gidan Aisha tare da Rukayya, Nana da Ummi.
Wannan ne zuwan Nafisa gidan na farko wanda kafin nan duk labaran da take samu a
kan Aisha na rashin mutunci ne don haka tana dari-dari ta shiga gidan. Cikin
mutunci da girmamawa suka gaisa da Aishan, ta sa Rukayya ta tayata suka kawo ruwa
da lemo ga kuma cake da nama. Suka dan taba hira sukayi sallama zasu tafi.
Aisha ta tsayar da su ta shiga daki ta fito da sabbin kudi 'yan dari bibbiyu ta
bawa Nafisan guda goma sannan ta bawa yaran ‘yan hamsin kowa guda biyu. Bayan ta
bawa kowa harda Nana wadda ta karba a raine sai ta boye sauran a bayanta ta dubi
Ummi tace
Sukayi dariya gaba daya ta kawo kudin ta bata. Ta sa Rukayya ta kullowa Nafisa nama
a kicin, nan da nan Nana ta bita.
Suka fito da kullin naman ta bawa Nafisa sukayi godiya suka tafi.
Suna komawa gidan Zahra suka yi mata sallama suka kama hanya.
Saida ta haye sama sannan ta kwalawa Nana kira, da hanzari ta tashi ta hau saman.
Ba zata tamabayi Rukayya ba domin tun tuni ta fuskanci Rukayyan ba zata gaya mata
abinda take son ji ba, kuma dama tun kafin a auro Aisha ta kance Rukayya 'yar
Abbanta ce domin ta fi son shi.
Sai da suka shiga kuryar daki sannan ta tambayi Nana
‘Nana wai Antin nama aka kawo mata ne da yawa take ta rabo haka?’
Ta gyara zama
‘Ai gaskiya Mommy sai dai idan rago aka yanka mata fa, kin ga naman kuwa? Manyan
robobi ne fa guda biyu duka a cike da nama kuma ga karamar roba ta kayan ciki. Ina
ga ma harda danye don kwanukan da aka ci abincin rana gasu nan duk kashi a kai.’
Ta dan numfasa
‘Allah Mommy. Kudin ma fa da bamu tana da su da yawa don ‘yan dari bibbiyu ma ta
bawa Anti Nafisan kuma da yawa za su kai ten ko twenty. Ita ta samu sabon kudi mu
kuwa da yake Abban baya nan bamu samu ba.’
Tana fita ta mike tsaye tana kaiwa da kawowa a daki; kenan Abba ya munafunceta, nan
ya ce a bawa Aisha nama ashe kuma ya zagaya ya saya mata rago. Ko kuma Aishan ce ta
gaya masa ba a kai nama ba shine ya sa aka kawo mata daga wani wajen? Yanzu haka
kuma munafuncin Malam Sule ne, don shima ta rasa yanda zatayi da shi ne da tuni ta
sa Abban ya koreshi.
Ta cigaba da tunani; gashi harda sabon kudi ya bata, kenan yanzu haka kafin ya fita
ya bata ko kuma daga baya ya sa aka kawo mata.
Yanzu kiri-kiri Yusuf ya koma munafiki, buya kenan yakeyi yana yiwa Aishan abubuwa
wadanda ita ba zai yi mata ba. Tayi kwafa tace
Haka ta wuni ranar tana shirin yanda zata bullo masa idan ya dawo.
Bata son ta ga Aisha a cikin walwala, tunda dai ta kasa rabasu da Yusuf to ta fi so
ta ganta cikin damuwa da takura. Idan dai farin ciki take so to taje ta nemi
mijinta ta bar mata Yusuf.
------
Kamar duk Babbar Sallah ranar hudu ga Sallah a gidan Umma suke wuni, don haka ma
wannan sallar duka suka hadu da yaransu.
Zainab da matar Abubakar Fauziyya suna daki waken Hajiya yayinda Aisha, Zahida da
Zuwaira sune a zaune a falo yaran kuma suna ta kaiwa da kawowarsu.
Aisha ta dubi Zainab tace
‘Haba! Ko ke fa? Tun tuni kike maganar nan amma sai wani jan kafa kike.’
‘Ba zaki gane ba Yaya Zainab. Kin san shi Yusuf da a tsarinsa yana da driver wanda
ya kamata ya kaimu duk inda zamuje, amma matarsa ta hanani morar direban nan. In
kika ga na hau motar nan to mai ita yana nan a gabansa ne amma yana juya baya haka
zata barni da hawa motar haya.’
Zahida tace
Zainab tace
‘Eh, next month zan dauki adashi dubu dari uku idan na debi wasu a kudaden hayar
gidana da nake tarawa na hada kamar miliyan daya da rabi na san zan sami mota mai
kyau kuma kinga tunda Yaya Abubakar zan bawa ya siya min na san idan da ciko zai
cika min.’
Haka suka gama hirarrakinsu Aisha ta gama yanke shawara zata sayi mota saboda ta
huta da wulakanci da Zahra take mata akan motar gidan.
………
Ya rigar ya sanar da su ranar Lahadi da sassafe zai dawo don haka duka suke ta
shirin tarbarsa.
Wajen karfe bakwai na safe aka bugawa Aisha gate, Rukayya ce da kayanta niki-niki.
Aishan ta dubeta bayan ta bude mata ta shigo tace
‘To shiga muje ga Amira can tana bacci a dakin sai ta tayaki ki ajiye kayan ku fito
muyi breakfast.’
Ta amsa ta wuce dakin, ita kuma Aisha ta koma kicin inda take aiyukanta.
Tana aiki tana dariyar Zahra; tabbas ta tabbata mai fuska biyu. Wato yana tafiya ta
turo aka kirawo mata ‘yarta saboda kada ta tayata kwana, yanzu kuma da yake ya ce
yau zai dawo shine har ta turota. Wato duk tsagerancinta ma akwai wanda take tsoro,
sai dai tsoron Allah ne kawai bata yi. Haka tayi ta aiki tana dariya ita kadai.
Karfe shida da rabi na safe jirgin su Abba ya sauka a Nigeria. Suna sauka Malam
Sule yana jiransu, a nan airport din ya sami taxi ya sa Yaya Bello don a kai shi
gida kai tsaye.
Tun da suka fara shirin dawowa dama ya sanar da su a gidan Zahra zai sauka. Tayi
shiri sosai na dawowarsa, an gyara gida sosai sannan ga abinci ta shirya masa
funkaso da farfaesun naman Sallah ga zobo kuma sai kamshi kawai ke tashi.
Karfe takwas saura kwata motar Malam Sule ta tsaya a bakin gate din gidan Zahra,
Malam Sule ya danna horn suna jiran mai gadi ya zo ya bude.
Dan ga ruwan da yake kawowa Aisha ruwa ne ya zo ya tsaya a bakin gate dinta, Abban
yana hangoshi. Ya dauki dutse ya kwankwasa gate din ya dawo ya fara sauke jarkokin
ruwan a wajen.
‘Ah, yallabai Ina ga ai ruwa ya kawo amma ban sani ba, ko na karasa na tambayo
Hajiyar?’
A dai-dai lokacin mai gadi ya zuge gate din, Abban ya bude kofar motar yana fadin
Yana isa gate din Aisha tana budewa, sanye da jilbab dinta. Ta dubi me ruwa tace
Abba yace
‘Eh ai saboda nauyi, in na kai sai na dawo na kara kaiwa har na cika drum din.’
‘Gafara.’
Yana shiga falon Rukayya da Amira suna zaune suna kallon TV. Duka suka mike suka yi
masa sannu da zuwa ya amsa ya wuce kicin ya juye ruwan. Ya dawo ya sake dauko wata
jarkar ya komo ciki.
Ta fice da gudu suka hadu da Abban a tsakar gidan yana dauke da jarka tace
Ta fice da gudu.
Haka ya gama juye mata ruwan ya cika mata drum biyu sannan ya fito ya sallami Dan
ga ruwa ya koma ciki.
A daki ya sameta tana goge inda ruwa ya zuzzube, ya tsaya yana kallonta yana
murmushi.
Bayan sun fito falon ta ajiye masa kunun aya mai sanyi da cake, ya ci ya koshi suna
dan taba hira sannan yayi mata sallama ya wuce gidan Zahra.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
18
Tunda Rukayya ta kawo labarin ya dawo yana can yana diban ruwa Mommy take faman
cika tana batsewa, dama Malam Sule ya shigo da karamar jakarsa.
Sai a lokacin sannan Mommy ta tuna Sadik ya yanke wayar injin janyo ruwan, ta
dubeshi tace
Duk nishadin da take ciki ya gushe saboda gaya mata da akayi yana can gidan Aisha
yana kai mata ruwa. Ce mata yayi a nan wajenta zai sauka amma saboda munafinci yana
can wajen amaryarsa yana hutawa, tabbas zai zo ya sameta.
Da sallama ya shigo gidan, tana sama ta jiyo yara suna oyoyo. A falon saman tayi
zamanta tana jiransa tunda dama a nan ta saka masa abincinsa.
A zaune ya sameta a kan kujera tana ta cika tana batsewa, bai ma kula da yanayin
fuskarta ba.
Yana rike da hannun Ummi ya shiga falon da sallama, bayan ta amsa sallamarsa ta
bude baki kamar wadda aka yi wa dole tace
‘Sannu da zuwa.’
‘Ya akayi babu ruwa a gidan Aisha ne, me ya sa ba a kunnawa ruwa yaje can na ga
kuma nan da ruwa don fanfon waje ma a kunne yake?’
Ya gyara zama ya zaro waya, ya lalubo lambar wayar plumber ya danna masa kira, tana
ji yana cewa lallai ya zo kafin la’asar don yau yake so a gyara ruwan nan.
Ranta ya kara matukar baci; tun da ya dawo unguwarnan yake hidimar Aisha kuma har
yanzu ma ya shigo wajenta kallon kirki bata isheshi ba balle ma ya san yanayin da
take ciki.
Ta daure ta tashi ta nufi dining table don ta kula sai ma tayi da gaske sannan zai
dubeta. Ta dauko jug din zobon da kofi ta dora a kan tray ta kawo inda yake zaune
shi da Ummi ta ajiye. Ta fara zubawa yace
Ta dauke zobon ta mayar kan table ta dauko masa ruwan roba ta kawo masa ta koma ta
zauna.
‘Lafiya kalau, mun gode Allah. Bari na watsa ruwa na fito na ci abinci kin san ban
yi breakfast ba.’
‘Sai ka fito.’
Sai da ya dauki lokaci ya shirya sannan ya fito, ya ce ta saka masa abincinsa a kan
kafet ba zai ci a tebur ba don haka nan ya baje a kan kafet ya ci funkaso sosai ya
shanye romonsa.
Naman sallan da ta sa masa a plate kuma ya ajiye a gefensa yana ci suna hira da
yara. Sai a lokacin ne take jajanta masa barin da Aisha tayi, duk ba bata je ko
kofar gidan ba haka kiri-kiri tace masa ta je.
Can zuwa azahar yana zaune a falo yana hutawa maigadi ya shigo ya sanar da shi
isowar plumber, don haka ya tashi ya fice.
Kamar yanda al’adarsa take idan dai za ayi wani gyara a gidan nan to sai dai ayi a
gabansa, don haka yau din ma tare suka zagaya bayan gidan.
Ya janyo wata waya ya dan matsa yadda Abban zai hango yana fadin
‘Ka ga wayar da aka yanke nan Alhaji, don gaskiya ba tsinkewa tayi ba sai dai ko
idan reza aka saka aka yanketa gaskiya. Tunda kuma ka ga ita kadai aka yanke balle
ace bera ne ko wani abu, kuma idan bata jiki ruwa ba zai shiga wancan tankin ba.’
‘Kada ka damu yallabai, ai yanzu za a fiketa a hada ai wannan karamin aiki ne.’
Nan da nan kuwa aka gyara wayar, ya sallami mai gyran ya saka kujera a tsakar gidan
ya zauna yana tunani.
Ya gaji da zama ya tashi ya shiga ciki ya sanar da Mommy zai je gidan Aisha.
A tsakar gida ya sami Rukayya da Amira suna ‘yar gala-gala, bayan ya amsa sannu da
zuwan da suke masa ya shige ciki.
Tana zaune a kan kujerar dining table tana cin dabino wanda shine yazo da shi
yayinda take karatun littafi.
Tayi masa sannu da zuwa bayan ta amsa sallamarsa. Ya karasa ya ja kujera kusa da
ita ya zauna yana fadin
‘Matar Alhaji, dabino kika saka a gaba haka kina ci kamar wani nama.’
Tace
Ta tashi ta shiga kicin, jimawa kadan ta fito da nama a faranti tangaran ta ajiye
masa. Ta koma ta dauko kunun aya a fridge ta ajiye tana fadin
Ta zauna tana dariya. Ya dan ci naman ya kora da kunun aya, bayan ya ajiye kofin
yace
‘Wannan ma ai naman rago ne, ina naman san yake. Naman ragon ma da ba wani yawa ne
da shi ba amma shi kika soya har ya kawo yanzu?’
Tayi dariya
‘Kai dai kaci nama, bari in sa maka filo a bayan kujerar kada ka fadi saboda santi
don naman nan ya ji onga.’
Shima dariyar yayi, ya rike hannunta wanda take kokarin karo bayansa da shi ya
kalleta suka hada ido na dan lokaci, ta sunkuyar da kanta. Ya kirawo sunanta
‘Aisha.’
Tayi murmushin yake ta kawar da kai, ta so ace ya bari idan aka kwana biyu ya huta
sai ayi wannan maganar amma daga dawowa ya rutsa ta. Tace
Ta kalleshi tace
‘Nayi layya fa kuma ka sani, a gidan Umma aka yanka aka soya danyen kuma yana
freezer na sawa a miya.’
‘Kice bana baki barwa Umma naman ba gaba daya ragon kika kwaso.’
‘A’a wallahi, Umma kam nama ai sai dai ta bayar don ya ma yi mata yawa.’
Ya cigaba da cin naman yana dan janta da hira; sai dai ko ita kanta tana iya gane
ransa a bace yake. Suna hirar yana tunani; shekara ta kusan biyu kenan da aurensa
da Aisha amma zai iya cewa bai taba bata naman layya ba kawai saboda mugunta irin
ta Zahra. Yana mamakin ma yanda ita Aishan wadannan abubuwan basu dameta ba, don
bata ma so ayi zancen. Ya tabbatar da Zahra aka yiwa haka tabbas da duk garin nan
sai kowa ya ji.
Rukayya da Amira suna nan a inda ya wuce su da zai shiga, ya kirawo Rukayya ta taho
wajensa da sauri ta sameshi a kan barandar falon.
‘Gani Abba.’
‘Rukayya bayan kwana biyu da tafiyata Hajji Anti tace ki kunna mata ruwa me yasa
baki kunna ba?’
‘Wallahi ban sani Abba, nifa ban ma san gidan nan babu ruwa ba sai yau da na dawo.’
Ta zaro ido tare da rufe bakinta saboda ta tuna wannan abu ne da Mommy tace mata
kada ta sake Abban ya sani amma bata san yanda akayi tayi wannan maganar ba. Ta
kalleshi idonta ya ciko da kwalla tace
‘To maza ki share hawayenki, babu abinda zan yi miki kuma na tabbatar bakiyi min
laifi ba.’
‘Kada kiyi min karya, tunda dama karya ba dabi’arki bace gaskiya kawai zaki gaya
min.’
Da kyar ta bude baki tayi magana saboda ta san zata sha fada a wajen Mommy
‘Dama ranar da ka tafi da daddare shine Mommy ta turo Yaya Sadik da Yaya Yusra suka
tafi dani tace ba sai na dinga taya Anti kwana ba, shine sai yau da safe tace na
dawo.’
Mamaki ya kara cikashi, yana so ya boye tsananin fushin da yake ciki a gaban
Rukayya don haka ya dan yi gyaran murya yace
‘Sai me kuma ya faru?’
‘Shikenan Abba.’
Ta tashi cikin sanyin jiki ta shige falon domin tun tuni Amiran ta shige ta barta.
Shi kuwa Abba kasa tashi yayi daga inda yake zaune, zuciyarshi sai kuna take saboda
takaici. Kenan ma bai isa yace ga yanda yake so ayi a gidansa ba idan Zahra bata
yarda ba; lallai dole ya nunawa Zahra bata isa ba.
Yana bude gate din yaci karo da Malam Sule yana shirin kwankwasa gate din
‘A’a Yallabai, zuwa dai nayi nayi maka bayani kuma na ce ka kara bawa Hajiyan
hakuri, duk da dai tace min ba fushi tayi ba amma dai a bata hakurin.’
Ya kalli Abban ya dan zaro Ido, don ya zata Aishan ta gaya masa shi yasa yake sauri
yazo ya wanke kansa kada Abban yayi fushi da shi. Ya dan yi gyaran murya yace
‘Uhm, Ranka ya dade dama da baka nan ne bama samun tafiya da ita mu kaita makaranta
saboda Hajiya Babba tace yara suna makara, to kuma ko nace mata zan dawo na kaita
sai tace na bari ta tafi a motar haya.’
‘Malam Suleman! Kana nufin tunda na tafi a motar haya Aisha take zuwa aiki?’
‘Wallahi Alhaji ba laifina bane, babu bayanin da banyiwa Hajiya ba. To tace yara
suna makara, to ba yanda zanyi.’
Ya sake rankwafawa
‘To Alhaji tuba dai nake, a kara bata hakuri. Um idan ba wani aiki ina so naje gida
ne.’
Ya rasa tunanin me zai yi, kenan tunda ya tafi Aisha take zaman hakuri gashi har
bari tayi amma bata nuna wata damuwa ba. To kenan ma ba Malam Sule ne ya kaisu
asibitin ba da ta ce masa suna asibiti. Tabbas yau dole Zahra ta gane kurenta.
Yana bude gate din gidan zai shiga aka fara kiran sallar la’asar don haka kawai sai
ya tsaya a fanfon tsakar gida yayi alwala suka jera da maigadinsa suka nufi
masallacin da yake nan kan layin.
Bayan an idar da Sallah saida ya tsaya suka gaggaisa da mutane don haka sai wajen
karfe biyar saura ya shiga gidan. Yana shiga ya kirawo maigadi yana tambayarsa
wanda ya taba injin ruwa, yace
‘Wallahi ban sani ba Alhaji, ai kaga ba ni nake kunnawa ba Sadiku ne kawai yake
taba wajen nan sai ko kannensa da wani lokacin suke kunnawa.’
Ya sallameshi ya karasa cikin gidan, babu kowa a falon domin yaran sun tafi
islamiyya. Sadik ne kawai a dakinsa domin tunda ya shiga SS 3 ya daina zuwa
islamiyya; sai yace wai karatu yake, ita kuma Mommy sai tace a barshi tunda Shirin
jarrabawa yake.
Yana shiga tsakiyar falon ya kwalawa Sadik kira, tana zaune a falon sama da Sumayya
a hannunta tana jiyo kiran da yakewa Sadiku ta san wani laifin yayi, ta ja tsaki ta
fada a fili
‘Daga dawowa mutum ya ishi mutane da fada akan mace sai kace wata ‘yar gwal.’
‘Gani Abba.’
‘Wanene ya yanke min waya a injin zuko ruwa?’
Bai yi zaton tambayar ba don haka ya dan diririce, idanuwan Abban suna kansa don
haka ya sunkuyar da kai yana wani cin magani cikin in ina yace
‘Ba ni bane.’
‘To wane shegen ne idan ba kai bane? Waye yake kunna injin kuma waye ya iya kwance
kayan wuta a gidan.’
‘Abba ni dai ba ni bane, sai dai idan ko bera ne don gaskiya ba ni bane.’
Bai yi aune ba sai saukar mari yaji a fuskarsa, ya dafe kumatun yana fitar da
kwalla. Abban ya nuna shi yace
‘Kaine ka sa reza ka yanke wayar saboda kada ruwa ya dinga shiga tankin gidan
Aisha, to Ina tabbatar maka ba zan dauka ba. Gidana ne don haka yanda nake so dole
haka za ayi, da kai da duk wanda yake saka ku sani ba zan dauka ba.’
Har ya gotta Sadik din zai wuce ya dawo ya tsaya a gabansa yace
‘Na sa plumber ya gyara wayar sai ka sake zagayawa ka yanketa tunda kaine ka ajiye
ni.’
Ya haye saman ya barshi a nan tsaye yana fitar da kwalla saboda takaici; ya manta
rabon da Abba ya daukeshi. Tun yana JS 1 da sukayi fada a makaranta Abban ya
zaneshi, sai yanzu zai mareshi saboda wannan banzar matar tasa. Dama Mommy saida ta
fada zuwa zatayi ta rabasu da Abba; ai dole ma ya koyawa matar nan hankali. Yayi
kwafa ya shige daki ya mako kofa.
………
Duk abinda ya faru tsakaninsa da Sadiku tana jiyowa, don haka yana shiga falon tace
Kafin ta amsa ya shige dakin ya mako kofar, don haka ta tashi ta wuce dakinta ta
kwantar da Sumayya wadda ta riga tayi bacci.
Ta fuskanci da fada ya shigo don haka itama ranta a bace ta shiga dakin, yana tsaye
a gaban mudubi ya rungume hannayensa ita kuma ta wuce gefen gado ta zauna.
‘Gani.’
Ya zuba mata ido har saida ta gaji da kallon da yake mata ta kawar da kai.
Yace
‘Zahra.’
‘Ranar da na tafi Sadik yaje ya yanke waya wadda take kai ruwa tankin gidan Aisha,
na barku a kan Malam Sule ya cigaba da kaita aiki tare da ‘yan makaranta amma tunda
na tafi kika hana kika ce yara suna makara kuma basa makara. Na bar Rukayya ta
tayata kwana amma ina tafiya kika turo aka kirawota kika barta ita kadai. Na ce a
kai mata danyen naman sallah kika hana a bata, kuma waccan sallar ma haka kika sam
mata naman shine wannan kika hanata gaba daya. Me yasa? Wanne irin wulakanci ne
wannan Zahra? Kika barta tana yawo a motar haya kuma tana sayen ruwa, saboda me?’
Maganganun nashi duka sun shammaceta don haka tayi tsamo-tsamo a wajen, ta muskuta
kadan ta gyara zama. Ta gagara bashi amsa sai wani muzurai kawai da takeyi, yace
‘Ni da gidana ban isa na fadi yanda nake so ayi ba kenan saboda kin ga ina kyaleki
ko Zahra? Ba kya ma tsoron koyawa yara rashin kunya kiri-kiri kike aikata abubuwan
da basu dace ba a gabansu saboda tsabar wulakanci da raini…'
A fusace ta katseshi
‘Kada fa ka zageni! Ai nima sai ka tambayeni kaji ta bakina amma daga dawowa ta
gaya maka karya da gaskiya ka zo kana ta fada.’
‘To shikenan kinyi yanda kike so nima zanyi yanda nake so, yara kuma ki cigaba da
koya musu rashin mutunci. Amma ki sani, kin bani mamaki don a ya da nake dake na
zata ko kare na ajiye nace ki tayani kula da shi zaki yi, balle na ajiye matar aure
wadda ban ce ki kula da ita ba kawai hakkinta nace a bata amma kika haye Kai saboda
hadama. Fice min daga daki.’
Ta kalleshi da mamaki kwakwalwarta tana nanata mata “fice min daga daki”, yau ita
Yusuf yacewa ta fice masa daga daki saboda wata amarya.
Ta tashi cikin sanyin jiki tana kallonsa tana mamaki, sai yanzu ne ma taga tsananin
fushin da yake ciki. Dole ta dauki matakin a kan duk wanda yake da hannu a cikin
kulla mata wannan munafurcin.
Tana fita hawayen da take makalewa ya kwace, haka ta barshi yana zuba har ta karasa
dakinta ta shige ta turo kofar. Ta zauna a gefen gado kamar wadda aka tunkuda, ta
rufe fuskarta da tafukan hannunta tana fitar da hawaye masu zafi harda shesshekar.
Wai yau ita Yusuf yake kora daga dakinsa saboda tsabar wulakanci Kuma harda ce mata
hadamammiya duk don yana da wata matar. Dole ta dauki matakin a kan Yusuf da wannan
matar tasa don ba a isa a zo daga baya ba a rabata da mijinta.
Haka ta karasa wunin cikin kunci, ko da yara suka dawo daga islamiyya haka tace
musu bata da lafiya don haka sukayi jugum-jugum.
Ta dafa abincin dare amma ko kallon table din bai yi ba har lokacin kwanciyar
bacci.
Bata yi niyyar zuwa dakinsa ba don haka a dakinta ta kwanta, sai dai duk sata irin
ta bacci kasa daukarta yayi. Juyi kawai take a kan gadon, zuciyarta sai kuna takeyi
saboda takaici. Ga kayan matan da ta sha duk sun hadu sun birkita ta; tun saura
sati daya ya dawo aka yi mata kaza ta cinye ga tsumi galan guda wanda shima tsaf ta
shanye duk don shirin dawowarsa amma ga da abinda ya dawo mata da shi.
Haka ta kwana tana juyi tana tunanin mafita don dole ta dauki mataki.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
19
Ko da gari ya waye haka Zahra ta tashi da idanuwanta a kumbure saboda rashin bacci,
gashi ranar litinin ce don haka dole ta shirya yara zuwa makaranta. Haka ta goya
Sumayya ta shiga hidima, da taimakon Yusra nan da nan suka gama.
Karfe bakwai da rabi Malam Sule ya juya mota yana jiransu a tsakar gidan.
Daidai lokacin Abba ya sauko bayan sun gaggaisa da yaran da kuma Malam Sule ya
kunna tashi motar ya fice daga gidan. Yana fita daga gate din yaci karo da Rukayya
ta fito a shirye, bayan ya amsa gaisuwar ta yace
Tace
Yayi mata sallama ya wuce yayi parking a bakin gate din gidan Aisha, ya fito ya
shiga ciki.
Amira ce a falo bayan ta gaisheshi ya shige daki inda ya sami Aisha a tsaye ta saka
hijabinta ta dauko jakarta. Bayan sun gaisa yace
Da mamaki tace
‘Kai da kanka?’
Suka fito tare har bakin gate, ita da Amira suna cikin shiga motar Malam Sule ya zo
wucesu da yara.
Saida Abba ya kai Amira makaranta ya dawo ya ajiye Aisha ya sanar da ita zai zo ya
dauketa sai su dauko Amira in ya so sai ya kaita ta mayar da Amiran gidansu kamar
yanda ta sanar masa.
Duk da ta ajiye abincin safe amma bai ko kalli tebur din ba ya shirya ya fice ba
tare da ya bi ta kanta ba.
Tunda take da shi bai taba fushi da ita har ya ki cin abincinta ba sai yau. Tsayawa
kawai tayi tana kallon abincin a dinig table bayan ya fice; lallai an juya mata kan
miji kuma dole ta dau mataki. Dole ta san yanda zata yi ta janyo hankalin mijinta
ya dawo kanta kafin a saka shi ya koreta.
Abban bai dade da fita ba Jummai ta shigo gidan, don haka ta mikawa Jummai Sumayya
tace mata ciwon kai yana damunta. Ta koma dakinta ta rufo kofa, ta zauna a gefen
gado ta kafa tagumi.
Jimawa kadan ta tashi ta dauki wayarta ta fara lalube a ciki, har ta zo kan Yaya
Murja sai kuma ta fasa dannan kiran. Idan dai Yaya Murja ce ta san hakuri kawai
zata bata tace tayi addu’a , kuma ai kullum tana addu’a itama. Idan kuma ta kirawo
Suwaiba itama hakurin zata bata don ita wannan bata ma san menene rayuwar ba.
Haka ta koma ta lalubo lambar Amina, kara daya wayar tayi aka dauka. Bayan sun gama
gaisawa tace
‘Kawata ina son ganinki yanzun nan, gashi kuma ni bazan iya fitowa ba balle na zo.’
Tace
‘To nima dai gani a office amma bari mu gani watakila zan iya fitowa nan da minti
ashirin haka sai na karaso gidan. Allah yasa dai lafiya.’
An dauki kamar awa daya domin har ta gaji da jiran Hajiya Amina kafin taji tsayuwar
motarta a bakin gate. Cikin kankanin lokaci kuwa Jummai ta buga mata kofa ta sanar
da ita isowar Aminan, nan take ta bada umarnin Aminan ta shigo ta sameta a dakin.
Tana shiga ta tura kofar ta karasa ta zauna a kusa da ita tana fadin
‘Yaya dai Uwar Sadiku? Ya zan ganki cikin duwa bayan kuma jiya maigida ya dawo? Me
yake faruwa ne?’
Ta share kwallar da take kwarmin idonta tana ajiyar zuciya yayinda Aminan ta bita
da kallon mamaki
‘Ni za ayiwa bura uba Aminoni? Tunda ya sauka a garin nan yake min wulakanci saboda
wata banzar matarsa; wai ni Abban Sadik ya kalla yacewa hadamammiya yana wani
korata daga dakinsa kamar kare.’
‘Allah kawata? Yanzu wannan matar tasa mai kama da abun tausayi ta kai ta kulla
wata tsiya haka?’
Nan ta karantowa Amina abubuwan da suka faru da yanda take jin janye hankalinsa
akayi daga kanta aka saka shi ya zo yana yi mata wulakanci.
Aminan tace
‘Ikon Allah, lallai kishiya bata kadan. Shi yasa wallahi ba zan taba bari Habibi ya
kara aure ba sai inda karfi na ya kare. Ka rayu da mutum tun bashi da komai amma
yanzu yana jin yana da bakin kiranki hadamammaiya, kai maza basu da mutunci!’
‘Ni yanzu kin san me nake so? Duk inda kudi suke dole na nemosu don kin san munyi
da Malam Hatimu zai raba min su gaba daya.’
‘Hakane. To yanzu ina zaki sami kudin bayan tuntuni kike cewa baki da su, kuma
kinga dai nima bani da su.’
Tashi kawai tayi ta matsa gaban wardrobe dinta ta bude, ta dauki lokaci tana lalube
sannan ta mayar ta rufe. Ta dawo kusa da Aminan ta zauna tana dauke da wani dan
akwati mai dauke da sarkoki.
‘Zan cire wasu daga cikin sarkokin nan ki kai ki sayar min, kafin a gama ciniki na
dan sami kaina sai mu sa rana muje wajen Malam. Gara ayita ya kare kawai na gaji
wallahi.’
‘Yanzu kikayi magana Hajiyata, amma ki zauna yarinya kamar wannan tana ta faman
kasa miki hankalin miji ai ba daraja.’
Ta bude akwatin sarkokin ta dauko zobenta guda daya na gwal babba ta mikawa Amina.
Ta dauko wani karamin saiti na sarka da dan kunne mai karamin kwado ta kara mika
mata tana fadin
‘Wannan ma na Yusra ne amma a hada dashi a sayar don na san wannan zoben ba zai kai
dubu dari ba ma, nawa saitin kuma yayi girma da yawa. A sayar da wadannan abinda ya
kama sai na cika tunda ina da wasu ‘yan kudaden.’
‘Yanzu kikayi magana Uwar Saddiku, in sha Allah gobe da safe zan kaisu kasuwa. Zaki
ji duk wani bayani.’
‘Shike nan, zuwa nan da kwanaki biyu zanyi kokari mu shirya don na samu muje Gaya
tare, nafi so naje gani ga Malam na karanta masa abinda nake so.’
Nan suka karasa hirarrakinsu da shirin yanda za su je Gaya wajen Malam Hatimu.
Kafin azahar Aminan tayi mata sallama ta tafi.
……..
Wajen karfe biyu da Rabi Malam Sule ya dawo da Yusra, Rukayya da Nana daga
makaranta; ita Ummi da yake a nursery take tun sha biyu aka dawo da ita.
Suna shiga gidan suka sami Jummai a kicin, Yusra ta dubeta tace
‘Tana sama, inaga dai bata jin dadi yau din nan.’
Kafin ta gama jin amsar da Jummai ta bata ta haye saman da gudu, tana shiga dakin
ta zauna a gefen gadon kusa da kafar Mommy
‘Um.’
Cikin kosawa ta zaro ido tana duban Mommy tace
Tace
‘Mommy Abba ne fa ya kai matarshi makaranta da ita da ‘yarta, kuma yanzu ma motarsa
tana kofar gidan nata na san dauko su yayi ya tsaya yin wani abun a gidan.’
‘Yusra duk abinda Abbanku yayi ba zan yi mamaki ba, an riga an juyar masa da tunani
sai addu’a kawai. Inaga saboda na hana Malam Sule kaita makaranta da baya nan shine
yanzu yaje ya kaita don ya bani haushi.’
Wato saboda ta hana Malam Sule ya kaita aiki shine shi ya dawo ya fara kaita, kwana
biyun nan nata ne amma gaba daya a wajen Aisha yake karewa; don ta tabbatar wannan
shigar da yayi gidan sai ya kaiwa Aishan kwananta. Lallai yanzu ta sake tabbatarwa
da cewa Aisha bata barsa haka ba, don haka itama dole ta tashi tsaye. Kokari zata
yi taga sun shirya domin bata jure fushinsa musamman da yake yana da inda zaije a
debe masa kewa. Idan suka shirya sai ta fi samun natsuwar aiwatar da abubuwan da
take shirin yi.
-------
Kamar kullum yauma Jummai ta gama duk wani aiki na cikin gida, ta fito tana share
tsakar gida.
Can daga gefe daya akwai boys quarters mai daki biya; daki daya maigadin gidan ne
Malam Sajo yake amfani da shi, daya dakin kuma kwanan nan da Sadik ya shiga SS 3 ne
ya gyara saboda idan abokansa sun zo nan suke zama karatu kamar yanda yake fada.
Jummai bata share cikin dakunan, amma idan tana share tsakar gidan takan zagaya har
farfajiyar boys quarters din ta share.
‘Yan kwanakin nan kullum ta zagaya sharar haka take ganin murafun kwalba kamar
kwalbar magani a watse a farfajiyar wajen. Bata san na menene ba amma dai ta san
Sadik lafiyarsa kalau kuma Malam Sajo ma bai ce bashi da lafiya ba; kuma koda mutum
bashi da lafiya ma ai akalla ayi kwana biyar kafin a shanye kwalba guda ta magani.
Amma yanzu kusan kullum sai ta share murafun nan guda uku zuwa biyar.
Haka ta tattara sharar zata kwashe sai kuma ta sa hannu ta tsince murafun kwalabar
guda hudu ta rike a hannunta sannan ta kwashe sauran sharar. Ta dauki kayan
shararta ta juye a kwandon sharar tsakar gidan wanda yake kusa da gate.
Bayan ta juye ta nufo wajen Malam Sajo wanda yake zaune a gefen fulawoyi yana
hutawa.
‘Ni kaina Jummalo? Nan da kika ganni lafiyata ras ai ko ciwon kai na manta rabon da
nayi balle ace bani da lafiya. Wani ne yace miki bani da lafiya?’
‘A’a’
‘Gani nayi ‘yan kwanakin nan kusan kullum sai na share murafun nan na kwalabar
magani a wajen dakin naka, to idan ana da lafiya ai ba za a sha magani ba.’
‘A to gaskiya dai wannan ba nawa bane, nima dai kwana biyun ina ganinsu. Amma sai
dai ko ki tambayi Sadiku da abokansa tunda sune ke zama a daya dakin. Ni kam ai ko
bani da lafiya bana shan maganin asibiti Malama Jummai shi ya sa kika ganni gatagau
nan.’
Tayi ‘yar dariya saboda yanda yake magana yana jijjiga jiki
Ya kama haba yana sake duban murafun da har yanzu suna hannunta yana fadin
‘To amma fa gaskiya ki bincika, ko kuma kiyiwa Hajiya magana ta bincika don gaskiya
matasan yanzu abun tsoro ne tunda har magungunan ma sha sukeyi masu bugarwa da wani
sirab suke kiranshi ko sirap ni ban rike ba. A dai binciki Sadiku da abokansa.’
Har yamma abun yana ranta, tana so ta yiwa Mommy maganar amma tana tsoro don ta san
yanda Mommy bata son laifin Sadiku, sannan kuma ko ta fada idan yazo yace ba haka
bane babu abinda Mommy din zata yi a kai.
Sai can bayan la’asar lokacin yara sun tafi Islamiyya shi kuma Sadiku bai dawo daga
makaranta ba sannan Mommy ta sauko daga sama. Har yanzu tana da sauran damuwa sai
dai abun da sauki tunda zuwa yau Talata ta samu Abban yana cin abincinta; damuwarta
daya yau zai koma kwanan Aisha. Duk da haka tunda akwai tanadin da takeyi wannan ba
damuwa bace.
A falo ta sami Jummai a zaune a bayan kujera tana hutawa saboda babu wani aiki da
zata yi.
‘Jummai ai sai ki fito daga bayan kujerar kiyi kallo kafin aminiyarki ta tashi daga
bacci ta isheki da gwaranci.’
Tana kaunar Zahra saboda yanda take kyautata mata, matsalarta duk da ta yaranta
idan ta rasa yanda zata yi haka Uwar Sadiku take wuce mata gaba ayi komai. Ba zata
so taga abinda zai cutar da ita ba ko yaranta su sami matsala; duk da tana son
aikinta bata son abinda zai rabata da aikin.
Jimawa kadan ta fito da murafun maganin nan a hannunta ta tsuguna a gaban Mommy ta
mika mata tana fadin
‘Hajiya kinga murafun maganin nan, a nan boys quarters na tsinto su, ‘yan kwanakin
nan kuma kullum sai na gansu a shara. Na tambayi Malam Sajo yace ba nashi bane,
amma fa kullum sai na gansu na share don yanzu nan haka gobe ma idan nazo shara sai
na share wasu.’
Ta sunkuyar da kai
‘To Hajiya sai dai ki binciki Sadiku tunda kinga yanzu yana shigo da abokai wajen,
kuma kin san samarin zamanin nan basa raina abun maye tunda kinga har maganin ma
sha sukeyi. Sai ka gama tarbiyyar naka yaron a sami bata gari su bata maka aiki.’
‘Eh, da wannan. Amma dai Sadiku ya san me yake ba zai sha wannan ba sai dai ko
abokan nasa. Bari ya zo muji idan sune ma ai dole ya rabu da su kowa ya koma gidan
ubansa ya dinga karatun a can.’
‘E gara kam a bincika Hajiya, yaran yanzu sai ana sa musu ido.’
Suna nan zaune Sadikun ya shigo daga makaranta, Mommy ta tsayar da shi ta nuna masa
murafun tana tambayarsa a kansu. A take yace shi bai taba gani ba gaskiya sai dai
idan yaran makota ne suke watsowa ta katanga.
Ta gamsu da bayaninsa don haka ta juya ta bawa Jummai murafun tana fadin
‘Kin ji ko? Ai dama na san ba shi bane don abokan nasa ma duk na san su. Zai iya
yiwuwa yara ne da suke wasa da shi kin san suna yin mota da shi. Kuma idan barnar
su Sayyad ta tashi zasu iya watsowa nan din. Kawai ki dinga sharewa idan kin gani.’
Ta kwashe ta nufi kicin tana zullumi a ranta; domin tabbas bata jin yaran makota
zasu jefo wannan murafun tunda ta san yara kanana ne. Ta dai fi zargin Sadikun da
abokansa amma dama ta san a wajen Hajiya duk abinda Sadiku ya fada shine gaskiya.
Don haka ta zubar da murafun ta bar maganar tana fatan Allah ya sa abinda Sadikun
ya fada gaskiya ne.
__
Kafin ya koma kwanan Aisha saida Zahra ta tabbatar ya sauko daga fushin da yake da
ita; da taga kamar ba zai daina shareta ba ma dakanta ta same shi a daki ta bashi
hakuri. Harda kukanta duk da dai a cikin ban hakurin ta gaya masa babu abinda tayi
da niyya komai ta bayarda dalili. Ya riga ya santa da wannan halin ba zata taba
daukar laifinta ba, shi kuma baya son kukanta don haka ya hakura da sharadin ba
zata sake yi masa irin haka ba. Dare nayi ya wuce wajen Aisha.
__
Yana fita wajen Aisha a daren ta kirawo Amina don taji yanda akayi da gwal din da
ta bayar a siyar. Tayi mata bayani an sayar sai dai gaba daya basu kai dubu dari
biyu ba; bata ji dadin hakan ba saboda tana bukatar akalla dubu dari hudu ta tafi
da su domin so take ayi mata aiki mai kyau musamman da yake zuwa yanzu duk wani
ragowar hakuri da zata iya yi ya kare.
Tace
‘To ki ajiye min kudin na san zuwa karshe wata na danyi ciniki wasu sun biya bashi
ba zan rasa dubu dari ba, in ya so dubu dari ko rantowa sai nayi.’
‘Hmmm! Kawata barshi kawai ai yanzu baya hayyacinsa, zan nemo dai in ya so sai ya
biya idan ya shiga hannuna don wannan aiyukan da kayan gyaran da na sha kafin ya
dawo duk wallahi sai ya biya.’
Haka ta kwana tana tunanin inda zata sami rancen dubu dari.
Suwaiba zata fara tambaya tunda ta san tana aiki kuma ko bata da shi ta san zata
ranto mata a wani wajen.
Kawai dai dole ta jira sai karshen wata ta dan hada ciniki, gashi yanzu watan ya
kama. Amma bata da wani zabi haka zatayi ta zaman hakuri har karshen wata.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
20
Baifi sati daya da dawowa ba ta gama hada kudin motar da take son siya, don haka
ranar da ya kaita ta mayar da Amira gida sai da ta sakashi ya biya da ita gidan
Yaya Abubakar. Baya nan don haka ta barwa Anti Fauziya sako kan zata tura masa
kudin ta account dinsa.
Duk wannan shirin da take yi bata bari Abban ya sani ba, bata son ta gaya masa don
idan ta gaya masa akwai yiwuwar Zahra taji labari wanda ta san sai ta san yanda
tayi ta sa ya hana sayen motar.
Sati biyu da gama maganarsu da Yaya Abubakar ya kirawota ya sanar da ita gobe zai
kawo mata motar.
Yana zaune a falonta bayan sallar magriba da faranti gireba a gabansa yana ci suna
hira tace
‘Yallabai gobe fa Yaya Abubakar zai kawo min motata, ka san tun kwanaki nace maka
zan sayi mota.’
‘Haba dai, to yanzu ba shikenan ba na hutar da kai in ya so sai ka sayawa Mommy din
kawai tunda ni na riga na saya. Ka san fa tun kafin a fara maganar bikinmu kudin
motar suke a hannunsa shi yasa yanzu yana yi min maganar kawai nace ya siyo.’
‘To Allah ya sa albarka, Allah ya tsare hanya. Ko nima na sami ta zaga gari ko kuma
idan na fara neman aure na sami ta tsara bazawarata.'
Ta harareshi, ya kauda kai yana kallon gafe. Ta sa kafa ta dungureshi tana zumbura
baki tace
‘Bazawara ko?’
Shima yaji dadin sayen motar amma dai ya so ace ta bari shi ya saya, sai dai hakan
ma yayi masa dadi tunda a halin yanzu dama baya son sayawa Zahra mota domin ya kula
gaba daya ta canza hali.
Haka suka karasa hirarrakinsu yayi mata sallama ya tafi ya barsu ita da Rukayya.
Ranar babu aiki saboda gwamnati ta bayar da hutu. Yana zaune a falon sama ya gama
cin abinci tana zaune suna dan taba hira. Wayarsa ce da take ajiye a gefensa ta
dauki waka, saida ta dan yi dogon wuya ta leko screen din kafin ya dauke wayar.
Sunan A’eesh ne ya fito a kan screen din wanda ta san Aisha ce, don haka ta kara
nutsuwa ta tada kunnuwanta ko zata tsinci wani abun.
‘Eh, an kawo.'
Ta dubeshi tace
Da fara’arsa yace
‘Aisha ce ta sayi mota shine aka kawo mata, ai kinga dole na bayarda tukwici.’
Tana nan zaune ya fito daga dakin a shirye yayi mata sallama ya fice.
Tabi bayansa da harara har tana kwafa; wato mota ma ya sayawa Aisha kenan? Bayan ta
bashi hakuri kuma tana kallo yana zuwa yana kaita aiki yana daukota shine zai saya
mata mota ita kuma ta barta da Malam Sule? Tabbas yau za ayi bala’i don bazata
yarda ba. Ai tun kafin ya auri Aisha take lallabarsa ya saya mata mota amma kullum
yana shirya mata zance don haka wallahi dole ma ya zo yaji bayaninta.
………..
A tsakar gidan ya samesu a tsaye da Yaya Abubakar din da kuma Yaya Zainab suna ta
duba motar; baka ce kirar Honda Accord ta zamani sai sheki takeyi. Kudin da Aishan
ta tura masa naira miliyan dayane da dubu dari ta san bazasu sayi wannan motar ba
don haka tana tsaye ta rike hannun Yaya Abubakar din sai faman tsalle take ta kasa
tsayuwa guri daya saboda tsabar murna. Ko shi ma Abban da yaga motar yayi mamaki
don bai yi zaton Aisha tana da kudin da zata iya sayen wannan motar ba.
Ya karasa suka gaisa sannan ya ja hannun Abubakar suka koma falo, ta kawo musu lemo
da cake sannan ta ja Zainab suka dawo wajen motar. Zainab ta dubeta tace
‘Allah ya sa dai baki manta tuki ba, don fa tun rasuwar Abban su Abdallah rabonki
da tuki.’
‘Ban manta ba, kuma shima yace zamu dan fita tare na kwana biyu ya tuna min kafin
na fara fita ni kadai.’
Suka dan taba hira sannan sukayi sallama, Abban Sadik ya kawo naira dubu ashirin
sababbi kar ya bawa Zainab yace tayi tukwici.
Nan suka bar Aisha ita da Abba tana ta murna ta kasa barin wajen motar.
Saida aka fara kiran Magriba sannan ya fita masallaci daga can ya koma gidan Zahra
tunda dama kwananta ne.
Tunda ya shiga gidan ya kula da yanayinta ya san a kan taji ya ambaci mota ne, don
haka shima ya shirya mata. Ta riga ta fara bayyana masa halayenta don haka yanzu
kwata-kwata ba zai sake saurara mata ba.
Ta so ta danne ta bari sai yaje sunyi sallama da Aisha idan ya dawo sai ta tada
maganar amma ta kasa hakuri.
A zaune suke a falon sama suna cin abincin dare, tuwon ne miyar kubewa danya tayi.
Gaba daya hankalinsa yana kan abincin yayinda ita kuma take yafutar abincin tana
satar kallonsa. Ta dai kasa daurewa tace
‘Wai ni dazu mota ka siya ne naji kana zaka bada tukwici, ban fahimci zancen ba.’
Ya hadiye lomar da take bakinsa ya mayar da cokalin cikin kwanon sannan ya dubeta
yace
‘Bakiji me nace miki ba dazun, Aisha ce ta sayi mota shine Yayyanta suka kawo mata.
To kinga ai dole na bada tukwici tunda an kawo mana abun arziki.’
‘Ban gane Aisha ta sayi mota ba, ko dai ka saya mata mota?’
‘Ni ban saya mata mota ba, idan da na saya mata ai tare zan saya muku. Ita da
kudinta ta sayi mota sai dai ko idan Yayan nata yayi mata ciko don shima yana da
dukiya sosai.’
Ta kalleshi yana ta faman zura lomar tuwonsa ba tare da wata damuwa, ta kare masa
harara sannan tace
‘Kana nufin kace min albashin malamin makarantar ne ya sayi mota? Koko dai kana
nufin kace min kun hada baki ka saya mata mota don kayi min wulakanci.’
Sai da ya kalleta suka hada ido sannan ya kai lomar tuwonsa, ya ture kwanon ya sha
ruwa sannan ya sake dubanta yace
‘Ni ban saya mata mota ba domin idan na saya mata mota zan gaya miki don baki isa
nayi miki karya ba, Aisha ta siya mota. Idan baki manta ba lokacin da kike ikirarin
ta aureni saboda kudina na gaya miki ba haka bane don itama nan da kike gani mai
kudin kantace, abun duniya ne bai dameta ba shiyasa kika ga tana rayuwarta haka.’
‘Yanda na saba yi dake mana! Naga ga Malam Sule nan wanda dama kin hanashi yayi
aikinta, kinga yanzu hankalinki kwance iya ke kadai da ‘yayanki Malam Sule zai
dinga yiwa hidima. Ita idan na bata kudin mai sai ta kai kanta inda zata je.’
Ta share kwalla
‘Amma Abban Sadik tun yaushe nake maka magiyar ka saya min mota shine yanzu zaka
zaga ka sayawa amaryarka kuma kazo kana ninkeni bai-bai ko!’
‘Zahra! Bani na sayawa Aisha mota ba, ita ta saya. Ke kuma ba zan saya miki mota ba
saboda na gaya miki bani da ra’ayin matata ta ja mota na fi so na sa driver ya
kaiku duk inda zakuje. Itama din da kin bari Malam Sule yana kaita inda zata da ba
zan bari ta sayi mota ba to amma kin hanashi yayi mata aiki. Ba zan iya daukar mata
wani driver din ba kuma ba zan iya barinta tana yawo a motar haya ba kamar yanda
bana barinki don haka kinga dole na barta ta sayi mota da kanta ko zan samu na huta
da kaita unguwa da daukota. Wannan din tsarinki ne ai tunda da alama haka kika fi
so, amma ni babu wata mota da zan siya.’
Ta dauki lokaci tana zaune a wajen tana mamakin maganganusa, ita tunda take da shi
ma bata taba tunani ya iya maganganu na tura haushi kamar haka ba.
Haka ta kwana ita kadai a dakinta tana tunanin yanda zata bullowa lamarin nan; don
tana son mota kuma ba zata taba bari ace kishiyarta tana da mota ita kuma bata da
ita ba.
------
Tunda aka ce Aisha ta sayi motar nan Zahra ta kasa samun natsuwa, gashi bata son
taja doguwar rigima da Abba tunda bata so ya bata mata shiri. Gaba daya ma yanzu
zargi takeyi Abban yana kaiwa Aishan abubuwan da baya kawo mata, don haka a hankali
ta samu take tura Yusra da Nana gidan don su gano mata abinda akeyi a gidan.
Aisha bata son suna shiga, musamman Yusra to amma babu yanda zatayi da su saboda
gidan ubansu ne. Sai dai kawai idan suka shiga gidan sai ta sa mukulli ta kulle
kicin dinta, dama basa shigar mata dakuna don haka suna falo itama sai ta zauna a
dining table tana kula da motsin kowa. Basu cika dadewa ba saboda suma suna kula da
yanda Aishan take kaffa kaffa da su.
………..
Ranar Juma’a ce don haka kamar yanda ta saba tana tashi daga aiki ta wuce ta dauki
su Abdallah a makaranta suka je gidan Umma ta hado musu kayansu don gidanta zasuyi
weekend.
Duk lokacin da sukayi irin wannan zuwan ta saba sai tayi musu cake ko wani snack,
suci su koshi sannan su tafi da shi gidan Umma.
‘Mama yau ki soya mana kaza da yawa, Umma bata soyawa kullum a miya take sawa ba
dadi.’
‘Mama wallahi karyane, idan an dafa ma da dadi. Kullum fa idan Anti Uwani ta soya
na sawa a miya sai ta bamu dai dai.’
Tace
‘To idan kun yarda na soya muku kaza amma fa ba zan yi muku cake ba, kun yarda?’
Tana da kaza a gida amma wannan Abban Sadik ne ya siyo kuma miya takeyi da su tana
yi musu peppersoup, don haka a hanya suka tsaya ta siyo kaji gidan gona manya guda
hudu sannan suka wuce gidan.
Saida ta gama abinda takeyi wajen bayan la’asar sannan ta shiga kicin din, nan da
nan ta gyare kajin nan ta sulalasu sannan ta zauna ta fara suya.
Kafin ta kwashe suyar farko Yusra da Nana suka shigo tare da Rukayya. Bayan sun
gaisheta duka suka zauna a falo suna kallon TV.
Wajen Rukayya Abdallah da Farha suka samu suka zauna sunata yi mata surutu domin
sun saba da ita, ita kuwa Yusar saboda yanda take kyararsu basa ko zuwa kusa da
ita. Tana yawan kiransu Agola, ko kuma tace da su sun zo cin arziki kullum sai dai
Aishan tayi ta yi musu bayani tana basu hakuri.
Tana kwashe suyar farko ta zubo a tray ta kawo falon kowa a cikin yaran ya dauki
guda suka kama ci, Yusra ce kawai tace ta koshi don haka ta koma da yanka dayan
nata.
Nan da nan ta gama, tana cikin juyewa a tray don ya sha iska Abban Sadik ya shigo,
bayan yaran sun gaisheshi ya wuce kicin inda ya jiyo motsinta.
‘Hmm! Dabge ake mana ne nake jiyo kamshi tun daga kan kwana.’
‘Kaji ne nake soyawa yara, yau Farha tace basa son cake kaza suke so.’
Ya karasa ya sa hannu ya dauka, ta bude fridge ta zuba masa zobo a kofi ta mika
masa tana fadin
Ya karbi kofin a hannu daya daya hannun kuma yana dauke da naman da ya fara ci ya
fice daga kicin din ya shige dakinsa.
Ta dauki dan faranti ta zuba masa naman ta fito don ta kai masa. Farha ta taso da
gudu ta sha gabanta tana fadin
‘Mama ki kara min, ki bani gizzard.’
Tana shiga dakin ta wuce kan mudubi ta ajiye masa naman tana fadin
‘Ga kari.’
Ya mika hannu ya kara daukan yanka daya yana dariya yana fadin
‘So kike ki cika min ciki idan ban ci abincin Yayarki ba ta hanani sukuni ko?’
‘Kada ka damu duka zaka cinye cikin ai danyar fata ce bata fashewa.’
Sukayi dariya.
A daidai nan ta jiyo Farha ta tsandara ihu, da hanzari ta fito yayinda Abban ya
rufo mata baya domin ihun bai yi kama da na lafiya ba.
Tana isowa falon Yusra da Nana suna ficewa suka mako kofar.
Ta karasa da sauri tsakiyar falon inda Farha ke tsaye tana shesshekar kuka Abdallah
yana tsaye rungume da ita shima yana kwalla. Rukayya tana shafa kansu tana basu
hakuri.
Da gudu Farha ta karasa jikin Aisha tana kara kuka rike da kumatunta, ta dauketa
suka karasa kan kujera ta zauna ta dorata a cinya yayinda Abba ya tsaya a bayan
kujerar.
Aisha tace
‘Yusra ce ta mareta.’
‘Mari?’
Sai a lokacin ta dagata ta duba kumatunta. Yayi jazur musamman da yake Farhan fara
ce sosai, ga alamar yatsu nan a fuskar har kan kunnenta.
Ta sake rungumeta saboda yanda take kuka har jikinta yana rawa.
‘Ban kula ba ina jin dai bayan ta dauko naman ta zo wucewa ta takata shine ta
mareta.’
Abdallah yace
‘Nima ta tureni saida na fadi na buge kaina, kuma tace mana shegu agololo ‘yan cin
arziki.’
Ya karasa jikin Aishan yana fadin
Abban Sadik ya zagayo ya zauna ya ja Abdallah yana shafa kansa tana fadin
‘Nan ma ai gidankune Abdallah kaji, bari naje naji yanzu zan gamu da Yusran.’
Yana shiga ya samesu a falon kasa suna zaune da Mommy suna mayarda maganar.
‘Abba takani tayi, nayi mata magana tace min me siffar karuwai shi kuma Abdallah ya
kawo min duka wai zai tare mata.’
Mommy tace
‘Kai daga jin wannan maganar ka san fada akeyi a gabanta tana ji tunda karamar
yarinya kamar wannan ai bata kai ta san menene karuwa ba. Kuma idan banda cin fuska
da wulakanci tana auren uban Yusra amma ta dinga ce mata me siffar karuwai, kawai
saboda tana takamar ka daure mata ginda. Idan ita yaranta cikin gari suke rayuwa
wadannan ai a nan muke da su cikin GRA a ina zasu koyi zagi irin wannan?’
Nana tace
Ya zauna yana jinjina zancen; tabbas yaransa basu iya zagi ba kuma basu saba yi
masa karya ba, amma gidan su Aisha a cikin gari yake unguwar kofar Nassarawa; duk
da dai suna da rufin asirinsu amma ya san tabbas babu mamaki idan Farha ta iya
zagin.
Yana fitowa daga gidan aka fara kiran sallar magriba don haka kawai sai ya wuce
masallaci, sai da aka idar da Sallah sannan ya dawo ya shiga gidan Aishan.
Rukayya ce a falo ita kadai tana homework, bayan ya amsa sannu da zuwan da tayi
masa ya wuce dakin Aishan inda ya hango fitila.
Tana zaune a kan dadduma da hijabi, da alama Sallah ta idar. Farha tana kwance a
kan daddumar gefen Aishan yayinda Abdallah yake zaune a kusa da ita da alama tare
suka idar da Sallar.
Ya karasa ya zauna a gafen gado, kallon da take masa kallone me cike da tuhuma
domin tana so taji dalilin da yasa aka mari Farha.
Yayi gyaran murya yace
‘Yusra tace Farha ce ta zageta, kin san su basu saba zagi ba shi yasa zata ji
haushi har tayi over reacting. Kin san basu saba zagi ba mu a nan amma tace Farha
tace mata me siffar karuwai, kinga wannan ai ko wa aka gayawa zai ji haushi. Ki
dinga yi musu fada, itama Yusran nayi mata fada.’
‘Toh.’
Ta sunkuyar da kanta tana kallon daddumar da take kai, ya san ba zata sake yi masa
magana ba don haka ya tashi ya fice daga dakin ya shiga dakinsa.
Mikewa tayi ta fara hada musu kayansu; gara ta mayar dasu inda ake kaunarsu. Ya za
ayi ace Farha ta san karuwa kuma har yana wani fada yaransa basa zagi saboda nata
yaran ne ba a musu tarbiyya don haka su suka iya zagi. Ba tun yau ba tana kula da
yanda Yusra ta tsani Farha; shi kanshi Abban tana kula da yanda yake nuna kishinsa
idan su Abdallah suka zo. Idan yaga tana hidimarsu ya dinga nuna kamar shi ta share
shi kenan, gaba daya dai ta kula ya fi natsuwa idan basa nan.
Ta dai kau da kai ne ga abun saboda bata so aure ya rabata da yaranta; yanzun ma
kuma bazata bari aure ya shiga tsakaninta da su ba.
Jimawa kadan ta gama hada musu kayansu ta janyo karamin akwatin ta fito falo yaran
suna biye da ita. Ta ajiye akwatin a bakin kofa ta wuce kicin ta sami roba ta juyo
kazar da ta soya musu tazo ta ajiye a kusa da akwatin. Ta shige dakin Abban tana
rike da mukullin mota ta tsaya bayan ya amsa sallamarta tace
‘Daga dan wannan abun da ya faru, ki barsu su gama kwankinsu ranar Lahadi sa tafi.
Yusra nayi mata fada ba zata sake dukan kowa ba.’
‘Babu komai, sun fi so su tafi. Zan mayar dasu din ai yanzu zan dawo.’
Bai ga alamar zata fasa ba kuma baya son rigima da ita don haka yace
‘Allah ya tsare, sai kiyi sauri kafin dare yayi sosai. Bari na taso na fice sai ki
rufe gidan tunda ba nan zan kwana ba.’
‘Ki bi Abbanki Rukayya, idan na dawo zan masa waya sai ki dawo.’
Sai da ya rufe mata gate sannan ya kama hannun Rukayya suka nufi gida. Yana mamakin
irin wannan fushin na Aisha, ita idan akayi abu ko magana bata fiya son yi ba sai
dai kawai ta yi shiru tayi ta faman fushi. Yanzu ya san sai ya kai sati yana
lallabata kafin ta bari su dawo yanda suka saba.
Da sauri ta bude bakinta ta rufe da tafin hannunta tana zaro ido, ta ajiye hannun
tace
‘Tab, wallahi Abba babu wanda yayi zagi a falon nan. Tana taka ta ma tace sorry,
kafin ta gama magana ta mare ta, gaskiya bata zageta ba. Farha ma ai bana jin ta
iya zagi wallahi.’
Shiru kawai yayi saboda takaici; to ya akayi Yusra ta iya karya haka, gashi har
Mommy tana goya mata baya?
Zuciyarsa a jagule ya shiga gidan, suka rabu da Rukayya a falo ya haye sama.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
21
Babu kowa a falon saman don haka ya wuce ya zauna a kan kujerar zaman mutum uku ya
zuba tagumi. Wannan abun da ya faru yayi masa ciwo, yanzu Yusra har ta san ta
kirawo kanta mai siffar karuwa saboda tana so tayi wa Farha mugunta? To me ya
hadata da Farhan da har ta mare ta haka; don tabbas shi kansa yaga yanda yatsun
Yusra suka kwanta a kan fuskar Farhan. To Mommy ce ta tsara musu wannan karyar ko
sune suka tsara mata?
Ya tuno fuskar Aisha lokacin da yake ce mata ta dinga yi musu fada; tabbas bai
kyauta ba. Yanda Aisha tayi ya san taji zafin abun amma ya zata son zuciya ne kawai
saboda yanda take son yaranta.
Sai a lokacin ma yaga rashin kyautawarsa da bai je ya kaita gidan ba; take ya fara
nadamar barinta ta fita gashi baya son fitar dare.
Sallamar Mommy ce ta katse shi, bayan ya amsa sallamar ta wuce ta zauna a kusa da
shi. Bayan tayi masa sannu da zuwa tace
‘Eh, bari nayi sallar a daki don masallaci ma kafin na kai sun idar.’
Sai da yayi Sallah ya fito yaci abinci ya gama, ya dawo tsakiyar falon ya zauna
yana kallon labarai a Aljazeera. Mommy tana zaune a kusa da shi tana rike da
Sumayya ya dubeta yace
Ta tashi ta fice ta tsaya a kafar bene ta kwalawa Yusra kira,nan da nan ta hawo
saman. Abban ya dubeta yace
Nan suka zauna a gaban Abban, saida ya dan dauki lokaci sannan ya dubi Yusra yace
Cike da tabbas ta ce
‘Eh Abba.’
Yayi gajeriyar dariyar takaici da mamakin yanda Yusra ta kware da karya haka. Yace
‘Akwai CCTV camera a falon, da na duba ba haka na gani ba. Ta fito daga kicin ta
takaki kuma kamar ma tace miki sorry shine kika mareta kamar kina marin sa’arki shi
kuma Abdallah yana tasowa kafin ya karaso kusa dake ma kikayi fatali da shi kuma
kika zage su. Ko na gaya miki zagin da kika yi musu?’
Cikin sanyin jiki ta sunkuyar da kai yayinda Nana ta fara kokarin buya a bayanta
itama tana sunkuyar da kai.
‘Kika sa naje ina yiwa yara fada ashe kece makaryaciya kuma kece me yin zagin
sannan kika zo kika kirawo kanki mai siffar karuwa, ke kin san meye karuwa kuwa? Ki
rasa abinda zaki siffanta kanki da shi sai karuwa?’
Sukayi tsamo-tsamo babu wanda ya iya magana. Yayi shiru yana sauraronsu, Mommy tace
‘Au yanzu dama ba haka aka yi ba Yusra kuka zo kuka tsarawa mutane karya?’
Nana tace
‘Allah ya shiryeka, amma dai ki sani wannan abun da kika yi karya ce da annamimanci
kuma kin kai shekarun da komai kikayi Allah zai tambayeki a kai. Duk hakkin wanda
kika dauka kuma idan bai yafe ba sai kin biya.’
Ya mayarda dubansa ga Mommy; wadda itama jikinta yayi sanyi saboda bata taba zata
karyane abunda suka gaya mata ba, domin suna shigowa suka gaya mata haka itakuma
tacewa Yusran tayi dai-dai; yace
‘Kada ki sake yi min irin wannan, sai ki gaya min ainahin abinda ya faru in ya so
sai na san yanda za ayi. Ku tashi ku bani waje.’
Wajen karfe tara na dare saura kwata suka shiga gidan Umma. Waya tayiwa Umma don
haka tana danna horn Anti Uwani ta bude kofa, bata shigar da motar ba tayi parking
a nan bakin gate.
Ta dauki Farha wadda ta fara bacci shi kuma Abdallah yabi bayanta, suna shiga
farfajiyar gidan Anti Uwani ta karbi Farha tana fadin
Umma tana zaune a falo don haka suka zauna nan. Bayan sun gaggaisa da yake da wuta
Anti Uwani sai ta kunna musu cartoon, suka zauna har Farha wadda ta tashi daga
baccin suka fara kallo.
Aisha ta tashi ta shige dakin Hajiya, tana shiga ta zauna a gefen gado ta zuba
fuskarta a tafukan hannunta tana ajiyar zuciya. Jimawa kadan Anti Uwani ta shigo
dakin, takarasa ta zauna a kan kujerar gaban mudubi tana fadin
‘Ikon Allah, wai lafiya kike Aisha naga dazu kika tafi da yaran nan kuma Lahadi
kika ce zaku dawo wai me ya faru ne?’
Ta sauke hannuwanta ta bude baki zatayi magana sai hawaye, Anti Uwani ta mike ta
leka falo ta kirawo Umma. Suka saka Aisha a gaba suna tamabayarta tana share
hawaye, saida ta gama share hawayen sannan ta basu labarin abinda ya faru.
Umma tace
‘To ai wannan ba abun kuka bane, suma su Farhan ai da gatanasu ba gashi kin dawo da
su ba. Kuma kin san halin yaran yanzu tunda dama ke da kanki kince yarinyar nan
uwarta take tayawa kishi ai kuwa kinga zatayi abinda yafi haka ma.’
‘Nima abinda tayi bai bani haushi ba, abinda ubanta yayi ne ya fi bata min rai. Ai
dama ba tun yau ba na gaya miki baya son su Abdallah suje don idan suna nan yayi ta
muzurai kenan yana faman saka ni aiki. Da zarar na mike zanyi hidimarsu sai ya san
abinda yace nayi masa, har gara ma idan ba kwanana bane sai mu sake ni da su.
Yanzun kuma yana kallon shatin yatsun Yusra a kan fuskar Farha amma bai wani damu
ba, bayan yaje sun tsaro masa karya da gaskiya ya dawo yace min wai Farha ta cewa
Yusra mai siffar karuwa. Don Allah Umma yaushe Farha ta san karuwa, ai ko kalmar
siffa ma bana jin Farha ta san ma’anarta; shekarunta hudu fa kacal.’
‘Ai ce masa zasuyi ke kika gaya mata shi yasa zai hau kai ya zauna, idan dai son
kai ne ai kika sami namiji kin kure.’
‘Duk wannan ba wani abu bane, wannan ya wuce ai sai ki tashi ki koma dare yana yi.’
‘Shi da kansa yake yaba tarbiyyata amma yanzu da yake yaso son zuciya ce min yake
yaransa basu iya zagi ba nawa ne suka iya.’
Tayi kwafa.
‘Yi hakuri kin ji Shatu, sai dai su gani a kansu ba dai mu ba.’
Haka suka sakata a gaba sunata bata baki, zuwa tara da rabi ta taso ta fito ta kamo
hanya.
‘Uwani ki daina taya yarinyar nan rigima fa, kin santa da taurin kai ga fushi.’
‘Yaya wallahi dole na tayata, duk taurin kanta da ake gani amma tana da hakuri. Ba
karamin kureta akeyi ba kafin ta fara fushin da taurin kai, Allah ne kawai ya san
abubuwan da take hadiyewa a wannan gidan don haka duk abinda ta fada ai dole na
tayata Yaya.’
‘Ai shikenan.’
…………
Har karfe goma na dare yana zaune shi kadai a dakinsa, babu abinda yakeyi kawai
tunani kala-kala suke yawo a kwakwalwarsa. Tunda ya zauna yake kallon wayarsa yana
jiran Aisha ta kirawoshi tace masa ta dawo amma har yanzu shiru. Ya sake kallon
lokaci nan take ya lalubo lambarta ya danna mata kira. Wayar tana dab da tsinkewa
ta amsa, yace
Sukayi shiru na dan lokaci kadan, ya ma rasa me zai ce don ya san tabbas bai
kyautawa Aisha ba. Ya gaji da sauraron numfashinsu yace
‘Eh.’
Ya fahimci gajiyawa a cikin muryarta kuma shima bashi da sauran abinda zai ce mata
don haka yayi mata sai da safe, suka ajiye waya.
Yanda Aisha ta kwana tana fushi da shi haka ya kwana yana fushi da Zahra, duk yanda
ta kai ga shisshige masa ya ki ya saurareta har ta gaji ta kyaleshi.
Ko da gari ya waye tun wajen tara saura ya gama shiryawa don yana da daurin aure,
yana fatan kafin lokacin Aisha ta tashi; don bata tashi da wuri ranakun Asabar da
Lahadi; in ya so sai ya shiga wajenta kafin ya wuce.
Yana tsaye a gaban mudubi yana gyara karin hularsa Mommy ta shigo dakin, ta wuce ta
zauna a kan gado don ta kula har yanzu fushi yakeyi.
Ya gama gyara hular ya daura agogonsa ya dauki mukullan motarsa tare da wayarsa da
suke ajiye a kan mudubin ya dubeta yace
‘Kada ki ajiye min abincin rana a gidan Hajiya zan ci, sai da yamma zan dawo.’
Da murmushi a fuskarta tace
Ba zata iya hakura ba don tana ganin wannan itace damarta ta karshe idan bata yi
masa magana yanzu ba abun yana kara wucewa haka za ayi ta cutarsu ita da yaranta.
Don haka har ya juya ya nufi kofa ta tashi ta murmushi ta biyo shi, sai da ta zo
dab dashi ta kirawo sunansa
‘Abban Sadik.’
Ya juyo ya bita da kallo alamar yana sauraronta, ta dan bata rai sannan tace
‘Kaji kuma? Wannan watan da akayi cefane ba a kawo harda kaji bane? Ko da yake idan
ma sun kare ai sai kuci nama ko kifi tunda duk an kawo ko?’
‘Kajin da aka kaiwa Aisha ta soyawa yara su nake magana, wadannan ma ai sun gani ko
ladan ganin ido ai sai a bamu.’
Binta kawai yake da kallo yana mamaki, ya gyara tsaiwa ya kare mata kallo. Ya ma
rasa me zai ce mata, yace
‘Allah ya sauwake. In dai kajin da Aisha ta soyawa yara ne ba ni na saya mata ba,
kudinta ta sa ta siyo don ta soyawa yaranta kuma da ta soya duk yaron da yake cikin
gidan saida ta bashi. Idan kina da kudi kema ki bayar a sayo miki kaji ki soya ku
cinye ko kuma ragowar na miyar ki soya muku idan kun cinye sai kiyi miyar lami.’
Kafin tace wani abu ya juya ya fice; idonsa har rufewa yake saboda takaici da
mamakin Zahra; Yaushe ta zama haka ne? Dama tura yaran take su gano mata abinda
akeyi a gidan Aishan kenan?
A can gidan Aisha ma bai sami yanda yake so ba don haka ranar dai haka ya fita
zuciyarsa a jagule.
_
Duk wanda Zahra take bi bashi wannan watan saida ta kirawo su, don haka sosai aka
biyata bashi. Sai dai duk yanda ta so kudaden da ta hada su kai dubu dari uku basu
kai ba, gashi bazata iya tambayar Abban ba don har yanzu bai koma kamar da da ita
ba.
Ta riga ta tsarawa Abba cewa akwai kawarsu ita da Amina wadda mijinta ya rasu, don
haka zasu je mata gaisuwa can Gaya. Ko da yace mata Malam Sule ya kaita sai ta ce
masa da motar Amina zasu je don su uku zasu je. Don haka ya bata izinin zuwa.
__
Ranar Lahadi suka yi shirin tafiya Gaya, tun karfe takwas da rabi na safe tasa
Malam Sule yazo ya kaita gidan Amina. Daga can suka kama hanya a motar Aminan.
Idan aka shiga Gayan ma sai an nufi can bayan gari kamar za a fita daga garin
sannan a hau wani kwararo. Dan karamin kauye ne, duk da gidan ba wani babba bane
amma dai yafi duk gidajen da suke kewaye da shi girma.
A share farfajiyar gidan take tsaf ga rumfuna kamar guda hudu wanda kowacce cike
take da almajirai ana ta karatu.
Malam ya san da zuwansu don haka motarsu tana tsayawa wani matashi a cikin
almajiran ya taso da hanzari ya taresu. Ya jagorancesu cikin gida.
Suna shiga soron farko ya nuna musu kofar wani daki yace
Suka daga labule suka shige da sallama yayinda shi kuma almajirin Malam ya juya ya
koma waje.
Da fara'a Malam ya taresu; su biyu ne a dakin shi da wani babban almajirinsa wanda
shi yayi yawo da yawa don haka ya tara ilimi sosai musamman irin wannan na kauce
hanya.
A kan dadduma suke zaune, yaron Malam ya nuna musu daya daddumar wadda take dama da
Malam yace su zauna. Akwai ruwan roba daga gefe guda a dakin ya balle ledar ya
dauko guda biyu ya ajiye musu a gabansu.
‘Wallahi Malam.’
‘Gaskiya Malam ni dai so nake a rabasu kawai, auren ya rabu muyi zamanmu ni da
shi.’
‘Ka ji bayani.’
Ya gyada kai ya mike ya dauko wata tsummar fata a nannade. Ya dawo ya zauna a gaban
Malam ya kwance fatar ya shimfida, yashi ne mai laushin gaske a kan fatar, ya gyara
mata zama ya sake baza yashin. Ya rufe ido ya fuskanci sama yayi wani karatu wanda
duka basa ji saidai suna ganin motsin bakinsa. Jimawa kadan ya sauke fuskarsa yayi
busa a kan yashin a hankali. Ya sa yatsansa manuniya yayi digo guda uku a kan
yashin ya dauke hannunsa ya zubawa yashin ido.
A take aka fara jan layi daga kan digon nan guda uku; ba shi yake jan layi ba kuma
basu ga alamar akwai wani wanda yake jan layi ba.
Tun kafin layikan suyi nisa aka daina jan daya, sai guda biyun aka cigaba da ja har
aka kai karshen fatar aka dire kasa har zuwa inda birbishin yashin ya kare.
Yaron Malam ya dubi Malam Hatimu yace
‘Ka gani Malam, Yusufa da Aisha tafiyarsu mai nisan gaske ce. Ko da zamu iya raba
auren nan to sai an yi aiki da gaske wanda yake butara lokaci don sai dai na kaiwa
Malam na gabas, kuma abun zai dauki akalla watanni takwas; amma komai fitnarsu za a
rabasu.’
‘Kin ji ko Hajiya.’
Ta kara zare ido ta dubi Amina suka yi shiru na dan lokaci. Jim kadan tace
‘Malam to yanzu babu wani abun da za a iya yi a kai? Ni dai ko basu rabu ba ina so
ya daina kulata, ta zauna a matarsa amma ya kasa nutsuwa da ita sai ya zo wajena.’
‘Wannan mai sauki me Malam, in dai da kayan aiki wannan ba zai dauki sati biyu ba
ma an gama in dai sunyi abinda muka ce da kanshi zai gujeta.’
Zahra tace
‘Hakan ma yayi Malam, in ya so wancan babban aikin shima sai a fara tanadinsa don
gaskiya zan fi so a rabasu.’
Yaron Malam ya matsa kusa da Malam sukayi kus-kus, Malam ya dubeta yace
‘Naira dubu dari biyu shine kudin aikinki Hajiya, da zarar kin kawo za a fara
aiki.’
Ta dubi Amina wadda kudin suke jakarta, nan take ta zaro kudi suka kirga dubu dari
biyu suka ajiye a gaban Malam.
Yaron Malam ya dauka ya kirga, bayan ya gama kirgawa ya mayar ya ajiye sannan ya
dubi Malam yace
‘Hakane Malam, a daren yau za a fara aiki idan an gama sai ayi musu waya su zo su
karba.’
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
22
Duk da Aisha tace ta hakura ba fushi takeyi da shi ba amma shi dai bai gamsu ba,
yana ganin kamar har yanzu bata huce ba don taki sakewa da shi.
Ya santa da son ice cream don haka ranar da zai koma kwananta yana idar da sallar
isha’i ya tafi neman ice cream. Saida ya fara tsayawa a Green Park ya siyo
gasasshen kifi da chips irin wanda take so sannan ya siyo ice cream din ya dawo.
A bakin gate din gidan Zahra yayi parking ya fitar da nasu ita da Yara ya kai musu,
bayan ya fito ya ja motar ya wuce gidan Aishan.
Tana kwance a falo a kan doguwar kujera ya shiga, bayan ya amsa sannu da zuwa ta ya
wuce ya ajiye ledodin a kan dining table, ya dawo ya zauna a kusa da ita yana duban
fuskarta. Yace
Tayi murmushi
‘Babu daya, kwanciya dai nayi kawai ashe bacci ya daukeni don ban ma san sun kawo
wuta ba.’
‘Kinyi abincin dare?’
‘Yauwa sai a rufe mana shi mayi dumame don ga kifi da chips na siyo, harda ice
cream.’
‘Ai kuwa ka taimaka min don wallahi kwadayi nake ji kamar naci babu.’
Ya shige daki, ita kuma ta karasa gaba dining table din ta duba kayan da ya siyo.
Ta shiga kicin ta dauko babban faranti ta juye musu kifin gaba daya da chips din
kamar yanda suka saba, ta dauko ta dawo da shi tsakiyar falon kan kafet din ta
ajiye musu; don in ya siyo irin wannan cimar basa zama a table a kasa ake bajewa.
Bayan ta ajiye ta dauko ice cream din roba daya ta zauna ta fara sha.
Ya shigo falon da sallama ya karasa ya zauna a gaban tray din yana fadin
‘Ice cream din ai zai fi dadi idan kika gama cin kifin sarkin shan sanyi.’
Tace
Saida ya gaji ya fara cin kifin sannan ta ajiye robar ice cream din ta sauko, ta
zauna a gaban farantin sai kuma ta dube shi tace
‘Wallahi kamar ma ba zan ci kifin ba, karninsa hawa kaina yake babu dadi.’
Da mamaki ya dubeta
‘Haba dai, ai ko yaya ne kya ci. Don ke fa na siyo kifin nan kuma kice ba zaki ci
ba.’
Ya yago tsokar kifin ya nade yankan dankali guda biyu a ciki ya dora yankan albasa
a kai ya nufo bakinta yana fadin
‘Naga kwana biyu laziness ya miki yawa bari kawai na baki a baki ki huta.’
Tana dariya ta bude bakin ya saka mata ba don tana so ba sai don bata so yaga kamar
wani abune ya sa bata son ci don ta san duk cikin neman shiri ne kuma ita abun ya
wuce a wajenta.
Da kyar ta hadiye lomar kifin nan, tana hadiyewa amai ya taso mata. Nan take ta
mike ta fada bandaki da yake cikin falon, ba tare da bata lokaci ba ya bi bayanta.
A gaban toilet ta tsuguna tayi ta amai yana mata sannu; har saida ta amayar da duk
wani abu da yake cikinta. Tana mikewa zata fito daga bandakin kuma jiri ya fara
dibanta, don haka nan da nan ya riketa suka dawo falo ya zaunar da ita.
‘Sannu Aisha, baki da lafiya ne ko yau kifin karni yake da yawa haka?’
‘Bana jin dadi dama kwana biyun nan jiri yana dan damuna.’
Duk yanda ta so ya kyaleta ta kwanta ki yayi saida ta tashi a daren suka tafi
asibiti. Asibitin da yake zuwa nan ya kaita kuma da yake na kudine suna zuwa aka
samu likita ya dubata.
Nan take aka tabbatar masa da Aisha tana dauke da ciki sati hudu, sai dai likita
yace lallai ta dinga cin abinci kuma tana shan ruwa don yunwa ce take galabaitar da
ita.
Tun a hanya yake tamabayarta ko da akwai wani abu da take son ci tace tuwo take
so, don haka suna dawowa gidan ya zuba mata tuwon da ta dafa ya hada mata shayi ya
sata a gaba saida taci. Bayan ya kwashe kwanukan ya dawo ya zauna ya dubeta yace
‘Sannu, ina jin ma dai wannan ‘yan biyu ne shi yasa ya zo da karfinsa.’
Ta harareshi ta bude baki a jigace tace
Haka ya kare kwana biyun nan cikin tattalin Aisha, sosai kuma taji kwarin jikinta
tunda baya barinta da yunwa. Sata yake a gaba duk mitarta sai taci abinci don yana
ce mata yanzu haka wancan cikin ma yana tafiya Saudiya ta fara zama da yunwa shi
yasa cikin ya zube.
………
Ko da ya dawo kwanan Zahra ma haka ya cigaba da zarya wajen Aisha, tun bai gaya
mata ba har dai ya gaji da yanda take masa kallon zargi ya sanar da ita Aishan ce
bata da lafiya. Tun daga wannan lokacin ta saka Rukayya a gaba da tambayoyi har
saida ta gane ciki ne da ita.
Tana samun wannan tabbacin ta kirawo Malam ta sanar dashi; domin bata so Aisha ta
haihu ko sau daya tunda akwai yiwuwar ta haifi namiji. Ita kuma yanda ta cika gidan
da yara mata ba zata taba bari haka ta kasance ma. Auren Aishan ma da take fatan
nan da wani lokaci ta kawo karshensa kuma bata so a fita a bar mata wani yaro don
haka ma gara kawai kada Aishan ta haihu.
A nan Malam yayi mata alkawarin cewa Aisha bazata haifi wannan cikin ba amma dai ta
bari zuwa lokacin da za a gama aikinta wanda akeyi yanzu sannan sai a san yanda za
ayi da cikin.
Sai a lokacin ta samu natsuwa ta cigaba da harkokinta, duk wata rawar kai da Abban
yakeyi ta daina damunta don ta san da an gama mata aiki gidan Aishan zai gagareshi
shiga kamar yanda Malam ya gaya mata.
……….
Ranar da suka cika sati biyu da zuwa gaya Malam ya kirawota ya sanar da ita an gama
aiki don haka ta zo ko ta turo a karba. Nan da nan ta kirawo Amina domin ita take
so ta je ta karbo mata. Bayan ta gama yiwa Aminan bayani tace
‘Yanzu ya za ayi kawata, bana son tura wani ayi min wasa da aiken nan kuma wallahi
ba lallai na samu ya barni komawa Gaya ba kwanan nan.’
Aminan tace
‘Kinga ma ni wallahi motata ta sami matsala, naira dubu hamsin makanike yake nema a
wajena ta gagareni shi yasa ma kwana biyu bana fita da motar.’
‘kai kwata.’
‘Allah, kuma kinga ba zan iya zuwa Gaya a motar haya ba, ko kece ma zaki ba zan
raka ki ba wallahi in dai a motar haya ne.’
Sukayi shiru na dan lokaci kowa da abinda yake tunani. Ragowar kudin Zahra ne a
hannun Aminan wajen Naira dubu dari da sittin da tace ta cigaba da ajiye mata su
zata hada na daya babban aikin a wajenta. Ta riga ta kashe kudin gaba daya don haka
take neman hanyar da zata bi ba sai ta biya ba. Zahran ce ta katse mata tunani
‘To kawata ki dauka mana a cikin ragowar kudin nan, ko nawane ki dauka in dai za a
samu a gyara motar zuwa gobe ki sami damar zuwa.’
Da fara’arta ta amsa
‘Ai kuwa nagode, yanzu zan kirawo makanike yaje gida ya dauki motar in sha Allah
zaki jini idan na dawo.’
Washegari sai can bayan la’asar sannan Amina ta kirawo Zahra ta sanar da ita ta
dawo kuma yanzu zata zarto ta kai mata.
A bakar leda irin ta VIVA ta shiga gidan da sakon, nan da nan Mommy ta mikawa
Jummai Sumayya suka shige dakin baki na nan kasa suk kullo kofa.
Ta zaro ido
‘Allah kawata bana jin komai idan bukata zata biya, kinga kuwa yanda matar nan take
kokarin mayar da ni kalar kwatance? Ai komai ma zan iya yi.’
Ta zura hannu a ledar ta zaro wata karamar farar roba irin ta man shafawa ta mika
mata, ta bude tana kallo ita kuma tana yi mata bayani.
‘Yaron Malam yace wannan abun sunanshi kwarjini, kuma sai da kara masa dubu talatin
ya bayar. Yace idan kika kusa sauke abincinsa zaki saka a ciki, narkewa yake kamar
kitse kuma bashi da wari. An yi sa ne musamman da sunanki a jiki, in dai yaci
wannan ba zai sake yi miki musu ba duk abinda kike so shi zai yi.’
Amina ta sake zura hannu cikin ledar ta fito da wata buta irin ta alwala, amma da
bakin karfe aka yi ta. Ta mika mata tana fadin
‘Kada ki bude don Malam yace azabar wari gareshi. Shi kuma binnewa zakiyi a tsakar
gidanta, yace in dai kika binne wannan a gidan da take to ko yaje ba zai iya zama
ba balle ayi wata mu’amalar aure. Yana shiga zai fito.’
‘Yanzu inda matsalar take yanda za ayi na sami wanda zai shiga gidan ya binne min
wannan abun, don kin san nifa ban taba shiga ba don ba zan iya kayan takaici ba.’
Sukayi shiru na dan lokaci kowa yana tunanin yanda za ayi. Jimawa kadan Aminan tace
‘Kinga tunda shi yana da mukullin ki faki ido ki dauki hotonsa yau da daddarem nan
in ya so sai ki turo min hoton ni kuma zan sa a samo me kama da shi a kawo miki
zuwa gobe da safe. Jibi da safe sai ki faki idonsa ki zare na wajensa ki musanya
masa don kar ya gane, tunda tana zuwa aiki yaron da zai kawo miki zai jiri in ya so
da zarar Abban ya fita sai kawai ki bashi yaje ya bude gate ya shiga ya nemi waje
can gefe daya ya binne. Yana dawowa tunda wajenki yake fara zuwa sai ki yi sauri ki
mayar masa da mukullin.’
‘kawata kin san kan tsiya wallahi, gaskiya ban ma san irin godiyar da zan yi miki
ba. In Sha Allahu yana dawowa zan turo miki hoton.’
Nan da nan suka gama sukayi sallama Aminan ta kama hanya saboda magriba ta kusa,
tana tafe tana jin dadin ribar dubu talatin din da ta ci. Yanzu kudin Zahra saura
dubu saba’in kenan a hannunta kuma su din ma cinyesu zata yi.
--------
Yanda Abban yake kula da ita ya sa laulayin yana yi mata sauki, wani abun har da
gangan ma yi take yana biye mata sai kace wanda ba a taba yiwa haihuwa ba. Ya na
yawan gaya mata yana sonta shi yasa yake so ta haifa masa yara masu kama da ita
kuma masu irin dabi’arta.
Tun shekarar da ta wuce taso tayi masa bikin zagayowar ranar haihuwa; duk da ba
kowa zata gayyato ba iya su biyu kawai; sai kuma ya zama waccan shekarar bata sami
dama ba a daidai lokacin. Don haka ta shiryawa wannan shekarar duk da laulayin nan
yayi mata bazata.
Tun saura kwana biyu ranar ta tanadi duk wasu abubuwa da take bukata wadanda zata
shirya masa abinci.
Ranar ta kama ranar Talata sannan kuma ba kwananta ba don haka haka dai ta shirya
ta fice wajen aiki da niyyar idan ta dawo sai ta zo ta fara shiri. Batayi niyyar
rikeshi ba don haka ta shirya idan ma abun zai zama damuwa tunda ba kwananta bane
to idan ya shigo ya kwasa yaje can gidan Zahra din yaci. Ita dai kawai tana so ta
burgeshi a ranar.
Bata gane an shiga gidan ba data dawo daga aiki domin yaron da Amina ta turowa
Zahran irin yaran nan ne na unguwa da suka saba haura gidajen mutane suna yin sata.
Yanda suka tsara masa haka yayi kuma kafin ya fito saida ya tabbatar ya kawar da
duk wata alama da zata sa a zargi wani abu. Inda ya binne abun kuwa ma tsaf ya baje
wajen kuma da yake baya ne daga nesa kadan da tagar dakin maigidan babu ma wanda
zai gane.
Don haka tana dawowa daga aiki ta fada kicin; ta gasa cake dinta dan karamin don
haka kwalliya kawai tayi masa ta mayar da shi fridge, ta gasa kaza gashin larabawa
sannan ta hada masa lafiyayyaen salad da kunun aya. Ta siyo masa agogo mai matukar
kyau da turare mai i dankaren tsada ta hada ta ninke a takarda mai kyalli ta ajiye
masa a kan mudubi tare da wata karamar farar takarda da aka rubuta
Idan ba kwananta bane sai an idar da sallar Isha’i yake shigowa, in ya gama hirarsa
shine in ya koma can sai ya dawo mata da Rukayya. Don haka tana idar da sallar
Magriba ta fada wanka, doguwar riga kawai tasa irin ta zaman gida sai turaruka da
ta feshe jikinta da su. Duk da kamshin da gidan yake sai da ta kawo turarukan wuta
masu dadin kamshi ta kara kunnawa domin so take ya ji dadi kuma ya tafi kwana biyun
nan da kewarta.
Nan da nan gidan ya dau kamshi ga sanyi, Kuma da yake da akwai wuta sai abun ya
kara armashi.
Kamar yanda ta zata kuwa ana idar da sallar isha’i ya shigo gidan.
Da sallama ya shigo kafin ya karaso ciki ta mike ta tareshi kamar yanda ta saba, ta
fada jikinsa tana fadin
‘Sannu da zuwa.’
‘Wani wari nake ji wallahi kuma a cikin gidan nan ne, ko kinyi amfani da wani abun
ne me wari?’
Mamakinta ya karu, ya wuceta ya zauna a kujerar zaman mutum daya yayinda tabi
bayansa tana fadin
‘A’a, wari ne mai karfi wallahi don har kaina ya fara ciwo.’
Ta karaso ta zauna a kusa da shi, tana zama ya mike kamar wanda aka tsikara. Ya
dubeta yace
‘Babu.’
Ya fara karewa gidan kallo yana dafe goshi, tana tsaye tana kallonsa tana mamakin
da ya fara komawa tsoro. Ya dan kara matsawa daga kusa da ita yace
‘Bari na tafi kaina har ya fara ciwo, dama zuwa nayi nayi miki sai da safe zan turo
miki Rukayyan yanzu.’
Kafin ta amsa ya wuceta ya fice daga falon ba tare da ya dubi dining table din da
ta jera abincin ba harda balloon da ta rataye.
Tabi bayansa da kallo tana mamaki, ta kara bude kofofin hancinta ko zata ji warin
da yace yana ji amma ita kamshi kawai take ji kuma kamshi mai dadi. Ta shansahana
jikinta nan ma kamshi taji, ta dai tabbatar babu wari a gidan. To me yake faruwa?
Me yasa da can bai ji warin ba saida shigo gidan?
Ta kalli abincin da ta ajiye a dining table, take kwalla ta cicciko mata ido, ta sa
hannu ta goge.
Ta kashe kudi gashi ba dadi take ji ba ta daure ta hada masa abincin kawai don ta
burgeshi kuma ya shigo da wannan matsalar. Take wani bakin ciki ya tokare mata
kirji, ta dafe kirjin tana Lahaula.
Tana nan a zaune ta ji shigowar Rukayya, ya bude mata gate ya turo ta shi ya koma.
Nan da nan tayi sauri ta tsige balloon din ta kai kicin ta Huda ta sa a shara, tana
fitowa ta sa hannu ta shafe rubutun da yake kan cake din sannan ta budewa Rukayya
kofar falon ta shigo.
Ta karfin tsiya ta danne damuwarta, ta yanka kazar ta bawa Rukayya tata sannan
itama ta dan ci wanda zata iya. Ta hade kayan ta saka a fridge tana mamaki da
takaici da fatan gobe kada ya shigo da wannan matsalar.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
23
Yana leko da kansa bakin gate din gidan Aisha yaji kamar an dauke wani gungumemen
dutse da aka dora masa a kirjinsa, nan da nan ya nemi ciwon kai ya rasa. Ya kalli
gefe da gefe ya ya kara bude kofofin hancinsa ya shaki iska ya ji babu wani wari.
Ya juya ya kalli gate din yana mamaki, ya jijjiga kai cikin damuwa sannan ya kama
hanyar gidan Zahra.
To wannan warin da takurar da yaji a gidan Aishan me ya kawota? Yana zaton dai
warin da yaji ne ya haifar masa da duk sauran damuwar, to amma bai taba jin wari
irin wannan ba. Abinda yafi bashi tsoro shine yanda kamar warin yake fitowa daga
jikin Aisha. Shi tunda ya auri Aisha ko warin gumi bai taba ji a jikinta ba tunda
ita din gwanar shafa turare ce. To me ta shafa yau din? Ko wani maganin ne? Amma ai
lafiyarta kalau sai laulayi wanda shima yayi sauki sosai.
Haka ya shiga gidan yana ta faman neman dalili a kwakwalwarsa amma bai samu ba, sai
dai yana fatan Allah ya sa tayi wanka ta shafa turare kafin gobe domin goben ne
zata karbi kwana.
………
Da yake jiya shinkafa dafa duka ta dafa da daddare bata samu tayi amfani da maganin
kwarjinin da aka bata ba, sai yau ta shirya tuwo miyar kuka. Ta sami ‘yar karamar
tukunya ta debar masa tashi miyar ta mayar wuta ta saka maganin, tsaf ya bace kamar
ba a sa wani abu ba. Ta lashi kadan a harshenta taji babu abinda ya canza na
dandanon miyar, cikin murna ta juye a flsak ta kawo ta jera a dining table.
Yana dawowa daga gidan Aisha ya zauna a table ya cinye tuwonsa tas, tana gefensa
tana yi masa hira domin ita tace masa yunwa take ji shi yasa ana yin magriba ta ci
nata tuwon.
……..
Duk matar da ba a wajenta ya kwana ba ya saba shiga gidanta da safe, tun asuba yake
tunanin yanda zaiyi ya shiga gidan Aisha don yana tsoron ya shiga yanayin da ya
shiga jiya.
Bai ankara ba har takwas da rabi ta wuce, ya riga ya san ta tafi aiki. Don haka
kawai sai ya cigaba da shirinsa.
Sai da ya shirya tsaf ya kama hanyar office sannan ya kirawota.
Lafiya kalau suka gaisa, yanda yaji walwalarta shima ya saukar masa da walwala. Ya
sanar da ita bai fito da wuri ba ya zo ya tarar ta fice don haka sai ya dawo zasu
hadu.
Sukayi sallama kowa yana walwala. Itama Aishan tsoron da ta kwana da shi na abinda
ya faru ya gushe, don haka cikin walwala ta cigaba da gudanar da aikinta.
……….
Kamar yanda ta saba kafin a idar da sallar Magriba ta shirya abincin dare, ta bi
gidan da turare haka ma jikinta. Kamshine kawai yake tashi ko ta ina.
Bayan yayi sallama da Zahra ya nufo gidan,gaba daya ma ya manta da abinda ya faru
jiya sauri kawai yake ya je ya ganta saboda bai gantaba da safe.
‘Subhanallahi.’
Ya karewa farfajiyar gidan kallo kamar mai neman wani abu. Ya daure ya karasa cikin
gidan.
Yana shiga falon kamar a nan warin yake; ta taso daga inda take zaune da fara’arta
ta nufi shi, sai dai kafin ta karaso inda yake ta kula da yanayin da fuskarsa ta
shiga. Ta dan tsaya nesa da shi tana kallonsa, cikin sanyin murya tace
‘Sannu da zuwa.’
‘Yauwa, wai me kike shafawa ne ko kike sakawa a gidan nan mai wannan azabar wari?’
‘Babu fa abinda na saka, turaren wuta na ne kawai wanda ka saba dashi kuma kaima
kana yaba dadinsa.’
‘Kai! wannan ba turare bane. Gashi kaina har ya fara juyawa, bari naje daga waje na
sha iska amma don Allah ki caje gidan nan ko mushen wani abun nema a ciki ba a sani
ba.’
Tana zaune a falon sama tana jiransa domin yaron Malam ya tabbatar mata indai an
binne wannan abun to Abban Sadik ba zai sake iya kwana a gidan ba.
Tana jiyo motsin bude gate ta kyalkyale da dariya saboda jin dadi, tana jiyo
takunsa a bene ta gyara zama ta saita fuskarta.
‘Um um, babu abinda na manta. Akwai wata ‘yar matsala ne don haka a nan zan kwana,
amma na kai Rukayya ta tayata kwana.’
‘Amin. Ki saka min abinci idan na dan huta zan fito na ci.’
‘Ka zo hannu!’
……….
Yanda Aisha ta kwana cikin damuwa da rashin bacci shima haka ya kwana. Duk yanda
Zahra ta so ta kwana a dakinsa sai hakura tayi, domin kiri-kiri ya gaya mata ba
kwananta bane don haka ta bari sai kwananta.
Wannan bai dameta ba saboda ko babu komai ta san yana nan a cikin gidan, kuma
kwanan ma ta san nan da wani dan lokaci zai fara bata.
……….
Duk yanda Aisha ta so yin bacci a daren nan gagararta yayi, har wajen karfe biyu na
dare idonta biyu. A hankali ta tashi ta fice daga dakin, ta koma dakinta ta yi
alwala ta tayar da sallar nafila; shine kawai abinda ta tabbatar zata iya yi ta
sami natsuwa.
Wunin ranar gaba daya bata gansa ba sai dai kawai yayi mata waya da safe sun gaisa,
da dare yayi kuwa ko shigowa bai yi ba ya turo mata Rukayya.
__
Yau sati biyu kenan rabon da Abban Sadik ya shiga gidan Aisha, tun tana kasa bacci
har ta hakura yanzu baccinta takeyi.
Wasu lokutan tana jinsa zai bude gate ya shigo sai ya kusa shigowa falon sai ya
koma da sauri.
Tun abun yana bata mamaki har ya fara bata tsoro, addu’a kawai takeyi tana sadaka.
Duk karshen wata da kansa yake kawo mata cefanenta har cikin gida, amma wannan
watan da akayiwo cefanen Malam Sule aka bawa ya miko mata. Ya ajiye mata a kan
baranda ta kwashe ta shigar ciki, washegari kuma ya turo mata kudin cefane ta
account dinta.
Kiri-kiri yanzu sun koma tsakaninta da shi sai waya. Idan suna magana a waya sai ta
zata babu wata fitna da zata hanashi zuwa wajenta, amma haka za a sakeyi ba zai iya
zuwa inda take ba.
------
Ta gaji da zaman gidan saboda komai baya mata dadi, idan ta taso daga aiki sai dai
kawai ta zauna tayi ta zare ido tana tunani. Don haka ta yanke shawarar tunda yau
Juma’a idan ta tashi daga makaranta zata wuce gidan Zahida; tunda ta riga ta sanar
da shi ta waya.
Sai da suka tashi daga makaranta sannan ta kirawo Zahida ta sanar da ita, inda
Zahidan ta sanar da ita suna gidan Hajiya ita da yaranta a nan zasu wuni. Don haka
itama sai ta wuce gidan Hajiya kawai.
A nan ta tarar da Zahida da yaranta, ta gaya mata Yaya Zainab ma tace bayan
masallaci zata zo.
Bayan ta gaida Umma ta karasa kusa da Anti Uwani, bayan sun gaisa Anti Uwani tace
‘Shatu cikin nan dai yana baki wahala, naga duk kin wani kara figewa gashi ko wata
uku bai karasa ba. Don Allah ki dinga dan cin abinci, idan kuma wani abu kike so a
dafa miki kiyi min waya ni sai na dafa na rufo kaina na kawo miki har gidan.’
Kowa ya kula da ramar da Aisha tayi amma gaba daya su sun dauka cikin da take da
shine ya saka ta ramar don haka babu ma wanda ya tambayi wani bahasi.
Har bayan la’asar anata kaiwa da kawowa, su Farha sai murna sukeyi Mama ta zo ga
kuma ‘yan wasa.
Aisha da Zahida tare sukayi Sallar la'asar a dakin Anti Uwani, bayan sun idar da
sallar ne Zahida ta mike tana nade daddumar tana fadin
‘To bari mu zo mu kama hanya mu da bamu da mota don yau babansu baya gari balle
yazo daukanmu.’
Aisha tace
‘Don Allah ki bari sai munyi sallar Magriba sai mu fita gaba daya in ya so sai na
kaiki gida na wuce tunda ma maigidanki baya nan.’
Da fara’arta tace
Zahida ta gama ninke daddumar ta matsa lokon mudubi inda ake ajiye dadduman ta
ajiye, ta juyo ta zauna a gaban Aisha wadda har yanzu take kan daddumar ta dubeta
tace
‘Wai ni ina Yayarki ne? Bata saki sabon film bane ko har idea ta kare.’
‘To ina ga dai wannan film din nata ta hannun ‘yan tsubbu ta biyo don yanzu abinda
ke faruwa idan na gaya miki ji zakiyi kamar almara.’
Ta zaro ido
‘Ke haba?’
‘Yau kusan sati biyu kenan baya shigowa gidan, ina jinsa zai shigo har kofar falon
amma nan da nan zai koma kamar wanda aka razana. Kuma wallahi babu wani wari; kin
san ni dai da turare ko? To bayan yayi maganar ma sai da nayi order din wasu daga
Xee Yazeed Incense and Perfumes amma duk da haka mutumin nan wai wari gidan yakeyi
har yana sa masa ciwon kai. Yanzu tsakani na da shi sai waya amma sati biyun nan ni
ban sa shi a ido na na.’
‘Wannan ma ai daga ji kin san aikin asiri ne, ke kuma kina zaune baki fada ba balle
a nemi magani. To jira kike ta kasheki ko me?’
‘To me zan ce Hida, kin san yanzu da na gayawa Hajiya zata ce a gayawa Yaya
Abubakar, kuma shi ba lallai ya yarda cewa asiri bane. Cewa zai yi sai an yiwa
Yusuf din magana, kuma wannan ba zai magance komai ba tunda kana magana ne da
mutumin da yake a hayyacinsa shi kuwa kina ganin yanda yake birkicewa ma kin san ba
lafiya ba.’
‘To ina dai addu’a kuma ina sadaka, na san babu abinda ya gagari Allah. Don ni
tsoron ma fada nake kada nima naje na kauce hanya gara idan wuta take son shiga
taje ta shiga ita kadai abinta.’
‘Hakane, amma gaskiya cikin biyu ayi daya; ko a gayawa Hajiya duk da na san yanzu
ana gaya mata zata tada hankali har sai jininta ya sake hawa ko kuma dole mu gayawa
Yaya Zuwaira sai a nemi mafita. Ai akwai malaman da zasu baka adduoi kana yi suna
tayaka har a sami lafiyar abun.’
‘Gara dai Yaya Zuwaira, duk da dai kin san duk abinda aka gaya mata sai ta gayawa
Hajiya amma dai duk da haka gara a gaya matan.’
Nan suka yanke shawarar zasu tafi kafin magriba in ya so sai su fara biyawa gidan
Zuwaira kafin su wuce gida.
Sai wajen biyar da rabi sannan suka kama hanya, Yaya Zainab ma da ita suka tafi don
ita kadai ta zo ba tare da yara ba. A hanya Zahida ta sanar da ita abinda yake
faruwa suka hadu suka yita sallallami.
A kitchen suka sami Yaya Zuwaira tana kwashe tuwo don haka nan suka zauna a kichin
din suka mayar mata da abinda ya kawo su.
Saida ta gama kwashe tuwon suka dawo falo sannan ta dubi Aishan tace
‘Sannu! Yanzu da da kika yi shiru haka zakiyi ta zama tsakaninki da miji sai waya?
Wannan ma ai ba sai an fada ba kowa ya san tsafi ne. Akwai malamai sosai da muke
karatu da su wasu ma su ke karantar da mu a islamiyya, in Sha Allah gobe asabar
idan naje zan nemi malamai na tambaya.’
‘Wasu abubuwan kana jinsu kamar almara ashe suna faruwa, Allah ka shirya
zukatanmu.’
‘Amin.’
__
Cikin walwala Zahra take gudanara da lamuranta musamman tunda ta gane Abban Sadik
ya daina musa duk wani abu da ta fada ko dai-dai ne ko ba dai-dai bane. Gaba daya
ma ya rage magana da walwala, sai dai wannan bai dameta ba tunda yanzu duk yanda ta
tsara haka akeyi.
Sadik ya gama jarrabawarsa ta WAEC da NECO don har ma sunyi candy, sai dai bai fasa
tara abokai a boys quarters din gidan ba. Duk yanda Jummai ta so ta karkatar da
hankalin Zahra ta duba abinda Sadik yake aikatawa ta ki ta duba, sai dai kullum ta
tambayeshi inda kai tsaye zai ce mata ba haka bane.
……….
Ya riga ya amsa zai saya mata mota sai dai ya gaya mata ta saurara zuwa nan da sati
daya akwai kudin da yake sa ran zai samu in ya so sai ya saya mata motar.
Ya gama cin abincin darensa yana zaune a falon sama yana kallon tasahar Aljazeera
inda take zaune a kusa da shi tana chatting a waya. Ta ajiye wayar ta dan matso
kusa da shi tace
Yayi murmushin yake wanda yanzu ya zamar masa dabi’a, duk murmushin da zai yi baya
kaiwa zuciyarsa. Yace
‘Tana nan mana, na ma biya kudin sai dai akwai dan ciko da zanyi musu next week sai
a kawo motar.’
‘To gaskiya a sallami Malam Sule don bana son ya koya min mota tunda kai kace baka
da lokaci, sai a kawo wani direban.’
‘Wannan babu matsala, Malam Sule dama direban gwamnati ne ai. Ranar litinin mai
zuwa sai ya koma office, akwai Alin Kano sai ya karbi aikin.’
‘Gaskiya ni dai dama ka bari na samo direban, tunda kaga akwai matasa sosai a ‘yan
uwan Abban mu don wasun suma direbobin motar haya ne. Idan na samo a dangi ai ya fi
ko, sai ya koya min kuma ya cigaba da rike aikin Malam Sule.’
‘To babu laifi, ki duba din in ya so idan an samu sai ya karbi aikin Malam Sule
din.’
A cikin daren ta kirawo Amina tace ta samo mata direba, ita dai ba komai ta damu da
shi ba kawai tana son wanda zai yi duk abinda tace ba tare da ya kawo mata tangarda
ba. Idan ya gama koya mata tuki sai kuma ya dinga kai yara makaranta da motar Malam
Sule da za a bashi.
Haka ta kwana cikin walwala saboda burinta ya kusan cika, itama zata mallaki mota
ta dinga fita a gari kowa yana kallonta.
………
Ya riga ya sanar da Malam Sule cewa sati mai zuwa zai koma office da aiki saboda za
a kawowa Zahra mota da sabon direba. Ko daya Malam Sule bai nuna damuwa ba saboda
wannan abune da yake ta jiran faruwarsa saboda abubuwan da suke faruwa ‘yan
kwanakin nan.
Yana office aka kirawoshi aka sanar da shi ga motar da ya saya ya fadi inda za a
kai masa, nan take yace a kai masa gida amma idan an kai a jirashi a bakin gate.
Kusan lokaci guda suka Isa gidan da yaron da ya kai motar, maigadi ya bude musu
gate suka shiga gaba daya. Bai gaya mata yau za a kawo motar ba don haka bata sa
rai ba, ko da taji shigowar mota biyu ma tayi zaton shi da Malam Sule ne suka dawo
a lokaci guda. Sun gama magana da Abban yau Malam Sule zai bar aiki kuma bata so ya
dameta da wata sallama don haka tayi zamanta a falo.
Basu gama gyarawa motocin tsayuwa ba Malam Sule shima ya iso, bayan ya gaida Abban
ya mika masa mukulli yayi masa sallama a kan zasu hadu a office.
Malam Sule yana fita ya sallami daya yaron ya karbi mukullin motar.
A falon kasa ya sameta tana chatting a waya yayinda Sumayya take wasanninta a
tsakar falon.
Bayan ya amsa sannu da zuwa ta ya mika mata mukullin motar yana fadin
‘Ga mota, Allah ya sa direban naki ya shirya ku fara fita gobe don na san kin matsu
ki fara yawo a mota.’
Kafin ya rufe bakinsa tayi tsalle ta mike ta karbe mukullin dake hannunsa tana
godiya. Ta fice ta barshi yana kokarin daukar Sumayya.
Tana hango motar jikinta yayi sanyi, taci birki kamar wadda aka tare. Ta sake
karewa tsakar gidan kallo don ta tabbatar wannan itace kadai bakuwar mota.
Dukkan alamu sun nuna hakan ne; yanzu wannan ce motar da Abban Sadik zai bata don
ta dinga tukawa? Ita da take son mota ta kece raini kamar ta Aisha ko kuma wadda
tafi ta Aisha amma ya siyo mata wannan? Ta matsa kusa ta karewa motar kallo, Honda
Civic ce kirar 2009, ba wai muni tayi ba ko tsufa da yawa don fes take amma dai
tana ga babu girma ace ta hau wannan Aisha kuma ta hau dalleliyar Honda Accord
kirar 2013. Ko babu komai yanzu a 2018 ake, ina ma laifi ya bata koda accord din ce
itana kuma ta 2013 misali.
Ta juya ta kalli kofar falon ko zata ga ya biyota amma sai ta ga babu kowa, tayi
kwafa a fili tace
‘Haba ai da kunya ma ya bani wannan yace ya bani mota.’
A daki ta sameshi ya ajiye Sumayya a kan gado yana kokarin cire kaya, bayan ya amsa
sallamarta tace
‘Naga motar, nagode Allah ya kara budi. Ni da na sa rai da wata dankareriyar mota,
wannan ma ai ta Malam Sule ta fita kyan gani.’
‘To sai ki ajiyeta ki dauki ta Malam Sule, wannan din sai a dinga kai yara
makaranta ko?’
So take tace motar bata ma kai ta Aisha ba amma bata son janyo matsala; 'yan
kwanakin nan duk lokacin da tayi maganar Aisha to fa sai ta kwana biyu bata gane
kansa ba, haka zai yi ta kunci yana muzurai. Don haka ta ja bakinta tayi shiru.
……….
Tana zaune a falon kasa yara suka dawo daga islamiyya, bayan sun yi mata sannu da
gida Yusra tace
‘Mommy gaskiya Abba ya raina ki wallahi, wannan motar fa ina jin '98 ce ko rabin
kyan ta amaryarsa bata kai ba. Ya za ayi ace tana hawa wannan motar ke kuma kina
hawa wannan. Shima dai Abba!’
Kafin ta rufe baki Rukayya ta karasa kusa da Mommy ta dafata tana fadin
‘Congrats Mommy! Wataran muma kya dinga zuwa daukarmu a makaranta ko na cewa
kawayena Mommy ta zo yanda suke min. Bari naje na kara kallonta, wallahi Mommy ta
min kyau ina son mota kalar silver.’
Kafin Mommy tace wani abu tayi waje da gudu, Ummi ta rufa mata baya sunata murna
Mommy zata dinga kaisu school.
Yusra tayi tsaki tace
‘Mommy ya fa kamata ma ki hannan wannan tayin kwanan da Rukayya take zuwa, ace
kullum mutum yana faman yawo wajen kwana. Kawai kowa tashi ta fissheshi.’
Sai yanzu tunanin ya fado mata, don da tayi wannan tunanin da tuni ta hana tunda
yanzu duk abinda ta fada shi Abban yakeyi.
‘Mommy kika ce Malam Sule ya bar aiki, yaushe za a kawo Sabon direba?’
Ya ma zo dazu kun tahfiz, gobe shi zai zo ya kai ku makaranta. Sunansa Balele, sai
goben za ki ganshi.
………..
Yana zaune a a falo shi da yaran gaba daya bayan sallar isha’i. Yusra tana zaune a
dining table tana karatu su kuma Ummi da Nana suna zaune yana yi musu homework.
Rukayya ce ta fito daga daki dauke da jakar makarantarta, ta wuce kicin inda ta
jiyo motsin Mommy. Bayan tayi mata sannu da aiki tace
‘Ke na gaji da wannan tayin kwanan, koma ki ajiye jakarnan an gama daga yau. Ai
naga itama a danginsu tana da ‘yaya don haka ta dauko mai tayata.’
Ta sunkuyar da kanta saboda damuwa, sai dai ta san babu yanda zatayi don haka ta ja
kafa ta fice daga kicin din.
Daga inda yake zaune yana jiyo abinda take fada don da karfi tayi maganar, ba zai
iya hanata ba don haka ya tashi ya tsallake yaran ya haye sama.
‘Ya tafi sama, yace ki karasa mana homework din ko ke ko Yaya Rukayya.’
Tayi murmushi ta janyo littafin Ummi; ta san ya jiyo abinda ta fada ne kuma babu
yanda zai yi da ita.
………
Bai iya yiwa Aisha waya ba sai dai text kawai yayi mata ya sanar da ita ta rufe
kofa don Rukayya bazata zo ba yau.
Batayi mamaki ba don tuntuni take tsammanin hakan; ita din ma hakan ya fi mata
nutsuwa don gani take kamar za a iya amfani da Rukayyan a cuceta. Don haka nan take
ta tashi ta rufe gidan tayi kwanciyarta; ta bari sai nan da sati daya sai ta dauko
Amira ta cigaba da tayata kwanan suga abinda hali zaiyi.
--------
Kamar yanda Yaya Zuwaira tayi alkawarin zata nemi shawara a wajen malamai hakan
kuwa tayi. Ta sami Malama Halima wadda bayan ta ji duk wani bayani ta ja ta suka
sami Malam Muhammad.
Yayi musu bayani sosai, ya tabbatar musu tsafi ne tunda daga karshe Aishan tace
Abban yace kamar daga jikinta yake jin warin. Sai dai ya tabbatar musu idan aka
cigaba da addu’a abun zai karye. Ya tunasar da ita azkar sannan kuma ya tuna mata
addu’oin karya sihiri, ya sanar da ita ta dinga karanta surarul baqara kullum dare
a gidan kuma ta dinga yawan sadaka da sallar dare.
Ya sanar dasu kada suce zasu rabata da shi domin don haka akayi wannan asirin, idan
suka bari aka cigaba da addu’a komai zai wuce.
Tun da Zuwaira ta sanar da ita ta mayarwa kanta ka’ida kullum kafin ta kwanta bacci
sai ta karanta suratul baqara, idan kuma ta kwanta karfe biyu da rabi na dare tana
yi zata tashi tayi sallar dare sannan ta koma bacci.
…………
Ko da aka hana Rukayya zuwa sai tashi ya dan fara yi mata wahala kasancewar dama
cikin da yake jikinta yana sakata bacci sosai sannan kuma idan ta tashi kasancewar
ita kadai ce a gidan bata jin dadi sosai. Idan tana jin motsin Rukayya tafi
natsuwa, ta dai tabbatarwa kanta lallai gobe zata dauko Amira tunda ma an gama
jarrabawa hutun makaranta za ayi.
Yau ma kamar kullum karfe biyu da rabi na dare alarm din wayarta ya fara waka, ta
lalubi wayar ta kashe alarm din sai dai ta kasa tashi. Wajen karfe uku saura kwata
alarm din ya kara daukan kara; ta daure dai ta mike zaune bayan ta katse alrma din.
Ta kunna fitlar wayarta ta ajiye a kan durowar gefen gadon saboda babu wuta a
lokacin. Ta zauna tana hamma tana muttsike idanu tana kokarin ta wattsake ta tashi
tayi sallah.
Haka kawai sai taji tsoro ya shiga ranta, nan take baccin ya bar kanta. Ta karewa
dakin kallo duk da dai babu wuta amma tana iya ganin komai dake ciki dakin saboda
fitilar wayarta da take kunne. A hankali sai ta fara jin kamar ba ita kadai ce a
dakin ba, sai taji kamar akwai motsin mutum a dakin kuma motsin ma a nan kusa da
ita inda take zaune a gefen gado. Ta duba har tana shafa gadon ta tabbatar babu
kowa amma kuma kamar tana jin alamar da wani a kusa da ita.
Ta kasa tashi ta bar wajen kuma ta kasa aikata komai, har jikinta ya fara rawa a
hankali saboda tsoro.
Ta dan muskuta kadan ta janyo abun rufar da ta rufe kafafunta da shi ta rufe
kirjinta da shi ta kankame jiki.
Motsi ta sake ji kamar an tsallake kafafunta sai dai bata ga wanda ya tsallake din
ba, kafin tayi wani abu taji kamar an cafke cibiyarta wanda ya sa mararta tayi wani
irin suka gumi ya karyo mata. Ko minti daya ba ayi ba taji an finciki cibiyarta
kwatankwacin yanda ake balle murfin kwalabar lemo; da hanzari ta kai hannu ta dafe
cibiyarta tana fadin
Gumi ya cigaba da karyo mata saboda yanda mararta take kara kartawa da ciwo. Ta dan
muskuta ta gyara zama ta cigaba da ambaton
A hankali ta dan fara samun natsuwa, dakin ya dawo dai-dai sai dai mararta da bata
daina murdawa ba.
Ta tuna sallar dare ma ta tashi yi don haka a hankali ta zuro kafafunta daga kan
gadon don taje bandaki tayiwo alwala.
Yanda taji danshi a jikinta ta tabbatar fitsari tayi ko kuma jini ne yake binta,
cikin hanzari ta karasa bandaki. Tana kwabe kayanta taga jini ne yake binta gashi
mararta tana kara kartawa. Da kyar ta daure ta wanke jikinta sannan ta lallabo ta
dawo dakin ta kwanta. Ta duba wayar tata taga karfe uku da minti biyar na dare, ta
gyara kwanciyarta ta kashe fitilar wayar don yanzu babu wanda zata iya tashi daga
barci.
Haka ta kwanta tanata juyi tana ambaton Allah ga mararta tana ciwo har akayi kiran
asuba. Ta lallaba ta hada ruwan zafi tayi wanka sannan ta hada shayi. Ta dawo ta
zauna a kan dining table ta saka kofin shayin a gaba tana kallonsa; karo na biyu
kenan tana barar da ciki a gidan nan, to me yake faruwa? Ta san dai bawa baya wuce
kaddararsa amma abun ya fara bata tsoro musamman na jiya da daddare da yayi kama da
zuwa akayi musamman aka cire cikin aka tafi.
Kusan shekaru hudu kenan da aurensu amma bazata iya cewa sunyi wata shida cikin
nutsuwa ba, fitna daga wannan sai wannan.
Yanzu gashi sati wajen uku kenan an shiga na hudu rabon da Yusuf yazo inda take,
sai dai kawai waya. Wayar ma yanzu ba kullum yake kira ba.
Saida shayin nan ya fara hucewa sannan ta dauka ta sha. Ta sami Panadol ta sha
saboda yanda mararta take ciwo sannan ta koma ta kwanta a kan doguwar kujera.
Sai wajen bakwai da rabi na safe sannan ta kirawo Yaya Zuwaira ta sanar da ita
halin da take ciki, wajen takwas da rabi ta iso gidan suka kama hanyar asibiti.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
24
Suna zuwa asibiti suka wuce emergency, nan take likita yace suyi scanning. Bayan
sun kawo sakamakon likita yayi musu bayani cewa cikin ya fita amma za a yi mata
wankin ciki. A nan suka sami waje Zuwaira tace Aishan ta zauna zata je ta biya
kudin ta dawo.
Bayan ta dawo kafin su koma waje likita ta dubeta tace
Ta kau da kai
‘To me zan ce masa baya iya zuwa kusa dani, ni ban gaya masa ba.’
‘To bari na dawo sai na gaya masa, ai gara ya sani ko don ya san cikin jikinki ya
bare.’
Yana hanyar tafiya office wayarsa tayi kara, yana dubawa yaga Zuwaira. Da rawar
jiki ya dauki wayar wanda shi kansa bai san dalilin hakan ba. Bayan sun gaisa ta
sanar da shi Aisha tayi bari suna Asibitin Nassarawa.
Yana shiga asibitin yayi tambaya aka nuna masa inda suke, kai tsaye ya wuce.
Kafin ya karasa wajen ya hango Zuwaira a zaune a kan kujera tana jira a fito da
Aisha daga wankin cikin.
Yana dab da karasawa nurse ta bude kofar dakin wankin cikin Aisha ta fito, nurse
din tana mata sannu tana kokarin dafa ta. Zuwaira ta mike da hanzari ta nufota
daidai lokacin da Abban ya karaso kusa da ita.
‘Aisha.’
Ta dauke kanta tana kokarin mikewa sosai saboda yanda take jin jikinta babu kwari.
Kafin ta karasa mikewa ya tareta, gaba daya ya rungumeta yana mayar da numfashi.
Suka dauki kamar minti daya bashi da niyyar sakinta. Yaya Zuwaira tana tsaye tana
kallon ikon Allah ita kuwa nurse tuni ta wuce ta basu waje.
Bashi da niyyar sakinta don haka ta dan fara mutsu-mutsu tana son ta zare jikinta.
Ta rada masa.
Ya saketa, sai dai yana rike da hannunta yana kallon fuskarta. Cikin damuwa da
tausayawa yace
‘Sannu.’
Suka karasa suka zauna a kan kujera suna jiran a rubuta mata sallama.
Tana ta faman gyara zama don haka ya matsa ya janyota jikinsa ta kwanta.
Suna nan zaune likita ya fito daga dakin wankin cikin ya shige ofishinsa. Zuwaira
ce ta mike ta bishi don shi baya jin zai iya barin Aisha a nan ita kadai ba.
Jimawa kadan Zuwaira ta fito rike da takardu, ta mikawa Abban takardun tace
‘Ga wanna magunguna aka rubuta, likitan yace zamu iya tafiya. Idan taci abinci ta
huta zata ji kwari a jikinta, idan akwai wata matsala yace sai a dawo.’
Duk da tace masa zata iya tashi amma sai da ya riketa ya kamata sannan ta tashi,
yana rike da ita har suka zo wajen motarsa. Sai da ya kwantar da kujerar gaban
motarsa sannan ya sa Aisha ta dan kashingida. Ya rufe kofar motar ya matso kusa da
Zuwaira wadda take tsaye jikin motar da direbanta ya kawota. Yace
Saboda haka gaba daya suka shiga motar Abban suka nufi gidan Aisha.
Sai da ya tsaya a super market ya siyowa Aisha kaji da yoghurt mai sanyi kuma ya
hada da apple ya zuba a mota sannan suka wuce gidan.
A bakin gate yayi parking, kafin ya zagayo ya budewa Aisha kofa ta bude ta fito. Ya
fito da ledojin da yayi sayayya ya mikawa Zuwaira yana fadin
‘Bari na rakaku ciki sai na fito na wuce office don ko isa ban yi ba na sami
kiranki.’
Yana rike da Aishan suka nufo gidan, tunda ya bude gate din ya sako kafarsa cikin
gidan ya fara jin wannan warin da yake firgita shi. Daga hannunsa da take rike da
shi ta fuskanci abinda yake faruwa da shi, tana kokarin duba fuskarsa ya zare
hannun nasa daga cikin nata.
Suna daf da taka barandar falon ya ja baya, yana juyowa ya fuskanci Zuwaira wadda
take biye da su a baya wadda itama sauyawar da fuskarshi tayi yayi matukar bata
mamaki. Kafin tace wani abu yace
‘Yauwa ku shiga, bari nayi sauri naje sai na dawo.’
Bata yi tsammanin ya ji a dawo lafiyar da takeyi masa ba don kamar a guje ya fice
har yana yin tuntube.
Suka kalli juna ita da Aisha, ta matsa kusa da Aishan tana mamaki. Aisha tayi
murmushi tace
Kafin azahar dangi duk sun hadu a gidan don wannan karon Hajiya ma cewa tayi sai ta
zo, don haka gaba daya suka taho da yaran da Anti Uwani. Sai da yamma suka tafi
suka barta da Amira bayan da suka tabbatar ta wattsake.
-------
Kafin ya fita daga gidan har kansa ya fara sarawa, yana fita daga gate din ya kama
hanyar ya nufi gidan Zahra.
Sai da ya kusa zuwa gate sannan ya kalli hannunsa ya ga mukullin motarsa, a take ya
tuna da motarsa kuma ya tuna office ya kamata ya tafi.
A hankali ya janyo kafarsa ya dawo ya shiga motarsa ya kama hanyar office.
Zuciyarsa tana begen Aisha amma ya kasa shiga inda take. Ya tuno kamar dai lokacin
da suna asibiti bai ji wani wari ba, shi ya manta ma da wannan matsalar gaba daya.
Abun yana ransa kullum yana cewa zai nemi taimako ko addu’a a yi masa amma sai ya
dinga mantawa, wasu lokutan ma yana rasa abinda ya sa baya magana a kan matsalar
nan. Sau biyu yana zuwa gidan Yaya Bello don ya sanar da shi matsalar amma idan
yaje sai suyita wasu hirarrakin gaba daya ma ya manta da abinda ya kaishi.
Yana tukin ma abinda yake ransa shine ya wuce wajen wani malami da ya sani mai
Islamic chemist yaji ko zai sami wani taimako. Kafin ya gama tsara abinda zai
gayawa Malam din kawai ya tsinci kansa a farfajiyar office anata faman yi masa
sannu da zuwa.
Haka ya hakura ya shiga office din da niyyar idan ya tashi daga aiki ya biya ta
wajen Malam din.
__
Tun ranar da Balele ya fara zuwa aiki suka fara fita da Zahra, da yake ta maida
hankali kuma hawa motar tana ranta kafin sati hannunta ya fada. Tunda kuwa taga ta
fara iya fita ita kadai ta bawa Balele tata motar ta karbi Fijo din da Malam Sule
ya bar masa, don tana ganin ko Yaya dai wannan din tafi wadda Abban ya bata tsada.
Tunda motar tazo hannu kuma sai ta fara yi masa tunin yayi mata alkawarin kujerar
Umra, wadda ta ce masa ta azumi take so kuma shi ma goman karshe. Ya tabbatar mata
kujerarta tana nan in Sha Allahu da lokacin yayi za a bata.
………
Tunda Balele ya fara aiki Sadik ya makale masa saida ya koyi mota, dama tun a wajen
Malam Sule ya so koya Abbanshi ya hana.
Jarrabawarsa ta WAEC ta kusan fitowa, shi da Mommy sun hadu sun saka Abban a gaba a
kan lallai sai an kai shi Dubai zai yi degree. Da fari Abban ya ki amincewa amma
daga baya ya amsa don haka sakamakon WAEC din kawai ake jira.
A labarai Network News Abban ya gani cewa WAEC sun fitar da sakamakon don haka a
take ya ce a kirawo Sadik ya zo a duba masa nasa a computer din Abban.
Yusra aka tura taje dakinsa wanda yanzu ya koma boys quarters ta kirawoshi, an yi
sa a yana nan don haka kafin Yusran ta gama gyara zamanta ya shigo falon.
Da mamaki Abban ya kalleshi, har ya karaso kusa da shi ya zauna sannan yace
‘Kai meye haka ne zaka taho kamar zaka fada kan mutane.’
Nan ya umarceshu ya dauko katin inda yace masa yana wajen Mommy. Ba tare da bata
lokaci ba ta tashi ta dauko katin tare da computer din Abban ya karba ya duba masa
sakamakon.
Yaci komai da sakamakon mai kyau sai dai bai ci English ba, wanda kuma dole sai da
shi ake admission a halin yanzu.
Ya shafa kai
‘Wallahi Abba ina jin matsala muka samu don duk ‘yan makarantar tamu da muka yi
exam tare har yanzu bamu ga wanda yaci English din ba.’
‘Babu wata matsala, kun dai fadi kawai. Ai da matsala kuka samu rike sakamakon za
ayi a saka muku pending ko awaiting result. Kun dai fadi English kawai, amma zanje
makarantar naji.’
Mommy tace
‘Ai babu wannan zancen kuma har sai ya sake jarrabawa ya sami English wannan ai ko
a nan Nigeria ba zai sami admission din ba. Kasashen waje kuma ko sun bashi
admission rashin wanna English din sai yayi affecting dinsa a nan gida. Next year
sai ya gyara mu gani, amma dai gobe zanje makarantar naji yanda za a yi.’
…………
Kamar yanda yayi alkawari haka yayi, yana fita ya tsaya a makarantar su Sadik. A
nan principal yayi masa bayanin cewa su Sadik su biyar ne suka sami F a English,
saboda sun yiwa malamin da ya zo da jarabawar rashin kunya; su dai a makarantar
suna tunanin abinda ya sa ya kada su English din kenan.
‘Yallabai kuma a dan duba yaron nan don ka ga da yaron babu ruwanshi amma zuwa
lokacin da suka gama jarrabawa gaskiya yaran da yake bi gaskiya duk suna shaye-
shaye. Gara dai a bincika kafin abun yayi nisa.’
Yayi masa sallama ya tafi yana mamaki; Bai taba zargin Sadik ba amma yanzu kam dole
ya dau mataki.
Bayan ya dawo daga aiki ko abinci bai ci ba ya sa Mommy ta kirawo masa Sadik, har
zata fita ta barsu yace ta dawo ta zauna.
‘Su waye abokanka? Kuma meye gaskiyar magana da aka ce min kuna shaye-shaye?’
Ya zare ido
‘Wallahi Abba babu abinda muke sha, gaba dayan abokan nawa ma Mommy ta san su.’
Ya kalli Mommy.
Tace
‘Gaskiya na san abokansa dukansu babu wanda yake shaye-shaye, yaran da har nan din
ma suna zuwa.’
Duk yanda ya so yayiwa Sadik fada Mommy bata bari ba, tun yana kokarin fadan har ya
gaji yayi musu shiru.
Kuma da yake gaba daya yaran sun riga sun gane duk yanda Mommy ta fada haka akeyi
don haka duk abinda basa so yayi magana a kai sai su tsara Mommy, don haka haka
Sadik ya sa ta gaba a kan karya akeyi masa. Shikenan a haka zancen ya wuce.
Jummai tana kallon abubuwan da suke faruwa amma babu yanda zata yi don haka ta sawa
abun ido.
--------
Tun ranar da suka dawo daga asibiti bai sake shiga gidan Aisha ba, wayar ma yanzu
ba sosai sukeyi ba.
Ga shi idan yayiwo cefane a gidan Zahra zai ajiye ya raba sannan yace Balele ya
kwashi na Aisha ya kai mata; don haka a nan Zahra zata samu ta zare duk abinda take
ganin bata so a kaiwa Aishan. Ta kwashe kaji da kifi wani lokacin harda kayan shayi
duk kwashewa takeyi, don haka duk wata sai Aisha tayi ciko a cefanenta. Ta riga ta
san me yake faruwa don haka abun baya wani damunta.
…………
Tunda aka siyo motar nan kuwa Zahra ta sami kafar yawo, gashi yanzu baya iya yi
mata fada. Wasu abubuwan suna damunsa amma sai ya rasa yanda zai yi da ita.
Ya raina hankalin Sadik don haka ma ya hana a bashi mota, amma yana ji yana gani
Zahra ta barshi yana hawa motarta. Gashi bazai sami admission ba sai shekara ta
zagayo idan ya gyara jarrabawarsa.
Haka dai ya zubawa gidan ido ita da yaranta suna yin yanda suka ga dama.
………..
Tunda suka bar gidan Aisha Hajiya da Anti Uwani suka kasa nutsuwa, ta san Allah ne
yake bada haihuwa amma tana ganin gara a nemi taimako a kan yawan barin nan. Don
haka suna komawa gida ta sa Anti Uwani ta kai abun sadaka makarantar allo ayi mata
addu’a.
Bayan ta yiwa malamin bayani kuma yace ta sami ruwan zamzam ta dinga tofa fatiha
kafa bakwai tana sha kullum safe da yamma, ko menene zai warware da izinin Allah.
Don haka yanzu bata rabuwa da ruwan zamzam kullum cikin tofi take tana sha. Ga
sallar dare da adduointa da bata fasa ba.
Sai dai duk yanda ta so abun kar ya dameta ta kasa jurewa. Ta rame ta dan yi duhu,
idan dai mutum ya santa ya san tana cikin damuwa. Da tana tsammanin ramar da takeyi
ciki ne amma yanzu da babu cikin ta gane lallai tana cikin damuwa.
Duk da motsin Amira a gidan yana debe mata kewa amma dai gaskiya yanzu abun ya fara
damunta sosai, tana kewar mijinta kuma zaman a haka yana damunta.
Ta sami islamiyya a kusa da unguwar tasu ta shiga duk don ta debewa kanta kewa amma
dai ita kanta ta san lallabawa takeyi.
Lokuta da dama idan ta kwanta da daddare sai dai tayi ta juyi a gadon, idan kuma
abun ya ciyota sai ta kwana tana kuka.
Tun tana lissafi yanzu har ta bata a lissafi, ta san dai an fi wata hudu.
__
Tunda aka fara lissafi azumi saura sati biyu tayiwa Abba tunin Umrarta, a take ya
sanar da ita cewa duk wasu shirye-shirye ma ya gama su tunda tace a goman karshe
take so.
Saura kwana biyu azumi yana zaune a falonsa yana karatun jarida ta shigo falon, ta
mika masa takardar da take hannunta tace
‘A’a ai na gaya miki ni bazani Umra ba, Hajji nake son komawa kuma akwai wani
business da nake son yi a Dubai don haka sai na hada kudin gaba daya da na aikin
Hajji da kuma na business din in ya so ko shekara mai zuwa ko ta sama idan na gama
aikin Hajji sai na wuce Dubai din.’
‘To bari naje na dage da addu’a wata kila da ni za a je Dubai din. Amma dai ka san
gaskiya Umrar azumi akwai sa nutsuwa ko? Wallahi shi yasa na so mu tafi tare.’
Duk yanda ta so ya shirya su tafi Umrar nan tare yaki domin ya tabbatar mata shi
Hajj zai je kuma ba zai yiwu da shi da ita su tafi su bar yara ba, don haka dai ta
hakura.
Fargabarta daya kada ta tafi kafin ta dawo ya koma wajen matarsa; duk da cewa ko a
daren jiya saida sukayi magana ta Whatsapp da yaron Malam ya tabbatar mata ko
shekara nawa zatayi bata dawo ba ba zai iya kusantar Aisha ba, ya ma tabbatar mata
ba Aisha ba ko wata mace ce ma babu abinda zai shiga tsakaninsa da ita.
Ana i gobe azumi ya yiwo duk wata sayayya, kowacce list din da ta bayar shi yayi
amfani da shi ya siyo mata. A nan kan barandar gidan Zahra ya sauke kayan ya kirawo
Balele ya ware na Aisha yace ya kai mata yanzu shi kuma ya shige gida.
Yana shigewa Zahra ta dakatar da Balele ta caje ledodin kusan duk wani abu da yake
kwalba ko roba saida ta kwashe shi irinsu mayonnaise da salad cream, butter. Ta
dauke kayan shayi ma sannan ta kwashe kwai da kaji. A karshe idomie kawai ta bari
rabin carton da macaroni da semovita sai sabulun wanka da Omo aka kaiwa Aishan.
Haka ta karba tana mamaki; to ya san wannan zai siyo menene zai sa yace ta rubuto
list. Haka ta adana kayan ta dauki Amira suka je suka karasa nasu shopping din na
kayan bukata saboda azumi.
-------
Tun saura kwana uku jurgin su Zahra ya tashi Rahma; ‘yar uwarta wadda ta zauna mata
da ta haifi Sumayya ta dawo gidan, domin itace zata kula mata da yara da gidan
kafin ta dawo.
Sallah saura kwana goma sha uku jirginsu ya tashi sai kasa mai tsarki.
-------
Ranar da Mommy ta tafi da yamma ana dab da shan ruwa Rukayya ta sami Abban a falo,
yana kwance a kan doguwar kujera ta shiga da sallama. Bayan ya amsa sallamarta ta
karasa ta zauna a gabansa, yace
Tace
‘Abba naje gidan Anti Aisha na dinga tayata kwana kafin Mommy ta dawo?’
Da fara’a ya sa mata
‘Eh, ki je Rukayya.’
Zumbur ta daka tsalle ta mike, kafin yace wani abu tayi kasa da gudu.
Ya jijjiga kai yana murmushi; Rukayya tana son Aisha kuma Aisha tana son Rukayya
sai dai yana sane da yanda Zahra ta hana wannan alakar kulluwa.
Tunda Zahra ta tafi airport yake tunani ko yace Aishan ta dawo nan gidan don
watakila nata gidan ne yake warin sai dai idan ya tuna da fitnar Zahra sai ya fasa,
haka yayi ta tunani ba tare da ya samo mafita ba . Daga baya bacci ya kwashe shi a
kan kujerar.
Ita kuwa Rukayya tana saukowa ta gayawa Anti Rahma Abba yace taje don zata dinga
taya Anti Aisha kwana. Nan take kuwa ta hada kayanta ta fice daga gidan.
Duk yanda Rahma ta so Yusra ta sa hannu wajen hidimar gidan nan ta ki, ta fahimci
Zahra ce kawai take saka Yusra abu tayi don haka ta kyaleta. Ita da Jummai suke duk
aiki. Don haka a dole ta nemi Jummai da ta dinga bari bayan isha’i ta dinga tafiya.
Sai wajen goman na dare a lokacin Nigeria sannan Zahra ta sami layi ta kirawo
mutanen gida.
Bayan sun gaisa da Abba ta sanar da shi abinda ake ciki ta nemi ya bata yaran. Nan
take ya kirawo Yusra ya mika mata wayar yana fadin
Sai da Mommy ta gaisa da kowa har Rahama, har Sumayya ma saida tayi ta surutunta a
waya, da suka gama Yusra ta karbi wayar. Tana karba Mommy tace
Tace
‘Hmm! Mommy ai kina tafiya yace ta hada kayanta ta koma gidan matarsa.’
Take jikinta yayi matukar sanyi. Tsoronta daya kada yaje kafin ta dawo ya koma zuwa
gidan Aisha. Ta tuna da alkawarin da Yaron Malam yayi mata; to amma gashi tana
tafiya har ya tura Rukayya, lallai idan bata yi da gaske ba idan ta dawo sai an
sake mata aiki a kan Abba.
Shirun yayi yawa don haka Yusra tace
………..
Tunda Yusra ta gaya mata Rukayya ta koma gidan Aisha ta kasa sukuni, duka wani buri
da ta ciwo a kan zata zo tayi ta tuba tana ibada a nan ta watsar . Hankalinta gaba
daya ya taho gida; ita da yaron Malam yace mata ko shekara nawa zatayi a Saudi Abba
ba zai nemi Aisha ba gashi har ya fara shinshine-shinshine?
Tun a wannan lokacin ta fara Allah-Allah ta gama Umrar ta koma gida, haka dai ta
kasa natsuwa tayi ibada yanda ya kamata.
Ta sanarwa Yusrar ta sa mata ido da zarar ta ga wani canji a wajen Abban idan ta
bugo ta sanar da ita. Kasancewar ta san ta bar Yusran a gidan ya sa ta dan sami
natsuwa don ta san duk abinda ya faru a gidan sai ta gaya mata kuma tana dawowa
zata dauki matakin da ya dace.
---------
Lokacin Sahur ne, kowa ya sauko ya ci abincinsa amma har an kusa ayi assalatu bata
ga Sadik ya shigo daukar nasa abincin ba kamar yanda ya saba. Don haka ta zuba masa
abincin ta bude kofar gidan ta fito a wannan daren ta nufi boys quarters din.
Da akwai wuta don haka bata bukatar fitila, ta zagaya ta hau barandar boys quarters
din a hankali, kofar dakin a bude take kuma da alama basu ji motsin shigowarta ba
sai da ta karasa har bakin kofa.
Sadik din yana tsaye a gaban irin teburin robar nan, kwalbar magani ce a hannunsa
wadda yake juyewa a cikin robar lemon coke babbar, kusa da robar kuma kwayoyin
magani ne kanana guda hudu a kan takarda. Kafin ta karasa sallamar da ta fara yayi
sauri ya dure maganin ya ajiye kwalbar ya gyara tsayuwarsa ya kare abinda yakeyi.
Abokinsa wanda yake kuryar dakin wanda bai hango me yake faruwa ba yace
‘Kana da matsala, kayi sauri ka hada mana kayan nan don wallahi ni ko an yi
assalatu sai na sha don ba zan iya kai azumin ba idan ban chake ba wallahi.’
Saida ta karasa shigowa dakin sannan abokin nasa ya gane dalilin daga masa hannun
da Sadik din yake faman yi. Ta ajiye flask din a gefen Sadik din tana fadin
‘Abincin Sahur ne ba kazo ka karba ba Sadiku shi yasa na kawo maka ka na ga an kusa
assalatu.’
Har tayi kamar zata tafi tayi wuf ta shammaceshi ta dauke robar coke din, da
kwalabar maganin da kwayoyin da bai riga ya dura a robar ba; ta fice daga dakin
tana fadin
‘Wallahi shaye-shaye kakeyi Saddiku sai na nunawa Abbanka, har Mommy ma sai na nuna
mata.’
Tana fita shi da abokin nasa sukayi tsuru-tsuru; nan da nan dabara ta fadowa
Sadikun. Ya sallami abokin nasa ya sa maigadi ya bude masa gate ya fice. Ya koma
dakin ya dauki abincin ya juya kamar yaci sannan ya koma ya kwanta. Ya dauki waya
ya kirawo Mommy, tana dauka yace
‘Mommy kinga Anti Rahma ko, haka kawai ban san me ya kawota dakina ba yanzun nan
tana shigowa ta ga robobi a kan tebur tace wai Ina shaye-shaye. Kuma wallahi Mommy
ba nawa bane Balele ne ya manta su da yake a nan ya Sha ruwa don ni ban ma san
menene ba tunda a robar coke ne. Na gaya mata ba nawa bane amma ta tafi da su wai
sai ta gayawa Abba ina shaye-shaye.’
‘Subhanallah! Bana son karya Saddiku, idan kana shan wani abu ka gaya min idan ma
baka sha ka gaya min.’
‘Wallahi Mommy kema kin san babu abinda nake sha haka kawai dai take son yin min
sharri. Kuma ina jin Jummai ce ta saka ta don itace me cewa ta ga murfin magani a
bq din.’
‘Tabbasa biri yayi kama da mutum! Bari na kirawo Abban naka, su kuma duk zasu ji
daga gareni. Na rasa me yasa suke nemana da sharri musamman ma Jummai.’
Motsin Abban ya jiyo ya taho dakin a fusace yayi sauri ya katse wayar ya kifeta, ya
juya kamar yana bacci.
‘Sadik.’
A tsaye Sadik din yake a kan katifarsa ya jingina da bango da alamar razana a
fuskarsa.
‘Na’am.’
Ya amsa a firgice.
Ya karewa dakin kallo sannan yace
Ya zaro ido
‘Shaye-shaye Abba? Ai babu kowa ni kadai nake kwana, jiya ne ma da aka sha ruwa
abokaina suka zo su uku kuma da muka tafi asham daga can suka wuce ni kadai nake
kwana.’
‘Ai kuwa sai dai in yanzu yaron nan ya fita don yana nan har maganar da yake fada
naji.’
‘Wallahi Abba ni ban san wa ta gani ba kuma ni kadai na kwana a dakin nan kuma ka
gani.’
Ya mariraice
‘Ba nawa bane Abba. Balele ne ya sha ruwa a nan jiya shine ya mantasu, wallahi ban
san ma menene ba kuma ba nawa bane shi yasa ban dauke ba.’
‘Sadik, Sadiku ka bi a hankali. Zan bincika idan na kamaka da wani laifi tamu ce ni
da kai. Shi kuma Balelen zai zo ya sameni, gobe zai bar min gidana. Daman na san
yaron nan yana shaye-shaye sai anyi magana Mommy tace ba haka bane, gobe zai bar
min gidana.’
Ba tare da yayi magana ba ya fice daga dakin.
Rahama ta kalli Sadiku suka hada ido yayi mata wata gajeriyar dariya ya fada kan
katifarsa ya kwanta yana dariya.
‘Kada ki damu zan bincika, yaran nan sun iya karya da dabara a kan abinda suke so,
zan yi maganinsu. Gobe Malam Sule zai dawo ya karbi aiki, Balele ba zai sake shigo
min gida ba.’
Jijjiga kai kawai tayi ta shige kichin; duk da Balele yana kama da ‘yan shaye-shaye
ta san wannan ba kayansa bane za dai a koreshi ne ba da hakkinsa ba. Har yanzu tana
mamakin Sadiku, lallai yaraon yau sai a barshi.
An riga na gama assalatu har an tayar da sallar asuba, don haka ta wuce dakin baki
inda a nan take kwana tare da Sumayya da Ummi. Tayi alwala ta tayar da Sallah.
Bayan ta idar da sallah ta gama azkar dinta ta dauki wayarta don taga lokaci, tana
dubawa taga ashe Zahra ta kirawota wajen sai biyar. Tana da dan credit dinta don
haka ta dannawa Zahran flashing. Jimawa kadan ta kirawo, bayan sun gaisa tace
‘Sadik yace min kin dauki abinda ba shi ya ajiye a dakinsa ba kin kaiwa Abbansa.’
‘Eh, dama rashin fahimta me amma ai ya yiwa Abban bayani ma shike nan.’
‘To don Allah dai ko menene yaran nan sukayi a yi hakuri a jira sai na dawo ko a yi
min waya, a daina saurin hadasu da ubansu; ni na baki amanarsu in sunyi wani abu ni
zaki gayawa ba wani ba.’
‘To in Sha Allahu. Babu ma abinda sukeyi muna zaune lafiya ai.’
Sukayi sallama.
Rahma ta bi wayar da kallo; wato warning Zahra take mata a kan kada ta hada Sadik
da Ubansa; lallai! Da ba dan anyi abu cikin girma da arziki da ita ba ma da yau
zata bar gidan nan, amma tabbas idan ta tafi ba zata sake zama a gidan nan ba. Wato
kenan su yaran Zahra ba za suyi laifi; tabbas ita ta san abinda ta gani kuma shima
Sadikun ya sani don haka ma har ya kirawo me kare ma sa ya tsara mata karya da
gaskiya . Um!
___
Kiri-kiri Abba ya kori Balele daga aiki, sai dai ba a bashi dama ya kare kansa ba
domin tabbas shi din ma yana shaye-shayen amma bai taba zuwa da abun maye gidan ba
kuma bai taba zuwa gidan a buge ba. Gashi yana da in-ina don haka ma kafin yace
wani abu aka yanke masa hukunci. Ya mikawa Abban mukullin mota ya fice, a ranar
kuma ya dawo da Malam Sule aiki.
…………..
Bayan an sha ruwa Mommy din ta yiwo waya Yusra ta sanar da ita an dawo da Malam
Sule, a lokacin ta kara shiga damuwa. Kamar dai duk wata tufka da ta taho ta bari
an fara biyota da warwara. Ta zata wani direnban za a dauka amma an dawo da Malam
Sule. Wannan ya kara kasa mata hankali acan Saudiya din.
__
Duk wani shirye-shiryen bikin Sallah an kammala don a yanzu saura kwana uku Sallah.
Makocin gidan Zahra wanda gidansa yake kallon gidan shine commissioner of
Environment na Jihar Kano wato Alhaji Mamman Ahmad Yakasai.
Tun kafin a fara azumi gwamnatin Jiha take gangamin dashen bishiyoyi, ko ina an
shuka. A yau commissioner ya ciko motar Hilux guda biyu da bishiyoyi don mutan
unguwar su samu su shuka a unguwa da kuma gidajensu.
Bishiyun sun hada da na goba, gwanda, umbrella sai kuma bishiyar malmo da kuma ta
madaci.
Gidan commissioner akwai masallacin a jiki wanda yawancin mutanen kan layin a nan
suke khamsi salawati. Kuma da yake commissioner mutum ne mai son mutane da alkhairi
in dai yana nan wajen baya rabuwa da mutane.
Nan kofar masallaci commissioner ya sa aka sauke bishiyun ga kuma matasa su kamar
shida wadanda zasu shuka bishiyun.
Abba yana cikin mutane da suka fito daga masallacin daga karshe tare da liman, suna
fita suka tsaya da commissioner da mutanen unguwa ana gaggaisawa.
‘Malam liman gasu fa, kaga goba da fruit kowa ya dauka a shukawa yara a cikin gidan
don kaga gobar nan mai dadi ce kuma ‘yayanta manya ne sosai. Wadannan kuma da basa
‘yaya duk a shuka mana su a unguwa.’
‘Education! Teacher uban karatu. Ga goba nan a shukawa amarya don ina hango gidanta
ko ganye babu.’
‘Kaina bisa wuyana kar kasa a mayar dani kauye, Uwargida ma a shuka mata goba harda
fruit duk a hada.’
Nan liman ya sa hannu aka rarraba bishiyun, guda biyar aka warewa Abba goba biyu
fruit biyu da kuma malmo wanda za a shuka a kofar gidan Aisha don gate din gidan
Zahra bishiyar har guda hudu ne a wajen.
Yaran da aka taho dasu don shuka bishiyun suka fara dauka kowanne mai gida yana
nuna musu gidan da zasu je su shuka masa.
Wani yarone matashi ya kwashi na gidan Abba, da hannu Abban ya nuno masa gidan
Aisha yace duka a nan za a shuka domin gidan Zahra akwai bishiyar mangoro da kuma
bishiyar ayaba, ga gwanda wajen bishiya hudu a jikin katanga.
Har ya juya zai wuce gaba ya rakasu sai kuma ya fasa, ya dauki waya ya kirawota.
Bayan sun gaisa yace mata ga yaro nan zai shuka bishiya a cikin gidan ta bude gate.
Suna ajiye waya ya nunawa yaron gidan yace yaje za a bude masa.
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
25
Daidai lokacin da yaron da zai shuka bishiyar ya tsallako tare da abokin aikinsa
dai-dai lokacin ta bude gate din. Suka gaisheta, bayan ta amsa ta ja baya suka wuce
ciki. Har ta kama hanya zata koma ciki yaron wanda ake kira Masta yace
‘Hajiya a dai-dai ina zamu shuka, Alhaji cewa yayi a sa hudu a cikin gida biyu a
waje; naga cikin gidan da dan fili ta wane gefen zamu saka?’
‘Kusa biyu a nan gaba, biyun kuma sai ku saka a bayan gida.’
Har ta juya kuma sai ta sake tsayawa ta juyo ta nuna gefen gidan in an tafi za a
zagaya dai-dai tagar dakin Abban tace
‘Ka shuka daya a nan, yanda idan ta girma zata dinga kare rana don da rana ta fito
take shiga dakin nan ta taga.’
An kusa shan ruwa kuma so suke su gama kafin a sha ruwan don haka nan da nan suka
fara aiki.
Suka shuka bishiyar umbrella guda daya da kuma goba guda daya a gaban gidan. Suka
zagaya bayan gidan suka shuka bishiyar goba guda daya don wajen bashi da sarari
sosai umbrella ba zata sami wajen budewa sosai ba.
Wajen tagar dakin Abba nan ne karshe, sai da Masta ya auna sosai tunda an ce masa
ana so ta dinga kare rana, ya dan bada tazara kadan ya kara kusantar katangar tunda
tagar dama bata da nisa sosai daga katangar. Yana hakawa daya yaron yana kwashe
kasar.
Yana cikin hakawa ya daki roba, daya yaron yace
‘Haba Baabaa, sai dai ko wata robar banza don da da dapipe a wajen nan Hajiya ba
zata ce a shuka bishiyar a wajen ba.’
Ya saka hannu ya ficiko gutsuren robar, gaba daya ta taho amma sai dai ta riga ta
dagargaje. Take suka kunduma ashar saboda wani wari da doyi da ya dumame wajen.
Abinda yake cikin butar yayi tsalle waje daya saboda yanda aka finciko butar.
Baabaa yace
Ya goge hancinsa ya karasa kan abinda ya fita daga cikin butar, ya sa fatanyar
hannunsa ta dungurin abun da yake nade a bakin kyalle yace
‘Bari na dauko ledar da muka cire sauran bishiyun mu nade a ciki kawai mu jefa a
shara.’
‘Ai wallahi sai na bude bakin kyallen naga ko menene wannan, nifa ji nake kamar
warin jaba ne kuma aka hada shi da wani abun da yafi jabar wari.’
Ya wuce ya nufi dauko ledar yana mita
‘Kai wallahi masta ka fiye jangwale-jangwale, daga hako abu sai kace sai ka bude.
Yanzu ba zaka bari muyi mu gama aikin nan kafin a sha ruwan ba sai ka bata mana
lokaci.’
Yana bude bakin kyallen yana toshe hanci kuma yana bawa Baabaa amsa
‘Ai ni na fi so mu sha ruwa a nan, Alhaji sawa zai yi a bamu dankali da kwai harda
shayi, in muka tafi kuwa ka san sai da kyar ma zamu sami kunu da kosan.'
Suka saki baki gaba daya suna kallon ikon Allah, bayan ya gama cire bakin kyallen
abinda yake ciki ya bayyana.
Kan jaba ne wanda gaba dayansa an rubuceshi da hatimi da wasu kalmomi sannan an
tsiyaye idanuwan jabar. Bakin jabar kuma an kawo wani bakin kwado an huda sama da
kasan bakin an datse kwadon, ga kuma wata laya da aka ajiye daga kan goshin jabar
aka kawo allura aka soke layar a jiki.
‘Wallahi wannan abun tsafine, ai wannan ma idan bamu fitar dashi ba gidan nan ba
zai zaunu ba don ciki ma sai dai su fito su fice.’
Take Masta ya mayar da kan cikin bakin kyallen ya dauka ya nufo gate, Baabaa ya
rufo masa baya.
Suna fitowa ya nufi kwalbatin da yake kofar gidan zai jefe, sai Baabaa ya dafa
kafadarsa yace
‘Shikenan asirinsa ya tonu don kaga ina jin wancan mutumin limami ne kuma da alama
da iliminsa.’
Ya fada yana nuna Abba wanda yanzu su uku suka rage a kofar gidan commissioner; shi
da liman da kuma commissioner.
Masta yace
‘Kuma ka san yanzu mutane har makota suke yiwa asiri ba, rike min nan na tsallaka
na kirawosu su su gani.’
Ya mikawa Masta bakin kyallen ya karba yana tofar da yawu, shi kuma ya tsallaka.
Commissioner yace
Suka tsallako Abban yana addu’ar Allah ya sa a kofar gidan ne don baya so ya shiga
gidan a gaban commissioner da liman don ba zai iya tsayawa a gidan ya dade ba.
Tun kafin su karasa tsallakowa gaba dayansu suka ji wari, haka suka daure suka
karasa.
Commissioner yace
Masta yace
‘Yallabai ai abun da muka hako ne garin shuka bishiyar, shine nace gara dai shi
Alhaji ya duba kafin mu yar.’
Liman yace
‘Wannan ma ai baza a yar ba sai dai ko a binne din don idan an yar ma haka zai yi
ta damun mutane da wari; kana azumi wannan warin ai sai ya bugar da kai.’
Suna karasawa bakin gate din Abba ya dafe kai, ya dan tsaya kafin su kai kusa da
Baabaa wanda yake rike da abun. Commissioner da yake kusa da shi yace
‘Alhaji Yusufa yaya dai, naga fa kamar tsayuwar tana neman gagararka?’
‘Malam liman duba su binne wannan abun kawai, bari mu sami wajen zama kada Alhaji
Yusuf ya fadi fa ka san akwai kishin ruwa.’
Ya karasa shi da Abba, suka sami waje suka zauna a kan kwalbatin da yake gidan kusa
da gidan Aishan. Shi dai Abban ya zauna ne kawai don baya son ace matsalar daga
gidansa ce kuma ya tafi ya barsu, amma har nan inda ya zauna yana jin warin kuma
kansa juyawa kawai yakeyi.
Su Abba suna barin wajen Baabaa ya tsuguna ya budewa liman abinda yake cikin bakin
yadin. Ya tsuguna yana dubawa bayan ya toshe hancinsa.
‘Subhanallah.’
Ya saka tsinke ya gama jujjuya kan jabar ya kare masa kallo tas, ya sa waya ya
dauki hoton abun sannan ya fara karanta addu’oi yana tofawa abun. Ya tofa kul
a’uzai, kulhuwallahu, ayatul kirsiyyi sannan ya tofa la haula.
Yana cikin tofawa da yake zuwa lokacin kan ya dan yiwa Abba sauki commissioner ya
taso ya zo ya sami Malam liman, ya tsuguna a kusa da shi da hancinsa a rike da
hannunsa yana kallon ikon Allah. Bayan liman ya gama tofin commissioner yace
‘Alhaji wannan da ka gani tsafi ne, ka ga wannan bakin kwadon da wannan allurar da
aka soka a goshin kan nan Allah ne kadai ya san fitnar da suke haddasawa wanda
akayi wannan ta’asar domin a cuce shi.’
‘Eh wallahi, don ma mun dan haka ramin bishiyar da zurfi ne da ba zamu sameshi ba
don an binneshi da zurfi.’
‘Balle min kwadon nan ka zare wannan allurar, yanzu sai a kunna wuta a kona shi.
Shikenan ba zai sake tasiri ba da izinin Allah.’
Nan ya fara cukucukun balle kwadon yayinda Abba ya dubi Baabaa yace
Kafin ya kawo ashanar Masta ya balle kwadon ya zare allurar, nan take liman ya
matsa gefe daya ya hada ‘yan karare ya jefe abun ya kunna wuta. Suka dan matsa gefe
shi da commissioner suna kallon abun yana ci da wuta, yayinda ya umarci su Masta da
su shiga su shuka bishiyar amma su dan matsar da ita kadan daga inda suka cire
abun.
Suna nan tsaye abun yana ci da wuta Abba ya dan ji ciwon kan ya sauka har ya fara
samun nutsuwa, don haka ya taso ya zo ya samesu.
‘Malam liman me ya faru ne, menene yake wannan azabar warin don Allah.’
‘Ikon Allah, to meye wannan din Malam Liman? Kuma a cikin gidan suka samo shi?’
‘Eh, a ciki suka samo shi mana. Amma gashi an koneshi, kaji warin ma ai ya ragu
sosai kuma da zarar ya gama konewa zai bi iska shikenan. Idan muka hadu a masallaci
bayan tarawih in sha Allahu zaka ji bayani; don ka ga yanzu zan karasa gida ne
kafin na sake fitowa masallaci.’
Kafin Abban ya bar wajen su Masta suka fito suka ce masa sun gama. Ya tambayesu ko
a nan zasu sha ruwa suka amsa da eh, don haka yace maigadinsa zai miko musu abinci
gidan commissioner din su kara.
Har zai shiga gidan kuma sai ya fasa ya kama hanyar gidan Zahra. Wannan warin da ya
shaka yau ya kusa sumar da shi gashi azumin yau ya wahalar da shi, baya son ya
shiga gidan ya shan wahala.
…………
‘Wai meye wannan din Malam liman, nifa ban gane ba?’
‘Ai kwarai kuwa. Kaga wannan kwadon da yake bakin abun nan to duk wanda aka yiwa
wannan tsafin ba zai iya bawa wani labarin abubuwan da yake ji yake gani ba balle
ma a taimaka masa da wani abu na magani. Wannan allurar kuwa da aka caka ina
tabbatar maka itace musabbabin wannan ciwon kan da yayi da yaji wari. Yallabai ka
kalli fuskarshi kuwa lokacin da ya shaqi warin nan? Baki fa fuskarshi tayi, don ni
gani nayi ma kamar shirin zurawa da gudu yakeyi sai naga ka dafe shi.'
‘Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun! Malam Liman kaji wata fitna, kai da iyalinka a
shiga tsakaninki.’
Sukayi shiru kowa da abinda yake ransa, jimawa kadan commissioner yace
‘Ai kuwa sai ka san yanda zaka bashi labarin nan don kada yaje ya fara zargin
mutane fa, kaga bamu da wani tabbas. Musamman ita daya matar tasa. Tab! Allah abun
tsoro dan Adam abun tsoro.’
‘Ai in sha Allah ba zan masa bayani sosai ba, tunda kaga ko a danginsa ma ko nata
ita matar wanda ke jin haushinsu zai iya yi, ko kuma manemanta wadanda ya kasa ya
aurota ko ma a kawayenta; komai zai iya faruwa. Shi yasa nace ya bari sai an jima
don kafin nan na tsara abinda zan ce masa.’
Haka kawai yake jin kansa cikin walwala, duk da azumin yayi wahala kuma gashi da
la’asar da ya shaki warin nan ya galabaita; amma yanzu har ji yake kamar ma ya rage
nauyi ko kuma an dauke wani abu mai nauyi da aka dade da dora masa a ka.
Cikin walwala ya sha ruwansa tare da yara, su kansu yaran har suna mamaki. Domin
Yusra ita a tunaninta ma murna yake saboda saura kwana biyar Mommy ta dawo.
Tunda ta tafi yau ne kadai ya sha ruwa a falon kasa. Rahma da Jummai sai daki suka
wuce bayan sun ajiye musu abincin suka barsu shi da yaransa.
Ana gama shan ruwa Mommy ta kirawo wayarsa kamar yanda ta sabarwa kanta; yana dauka
ya fara yi mata korafin da kusan kullum sai yayi mata shi amma bata fasa ba.
‘Madam. Yanzu fa a nan Saudiya tarawih akeyi kuma yau daren ashirin da bakwai ai ya
kamata ace kin manta damu kina can kina ibada fa, kar a ga daren lailatul kadari
kina waya.’
Tace
‘Toh idan na jiku ai shine zan fi samun natsuwar ibadar ko? Ina masallacin ma
fitowa nayi, da na gaisa da yara zan koma.’
Suka gaisa yana mamakin dalilin da ya sa kullum sai ta kirawosu kuma a dai-dai
wannan lokacin. Ita kuwa dalilinta shine a lokacin ne kawai zata samesu gaba daya a
tare kuma sannan Yusra zata karbi wayar ta shige daki tayi ta yi mata tambayoyi.
Gaba daya yaran sai da ta gaisa da su sannan daga karshe Yusra ta karbi wayar ta
haye sama ta shiga dakinsu sannan suka fara magana da mommy.
Bayan ta gama bawa Mommy labarin abubuwan da suka faru a gidan tace
‘Shima Abban yau na ga sai wani jin dadi yake ko don kin kusa dawowa ne oho.’
‘Wallahi Mommy sai wani jin dadi yake, kinganshi can ma fa a kasa ya sha ruwa sai
hira yake da kowa.’
‘Um, yanzu haka dadi kawai yake ji. Idan kin ga wani abu dai mayi magana gobe.’
Tun da suka gama waya da Yusran kuma sai ta shiga wasi-wasin dalilin da ya sa Abban
yake walwala. Bata alakanta hakan da dawowarta ba ta fi dai tunanin ko yanayinsa ne
haka a ranar, ta dai san ko menene babu Aisha a ciki tunda Yusra ta tabbatar mata
baya shiga gidan Aishan. Haka ta cigaba da ibada tana tunanin abinda ya sa shi
walwalar, don ji take kamar tayi tsuntsuwa taje ta gani.
--------
Wajen karfe tara da kwata bayan an idar da sallar tarawih Abba ya riko hannun Liman
suka fito daga masallaci, suka dan matsa daga cikin mutane. Bayan sun gaisa Abba
yace
‘Wato Alhaji Yusuf wannan abun gaskiya irin suddabarun nan ne, tana iya yiwuwa anyi
ne don a rabaka da ita amaryar kuma tana iya yiwuwa ma mutanen da suka zauna a
gidan kafin ka zo sune suka binne. Amma yanda mukayi masa haka aka konashi to ko ma
wa aka yiwa ba zai sake tasiri ba in sha Allah.’
‘Allah ko Alhaji?’
‘Kasan an dauki lokaci bana iya shiga gidan nan duk yanda zan yi, ikon Allah. To
yanzu wa zai yi min haka? Kai!’
‘Ai ba za a iya cewa ga wanda yayi ba Alhaji, irin wannan abune wanda ake hadawa da
shaidanu. Su kuma shaidanu ka san zantukansu duk karya ne. Kowa ma zai iya yi; ko a
kawayen ita matar gidan idan akwai wadda take jin haushinta zata iya yi ko wani
cikin manemanta wadanda ka kasa. Abun dai sai addu’a, ko a hakan ma za a iya cewa
addu’a ce ta kawo dalilin da yasa aka tono abun yanzu haka da ba za a ganshi ba.’
Ya jijjiga kai
Yana tafe yana tunani kala-kala; wa zai yi masa wannan muguntar. Yanzu dama wannan
wahalar da yake sha idan ya shiga gidan Aisha dama da hannun wani? To waye zai masa
haka? Zahra? Kai ya za ayi Zahra tayi irin wannan aika-aikar? To idan ba ita ba
waye zai yi haka? To ko dai a kawayen Zahran ne kamar yanda ya fada ko kuma
‘yanuwanta wadanda suke jin haushinta?
Har ya je gida bai samo amsar ba, yana kara tambayar kansa abun yana neman ya sa
masa ciwon kai. Ya hakura ya bude gate ya shiga.
Babu kowa a falon kasan duk sun kwanta don haka kai tsaye ya haye sama.
A falo ya zauna ya jefa wayar a kan kujera kusa da shi.
Babu abinda yake so yanzu kamar yaje ya ga Aisha. Ya mike kamar wanda aka tsikara
ya nufi dining table, ya bude kwanukan ya duba. Salad ne da kuma madarar waken suya
a jug wanda Yusra ta ajiye masa. Ya zauna ya ci salad din ya sha madara sannan ya
mike ya shiga daki, mintuna kadan ya fito a shirye ya kulle dakin.
Sai da ya sauko falon kasa sannan ya kirawo Rahama a waya, ta bude dakin baki wanda
yake kasan ta fito.
‘Anti Rahma zan fita ne, a gidan Aisha zan kwana dauki mukulli ki kulle muku wannan
kofar sai da safe zan dawo. Yaran suna bacci ban tashe su ba.’
‘To.’
Karar bude kofarsa ya janyo hankalin Yusra wadda dama bata yi bacci ba.
Yana ficewa ta sauko falon lokacin Rahma ta gama kulle kofa ta juyo zata koma daki.
Tace
‘Um.’
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
26
Tunda Rukayya ta zo suka hadu da Amira sai ta bar musu dakin baki, ita kuma ta koma
tana kwana a dakinta ita kadai.
Tana kwance a kan gadonta Amma ba bacci takeyi ba, ta kashe fitilar dakin sai irin
fitilar nan mara haske ta kan durowar ta bari a kunne. Karatun kur’ani ne yake
tashi kasa-kasa a dakin wanda ta kunna a mp3 dinta take bi tana daga kwance. Kamar
a mafarki ta jiyo motsin bude gate, da sauri ta tashi ta leka ta taga wadda take
kallon gate din. Zuciyarta na dakan uku-uku saboda a tunaninta ko wani ne ya shigo
musu gidan daga ita sai yara.
Sai da ya gama shigowa gaba daya sannan ta gane shi, ta dafe kirji ta mayar da
numfashi. Ta san iyakarsa kofar falo ba iya shigowa zai yi ba, ta tabe baki ta koma
ta kwanta ta cigaba da bin karatunta.
Ta baza kunnuwanta tana sauraro taji fitarsa sai kuma taji motsin bude kofar falo,
yana kunna fitilar falon ta hango haske ta kasan kofar. Mamaki ya cikata, a fili
tace
‘Toh!’
Duk da haka dai sa rai takeyi taji fitarsa, sai kuma taji ya shiga dakinsa wanda a
jikin nata dakin yake. A ranta tace yanzu haka wani abune mai mahimmanci da ake
bukata yanzu ya bari a dakin shine ya daure ya shigo ya dauka.
Tun daga bakin gate yake mamaki yana godewa Allah saboda kwata-kwata babu wani
wari, duk wani nauyi da yake ji a kirjinsa idan ya shigo gidan yau babu. Ya karewa
farfajiyar gidan kallo duk da cewa akwai duhu sai fitila guda daya dake haska
wajen. Ya wuce ya nufi cikin gida.
Yana shiga falon kamshin turarenta ya doki hancinsa, tabbas yayi kewar kamshin nan
da kuma mai kamshin.
Kai tsaye dakinsa ya wuce domin a tunaninsa a nan zai sameta sai dai ga mamakinsa
bata ciki. Ba tare da bata lokaci ba ya fito ya nufi dakinta, tun daga bakin kofa
ya jiyo sauti don haka ya tabbatar tana ciki. Yayi zaton waya takeyi don haka ya
murda hannun kofar ya shiga a hankali, sai da ya bude kofar sannan ya fahimci
sautin karatun kur’ani yake jiyowa.
Ya hangota a kwance a kan gado; ji yayi kamar zuciyarsa zata fito daga kirjinsa ta
riga jikinsa isa inda take kwance.
Kafin ya karasa ta tashi zaune, ta kunna fitilar wayarta don ta tabbatar shine.
Yayi zaton bacci takeyi, amma da yaga ta kunna fitilar wayar sai ya dan ja baya ya
kunna fitilar dakin.
Ta bishi da kallo mai cike da tambayoyi, shima kallonta yake yana murmushi a
lokacin da yake karasawa inda take. Ta dan muskuta kadan ya zauna a gefen kafafunta
da suke mike a kan gadon.
Ya cigaba da binta da kallo har ta dauke idonta tana kokarin tare kwallar da ta
taso mata, ya dan matsa kadan ya kama hannunta. Ya kirawo sunanta kamar daga can
kasan makogoronsa
‘Aisha.’
‘Um.’
Ya dan kara matsawa kusa da ita, so yake ya rungumeta amma ta ki motsawa. Ya kamo
daya hannun nata ya rike, yayi shiru na dan lokaci yana tunanin ta inda zai fara.
Kusan wata shida kenan rabonshi da ita, fuskarta kawai da yake kallo yanzu ya
tabbatar masa da cewa ya saka ta a cikin damuwa ga kuma wata rama da yaga tayi;
domin rigar bacci ce a jikinta mai hannun shimi don haka yana kallon wuyanta.
Yace
‘Aisha kiyi hakuri, na san mun sha wahala amma Alhamdulillah yanzu komai ya wuce.
Na sami maganin abinda yake hanani shigowa gidan nan, in sha Allah Allah ba zai
bari a wani abu ya sake shiga tsakaninmu ba.’
Ta zare daya hannun nata ta sauko daga kan gadon, kafin yace wani abu ta fice daga
dakin.
Tana fita daga dakin hawayen da take rikewa ya kwace, fita hawaye yake daga idonta
tana sharewa har ta karasa dakin baki inda Rukayya da Amira suke bacci.
Ba so take ta tashesu daga bacci ba don haka cikin sanda ta karasa kan kafet din
dake tsakar dakin, ta mika hannu ta dauko filo wanda ga dukkan alamu na Amira ne ta
jefo shi kasa garin bacci. Ta gyara filon ta ajiye a kan kafet din ta kwanta.
Hawayen da yake bin idonta ya cigaba da zarya babu kakkautawa; sai yanzu ya tuna da
ita? Wata kusan shida? Ko jiya da za ayi shuka ta san warin da yace yana ji ne baya
so ya ji shi yasa bai shigo ba ya kirawota. Me zai ce mata yanzun? Nan da ya shigo
mata daki so yake ta rungumeshi shikenan ko me? To idan fa ma yanzu ta saki jiki da
shi matarshi ta dawo ya koma wajenta ya kyaleta fa?
Zuciyarta ta fara harbawa da sauri yayinda hawayenta ya kara yawa; tabbas tana iya
yiwuwa don matarsa bata nan ne don ta san tabbas ko ma menene ya shiga tsakaninsa
itace. Idan kuwa hakane akwai yiwuwar ya zo ya hilaceta ta saki jiki da shi ana
sallacewa matarsa ta dawo ya koma wajenta yace idan ya shigo nan din yana jin wari.
Gaskiya a yanzu ba zata iya sakar masa kanta ba, gara ma kawai ita kada ya takura
mata, ko kuma a kalla ya jira matarsa ta dawo sai a cigaba da rabon kwana. A
lokacin sai ta san ba rashin matarsa ne ya kawo shi inda take ba.
………..
Yana nan zaune yana jiran Aisha har wajen minti talatin suka shude, mamaki ya
cikashi. To me take yi a dakin su Rukayyan? Ya taso ya fito daga dakin ya shiga
nashi dakin bata nan, ya duba kofar falon yaga babu alamar an budeta. Wannan ya
tabbatar masa da cewa dakin yaran ta shiga kenan. To me takeyi har yanzu bata fito
ba?
Ya dawo falo ya kunna fitila ya zauna yana tunani; to ko dai Aisha fushi tayi
dashi? Baya jin zatayi fushi tunda ai ta san ba yin kansa bane.
Ya tashi ya zo kofar dakin su Rukayyan ya tsaya ya kasa kunne ko zai ji motsinsu
Bai ji komai ba, to ko dai Aisha fushi tayi da shi?
Ya Kuma kan kujera ya zauna; baya son shiga dakin yaran da wannan daren tunda su
din mata ne kuma gashi harda Amira a ciki.
Haka ya gaji da zama a falon ya tashi ya koma dakin Aishan ya kwanta; sai dai da
yake zuciyarsa bata da nutsuwa haka ya kasa bacci yana ta juyi.
……..
Karfe uku na dare da minti arba’in da biyar agogon dakin mai alarm ya fara
kararrawa, a gefen Rukayya yake don haka cikin magagin bacci ta mika hannu ta
katseshi.
A take Aisha ta tashi tunda dama ba bacci takeyi ba, ta fada bandaki ta wanko fuska
ta dauro alwala sannan ta fito ta tashi yaran. Da akwai kayanta a dakin don haka ta
dauki zaninta ta daura a kan kayan baccin. Saida tayi musu bayanin cewa Abban
Rukayya yana nan don su san irin shigar da zasuyi kada su fito yanda suka saba da
kayan bacci.
Tayi tsammanin yana falon don bata jin ya fita daga gidan, amma sai taga babu kowa,
don haka kai tsaye ta fada kichin. Ta dora indomie da kuma ruwan shayi sannan ta
tsaya yanka albasa.
A nan su Amira suka fito suka sameta, suka tayata har indomie din ta dahu sannan ta
zuba nata ita da yaran a tray Amira ta dauka ta kai musu kan kafet din falo. Shi
kuma Abba ta zuba masa nashi a plate ta hada masa shayi ta dora a kan dining table.
Rukayyace ta hado musu shayi gaba daya ta ajiye sannan ta dauko musu ruwan sha ta
ajiye.
Aisha ta duba agogo taga karfe hudu da kwata don haka tace da su Rukayya su fara
cin abincin kafin ta taso Abban.
‘Nayi serving abincin sahur, gara ka fito kaci don an kusa assalatu.’
‘Aisha.’
Ta kalleshi suka hada ido alamar tana sauraronsa, ya cigaba yana mika mata hannunsa
‘Zo nan.’
‘Zamu makara fa, saura bai fi minti ashirin ba ayi assalatu gara ka fito kawai muci
abinci.’
Kafin yace wani abu ta juya ta fice.
Ya dauki wayarsa ya duba lokaci, tabbas idan bai yi da gaske ba zai makara. Nan da
nan ya kintsa ya fito falon. Tana zaune tare da su Rukayya suna cin abinci; suka
hada baki suka gaisheshi bayan ya amsa ya wuce dining table ya zauna ya fara cin
abincinsa.
Yana ci yana jiyo Aisha tana ta hira da yara suna dariya; tabbas ya san fushi
takeyi da shi.
Ya san yana da aiki domin Aisha sarauniya ce, dole ya lallabata su shirya.
Kafin ya gama sahur sun gama ita da yaran, ta shiga dakinta ta dauko wayarta da
kayan sawarta. Yana nan zaune ta wuceshi ta koma dakin yaran.
Tana shiga ita da yaran suka fara Sallah. Dama haka suke da sun gama sahur ragowar
lokacin sai suyita ibadarsu har asuba tayi.
Haka ya gama cin abincinsa ya koma daki, da aka yi assalatu ya shirya ya wuce
masallaci.
__
Tunda Rahma ta tabbatarwa Yusra cewa Abbansu ya tafi wajen amarya ta kasa nutsuwa,
so take ta gayawa Mommy amma kuma bata da waya. Dama wayar Abban suke kiranta da
ita kuma ya fita da kayarsa, shi kuma Saddiku yana bq balle ta ari tashi, ba ta so
ta ari ta Rahma don kada ta zargi wani abun. Haka ta hakura ta kwanta da shawarar
idan sun tashi sahur sai ta ari wayar Rahma ta kirawo Mommy din, tunda ko flashing
tayi mata ta san zata kirawo.
Wajen karfe uku na dare suka tashi sahur, Yusra da Nana suka daga dakinsu. A nan
falo Nana ta zauna yayinda Yusra ta wuce kichin inda ta jiyo motsin Rahma.
‘Anti Rahma don Allah ki bani aron wayarki na yiwa Mommy message.’
‘Tana daki ki dauka, amma don Allah ki shiga dakin a hankali kada ki tayarin da
Sumayya.’
Tana daukan wayar ta haye sama ta shige dakinsu, credit din wayar ta fara dubawa
taga naira dari da ashirin. Ta san ba zai isheta waya ba amma ta san zai isa ta
cewa Mommy din ta kirawota.
Nan da nan ta dannan lambar Mommy ta Saudiya, ringing daya Mommy ta dauko kafin
tayi magana Yusra tace
Saida gabanta ya fadi, jikinta har rawa yakeyi lokacin da take kokarin kiran lambar
Rahman. To me ya faru Yusra take nemanta a wannan lokacin? Allah ya sa dai ba wani
abun ne ya faru da gidan ba.
Muryar Yusra ce ta katse mata tunaninta, ta amsa gaisuwar Yusran sannan tace
‘Mommy kin san jiya tun wajen sha daya na dare Abba ya fita, wai ya tafi gidan
matarsa kuma a chan zai kwana.’
‘Kwana Yusra?’
‘Wallahi Mommy, har yanzu ma yana can don bai dawo nan ba.’
‘Um, ba zama ta barshi ya dinga kwana inda kuke ba tunda ba na nan, shine ta janye
shi ta barku ku kadai? Ai shike nan.’
‘Babu komai, ki cigaba da kular min da gidan kiga zuwa lokacin da zai dawo. Duk
wani abu da yayi zuwa na dawo ki kular min. Zan kirawo ki da safe.’
Duk da Rahma bata san menene dalilin da ya sa Yusran ta kirawo Mommy ba amma ta
zargi cewa zata gaya mata ne yau Abbansu ba a nan ya kwana ba; domin tana sane da
yanda duk wani motsi da akayi a gidan Yusra sai ta sanar da uwarta.
…
Sallah takeyi a lokacin da ta sallame ta amsa kiran Yusra, sai dai zuwa lokacin da
suka gama waya da Yusran ta ma manta me takeyi. Abinda Yusran ta gaya mata ya
girgizata sosai.
Ya za ayi ace Abban ya tafi kwana gidan Aisha? Ita da a gaban idonta ta ga cewa ya
kasa shiga gidan. Kuma yaron Malam ya tabbatar mata muddin wannan abun da ya bata
yana binne a gidan Aishan to Abban ba zai taba iya shiga gidan ba, to yanzu me ya
faru? Zuciyarta ta kara harbawa da sauri a daidai lokacin da tayi tunanin watakila
fa Aishan ta saka an hake abun nan; lallai yarinyar nan hatsabibiya ce kamar yanda
yaron Malam ya fada. Yanzu kenan Abban yana can wajen Aishan ya bar mata yaran yana
jin dadi; anya kuwa Aisha ba so take ta raba Abba da iyalansa ba? Ai kuwa doke ta
dauki duk wani mataki da ya dace don ba zata zauna wata banza tazo ta rabata da
mijinta uban ‘yayanta ba.
Ta dauki wayarta ta fara laluben lambar yaron Malam, sai dai ta tuna a babbar
wayarta kawai take da lambarsa wadda kuma a gida ta barta ta taho da karamar duk
saboda kada tazo da babbar wayar ta hanata ibada yanda ya kamata.
‘Hajiya Zahra ya dai, lafiya dai yaran suke ko? Naga kina gama waya da Yusran kin
shiga damuwa.’
‘To ki barwa Allah, ai idan kana nan baka da matsala sai kawai kiyi ta roka kafin
kije gidan komai ya daidaita.’
‘Umm.’
A nan Falmata ta barta ta wuce bandaki don tayo alwala ta wuce masallaci inda
ragowar ‘yan dakin nasu a can suka kwana suna ibada.
__
Bayan ya dawo daga sallar asuba ya jiyo motsinsu ita da yara a kicin, bai leka ba
ya wuce dakinsa ya kwanta. Bacci ne me nauyi ya kwasheshi saboda yanda ya kwana ba
tare da yayi bacci ba.
Kafin karfe bakwai sun gama gyara gidan sun shirya tsaf ita da su Amira.
Bata ji motsinsa ba don haka ta san bacci yakeyi, ta dauki wayarta ta shiga kicin
ta kirawo shi. Bugu daya ya dauki wayar, tana jin muryarsa ta san bacci yakeyi,
tace
‘Sorry, na tasheka. Zamu je kitso ni da yara kada ka tashi kaga bama nan.’
‘Oh, to ku dan jirani ina zuwa.’
‘Ka san na Sallah ne akwai layi, yanzu ma kada kayi mamaki mu sami wasu a wajen.
Kuma sai an wanke kan an yi kitso sannan ayi kunshi, idan bamu tafi yanzu ba a can
zamu sha ruwa.’
Tayi masa sallama ta wuce suka kama hanya yayinda shi kuma ya koma ya cigaba da
baccinsa.
Kafin su isa wajen kitson sako ya shigo wayarta, tana dubawa taga shine ya turo
mata naira dubu ashirin kudin kitsonsu ita da yaran.
Bai fi mutum biyu suka samu a wajen ba don haka nan da nan suka fara tunda sun riga
sunyi booking. A da tace ba zata yi gyaran jiki ba sai bayan Sallah amma tunda taga
ya turo kudi har dubu ashirin haka ta sa saida aka yi mata gyaran jiki sannan aka
gyara gashin aka dandasa mata kunshi. Suma Rukayya da Amira kowacce an dandasa mata
kunshi da kitso.
Sai wajen karfe hudu saura suka gama, suna fitowa suka biya ta gidan kawarta inda
ta kai musu dinkinsu; leshi ne mai kyau ta siya yadi goma ta kai a dinkawa Amira,
Rukayya da kuma Farha, a nan wajen kawar tata da ta bayar da dinki ta saya musu
kowa jaka da takalmi sannan da mayafi. Bayan sun karba suka wuce gidan Hajiya suka
ajiyewa Farha nata kayan.
Farha taso tayi bori a kan sai ta bi Mama, domin da Rukayyan da Amiran duk ta saba
da su; cikin dabara Aisha ta lallabata a kan jibi ne sallah idan tayi kallon sarki
ta gama Baba Abba zai zo ya kawota wajen Mommy.
Har sun zauna a mota Rukayya tace
‘No, za mu bar wa Hajiya gidan ba hayaniyar Sallah. Bayan Sallah dai zasu zo in Sha
Allah.’
Bayan sallar la’asar suka shiga gidan; Abba yana zaune a falo yana kallon TV tunda
ranar Lahadi ce babu aiki duk da yaje gidan Zahra don ya dubo yaran sai dai bai
dade ba ya dawo nan din ya zauna.
Bayan ya amsa gaisuwar su Amira suka shige dakinsu ita kuma Aisha ta shige nata
dakin. Suna wucewa ya bi bayan Aisha.
Ta riga ta shiga bandakin don haka ya zauna a gefen gado yana jiranta. Bai dade da
zama ba ta fito daga bandakin da alwalarta. Tana fitowa dakin ya mike tsaye
‘Aisha.’
Ta amsa yayinda ta dauki hijabinta ta fara kokarin sakawa.
‘A’a, ni ba fushi nake ba. Amma dai yanzu kaga ban yi la’asar ba gashi kuma an kusa
shan ruwa ban dora komai ba.’
‘Hakane. Nima a nan zan sha ruwa ki ajiye min abinci na.’
‘To.’
Nan da nan ta idar da sallah ta fito suka shiga kicin ita da su Rukayya.
……….
Duk yanda ya zata zai samu ganawa da Aisha abun ya ci tura, idan ta zuba abinci to
sai ta zauna cikin yara ta ci nata. Da daddare kuma idan ya fita sallar tarawih duk
saurinsa kafin ya dawo ta zuba yara a daki sun kwanta har ita.
Tabbas da Rukayya ce ita kadai da tuni yace ta koma gidansu, to amma Amira ma tana
nan. Sun yi bake-bake sun hanashi sakat a gidan ita kuma Aishan taki ta bashi
fuska. Lokutan da yake samunta ita kadai kuma yawanci da yamma na, ya san idan ya
takura sai ya karya musu azumin don haka ya hakura wadannan kwana biyun tsakaninta
da shi sai kallo daga nesa; gaba daya taki sauraronsa.
___
Ranar Talata aka tashi da sallah karama; tun asuba ita da su Rukayya suka fada
kicin, da yake abincin ba mai yawa takeyi ba nan da nan suka hada tuwon shinkafa da
miyar gyada, ga kuma funkaso da farfaesun kaji. Amira ta hada kunun aya suka zuba a
firji.
Karfe takwas saura Abban ya fito a shirye, yayi mata sallama sannan ya wuce gidan
Zahra.
Suma duk sun gama wani shirin Sallah sai tuwo wanda Jummai take karasa kwashewa.
Sadiku kawai ya dauka suka wuce masallacin idi.
Bayan sun dawo daga idi ne kamar yanda aka saba duk shekara ya kirawo Sadiku ya
bashi abincin sallar gidan Aisha ya hada da na gidan Mommy yace Ali direba ya
kaishi tare da Nana da Ummi su kaiwa Hajiya.
A falon Aishan ya zauna ta kawo masa abinci; ta sha kwalliyar sallarta cikin
leshinta me ruwan hoda, tayi kyau matuka sai dai kawai yanda take daure fuska ne
yake gundurar dashi.
Yana zaune a falo yayinda Aishan take kwashe kwanukan da yaci abinci Rukayya da
Amira suka fito daga daki, bayan sun gaisheshi yace
‘Iyye ‘yan man Anti. Bari ni kuma na baku barka da da sallah kada ayi ta yawo jakar
‘yan mata ba ko sisi.’
Ya zaro sabbin kudi 'yan Naira hamsin ya basu kowa dari biyar, sukayi godiya suka
wuce kicin inda suka jiyo motsin Aishan.
‘Um Anti don Allah ki bamu kudin mota muje gidan Anti Hida, itama Rukayyan tana son
zuwa wallahi.’
Ta kyalkyale da dariya
‘Lallai yaran nan, na baku kudin mota ku tafi a motar haya ko? To ba inda zaku je.
In dai cikin gari ne na gaya muku ku shirya gobe sai muje ko kuma ku bari da yamma
ma je tare.’
‘Anti don Allah, wallahi zamu gane ko Rukayya. Kinga Anti idan bamu je da wuri ba
kafin muje duk su Farha sun je kuma Baban Anwar zai kai su cikin gidan sarki banda
mu.’
‘To ke Amira duk shekara ai dake ake zuwa gidan sarkin menene idan yau daya baki je
ba, kya je da Babbar sallah.’
‘Anti da Rukayya nake so na nunawa bata taba shiga gidan sarki ba ita.’
Aishan ce ta amsa
‘Wai gidan Zahida suke son zuwa a motar haya don bazasu jirani muje gobe ba.’
‘A’a gidan Zahida ai ba matsala bane, bari na kirawo Aliko ya kai ku in ya so idan
kuka gama sai kuyi waya na turo shi ya dauko ku.’
Gaba daya suka hada baki suna masa godiya, suka koma dakin da gudu suka fara shiri.
Ta ajiye kwanukan da take kifewa ta nufo kicin din da niyyar fita tana fadin
Tana zuwa zata wuce ya dan matso ya takureta a bakin kofar ya kawo bakinsa kusa da
kunnenta ya rada mata
Ya hura mata iska a kunnen nata har ta dan noke sannan ya wuce inda ya taso ya
dauki wayarsa ya kirawo Aliko; wanda dama yana gidan Mommy.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
27
Takaicinsa ne ya kuleta, tunda take aurensa bai taba cewa ya hanata fita unguwa ba
sai yau. Ta san manufarsa amma bata jin zata iya bashi hadin kai; haka kawai
matarsa ta dawo ya sake mantawa da ita.
Tana nan su Amira suka fito sukayi mata sallama suna ta jin dadi suka fice.
Tana jinsa yana nemanta bayan ya sallami direban. Sai da ya duba kichin da dakinsa
sannan ya shigo dakin nata.
Tana kashingide a gefen gadonta ta jingine kanta jikin gadon; bata amsa sallamar da
yayi ba haka ya karasa inda take.
‘Aisha.’
Ta share hawayen da yake fuskarta tana shesshekar kuka. Da sauri ya karasa ya zauna
a gefenta cikin matsananciyar damuwa.
‘Aisha kukan me kike yi? Don na hanaki fita ne kike kuka? In dai wannan ne idan
nayi sallar la’asar s na kaiki da kaina.’
Ta sake share hawaye ta muskuta ba tare da tace masa komai. Sukayi shiru na dan
lokaci yana tunanin ta inda zai fara.
‘Don Allah ki daina kukan nan Aisha, kin san bana son damuwarki.’
Suka sake yin shiru ba tare da ta motsa ba, ya gaji da sauraron ta tayi magana
batayi ba. Ya dawo gabanta ya tsuguna daga gaban gadon yanda zai dinga ganin
fuskarta. Yace
‘Aisha don Allah kiyi hakuri, ki gaya min me ya saki kukan nan. Idan rashin zuwa
wajenki ne da bana yi wallahi ba yin kaina bane, abun ne yafi karfina. Yanzu kuma
da kika ganni Allah ya kawo karshen abun ne don malamin da ya warware abun ma yana
tunanin aljanu ne ko tsafi, ai sai mu godewa Allah da abun ya tsaya haka ko? Kiyi
hakuri Aisha, kin san ba zan taba gudunki ba.’
‘Aisha, don Allah kiyi hakuri ki daina fushin nan kin san bana son kukan ki kuma
bana son kina fushi da ni. Kiyi hakuri kin ji.’
Ya taso ya dawo kan gadon gefenta, ya kama hannunta, tana nokewa yana jan hannun
yana fadin
‘Bana son kukan nan.’
So yake ta saki jiki ya janyota jikinsa amma ta ki, don haka ya kara dagewa ya
janyota har saida ta dan fado jikinsa. Ya sa hannunsa yana goge mata hawayen, daya
hannun kuma yana janyo kafadarta don ta kara kwantawa a jikinsa.
‘Shikenan, ni dama ba fushi nayi ba. Amma dai ina so ka koma can gidan idan Mommy
din ta dawo sai ka fara rabon kwanan ta kanta sai a cigaba.’
Ya dan muskuta ya kawo bakinsa daidai kunneta sannan yace a can kasan makoshinsa
Ya cigaba da lalube jikinta sako da Loko, tun tana kokarin kwacewa har ta hakura ta
bada kai bori ya hau.
Nan suka balbalce har aka fara kiran sallar la’asar; yana ta tsara mata dadadan
kalamansa na lallashi da ban hakuri.
‘Subhanallah, kin san an fara kiran azahar lokacin da na shigo kuma sai na manta.’
Sai da suka shirya suka yi Sallah sannan ya sanar da ita ta kirawo su Rukayya tace
idan anyi sallar isha’i zai kaita ta su daukosu.
Ya san duk halin da aka shiga dole ‘yanuwanta sun sani don haka zai yi amfani da
wannan damar ya nunawa ‘yan uwanta cewa komai ya dawo dai-dai.
__
Tun washegarin Sallah yara suke shirin taren Mommy, don ya zama saura kwana biyu
kenan ta dawo. Ko ina an share an goge tsaf banda dakinta wanda ta bayar da umarni
kada a bude mata.
Rukayya ta hada kayan hadi zata yiwa Mommy cake, ta so ace ita da Amira ne zasu yi
cake din sai dai tana tsoron ta shiga da Amira gidan Yusra tayi mata wulakanci don
ta san Amiran ma ba zata dauki raini ba musamman tunda kusan sa’ar Yusran ce. Tana
hada kan kayan cake din Yusra tana mata dariya a kan bata iya wani cake ba ta bari
kawai suyi order kada ta bawa Mommy kunya; ita dai ta kafe a kan lallai sai tayi
cake.
Kuma daga karshe da tayi cake din kowa sai da ya yaba.
…………
Wunin ranar Sallah gaba daya tana ta faman kiran Abban yana gaya mata baya tare da
yara, bai gaya mata inda yake ba amma ta san yana gidan Aisha. Ta gaji da wannan
abun takaicin gashi bata taho da wayarta ba balle ta kirawo yaron Malam, don haka
tun safe take faman kiran Amina amma bata dauka ba. Don haka kusan ba a hayyacinta
ta wuni ba. Ya kamata ace taje ta karasa sayayya amma ta kasa zuwa; kudin ma duk da
ta riga ta kashe mafi yawa amma dai tana jin ba zata sake kashe kudi ba don ta san
idan ta dawo tana bukatar kudi sosai; a halin yanzu ma duk tunaninta yana kan yanda
zata sami kudi ne don ta fara tunanin canza malami tunda shi yaron Malam kamar
aikinsa baya nisan zango.
Sai dare ta sami Amina, tayi mata bayanin halin da ake ciki. Suna ajiye waya ta
tura mata lambar yaron Malam.
Kauyen su yaron Malam babu network sosai don haka duk kokarinta na ganin ta sameshi
basu iya magana ba; shi baya jinta kwata-kwata. Daga karshe dai ya gaji ya turo
mata sako cewa suyi magana ta Whatsapp kawai. Kwana biyun nan jinta take kamar a
kan kaya, don haka ba cikin nutsuwa ta karasa su ba.
-------
Ranar Juma’a itace ta kama kwana hudu ga Sallah kuma tayi dai-dai da ranar da Zahra
Uwar Saddiku zata dawo daga kasa mai tsarki.
Tun dare ta kirawo Abban ta sanar da shi jirginsu zai sauka da misalin karfe biyar
na yamma; ta so kwarai ya zo daukanta da kanshi a airport sai dai ya sanar da ita
zai fita bayan la’asar don haka dai Malam Ali ne zai zo.
Tunda Abba ya kirawo Malam Ali direba yazo yayi aikin Sallah Malama Sule ya sami
damar gujewa gidan; cikin dabara ya tsara Abban a kan a bar Malam Ali ya cigaba da
kai yara makaranta yana daukosu. Don haka tun safe Abba ya sanar masa ya zama cikin
shiri jirgin su Mommy ana sa rana saukarsa karfe biyar na yamma.
Lokacin yana yi Sadiku ya shige gaban mota Aliko ya ja suka kama hanyar airport.
………..
Alhaji Salihi Bello abokin Abban ne tun na kuruciya, tun cikin azumi aka yi masa
ministan lafiya. Tun lokacin ya so shirya walima amma bai sami dama ba, sai ranar
hudu ga watan Sallah shine ranar da aka ware domin yin wannan walimar ta taya shi
murna a hotel din Bristol dake Kano.
An gayyaci Abba wannan taro kuma ya gama shiri shi da Aisha zasu je, hakan nema
dalilin da yasa ya ce wa Mommy ba zai je daukota ba don yana so ya biya ta gidan
Hajiya ya kai Aishan tayi mata gaisuwar Sallah sannan kuma su biya gidan Yaya Bello
inda daga can idan sukayi Sallar Magriba sai su wuce wajen taron.
Bata taba shiga cikin abokansa da matansu ba, don a abokansa ma bai fi mutum biyu
ba wadanda ta sani; duk sai sunayensu da take ji. Da farkon aurenta ya kai ta gidan
mutum biyu sai dai tun a lokacin ta fahimci matansu duka kawayen Zahra ne don haka
ta ja jikinta.
Sai da tayi alwala sannan ta tsantsara kwalliyarta cikin farar atamfa mai ratsin
shudi, ta kawo luffaya mai kalar shudi wadda ta sha ado da fulawowi farare da
duwatsu masu kyalli ta nade jikinta da ita.
Kunshin sallarta yana nan radau don haka ya kara fito da yatsunta da ta sakawa zobe
me ruwan tasa sannan ta daura agogonta Fendi. Ta kawo takalminta mai matsakaicin
tudu wanda ake kira wedge ta saka da jakarta Yar karama wadda ta dace da shigar.
Goge fuskarta kawai tayi sannan ta dora jan janbakinta wanda yake karawa labbanta
kyau, ta fito falo ta sameshi inda yake zaune sanye da farar shadda dinkin doguwar
riga da wando da jar dara kamar yanda ya saba.
‘Na gama.’
Ta fada tana daga tsaye a bayan kujera, ya juyo ya dubeta ya mike yana murmushi
yana fadin
‘Allah Amin.’
Ya dubi agogon bangon dake falon yaga karfe biyar harda rabi, yazagayo yana fadin
‘Mu tafi.’
Motarsa tana bakin gate don haka har nan suka fita.
Dai-dai lokacin da suka fito daga gate din suna hirarraki a lokacin Yusra ta fito
daga gidan commissioner tare da yarinyar gidan Rafi’a wadda kawarta ce. Tar ta
hangosu ta kawar da kai; a ranta tace dama shi yasa ya cewa Mommy zai fita ba zai
je daukanta a airport ba. Tabbasa tana dawowa sai ta gaya mata.
Nan da nan gida ya rude yara suka hau sowa da tsalle ana ta oyoyo. A falon kasa ta
zauna duk yaran da Jummai da Rahama suka gaisheta suna mata maraba; tuni Sumayya ta
makale mata. Tana nan zaune a falon ta bawa Yusra da Rukayya mukullin dakinta ta
bude ta share ta canza zanin gado sannan suka haye saman ita da yara.
Bata jima da zama ba akayi kiran sallar Magriba, ta lallaba Sumayya ta zauna a
wajen Yusra taje ta yiwo alwala.
Tana fitowa daga alwala tace yaran duka suje suyi Sallah sai su zo ta basu dabino
da bagaruwa wadanda ta zubo a jakar hannunta.
Nan da nan duka yaran suka ruga da gudu suka fice daga dakin, Yusra ce kawai tayi
saura tana zaune a gefen gadon Mommy. Kafin Mommy tayi magana tace
‘Mommy wai Abba ya gaya miki inda suka tafi shi da matarsa?’
Da mamaki ta dubeta
‘Aisha? Ce min kawai yayi zai fita, ina yace miki sun tafi?’
'Nima bai gaya min ba, kawai dai naga lokacin da suka fita dab da ki dawo. Kinga
kuwa yanda taci gayu kamar wata matar gonna, ina jin ma dai dinner zasu je fa.’
‘Um.’
Sukayi shiru na dan lokaci, daga baya Mommy ta dubi Yusran tace
Wai yaushe Yusuf ya zama munafiki ne? Ba zai ma gaya mata zai fita da Aisha ba sai
yace mata kawai zai fita? Har yanzu bata daina mamakin yanda akayi ya koma wajen
Aisha ba.
Tana nan tsaye ba tare da tayi sallar ba yara suka shigo da murnarsu sunyi tasu
sallar a basu dabino da bagaruwa.
Ta bude jakarta ta bawa kowa nashi sannan ta basu wani a leda tace su kaiwa Rahma
daga nan sai su zauna a can tayi sallah.
Suna fita ta bude wardrobe ta lalubi wayarta wadda ta bari a gida, ta kunna wayar
sannan ta sayi data. Ta kunna data din sannan ta ajiye wayar a kan gadon ta tayar
da Sallah, ta san kafin ta idar da sallah sakonninta sun gama shigowa.
Tana idar da sallar ta mika hannu ta dauko wayar tana daga zaune a kan daddumar,
nan da nan ta bude wayar ta fara duba sakonninta.
Sakon Hajiya Sharifa ne a sama wanda da alama ma yanzu yake shigowa; Sharifa matar
abokin Abba ce wato Alhaji Jibrin Muhammad Minjibir; suna aminci sosai da Mommy,
don ko da zata tafi Umra ma musamman tayi mata waya sukayi sallama.
Tana ganin sakon Sharifa tayi murmushi; yanzu haka har ta sami labarin dawowarta
shine take mata maraba. Ba tare da bata lokaci ba ta danna sakon ya bude:
“Hajiyata ya ibada? Na san dai yanzu kun hado kaya ko ma kuna hanya.”
“Kina jin dadin kasa mai tsarki kin bar maigidan a hannun yara.”
“Ai gamu nan muna kallon soyayya shi da kanwarki, naga ta goge fes da ita.”
Sai hoto ya biyo baya, yana budewa taci karo da hoton Aisha da Abban Sadiku. Bata
san me ya basu dariya ba don dariya suke a hoton sosai, ta kalli laffayan dake
jikin Aishan; wato da yake bata nan shine ya sayowa Aishan wannan dandatsetsen
laffayan. Ita kuwa ko da tayi maganar kayan Sallah cewa yayi banda ita tunda an
kwashe kudi an biya mata Umra, idan taje ta saya a guzurinta.
Shiru babu amsa ga dukkan alamu Hajiya Sharifa ta sauka daga online don haka ta
fita daga sakonnin Sharifan.
Nan da nan ta lalubi lambar Yaron Malam don dama shine abinda take nema, ta budo ta
fara yi mishi sako na murya wato voice note:
“Yaron Malam duk wani aiki ya rushe wallahi, don yanzu haka maganar da nake maka ya
san zan dawo amma ya dauketa suka fice. Sati biyu kawai nayi da ‘yan kwanaki amma
duk wani aiki da kayi min sun lalata shi wallahi. Gaskiya na gaji da zama da
yarinyar nan yaron Malam, ban taba tunanin akwai matar da zata iya kasa min
hankalin miji kamar yanda yarinyar nan takeyi ba. Ya kamata dai a tumbuketa daga
rayuwarmu ni da mijina Malam.”
Kamar daman jira yake tayi magana nan take taga alamar yana kokarin turo da amsa,
don haka ta dan saurara kadan. Nan da nan sakonshi ya shigo shima ta voice note
kamar yanda ta tura masa:
“Hajiya ai na gaya miki yarinyar nan hatsabibiya ce, kuma wasu lokutan bata tabuwa
don haka kinga dole sai mun bi lamarinta a hankali. Idan kika sami lokaci ki shigo
sai kiji cikakken bayanin yanda za ayi. Amma nayi miki alkawarin ko ta karya komai
kwarjinin da na baki in dai kin masa amfani da shi yana nan don ba zata iya karya
wannan ba sai dai idan shi da kansa ne zai karya. Ki kwantar da hankalinki. Sai kin
shigo din.”
Ta dan sami natsuwa bayan ta saurari wannan sakon don ta san ko da akwai wani
dalilin da zai sa Abban yace zai mata wata tijara to ba zai iya ba saboda kwarjinin
yana aiki.
A nan ta kirawo Amina ta sanar da ita dawowarta da kumma halin da ake ciki sannan
daga baya ta kirawo su Yaya Murja da sauran dangi ta sanar da su dawowarta.
……….
Sai wajen goman na dare saura sannan Abban ya shiga gidan, tana jiyoshi ta tashi
daga falon saman ta shige dakinta ta turo kofar. Bata dade da mike kafa a kan gadon
ba ya tura mata kofa ya shiga da sallama; yana dauke da Sumayya yayinda Ummi take
biye da shi tana surutu.
‘Alhamdulillah duk gamu nan lafiya kalau. Ummi tace an bawa kowa dabino da
chocolate nima a bani nawa '.
Suka dan taba hira kadan, tayi kamar bata san daga gidan Aisha yake ba. Daga karshe
tace
‘Ga abinci can a dining table an dora, naga dare yanayi baka ci abinci ba.’
‘Haba Hajiya, daga dawowa sai ki sa mana baki a harkar gida ke da zaki huta. Ai
Rahaman ta san ba a nan zan ci abinci ba, don na ma riga na ci abincin dare na.’
‘Bari naje, ina gidan kanwarki a can zan kwana in ya so gobe sai a fara rabon
kwanan daga nan kafin nan kin dan rage baccin gajiya ko?’
Ya mike ya jefa Sumayya dake kan cinyarsa sama ya cafeta ta kyalkyale da dariya,
shima ya sa dariyar yana fadin
‘Sarkin tsalle-tsalle, muje na mayar dake inda na daukoki Mommy ta huta ko kafin
gobe a kara mana dabino da chocolate.’
Ya dubeta yace
‘Amin.’
Ba tare da ya kalli fuskarta ba ya fice daga dakin ya ja mata kofa, yana saukowa
kasa ya ajiye Sumayya ya cewa Sadiku wanda yake zaune a falon ya tashi ya fita ya
koma dakinsa Rahma ta rufe cikin gidan.
Duk gajiyar da ta kwaso bata samu tayi baccin kirki ba saboda yanda take takaicin
kasancewar Abban a wajen Aisha; kusan sati uku basu ga juna ba amma shi ko dokin
ganinta baya yi, ya tafi wajen amaryarsa saboda ya nuna mata bata isa ba.
------
Ko da gari ya waye ranar asabar ce babu aiki don haka sai wajen karfe goma suka
tashi daga bacci. Nan da nan ta hada musu abincin safe suka ci suka shirya.
Wajen sha daya da rabi yace mata zai je gidan Zahra, take ta dauki mayafin abayar
da take jikinta tana fadin
‘Bari na zo muje sai nayiwa Mommy sannu da zuwa na dawo kada tsaraba ta kare gara
na karbo tawa da wuri.’
Babu yabo babu fallasa ta tarbesu don har ruwa da lemo ta sa aka kawowa Aishan; sai
dai hakan bai hana Aishan ta gane yanda Zahra take kare mata kallo ba kamar
mayunwacin karen da ya ga abinci. Suka gaisa tayi mata Allah ya sanya alkhairi,
jimawa kadan tayi musu sallama; Mommy ta mike da kanta ta debo mata dabino da
bagaruwa ta bata sukayi sallama ta tafi ta bar Abban a nan.
Kafin Abban ya shigo sunyi waya da Amina ta gaya mata idan Abban ya shigo kada ta
wani tada hankali, ta gaya mata ta lallaba shi domin akwai wani malami ta da zata
kaita wajenshi domin shi aikinsa kamar yankan wuka ne. Idan suka je sai yanda taga
dama zata yi da Abban don haka ta bata shawara kada ta daga masa hankali; ta huta
na sati daya in ya so sai ta zo suje. Kawai dai ta sanar da ita ta tanadi kudi
domin su hada aikin biyu; da na yaron Malam da na wannan sabon Malamin domin ayita
ta kare kawai a gama labarin Aisha.
Don haka duk wata fitna da ta tanada zata yi bata yi ba, musamman da ta ga alamar
har yanzu yana shakkarta kamar yanda ta tafi ta barshi.
_
Tunda ta dawo take tunanin inda zata sami kudi, amma duk wata dabara ta kare mata.
Business din ma ya dan durkushe tunda harda kudaden business din ta hada ta tafi
Saudiyya da niyyar zata saro abaya; sai dai bata saro abayar ba kuma ta kashe
kudin.
Tana dan samun a wajen Abban amma da dabara take yaga da dubu ashirin da goma, zata
dauki lokaci bata tara yawan abinda take so ba. Gashi ita ba ma’aikaciya ba balle
ta tara albashinta. Tayi tunanin ko zata sayar da babban saitin gwal dinta amma
gaskiya bata jin zata iya saboda tana sonshi kuma idan ta siyar shine kadararta ta
karshe; don haka wannan ma ba zai yiwu ba. Ta san Suwaiba zata iya bata kudin rance
to amma idan ta bata sai ta gayawa Yaya Murja, don haka ta hakura.
Bayan yayi mata sallama ya tafi wajen Aisha tunda a can zai kwana; Saida ta
tabbatar kowa yayi bacci a gidan sannan ta shiga dakin Abban ta turo kofa. Ta riga
ta san inda yake duk wata ajiya, duk wata takarda da yake ajiye da ita ta san inda
take.
Wani karamin bakin akwati ta dauko daga wardrobe din can saman, ta koma kan gado ta
zauna. Akwatin yana da password amma ta dade da sanin password din ba tare da Abban
ya sani ba.
Nan da nan ta bude akwatin ta fara duba envelope din ciki tana neman takardar, sai
da ta bude kusan guda biyar sannan ta sami takardun da take nema.
Tayi murmushi ta zare takardun daga cikin envelope din ta ajiye a kan gadon da take
zaune. Ta mayar da akwatin ta rufe ta tashi ta taka wardrobe din ta mayar da
akwatin.
Tana shiga dakinta ta zauna a gefen gado tana duba takardun tana yiwa kanta
murmushi; takardun fili ne wanda Abban ya saya da sunan Saddiku. Ya sanar da ita
lokacin da ya saya kuma ya gaya mata filin ba kato bane amma dai ya sayawa Sadikun
ne saboda nan gaba. Sun gama magana da Amina an samo mata wanda zasu sayi filin a
kan kudi sama da miliyan hudu, a hakan ma sunce don ba a kewaye filin bane. Ta gama
lissafin idan ta siyar ta biya malamanta suka yi mata aiki canjin sai ta zuba
abusiness dinta da ya durkushe.
Ta yiwa kanta dariya ta tashi ta adana takardun nan a kasan katifar dakinta, sannan
ta koma ta kwanta.
__
Tunda ta dawo daga Saudiya Saddiku ya hanata motarta, shi yake hawa motar nan
kullum musamman da yake baya wani karatu yana zaman jiran sake jarrabawa; sai dai
kawai ya zo ya tambayeta kudin mai ko kuma idan ya ballo gyara ya zo ta bashi
kudin.
Dole ta hakura da motar Malam Ali Direba da da ta kwace tunda tatan Sadiku ya hana;
sai dai shi Sadikun ya kaita duk inda zata ko Malam Ali ya kaita.
Duk lokacin da Abban yayi magana sai tace wai duk abokan Sadikun wadanda ma
iyayensu basu kai Abban kudi ba an basu mota amma shi ya hana Sadiku; idan kuma ya
bi abokan yace zai bi ‘yan shaye-shaye. Don haka ya hakura ya sa musu ido.
--------
Abokinsu ne Tijjani Tukur wanda suke kira TT yake birthday, don haka ya shirya
party a gidansu da yake unguwar Lodge Road; da yake iyayensa ba sa gari.
Sai wajen karfe tara na dare aka fara fatin, suka hadu maza da mata sukayi ta
sakarci, wadanda suke shaye-shaye a cikinsu ranar kowa kyauta TT ya basu kwaya irin
wadda suke so.
Saddiku ya san Abbansa yana gari don haka yake ta kokarin dawowa gida da wuri, shi
da abokinsa Munir wanda dama a wajen Saddikun zai kwana. Sai wajen goma da rabi na
dare suka samu suka fito daga wajen kuma duk su biyun a buge suke.
Take Sadiku ya fada kujerar direba ya fizgi motar da gudu; babu mutane sosai don
haka suka sami sararin gudun.
Mutum suka hango a tsaye a gefen titi yana haska karamar tochila, Munir ya dubi
Saddiku yace
‘Kuma ba zan tsayaba ba, bari ka ga tsiyar da zan masa dan iska kawai.’
Ya kara taka motar yayi kan mutumin wanda ya zura da gudu, sunata dariya shi da
Munir din yayinda yayi wuf ya fara kokarin mayar da motar kan titi. Babu wanda ya
san yanda akayi sai gani akayi motar ta kwace ta daki fitilar titi ta dawo tsakiyar
titi tayi tsalle sannan ta kife. Gilasan motar suka tawarwatse sannan injin ya
mutu.
Tsirarun mutanen da suke wajen suka karaso da hanzari harda mutumin da suka kusa
kwashewa; nan da nan aka fara kokarin zaro su.
Ihun Munir kawai ake ji domin shi Sadiku tuni ya sume, sai jini da yake fita daga
wasu bangarori na jikinsu.
Kafin wani lokaci Jamai’an road safety sun bayyana, don haka aka kwashesu sai
asibitin Murtala.
Ba a sami wayar Munir ba amma jami’an road safety din sun sami waya guda daya wadda
ta Saddiku ce. Sai da aka shigar da yaran dakin bada taimakon gaggawa wato Accident
and Emergency na asibitin Murtala sannan jami’in da wayar ke hannunsa ya samu ya
bude wayar. Duba jerin sunayen dake cikin jerin lambobi yake har yazo kan lambar da
aka saka Daddy; ba tare da bata lokaci ba ya danna mata kira.
…………
A kwance yake a falo Aisha tana yi masa tausa, wayarsa da take chaji a gefe tayi
kara. Ta mike ta dauko wayar tana fadin
Yana dauka kafin yace wani abu aka yi masa sallama daga daya bangaren da muryar da
ba ta Saddiku ba. Cike da tsananin mamaki ya amsa sallamar inda kai tsaye mai
sallamar yace
‘Ni mahaifinshine.’
‘To Alhaji yaronka yayi hatsarin mota a nan kan tin gidan gwamna, a halin yanzu
muna dakin bayar da taimakon gaggawa na asibitin Murtala da yake cikin birni. Zamu
so ka zo domin kaga halin da yaranka suke ciki domin su biyu ne a motar.’
‘Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun! Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun. Officer
gani nan zuwa yanzu-yanzu in Sha Allah.’
‘Accident yayi, ina jin a motar Mommynshi ne. An dai ce yana Murtala yanzu zan je
na gani.’
Ya wuceta ya nufo falon da sauri, ta sha gabansa a falon yana dab da fita.
‘Tsaya kaji mana. Ka san fa yanzu babu security kada kaje fa trap ne aka yi maka
don ka fito, ka san yanzu babu wuya an yi kidnapping mutum.’
‘To ai da wayar Saddikun aka kirawo ni kinga ko ma wane yana tare da Saddikun
kenan, gara kawai naje dare yana kara yi.’
‘To Amma ka kirawo Mommy ka tambayeta ta duba maka dakin Saddikun ta tabbatar, ka
ga idan yana nan zai iya yiwuwa sace wayar aka yi. Tunda ka ga ka hanashi yawon
dare kuma yanzu fa duba ka gani wajen sha biyu saura, yaushe ya taba kaiwa haka a
waje?’
Ya dan yi tunani kadan, ya koma ya zauna a bayan kujera ya zaro wayarsa daga aljihu
yana fadin
Ya lalubo lambar Zahra ya danna mata kira, cikin yanayi na bacci ta amsa wayar
‘Yallabai.’
Ta dan dauke wayar daga kunnenta ta duba lokaci sannan ta bashi amsa
‘To don Allah ki je ki duba kiyi min confirming zan kira ki nan da minti biyar.’
Ita kuma tana ajiye wayar tana mamaki; har zuwa lokacin da ta kwanta wajen sha daya
dai ta san Saddiku bai dawo ba amma tayi masa waya yace mata yana hanya. To wani
munafukin ne kenan ya gaya masa bai dawo ba zai tashe ta daga bacci da wannan
tsohon daren. Ta saka hijabinta ta sauko ta fito daga cikin gidan, tana fitowa
farfajiyar gidan taga babu motarta don haka ta tabbar bai dawo ba. Ta haska fitila
ta kirawo Malam Sado, nan da nan ya karaso inda take.
Tace
‘Bai dawo ba Hajiya ai yana tafe dai ko da wanne lokaci zaki iya ganinsa.’
‘Don Allah da ya shigo kace nace ya kirawo ni a waya, bana son na kirawoshi yanzu
ya dauka yana tuki ga dare.’
‘Yana dakinsa, bacci ma yake don ta taga na leka ban zagaya ba saboda dare.’
‘To ai shi nake gaya maka, kada kaje trap ne kai ake nema ba Saddiku ba.’
‘Bari dai naje gidan na gani, ko babu komai na ji wanda ya bawa wayar tasa.’
‘Gara naje na gani don zai iya yiwuwa boye min takeyi don kada nayi masa fada da
safe. Idan na sameshi a gidan yanzu zan dawo, ko ma menene zan kirawo ki a waya in
Sha Allah.’
Yana taba gate din gidan Malam Sado ya taso yana haskawa, yana gane wanda yake bude
gate din ya ja baya ya kwashi gaisuwa. Ya karewa tsakar gidan kallo a takaice,
motar Zahra bata wajen da aka saba ajiyeta. Yace
‘Yallabai Sadiku ya fita da ita ai tun kafin magriba, sai dai ma yau yayi dare
sosai amma na san yana tafe da izinin Allah.’
Ko sauraronsa bai yi ba ya nufi kofar shiga gidan a fusace, iya karfinsa ya buga
kofar saida ya buga sannan ya tuna akwai mukullin kofar a hannunsa. Ya saka
mukullin ya bude kofar ya shiga, kai tsaye ya haye saman.
Tana zaune a kan gado tana muttsike ido tana shirin saukowa don ta zata Saddiku ne
ya dawo. Ta ja tsaki ta mika hannu ta janyo hijabinta a daidai lokacin da ya bude
kofar ya shiga dakin.
Ta san fada zaiyi a kan fitar Sadiku don haka ta kara tsuke fuska tayi shirin kora
masa jawabi.
‘Zahra, kika ce min Saddiku yana nan yanzu kuma naga baya nan, ina ya tafi? Don me
zakiyi min karya?’
Ba zai iya sauraronta ba don haka ya katseta da murya mai cike da damuwa
‘Zahra garin ki cutar da ni kina cutar da kanki, kin bashi mota duk da na hanaki
baki ji ba, na saka masa doka kina taimaka masa yana karyawa. Waya aka bugo min da
wayarsa cewa yana asibiti yayi hatsari a motar, yana can rai a hannun Allah. Nayi
tunanin ya kamata a ce yana gida shi yasa na zata ko wani wasa ne ko karya don na
san ya kamata ace yanzu yana gida, ashe baya nan. Allah ya sauwake, kin cutar da
kanki kin cutar da mu baki daya.’
Tuni ta daskare jiri ya fara dibanta, kwakwalwarta ta daskare don tun bayan rasuwar
mahaifiyarsu bata kara shiga tashin hankali irin wanda ta shiga yanzu ba da yake
gaya mata Sadiku yayi hatsari. Ya juya zai fice daga dakin, cikin zafin nama ta
dafa kafadarsa tana fadin
‘Sadiku fa kace min, la ilaha illallah! To yanzu yana ina? bari na taho muje.’
Hannu ya saka ya tureta daga jikinsa ta koma kamar zata fada kan gadon, ya fice ba
tare da ya sake kallonta ba.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
28
Nan ta zube tana fitar da hawaye masu zafi; Sadiku yayi accident? A wannan daren?
Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun.
Ta dafe kirjinta wanda yake kara kuntata zuciyarta ta ja jiki daga inda ta zube ta
koma kan gadon. Ta kifa kanta a kan filo ta fashe da kuka.
Bata san tsawon lokacin da ta dauka a haka ba amma lokacin da ta daga ta duba
agogon wayarta karfe uku na dare saura kwata. Nan da nan ta dauki waya ta bugawa
Abban don bai gaya mata koda asibitin da aka kai Saddikun ba. Ta kirawo shi ya kai
sau goma amma bai dauka ba, don haka hankalinta ya kara tashi.
Bata yi niyyar saukowa ta shirya yara su tafi makaranta ba amma sai ta tuna idan
basu tafi makarantar ba damunta zasuyi tayi; musamman da yake Rahma ta tafi, don
haka ta sauko bayan ta idar da sallar asuba ta fara shirinsu.
Har karfe goma na safe bai dauki wayarta ba, so take kawai ya gaya mata inda Sadik
din yake amma ya ki daga wayar. Haka ta hakura ta zauna tana ta abu kamar
zautacciya.
--------
Yana fita ya kirawo Aisha ya sanar da ita halin da ake ciki, ya wuce asibitin.
A emergency ya samesu; kusan a sume Saddikun yake duk da dai likitocin sun sanar da
shi allura akayi masa ta sashi barchi. Ya sami karaya a hannun hagu, sannan kuma ya
yanke a cinyarsa wanda sun riga sun yi masa dressing sannan kuma akwai sauran
ciwuka kanana a waje daban-daban a jikinsa. A take likitan ya bawa Abban shawara a
mayar da shi asibitin kashi saboda a duba hannunsa sosai.
An nuna masa Munir sai dai Abban bai san yaron ba, kuma ba a sami lambar iyayen
yaron ba don tun a wajen da akayi accident din aka sami wani ya dauke wayar tasa.
Bai sami wani babban ciwo ba sai kurjewa nan da can sannan kuma da firgita da yayi,
don haka aka yi masa allura yake ta barci bayan an wanke masa ciwukan.
Kafin asuba an gama duk wasu shirye-shirye aka saka Saddiku a ambulance Abba ya bi
su a baya bayan ya sami wanda zai tsaya masa a kan Munir. Suna zuwa aka kwantar da
shi; wajen karfe takwas da rabi likitocin suka shigo.
Nan da nan aka duba Saddiku aka yi masa hotuna, aka tabbatarwa Abban karayar
hannunce kawai matsala. Kafin a gama hotunan nan ya faraka, babu abinda yakeyi sai
kuka da kiran Mommy. Don kamar ma baya gane mutanen da suke kansa balle ya gane
Abban.
Nan da nan aka sake yi masa allura ya koma bacci, aka gyara shi aka kwantar da shi.
Lokacin wajen karfe tara da rabi.
A take Abban ya dauki waya ya kirawo Rahama ya sanar da ita halin da ake ciki ya
roki alfarma tazo ta zauna da Saddiku a asibiti; ta jajanta masa hatsarin sannan ta
fara shiri. Tana shiryawa tana mita don tayi alkawarin ba zata sake zuwa gidan ta
zauna da yara ba ko yanzun ma da Zahra ce ta kirawota ba zata je ba.
Amma tana jin nauyin Abba, ba zata iya ki ba. Tayiwa Ummansu sallama ta nufi
asibitin.
Rahama tana fita Ummanta ta fara waya tana gayawa dangi Saddiku yayi accident;
bayan ta kirawo su Murja ta kirawo Zahra ta jajanta mata. Sai a lokacin ta sanar da
ita ai Rahama ta tafi asibitin kashi wajen Saddiku.
Taji haushin Abban da yaki daga wayarta har ya gayawa danginta inda Saddikun yake
amma ita bai sanar da ita ba. Su Yaya Murja duk sun mata waya a kan kafin azahar
zasu sameta a asibitin. Nan da nan ta tashi ta soya kwai da dankali ta zuba ruwan
zafi a flask sannan ta shiga wanka.
Saida ta gama shiryawa ta kirawo Abban taci sa’a ya dauka, kafin ta gaisheshi tace
‘Ya Saddikun? Sai kiranka nake baka dauka ba, don Allah kuna ina?’
‘Mtsewww. Ki zo nan asibitin Murtala, akwai yaron da sukayi accident din tare da
Saddikun ko zaki gane shi don ni ban sanshi ba . Har yanzu bamu sami iyayensa ba,
ki zo ki gani ko kin san iyayensa in ya so daga nan kya wuce asibitin kashi.’
‘Ina jin Munir ne yaron kuma wallahi nima ban san iyayenshi ba, sai dai ko idan ya
farfado a tambayeshi.’
Sukayi sallama ta ajiye wayar, ta karasa shiryawa ta shiga mota Malam Ali ya ja
suka wuce asibitin kashi.
Haka Abban Sadiku ya zauna a asibitin Murtala wajen Munir har saida Munir din ya
farfado, aka samu aka tambayeshi. Nan ya bayar da lambar babansa aka kirawoshi, ba
a gari yake ba don haka kaninsa ya turo. Kafin ya iso Abba ya gama biyan duk wani
abu da ake bukata an canzawa Munir daki, an sayo magungunan da yake bukata; duk da
ma likitan yace zasu iya sallamarsa zuwa gobe.
………..
Bayan yayi bacci ta barshi da Rahama ta fito daga dakin ta sami waje kan wata
baranda ta zauna; ta rasa me yake mata dadi. Matse hawaye kawai take tana ajiyar
zuciya.
Tana na zaune tana kirga motocin da suke shigowa wajen ta hango motar Amina, da
sauri ta fito daga motar ta karaso wajen Zahran. Tana zama ta fada jikinta ta fashe
da kuka, Saida tayi mai isarta sannan ta dago ta kalli Amina tana share kwalla
‘Hmm! Na dai ga motar da ina tahowa Zahra, wallahi wannan motar ma idan aka ce na
ciki duka sun mutu ba zan yi mamaki ba. Kuma kamar ita kadai ce motar ba tare da
sun bige kowa ba sukayi hatsarin. Gaskiya abun da mamaki.’
Ta mike tana fadin
Suka tsaya a gefen gadon nasa bayan sun gaisa da Rahma, har yanzu bacci yakeyi sai
dai kana kallon fuskarsa ka san a cikin wahala yake baccin.
‘Kin ganshi ko Amina, duk jikinsa ciwo ne kuma an ce karaya ce a wannan hannun sai
gobe za a yi masa aiki.’
Ta jata suka fito suka koma inda suka tashi suka suka zauna, suna zama ta share
kwalla tace
‘Kin ganshi ko Amina? Kuma fa Abban yace daya yaron da suke tare a motar shi buguwa
kadan yayi, amma dubi Saddiku. Ya za ayi na yarda ba hannu aka sa masa ba, wannan
ma ina jin kasheshi aka so yi Allah ya ja kwanansa.’
‘Gaskiya ne kawata, sai ma kin ga motar yanda ta lalace gaba daya zaki san nisan
kwana ne ya hanashi mutuwa. Gaskiya wannan abun kam sai kin mike tsaye.’
‘Wallahi ba zan yarda ba, babu wanda nake zargi sai matar ubansu don motar ma ai
tunda tana hawa ba zata so na hau ba. Na samo takardun filin nan ma amma bari a
kwana biyu mu ga jikin Saddikun sai muje a gama komai; in sha Allahu matsalar kudi
ta kare komai tsadar aiki sai inda karfina ya kare.’
‘Gaskiyarki kawata, kin san hatta faduwar Saddiku jarrabawa ma kawai shiru nayi
miki amma ina zargin matar nan. Tunda kin ga Saddiku yana da kokarinsa amma ace
jarrabawa ta gagareshi.’
Haka suka cigaba da tattaunawa Amina tana kara zuga ta a kan su dauki mataki.
Kafin yamma dangi duk sun zo anata duba Saddiku, don saida likita ya hanasu shiga
dakin yace su daina damunsa.
Har dare yayi Zahra tana nan a asibitin, sauran yaran kuma suna gidan ta barsu da
Jummai. A yanda ta tsara Rahma ta tafi ta kular mata da gidan ita zata zauna da
Saddiku zuwa a yi masa aiki don an ce da safe karfe bakwai za a shiga.
Bayan sallar Isha’i Aisha ta dafa macaroni da sauce din kaza, ta sami flask ta zuba
na asibiti. Ta zuba madarar waken suya mai dumi a flask ta hada Abban ya dauketa
suka nufi asibitin.
Babu kowa a wajenshi daga Mommy sai Rahma, ya dan sami sauki don idonsa biyu kuma
ba kuka yake ba. Da kyar ta bude baki ta amsa gaisuwar Aisha, itama Aishan sai taja
jikinta. Ta yiwa Sadikun sannu ta koma kan dadduma kusa da Rahma ta zauna, suka
gaisa da Rahman suka dan taba hira.
Basu fi minti goma Sha biyar ba Abban yace ta tashi su tafi, ya dubi Zahra yace
‘Kema ki tashi mu tafi, Rahma ta kwana da shi in ya so da safe kya dawo.’
‘Kada ki bashi abincin da matar ubanshi ta kawo, akwai ragowar burodi da ruwan zafi
a flask din da na zo da shi ki hada masa kawai tunda da kyar yake cin abinci. Wanda
ta kawo ki bada shi kawai.’
‘To.’
Sukayi sallama ta fice; Rahma ta bi bayanta da kallo tana jijjiga kai tana mamakin
wannan kiyayya da zargi da ake wa Aisha don ita bata ga alamar cutarwa a tare da
Aishan ba.
……..
A hankali ta biyo bayansu domin ta shirya tijarar da zatayiwa Abban idan Aisha ta
shiga gaban mota; a nan zata nuna musu iyakarsu don babu yarinyar da ta isa ta
shigar mata gaban motar miji.
Shida Aishan suka fara isa wajen motar, yana budewa ta shige bayan motar. Bayan ya
zauna ya juyo ya dubeta
‘To mai guri ya zo ai dole mai tabarma ya nade ko, naji kace da Mommy zamu tafi
kaga kuwa ita ya kamata ta zauna a nan.’
Kafin ya bata amsa Zahra ta karaso, babu haske sosai a wajen don haka bata hango
Aisha ba. Cikin isa ta fizgi murfin kofar motar, sai dai ga mamakinta babu kowa a
wajen; ta hango Aishan a bayan motar. Ta shiga ta zauna cike da isa tana ta wani
cin magani ta rufe kofar motar.
Ba tare da kowa yayi magana ba Abban yaja motar suka nufi gida.
Kwanan Zahra ne don haka Aisha ya fara ajiyewa sannan suka wuce.
Ta tanadi tsiya kala kala da magnaganu masu zafi da zata gaya masa idan har ya
kuskura yayi mata maganar bawa Sadiku mota, sai dai ga mamakinta suna shiga gidan
ya rufe gidan; bayan yara sun sanar da shi Jummai ta tafi; ya shige dakinsa ya
barta da yara suna tamabayarta labarin Saddiku.
Iya haushi ta shaki haushin Abba sai dai ko sauraronta bai yi ba sannan kuma ita
kanta damuwar halin da ta baro Saddiku ya isheta. Haka ta kwana cikin matsananciyar
damuwa.
-------
Karfe bakwai aka ce za a shiga da Saddiku tiyata don haka tun karfe shida da rabi
Abban ya gama shiryawa. Ya riga ya sanarwa Aisha ta hada masa abincin safe da nashi
da na ‘yan asibiti don haka ko abinci bai nema ba a shirye ya sauko.
Yara sunata shirin makaranta duka suka gaisheshi. Ya wuce kichin inda ya jiyo
motsinta; bayan ta gaishe shi tace
‘Ba zaka ci abinci ba? Kafin ka gama Jummai ta karaso sai mu tafi tare.’
‘Yanzu zan tafi na karya a can, ki jira Malam Ali idan ya kaisu makaranta sai ya
dawo ya kaiki, don akwai takardun da sai na saka hannu sannan zasu shiga da shi
tiyata. Ni na tafi.’
Bai saurari amsarta ba ya fice.
Ta share kwalla; itama tana so ta ga Sadikun kafin a shiga da shi tiyata shi yasa
ma taso tafiya yanzun, tayi kwafa ta cigaba da aikinta.
Ko da Malam Ali yazo daukan yara da kanta ta fito tace masa da ya ajiye yaran a
makarantar ya zo ya kaita asibiti. Ya amsa suka fice shi da yara.
Yana ajiye yara a makarantar kiran Abban ya shigo wayarsa, bayan sun gaisa Abban ya
tambayeshi inda yake ya sanar dashi. Abban yace
‘To ranka ya dade Hajiya dai tace idan na saukesu naje na kaita asibiti, idan na
kaita asibiti sai na zarto office din kenan Ranka ya dade.’
‘Daga nan inda kake ka kai min mota office ka zauna ka jirani.’
A take shi kuwa ya karkata kan motar ya tafi office. Ya san Mommy tana da lambarsa
kuma bai san me zai gaya mata ba idan ta kirawoshi don haka yana shiga office din
ya kashe wayarsa tunda ya san idan Abba yana nemansa zai kirawo wani a office din
yace a bashi.
Haka tayi ta jiran Ali bai dawo ba, shi kuwa Abba tunda ta kirawoshi ya ki dauka ta
sa a ranta ba zata sake kiranshi ba a kan maganar Saddiku.
Sai can wajen sha daya Suwaiba ta kirawota zata tafi asibitin don haka sai tace ta
biyo mata su tafi.
………..
An yi aiki kuma komai ya tafi daidai sai dai likitan ya bada umarnin ‘yan dubiya su
dan saurara zuwa awa ashirin da hudu kafin nan zugin hannun yayi sauki. Don haka
mommy da Abban ne kawai suke zuwa.
Musamman Amina ta dauko mata hoton motar yanda ta kwankwatse kafin daga baya road
safety suka janye motar.
--------
Tunda Hajiya ta sami labarin hatsarin hankalinta yake kan ta zo taga Saddiku, sai
dai Abba ya hanasu zuwa. Saida ya kwana biyar a asibiti lokacin ciwon yayi masa
sauki tunda har ana hira da shi, kuma duk ciwukan jikinsa sun fara nuna alamar
warkewa tunda tun a asibitin Murtala aka yi masa dressing dinsu.
Malam Ali ya tura ya dauko Hajiya tare da Yaya Saratu da kuma Innani, Yaya Bello
shima duk da kusan kullum sai ya zo haka ya biyosu suka taho.
A nan dakin aka shimfida musu tabarma suka zauna ana ta jajantawa ana ‘yan
hirarraki har Abban.
Wajen karfe sha daya sai ga mutanen gidan su Aisha; Hajiya, Anti Uwani da kuma Yaya
Zuwaira wanda Yaya Abubakar da kanshi ya kawosu.
Cikin mutunci da girmamawa suka gaisa da su Hajiya, itama Zahra da yake a gaban
Hajiya ne da Abba cikin mutunci aka gaisa. Suka jajanta musu sosai suka duba
Saddiku. Suka dan taba hira, jimawa kadan suka ajiye musu leda cike da kayan
marmari ga kuma wata ledar da kajin gidan gona guda shida gyararru. Yaya Abubakar
ya zaro kudi naira dubu goma ya ajiye a gaban Hajiya yace a saya masa abun tabawa.
Suka fito ana son barka, Abba ya biyosu yana rike da hannun Yaya Abubakar yana yi
musu godiya.
‘Ikon Allah, albasa batayi halin ruwa ba. Mutanen gidansu masu mutunci da karamci
amma kanwar taki kam babu hali.’
‘Hmmm! Don ma baki zauna da ita ba, ai micijin sari ka noke ce lamba daya.’
Jimawa kadan Abban yace Malam Ali ya mayar da su gida, ya bashi kajin yace ya kai
gida ya bawa Jummai. Sukayi musu sallama suna sake jajantawa suka fice.
_
Satin Sadik biyu a asibitin lafiya ta fara samuwa domin har likita ya sa masa ranar
sallama. Yana iya rataye hannunsa ya yita yawo a cikin asibitin sannan kuma
yawancin ciwukan jikinsa duk sun warke, sai karayar wadda dama zata dauki lokaci.
A zaune suke ita da Amina a farfajiyar asibitin, inda suke babu nisa da dakin
Saddikun don suna hango kofar dakin.
‘Ina jin ma zuwa gobe zasu sallameshi don kin ga yana yawonsa ko ina.’
‘Ma sha Allah ai haka ake so, zakaran da Allah ya nufa da cara kenan.’
‘Ina jin gobe zan fito miki da takardun filin nan tunda kin ce akwai mai saye a
hannu. Mun gama magana da Yaron Malam yace an daure min bakinsa duk abinda zan yi
na yi ba zai iya magana ba don haka a siyar kawai ki turo min kudin account dina.’
‘Na gaji ne kawata da cin kashin da mutumin nan yake min, don a kan accident din
nan ina jin da ya sami dama zai iya kai min duka.’
‘Ai kece kike abu da tsoro uwar Sadiku, da kin biye min da tuni an sa miki shi a
kwalba wallahi idan kika ce ya zauna ko uwar da ta haifeshi bata isa tace ya tashi
ba sai in ke kika so.’
‘Hmmm! Ai kuma yanzu dole ayi hakan kawata tunda yana so ya nuna min taurin kai.
Wannan wulakanci da yake min ba zan dauka ba don na ga kamar ya manta lokacin da
muke hannu baka hannu kwarya na hakura da komai na zauna da shi yanzu ya sami kudi
ya auro matar so zai yi min tijara. Wajen wancan Malamin naki zamu fara zuwa daga
baya sai muje wajen yaron Malam, na san kudin filin nan zai isheni.’
‘Zai isa sosai ma, magana ake fa ta wajen miliyan uku da rabi zuwa hudu kinga kuwa
ko Aisha kike son siya ai kin saya kin gama.’
Sukayi dariya suka tafa.
Suka karasa hirarrakinsu, daga baya Amina tayi mata sallama ta tafi.
……….
An sallami Saddiku ya dawo gida inda zai karasa jinya, dakinshi na cikin gida aka
gyara masa ba don yana so baya koma. Tun daga asibitin Rahama tayi musu sallama ta
wuce gida akan idan ta huta gobe zata samesu a gidan.
Ranar da aka sallameshi washegari Amina ta gama cefanar da filin da Mommy ta bata
takardunsa. Ko da aka gama ciniki akwai takarda da ake bukatar saka hannun mai fili
don haka ta kawowa Mommy takardar har gida. Sadikun ta sa a gaba ya sa hannu a
takardar ba tare da ta bari ya karanta ba balle ya gane ta mecece, burinta tunda
dai sunansa ne a kan takardar filin kuma ya balaga ko daga baya idan zancen ya
tashi to shi ya sayar da filinsa.
Naira miliyan hudu da dubu dari biyu aka sayi filin; a hakan ma ance don karami ne.
Amma duk da haka naira miliyan uku da rabi Amina ta kawowa Zahran ta haye kan
sauran, bayan ta gama godiya kuma ta tura mata dubu dari da hamsin tace ga tukuici
da alkawarin idan an gama aikin ma zata kara mata idan an yi canji. Ta kirga
kudinta dubu dari takwas da hamsin ta tafi tana murnar wannan kazamar ribar da ta
samu.
Sai daga baya da Sadikun ya kara samun lafiya sannan Amina ta yiwa Zahra bayani shi
malamin nata a can wani kauye yake a karamar hukumar Doguwa, Doguwan ma a cikin
daji. Don haka ita Amina tana da amintaccen yaronta wanda shi yake kaita saboda
nisa kuma ga hadari, nan suka saka rana a kan nan da sati mai zuwa idan an yiwa
motar Amina service zasu je in ya so idan suka dawo suka huta sai suje wajen yaron
Malam.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
29
Tun a lokacin Mommy ta sami Abban a kan yayi magana da malaman makarantarsu Sadiku
din za a samu mai yi masa amma yace sam bai yadda wani yayiwa Saddiku jarrabawar
ba. Gaba daya ma kin saurarta yayi, domin daga baya ma da yaga tana neman ta zagaya
ta bayan gida ayi masa jarrabawar ce mata yayi in dai shine zai biyawa Saddiku
kudin jamia to ya san baiyi wata jarrabawa a wannan shekarar ba kuma ba zai karbi
wani certificate mai dauke da kwanan watan wannan shekarar don nema masa admission
ba.
Duk wanda take jin zasu goya mata baya idan tayi magana sai suce ta bari Sadikun ya
sami lafiya tukunna. Don haka dole suna ji suna gani aka gama jarrabawa babu
Saddiku. Ya tabbata sai ya sake bata shekara guda a gida, daidai lokacin ‘yan
ajinsu sun gama level 1 sannan zai sami damar gyara jarrabawarsa lokacin zai kama
tare da Yusra kenan wadda a halin yanzu za ta shiga SS 3.
__
Tun bayan da ya biyawa Zahra Umra kamar yanda ta zaba yake tanadin biyawa kansa
Hajjin bana; sai dai a yanda ya shirya tare da Aisha yake so su tafi.
Saura abinda bai fi shekaru goma yayi retire ba don haka yana da niyyar idan sun
gama aikin Hajji sai ya sako Aisha a jirgi ta dawo gida shi kuma ya wuce Dubai;
yana so ya fara shigo da kayan electronics yana sayarwa a Nigeria zuwa lokacin da
zaiyi retire ya zama babban dealer. Da fari yana jiran sai ya bude shago amma
abokinsa wanda yake masa jagoranci a harkar yace ya shigo dasu haka sai a kama
hayar waje a ajiye ana siyarwa a kan sari, yayi na’am da shawarar don haka ya gama
lissafin zarcewa Dubai daga Saudiyya.
Ita kanta Aishan bata san zai biya mata aikin Hajji ba don bai gaya mata ba, ya
bari sai ya gama komai ya gaya mata; duk da dai yana sane da cewa ta taba yin aikin
Hajji.
__
Satin da aka gama service din motar Amina sun gama tsara tafiya Doguwa sai kuma
Amina ta kwanta zazzabi. Abu kamar wasa sai da ya kai ta kwanciya a asibiti kwana
biyu; aka tabbatar da cewa zazzabi ne na malariya ya kamata da yawa. Wannan ya sa
dole suka dakata da tafiyar.
Bayan an sallameta daga asibiti kuma akwai ‘yarta ta fari Asiya wadda take aure a
Abuja, shekara kenan da yin aurenta sai a lokacin tazo ganin gida hadi da dubiya ga
tsohon ciki; don haka dole suka kara daga tafiyar har Aminan ta kara samun lafiya
kuma ta sami mai zama da Asiya. Tunda wannan tafiyar idan sun tafi da sassafe to da
isa gari da samun ganin bokan zuwa dawowarsu gida wuni guda ne, don wata ran sai
anyi isha’i take dawowa gidan.
__
A zaune yake a kan gado ya mike kafa ya dora computer a kan cinyarsa yana aiki
yayinda ita kuma take kwance a rub da ciki a gefenshi. Kanta yana daidai wajen
kafafunsa tana karanta littafi a waya kuma a lokaci guda tana wasa da yatsun
kafarsa.
‘Aeesh.’
‘Yes My love.’
‘Na biya mana aikin Hajji fa, ni da ke zamu tafi nan da kwana goma. Gobe da safe ki
shirya mu fita don takardunki ba a gama hada su ba da passport dinki kuma a goben
nake son mu gama tunda kinga lokaci ya dan kure.’
Da hanzari ta mike ta dawo dai-dai fuskarsa, suna hada ido ta kyalkyale da dariyar
da ta sashi dariya. Tace
‘Amin.’
Mamakin murnar da takeyi yake, musamman da yake ya san ta taba zuwa aikin Hajji bai
zata abun zai rudata haka ba. Yanda kuma yaga tana murnar sai shima ya kara jin
dadi, ya dinga binta da kallo yana murmushi.
Ta lalubi wayarta a inda ta yar da ita tana fadin
‘Bari na gayawa Hajiya.’
Har ta dauko wayar sai kuma ta sake jefar da wayar, ta dauke computer daga kan
cinyarsa ta ajiye a gefe sannan ta rungumeshi. Suka dan dauki lokaci a haka sannan
ta sakeshi ta kalli fuskarshi tace
‘Nagode sosai Yallabai, ba zaka gane yanda na ji dadi ba. Zan je na yiwa Abbana
dawafi nayi masa addu’a.’
Shima ya mika hannu ya dauki kwamfutarsa wadda ta ajiye masa a gefe ya cigaba da
aikinsa.
Gaban mudubi ta koma ta tsaya, sai dai madadin ta kirawo Hajiya kamar yanda ta fada
sai kawai ta kirawo Zahida. Tana dauka tace
‘Aaaah!’
Ta dawo gefen gadon ta zauna ta cigaba da waya tana gayawa ‘yanuwanta abun
alkhairi.
Ranar haka Aisha ta kwana cikin tsananin murna; babban abinda yake kara sakata
farin ciki shine zata je ta yiwa Abbanta da Mustafa addu’a. Sannan kuma zata kara
rokawa kanta tsari domin ta kula idan dai zata cigaba da zama da Uwar Saddiku to
tabbas tana bukatar tsari daga Allah.
………
Washegari suna zaune a falo suna cin abincin safe suna ‘yan hirarrakinsu ya dubeta
yace
‘Idan muka gama aikin Hajji sai na sako ki a jirgi ki dawo gida, ni kuma na wuce
Dubai. Akwai Abdurrahman zamu hadu da shi a can sai mu sayo kayan nan da nake gaya
miki.’
‘Alhaji.’
Ya kalleta da mamaki saboda ba haka ta saba kiransa ba, tayi murmushi tace
‘To ka tafi dani Dubai din mana, ai ko jaka ma na rike maka ko?’
‘Kuma ma ya za ayi ace kamar kai ka tafi Dubai ba tare da ni ba, haba mana. Ai ko
jaka ma sai na rike maka kuma in ka gaji ma ko tausa ai nayi maka.’
Ta dauko kwanon dankali ta ta dawo kujerar kusa da shi tana zumbura baki
‘To ba sai ka tsaru ba. Don Allah mu tafi tare kawai, ya za ayi ka tafi Dubai kai
kadai wai sai kace baka da gata.’
‘Nima ina son naje da ke amma dai ba yanzu ba, yanzu gaba daya kudin zan tattare
nayi sayayya. Idan abun ya kankama wata rana zamu je dake.’
Ta langabe kai
‘Bari dai nayi Sallah nayi addu’a, watakila ka taka kulli kafin lokacin sai kaga
mun tafi tare.’
Shima yana son tafiya da ita don ya san zai huta sosai, to amma tashin hankalin da
Zahra zata yi masa kadai ya isheshi sannan kuma kamar yanda ya fada kudaden
hannunsa bazasu kai ya tafi da Aisha ya kashe mata kudi yanda yake so ba; kwata-
kwata ma kwana biyu yake son yi a Dubai din ya wuto Nigeria.
Ita kuwa Aisha tana nan ta dana tarko don gaskiya tana son zuwa Dubai don haka ba
zata bari damar nan ta wuce ta ba.
__
A zaune yake a falon yana hutawa da yake ranar Lahadi ce, tana zaune a gefensa
yayinda Sumayya take wasanninta a gefe guda.
Da mamaki ya kalleta
‘Ohk. To babu damuwa amma dai da kin bari sai next weekend, dama ina son gaya miki
nextweek zan tafi aikin Hajji tare da kanwarki.’
Bata san yana shirin tafiya Hajjin ba don haka ta dan yi mamaki. Ta gatsina baki ta
dan yi murmushi
‘Kuma da gaggawa haka? Allah ya kai ku lafiya Allah ya amsa ibada. Kace mu kadai
zamuyi Sallah a gidan kenan.’
‘Eh daga ke sai yara ba, amma da an sallace zata dawo ni kuma na wuce Dubai na gaya
miki zan je Dubai.’
‘Amin ya Allah. Kinga idan muka tafi sai ki sami damar zuwa gaisuwar ko? Amma fa
sai kin dinga hakura da fita tunda kin ga Saddiku bai gama warkewa ba.’
‘Eh kusan daga wannan din ma babu wata fita da zan sakeyi in Sha Allah sai dai ko
gaisuwar Sallah in Sha Allah.’
Bata ji dadin yanda bai sanar da ita shirinsa ba, saboda ya za ayi tana nan yana
shirin tafiya Saudiyya amma ba zai sanar da ita ba.
Ta dai kyale zancen ne saboda tana da nata shirin, kuma da bata ji yace zai wuce da
Aishan Dubai ba bata da damuwa.
Ita din ma zata so ace baya gari zasuyi wannan tafiyar ita da Amina tunda zai zama
babu wani sauri da takeyi ta dawo gida sai lokacin da ta ga dama kawai. Don haka a
take ta yiwa Amina waya suka daga ranar tafiya, domin a lokacin dama Asiya bata
dade da haihuwa ba.
__
Ranar asabar ce wadda gobe Lahadi jirgin Abban Sadik da Aisha zai tashi.
Duk wani shiri da take bukata ta gama shi; abu dayane a ranta yanda zata tsara
Abban Sadik ya yarda ta biyawa kanta kudin zuwa Dubai ta bishi. Tunda yayi maganar
ta sa aka bincika mata aka gama yi mata lisaffi; kudin jirgi, hotel har zuwa kudin
da take so ta kashe ta lissafa kuma taga cewa tana da su zata iya biyawa kanta.
Jirgin safe zasu tafi don haka zuwa goman dare sun gama komai sun kwanta. Yana
kwance rigingine tana kwance a gefensa sai dai basu kashe fitila ba tukunna don
basuyi bacci ba.
Mirginawa tayi ta koma jikinsa, ta dora kanta a kan hannunsa sannan ta dora tafin
hannunta a tsakiyar kirjinsa, tace
‘Don Allah to ni zan biyawa kaina, kaga dama adashin da nace maka na dauka last
month 250k suna nan kuma inada wasu savings sai na kara.’
‘Um, kiyi abinda kika tsara zakiyi da kudinki in Sha Allah next time sai muje Dubai
din.’
‘To kayi tunani dai kafin muje, kudin suna dollar account dina Kuma kaga visa din
Dubai bata wahala. Kafin mu gama aikin Hajji kayi shawara. Kaga kafin ma mu dawo
gida mun huta, ko kwana biyun ne ina laifi.’
‘Saboda muje kiyi min addu’a, ki tsara ni kiyi min wayo ko?’
Ta kyalkyale da dariya.
Gari yana wayewa karfe tara na safe jirginsu ya daga sai Saudiyya.
___
Ranar litinin karfe shida na safe Uwar Sadiku suka kama hanyar garin Doguwa; a
motar Amina suka tafi sai dai akwai Alele yaronta shine yake tukasu.
Nisan garin ya bawa Zahra mamaki matuka, don gani tayi kamar za a fita daga garin
Kano.
Ko da suka Isa Doguwa ma wucewa sukayi sai da suka kusa fita Kano sannan suka sauka
daga kwalta suka fada wani daji, da ba don taga alamar motoci suna bi ba da zata ce
babu wanda yake shiga wajen.
Ta kalli Amina wadda suke zaune a bayan mota tare zuciyarta fal tsoro, Amina tayi
murmushi tace
‘Kada ki damu, kina hawowa nan layin kin zama bakuwar Malam Jani, babu abinda zai
cutar dake har ki fito ki kama hanya sosai.’
Ta dan gyara zama ta mayar da hankali ga kallon hanya duk da ba wani gani takeyi
sosai ba.
Sun kai kamar minti goma sha biyar suna zura gudu a lokon nan kawai sai taga sun
fado wani sarari mai fadin gaske; kamar wata karamar unguwa.
A gaban wani babban gida sukayi parking wanda yake kewaye da wasu gidajen tsilli-
tsilli sannan ga yara suna wucewa jefi-jefi. Yanayin wajen yanayi ne mai dadi, babu
sanyi kuma babu zafi sannan ko ina a share yake tsaf.
A kofar babban gidan sukayi parking kusa da wasu motoci guda biyu wanda ga dukkan
alamu masu kudine sosai kuma suma bakin wannan gidan ne.
Tun kafin su gama fitowa daga mota yaro ya fito daga cikin gidan yayi musu iso.
Madadin su shiga ta kofar gidan sai yaron ya zagaya da su ta wata kofar da take
bayan gidan.
Daki ne ya sha shimfidu na jajayen daddumai, har labulayen dakin duka jajaye ne. Ya
nuna musu wata bakar dadduma yace su zauna, bayan sun zauna yace
‘Za ayi muku iso idan Malama ya gama, yana da wasu bakin.’
Suna nan zaune tun wajen karfe tara na safe har sha biyu ta gota babu wanda ya sake
lekosu, idan suka taba hira sai su koma suyi shiru.
‘Nace miki yana sane, tunda naga motocin nan na san yana da baki sai ya gama da su
zai sauraremu.’
‘Sallah! Ki rufa mana asiri, ai sai dai idan mukaje gida ma hade. Wa ya gaya miki
ana kallon gabas a nan?’
Jimawa kadan wajen daya da rabi yaron da ya rakosu dakin ya leko yace shu shigo. Ya
wuce gaba suka bi bayansa. Kofar da suka shigo ba ita suka fito ba, wata kofar ce a
dakin ya shiga suka bishi. Siririn corridor suka bi wanda ya sada su da wani daki
mai kawanya.
Kusan komai na dakin ja ne sai fari tsilli-tsilli. Bangon da yake kallo kofar an bi
shi kaf an rataye tarkace kala-kala, kayuwan dabbobin ita dai Zahra kamar har
shekar tsuntsu ta hango.
Jar dadduma ce a shimfide a gaban bangon wadda kallo daya zaka yi mata ka san ta
hadiye datti da yawa. Yana zaune ya tankwashe kafafu babu wata sutura a jikinsa sai
gajeran wando da bai karasa gwiwarsa ba.
Tun da suka saka kafa a dakin Zahra ta damki hannun Amina ta rike gam saboda tsoro,
ita kuwa Aminan da yake ta saba kai tsaye ta wuce gaban wannan bakin katon suka
gurfana.
‘Um ni so nake kawai a rabata da mijina, su rabu har abada kuma kada ya sake auren
wata mace.’
Aka kyalkyale da dariya wadda har dakin saida ya amsa, sai dai ko da suka kalli
fuskar malamin da suke gabansa babu alamar shi yake dariyar.
Ya mika hannunsa baya ya zaro wata babbar tasa wadda kusan za a iya cewa hannu daya
ba zai iya dauka ba. Ya dire tasar wadda take dauke da ruwa a gabansu, ya dauki
wata bakar kwalba a gabansa ya diga wani mai a cikin tasar sannan ya fara motsi da
baki kamar mai wuridi. Lokaci kadan ya gama sambatun ya busa a tasar sannan ya dubi
Zahra yace
Amina ta dan dungureta suka matsa gaban tasar suka leka; Aisha ce sanye da abaya
suna tafiya tare da Abban Sadik a wani wajen kamar farfajiyar masallacin Madina.
Sai dai ita Aishan wani abu kamar glass ya yi mata kawanya shi kuma Abban yana
gefenta babu abinda yayi masa kawanya.
Aka sake bushewa da dariyar nan da basu san wanda yake yinta ba, sannan mutumin mai
kakkausar murya ya nuna Aisha a cikin tasar yace
‘Kinga wannan, ba zata tabu ba. Ko me za ayi mata ba zai yi tasiri sosai ba domin
ta fi ki shiri.’
Dariyar nan ta sake karade dakin, bayan ta lafa ya nuna Abba yace
‘Wannan za muyi miki aiki a kansa amma sai ya baro wajen nan da yake, idan ya dawo
gida sai ki sanar damu.’
Cikin in ina tace
‘Aikin da zamu yi miki shine; zamu shafe masa ita daga tunaninsa. Zai manta da ita
ya manta ya sake aure, ke duk wani wanda zai iya fada a ji ma a auren zamu mantar
dashi labarin Aisha. Idan aka yi haka to tabbas ita da danginta zasu raba auren don
bazasu iya tuna masa da ita ba, don auren ma ba shi zai saki ba sai dai suje kotu
alkali ya saki. Daga ranar da mukayi aikin ba zai sake tunawa da ita ba.’
Ita kanta saida tayi murmushi saboda wannan tsarin nashi yayi mata,tabbas idan Abba
ya manta da Aisha zuwa wani lokaci ne ‘yanuwanta zasu raba auren. Shikenan ta huta
da wannan alakakan.
Kamar daga sama aka jefo wata karamar bakar tasa gabansu, mutumin yace
Nan da nan Zahra ta bude jakarta ta fito da kudin da ta zo da shi naira dubu dari
biyu ta saka a tasar, a take tasar ta bace.
Mutumin yace
‘Idan ya dawo a zo a sanar da mu, zuwa lokacin dan matsuruto zai sanar da ku kudin
aikin da zaku ajiye masa kafin aiki ya fara. Ku tafi, ku tafi.’
Nan da nan suka mike, yaron da ya shigo da su ne ya sake shigowa ya wuce musu gaba.
Ya bi da su ta wata kofar da ban da ba ta nan suka shigo ba, sai a lokacin Zahra
taga sun fito ta kofar gaban gidan daidai inda suka ajiye mota. Motocin da suka
tarar da safe basa wajen sai dai wata bakar mota wadda da alama bayan sun shiga ne
masu ita suka zo.
Ba tare da bata lokaci ba suka shiga mota suka kama hanya, nan dinma hanyar da suka
bi ba ta ita suka fito ba.
Babu wanda yayi magana sai da suka fito daga daji suka hau kwalta. Amina ta dubi
Alele da yake tuki tace
‘Alele duk mai abun da ka gani ka tsaya mu siya mu dan sa wani abun a bakinmu, na
manta ban yiwo mana guzuri ba yunwa muke ji.’
‘To Hajiya, mun kusa zuwa wajen masu mangoron nan ai.’
‘Kawata kin ga inda za a magance miki matsalarki ko? Yanda yayi miki alkawarin haka
zai yi miki aiki zaki sha mamaki.’
‘Hmmmn! Ai na ga alama.’
Suka yi shiru kowacce tana kora ruwan robar da suka taho da shi.
‘Kawata naji yana maganar kudin aiki bayan kudin da na ajiye masa.’
‘Eh, ai in dai kin shiga da jaka wannan dakin sai kin ajiye duk kudin da yake jakar
a wannan tasar ko an yi aiki ko ba ayi ba. Kudin aiki kuma da ban za a sanar dake.
Kawai idan zamu dawo ki sake ciko jaka.’
‘Hmm!’
Suka sake yin shiru na dan lokaci, jimawa kadan Zahra tace
‘Ni abu daya ne yake bani haushi, duk inda naje sai ace wai mutuniyarki bazata tabu
ba. Na rasa waye malaminta a garin nan da bamu san shi ba.’
Amina tace
‘To tunda dai an sami makarinta ba shike nan ba, duk ma wanda yake mata aiki su
karata. Idan ta rabu da mijinki duk ma yanda tayi ba shikenan ba.’
Sai daga baya suka sami masu rogo sun fito daga wani kauye, suka saya sukayi ta ci
har suka rage yunwa.
Saida aka idar da Sallar Magriba sannan suka ajiye Zahra a gida suka wuce, a kan
idan alhazai sun dawo zasu koma a gama aiki.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
30
Tunda suka dawo daga Doguwa kuma sai Zahra ta cigaba da harkokinta cikin walwala,
musamman da yake yanzu gidan yana hannunta. Abu daya ne kawai bata sami yanda take
so ba; ta riga ta tsara yanda zata yi yawon Sallah a motar Abban, sai dai kawai
ranar da zasu tafi da motar ya fita ya kaita gidan Yaya Bello ya ajiye a can sanna
Ali ya wuce da su airport.
Da ya sanar da ita wannan tsarin nasa da wuri da tabbas ta hanashi don da ya saba
tafiya ya bar motarsa a gidan, amma dai wannan zuwa Doguwa ya wanke mata duk wata
damuwa.
Nan da nan ta cigaba da shirin babbar Sallah da lissafin yanda zata kasafta naman
san da ya bari a yanka.
__
Tunda suka isa kasa mai tsarki Aisha ta dukufa addu’a; duk abinda take so saida ta
roka kuma ta yiwa Abbanta addu’a sosai.
Tare da Abba suke a hotel don haka ma bata sake tayi wata kawa ba tunda yawancin
ibada ma tare suke zuwa, don haka ko kasuwa ma bata tunanin zuwa.
Saura kwana biyu arfa suna zaune ita da Abban sun gama cin abinci suna hutawa a
dakinsu na otel suna dan taba hira . Kamar wadda aka tunawa ta dubeshi tace
‘Uhm, Dubai din zamu wuce ko Yallabai don ka ga shi yasa ba zan yi tsaraba a nan ba
sai na je can.’
‘Allah, dadi kai! Ai bari ma kaga nayi Sallah na yiwa Allah godiya tukunna.’
Sai da ta gama murnar ta tambayeshi nawa zata turo a kudinta da tace zata biya,
yace ta turo dubu dari biyu account dinsa ya isa shi sai ya cika sauran.
Sai bayan ya nuna mata visa dinta sanna taga kwana bakwai yayi musu booking, ta ji
dadi sosai don haka ta fasa duk wata sayayya ta mayar da hankali wajen ibada da
kuma addu’a.
…………
Tunda suka tafi Saudiyya kusan kullum wayoyin Abban suna kashe, sai lokacin da ya
zaba sai ya kunna suyi waya ta Whatsapp don ya ji lafiyar iyali. Tayi mita har ta
gaji, don haka ya zama kawai sai dai ta bar masa sako a WhatsApp idan ya gani sai
ya kirawota.
Tunda suka tafi ya ke shawarar tafiya da Aisha Dubai kuma yake tunanin yanda zai
yiwa Zahra bayani ya rasa. Bayan Sallah da kwana hudu ya kama ranar zasu wuce Dubai
kuma har ranar bai gayawa Zahra ba.
Kaf suka shirya kayansu ana yin sallar Magriba suka bi jirgi sai Dubai.
Yana bude data kuwa kiran Zahra ya shigo kamar tana jiransa, a lokacin Aisha tana
wanka. Ya amsa wayar ya fice daga dakin, ya dawo falon kasa wato reception na hotel
din ya sami kujera ya zauna.
Bayan sun gaisa ya tambayi yaran, duka suna kusa da ita don haka ta bashi suka
gaisa da kowa har Saddiku. Bayan ta karbi wayar suka dan taba hira, jimawa kadan
yace
‘Yauwa ban gaya miki ba na wuce Dubai din fa, itama Aishan muna tare da ita a nan
din tare zamu dawo.’
‘Um ban gane ba. Kace ita nan gida zata wuto?’
‘Eh. Na canza shawara daga baya tunda itama ta biyawa kanta kudin zuwa Dubai din
kawai sai muka wuce.’
‘Amin.’
Yanda yaji muryarta ta canza nan take ya san da sauran bayani, ya san idan ta fara
mita abun zai daukesu lokaci don haka nan take yayi mata sallama ya kashe wayar.
…………
Kwanki biyun farko da sukayi a Dubai shi kadai yake fita tare da wanda aka hadashi
don ya raka shi kamfanin da zai yi sayayya. Yana fita Aisha take komawa bacci,
domin dama ta tara bacci a Saudiyya. Haka ya kwana biyu yana yawo ita kuma tana
hutawa, don ko abinci har dakin ake kawo mata.
Sun riga sun gama magana da Aisha a kan ya saya mata waya in ya so ita kuma sai
tayi tsaraba da kudinta; don haka fitarsu ta farko ya sayo mata Samsung hadaddiya
mai tsadar gaske.
Suna komawa daki ta kasa hakura, saida ta kunna wayar nan. Suka hadu sukayi
launching sabuwar waya.
Wayar ta hadu sosai kuma camera tana fitar da hoto don haka sai ya zama duk inda
suka je haka zasuyi ta hotuna.
Sun hutu kuma sun ji dadi domin Aisha zata iya cewa bata taba jin dadin zama da shi
ba kamar a wannan lokacin. Shi kansa yaji dadin tahowa da ita saboda yanda take
jiyar da shi dadi kuma tana saka shi walwala, don haka ya saki kudi sukayi ta yawo
suna sayayya. Hotuna kuwa Allah ne kawai ya san yawan wadanda Aisha ta dauka a
sabuwar wayarta; wasu a dakin otel, wasu a wajen cin abinci, wasu a wajen sayayya
wasu ma a kan hanya kawai. Ko wanne kuma sai ta makale a jikinsa take dauka ko ta
sami masu wucewa tace a daukesu.
Ranar da suka kwana uku a Dubai rana suka je wani club na larabawa, wajen an yi
masa tsari ne kamar a Sahara. Sanna ga rakuma da dawakai birjiki duk wanda kake so
shi zaka hau, kuma abinci kala kala na larabawa. Wajen yayi matukar burge Aisha.
Bayan sun gama hutawa rana ta fadi tace zata hau doki, suka karasa aka hada musu
doki. Ita bata iya doki sosai ba don haka da ta hau wani balarabe ya ja linzamin
dokin suka zagaya.
Daga baya Abba yace ta dawo su hau doki daya don su zagaya sosai.
Nan da nan ta sauka ta koma kan dokin Abba; ta zauna a gabansa ya rungumeta ta baya
sannan ya ja doki suka kama hanya. Suna tafiya sunata hira da dariya.
Bayan sun dawo wani balarabe ya nuna musu hotunansu da yayi ta dauka a camera dinsa
wanda idan suna so biyanshi zasuyi sai ya tura musu. Nan take ta mararaicewa Abba
ya biya aka tura hotunan wayarta.
A gajiye likis suka koma dakin sai dai zuciyarsu fari tas saboda wunin ranar yayi
musu dadi.
Washegari Aisha tana bude Whatsapp taci karo da sakon Zahida na murya wato voice
note, nan da nan ta bude tana saurara:
‘Wai mutum yana Dubai amma ba zai tura mana hotuna ba, to wallahi ni ko kasuwar
garinmu naje sai na ishi duniya da hoto balle na hau jirgi na keta hazo. Ko da yake
ma Yusuf din zan tambaya nake bata lokaci.’
Saida ta gama dariya sannan ta zabi hotunansu wajen kala goma ta tura mata. Ta
cigaba da dube-dubenta a waya.
_
Duk da bacin ran da take ciki na tafiyar da yayi da Aisha Dubai bata fasa shirin
tarbarsa ba kamar yanda ta saba; maganar Dubai ma ta riga ta bawa zuciyarta hakuri.
Kawai dai ta yiwa kanta alkawarin ko da tsiya ko da tsiya-tsiya idan zai kuma fita
kasar nan ko ina ne sai ya je da ita.
Hajja ta kawo mata kayan mata wadanda cikinsu harda na mallaka, duk ta fara amfani
ma da su. Sai dai jiya da suka yi waya da Amina ta sanar da ita akwai wasu kaya da
aka kawo mata daga Nijar, idan ta tashi daga office zata kawo mata su lallai ta
gwada don ta bata tabbacin sai sun sa mata mutum sambatu.
……….
Ma’aikatar kudi ta jiha ne inda Amina take aiki. Su biyu ne a office dinta ita da
abokiyar aikinta sai dai kowacce da teburinta. Daga gefe guda kuma akwai kafet
karami wanda nan ne suke Sallah ko kuma su dan mike idan suna hutawa.
Yau ma a nan suke zaune, ita Amina tana rubuce-rubucenta yayinda Hadiza ke ta faman
kalle-kalle a waya.
Hadiza ce ta budo wani status a wayarta tana kalla tana murmushi, can kuma a fili
tace
Amina tace
‘Keda wa?’
Ta dan matso tana nuna mata abinda ta gani a wayarta; mata da mije ne a kan doki
yana rungume da matar suna ta dariya, ita kuma matar tana rike da kofi me straw
tana zukar wani abu daga ciki. Yana wucewa wani ya fado suna tsaye ya rungumeta nan
ma dariyar suke, shi yana sanye da kananan kaya ita kuma tana sanye da abaya. Bayan
ya wuce wani ya fado yana kwance a kan yashin ita kuma ta tada Kai da bayansa tana
ta dube-dube a wayarta. A kasan hoton karshe an rubuta “sharholiya made in Dubai.
Allah ya maimaita mana.”
Wani status din ya fara budowa Aminan tace
‘don Allah mayar dashi na kara gani; matar kika sani ko mijin?’
‘Wallahi babu ko daya. Ina jin a group ma fa muka hadu da matar nan kuma fa ban san
ko itace a hoton ba ko ‘yaruwarta ce don bamu taba haduwa ba sai dai a group. Kawai
dai sun burgeni.’
‘Gaskiya a’a, sunanta Zahida M. K don haka take sawa a WhatsApp name dinta.’
‘To wannan ta hoton dai sunanta Aisha kuma kishiyar kawata ce don hotunan nan ma
hada baki sukayi da mijin ya tafi da ita suka bar Uwar gidan a nan tana fama da
yara.’
Ta zaro ido
‘Ke Amina?’
‘Wallahi kuwa, wannan tafiyar ta munafunci ce. Uwargidansa ya rainawa hankali don
maganar da nake miki ma suna can sai jibi yace mata zasu dawo.’
‘Kai kawata maza ‘yan bura uba ne! Wato Uwargida jakar gida an barta a gida an tafi
da amarya Dubai sharholiya. Kai Allah ya shiga tsakaninmu da irin wadannan
kishiyoyin, ki gama wahala da miji a zo a nuna miki iyawa.’
A nan ta saka Hadizan ta tura mata hotunan wayarta tunda dama idan ta tashi daga
office din gidan Uwar Sadikun zataje.
Tunda taga hotunan nan ta kasa zama a office din, sosai ranta ya baci don tana taya
Amina jin zafin wannan tafiyar da aka yi babu ita. Taci sa'a ana yin sallar azahar
ogansu ya fice daga office din don haka itama ta fice ta nufi gidan Zahra.
A falo ta sameta tana hutawa yayinda Jummai take aikace-aikacenta da goyon Sumayya.
Kafin su gaisa ta jata falon sama, bayan sun zauna ta ajiye mata ruwan sanyi da
lemo. Suna gama gaisawa Zahra tace
‘Wai ya na ganki kamar a fusace ne, ina dai fatan kin taho min da tsumin?’
‘Na taho miki da shi. Wani abun takaici na gani wallahi. Ni wai ba cewa kikayi
kwana biyu Abban Sadik zai yi a Dubai bane?’
‘Haka yace. Amma ai daga baya na gaya miki ya tafi da amaryarsa wai wani idan ya
dawo naji bayani, don haka yanzu kwana bakwai zasuyi shine sai jibi zasu dawo. Ai
duk wannan shirin da nake yi sai ya ji daga gareni don wallahi ina binsa bashin
zuwa Dubai.’
‘Hmmmn! Sai ma kinga abinda na gani sannan zaki tabbatar kina binsa bashi. Yana can
suna ta sharholiya shi da kanwarki baki gani ba kamar wasu saurayi da budurwa.’
Ta budo wayarta ta nuna mata hotunan da Hadiza ta tura mata; tana kalla tana
jijjiga kai zuciyarta tana zafi saboda takaici.
‘Ni zai rainawa hankali! Sai yanzu ma na gane babu wani business da yaje yi wallahi
kawai hutawa ya dauki amaryarsa ya tafi ya barni a nan da yaransa. Tunda mutumin
nan ya tsara tafiya Hajjin da matar nan na san ya shirya raina min hankali wallahi.
Kawai daga kara aure mutum ya zama wani karamin munafiki, komai zai yi sai boye-
boye? Kin san ko Hajjin ma ban san yana shirin tafiya ba sai da ya zama saura sati
daya su tafi ya sanar da ni.’
Ta dafa cinyarta
‘Kada ki damu kawata na karshe sukeyi, wannan hotunan ma gani nayi kamar kin yarda
da zancensa shi yasa nace sai na nuna miki. Amma kada ki wani damu da sun dawo za
ayi maganinsu.’
‘Hmmmn!’
Nan suka cigaba da hirarrakinsu, daga baya ta bata tsumin da ta kawo mata sukayi
sallama ta tafi ta barta tana takaicin hotunan.
Hotonsu a kan dokin nan yayi matukar tsaya mata a rai don ita bata ma taba sanin
Abban ya iya hawa doki ba.
__
Jirgin safe suka biyo don haka wajen sha daya na safe suka sauka a gida Nigeria.
Malam Ali yana jiransu a airport don haka nan da nan suka gama clearance suka dauki
kayansu gaba daya aka zuba a mota suka kamo hanyar gida.
Suna shiga unguwar Abba yace ya kai su gidan Aisha don haka can ya kaisu suka sauka
ya sauke musu kayan gaba daya. Duk da gidan ya dan yi kura amma haka Abban ya
tayata suka karkade dakinsa yayi wanka ya canza kaya sannan ya fito ya nufi wajen
Mommy.
……….
Tunda Malam Ali ya shiga dasu gidan Aisha yara suka kai mata labarin Abba ya dawo
yana gidan Anti; bata yi zaton haka ba don ta zata a gidanta zai sauke jakar
tsarabarsa amma duk da haka sai ta daure. Ta tare yaran gaba daya ta hanasu fita
don so take tayi kamar bata san ya dawo ba.
Sai dai kafin ya gama wanka ya zo ranta har ya gama baci; kenan wani abun ya tsaya
yi a wajen Aisha.
Tana zaune a falon sama tana ta faman cika tana batsewa ta jiyo yara suna ta
murnanr dawowarsa bayan da ya shigo gidan. Sai da ya gama hirarsa da yara ya
rarraba musu chocolate din da ya riko sannan ya hau saman ya sameta.
Da kyar ta daure ta amsa sallamarsa; ya fahimci damuwarta saboda dama tun lokacin
da yace mata ga su a Dubai shi da Aisha ta daina kiransa a waya sai dai shi ya
kirawo, Kuma da ya kirawo sai ta hadashi da yaran. Don haka ya shiryawa duk wata
rigimarta.
Bayan sun gaisa ya tambayeta gida da yara ta tashi ta dauko kunun aya ta ajiye ta
cika masa kofi, ta koma ta zauna a inda ta tashi kusa da shi. Sai da ya kwankwade
kunun ayan ya ajiye kofin sannan ya dubi fuskarta.
Sai cika take tana batsewa tana ta faman harare-harare. Ya mike tsaye yana magana
cikin halin ko in kula
Ya kama hannunta wanda ya sha kunshi yayinda ta kara shan kuna, yayi taku daya ya
matso gabanta sosai yace
‘To ai na ga kamar baki ji dadin dawowata bane shi yasa da zan dan koma na baki
waje ko.’
Ta murgude bake zatayi magana, kafin ta bude baki ya sumbaci lebenta yayi dariya
‘Allah ya nuna min ranar da za a daina murgude min bakin nan na rashin kunya.’
Ta zumburo baki, ya sa hannu ya kara janyota jikinsa. Duk wata tsiwa da ta haddace
zatayi ya goge mata haddarta, haushinsa take ji amma ta kasa ture shi. Yace
‘Na san dai kinyi kewata da yawa, to ba gani na dawo ba kuma shikenan sai a tare ni
da murguda baki sai kace wani wanda bashi da galihu. Ai dole na koma tunda dama
jakata a kulle take idan kika shirya sai na dawo.’
Shiru kawai tayi ta kwanta a kirjinsa ya rungumeta yana shafa bayanta. Tayi kewarsa
kamar yanda shima yayi kewarta. Suna nan a tsaye suka ji motsin hawowa saman wanda
kana ji ka san Ummi ne da Sumayya. Tayi gyaran murya ta dan ja baya don ta tabbatar
shi ba sakinta zaiyi ba, tace
Ya shige dakin bayan ta amsa; yana so yace tayi abinci da Aisha amma yana tsoron
fitna, don ya kula duk lokacin da yayi mata maganar Aisha to da fada suke rabuwa
don haka ya hakura.
…………
Bayan sallar la’asar ne suna zaune gaba dayansu a falon a kasa ana ta hira, ya duba
agogo lokacin karfe biyar da kwata. Ya san dai zuwa yanzu Aisha ta dan huta don
haka ya dubi Mommy yace
‘Bari muje da yara mu yiwa Anti sannu da zuwa, yanzu zamu dawo.’
Ya dauki Sumayya ya tasa yaran gaba daya har Saddiku suka nufi gidan Aisha; domin
ya san idan ba haka yayi ba bazasu je ba, shi kuma baya jin dadin wannan zaman da
sukeyi kamar suna gaba da juna.
A zaune take a falo tana hutawa lokacin da suka shiga; cikin fara’a dalwala ta
karbesu.
Bayan ta amsa gaisuwar kowa taki amsa gaisuwar Rukayya don haka bayan kowa ya gama
magana Rukayyan ta sake cewa
Ta harareta tace
Sukayi dariya gaba daya. Saddiku ne kawai bai saka musu baki a hirarsu ba yana
zaune da hannusa wanda bai gama warkewa ba a rungume yana ta muzurai.
Ta tashi ta shiga daki, jimawa kadan ta fito da kaya ta ajiye ta koma ta sake dauko
wasu ta fito ta ajiye sannan ta zauna. Ta janyo hannun Sumayya wadda take kan
cinyar Abbanta, ta noke alamar ba zata zo ba. Ta dauko ‘yar tsana daga leda ta mika
mata sannan ta mika mata alawa a 'yar karamar roba. Ta mika mata hannu tace
‘To zo mu shirya.’
‘Sumayya kiwa.’
Ta bawa Saddiku takalmi sau ciki, Yusra da Nana da Ummi kuma kowa ta bashi abaya da
agogo.
Akwai keken dinki mai aiki da wutar NEPA dan matsakaici na dorawa a kan tebur, ta
janyo kwalin ta mikawa Rukayya tace
Nan take tasa ihu, ta sunkuci kwalin ta mikawa Abba cikin murna tace
‘Abba ka ga.’
‘Umm! Wannan dai mayi magana daga baya idan kin dinka na ‘yar tsana dai mayi
magana.’
Duk gaba dayansu sukayi mata godiya, har sun mike ta mikawa Rukayya Leda tace kin
manta da taki abayar. Abba ya karbar mata duka yaran suka wuce suka barshi a nan
yana dauke da Sumayya. Ya dubeta yace
‘Wannan ai ke baki sayowa kanki komai ba yara kika siyowa, na zata ma kanki kika
siyowa keken dinki.’
Tayi dariya
‘Ai ni bana son dinki itace take so, tunda suka je gidan Zahida da sallah ta gano
kekuna kuma Zahida tayi mata alkawarin zata koya mata dinki shikenan ta kasa
nutsuwa kullum dinki.’
Rukayya sai murna take ta kasa zama guri daya saboda keken nan wanda ta riga ta
fitar da shi daga kwalinsa.
Da sallama ta shiga dakin, bayan ya amsa sallamarta ta zauna a gefen gadon wajen
kafarsa. Ya gyara kwanciyarsa yana kallonta alamar ita yake sauraro saboda ya san
wannan zaman da magana.
‘Kuma wannan keken da aka siyo guda daya ina na Yusra? Tunda ka san itace dai
Babba. Idan dai ba hada fada ba da so a raba min yara ai biyu ya kamata a siyo.
Kuma abayar ma ita Yusra sai aka siyo mata iri daya da Nana ita kuma Rukayya tata
ta fi kyau gashi harda wata jaka da turare bayan agogon. Idan ba hadin fada ba ai
jaka ma da turare Yusra ya kamata a bawa itace 'yan mata tunda ko a makaranta yanzu
SS 3 take yayinda Rukayyan take JS 3. Irin wadannan abubuwan ai su suke raban kan
‘yan uwa, duk abinda za a yi ko dai ayi musu tare ko kuma a fara yiwa Yusran tunda
itace babba.’
Tunda ta fara maganar yake binta da kallo yana mamaki, ya tashi zaune yana binta da
kallo yana murmushin takaici yayinda ita kuma take kara shan kunu. Yayi gyaran
murya yace
‘To yanzu dani kike wannan hayagagar ko kuwa Aishan zan kirawo kiyi mata?’
‘Au hayagaga ma nakeyi ko? Ka kasa yin adalci tsakanina da matarka kuma yaran naka
ma bazaka yi musu adalci ba saboda ana zuga ka ko?’
Ya tsani tace baya adalci saboda shi ya san iya karfinsa yana kwatantawa, yayi
tsaki
‘Zahra kada fa ki gaya min magana saboda kinga Ina sauraronki. Duk abinda kika gani
sun zo da shi Aisha ce ta siyo musu da kudinta don ni ban ma kwance kayan ba kuma
ba wannan korafin ya kamata kizo kina yi ba godiya ya kamata kije kiyi mata. Tunda
idan ban manta ba da kika je Umra banda dabino na ganin idona babu abinda kika bata
kuma har yau ban ji korafinta ba. Idan kuma tafi yiwa Rukayya tsaraba ina jin ba
sai na gaya miki dalili ba kema kin san dalilin ko. Saboda haka ki fita ki bani
waje so nake na huta ba wai surutunki nake son ji ba.’
A fusace tace
‘Dole ka koreni tunda ka kasa yi mana adalci, tafiya Dubai din ma ai ba haka aka
tsara ba amma da yake abun duk shiri ne sai kuka wuce da matarka saboda kai kanka
ka san ni ya kamata ka fara zuwa dani wata kasar ba ita ba. Yara kuma ai da kudin
ubansu aka yi sayayya don haka sai ayi musu adalci ni din dai da aka raina sai a
cigaba da murdewa hakki.’
Mamakinsa ya karu saboda ya kasa gane dalilin wadannan maganganun da take zubawa
haka barkatai. Yayi tsaki yace
‘Zahra, Aisha ita ta biyawa kanta kudin zuwa Dubai kuma duk wata tsaraba da ta yiwo
kudinta ta saka tayi, zabi ya rage naki ko ki yarda ko kada ki yarda. Idan dai
wannan shine rashin adalci to an ki ayi miki adalcin idan kina da karfi ki shake ni
nayi miki adalcin. Ki fice min daga daki so nake na huta bana son wannan
hayaniyar.’
‘Shikenan saboda ka auro fitinanniya ba zan gaya maka gaskiya ba sai ka dinga
korata, to wallahi…'
Ta share zafafan hawayen da ya gangaro kan kumatunta; ya kasa yi mata adalci yanzu
kuma zai raba mata kan yara. Ta tabbatar wanna shirin Aisha ne. Kuma saboda ita ya
mayar da ita ‘yar matsiyata shikenan komai sai ya bawa Aishan kudi yace da kudinta
takeyi bayan musamman ta sa aka tambayar mata albashin Malaman gwamnati. Ta
tabbatar kudinsa ne Aishan take facaka da su haka, amma zata yiwa tufkar hanci.
Yana fita ya kirawo Aliko suka fice, ya kaishi gidan Yaya Bello. Can ya zauna har
dare, ya shiga gidan Hajiya inda ya zauna suka ci abinci sannan ya kamo hanya ya
dawo.
Lokacin da ya shiga gidan babu kowa a falo sai Rukayya da take zaune bata komai
yayinda Yusra take kan dining table tana yin homework. Bayan ya amsa sannu da
zuwansu yace
Ta shige dakinsu na kasa inda nan suke ajiye tarkacensu shi kuma ya haye sama,
bayan ta fito ta haye sama.
Yana zaune a falon yayinda Mommy take zaune itama tana kallon TV, bayan Mommy ta
amsa sallamarta tace
‘To.'
‘Abba.’
Ta ajiye jakar makarantar dake bayanta a kasa ta koma dakin kasa da gudu ta dauko
keken a kwalinsa, yana jin lokacin da Yusra ta faki idonsa tayi tsaki yace
Tana zuwa kusa da shi ya karbar mata keken ita kuma ta dauki jakar suka fice.
Tunda aka shigo da keken take so a tayata ta hada amma kowa sai gwasaleta yake yi,
Saddiku yana so ya hada mata amma kiri-kiri Mommy tace a dauke keken a ajiye ba za
ayi amfani da shi ba sai an siyowa Yusra irinsa. Ita Yusra bata ma sha’awar dinki
kwata-kwata, jaka da turaren da aka bawa Rukayyan ya fi tsaye mata a rai saboda
tana jin itace babba ita ya kamata a fara bawa, amma da ta sami goyon bayan Mommy
sai ta koma jin haushin keken ma. Don ta ciwa kanta alwashin idan dai ba a saya
mata irinsa ba sai ta lalata shi.
Ko da suka fita da keken nan ba karamin dadi Rukayya taji ba; don dama tunda taga
yanda Mommy take gwalewa ta yanke shawara gidan Antin zata mayar da shi idan ya so
in tana can tayi dinki ko idan Amira ta zo.
Bayan ya kaita ya yiwa Aishan sallama kuwa yana fita suka saka keken a gaba ita da
Aisha saida suka hada shi wajen dayan dare sannan suka kwanta.
--------
Duk yanda Mommy ta so morewa a wannan daren bata samu ba domin yana dawowa ya rufe
gidan ya shige dakinsa ya kulle. Haka ta kwana tana takaicin yanda yake Raina mata
hankali.
__
Duk wata tsaraba da Abban ya siyowa yara haka ya tattara ya kulle ya ajiye a gidan
Aisha; tunda Zahra ta saka shi a gaba da maganganun nan yace ba zai bayar da
tsarabar don haka har abinda ya siyo mata duk ajiyewa yayi. Wasu ma duk sai ya
kwashe ya kaiwa mutan gidan Yaya Bello wadanda ba zai iya bayarwa ba kuma kamar
computer da wayar da ya siyowa Yusra da niyyar in ta gama SS 3 ya bata duk ya
tattara ya ajiye.
Saida sukayi sati da dawowa sanna Zahra ta samu ya dan fara sauraronta, don haka
nan da nan ta samu ta sanar da shi ana biki a gidan su Amina zasu je. Ba tare da
wata matsala ba ya bata dama.
…..
Kwanan su Abba goma sha uku da dawowa Zahra ta shirya ta fice ranar Alhamis da
sunan ta tafi biki, karfe goma na safe suka kama hanyar Doguwa.
Sun ci sa’a wannan zuwan babu kowa a wajen don haka kai tsaye aka kaisu dakin da
suka gurfane a gaban bokan.
Bayan sun gama yi masa bayani da sanar da shi Abban ya dawo yayi gyaran murya yace
‘Ba ma aiki ranar litinin, Alhamis da Juma’a . Don haka ranar asabar da daddare ki
tabbatar ya kwana da janaba mu kuma za muyi miki aiki.’
Ya ware tafi hannunsa sama, nan da an aka jefo masa wani mulmulallen farin gilas
mai fasalin kwai. Ya turowa Zahran yana fadin
‘Ki saka wannan a wannan bakar robar ta gabanki ki rufe, ki nemi waje ko ina ne ki
boyeta. Matukar ba a bude wannan robar ba to sai yanda kikayi da Yusuf, domin ko
Sallah kika ce kada yayi to bazai yi ba balle wani aiki na duniya.’
Ta karba ta fara kici-kicin sakawa a robar da take gabanta yayinda dakin ya rude da
dariya.
Haka aka dinga nanata musu har suka fice daga dakin suka kamo hanya.
Abun ya dan so ya tsorata Zahra sai dai idan ta tuna zai manta da Aisha a rayuwarsa
sai abun yayi mata dadi. Ta dai san ta kashe kudi da yawa, domin kusan miliyan guda
kenan wancan zuwan da wannan. Gashi ragowar kudaden da take shirin karawa a
business dinta duk tana ta facaka da su.
……….
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
31
A tsaye take a tsakar dakinta tana tunanin inda zata boye bakar robar nan da boka
ya bata. Ta duba robar ba zata shiga bayan wardrobe din ba kuma bata so ta saka ta
a cikin wardrobe din saboda waje ne da take yawan budewa. Kayan dakin nata irin
Turkish Furniture din nan ne masu girma da nauyi don haka kusan ba a taba motsasu
ba tunda aka kafa su. Nan take dabara ta fado mata.
Ta karasa ta ajiye robar a kan durowar gefen gadon sannan ta dage iya karfinta ta
daga katifar daga daidai kan gadon, ta daga katakon ma sannan ta dauko robar a
hankali ta ajiye a kasan katakon. Ta mayar da komai ta gyara gadonta; a nan kam
tana da yakinin babu wanda zai motsa mata gado sai idan itace ta saka kuma babu mai
duba mata.
Ta yiwa kanta murmushin jin dadi sannan ta fice daga dakin.
___
Ranar Juma’a ce don haka da yake Yaya Zainab bata zo wa Aisha sannu da zuwa ba sai
yau ta zo. Gaba daya ita da su Amira suka zo da yake babu islamiyya.
Lokacin da direbansu ya saukesu a bakin gate din gidan Aisha yayi dai-dai da
lokacin da Malam Ali ya kawo su Rukayya da makaranta.
Yusra ta balla musu harara duka su biyun, don haka sukayi shiru.
Har suka shiga gida Rukayya tana tunanin yanda zata samu ta je wajen Amira; tana
son taje ta nuna mata keken dinkinta don ita Amiran tana da nata ta ma fi Rukayyan
iya dinki, amma ta san ba za a barta taje ba.
Idan Abba ya rakata da daddare ta taya Aishan kwana, da safe idan ta fito suka tafi
makaranta to Mommy ta haramta mata komawa gidan har sai wani daren idan Abban yayi
magana. Idan bai yi magana ba to ita bata isa tace zata je gidan ba.
Yau din dai haka kawai take so taje gida su dan taba dinki kafin su Amira su tafi.
Ta riga ta fidda rai don in dai Yusra taga fitarta to ta san ko ba gidan Anti
Aishan taje ba cewa Mommy zata yi can taje, kuma ta san tabbas sai Mommy ta ci
mutuncinta.
Wajen karfe uku babu kowa a falon daga ita sai Ummi, ta mike ta dauki hijabinta.
Ummi ma duk da bata san ina zata je ba ta mike tace
Suna shiga ta gaida su Anti Aishan a falo ta ja Amira suka kule a daki suna ta fama
da keke, ita kuma Ummi ta zauna wajen su Hanan kannen Amira a falo suna wasa.
Nan sukayi la’asar sai wajen biyar na yamma sannan direban su Amira ya dawo ya
kwashesu, suna tafiya Rukayya tayiwa Aisha sallama ta ja Ummi suka fice.
Ta san zata sha fadan Mommy don haka a hankali ta shiga gidan tana fatan Mommy bata
nemeta ba.
Tana shiga falon taci karo da Mommy a zaune tare da Yusra da Nana, da sallama ta
shiga amma babu wanda ya amsa sallamarta. Kallon da Mommy take mata ya tabbatar
mata tana cikin matsala. Kafin ta gama tsara karyar da zata gayawa Mommy muryar
Mommy din ta katse mata tunani
‘Gani Mommy.’
‘Um Mommy gidan Anti Aisha daman naje wajen Amira, sun ma t…'
Kafin ta rufe baki ta dauketa da mari, ta dafe kumatun bakinta a bude ta sunkuyar
da kai tana fitar da kwalla. Ummi da take tsaye ta raba ta wuce bayan kujera saboda
kada a mareta itama. Cikin fushi Mommy ta cigaba
‘Ba na hanaki zuwa gidan matar nana ba? Itace ta haifar min ke ne ko me da zan ce
kada ki fita ki saci jiki ki fice harda daukar ‘yar rakiya? Uban me take baki idan
kin je da bazaki zauna cikin ‘yan uwanki ba? Wallahi ki shiga hankalinki Rukayya,
idan ba haka ba zamu sa kafar wando daya dake a gidan nan. Tashi ki bace min da
gani kafin na mangareki.’
‘Ummi.’
Mommy ta kirawota cikin tsawa, ta leko daga bayan kujera tana zare ido
‘Idan na sake ganin kin shiga wannan gidan sai na zaneki kuma na karya kafafunki.’
A sanyaye tace
Yusra tace
‘Mommy ba fa laifinta bane, waccan uwar shisshigin ce don ita kowa ma bata ki yaje
gidan ba tunda bata gane mai sonta da mara sonta.’
Ta tashi ta haye sama ta barsu a nan Yusra tana kara jawa Ummi kunne.
………….
Rukayya tana shiga dakin su ta wuce bandaki ta turo kofa, don ta san idan ta zauna
a dakin ma yanzu Yusra zata biyota ta zo tana gaya mata maganganu.
A bushe bandakin yake don haka tana shiga ta zauna a kasa daga gefen bahon wanka ta
hada kai da gwiwa ta kara rushewa da kuka.
Mommy bata dukansu, ba karamin laifi mutum zai yi a gidan nan ba Mommy ta dokeshi
amma ita gashi yau Mommy ta mareta kawai saboda ta je gidan Anti Aishan. Ta san
Mommy din ta hanata zuwa amma ai Abba ne yace ta dinga zuwa; ko kuwa Mommy kawai ya
kamata ta dinga yiwa biyayya? Ta san Yusra ce zata zauna ta tsarawa Mommy karya da
gaskiya kuma ita ta zuga akayi mata wannan marin; duk da haka kuma ta san Mommy din
ta fi son Yusra a kanta. Tunda da bakinta mommy din tana fada Rukayyan ‘yar Abba
ce, kuma duk wata mu’amalar da take yi da su yana nuna tana son duka yaran fiye da
yanda take sonta. Don ita ko doguwar hira bata fiya hadasu da Mommy ba saboda da
zarar ta fadi ra’ayinta sai Mommy din su hadu da Yusra suce bata da hankali bata
san ciwon kanta ba, ko kuma idan tayi wani abun Mommy tace wai bata da wayo kamar
Anti Murja ko tace halin Abbanta ta gado.
Ta sa hijabinta ta goge hawayenta, bata jin dadin yanda Mommy take mata; ta kasa
fahimtar abinda ya sa Mommy take ganin kamar Anti Aisha cutar dasu zatayi don ita
abubuwa da yawa na ‘yan mata a wajen Anti Aishan take koya saboda tana sauraronta
tayi surutu son ranta. Ba zata iya kinta ba ko don Abbanta, sai dai kawai tana son
Mommy ta so ta ko Yaya ne don a yanzu zata iya cewa Mommy bata sonta; duk da abu ne
da ta sani tun kafin Abba ya auro Aisha.
Ta mike tsaye ta fara wanke fuska tana fatan Allah yasa kada Yusra ta kulata don
yau idan ta kulata duk wani haushi da take ji sai ta huce a kanta.
Haka ta wuni cikin damuwa har dare yayi Abban ya rakata gidan Aisha, ita kanta
Aishan tana ta faman tamabayarta ko bata da lafiya saboda yanda ta ganta; sai kawai
tace mata cikinta ne yake ciwo amma ta sha magani. Haka ta kwana babu walwala.
___
Tunda suka dawo daga wajen boka take tunanin yanda zatayi ta sa Abban Sadiku ya
kwana da janaba. A iya zaman aurensu da shi zata iya cewa idan banda satin
amarcinsu na farko bai taba kwana da janaba ba, duk yanda ya kai ga shagala sai
yayi wanka yayi alwala. Ko da zai sake dawowa to sai dai idan yayi wanka kuma yana
gamawa zai sake yin wanka. Gaba daya tunaninta ya kare, gashi yau Juma’a ta rasa ta
ina zata kama abun.
Tana zaune a dakinta a kan dadduma ta idar da sallar Magriba dabara ta fado mata,
gara ta kirawo Amina don ta san ba zata rasa dabara ba.
Tana bugawa tayi sa’a, bugu daya Aminan ta dauka, bayan sun gaisa ta sanar da ita
halin da ake ciki. Tace
‘Ai da kin gaya min tuntuni, kin manta ne da Hajja. Akwai wani yaji da zata baki da
kuma turare, wallahi in kikayi amfani da shi to sai dai kawai nace kema ki shirya
don zai yi ta aiki ne daga ya juye zai sake laluboki. Ba zai ma sami sukunin wanka
ba. Bari nayi mata waya, ko da yake kema ki kirawota na san gobe da safe zata iya
kawo miki.’
Nan take tayi mata sallama suka ajiye waya ta kirawo Hajja, tayi mata bayanin duk
abinda take so ita kuma tayi mata alkawarin gobe kafin azahar zata kawo mata kayan
aiki.
Sai yanzu ne ta sami natsuwa, fatanta kawai kada a sami wata matsala musamman idan
Abban yaki bata hadin kai. Amma dole ne tayi iya yinta saboda ba zata yarda Aisha
ta rabata da mijinta ba, gashi yanzu kiri-kiri ta fara janye mata hankalin yara.
Tana mamakin abinda ya sa Rukayya take son matar nan duk da dai ta san karshenta a
wajen kwanan da take zuwa tayawa za a bata abubuwan da zasu saka a mallaketa.
Tabbas dole ta mike tsaye ta raba Rukayya da matar nan.
Tana matukar son Rukayya tun lokacin da ta haifeta kuma har kawo yanzu, duk cikin
yaranta babu wanda yake kama da mahaifiyrta kamar Rukayya, domin da ta haifi
Rukayyan ma sunan mahaifiyar ta taso sakawa. Sai dai lokacin da aka haifi Rukayyan
Abbanta ya tafi aikin Hajii don haka Yaya Bello ne a kan komai, shi kuma bai yi
shawara da kowa ba ya saka mata Rukayya. Wanda Abban yace hakan yayi, don haka suna
ya bita. Shine saida aka haifi Ummi aka sa sunan mahaifiyar tata.
Duk da haka Rukayyan tana fara girma dabi’unta suka koma kamar na babanta. Ga
saukin kai da hakuri, komai zata ce ba komai bane, ga rashin wayo. Sai kuma ya zama
ta fi shakuwa da Abban saboda ya fi sauraronta fiye da Mommy din.
Amma yanzu duk abinda ta gani a tattare da Rukayya gani take Aisha ce take sakata
don haka ta yi shirin dole sai ta rabasu ko ta wane hali.
---------
Ranar asabar tun kafin azahar Hajja ta kawo mata abin da ta bukata; wani gari ne
dan kadan wanda tace mata gaba daya zata juye masa a miya sannan kuma da wani
turare wanda zata shafa a jikinta dai-dai inda zai dinga shakar kamshin saboda
kamshin turaren zai dinga kara kunnashi koda ya gama biyan bukatarsa. Sannan kuma
ita kanta aka bata kayan da zata yi amfani da su saboda kada ta gaji.
Yana matukar son couscous da miyar alaiyahu wanda ita kuma bata son couscous din,
don haka ma bata yawan yin couscous. Amma yau da yake da akwai abinda ta shirya sai
ta dafa masa couscous din da miyar alaiyahu wadda ta sha kifi da nama duk don ta
badda kama.
Wajen karfe takwas da rabi na dare bayan ya dawo daga sallar isha’i ya raka Rukayya
gidan Aisha don ta tayata kwana kamar yanda ya saba. Kafin ya dawo ta riga ta jera
abincin a kan dining table. Bayan ya zauna ta zuba masa abincin ta ajiye sannan ta
wuce kitchen ta zubo indomie din da ta dafa domin ta ci, ta zauna a kujerar da take
gefen tasa. Ya dubeta yana dariya
Tayi dariya
‘Ai ko ban fada ba ma haka ne, wallahi ni ban san me kike ci na dadi ba a cikin
couscous gara nayi ta cin indomie.’
Haka ya cinye couscous din nan yana ta faman yi mata surutu har sai da ya kara.
Bayan ya rufe gidan ya dawo ya zauna a falon sama tare da ita suna hira yayinda
Sumayya da Ummi suke wasanninsu.
A al’adarsa sai wajen sha daya na dare yake kwanciya amma yau tun wajen karfe tara
ya fara neman dalili, sai dai Sumayya ta ki yin bacci. Don haka ya dubi Mommy yace
‘Bari naje idan kin shirya kya sameni a dakin, naga mutuniyar taki yau hira take
ji.’
Sai da ta gama yangarta ta gama nata yi lokacin wajen karfe sha daya, ya gama
zakuwa ta yanda shi kansa mamakin abinda ya janyo masa hakan yakeyi sanna ta shigo
dakin. Tana shiga dakin kuma ta yarda zaninta a gefen gadon da yake kwance ta tsiri
wata kaiwa da kawowa. Ta shiga bandakinsa tayi brush, ta fito ta kama zarya kamar
mai neman wani abu a daki. Sai da ta tabbatar ya gama zakuwa sannan ta kashe fitila
ta kwanta a kusa da shi. Tana kwanciya ya fada mata kamar wani mayunwacin zaki.
Tun sha biyun dare suke abu daya amma ya kasa gamsuwa, ko da ya gamsu kafin ya
tashi sai kuma yaji yana bukatar kari. Tun yana jin dadi har ya fara mamaki saboda
bai saba samun irin haka ba. Watakila dai zai iya tunawa ya sami shigen hakan
lokacin da ya dinga kasa yin komai a kwanan Aisha, sai dai a wancan lokacin ba kasa
gamsuwa yake ba sai bayan ya gamsu sai ita Zahran ta kara laluboshi. To ko dai
yanzun ma wani abun Zahra ta bashi yaci a abincin dare. Haka ya cigaba da hidimar
nan yana yi yana tunanin da safe tabbas sai ya binciki Zahra.
Sai can gefin asuba wani bacci mai nauyi ya dauke shi, tunda ta duba taga yayi
bacci kuma ta tabbatar baccin nasa yayi nauyi sosai sai ta zare jikinta ta fice
daga dakin; domin itama ta gaji duk jikinta ciwo yakeyi.
Sai da aka idar da sallar asuba a masallaci gari ya fara wayewa sannan ya farka
daga bacci.
Firgigit ya tashi zaune, ya janyo wayarsa ya duba lokaci yaga shida saura kwata.
Yace
‘Subhanallah.’
Ba zai iya tuna lokacin da ya makara sallar asuba ba koda kuwa bashi da lafiya, nan
yayi addu’a ya sauko daga kan gadon ya fada bandaki.
Har ya idar da sallah yana mamaki, sai dai ya kasa tuna mamakin me yakeyi, ya kasa
tuna abubuwan da suka faru a daren jiya. Yana nan zaune a kan daddumar har
kwakwalwarsa ta fara gajiya da kokarin da yakeyi ya tuno me ya makarar da shi
sallar asuba amma ya kasa. Bacci kawai yake ji don haka ya tashi lokacin ya fara
jiyo hayaniyar yara suna shirin tafiya tahafiz, ya koma kan gadon ya kwanta bacci
ya kwasheshi.
Sai wajen karfe goma sannan ya fito, zuwa lokacin ta riga ta jera abincin safe a
tebur. Nan ya zauna ya gama cin abincin, bayan ya gama ya fice ya tafi gidan
Hajiya.
--------
Tunda suka dawo daga Dubai sai yanzu ne ta huta ta dawo dai dai duk wata gajiya ta
rabu da ita, don haka tun asuba da ta tashi ta sa Rukayya ta tayata suka gyara
gidan tsaf, har inda ma bata gyara ba tunda ta dawo. Karfe tara saura kwata Rukayya
tayi wanka ta shirya ta fice don tafiya tahfiz, tayi mata sallama a kan sai an
kwana biyu tunda ta san yau Abba a nan zai kwana.
Ko da taga Bai shigo ba da rana ta san gidan Hajiya ya wuce duk da ya saba yi mata
waya ya sanar mata in ya wuce Amma yau shiru. Ta dai San sai dare zai dawo.
Ragowar abincin da ta dafa da safe shi taci da rana, sai bayan la’asar sannan ta
tuka tuwon shinkafa da miyar agushi. Tana saukewa ta ci ta koshi sannan ta zuba
musu na dare a flask ta jera a table.
Ana yin sallar Magriba kamar yanda ta saba tayi wanka ta kunnawa gidan turaren
wuta, nan da nan kamshi ya karade gidan. Ta shirya ta dawo falo ta zauna tana jiran
shigowar maigidan.
Karfe tara daidai na dare NEPA suka kawo wuta don haka ta mike ta kunna TV, ta
kalli agogon bangon taga lokaci. Tana mamakin abinda ya sa har yanzu Abba bai shigo
ba; ya saba wuce karfe tara bai shigo ba amma indai zai yi haka to ana yi sallar
isha’i yake kiranta ya sanar da ita ba zai shigo da wuri ba. Amma yau din bai shigo
ba kuma bata son kiranshi musamman idan ta san yana gidan Zahra.
Ta zauna ta dauki remote ta fara canza channel tana laluben abinda zata kalla.
Ta cigaba da kallo duk da hankalinta ya kasa kwanciya kuma ta kasa kiransa. Wajen
karfe goma saura yunwa ta fara damunta don haka ta tashi ta zubi tuwonta ta zauna
ta fara ci. A hankali take cin abincin don haka ta dauki lokaci kafin ta gama.
Bayan ta kai kwanon kicin ta hado shayi ta dawo ta zauna, ta dauki wayarta ta duba
lokaci; karfe goma da minti goma.
Hankalinta bai kwanta da wannan rashin kiran nata da bai yi ba don haka ta daure ta
danna masa kira. Haka ta dauki lokaci tana ta faman kiransa amma wayar bata shiga,
kamar dai yana wajen da babu network.
Mamakinta ya tsananta don bai gaya mata zai tafi kauye ba ko wani waje da babu
network. Haka ta hakura ta ajiye wayar ta zauna tana ta wasi-wasi.
Tana nan zaune har wajen karfe sha biyu saura bai shigo ba kuma bai kirawota ba
gashi wayarsa ta ki shiga. Zabi daya ya rage mata taje gidan Zahra ta tambaya, to
amma gaskiya bata son shiga gidan nan ko da rana balle kuma da tsohon daren nan.
Tana da lambar wayar Zahra amma bata taba kiranta ta dauka ba, don haka ma ta
hakura ta daina kiran.
To yanzu wanne zata yi?
Idan zuwan ne ma ita ba zata iya fita waje yanzu ba. To amma ai tabbas da da wani
abu da zata ji; to kenan lafiya kalau zuwa gidan ne ba zai yi ba ko me?
Ta mike tsaye ta fara zarya a falon, sai da ta gajib ta zauna ta sake duba agogo;
karfe sha biyu da rabi.
Bata da wata mafita illa ta kirawo Zahra, a kalla ko da gaya mata tayi cewa yana
lafiya shikenan sai ta kwantar da hankalinta ta rufe gidan ta kwanta.
A al’ada da rana yake canza gida idan ya gama kwanan mace, idan ya ci abincin safe
shikenan kwanan sun kare sai an sake kwana biyu.
Ranar Lahadi a gidan Aishan ya kamata yaci abincin rana amma sai ta ga bayan ya
dawo daga gidan Hajiya ya shigo yace mata ta sa masa abinci zai zo ya ci. Ya shige
dakinsa ya barta tana neman taka rawa saboda murna. Ba ma ce mata yayi ta dafa masa
abinci ba kawai yi yayi kamar dama a nan ya saba cin abincinsa kullum. Nan da nan
ta shiga kicin ta zubi masa abinci ta sa a table.
Nan ya wuni bai sake fita ba kuma bai nuna alamar zai tafi gidan Aisha ba.
Dare nayi ta gabatar da abincin safe suka ci suka kwanta kamar yanda suka saba.
Fari tas take jin zuciyarta saboda dama tana bakin cikin raba kwanan da yake musu
da Aishan.
Shabiyun dare ta gota ta farka daga bacci, yana kwance a gefenta yana bacci. Bata
son ta tasheshi don haka ta dauki wayarta ta haska don ta dubo yara. Ta shiga dakin
su ta tashi Ummi ta sakata a fitsari, ta gyarawa Sumayya kwanciya da yake ita
diaper ce a jikinta. Ta fito daga dakin kenan wayarta ta fara vibration, ta kalli
screen din wayar tayi dariyar mugunta sannan ta amsa wayar ta shige dakinta.
A tsakiyar dakin ta tsaya don ba so take wayar ta dauki lokaci ba, bayan sun gaisa
tace
‘Dama Abban Sadikne bai shigo ba kuma na kirawo wayarsa bata shiga shine nace ko
lafiya.’
‘Kema ina baki shawara kije kiyi baccinki, idan dai mininane Yusuf uban Sadiku to
bazaki sake jin duriyarsa ba. Ya manta dake ya goge babinki a rayuwarsa, ko da me
kike takama kuma ya fi karfinki, duk lokacin da kika gaji sai ki tattara kayanaki
ki koma gidanku. Kuma don Allah kada ki sake kirana a irin wannan daren muna kwance
da mijina.’
Bata saurari amsarta ba ta katse wayar , ta kashe fitila ta koma dakin Abban tayi
kwanciyarta zuciyarta cike da jin dadi.
………..
Mutuwar tsaye Aisha tayi a nan inda take, bata san me take ji ba; mamaki ne ko kuma
takaici. Kafarta ta fara kasa daukarta don haka ta zagaya ta zauna a kan kujera ta
dafe kai. To wannan maganganun na Zahra me suke nufi? ‘duk lokacin da kika gaji sai
ki tattara kayanki ki koma gidanku’.
Ta muskuta tace
‘Ikon Allah!’
Kwakwalwarta ta kasa jeranta tunaninta, don haka kawai ta runtse idonta tana
maimaita
Ta jima a haka kafin ta bude ido, ta kalli agogon bangon wanda ya nuna karfe dayan
dare da minti biyar.
Duk da bata gane me yake faruwa ba amma dai ta san ba zai zo gidan ba, ko da zai zo
to ta san tabbas ba yau ba. Don haka ta mike ta sakawa kofar gidan kwado ta rufe ta
kashe fitilun ta shiga dakinsa da niyyar kwantawa. Har ta saka kayan bacci sai kuma
ta koma bandaki ta dauro alwala; babu yanda za ayi tayi bacci bayan wadannan
maganganun da Zahra ta gaya mata.
Sai da ta dauki lokaci tana Sallah sannan ta bi da addu’oi, tayi karatun kur’ani
sannan ta kwanta.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
32
Ko da gari ya waye ranar litinin ce don haka Aisha bata ma tsaya jiran wani abu ba
ta shirya ta wuce makaranta; sai dai kawai wunin ranar a cikin wasi-wasi tayi shi.
Haka ta wuni tana kiran layin Abban ko shiga wayar bata yi har ta gaji ta hakura.
Bata san abinda zata yi ba bayan wannan don haka ta hakura ta zubawa sarautar Allah
ido wata kila zuwa kwana biyu a sami mafita.
Abu daya ne yake firgita ta idan ta tuno abubuwan da suka dinga faruwa a lokacin da
yake kasa shiga gidanta; bata son ta yarda wani asirin aka sake yi yanzun amma dai
tabbas biri yayi kama da mutum
………..
A hankali har gashi an wayi gari yau Juma’a, ko sau daya Aisha bata ji daga Abba ba
kuma bata sa shi a idanunta ba.
Kamar yanda ta saba duk ranar Juma’a in ta tashi daga makaranta gidan Umma take
wucewa don taje wajen yaranta to yau din ma haka tayi. Ana tashi ta wuce ta dauki
su Abdallah a makaranta sannan suka wuce gidan Umma. Suka baje kayansu Anti Uwani
ta shiga hidima da su.
Can bayan sallar la’asar sai ga Zahida itama sun zo da yaranta harda maigidanta
wanda bayan ya gaida Umma ya fice ya barsu a can sai dare zai dawo ya daukesu.
Suna zaune a dakin Anti Uwani ita da Zahida suna hirarrakinsu Aishan tace
‘Kin san wani abu Zahida, ina jin fa mutuniyarki tayi sabon boka.’
‘Kai Jama’ah wannan Yaya taki ba dai himma ba! Allah ya sa dai bata taba ki ba.’
‘Ni ai na rigata na ce Allah kuma Allah ya sani bani da niyyar cutar da ita don
haka Allah ba zai bata iko a kaina ba in sha Allah, mijinta dai ta taba.’
Sukayi shiru na dan lokaci Zahida tana rike da bakinta tana kallon Aishan, jimawa
kadan Aishan ta cigaba, ta bata labarin abinda ya faru sannan tace
‘Yanzu dai maganar da nake miki tun lokacin rabona da shi don ko waya nayi masa
bata ma shiga ban san me yake faruwa ba.’
Zahida tace
‘Ke Yaya Aisha, to ke yanzu haka zakiyi ta zama? Kamar wata wadda take zaman
kanta.’
‘To ai sai ki dawo gida tunda kinga can kina zaune ne ke kadai, ki dawo nan in ya
dawo hayyacinsa sai ki koma.’
‘Kin san Allah Zahida, ba zan bar gidan nan ba ina nan a cikinsa. Abinda take so
kenan ace na bar gidan, ina jin ta kasa sakashi ya sakeni shi yasa ta bullo da haka
kinga idan na tafi ai daga nan sai na nemi saki ko da akotu ne. To wallahi ina nan
ko da me take tsafi sai naga karshensa, ita halittar Allah kaskantaciyya ta rike ni
kuwa Allah Azza wa Jalla shi kadai na rike don haka na san abun nata na lokaci ne.
Da ni da ita shege ka fasa!’
‘Kai Aisha nifa wannan abubuwan sun fara bani tsoro, to ai sai a gayawa Umma ko
addu’a nei ayi. Ni zaman ma nake ji ke kadai kamar wata mara gata.’
‘Na san dole zan fada amma na kara bawa abun lokaci tukunna, amma in sha Allahu sai
na nuna mata karya fure take bata ‘yaya.’
Nan suka karasa wuninsu sai bayan magriba sannan Aisha ta tuko motarta ta dawo
gida. Tana shiga ta mayar da gidan ta kulle don ta san babu wanda zai sake shigowa.
…………
Kwanci tashi har an yi sati biyu rabon da Abba ya nemeta, zaman gidan haka ita
kadai ya fara damunta. Gashi anyi hutun makaranta don haka babu inda take zuwa sai
dai kawai taje islamiyya ranar asabar da halidi sai gidan Hajiya.
Don haka taje ta tsara Yaya Zainab ta dauko Amira; tun da zuwa yanzu duk sun san
matsalar da take ciki, Yaya Abubakar ne kawai basu gayawa ba. Babu yanda basuyi da
ita ba a kan ta koma gidan Hajiya amma ta ki don haka ma aka kyaleta. Haka aka bata
Amira tunda Amiran tayi candy yanzu sai jiran admission da takeyi wanda ko da ya
fito Aisha zata iya daukar nauyin kaita makarantar da daukota.
Daga ita har Amiran ba fita suke a unguwar ba balle su hangi koda yaran ne, domin
itama Amiran Aishan ce take kaita islamiyya a motar ta daukota.
A haka karshen wata ya kare tana ta sa rai taga an kawo mata cefane ba a kawo ba,
don haka dole taje ta yiwo cefanenta da akayi albashi. Duk wani abu da suke bukata
ita da Amira ta siyo ta ajiye musu.
_
Cikin farin ciki take gudanar da rayuwarta tunda taga aikinta ya kama, ko da wasa
Abban Sadik bai sake maganar Aisha ba rayuwarsa kawai yakeyi kamar yanda ya saba
kafin ya auro Aishan.
Idan akwai wanda take jin zai iya bata matsala to Rukayya ce; don haka ta ja mata
kunne sosai kuma ta sanar da ‘yan uwan duk lokacin da aka ga Rukayyan ta shiga
gidan Aishan ko kuma ta kula Aishan ko da a unguwar ne a gaya mata. Don haka ta san
babu wanda zai yi maganar Aisha a gidan.
………..
Zuwa yanzu abu daya ta sa a gaba; mota take so Abban ya saya mata irin ta Aisha ko
kuma wadda ta fi ta Aishan. Ta riga tayi masa magana kuma ya amsa, ya dai sanar da
ita bashi da kudi amma ta bashi wata biyu zai samu sai a siya mata.
Gaba daya yanzu yanda ta tsara haka Abban yakeyi. Ta kula dai kamar bashi da
cikakkiyar nutsuwa amma wannan bai dameta ba tunda yana yi mata yanda take so.
Hannun Sadiku tuni ya warke, yana nan yana zaman jiran jarrabawar da zai maimaita
tare da ‘yan ajin su Yusra. Tun da hannunsa ya warke Abba ya saka shi a makarantar
da zai koyi computer kuma ya saya masa computer, sai dai bai je makarantar nan ya
kai na wata daya ba ya daina zuwa.
Idan ya fita sai kawai ya wuce gidan su abokinsa wanda suke kira Kolo su yi ta
shaye-shayensu a can, da yamma sai ya dawo gida. Duk lokacin da yake bukatar kudi
sai kawai ya cewa Abban zasu sayi wani abu a makarantar computer ko kuma ya gayawa
Mommy ita sai ta karbo masa kudin ta bashi ba tare da wani bincike ba.
Halin da Saddiku yake ciki yana sosa zuciyar Jummai saboda yanda take kaunar Uwar
Saddiku sai dai ta kasa gane abinda ya sa ita Uwar Saddiku bata ganin yanda yaron
yake canzawa. Ta san abinda ya faru da Rahma don tun daga wannan lokacin ma Rahma
ta ja jikinta don haka itama Jumman kawai sai ta kau da kai tana yi musu addu’a.
___
Yana zaune a falon sama wajen karfe uku na yamma yana kallon TV. Daga dakinta ta
fito inda ta kwantar da Sumayya ta karaso ta zauna a kusa da shi. Ya dubeta yace
Tayi murmushi
‘Uhm, ta kwanta ai in sha Allahu idan akayi hutu islamiyya za a sakata tunda ko
babu komai ta kai shekaru uku. Yanzu haka ma ta iya karatun kowa ga surutun tsiya.’
Suka yi shiru suka cigaba da kallon TV din kowa da abinda yake tunani.
‘To ai na gaya miki bani da kudi amma in sha Allahu kada ki damu kwanan nan za a
saya miki kota.’
‘To gani nayi ai saboda mota sai binka nake kana wani ja min rai, kullum sai kace
karshen wata amma in watan ya zo kuma sai kayi shiru. Ya dai kamata a duba don na
gaji da yawo a motar direba kawaye suna yi min dariya gaskiya.’
‘Kullum haka dai kake cewa, ai shike nan. Idan ma kudin ne naga ga dayar nan da ta
lalace a tsakar gida nace a hada da ita a sayar sai ka cika ka sayi motar.’
‘To ai motar da kike so a saya ta fi haka tsada, kada ki damu za a sayi mota. Ke
dai ki kara hakuri.’
Sukayi shiru na dan lokaci, jimawa kadan ta tashi ta fice ta nufi falon kasa.
Ta matsa sai ya siya mata mota kuma ga irin wadda take so; shi kuma a halin yanzu
bashi da kudin sayen irin wannan motar.
Gashi a halin yanzu baya iya yi mata musu kuma baya son ganinta a cikin damuwa,
wasu lokutan idan tace yayi mata abu har ji yake kamar an kuntata zuciyarsa har sai
yayi wannan abun da take so zai ji daidai. Don haka yanzun ma duk inda kudi suke
nemowa zai yi kawai ya saya mata mota.
………..
Kayan electronics din da ya siyo lokacin da suka je Dubai da Aisha suna nan anata
siyarwa, kokari yakeyi idan aka gama sayarwa ya hada uwar kudin da ribar ya sake
komawa ya siyo wasu kayan. Yana jin dadin yanda cinikin yake tafiya domin akwai
riba sosai, musamman da yake abokin kasuwancin nasa mai amana ne sosai.
…………
Ba wai dare ne yayi sosai ba amma da yake yanayi ne na sanyi yaran duk sun kwanta
har an rufe gidan. Shima Abban yana dakinsa a zaune a gefen gado yana 'yan dube-
dubensa a waya yayinda Uwar Saddiku take kasa tana kawar da abubuwan da suke a bude
kafin ta je ta kwanta.
Sai da ta gama kintsawa tsaf sannan ta sameshi a dakin. Bayan ya amsa sallamarta ta
kwanta a gefensa ta ja bargo ta rufe kafafunta.
Bata dade da kwanciya ba wayarsa tayi kara, ya amsa kiran sannan ya kara a
kunnensa.
Daga inda take kwance tana dan jiyo wasu daga cikin abubuwan da ake fada a daya
bangaren, bata ganewa amma so take ta gane don haka ta tattaro duk wata nutsuwarta
ta kara mikar da kunnuwanta don taji me za a cewa Abban.
Tun da suka fara gaisawa ta gane abokin kasuwancinsu ne Alhaji Abubakar; duk da
bata san shi ba dai amma ta saba da jin sunansa kuma ta san Abban yace shine yake
masa jagoranci wajen sayar da kayansa da ya siyo daga Dubai.
Bayan sun gaisa Alhaji Abubakar din ya sanar da shi akwai wani Alhaji da yake son
kayansa ya turo kudin kaya naira miliyan shida don haka Abban ya duba business
account dinsa yayi confirming don mutumin zai turo a debi kayan gobe da safe. Ya
kuma sanar da shi akwai wanda yake son kayan kallo da AC complete set guda biyu
amma shi so yake idan ya biya yaransu suje su hada masa kayan a gidansa sai ya biya
har kudin aiki. Sukayi sallama suka ajiye waya.
A take ya duba account dinsa ya tabbatar da shigar kudin, shi kansa sai da yayi
murmushi da yaga kudin. Ya tabbatar ya shiga harkar nan da kafar dama kamar yanda
Abubakar din yake gaya masa.
Ya kirawo Abubakar din ya sanar da shi kudin sun shigo don haka zai fito da wuri
gobe don suje gidan da ya ajiye kayan a dauka. Sukayi sallama suka ajiye waya.
‘Alhamdulillah gaskiya babu laifi in Sha Allahu kwanan nan zamu koma Dubai din a
kawo wasu kayan.’
Kwanakin nan har fargaba yake idan taji yana da kudi domin idan ta ji haka zata
dinga yi masa lissafin abubuwa yana siya har sai ta ga kudin nan sun [Link] ma
wannan maganar da tayi zuciyarsa ta fara bugawa da sauri ya san zata ce wani abu
don tabbas ya san sai ta ci kudin nan tunda ta ji su.
‘To ni dai gaskiya tunda an sami kudin nan a saya min motata in ya so daga baya ko
ma menene sai ayi, kada a bar ni ina ta jira. Ya kamata ace kafin satin nan ya kare
motata ta zo tunda dai kudin nan gasu nan sun shigo.’
‘Wannan ai kudin business ne ba da su za a saya miki mota ba, amma in Sha Allahu za
ayi kokari.’
‘Ka ji.’
Haka ta kwana tana farin ciki don ta san bai isa ya canza wannan maganar ba yayinda
shi kuma ya kwana yana lissafi; anya kuwa Zahra zata barshi ya hada kudin nan ya
sake yin business din, yanda take yiwa kudin gibi ya fara yawa.
…………
Tunda sukayi wannan maganar kuma sai ya zama kullum idan zai fita sai ta tuna masa
da motarta.
Don haka bayan kwana biyar da yin magana an gama cinikin kayan an diba haka ya
dauka a cikin kudin ya sayo mata mota irin ta Aisha sai dai ita tata ruwan gwal ce
ba baka ba.
Office aka kai masa motar bayan ya gama biya, daga nan kai tsaye yace a kai mata
gidan a bata mukullin; ya hada dan aiken da Malam Ali direba.
Suna fita ya kifa kansa a kan teburin da yake gabansa ya runtse idanuwansa; kwana
biyun nan jin kansa yake a cikin wani mawuyacin yanayi amma ya kasa fassara
yanayin. Komai ya daina yi masa dadi gashi zuciyarsa tayi kunci kullum yana cikin
damuwa amma be san me yasa yake duwar ba, ga kuma yawan fushi da yakeyi na rashin
dalili.
A waje daya ne yake jin dadi shine idan yana gidan Yaya Bello, don haka yanzu kusan
kullum idan ya tashi daga aiki gidan Yaya Bello yake tafiya yayi zamansa suyita
hira da Yaya har sai ya gaji sai ya fito ya koma gida. Yana kama hanyar gidan kuma
zuciyarsa zata sake komawa cikin damuwa.
Bayan son sayen motar nan amma idan Zahra tace yayi mata abu wasu lokutan baya ma
sanin yayi sai ya gama; motar ma a kan haka ya saya mata. Yana dai fatan Allah ya
sa kada ta kawo wata babbar bukatar idan ta gama dokin motar, don baifi wata daya
ba da ta saka shi a gaba sai ya bata dubu dari biyar ta kara jari kuma nan ma haka
dole ya bayar.
Ita kuwa Zahra ana kai mata mota da ta yi masa waya ya tabbatar mata tata ce ta
karbi mukullin mota ta fice, gidan Amina ta fara zuwa suka sha hira sannan daga nan
ta wuce gidan Yaya Murja ta nuna mata motar sannan ta dawo gida.
Ta riga ta saba yanzu sai wajen tara na dare Abban yake dawowa gidan, tunda ta
bincika ta tabbatar gidan Yaya Bello yake zuwa abun ya daina damunta.
Don haka yau din ma bayan sallar isha’i suka zauna a falon kasa ita da yaran don
cin abincin dare, suna ci suna hirarrakinsu wanda duk a kan motar Mommy ne.
‘Mommy ni dai don Allah ki sa Abban ya saya min waya, kinga mun kusa fara exam din
amma shi yace dole sai mun gama exams. Kawayena duk suna da waya kullum ayi ta
daukan hotuna babu ni ana min dariya. Kin ga Fathiyya Sulaiman ma iPhone ce da ita,
don Allah nima ki sashi ya saya min iPhone tunda na ga kamar yanzu yana da kudi.
Kin ga ma idan muka gama exam din ai an huta.’
‘Ai nace za a saya miki kafin ki gama exam din kuma iPhone din za a saya, yanzu ki
bari mu gani zuwa next week in sha Allah zai saya.’
Ummi tace
‘Mommy da Yaya Rukayya ma a saya mata wayar sai mu dinga yin game tare , ko Yaya
Rukayya?’
‘Ai na san Abban ba zai taba yarda ba ni na ma hakura sai na yi candy din tunda
Abba yace idan mutum yayi candy dashi za a je shop din ya zaba. Sai mu tafi tare ko
Ummi?’
Suka tafa.
Mommy tace
‘Ai kuwa kin hutar da mu.’
‘Mommy kin ji ikon Allah wai motarsu; wallahi Mommy ki hanashi hawa motarki tun
kafin a zo a kuma.’
‘Ki fadi alkhairi ko kiyi shiru, hatsarin irin wannan ba zamu sake ganinshi ba har
duniya ta nade.’
‘Gaya mata dai Mommy, mota dai sai na hau sai dai dan bakin ciki ya mutu.’
‘Sannu sarkin fin karfi, to wannan motar ba ta hawanka bace iyakacin ka da ita
kallo. Idan aka kwana biyu dai nayiwa Abban magana ya saya maka taka kaima.’
‘Allah Mommy, gaskiya amma da kin gama burgeni. Amma don Allah Mommy dalleliya nake
so kamar dai takin nan.’
‘Bari mu gani, ka maida hankali kaci jarrabawa kaga sai a ji dadin saya maka mota.’
Kafin ya amsa suka ji shigowar Abban gidan bayan da Malam Sajo ya bude masa gate.
Babu wanda ya mike da sunan yaje ya taro Abba sai Rukayya wadda ta mike tana fadin
Ta fice da sauri.
Jimawa kadan Rukayya ta shigo rike da jakar laptop din Abban da mukullin motarsa ta
wuce sama, bata gama hayewa benen ba yashigo yana rike da hannun Ummi yayinda yake
dauke da Sumayya.
‘Saboda motata ta tsufa shine aka saka min sabuwar mota a gareji aka koro tawa waje
ko?’
‘Wallahi mantawa nayi, lokacin da nayi parking din ne da akwai rana shi yasa wai da
naga mai wajen baya nan sai na dan fake ta a nan.’
Kafin ya kwanta bacci sai da ya yiwa abokansa waya ya sanar dasu an saya masa mota
gobe ma da ita zai fito.
Ko da gari ya waye da wuri Abban ya fita bayan Malam Ali ya fita da ‘yan makaranta,
shi kuwa Saddiku yana ta kaiwa da kawowarsa a falon kasa tare da Sumayya don ya
cewa Mommy sai karfe goma zai tafi computer school dinsa.
Sai da ya bari ta shiga wanka sannan ya shiga dakinta ya dauki mukullin motar ya
fice daga gidan.
Tana wanka ta ji an bude gate tayi zaton Malam Ali ne ya dawo don haka bata damu
ba.
A lissafinta idan ta fito daga wankan ma fita zatayi ta je gidan Suwaiba sannan ta
biya sahad tayi sayayya duk don ta kara dana motar; domin yanzu idan zata je unguwa
ta daina gayawa Abba sai dai idan babu direba a gidan ta kan gaya masa don ya turo
mata direba.
Sai da ta fito daga wankan ta gama shiryawa sannan ta fito daga dakin, tana fitowa
ta sauko falon ta sami Sumayya a kicin wajen Jummai, bayan sun gaisa da Jummai
tacewa Sumayya
Jummai tace
Har ta kama kafar benen hawa sama ta dawo ta leka tsakar gida, babu komi a garejin
Abba inda ta ajiye motarta. Take ranta ya baci; wato Saddiku sai da ya fitar mata
da mota kenan?
A fusace ta dawo cikin gidan ta haye sama, tana shiga dakin ta dauki wayarta ta
fara kiran lambar Saddiku. Ta kirawo shi ya fi sau goma amma bai dauka ba, don haka
dole ta hakura ta zauna tana ta faman cika tana batsewa. Gashi Malam Ali ma baya
nan balle tace masa ya kai ta.
Wuni guda Saddiku bai dawo gidan ba sai bayan magriba ya dawo; hakan ma don Abba ya
hanashi kaiwa dare a waje ne ya dawo. Ko da ta taso masa zata yi fada tsayawa yayi
yana mata muzurai yace mata jarabawa yayi a makaranta shi yasa bai dawo da wuri ba.
Haka tana ji tana gani ta hakura.
__
Sati biyu da sayen motar nan ta Zahra kuma ta saka shi a gaba da maganar ya sayawa
Yusra waya. Ko da Saddiku yaji ana maganar wayar Yusra shima sai ya sayar da tashi
wayar yace ta fadi. Don haka Mommy ta sa Abba a gaba saida ya sayi waya iPhone guda
biyu kowacce kusan dubu dari da saba’in.
__
Kwanci tashi Aisha tana lissafi yau wata shida rabon da Abba ya leka gidanta, duk
wata hanya da zata bi don taga tayi magana da shi abun ya ci tura. Duk wanda yake
da alaka da ita ko ta waya baya iya samun Abban a waya.
Idan Abba ya tashi biyan kudin hayar gidan Aisha na shekaru biyu yake biya, ita
bata ma sanin lokacin da yake biya domin kafin lokacin ya gama wucewa zai turawa
Jibrin kudin kawai ya biya.
Shekararsu ta hudu kenan da aure yanzu shekara ta hudun zata kare don haka lokaci
yayi na biyan kudin hayar.
Tun ana saura wata biyu shekarar ta kare Jibrin yake neman Abban, idan sun hadu sai
yayi ta zullewa yaki saurara maganar. Daga baya kuma sai ma ya kasa samunsa waya,
idan kuma yaje nemansa duk abinda zai faru ba zasu hadu ba. Masu gidan kuma duk da
sun san Abban amma sun saba ba shi yake biya ba Jibrin ne don haka suke ta faman
yiwa Jibrin din tuni.
Sosai ya shiga damuwa domin ya tabbatar karkari su kara wata biyu zasu sa Aisha ta
fitar musu daga gida su sa wani, tunda neman kudi suke da gidansu. Shi kuma gashi
bashi da kudi balle ya biya kuma ma saboda me zai biya?
Haka yayi ta kokarin ganin Abba amma basu hadu ba gashi yanzu ko ya kirawo Abban
wayar bata shiga. Baya son yaje gidan Aishan kuma tunda bai saba zuwa ba a zata
wani abu. Sai a hankali ya tuna ya taba kai matarsa wajen Aishan lokacin tana
amarya, don haka yana komawa gida ya sameta ya karbi lambar Aishan da niyyar gobe
idan ya shiga office sai ya kirawota domin gara ya sanar da ita koda tashi ne ta
tashi ba sai an zo an yi mata wani tozarci ba; don ya kula masu gidan sun fara jin
haushi.
__
A halin yanzu jarrabawa dalibansu sukeyi don haka malaman da basu da aiki su kan
zauna a gida suki zuwa makaranta. Haka itama Aishan tayi, domin tana kai Amira
makaranta sai ta dawo gida.
Zaman da take a gida ga damuwar Abba ya manta da ita ta kusan wata bakwai ya fara
damunta; don haka ta biya kudi aka koya mata yanda ake yin mayafai na zamani kuma
nan take ta sayi injin stoning da sauran kayan aiki ta fara yi.
Yau din ma da taki zuwa aiki zama tayi a gida ta yi wasu mayafai da aka bata
aikinsu guda shida.
Tana cikin aikinta wayarta tayi kara. Kafin su gama gaisawa ta gane muryar duk da
bata tabbatar ba. Yana yi mata bayanin kansa ta fara tambayarsa matarsa da sauran
iyalai. Bayan sun gama gaisawa yace
Nan yayi mata bayanin halin da ake ciki game da kudin hayar gidan da take ciki.
Bata taba wannan lissafin ba don haka bayanin nashi ya shammaceta. Ta dan yi jim
sannan tace
‘Um. Don Allah kace su dan yi hakuri zuwa gobe zan kirawo ka in Sha Allah kafin nan
munyi magana da shi.’
Sukayi sallama suka ajiye wayar.
Ita ta manta ma cewa a gidan haya take; gashi yanzu babu yanda zatayi taga Abba sai
ta hannun Zahra wadda ta san idan banda tozarci babu abinda zata yi mata.
To kuma ta san idan ta bari tabbas masu gidan zasu zo ne su tasheta; ita kuma tayi
alkawarin ba zata bar gidan nan ba har sai wannan tsafin da Zahra tayi ya karye
domin ta tabbatar yanda take addu’a da sadaka lokaci kawai ake jira.
Ta tuna bata ma san nawane kudin hayar ba don haka ta dauki waya ta kirawo Jibrin
din ta tambaye shi. Ya sanar da ita wancan karon dai dubu dari biyu da hamsin aka
biya amma yanzu sun ce dubu dari uku za a biya.
Yaya Abubakar ya kamata ta gayawa domin zai iya biya mata, sai dai ta san shi yanzu
zai ce ta tashi daga gidan don tun da yaji labarin yake so ta koma gidan Hajiya.
Sai da Baffa yayi masa magana yace ya bari abi komai a hankali domin shima ya sa
ana addu’a, kuma tunda Aishan ta nuna ita zata zauna bai kamata a raba ta da gidan
ba har sai komai ya warware. Don haka ta san yanzu idan taje masa da wannan maganar
kamar tana tuna masa ne.
To yanzu ya zata yi; ai duk inda ma kudi suke dole ta nemosu tazo ta biya kudin
hayar nan don ba zata bar gidan ba har sai Abba ya dawo hayyacinsa.
Gashi yanzu cefane da kula da gida ya koma kanta duk ita takeyi; lokacin da Abban
yana zuwa kuwa ko man motarta bata taba saye ba, da zarar tace babu mai zai turo
direbansa ya dau motar a ciko mata tanki; haka yake mata har wancan lokacin ma da
ya kasa shiga gidan bai taba fasawa ba.
Amma yanzu komai ita takeyi, hatta katin wutar NEPA duk ita take siya ga
subscription na TV da sauran cefanen gidan. Yanzu kuma gashi an ce mata kudin hayar
ya kare; tabbas dole ta nemi kudi.
Ta fara jiyo kiran sallar la’asar don haka ta mike; gara tayi sallah sai ta wuce
gidan Zahida suyi shawara tunda yanzu sai karfe biyar zata je ta dauko Amira daga
makaranta.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
33
Zahida tana kallonta ta tabbatar da matsala; bayan sun gaisa ta dubeta tana dariya
tace
Tayi dan murmushi tana mamakin yanda Zahida take iya fassara duk wani motsi nata
tun kafin ma tace wani abu, ta gyara zama tace
Ta dafa cinyarta
‘To ke Yaya Aisha ki koma gida mana, ya za ayi ma ki biya masa kudin haya? Ki tashi
ki basu gidansu ki koma gidan Hajiya tunda idan ya dawo hayyacinsa ya san inda zai
sameki.’
Ta jijjiga kai, tace
‘Ba zaki gane ba Hida. Ai na gaya miki ko zan bar gidan nan to sai ya dawo
hayyacinsa; kin san matarsa cewa tayi wai tana bani shawara na koma gidanmu, idan
na tafi ai bukatarta ta biya kuma in Sha Allahu bata isa ba. Ina nan sai karyarta
ta kare.’
‘Wa! Wannan ai kadan yake jira ya murdewa auren nawa wuya saboda takaici, ba zan
gaya masa ba wallahi.’
‘Ni kin san me nake tunani? Account din da nake tara kudin hayar gidan zoo road ina
da kudi sosai a ciki, duk da kudin kinga ni da su Abdallah ne. Da na yi niyyar ba
zan taba account din ba sai nan da shekaru kamar goma lokacin Abdallah ya gama
secondary watakila ma ya gama jami’an, amma dai inaga a ciki zan biya.’
‘Kinga kuwa Abdallah yanzu ma zai shiga secondary din. To amma ai zaki iya yin
hakan mu gani, Allah yasa dai kada abun ya dauki lokaci. Kuma ma kafin Abdallah ya
gama secondary din inaga zaki samu ki mayar da kudin sai kiyi abunda kika tsara da
su.'
‘Uhm, hakane.’
Haka suka karasa hirarrakinsu bayan sallar la’asar Aisha tayi mata sallama ta wuce
ta dauko Amira daga makaranta sannan suka koma gidan.
……….
Bata son Jibrin ya san itace ta biya kudin hayar don haka sai da ta bari washegari
taje banki ta turawa mai POS kudin, daga baya ta turawa mai POS din account number
din Jibrin din shi kuma ya tura masa kudin.
Bayan ya biya kudin ya tattara rasit din da sauran takardun biyan kudin ya bayar
aka kai mata, ta karbi takardun ta adana.
Haka rayuwar Aisha ta cigaba, tun tana lissafin rabonta da Abba har ta daina
rayuwarta kawai takeyi.
__
Kwanci tashi har lokaci yayi; duk yanda Sadiku ya so Abba ya canza masa makarantar
da zai sake zana jarrabawar WAEC da NECO ya ki don haka dole ya hakura ya shiga
cikin ‘yan ajin su Yusra.
Tun kafin a gama jarrabawar Sadikun suka hada baki da Yusra suka saka Mommy a gaba
da magiyar so suke idan jarrabawa ta fito Abba ya kaisu Dubai ko Malaysia. Don haka
ta saka Abban a gaba, kuma da yake sai yanda tayi da shi ba tare da wata matsala ba
ya amince.
Musamman ya nemi agent wadanda sukewa mutane hanya zuwa kasashen; duk wani lissafi
an yi masa kuma an bashi zabin jami’oi biyu a Dubai daya a Malaysia. Kudaden da aka
lissafa masa suna da matukar yawa; ba wai ba zai iya biya bane to amma abu ne da za
a dinga biya duk shekara. Gashi yau saura abinda bai fi shekaru biyar zuwa shida ba
yayi retire. Duk wasu kudi da ya tanada don yayi business Zahra ta cinye; domin
idan tace yayi mata abu baya iya musa mata, ita kuma gani take kamar daman kudi ya
tara don haka da ta fadi abu daya yayi sai ta fado wani. Tun tuni yayiwa kudin
business din illa don shine ma dalilin da ya sa ya kasa komawa Dubai din, tun
Alhaji Abubakar yana masa tuni har ya gaji ya kyale shi. Yanzun ma kuma da take
maganar a kai yara Dubai karatu ragowar kudin business din zai kwashe ya kaisu
tunda registration din farko yana da tsada sosai.
……………
Kamar yanda ya saba kwanakin nan idan damuwa tayi masa yawa gidan Yaya Bello yake
tafiya ya samu ya huta su yi hira domin a can baya samun wata damuwa, yau din ma
bayan ya tashi daga aiki can ya nufa.
Tun safe yake lissafi a office din domin kansa har ciwo yake; a yau ne ya kamata ya
biyawa Yusra da Sadiku kudin wata jarrabawa da suke bukatar su rubuta kafin tafiya
kasar Dubai karatu. Sai dai har yanzu ya kasa tsayar da tunaninsa guri guda duk da
dai ya amsawa Zahra.
Wajen karfe biyar saura kwata ya shiga gidan, nan take Karima ta bude masa falon
baki ya zauna. Bayan sun gaisa ya tambayeta yaran tace suna islamiyya. Yace
‘Ya dawo, kayansa kawai ya ajiye ya tafi masallaci ina jin hira ya tsaya a can.’
Ta fice daga falon domin kawo masa ruwa yayinda shi kuma ya kashingide domin ya
jira dan uwan nasa.
Bai dade da zama ba Yaya Bello ya shigo gidan da sallama, nan take ya shige falon
wajen dannuwan nasa.
Ya fahimci dan uwan nasa yana da damuwa amma sai dai duk wata dabara da zai masa
don yaji cikinsa ya gagara. Duk da yana gani kamar wata fitnar ce mata suke masa a
gidan tunda dama masu mace sama da daya basa rasa irin wannan abubuwan, don haka
sai ya kyaleshi kawai yana yi masa addu’a. Domin ya kula idan ya cigaba da takura
masa to lallai zai iya daina zuwa gidan ma.
‘Yana yi.’
‘To ma Sha Allah, Allah ya bada sa’a. Ai jiran ya isa haka idan ba ayi wani abu ba
sai kaga yaro ya kama shiririta. Ga Hauwa’u nan itace ‘yar ajinsu yanzu har ta
shiga level 2 a Bayero.’
‘Hakane Yaya. Shi din ma ai shi yayiwa kansa shirirta kuma uwarsa ta goya masa
baya.’
‘Ai ka san sha’anin mata sai a hankali, sai kasa ido sosai.’
Yaya Bello ya tashi zaune daga kashingidar da yayi ya dubi Abban yace
‘To Yaya ne me zance, sun hada kai da uwarsu sai faman magiya sukeyi.’
‘Wannan ma zance ne wanda bai kamata ka saurareshi ba, tarbiyyar nan mai wahala
sannan ka dauki yaro dan shekara goma sha ka mikawa duniya. A’a ni ban yarda da
wannan shirin ba. Da su da uwarsu tunaninsu duk ai iri daya ne idan ka barsu zasu
kai ka su baro ka ne. Ga jami’oi nan muna da su a nan cikin garin Kano harda ma na
kudi, ka zabi wadda zaka iya ka saka su. In ya so shi Saddiku idan ya fito da
sakamako mai kyau sai a tattare kudi a biya masa ya tafi Dubai din yayi degree na
biyu, ita kuwa Yusra ai kaga mace ce sai abinda hali yayi, tunda ko kafin ta gama
Allah ya fito mata da miji aure za ayi mata.’
Ya jijjiga kai
‘Hakane Yaya.’
‘To ai ba saurara mata zakayi ba, idan Kuma tsoronta kake ji ni sai na zo gidan na
sameta. Amma yara babu inda zasu je gaskiya, kuma musamman shi Saddikun wanda nake
ta gaya maka sai ka kara sa masa ido.’
‘Hakane Yaya, in Sha Allah an bar wannan maganar tunda kace haka, ko babu komai
kuma zancenka gaskiya ne.’
Haka suka gama hirarsu Saida sukayi Sallar Magriba sannan Abba yayi masa sallama ya
kama hanya.
……….
Tunda suka rabu da Yaya Bello yake neman hanyar da zai sanarda Zahra ya fasa kai su
Saddiku Dubai karatu amma ya rasa, ya dai sanarwa agent din da yake masa aiki cewa
ya fasa. Har sati ya zagayo bai sanarwa Zahra ba sai dai kawai shi a zuciyarsa ya
yanke ba zai kaisu din ba.
Ranar Lahadi ce lokacin yara sun tafi tahfiz sai Yusra da Saddiku wadanda
kowannensu yana dakinsa.
Yana zaune a falon sama yana kallon TV yayinda take kasa tana yiwa Jummai bayanin
aiyukan da zata yi mata a gidan. Bayan ta gama bayar da bayanin ta haye falon saman
ta shiga da sallama, bayan ya amsa sallamarta ta karasa ta zauna a kusa da shi tana
fadin
‘Barka da hutawa.’
‘Yauwa.’
Dukansu suka mayar da hankali kan kallon talabijin din da take gabansu, jimawa
kadan tace
‘Uhm, jarrabawar su Yusra ta tafiya Dubai din an saka ranar ko har yanzu shiru?’
‘Oh, ashe fa ban gaya muku ba Yaya Bello yace ma a barsu a nan in ya so duk wanda
ya gama degree dinsa na farko da sakamakon mai kyau sai a kaishi Dubai din yayi
degree na biyu. Ai na ma sallami agent din ina ga su fara a nan BUK.’
‘Yaya Bello kuma? To yanzu don Allah yaushe ya fara zaba maka abinda zaka yiwa
yaranka? Shi da ba shi zai biya musu kudin makaranta ba. Kuma sai da aka gama
magana ni da yara duka mun gayawa dangi zasu tafi Dubai karatu kuma sai kazo ka
fasa.’
‘To sai ki gaya musu sai sun gama first degree zasu je Dubai din, tunda kin ga dai
ai ba zan saba maganar Yaya Bello ba ko?’
‘Wannan ai sai ya koma bakin ciki, don mutum ba zai iya kai yaransa ba sai ya hana
a kai na wani? Gaskiya sai ka sake shawara don wannan ai mayar da aiki baya ne.’
‘Ban tara kudin da na isa Yaya Bello yayi min bakin ciki ba kuma bana taba jin zan
taba yi, kuma yana da damar ya yanke hukunci a kan dukiyata ko ‘yayana. Sai dai
idan hukuncin bai yi miki ba ki sameshi kiyi masa magana.’
Ta bi bayansa da kallo cike da takaici; tabbas wannan bakin ciki ne muraran ina
ruwan wani Yaya Bello da kai yara karatu shi da ba da kudinsa za a kai yara
makaranta ba. Kuma ya za ayi yace ta yiwa Bello magana. Kaf danginsa babu mutumin
da yake mata kwarjini kamar Bello, ita gara ma ace ta yiwa Hajiya magana a kan ace
ta yiwa Bello.
Yaya Bello bai saba yi musu shisshigi a al’amuransu ba, kwata kwata ma sau daya ya
taba bata haushi lokacin da ya sa sunan Rukayya ba tare da yayi shawara da ita ba.
Amma yanzu tana zargin yawan zuwan da Abban yakeyi gidansa a nan yake zuwa ya
zazzage masa cikinsa shi kuma ya sami damar yi musu shisshigi. Yanzu ta riga ta
gama gayawa danginta da kawaye cewa yaranta Dubai zasu tafi karatu yanzu kuma ya zo
ya sa a fasa. Su kansu yaran bata san yadda zasu dauki abun ba musamman Saddiku. Ba
zata iya yiwa Bello magana ba amma tabbas zata san yadda zatayi don ita kanta ta fi
gamsuwa da karatunsu a Dubai din.
Tana jinsa ya fita, sai dai duk da bai gaya mata inda zai je ba ta san gidan Hajiya
zai je kuma daga nan yaje gidan Yaya Bello.
Sai da ta tabbatar ya fita sannan ta fito daga dakin ta wuce falo ta dauko wayarta
ta koma dakinta ta zauna a kan gado. Ta lalubo lambar Yaron Malam ta danna masa
kira; domin tana ganin gara kawai a toshe mata bakin Yaya Bello ya fita daga
idonta.
Tana daf da tsinkewa ya dauka, bayan ya amsa sallamarta yace
‘Hajiya yi hakuri ina kan wani aiki ne, idan kina son magana dani da gaggawa ki
turo sako ta Whatsapp idan ba haka ba kuma da na gama aikin zan kirawo ki.’
Ba zata iya jira ba don haka ta budo Whatsapp ta fara tura masa sakon voice note
“Yaron Malam wani aiki nake son ayi min. Akwai wani wan mijina wanda ya fara yi min
shisshigi ni da yarana saboda ya ga danuwanshi ya fara samun kudi. Ina so a kawar
min da idonsa daga kanmu ko kuma ma a hana dan uwan zuwa inda yake.”
Sai can bayan la’asar sannan Yaron Malam ya kirawota; tayi masa bayanin abinda take
so wato Yaya Bello ya fita daga harkarta. Yayi mata alkawarin zai yi mata aiki inda
suka amince zata tura masa naira dubu talatin kudin aiki. Suna ajiye waya ta tura
masa kudin, bayan kudin sun shiga ya sake kiranta ya sanar da ita yaga kudin,
sannan yace
‘Bayan kwana biyar ki sake tayar da maganar, in Sha Allah ba zai sake yi miki
shisshigi ba.’
Saida ta bawa maganar sati biyu sannan ta sake tayar da ita. Sai dai abinda ta
sakankance zai faru ba shine ya faru ba, domin Abba yana nan a kan bakansa. Ya
jaddada mata cewa yara babu inda zasu je karatu suna nan a Nigeria sai dai idan
Yaya Bello ya yarda. Ya sanar da ita cewa jiya ma sun yi magana da Yaya Bello kuma
yace da zarar result dinsu ya fito a bashi akwai wanda zai bawa a samar musu
admission a BUK ko Northwest.
Sosai hankalinta ya tashi don ta zata an bar wannan maganar. Duk yanda ta so ya
saurareta ya ki, sai dai ya bata dama taje ta sami Yaya Bello idan har yace a kai
yara Dubai to za a kaisu amma muddin bai ce ba to suna nan a BUK.
Ranar da sukayi magana ranar Juma’a ce da daddare don haka ranar asabar wajen karfe
takwas na safe ta dauki mota ta wuce gidan Yaya Bello; ta gaji da wannan fin karfin
gara taje taji da kanta musamman da yake yaron Malam yace mata yayi aiki a kansa.
Lokacin da ta shiga gidan daga Yaya Bello sai Umman su Muhammad wadda, suna zaune a
falo suna karin kumallo domin yaran gidan duk sun tafi tahfiz sai Muhammad kawai da
Shukuriyya wadanda sune manya kuma su ‘yan Jami’a ne.
Bayan sun gaisa Umman Muhammad ta kwalawa Shukuriyya kira daga kicin tace
‘Ki barmu a nan ma daman wajen Yaya nazo, sai dai ko muje ya gama cin abincin
tukunna.’
‘Na ma gama, kuyi zamanku. Ya yaran nawa? Duk lafiya kuke ko?’
Sukayi shiru na dan lokaci alamar yana sauraronta. Ta gama nukunukunta tace
‘Yaya dama a kan maganar yara ne, Saddiku da Yusra da suke WAEC yanzu. Mun gama
magana da babansu za a sama musu admission a Dubai kuma an fara shirye-shirye yanzu
ya zo yace wai BUK zasu yi. To kuma Yaya yaran duka suna da kokari su don saura ma
kadan a sami admission din yace a bari.’
‘Eh, munyi magana da shi don nine ma nace masa ya barsu su fara a nan din idan sun
fito da sakamakon mai kyau sai su tafi kasar waje karatun degree na biyu. Ina ganin
kamar hakan zai fi tsari da tarbiyya musamman a wajen ita Yusra din. Kuma karatun
ma na nan ai ba gagararsu zai yi ba kamar yaune zaki ga sun gama musamman da yake
dukkansu suna da kokari sosai.’
‘Uhmm!’
Har yanzu ta kasa gane dalilin da yasa mutumin nan yake mata kwarjini, duk inda ka
tsaya a gabansa sai ya sha gabanta ya cika maka ido. Yau din nan zuwa tayi ta kora
masa jawabi amma gashi ta kasa, tayi zaton ma zata ga ya rage kwarjini saboda aikin
da akayi a kansa amma sai taga kamar ma kara masa kwarjini aka yi.
‘Hmmm! Ka san dai karatun a can yafi a nan nutsuwa da sauri Alhaji, sai dai kawai
da yake kayi maganar taribiyya amma fa da banbanci.’
‘To ai komai lokacine, yaran da wataran ma da kansu zasu kai kansu duk inda suke so
a duniya musamman shi Saddikun da yake namiji.’
Suka mike kusan lokaci guda ita da Umman su Muhammad a dai-dai lokacin da
Shukuriyya ta fito dauke da tray ta doro waina da kili_kuli.
Nan da nan Umman ta karba ta koma kicin din ta juyo a roba ta fito mata dashi sai
dai kafin ta zo har ta ja mota ta tafi. Ta dubi Yaya Bello da yake tsaye a bakin
kofar falon tace
‘Laa! Kuma sai ka barta ta tafi bata karbi wainar ba Alhaji ai abun marmari ne kuma
mutum ya gani.’
Yayi murmushi
‘Bata so karba ba. Ba zuwa tayi muyi magana ba zuwa tayi ta yi min rashin kunya
kuma bata isa ba. Ina jin ya gaya mata na hana ya kai yara waje karatu shine ta zo
kuma bata sami yanda take so ba, ko baki kula da yanda take magana bane?’
‘A’a ina kula sai dai da yake ni tunda ya kara aure haka muke da ita, da kyar take
kulani don haka ni bata ma damuna shi yasa yanzun ma na zata nice bata son gani
ashe kai din ma ka shiga gonarta.’
‘Ba zan kyalesu ba! Yusufa ai danuwana ne kuma idan yaransa suka lalace dole abun
ya shafi zuri’armu. Da ma wasu nutsattsun yara ne da sai ace, musamman shi
Saddikun. Bari su gama a nan din tukunna muga hankalinsu.’
--------
Tunda ta dawo daga gidan Yaya Bello Abba yaga yanda take cika tana batsewa ya san
bata sami yanda take so ba, don haka ya kawar da kai kamar bai ganta ba. Haka ta
karasa wunin tana ta faman kunci, tunaninta ma yanda zata gayawa yaran musamman
Saddiku wanda yake ta faman murna yana gayawa abokansa wadanda yanzu yawanci suna
level 2 cewa shi Dubai zai tafi kuma ba zasu rigashi gama degree ba.
Sai dai shi Abban yaji dadin wannan hukuncin kawai dai yana mamakin yanda tafi
shakkar Yaya Bello fiye da shi.
Bayan Sallar isha’i ne suna zaune a falon sama har yaran suna hirarsu, Yusra ce ta
shigo da sallama daga falon kasa. Kujerar da take kusa da ta Abban ta zauna, bata
jima da zama ba tace
‘Abba wai yaushe zamu yi jarrabawar ne? Wadda kace zamuyi don samun admission a
Dubai din.’
Ya kalleta
‘Oh, Mommy bata gaya muku ba ko? Ai an fasa zuwa Dubai din, na yanke hukunci da ke
da Yayan naki kuyi first degree a nan BUK in ya so idan kun gama sai ku tafi duka
kasar da kuke so don yin second degree. So yanzu idan result ya fito BUK za a nema,
daman kin ga ita kuka cike a JAMB form ko?’
Nan take idonta ya ciko da kwalla, Mommy wadda take zaune a kusa da shi ta tashi ta
shige dakinta. Yusran ta zumburo baki
‘An gama magana Yusra, nan din ma degree zakuyi irin na can so babu wannan zancen.
Amma nayi miki alkawarin idan dai kika fita da first class to in Sha Allahu ko ban
biya miki ba zan nemar miki scholarahip ki je UK ma kiyi masters kinga na can ya fi
daraja.’
Ta share zafafan hawayen da suka gangaro kan fuskarta, ta tashi ta shige dakinsu na
sama ba tare da tace masa komai ba. Ya bi bayanta da kallo yana jijjiga kai, ya san
abun da haushi amma bai ji dadin yanda tayi masa hakan ba sai dai ya san wannan din
dabi’ar uwarsu ce. Ya cigaba da hirarsa da suaran yaran, sai daga baya suka tashi
kowa ya tafi makwancinsa.
Tun kafin gari ya waye Yusra ta sanar da Saddiku abinda Abba yace, nan da nan ya
rikice. Ya sami Mommy a dakinta ya sa mata kuka; yana tsugune a gabanta Yusra ta
shigo ta zauna a gefen gado kusa da Mommy din. Ta kalli Saddikun ta kawar da kai,
tace
‘Mommy don Allah ki yiwa Abban magana mana, wai me ma yasa zai canza magana bayan
an gama maganar nan?’
‘Wai ubanku ne Bello yace ba zaku je Dubai din ba sai dai BUK, nima babu yanda
banyi dasu ba don jiya ma da safe da na fita gidan Bellon naje. Yace wai a barku
saboda tarbiyya, ko kuma tsabar bakin ciki ne oho! Tunda yaransa BUK sukeyi to dan
kowa ma yayi BUK.’
‘Wallahi Mommy na dade da sanin mutumin nan dan bakin ciki ne, ina ruwansa tunda ba
da kudinsa za a je ba?’
Yusra tace
‘Uhm! Yanzu ai sai ya zuba ruwa a kasa ya sha tunda zamu zauna muyi BUK kamar
yaransa. Mtsewww! Na tsani dan sa ido wallahi.’
‘Amma gaskiya ya cuceni Mommy, duk friends dina na gama gaya musu zan tafi Dubai
amma gayen nan ya sa aka fasa. Allah ya isa wallahi.’
Tace
Nan suka gama hirarrakinsu suna ta zagin Yaya Bello. Daga baya suka sanar da Mommy
cewa idan hakane ta yiwa Abban magana su in ba za a kai su Dubai din ba to sun fi
son Maryam Abacha University. Duk da bata san yanda zai dauki wannan zabin nasu ba
amma tayi musu alkawarin zata yi iya yinta taga a kalla sun sami nan domin ko babu
komai dai kada suyi Jami'ar da ‘yayan Bellon suke yi wato BUK.
__
Kwanci tashi har an fara yiwa azumi lissafin abinda bai fi wata daya ba. Zuwa yanzu
duk wanda ya ga Aisha ya san tana da damuwa, sai dai duk yanda ‘yan uwanta suke so
su rabata da gidan Yusuf ta ki yarda. Suna nan dai ita da Amira, duk da bata rasa
komai ba amma rashin ganin Abban yana damunta. Ko a hanya bata ganinsa, kusan kamar
ma dai suna rayuwa a mabanbanta duniyoyi.
Bata taba fasa addu’a da sadaka ba, ga addu’ar karya sihiri wadda kullum sai tayi
kuma Hajiya ma sai ta yi ta aiko mata da ruwan. Tun tana lissafin kwanaki har ta
gaji ta daina; abinda ta rike kawai shine Allah ya amsa addu’arta lokaci kawai ake
jira.
………..
Ranar Juma’a ce kuma da yake ta kama ranar hutun aiki Zuwaira, Zainab da Aisha da
Zahida gaba daya su da yaransu sun hallara a gidan Hajiya. Don haka sai kaiwa da
kawowa akeyi, Farha da Abdallah wanda yake shirin zana common entrance suma suna
nan a cikin dangi. Mijin Zahida ne ya bawa Hajiya kujerar Umra wadda zasu tafi
cikin azumi don haka kowa murna yakeyi.
Can wajen karfe biyar na yamma lokacin kowa ya fara shirin tafiya Yaya Abubakar
shima ya shigo tare da babban yaronsa Abulkhairi. Bayan sun gaisa ya dubi Anti
Uwani yace
‘A’a wa ya isa ya wareka? Nan da ka gansu duk dadin baki suka zo su yiwa ‘yar uwata
zata tafi Umra su samu ta tafi dasu ni kuwa ina kallonsu da ni zata duk a Nigeria
zamu barsu.’
‘Ai kuwa a Nigeria zaku barsu Anti Uwani don kema da taki kujerar nazo.’
Ya daga kai
‘In Sha Allah na ma gama biyan kudin sai su tafi tare, nima don dai ban dade da
komawa sabon office bane da dani za a.’
Nan take Zahida ta zabga guda, kafin ta dire Yaya Zainab ta harareta tace
Nan suka hau sabuwar murna gaba daya. Hajiya ma sai tafi Anti Uwanin murna domin
sai da ta matse kwalla saboda jin dadi. Haka ta dinga sakawa Abubakar albarka tana
addu’a Allah ya kara masa arziki.
Haka Anti Uwani ma sai ta rasa inda zata saka ranta don murna, tayi ta sa musu
albarka tana musu addu’a. Ta matsa kusa da Hajiya ta dafa ta tace
‘Yaya, Yaya Kinga dana ko? Na rasa bakin godiya Yaya. Tunda kika haihu ban taba
kukan rashin haihuwa ba, kullum godewa Allah nake da bai bari na sha wahalar goyon
ciki ba kika sha mana wahalar ke kadai kika haifo min ‘yaya. Gashi nan kinyi shuka
sai girbar alkhairi nakeyi hankalina kwance.’
‘To ga ‘yarki nan baure sarkin kuka zata tayaki muna murna zaku saka mu kuka.’
Ana idar da sallar Magriba duk suka watse suka bar Aisha da Amira wadanda sai bayan
sallar isha’i zasu tafi.
A nan falon Hajiya suka ci abinci suna ta hirarsu, sai da aka idar da sallar isha’i
suka tashi tafiya. Lokacin Farha tayi bacci don haka Abdallah da Anti Uwani suka
rakosu farfajiyar gidan.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
34
Babu yanda Zahra ta iya, tana ji tana gani aka fasa kai yaran Dubai karatu. Ta dai
samu ta karfin tsiya ta takura Abban ya amince zai saka su a Maryam Abacha
University. Yayi magana da Yaya Bello shima ya amince da haka, tunda dama abinda
yake gaya masa shine ya kasance yaronka yana kwana a gida har sai ka ga yanayin
fahimtarsa a rayuwa tukunna. Don haka nan da nan aka fara shirin shiga MAUN.
Sai dai kawai ta yiwa kanta alkawarin sai ta kai Yaya Bello wajen boka don ta
fuskanci tunda yanzu dan uwansa ya kara kusanci da shi to lallai hukuncinta zai ci
gaba da cin karo da nasa. Yanda take jin yanzu ta sami Abba a hannunta bata jin
zata sake bari ya subuce mata, duk wata hanya da zata bi sai ta bi don ta tabbatar
babu wanda ya sha gabanta a wajen Abba. Domin a yanzu ma gani takeyi kamar Abban
yana bawa Yaya Bello wasu kudade ne.
__
Tun lokacin da ta gane aikin boka yayi tasiri take kula da motsin Aisha, musamman
ta sami mai aikin gidan commissioner wadda dattijuwa ce take sa mata ido tana kular
mata da motsin Aishan. Tana so ta san lokacin da Aishan zata bar gidan. Zuwa yanzu
kusan watanni goma an sanar da ita Aishan tana na; ta kasa gane wanne irin naci ne
wannan. Miji baya kula ki amma ace ba zaki bar masa gida ba? Ta dai bata daga nan
zuwa babbar Sallah ta san in Sha Allahu zuwa lokacin ko bata gaji ba to tabbas
kudin hayar gidan zai kare.
Maganar boka ta tuno da ya ja layi guda biyu yace mata tafiyar Aisha da Yusuf mai
tsawo ce; yanzu haka tsawon kenan kuma in Sha Allahu sai ta ga karshen wannan
tafiyar.
__
Kwanci tashi har azumi ya karaso; duk wani abu da Aisha take bukata na azumi haka
ta dauki Amira suka je suka siya, kuma da yake Yaya Abubakar ya san halin da take
ciki ranar da aka ga watan azumi sai ga sako ya aiko mata. Buhun shinkafa, dankalin
bature, doya, kifi da suga haka aka kawo mata.
Ranar goma sha takwas ga watan azumi jirgin su Hajiya zai tashi tare da Aisha.
Ranar sha biyar ga wata ta shirya suka tafi gidan Hajiya ita da Amira; bayan ta
kwashe duk wani abu mai amfani nata saboda bata barwa kowa ajiyar gidan ba. Sai da
ta kulle ko ina tayi addu’a sannan suka fito, har zata saka kwado a gate din ta
tuna duk wanda ya zo yaga kwado daga waje ya san babu kowa a gidan don haka sai ta
fasa saka kwadon kawai ta kulle da mukullin. Babu wanda take harka da su a kan
layin don haka bata bukatar yiwa kowa sallama, ta ja motarta suka bar unguwar.
Ranar da aka dauki azumi na sha takwas da safe Aisha da kanta ta dauki Abdallah da
Farha ta kaisu gidan Umma, kakarsu ta wajen Uba. Ba karamin dadi Umma taji ba don
dama sun dade basu je mata kwana ba. Sukayi sallama a kan sai bayan Sallah idan ta
dawo zata zo ta daukesu. Da yamma jirginsu ya tashi sai kasa mai tsarki, tana
tsakiyar Hajiyanta da Anti Uwani.
____
Ranar da aka kai azumi na ashirin da biyar Baba Salamatu wato mai aikin gidan
commissioner ta shigo gidan Zahra. Lokacin yara duk sun tafi masallaci sallar asham
sai Jummai wadda take aiyukanta a kichin yayinda Mommy din take hutawa a falon
sama. Bayan sun gaisa da Jummai ta hau saman ta kirawo Mommy.
Nan da nan ta sauko saboda ta san akwai labari tunda Sala ta zo. Bayan sun gaisa
tace
‘Kai gaskiya ba unguwa ta tafi ba Hajiya. Don Kinga fa tun azumi na kusan goma na
daina ganin motsinta, almajiran ma da suke zama kofar gidan jiya sun tabbatar min
bata nan don farkon azumi kullum da magriba sai ta basu sadaka amma yanzu an kwana
biyu basu ga motsi a gidan ba.’
Nan da nan ta washe baki da addu’a tana ta faman godiya, tayi mata sallama ta fice.
……….
Cikin walwala suka tashi ranar idi, nan da nan aka shirya yara kowa ya sha
kwallaiya. Karfe takwas saura Abba ya fito ya zuba su a mota suka wuce masallacin
idi.
Sai da kowa yaci ya koshi sannan Mommy ta ware na makota, Jummai ta dauka suka tafi
tare da Nana da Ummi. Gidaje uku suka kai, gidan commissioner ne na karshe kuma
shine cikon na hudun. Bayan sun gaisa da matarsa wato Dr. Maimuna wadda ake kira
Mama suka bayar da tuwon, aka juye aka basu kwanukan da kuma tukwici.
Salamatu ta dauko kwanukan ta biyosu suna ‘yar hira da Jummai kamar zata yi mata
rakiya. Kasa-kasa suke yin maganar don haka Ummi da Nana da suka wuce gaba basa
jinsu. Salamatu tace
‘Babu mamaki fa, don na manta rabon da maigidan ma yayi rabon kwana da ita; ko ba
ayi shekara ba an kusa. Ina ga sakinta yayi ko kuma dai wata matsala aka samu.’
‘Gaakiya da alama, tunda kin ga ta bar gidan fa tun farkon azumi. Yanzu haka dai
auren ya kare. To ko Uwar dakinki ce ta kar auren ne?’
Ta tabe baki
Tun daga wannan lokacin gulma ta fara yawo a unguwar cewa Abba ya saki Aisha.
Bayan da su Nana suka dawo ne kuma Malam Ali ya kwashesu da tuwon gidan Hajiya suka
tafi kai mata. Mommy ta riga ta gayawa Yusra cewa idan Hajiya ta tambaya Ina
abincin gidan Aisha tace tare suka yi don haka suna ajiye tuwon ma kafin a tambaya
Yusra ta cewa Hajiyan
Ta yashe baki
Bata jin dadi sosai saboda ciwon diabetes wanda tun goman karshe ya tasar mata
saboda an hanata azumi tace sai tayi, don haka ta san ba cin tuwon zata yi ba. Nan
ta bawa Yusra umarni ta kaiwa Anisa ta ajiye a kicin. Ta gyara kwanciyarta ta kara
muryar rediyonta yayinda su kuma yaran suka fito tsakar gida suka cigaba da
hidimominsu.
_
Bayan Sallah da sati daya su Aisha suka dawo Nigeria; tayi sallah kuma tayi addu’a
a kan Allah ya karya wannan kulli da aka yi tsakaninta da mijinta, sannan kuma ta
roki Allah ya saka mata ko ma waye yake mata wannan zaluncin kuma Allah ya toni
asirin me yi mata hakan.
Tabbas ta sami natsuwa kuma ta dawo da wani sabon karsashi na zaman jiran lokacin
da wannan asirin zai karye, in Sha Allahu ko zata rabu da Yusuf to ba yanzu ba sai
dai idan ya dawo hayyacinsa yace ta tafi to tabbas a lokacin zata tafi.
Kwanansu biyar da dawowa Aisha tana hutawa a gidan Hajiya; an dauko su Abdallah
duka ta basu tsarabarsu har sun je gidan ‘yanuwanta yawon zumunci.
‘Hajiya gobe ni da su Abdallah zamu je gidan Yaya Zainab, daga nan zan dauko ‘yata
ranar Juma’a sai mu koma gida.’
Sai da Hajiyan ta tashi zaune sannan ta bata amsa
‘Tun last week dai da yazo, ranar da muka je gidansa har muka taho bai dawo ba kuma
da ya zo nan shekaranjiya bana nan, amma idan bai zo ba zan kirawoshi kafin mu
tafi.’
‘Uhm! To ai munyi magana ba zaki koma gidan Yusufa ba tunda ko kin koma dake da
wadda bata da miji duk daya kuke. Ki zauna a nan, ba zamu kashe miki aure ba, duk
lokacin da ya dawo hayyacinsa sai ya zo ya daukeki ku koma.’
Tuni idonta ya cicciko da kwalla tace
‘Hajiya don….’
‘Ba shawara na zauna yi dake ba, idan ke baki san ciwon kanki ba mu muna kishinki.
Na gama magana babu inda zaki koma har sai Yusufa ya zo nan da kanshi sai ku tafi.’
‘To.’
Ta tashi jikihta babu kwari ta koma cikin gidan, kai tsaye dakin Anti Uwani ta wuce
ta fada kan gado ta sa kuka.
‘Yaya don Allah ku bar maganar nan, ku bar yarinyar nan ta koma gidanta tunda ita
ta ji ta gani. Idan tana can ma sai tafi dagewa da addu’a amma yanzu idan an rike
ta a nan ba zata nutsu ba tunda ta fi son can din. Idan babu hali ma ni sai na koma
can na dinga tayata zaman zuwa lokacin da komai zai warware.’
‘Ni dai Yaya gaskiya ki barta ta koma, shima Abubakar din zai zo ya same ni.’
Kai tsaye dakinta ta wuce don ta san a nan ne zata sameta. Ta zauna a gefen gadon
ta dafa bayan Aishan tace
‘Yi hakuri Shatu, Abubakar din zai zo ya same ni. Wannan abun ba komai bane face
jarrabawa kuma da izinin Allah zai wuce, mu da muka je har kasa mai tsarki muka
roki Allah a kan wannan lamarin ai ya kamata a ce mu barki ki zauna a dakinki zuwa
lokacin da komai zai warware.’
Ta share kwallarta da zanin gadon ta mayar da kanta ta kwantar a kan cinyar Anti
Uwani sannan tace
‘Gara na zauna a can ni dai, kuma ina ji a jikina wannan matsalar ta kusa zuwa
karshe in Sha Allah. Kuma Anti Uwani ita matarsa so take na bar gidan kin ga yanzu
idan ta bude ido taga bana nan ai ta ci nasara ko?’
‘Kada ki damu ki cigaba da shiri in Sha Allahu don ranar Juma’ar zaki koma, idan ma
sun ki saurarata har gidan baffanki zan je na kirawoshi ya mayar dake don na san ba
zai goyi bayan wannan aika-aikar ba.’
Haka ta dauki lokaci tana lallashinta.
………..
Washegari da yamma suna zaune sai ga Baffa, Suhail ne babban yaronsa ya kawo shi
saboda shi tun tuni ya hakura da tuki saboda baya gani sosai daga nesa, don haka
idan zai fita sai ya jira yara.
‘Kwana biyu, kin san idona ya ki ina ta so nazo na ganku to yara duk kowa ya bazama
nema babu lokaci.’
Tace
‘Babu komai Baffa, ai dama komai lokacine. Allah ya kara lafiya ya ja kwana.’
‘Amin ya Allah.’
Suna nan zaune suna hirarrakinsu Aisha da su Abdallah suka shigo, sun dawo daga
gidan Anti Zainab.
‘Yanzu kika zo Shatu da magaribar nan, ba kya gudun kiyi dare a hanya? Ya maigidan
naki? Ina fatan dai komai ya warware.’
‘Lafiya kalau.’
‘Ai tunda muka dawo daga Umra dama bata tafi ba.’
Hajiya tace
‘Itace dai har yanzu babu wani cigaba, don shi yasa ma nace ta zauna a nan idan ya
dawo hayyacinsa ya zo su tafi.’
‘Ikon Allah! Ko da yake malamin da na sa yake addu’a ya gaya min abun zai iya
daukar lokaci amma komai daren dadewa zai yi karshe.’
‘Shatu da kinyi hakuri kinyi zamanki a can tunda ance min an baki mai tayaki kwana,
jarrabawa ce ta ubangiji kuma idan kina can din ai sai abun ya fi saurin
warwarewa.’
‘To ai Yayan ce ta hanata komawa ita da Abubakar, amma ita ai tana son ta koma
gidanta kuma nima na goyi da bayan hakan an dai fi karfinmu ne kawai.’
‘Ki koma Shatu kiyi zamanki, sai dai idan shine yace ki tafi to tabbas muma ba zamu
barki ki zauna ba. Amma yanzu hakuri zakiyi ki zauna gaba daya mu cigaba da
addu’a.’
‘Um,shikenan Baffa. Dama gani nayi tana can tana zama kamar me zaman kanta shi yasa
nace ta dawo gida, amma in Sha Allah goben zata koma.’
‘Yauwa.’
Aishan ta tashi ta wuce daki inda su Abdallah suke can suna wasansu.
Hajiya da Anti Uwani kuma da Baffa suka karasa hirarrakinsu, sai dab da magriba
Baffa yayi musu sallama ya tafi.
Yana fita Hajiya ta dubi Anti Uwani tace
‘Kun sami yanda kuke so ai sai kije ku fara shiri ke da ‘yar taki ko?’
‘Eh, bari muje mu hada kayanmu ai zaman aure ba wasa bane kuma kowa da
jarrabawarsa.’
Cikin daren nan Anti Uwani ta taya Aisha suka hada kayanta. Washe gari Juma’a wajen
karfe goma suka kama hanya tare da Anti Uwanin suka tsaya suka dauki Amira sannan
suka wuce.
Sai da suka gama gyara gidan tsaf sannan Anti Uwani ta hau mota ta koma gidan
Hajiya, ta bar Aisha da Amira.
Gaba daya Aisha ta manta basu siyo burodin karin kumallo ba gashi kuma basu da
indomie a gidan. Don haka da safe wajen karfe takwas da rabi Aisha ta bawa Amira
kudi ta siyo musu burodi da kwai su karya.
Tana fitowa daga gate din gidan su kuma su Yusra sun fito daga gidansu zasu tafi
tahfiz don ranar aka koma hutu. Yusra ta balla mata harara, ita kuwa tayi dariya ta
dagowa Rukayya hannu wadda ta mayar mata da murmushi ta daga mata hannu itama. Ta
wuce ta barsu a nan Yusra tana ta faman hararar Rukayya.
--------
Tun bayan da ta haifi Sumayya bata sake yin wani tsarin iyali ba, ba wai ta damu da
haihuwar bane amma tabbas a halin yanzu idan ta zo ba zata Hana ba. Duk da har
yanzu Aisha bata haihu ba amma dai tana so ta haifi da namiji sannan Kuma tana so
ta cika gidan da ‘yaya.
Tun cikin azumi take jin jikinta babu dadi, lokacin da ya kamata tayi al’ada har ya
wuce bata sha azumi ko daya ba don haka zuwa yanzu tana da yakinin ciki ne da ita.
Lafiya kalau take daukar ciki ta haihu don haka ta yanke shawarar ba zata je
asibiti ba har sai cikin yayi wata hudu, zuwa lokacin idan aka yi scanning za a iya
gaya mata mace ne ko namiji.
Tun kafin yaran su tafi tahfiz Jummai ta zo, don haka suma tafiya ta sallami Jummai
da ayyukan da zata yi mata ta haye sama ta kwanta a dakinta. Bata Dade da kwanciya
ba Shima Abban yayi mata sallama ya wuce gidan Hajiya.
Bata farka daga wannan baccin ba sai wajen Sha biyu da kwata lokacin da yara suka
dawo daga tahfiz wanda shigar Sumayya da Ummi dakin shine ya farkar da ita. Bayan
sun gama yi mata sannu da gida tace su sauko wajen Jummai su ci abinci sannan su
kunna TV suyi kallo. Suna fita daga dakin ragowar yaran ma suka shigo sukayi mata
sannu da gida sannan suka fice
Yusra ce ta karshen shigowa ta sami waje a gefen gadon ta zauna, ta dubi Mommy din
wadda har yanzu take kwance tace
‘To gaskiya Mommy ko dai bata tafi ba ko kuma ta dawo don gaskiya yau na wannan
mara kunyar ‘yar tata ta fito daga gidan, don har hannu ma ta dagowa Rukayya.’
Ta jijjiga kai
‘Um! To shikenan idan kin sake ganin motsi a gidan kiyi min magana.’
Duk da Yusra ta san cewa uwarta tana bin malamai amma bata san itace tayi abinda
Abba ya daina kula Aisha ba, ba wai ta dauka bin malaman kuskure bane. Hasali ma a
wajenta shine dai-dai tunda Mommy tace tsari ne ake nema musu. Lokacin da taga Abba
ya daina kula Aisha tayi zaton asirin da Mommy tace musu ta yiwa Abban ne ya karye
shi yasa ya manta da ita, don haka yanzu da ta ganta tsoro take ji kada ta sake
yiwa Abbansu wani asirin duk da ta san Mommy a tsaye take a kansu.
Yusra tana fita daga dakin ta gyara zama ta kafa tagumi; Aishan nan wai me take
nufi ne? Kusan shekara guda miji baya zuwa inda kike amma kin ki fita daga
rayuwarsa? Wannan din wanne irin naci ne? Gashi zuwa yanzu matan unguwar da take
harka da su sun fara tambayarta labarin Aisha a kan sunji a unguwa cewa auren
Aishan ya mutu; duk da dai ta gaya musu itama bata san me ake ciki ba domin da ta
tambaya ma Abban yace kada ta sake yi masa maganar.
Tabbas dole ta koma Doguwa; tunda dama akwai maganar Yaya Bello da take so a
rabashi da Abban. Dama azumi ne ya hanata zuwa da aka sallace kuma bata da aiki sai
bacci saboda cikin da take dauke da shi; ko da yake lokaci zata saka taje gidan
Amina su tsara yanda za ayi don watakila ma Aminan zata iya zuwa mata Doguwan.
Haka ta karasa wunin ranar tana tunanin mafita.
--------
Ita kuwa Aisha tunda ta dawo gidanta sai ta sake mayar da hankali wajen addu’a,
ranakun aiki taje aiki ta dawo ranakun Asabar da Lahadi kuma sai taje islamiyya.
Rashin kulata da Abban yakeyi yana damunta sai dai da yake dinkin mayafai da takeyi
yana rage mata zama haka nan sai abun yayi mata sauki;kuma ta samu ana sayen
mayafan sosai don haka kusan kullam cikin aiki take Amira tana tayata.
---------
Ranar Alhamis ce don haka yara babu islamiyya da yamma, tun safe ta gayawa Saddiku
kada ya fitar mata da mota don zata fita da yamma amma ga mamakinta sai da ya fita;
koda yake yanzu ta kula ko sauraron maganarta baya yi, yanda yayi niyya haka yake
aikatawa. Malam Ali yana kawo yara daga makaranta tace ya tsaya zai kaita unguwa
don haka nan ya zauna ya jirata.
Saida ta gama abinda takeyi tayi sallar la’asar sannan ta fito suka kama hanyar
gidan Amina.
Duk da gidan Amina bai kai girman na Zahra ba amma shima ya tsaru, domin maigidanta
ma ya fi Abba Saddiku dukiya. Cikin walwala ta sauketa ta ajiye mata lemo da cake
sannan suka gaisa.
Bayan sun gaisa Aminan ta dubi Zahra wadda damuwa ta bayyana a fuskarta tace
‘Bai ma san da ita ba komai normal, kawai dai bana son zamanta a gidan ne. Nifa na
fi so ace babu igiyar aurenta a wuyansa shine kawai zan huta.’
Ta dafa cinyarta
‘Ki daina damuwa, ki bawa banza ajiyarta kawai tunda dai maigidan yana hannunki.
Kuma na gaya miki aikin bokan nan ba zata iya karyashi ba ko waye malaminta a garin
nan.’
‘Hmm! Kin san kuma da maganar Yayansa da nace miki yana mun shisshigi, duk da dai
na sa Yaron Malam yayi min aiki amma dai naga alama aikinsa bai yi ba. Ni wallahi
Doguwan ma nake son zuwa don dai kawai cikin da yake jikina ne ya sa bana son
zuwa.’
‘Da kyau kawata. Nima wallahi ina son zuwa Doguwa saboda mijin Asiya, ya fara kawo
mata wargi gara na nema mata taimako. To amma gaskiya sai an dan kara kwana biyu,
in kina so idan na shirya sai muje ko kuma na tafi da sakonki mu gani ko zai karba.
Sai dai shi kinsan fa baya aiki da sako sai dai kai da kake da bukata kaje da
kanka, kuma gaskiya ba zan baki shawarar zuwa wajen nan da ciki ba.’
Ta dan yi tsaki
‘Wallahi nima abinda nake ji kenan, to amma bari mu gani a kwana biyu tunda ma
yanzu babu wata major matsala.’
‘Gaskiya dai. Idan kuma wani abun ya taso ai sai kiyi maleji da Yaron Malam tunda
shi ko ta waya zaku gama komai.’
Suka karasa hirarrakinsu sai gefin magriba sukayi sallama Zahra ta shiga mota Malam
Ali wanda yake jiranta ya mayar da ita gida.
Haka ta hakura ta cigaba da rainon cikinta tana fatan ya zama namiji; tunda ko babu
komai yanda bokan nan yayi mata alkawarin babu wanda yake maganar Aisha. Domin har
dangin Abba ma babu wanda yake maganarta kamar ma babu ita, kuma tana da yakinin
kwanan nan kudin hayar gidan zai kare ta san dole Aisha ta tashi tunda babu mai
biya mata.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
35
Duk yanda Aisha ta kai ga son boye damuwarta game da rashin ganin mijinta abun yana
mata wahala; lokuta da dama ta kan kwana tana kuka. Wasu lokutan kuma idan ta yi
sujuda da nufin ta roki Allah sai kuka yaci karfinta, haka zatayi mai isarta sannan
ta dago daga sujudar. Tana zuwa aiki da islamiyya ga kuma cinikin mayafanta amma
duk wannan bai isa ya debe mata kewar mijinta ba.
Yau din ma haka ta tashi cikin yanayi na damuwa, gashi ranar hutu ce don haka babu
aiki kuma gashi da wuri Amira ta fita saboda ana bikin babbar kawarta; don haka ita
kadai ce a gidan.
Duk yanda ta so ta kawar da damuwar daga ranta abun ya faskara, haka tayi ta faman
aikace-aikace, har aikin ma da batayi niyyar yi ba. Sai wajen karfe biyu ta gama
goge gidan, ta dauko tsumman ta fito ta wanke a faffon tsakar gida ta shanya. Har
ta kama hanyar shiga gidan sai kuma ta zauna a kan dankalin da fulawoyi suke ciki;
ta karewa tsakar gidan kallo kamar mai neman wani abu.
Haka kawai kuma sai ta ji kamar ita kadai ce a duniyar; ya za ayi ace tana zaune a
gidan mijinta amman saboda Zahra babu mai kulata? Makota gaba daya basa harka da
ita gashi mijin ma yanzu ya daina kulata. Ta manta rabon da a buga mata gate don
daga ita sai Amira suke rayuwarsa, sai dai da yake duk sati sai Anti Uwani ta kawo
su Abdallah. Ta share zazzafar kwallar da ta zubo a kan fuskarta.
Tabbas ba zata taba yafewa Zahra ba da ma duk wani wanda yake da hannu wajen sakata
a wannan halin.
A da ta yiwa kanta alkawarin zata zauna tayi jiran har mijinta ya dawo hayyacinsa
amma kawo yanzu bata sani ba ko zata iya cika wannan alkawarin. Domin zaman ya fara
isarta, ta fara rasa walwala gaba daya tunda komai ya daina bata farin ciki. Tabbas
bata san zuwa yaushe zata iya jira ba amma dai ta fara tunanin yiwuwar ta koma
gidan Hajiya kawai ko jiran ne tayi a can.
Ta share hawayenta lokacin da ta tuna la’asar ta kusa kuma bata ma yi azahar ba, ta
mike cikin sanyin jiki ta shige cikin gidan domin yin sallar azahar.
___
Da yake tazarar dake tsakanin karamar Sallah da babbar Sallah babu yawa har har an
fara lissafin babbar Sallah.
Kamar yanda ya saba haka yayi wa kowa kayan Sallah; baiyi maganar Aisha ba wanda
wannan ya kara kwantarwa da Zahra hankali ta kara sakankancewa lallai aikin boka na
Doguwa ya kama.
Sa ya siyo da rago daya wanda aka yanka Uwara Saddiku tayi yanda take so da shi
cikin walwala. Cikinta ya fara girma domin ya shiga wata na hudu don haka ba da ita
akayi aikin suya naman ba, masu aiki ne su uku sukayi. Sai dai kawai tana zaune
daga gefe a kan tabarma tana nuna yanda take so ayi.
Haka suka gama aikin suka tattare mata naman aka saka a cikin gida.
Ita kuwa Aisha tun ana i gobe Sallah suka tafi gidan Hajiya, a can aka yanka mata
ragonta aka gyara aka soya. Saida suka gama yawon Sallah lokacin bayan Sallah da
kwana biyar sannan suka koma.
Haka rayuwa ta cigaba.
__
Ranar Talata ce tana zaune a staffroom, bata da aiki a daidai lokacin don haka take
ta faman duba wayarta tana kallon status; daga kan wannan ta koma kan wannan. Suna
ta wucewa har tazo kan status din Anti Karima, matar Yaya Bello.
Hotuna ne na yaronta na uku wato Yusuf wanda suke kira Adil, daga kallon hotunan
zaka gane bikin sauka ake yiwa Adil din wanda tabbas ta tuna kamar wancan satin ta
ga hoton katin gayyatar bikin saukar a status din Yaya Saratu. Daga rubutun da Anti
Karima tayi a status din ne kuma ta gane saukar hadda yayi; tayi murmushi tana
kallon hoton zayyanar dake hannunsa.
Idan taga yaro ya haddace alkur’ani tabbas yana bata sha’awa kuma tana alfahari da
su domin Abdallah da farha ma tana fatan su haddace izu sittin.
Ana cikin bikin Sallah ta gani a status din Anti Karima an kawo kayan auren Asma’u
yayar Adil din, ta manta dalilin da ya hanata koda waya ne ta yiwa Anti Karima tayi
mata barka. Lallai yanzu ya kamata taje gidan nan don ba zata ma iya tuna rabonta
da su ba, ko babu komai dai ya kamata taje mata murnar auren Asma’u da ake shirin
yi kuma da saukar Adil din.
Nan take ta yanke shawarar ranar asabar idan ta tashi daga islamiyya zata je gidan
tunda dama karfe sha daya suke tashi kuma ranar Amira tana da lecture har karfe
daya; don haka daga islamiyya sai ta wuce gidan Yaya Bello daga can ta tsaya ta
gaida Hajiya sai ta wuce ta dauko Amira.
Ta dan gatsina fuska a lokacin da tayi tunanin zuwa gidan Hajiya; bata son zuwa
gidan Hajiya saboda yanda Hajiyan takeyi mata wanda ya sa Anisa ma da take gidan
bata ganin girmanta don ko gaisheta bata yi. Ta tuno zuwanta na karshe gidan wanda
bayan ta gaisa da Hajiyan haka Hajiyan ta tashi ta shige daki ta barta, itama Anisa
da mai aikin Hajiya suka shige kicin suka barta ita kadai a falon Hajiya. Saida ta
gaji da zama sannan ta taso ta fito kuma babu yanda bata yi ba Anisan ta kirawo
mata Hajiyan tayi mata sallama taki; sai ce mata kawai tayi tayi bacci kuma idan
tana bacci ba a tashinta. Haka ta hakura ta tafi tana mamakin dalilin da yasa suke
mata wannan kiyayyar. Kusan zata iya cewa kaf ‘yan gidan su Abba Yaya Bello ne
kawai da iyalansa suke zama da ita yanda ya kamata.
Tun ranar Juma’a ta tanadin alkur’ani izu sittin da turaren mai kamshi da agogon
hannu wanda ta saka a leda a kan zata kaiwa Adil. Da tayi tunanin zata dafawa
Hajiya funkason alkama da farfaesun kifi to amma gaskiya bata son ta sha wahala
taje su lalatar da abincin basu ci ba don haka ta yanke shawara gara ta sayawa
Hajiyan tuffa da kayan shayi irin wanda ya dace da masu ciwon suga ta kai mata.
Ranar asabar suna tashi daga islamiyya ta wuce gidan Yaya Bello.
Tana tsayar da motarta a bakin gate din gidan yaran gidan suna dawowa daga tahafiz;
tun daga nan yaran suka fara gaisheta, bayan ta amsa suka nufi cikin gidan a tare.
Suna tafe tana yiwa Adil murnar haddar da yayi.
Cikin girmamawa Anti Karima ta karbeta, Muhammad da Asma’u wadanda basu je tahfiz
ba suka gaisheta sannan Asma’u ta kawo ruwa da lemo. Suka zauna ita da Anti Karima
a falo sunata hirar yaushe gamo, daga baya kuma aka janyo akwatunan kayan auren
Asma’u aka bude mata ta gani tana ta sa albarka.
Da murmushinta tace
‘Anti to me ake shiri? Akwai wani anko da za ayi don gara na karbi nawa kafin na
tafi.’
‘Tab, ai Abbansu baya son anko babu ma wanda ya isa yayi wannan zance. Kina ji
event center ma yace ba za aje ba wai a nan gidan zamuyi gaba dayan bikin. Har
yanzu faman lallabarsa nake yana burtsewa; tunda kinga gidan ai ina muka ga filin
yin biki idan banda rigimarsa.’
‘Gaskiya dai Baban su Muhammad da ya bari munje event center din. Amma fa kin san
duk abun suna ne ko a nan din aka yi kalau za a gama shike nan, ai albarkar abun
ake nema.’
‘Hakane.’
Sai wajen sha biyu da kwata sannan Aisha ta mike zata tafi. Ta nemi wanda zai
rakata gidan Hajiya aka ce Asma’u ta shirya suje, don haka ta dan zauna tana jiran
Asma’u ta kintsa.
--------
Kamar yanda ya saba duk ranar da babu aiki da safe yake tafiya gidan Hajiya, idan
rana tayi sai ya wuce gidan Yaya Bello inda a can zai ci abincin rana. Ba zai koma
gidansa ba har sai anyi sallar Magriba. Duk yanda Zahra taso ya daina zuwa gidan
Yaya Bello ko kuma a kalla idan ya je ya daina dadewa abun yaci tura. Tunda yace
mata a can yake cin abincin rana ta fara zargin wani abun suke barbada masa a
abincin shi yasa ya kasa rabuwa da su.
Sau biyu tana turawa Yaron Malam kudi yayi mata aikin da zai raba Abban da Yaya
Bello amma ko sauyi bata gani ba. Daga karshe Yaron Malam din ya sanar da ita aikin
ba zai yiwu ba domin mutumin da ta bayar da bayaninsa idan sun tashi zasuyi aiki ko
ganinsa basa iya yi.
Sosai abun ya bata mata rai amma babu yanda zatayi tunda tana tsoron zuwa Doguwa da
cikin jikinta; musamman da yake sau biyu tana yin scanning a gurare daban-daban
kuma duka biyun sun tabbatar mata namiji take dauke da shi; bata son wani abu ya
sameshi.
Haka ta hakura ta daga musu kafa, amma tayi alkawarin idan ta haihu da zarar tayi
arba’in zata je Doguwa duk sai tayi maganinsu ko waye malamin Yaya Bello bai isa ya
mallake mata miji ba.
Yau din ma bayan ya gama cin abincin safe tana kallonsa ya shiryo ya fito, tun safe
take masa korafin bata jin dadi da nufin ya fasa fitar amma bai ma kulata ba. Kawai
sai ya sanar da ita idan da matsala tayi masa waya sai ya dawo. Da kyar ta bude
baki tayi masa a dawo lafiya shi kuwa ya amsa ya fice ya kama hanya lokacin wajen
karfe goma.
Kai tsaye gidan Hajiya ya wuce don ya san a yanzu Yaya Bello yana can, domin tunda
diabetes dinta ya tashi da azumi da kanshi yake zuwa yana bata abincin safe da na
dare. Sosai suke lallabata saboda bayan diabetes din kuma to tana yi musu rikici
irin na tsufa domin ko abincin ma idan ta ga dama sai tace sai taci abinda likita
ya hanata ci. Haka dai suke ta fama.
Lokacin da Abban ya shiga gidan Hajiya ta gama cin abincinta, suna zaune dai a falo
suna hira ita da Yaya Bello. Nan ya zauna suka cigaba da hirarrakinsu gaba daya.
Can zuwa shabiyu lokacin har Hajiya ta fara gyangyadi a falon, sukayi mata sallama
domin ta samu tayi baccinta. Suna fita suka nufi gidan Yaya Bello a motar Abba
tunda shi Yaya Bello bai zo da mota ba.
__
Lokacin da Yaya Bello da Abban Saddiku suke shiga gidan Yaya Bellon yayi daidai da
lokacin da Aisha suke fitowa tare da Asma’u yayinda Anti Zalihan take biye dasu
tana yiwa Aisha sallama da godiya.
Kana shiga gate din gidan dan karamin farfajiya ne inda daga nan zaka shiga wata
kofar mai irin siririn soron nan sannan ka fada tsakar gidan. Kasancewar kofar
falon baki wanda take a farfajiyar farko a rufe take sai Yaya Bello ya wuce gaba
suka nufi cikin gidan ta wannan soron.
Suna daf da kaiwa karshen soron Aisha ta sako kai Asma’u na biye da ita. Ganin Yaya
Bello ta tsaya ta fara kokarin kaucewa ta bashi hanya ya shige, tana shirin rage
tsawo ta gaisheshi ta hango Abban Sadik a bayansa.
Kamar bai ji abinda yace ba ya bude baki a hankali har yanzu idonsa a kan Aishan
cike da tsananin mamaki yace
Ta kawar da kai ta dan share kwallar da ta fito daga idonta, a dai-dai lokacin
Asma’u ta koma cikin tsakar gidan ta zauna a kan kujera domin jiransu.
Cike da mamaki Yaya Bello ya fara binsu da kallo daya bayan daya yana kokarin ya
fahimci abinda yake faruwa. Ya gyara tsayuwa yace
‘A’a! Me yake faruwa ne? Me yake faruwa ne? Ya zaka ce nan ta dawo bayan da na fita
ma bata zo ba.’
Kafin ya bashi amsa ya kama hannunsa ya dubi Aishan yana nuna mata cikin gidan yana
fadin
‘Mu koma naji abinda yake faruwa, kunata kallon juna kamar wasu baki.’
Ta bude baki zata yi magana yayinda Yaya Bello ya janyo Abban suka nufi cikin, bata
da wani zabi don haka ta wuce gaba suka bita a baya domin idan ta tsaya wajen ma ba
zai isa su wuce ba.
Babu wanda ya amsa mata don haka ta matsa Abban Sadik da Yaya Bello suka zauna a
kujerar zaman mutum uku yayinda ita da Aishan suka zauna a kujerun zaman mutum
daya. Yaya Bello ya dubi Aishan yace
‘Aisha me yake faruwa ne, kamar mamakin ganin juna kukeyi ke har kina share kwalla.
Me yake faruwa ne?’
Bata sami bakin bayar da amsa ba saboda hawayen da take ta faman tokarewa ne ya
kwace ya wanke mata fuska gaba daya, ta sa hannu ta fara share hawayen.
Cikin tsananin damuwa da mamaki Yaya Bello ya gyara zama yana dubansu daga wannan
ya dubi wannan. Yace
Ya sa hannu ya goge fuskarsa yana muttsike ido kamar wanda ya tashi daga bacci, a
hankali ya bude baki yace
‘Yaya babu komai fa, na dai dade ban ga Aishan bane kawai.’
‘Ikon Allah! To yaji tayi ko rabuwa kuka yi amma baku sanar ba.’
Gaba daya su suka yi shiru kowa yana ta faman zare ido, itama Anti Zulaiha sai
kallonsu take tana mamaki don bata ma fahimci kan zancen ba. Yaya Bello ya katse
shirun ya dubi Aishan yace
‘Aisha me yake faruwa ne? Ya sake ki ne ko me ya faru?’
‘A’a bai sake ni ba, ya dai kusa shekara biyu bai zo gidan da nake ba shi yasa muka
dade bamu hadu ba.’
Yaya Bello ya sake shiga rudani, ya kalli Aishan ya kalli Yusuf din. Aisha ta sake
share hawaye, ta bashi labarin yanda abubuwan suka faru. Binta kawai yake da kallo
yana mamaki. Ya dubi Abban Sadik din yace
‘Yusufa kai kuma kana auren mace kawai sai baka ganta ba kuma ba zaka nemeta ba?’
‘Wallahi Yaya ni kaina har yanzu ina mamaki, don ni sai yanzu ma fa da na ganta na
tuna da ita. Na kasa gane me yake faruwa ma gaba daya wallahi.’
‘Ikon Allah! To ni kaina ma ban fahimceku ba. Amma Yusufa ya za ayi ace kai da
matarka kuma ga gidan da take kusa da daya gidan amma kace wai ka kusa shekara baku
hadu ba. Wannan din wacce irin rayuwa ce?’
‘Wallahi Yaya nima sai yanzun nake mamaki, kamar ma gaba daya mantawa nayi da wani
bangaren na rayuwata. Gaba daya ma na kasa ganewa.’
Sukayi shiru kowa da abinda yake ransa. Jimawa kadan Anti Karima tayi gyaran murya
tace
‘Gaskiya Abban Muhammad ni ina ga ka kirawo Malam Sama’ila tunda yau asabar
watakila yana gida, domin wannan abun yayi kama da aljannu ko shaidanu. Gara ka
gane kan komai a dauki mataki kafin su bar nan su sake komawa ruwa.’
Yace
‘Hakane gaskiya, bari nayi masa waya na san yanzu zai shigo in sha Allah.’
Ya dauko waya ya kirawoshi, yace masa yana bakin titi zai fita amma yanzu zai dawo.
Jimawa kadan Yaya Bello ya kasa hakuri ya kirawo Muhammad yace masa ya fita waje da
zarar Malam Sama’ila ya zo su shigo tare. Yana fitowa suka hadu suka shigo ya nuna
masa falon.
Bayan sun gaisa Abban Muhammad yayi masa bayanin abinda yake faruwa, ya rufe da
‘To Malam Sama’ila abun ne naga kamar na mutanen boye, to shine nace gara ka zo
muji ko da akwai abinda za a taimaka da shi.’
‘To gaskiya Alhaji wannan bayanin da kayi min ya fi kama da sihiri, Allah ne ma ya
takaita abun. Watakila kai din kana da wata kariya ko kuma gidan naka na da makari
shi yasa da suka shigo suka ga juna. Tunda idan ban manta ba lokacin da na yiwa
Asma’u rukiyya na baka taimako kala-kala naka da na yaran.’
‘Hakane. To yanzu ya za ayi Malam? Na iya barinsu su koma gidan don ni gaskiya ina
tsoron su koma su sake mantawa.’
Suka sake yin shiru na dan lokaci.
‘Akwai Malam Audurahmanu, kai ka san shi ai wanda yake zuwa mana limancin sallar
dare da azumi. Sai dai shi a unguwar koki yake, shine ya kware a aikin sihiri ni
dai ka barni da rukiyya idan aljani ya bayyana a jikin mutum.’
Gaba daya suka mike suka fito, har sun kusan fita Yaya Bello ya koma yacewa Anti
Karima
‘Ina ga ki dauko mayafi muje saboda ita Aisha din kya zauna da ita.’
Don haka ta saka hijabinta suka shiga motar Abban Sadik Yaya Bello ya tuka suka
kama hanya.
A makaranta suka sami Malam Audurahmanu, babu dalibai don an tashi ‘yan islamiyya
don haka ya nuna musu aji suka zauna.
Bayan Malam Sama’ila yayi masa bayani ya tambayi Aisha itama tayi nata bayanin, shi
kuwa Abban Sadik da aka tambayeshi ma kasa bayanin yayi; abinda yake tunawa kawai
shine ya dade bai ga Aishan ba kuma ya san bai saketa ba.
Malam Audurahmanu ya dubi Yaya Bello yace
‘Ina zuwa.’
Jimawa kadan ya dawo dauke da robar ruwa karama guda biyu da kuma wani mai a 'yar
roba kamar ta Robb. Ya mikawa Aisha robar ruwan guda daya yace ta shanye, ta kalli
Anti Karima ta daga mata kai don haka tayi Bismillah ta shanye. Ya mikawa Abban
Sadik din dayan yace shima ya shanye, ba tare da wani musu ba ya shanye.
‘Ayoyin karya sihiri ne, sune matakin farko za a sha na kwana bakwai.’
Aisha tace
‘Ni dama tunda abun ya faru kullum sai na tofa ayoyin na sha sai dai a ruwan fanfo
ne ba na zamzam ba.’
Malam yace
‘Ma Sha Allahu to shi ya sa ma abun baiyi wani tasiri sosai a kanki ba, karanta min
ayoyin naji.’
Nan take ta karanta masa ayoyin ba tare da wani kuskure ba.
‘Ma sha Allah, in dai kika rike wannan babu wani sihiri da zai yi tasiri a kanki,
ko yayi ma na dan lokaci ne tunda Allah yana jarraba bawa da abinda ya so.’
Ya mikawa Abban Sadik ‘yar robar hannunsa yace ka lakaci wannan ka shafa a kanka.
Ya karbi robar ya rike amma ya kasa ko budewa, jujjuyata kawai yakeyi yana
kallonta. Kafin yace wani abu Yaya Bello ya karba ya bude, ya lakaci man da yake
ciki ya muttsike a hannunsa ya cire hular Abban Sadik din ya kama kan nasa ya shafe
masa man tas. Nan da nan idonsa yayi ja ya fara neman birkicewa, Malam Sama’ila da
yake gefensa ya dafe shi ya fara karatu.
Sai da suka shiga ofishinsa suka zauna sannan Malam yayi gyaran murya ya dubeshi
yace
‘Wato Malam Bello sihiri ne aka yiwa dan uwanka don a rabashi da mai dakinsa,
aljanine aka saka masa wanda gaba daya yake hanashi tunawa da ita. Saboda yanda
aljanine yake tare da shi kuma duk ma wanda ya so ya tuna masa ita to ba zai yarda
su hadu ba. Amma Allah ya kawo makarin abun tunda ka ga wannanan man da ka shafa
masa a kansa kamshin mutuwa yayiwa aljanin don haka ba zai sake dawowa ba. Sai dai
da yake yana da wata matar kuma ga maganganun da ta gayawa wannan din za a iya cewa
itace tayi wannan aika-aikar; duk da dai bai halatta a zargeta ba domin shaidanu
makaryata ne. Amma yanzu idan kun tafi to a barshi ya cigaba da kwana gidan ita
waccan din, zan bayar da ruwan tofi da zai dinga sha tsawon kwana bakwai kuma da
addu’oi. Sannan a samu ko shi ko wani a dinga karanta bakara a dakin da yake kwana.
In Sha Allah bayan kwana bakwai din sai ku dawo sannan sai ya koma rabon kwana
kamar da.’
Yaya Bello ya jijjiga kai yana mamakin yanda Zahra zata yi haka, tunda yake bai
taba jin matar da Hajiya take yabo kamar ita ba, don ko matarsa da ita aka fara
aurowa Hajiya bata sonta kamar yanda take son Zahra.
Nan suka koma ajin, bayan sun koma ya sake yi musu bayani gaba daya kuma ya gaya
musu kada su zargi kowa balle a sami wata sabuwar fitna don shaidanu haka suke so.
Ya basu umarni suje su cigaba da addu’a komai zai dawo dai-dai, ya sake bawa Aisha
hakuri sannan sukayi sallama suka tafi.
Sai da suka fito sannan Aisha ta tuna da Amira, take ta buga mata waya tace ta
zauna ko a library ne ta jirata nan da awa daya zata karaso.
Gidan Yaya Bellon suka koma inda sai da sukayi Sallah suka ci abinci sannan Aisha
tayi musu sallama ta ja motarta ta tafi.
Duk yanda yake tsananin son magana da Aisha haka ya hakura ta tafi, sai dai ya bari
kawai idan ya fito daga gidan Yaya Bello sai yayi mata waya ko yaya ne yaji
muryarta tunda Malam yace kada yaje gidan da take.
--------
Saida ta dauki Amira sannan suka wuce gidan, tana shiga tayi wanka ta canza kaya
sannan ta zauna ta kirawo Hajiya ta gaya mata abinda ake ciki. Nan take Hajiya ta
bata shawarar ta yi sadaka kuma ta cigaba da addu’a. Haka tabi ‘yan uwanta da kira
duk ta sanar da su su cigaba da tayata addu’a.
Duk da Malam yace kada ya zo gidanta sai an kwana bakwai wannan bai hanata walwala
ba, tunda dai an warware matsalar. Haka ta kwana tana Sallah da addu’a cikin
walwala.
---------
Tunda Aishan ta fita Abban Sadik yake kokarin cewa zai tafi amma Yaya Bello ya
hanashi, ya kula gidan Aishan yake son zuwa kuma Malam yace kada yaje sai an gama
addu’a. Nan ya rikeshi har saida sukayi Sallar Magriba kamar yanda ya saba. Ya
jaddada masa addu’oi da kuma karatun kur’ani wanda Malam yace yayi sannan yace
‘Idan bakayi karatun kur’ani a dakin ba ni zan iya dauko Malam muzo muyi maka
karatun ka dai sani don haka ka tabbatar kayi abinda Malam yace.’
Saida suka kusa shiga unguwar sannan ya sami waje yayi parking, ya zaro wayarsa da
nufin ya kirawo Aisha. Ga mamakinsa babu irin binciken da baiyi a wayar ba amma
babu lambar Aisha, ya budo Whatsapp ma ya duba ko zai sami chats din ya dauki
lambar daga nan amma bai samu ba. Gashi dama ya san bai taba haddace lambarta ba
lambar Zahra kawai ya haddace kuma da kunya ya kirawo wani yace a bashi lambar
Aisha bayan tana gidansa. Haka ya gaji ya hakura zuciyarsa babu dadi ya kama hanyar
gidan.
Ta gaban gate din gidan da Aishan take ya wuce, sai da yayi slow ya karewa gidan
kallo yana mamakin yanda ya dade bai ga gidan a wajen ba domin kullum ta nan yake
bi idan ya dawo daga aiki. Haka ya wuce gidan Zahra yana mamakin wannan abun.
-------
Yanda ta saba taryarsa cikin walwala idan ya dawo haka tayi masa; Saida ya huta
yayi sallar isha’i sannan ta kawo masa abincin dare. Binta kawai yakeyi da kallo
domin abubuwan da suka faru yau tabbas sun haifar masa da wasi-wasi game da wacece
Zahra; canza masa akayi ko kuwa dama can haka zuciyarta take. Baya jin zai iya
tunkarar ta da wannan zancen a yanzu musamman da yake Malam yace kada su tada wata
tarzoma kuma da dan sauran shakkarta a zuciyarsa. Don haka ya barwa tashi zuciyar
wannan batun.
Haka tayi ta hidima da shi tana jansa da hira, domin tun da ta gane ba zata iya
zuwa a raba shi da ‘yan uwansa yanzu ba sai ya zama duk lokacin da ya wuni wajensu
idan ya dawo haka zatayi ta kokarin faranta masa rai domin ya gane ta fi su sonshi.
Bata ga alamar damuwa a tattare da shi ba sai dai ta kula da yanda tunaninsa yake
yin nisa daga inda take, haka dai tayi ta fama. Ko da suka kwanta ma duk yanda ta
kai ga dagewa haka ta hakura ta barshi domin gaba daya nuna mata yayi bacci yake ji
ba zai iya ba. Bai fiya kin sauraron bukatarta a wannan lokacin ba don haka ta
kwana cikin damuwa da fatan Allah ya sa ba wani abu Yaya Bellon yayi masa ba.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
36
Tun bayan da suka dawo daga gidan Malam Aisha ta fara shirin tarbar Abba, tunda
tana ji aka ce bayan kwana bakwai zai fara rabon kwana.
Duka labulayen gidan ta bayar aka wanke, suka share ko ina suka gyara ita da Amira.
Ita kanta sai da gidan ya bata sha’awa saboda akwai abubuwa na gyaran gidan da ta
dade bata yi ba.
Musamman ta sami lokaci suka je sayayya ita da Amira saboda kayan gyaran fatar ta
duk sun kare bata sayi wasu ba.
Ranar Alhamis taje saloon aka yi mata gyaran jiki da kitso, tsaf aka goge mata fata
ta fara sheki.
Ita kanta bata san irin tarbar da zata yi masa ba domin gaskiya tana jin haushinsa
sai dai tayi shirin ne don tana so ya sameta yanda take so.
-------
Nasiha ya sake yi musu sannan ya basu addu’oin da kuma turare wanda yace Aisha ta
turara shi a gidanta yau din nan kafin maigidan ya shiga. Suka yi masa sallama suka
koma gidan Yaya Bello.
Sun dauki lokaci suna hirarsu ita da Anti Karima sannan tayi musu sallama ta fito,
ta sami Yaya Bello tare da Abban Sadik a falon. Ta yiwa Yaya Bello sallama tare da
godiya sannan ta fice.
Da hanzari Abban Sadik din ya mike ya bi bayanta, ta zauna a mota tana kokarin saka
mukulli ya bude kofar gaban motar ya zauna kafafunsa suna waje.
Hannunta yana kan sitiyarin motar ta kawar da kai ta dubi daya gefen, ya dubeta
yayi murmushi. A can kasan makogoronsa ya kirawo sunanta
‘Aisha.’
Yanayin muryar tasa sai da yasa taji kiran kamar a tsakar kanta. Ta juyo ta dube
shi ba tare da ta amsa ba. Murmushi ya sake yi mata sannan yace
A hankali tace
‘Toh.’
Ya sa hannu ya dauki wayarta wadda take ajiye a kusa da giyar motar, ya lalubo
lambarsa ya danna kira. Sai dai ga mamakinsa lambar ta ki shiga wanda ya sa ya gane
blocking din lambarta akayi a wayarsa. Nan da nan ya dauki tasa wayar ya duba jerin
blocked numbers, yana kalla kuwa ya gane lambar tata domin dama haddacewa ne bai yi
ba. Nan take ya cireta daga blocking kuma ya mayar yayi saving.
Suka dauki lokaci a zaune a haka; shi yana faman kare mata kallo ita kuma ta ki
kallonsa kuma taki magana.
Jimawa kadan ya kirawo sunanta yana murmushi, ta juyo ta kalleshi ba tare da ta
amsa ba. Suka hada ido, ta dauke kanta yayinda shi kuma yayi mata murmushi. Yace
Tace
‘A dawo lafiya.’
Sai da yayi kokawa da zuciyarsa sannan ya fita daga motar, kafin ya gama shigewa
cikin gidan ta ja mota ta kama hanya.
Yana shiga cikin gidan bayan ya zauna ya lalubo lambar account dinta ya tura mata
Naira dubu hamsin. Bayan kudin ya tafi ya tura mata sakon text message
“Ban san me ake bukata ba a gidan amma na turo 50k kiyi cefane kafin nazo.”
Yaran duk suna islamiyya don haka ita kadai ce a falo tana zaune tana ta cin
goriba. Bayan ta amsa sallamarsa tayi masa sannu da zuwa. Ya dubeta yace
Tace
‘Wallahi. Yarane suka siyo zasu tafi islamiyya shine na dauki guda biyu.’
Sai da ta gama cin gorubar sannan ta bi shi saman; yana kashingide a kan gado yana
hutawa. Bayan ya amsa sallamarta ta zauna a gefen gadon kusa da kafarsa tace
‘Sannu da hutawa yallabai.’
Da walwalarsa ya amsa
Ta kula kamar hutawa yake son yi don haka ta mike tana fadin
‘Yauwa, kada kiyi abincin dare da ni a wajen Aisha zan kwana yau.’
Ta kula da yanda yake kallon nata don haka ta rufe bakinta ta dan yi gyaran murya
tace
‘Uhm, to!’
Ya tashi ya gyara zama yabi kofar da kallo yana mamakin Zahra, tabbas yanzu ko ba a
gaya masa ba ya san tana da hannu a cikin abubuwan da suke faruwa.
To ya zai yi da Zahra? Gashi ta cika masa gida da ‘yaya, sannan kuma yana ganin
idan ma ya rabu da ita yanzu gaskiya bai yi mata adalci ba. Soyayya sukayi sosai ya
aurota, gashi yanzu gani yake kamar bata da kowa sai shi domin iyayenta duk sun
rasu kuma gidansu ma an raba gadon an siyar. Sai gidan Muhammad yayanta da shine
kamar waliyinsu da kuma gidan kakanni kawai. Kuma idan ya kori Zahra ma to ya zai
yi da ‘yayanta;shi har yanzu uwarsa tana nan yana jin dadin zama da ita baya yiwa
yaransa fatan su rayuwa babu uwa.
Ya fada a fili.
Ya gyara zama , ya dubi agogon bangon da yake dakin yaga karfe shida saura. Ya koma
ya sake kwanciya a gefen gadon yana tunanin yanda zai yi da Zahra.
………..
Tana fita daga dakin ta wuce dakinta, nema take tayi karo da bango saboda yanda
idonta yake rufewa. Ya za ayi ace aiki ya karye, kenan yanzu ya tuna da Aisha? Ita
yake gayawa gidan Aisha zai je?
Ido rufe ta fada kan gadon tana huci saboda takaici. To yanzu ya zata yi? Ta shafa
cikinta saboda yanda yake ta mutsu-mutsu. Ta ja numfashi, gaba daya kwakwalwarta
nema take ta daina aiki.
Ta lalubo wayarta sai kuma ta tuna wayar tana falon kasa, ta tashi tana bin bango
saboda yanda jiri yake kwasarta. Ta lallaba ta sauka ta dauko wayar ta dawo dakin.
Har ta zauna a gefen gado sai kuma ta tuna zai iya biyota kuma idan ya tsaya a
bayan kofar akwai yiwuwar ya jiyo abinda take fada, don haka ta tashi ta shige
bandaki ta turo kofa. Ta rufe toilet ta zauna a kai sanna ta lalubo lambar Amina ta
danna mata kira.
‘Mtsewwe! Amina Ina cikin damuwa yanzun nan Abban Sadik ya dubi tsabar idona yake
gaya min wai a gidan Aisha zai kwana.’
‘Eyee! Aisha kuma? To me ya faru? Don kuwa mutumin nan bai taba yin aikin ya karye
ba wallahi?’
‘To wallahi wannan dai ya karye don yanzun nan yake gaya min wai kada nayi masa
abincin dare a can zai kwana. Amina yarinyar nan so take ta kasheni da raina ba
zata bar min Yusuf ba.’
‘Wallahi ban sani ba Amina, bana son zuwa Doguwa da cikin nan kuma gashi kince shi
ba a masa waya.’
‘Shifa baya bada lambar waya ma don ka’idarsa ce ba waya gaskiya sai dai idan aje.
Kuma kinga ni yanzu ba zan iya zuwa ba saboda kinga Ummanmu ma jikinta yayi
tsananin shekaran jiya aka kawo ta nan don mu dinga zuwa asibiti, kinga ba zan fita
na barta ba.’
‘To ki daga musu kafa a kwana biyu in ya so ma ki gane inda ya sa gaba. Kinga yanzu
idan dai ina lissafi daidai cikin ki yayi wata biyar kinga nan da wata hudu zaki
sauka, da kinyi arba’in sai muje. Idan kuma ma nan da kwana biyu jikin Ummanmu yayi
sauki sai naje miki Doguwan. Ke dai kawai ki tanadi kudi.’
‘Uhm, kin ji wata matsalar kuma don wallahi bani da kudi ma amma dole na nemo. Bari
mu gani kafin lokacin ko wani abun sai na daga na siyar kawai aje.’
Suka ajiye wayar ta fito daga bandakin tana ta faman hada gumi, ta zauna a kan
gadon ta kafa tagumi.
Tunani daya ne a ranta kada taje Abba ya gane itace tayi wannan asirin. A hankali
hawaye ya fara bin fuskarta.
Lallai ta yarda Aisha ta fita hatsabibanci, amma tabbas idan dai da bokaye da
malamai a garin nan sai tayi maganin Aisha; sa’arta daya yanzu tana da ciki, ga
laulayi gashi kuma tunda aka tabbatar mata da namiji ne take kaffa kaffa da shi.
Bata son taje wani daji ta kwaso masa matsala.
Tana nan zaune bata san me take tunani ba taji shigowar ‘yan islamiyya. Yusra ce ta
fara shigowa ta sameta a dakin, nan ta gaya mata bata jin dadi su zauna a falon
kasa. Haka ta kwanta ta rufe idonta saboda kada su dameta, domin ko abincin dare
sai Jummai ta gayawa ta dafa musu.
Tana jin lokacin da Abban ya fito domin tafiya masallaci sallar Magriba, ta san
idan yayi tunanin tana kasa can zai wuce idan bai sameta ba kawai yaran zai gayawa
suce mata ya tafi masallaci. Hakan kuwa akayi, sai da ta lumshe Ido da ta ji
saukarsa kasa bai shigo dakin nata ba domin bata son ganinsa a halin yanzu.
…………
Ana idar da sallar Magriba Abban Sadik yayo sauri ya ja liman suka koma gefe, yayi
masa bayanin halin da ake ciki sai dai bai gaya masa daga gida bane. Nuna masa yayi
a office ne ake neman jifansa da sihiri. Ya bashi addu’oin da zai dinga yi sannan
kuma yayi masa alkawarin akwai abinda zai karbo masa zuwa wani satin, suna nan
tsaye suna hirarrakinsu har akayi kiran sallar isha’i don haka suka koma masallaci
suka tada Sallah.
………….
Tun bayan da aka idar da sallar Magriba take sauraron dawowarsa amma har akayi
isha’i bai shigo ba.
Da kyar ta tashi ta hade sallar Magriba da isha’i tana yin sallar tana tunani wato
ma wucewa yayi gidan Aishan ba tare da yayi mata ssallama ba.
Nan ta zauna a kan daddumar tana ta tunani kala-kala na yanda zata bullowa wannan
al’amari, domin ba zata yarda ba.
Bata ji lokacin da ya shigo gidan ba saboda tunaninta baya wajen, jinsa kawai tayi
ya turo kofar dakinta ya shigo.
‘To ni zan wuce, don Allah a rufe gidan da wuri kuma idan Saddiku ya kai goman dare
bai dawo ba kiyi min waya.’
---------
Ba karamar jarumta yayi ba da ya daure bai je wajen Aisha ba har akayi sallar
isha’i.
Tun daga bakin gate kamshin turaren wutarta yayi masa maraba, shi kanshi ya san
yayi kewar wannan turaren. Ya karasa ya sa mukullinsa ya shiga kofar falon. Babu
kowa a falon, ya dan tsaya ya karewa falon kallo; sai yanzu ya tabbatar ya dade
rabon da ya shigo gidan nan. Ya ji motsi a dakin baki wanda ya san Amira ce, bai
hango fitila a dakinsa ba sai a dakinta don haka ya tura kofar dakin a hankali ya
shiga da sallama.
Tana zaune a kan gado ta mike kafa tana ta faman danne danne a waya, bai sani ba ko
ta amsa sallamarsa ko bata amsa ba don shi dai bai ji muryarta ba.
Ya karasa ya zauna a gefen gadon yayinda ta dan janye kafarta, yana ta faman binta
da kallo kamar yau ya fara ganinta. Ta bude baki kamar bata so tace
‘Sannu da zuwa.’
‘Yauwa Aisha.’
Jimawa kadan ta gaji da kallon da yake mata, ta zuro kafafunta kasa daga kan gadon
ta mike tsaye tana fadin
‘Ga abincinka can a kan dining table muje na zuba maka kaci dare yana yi.’
Nan da nan shima ya mike ya sha gabanta, kafin tayi wani yunkuri ya janyota jikinsa
gaba daya ya rungumeta. Bata da kuzarin kwacewa domin itama tayi kewarsa don haka
ta rungumeshi. A hankali ya fara bin wuyanta yana sumbata yana kara kankameta, sai
da tayi da gaske ta tattara nutsuwarta ta dan tureshi tana fadin
‘Muje kaci abinci fa dare yana yi.’
Ya kalleta suka hada ido ya dan kara matsawa kusa da ita ya sumbaci lebenta, taja
baya. Yace
‘Aisha ba kiyi kewata ba kenan?’
‘Hmm!’
Ya dubeta yace
‘Na ci nawa.’
‘Ban tabbatar zaka zo ba har sai da na ganka yanzu, shi yasa dana idar da sallar
isha’i baka shigo ba na ci abincin.’
Duk yanda ya kai ga jun tausayin kansa sai da yaji tausayinta fiye da yanda yake
tausayin kansa, da kyar ya danne kwallar da ta taso masa saboda baya so ya kara
raunana mata zuciya. Ya mika hannunsa ya kama hannunta wanda yake ajiye a kan tebur
din, ya sumbaci hannun ya rike yana cigaba da shafawa. Yace
‘Ban san da bakin da zan baki hakuri ba Aisha, ban san kuma irin hakurin da zan
baki ba. An cutar dake kuma an cutar damu gaba daya.’
Tace
Ya saka hannunsa na dama yana cin abincin yayinda hannunsa na hagu yake rike da
hannunta na dama, yana cin abincin yana kallon fuskarta.
Bayan ya gama cin abincin sai da ya tayata ta kwashe kwanukan sanna ya jata suka
zauna a kan doguwar kujera falo.
Duk da TV a kashe take amma ita Aisha da ta zauna gaba take kallo shi kuma da ya
tashi sai ya zauna yana fuskantar Aishan. Ya kamo hannunta ya sumbata, ya juyo da
fuskarta wadda ba shi take kallo ba ya sumbaci lebenta. Ta bude baki zata yi magana
ya rigata
Yana rike da ita ya zagaya ya kashe fitilun falon domin gani yakeyi idan ya saketa
zata iya tafiya dakinta tace fushi take yi dashi. Sai da ya kashe fitilun tas
sannan ya jata suka shige daki.
Duk yanda ta so ta dage a wannan dare Abban Sadik bai bata dama ba, haka suka kwana
suna biyan bashin juna cikin walwala.
………..
Yanda Aisha da Yusuf suka kwana suna walwala haka Zahra ta kwana cikin kunci da
lissafin yanda zata yi da Aisha; domin ba zata taba bar mata Abban Sadik ba.
Gaba daya tunaninta ya kare, duk iya satar bacci haka ya kyaleta sai bayan asuba
sannan ta sami baccin.
__
Cikin walwala suka wayi gari Lahadi, sai wajen karfe goma sannan suka gama
breakfast a lokacin ya fice don ya dubo Zahra da yaran. Yanda ya barta jiya haka ya
sameta yau, ya riga ya san abinda yake damunta kishi ne na rashin tunani ta dorawa
kanta don haka ba tare da bata lokaci ba suka gaisa ya fito ya bar mata gidan tunda
yara duk suna tahfiz.
Tana so ta yarda bai fahimci wanda ya raba shi da Aisha ba amma kuma tana mamakin
yanda jiya zuwa yau yake nuna mata wani hali na ko in kula. Amma dai ta san dole ta
saurara yanzu zuwa lokacin da zata sami kanta.
…………..
Bayan azahar Abba ya dauki Aisha suka tafi gidan Hajiya, ya riga ya san yayi musu
laifi don haka suka je ya sami Hajiya da Anti Uwani ya basu hakuri. Daga nan suka
wuce gidan Yaya Abubakar shima ya sameshi yayi ta bashi hakuri. Sai bayan la’asar
sannan suka dawo gidan zuwa lokacin har Amira ta dora abincin dare.
Bayan sallar isha’I tana kicin tana jiyoshi yana waya da Jibrin.
Bayan ta shigo falon yake tambayarta rasit na biyan kudin hayar gidan, ta dauko
daga daki ta bashi. Kafin su kwanta bacci taji alert ya tura mata kudin hayar da ta
biya harda Karin dubu dari. Ta tambayeshi to karin na menene, yace
‘Duk tsawo lokacin nan ke kike ciyar da kanki kina yin komai wanda ba haka ya
kamata ba ai kinga dole na biya bashi ko. Na san abinda kika ci ma ya fi dubu dari
in Sha Allahu idan aka kwana biyu zan ciko sauran don na san matata akwai cinye
buhun shinkafa.’
Tayi dariya.
Babu yanda bata yi da shi a kan ba sai ya sake turowa ba amma ko sauraronta bai yi
ba, suka cigaba da hirarasu.
Da sati ya zagayo kuma haka ya sake daukan Aisha suka zaga danginsa.
Yanda Hajiya ta saba karbarta cikin halin ko in kula haka ta yi mata, shi kanshi
Abban sai da yaji babu dadi. Ya kara jin haushi Zahra saboda wannan matsalar da ta
kirkiro a lokacin da Hajiyan ta fara haduwa da Aisha itace dalilin wannan kiyayyar;
sannan kuma yanzu ga ciwo ga rikicin tsufa.
Sai da suka tsaya a gidan Yaya Bello sannan suka wuce gida.
Ita kuwa Zahra tun tana saka rai Abba zai tutsiyeta har ta sakankance bai gane
itace tayi musu asiri ba. Ta cigaba da kokarin tara kudi tunda tana son aje mata
wajen boka.
Shi kuma Abban ya kyaleta ne saboda cikin da yake jikinta da kuma tunanin da yakeyi
a kan makomar yaransa idan yace zai yi rigima da Zahra; yaran da daman yana ganin
kamar akwai gibi a tarbiyyarsu. Yana sane da yanda idan dai tana fushi da shi toh
gaba daya yaran suma sai su daina kulashi sai Rukayya da Sumayya ne kawai suke
kulashi ba zai ga walwalarsu ba har sai uwarsu ta daina fushi da shi. To idan ya
saketa yanzu yana jin yaki za a koma yi tsakaninshi da ‘yayanshi wanda shi din ba
haka yake so ba. Don haka ya kayaleta take cigaba da rayuwarta kamar bata yi masa
laifi ba, musamman da yake Malam Audurahmanu ya sanar da shi idan dai ya rike
addu’ar da ya bashi to lallai babu sihirin da zai sake tasiri a kansa.
__
Lokaci ya ja don haka kowa ya koma harkarsa kamar yanda aka saba.
Ranar Talata da yamma Zahra ta shirya ta tafi wajen scanning domin yanzu cikinta ya
kai kusan wata bakwai tunda yana motsi sosai har tana ganin motsinsa. So take a
kara tabbatar mata da cewa lallai namiji ne domin bata so abinda ya faru a haihuwar
Sumayya ya sake faruwa. Kamar yanda ta zata haka aka tabbatar mata da cewa lallai
namiji ne domin babu ma yanda za ayi ya zama mace.
Cikin walwala ta dawo gida, washegari kuma ta shirya ta tafi asibitin Nassarawa
awo. Aka duba ta sosai awajen awon, likita ya tabbatar mata da lafiyarta da kuma
lafiyar jaririnta. Don haka ta dawo gida cikin walwala bayan an rubuta mata
appointment ta dawo bayan sati hudu domin sake yin awo.
---------
Ranar Alhamis ce wadda ta kama saura kwana biyar Zahra ta koma awo.
Yau din tunda gari ya waye take jin jikinta babu dadi, gashi cikin yayi mata nauyi
sosai da kyar take jan kafa sannan ga mararta tana ciwo kadan-kadan. Nan da nan ta
gama abinda takeyi ta koma ta kwanta don bata ma jin kwari.
Har bacci ya fara kwasarta fitsari ya takura mararta, don haka ta tashi ta shiga
bandakin don yin fitsari. Tana sabule pant din da yake jikinta ta ga jini, nan da
nan hankalinta ya tashi. Tayi fitsarin ta fito tana kokarin fita daga dakin kuma
mararta ta kara tsanantawa da ciwo don haka ta koma ta durkusa a gefen gado.
Ta lalubo wayarta daga kan gadon ta kirawo Abban Sadik wanda yake office dinsa.
Bayan ta sanar da shi halin da ake ciki yace ta shirya ya zo su je asibiti domin
Malam Ali ya fita dauko Sumayya da Ummi daga makaranta.
Nan ya sameta a gefen gado tana faman dagewa saboda ciwo, ya kamata ta saka hijabi
sannan ya rikota suka sauko. Jummai bata san halin da ake ciki ba sai da suka
sauko; tayi mata sannu da fatan samun lafiya suka wuce asibiti.
Suna zuwa asibiti aka samu likita ya dubata saboda yanayi halin da take ciki.
Scanning likita ya turasu wanda da kyar Abba ya riketa suka je dakin da akayi mata,
aka bashi takardar ya rikota suka koma wajen likitan.
Cikin hanzari likitan ya karbi takardar ya fara dubawa, bayan ya gama dubawa ya
kalli Abban yace
‘Alhaji sai dai ayi hakuri, yaro ne a cikinta namiji amma Allah yayi masa rasuwa
shi yasa take bleeding. Yanzu zamu dubata mu taimaka mata ta haifeshi sai ayi masa
sutura.’
Nan take ita kuma ta fashe da kuka yayinda mararta take kara kartawa. Nan da nan
likita ya kirawo ma’aikatan jinya yace su saka ta a dakin labour room. Shi da Abban
suka bi bayansu.
Aka shige da ita yayinda Abban ya tsaya, jimawa kadan ya lalubo waya ya kirawo Yaya
Murja ya sanar da ita sannan ya kirawo Aisha da Yaya Bello ya sanar da suma halin
da ake ciki.
Ba tare da bata lokaci ba Yaya Murja ta iso asibitin,nan suka tsaya ita da Abban
suna ta jira. Sai wajen karfe uku na yamma sannan aka samu ta haifi yaron babu rai.
‘Sannu Hajiya, kin ganshi ko. Allah ya kawo wasu masu albarka.’
‘Allah ne ya kashe kayansa kinga kuwa sai muce Allah ya kawo masu albarka. Kar ki
damu Hajiya wannan ba wani bakin abu bane a wajen mace mai haihuwa tunda ma ke kina
da wasu yaran wannan ba zai zama matsala ba.’
Bayan an gama shiryata aka fito da ita aka bata daki inda likita yace zasu riketa
zuwa gobe saboda jininta ya dan hau. Aka nade gawar yaron aka bawa Abba. Bayan ya
tabbatar an bata daki sun zauna ita da Yaya Murja ya sanar da ita zai je ya kaiwa
Yaya Bello gawar ayi mata sutura sannan ya karbo musu abinci a gida.
‘Kiyi hakuri ki share wannan hawayen, in da rabo sai kiga kin haifi wani amma kina
ta kuka sai kace karamar yarinya.’
‘Yaya ya za ayi yaron da bai fi sati biyu ba aka duba aka tabbatar min kalau yake
kuma yanzu ace ya mutu?’
‘Hmm! Saboda ke baki taba yin bari bane shi yasa kike cewa haka. Ya za ayi ba zai
mutu ba tunda rayuwarsa tana hannun Allah. Ki kwantar da hankalinki wannan ba wani
abu bane, ke da kike da yara shida ai sai dai kawai ki cigaba da godiya ga Allah da
fatan Allah ya sa wahala ta zama kaffara.’
Ta janyo flask din da tazo da shi ta had a mata shayi mai kauri ta sakata a gaba
saida ta shanye. Jimawa kadan likita ya shigo yayi mata allura, kafin ya fita bacci
ya fara fuzgarta don haka ta hakura ta kwanta ba da son ranta ba. Yaya Murja ta
zauna a kan kujera tana jiran zuwan Suwaiba wadda tace zata biya ta taho da Rahma
saboda jinya.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
37
Tun kafin Suwaiba ta fito daga gida ta kirawo Rahama, sai dai bata dauka ba. Don
haka ta kirawo Innar su Rahman don ta sanar da ita zata zo sai ta dauki Rahma su
wuce.
Rahama tana daki a kwance tana kallon wayarta da taga Suwaiba ce taki dauka, haka
kawai jikinta ya bata gidan Zahra zasu ce taje ita kuma tayi alkawarin ba zata sake
komawa wannan gidan ba.
Tana jiyo Inna ta fara magana da Suwaiba a waya tayi tsalle ta fito tsakar gidan,
bayan Inna ta ajiye waya tace
‘Inna na gaya miki ba zan sake zuwa gidan nan ba, wallahi duk wani mutunci da kika
ga tana yi idan mutum bai taba yaranta bane. Ni dai gaskiya bana son zuwa gidan
nan.’
Haka Inna ta sakata a gaba tana bata baki, ba tare da bata lokaci ba Suwaiba ta zo
suka wuce asibitin.
Sai da yayi magana da likita kafin ya bar asibitin inda likitan ya tabbatar masa
zasu sallameta da zarar blood pressure dinta ya dawo dai-dai kuma ta daina ciwon
kai wanda take ta korafinsa tun bayan da ta haihu.
…………
Tun a daren Abba ya sanar da Aisha, tayi maganar abincin safe ya sanar da ita Yaya
Murja tace za a kai musu don haka ta bari idan yamma tayi sai ta dafa musu abincin
dare suje tare su dubota; idan ba a sallameta ba zuwa lokacin.
Ta sanar da mutanen gidansu wanda kafin wani lokaci Hajiyanta ta yiwa Hajiyan Abban
waya ta jajanta mata sannan kuma suka sa cewa gobe zasu je asibitin su dubota.
Suma su Yusra tunda Abban ya dawo gida suke ta tambayar labarin Mommy, don haka
yayi musu alkawarin gobe ko bai je da su duka ba zai je da wasunsu idan dai ba a
sallameta ba.
----------
Sai wajen karfe biyu Abba ya kirawo Aisha ya sanar da ita ta dafa wa Zahra abinci
zai zo da anyi sallar la’asar su wuce asibiti. Nan da nan ta fada kicin ta dafa
farfesun kaza sannan ta dafa shinkafa ta dafa macaroni tayi miyar dage-dage wadda
ta sha nama sannan ta hada coleslaw. Ta sami flask ta cika musu da ruwan zafi
saboda shan shayi.
Bayan ya fito daga office ne ya kirawo Yusra ya sanar da ita cewa su shirya ita da
kannenta in ya dawo zasu je asibiti, tunda ranar Juma’a ce babu islamiyya. Nan da
nan Jummai ta tayasu suka shirya ta tambayesu ko za a dafa wani abun Yusran tace
Abba yace Anti Murja ce take kaiwa.
---------
Sai da ya tsaya a wajen Aisha ya ci abinci sannan Aisha ta shirya cikin abayarta
mai kyau ta rufe kanta da mayafi mai kalar olive green ta dauki 'yar jakarta sannan
suka fito. Suna fitowa ta zare mukullan motar daga aljihunsa tana dariya tana fadin
Suka zuba abincin ya zauna a gaban motar ta ja suka fito daga gidan.
Tayi parking a kofar gidan Zahra, Abban ya fita ya shiga don ya fito da yaran.
Gaba daya su sun riga sun shirya don haka yana shiga suka fito yana dauke da
Sumayya yayinda yake rike da hannun Ummi ragowar suna biye da shi. Sai da Yusra
tayi turus da ta hango Aisha a motar Abba tana tukawa, ya karaso da su duk suka
shiga bayan motar.
Rukayya ce ta fara gaida Aisha wadda ta juya tana amsawa, suka suka gaisheta har
Yusra saboda Abban ya riga ya shiga motar. Ta ja motar suka kama hanya.
Sai da suka kamo hanya sosai yacewa Aishan idan sun zo kan tin gidan gwamna ta
tsaya zasu sayi fruit. Don haka suna zuwa ‘yar kasuwar nan da take kusa da Yahuza
suya ta tsaya; da hannu ya yafito mai fruit din wanda ya taho da guda. Yayi masa
lissafin lemon, ayaba da kuma apple na kusan dubu bakwai yace a saka a leda kuma ya
taho da POS machine ya karbi kudin.
Nan da nan mutumin ya juya da hanzari ya dauki leda ya fara cikawa yayinda shi kuma
Abban ya gyara zama ya fara laluben aljihunsa don dauko wallet dinsa wadda ATM card
dinsa suke ciki. Sai dai ga mamakinsa babu komai a cikin aljihun; ya dan yi tunani
yana rike da aljihun ya kalli Aisha wadda take kallonsa yace
Yayi dariya yayinda ta mika hannu inda kafarsa take ta dauko jakarta, ta zaro ATM
card dinta ta mikawa Abban a daidai lokacin da mai fruits din ya karaso dauke da
manyan ledodi guda biyu.
Abban ya fita ya karbi kayan ya saka a booth yayi amfani da katin Aisha ya biya
kudin sannan ya dawo ya zauna, ta ja motar suka wuce.
Abban ne a kan gaba har suka hau benen da dakin da aka kwantar da Zahran yake, suna
biye da shi sai da aka zo bakin kofa saboda ya san Rahma tana ciki ya ja baya yace
duka su shige. Ummi ce ta bude kofar suka shige gaba daya.
Rahma da Yaya Murja suna zaune a kan tabarma daga gefe yayinda ita kuma take gefe
guda yayinda ita kuma Zahran take kwance a kan gadon tana danna waya.
A hankali ta tashi ta gyara zamanta yayinda suka karasa suka tsattsaya a gefen
gadon, ta dan muskuta Yusra ta dauki Sumayya ta dora mata a gefen gadon. Aisha ta
karasa shiga dakin da sallama Abban yana biye da ita. Ta wuce ta zauna can daga
kusa da Yaya Murja yayinda shi kuma Abban ya ja kujerar da take ajiye daga daya
gefen ya zauna.
Ya gaida Yaya Murja da Rahma yayi musu ya mai jiki sannan ya mike ya karasa wajen
Zahran ya tsaya a bayan yaran.
Itama Aishan suka gaisa da Rahma da Yaya Murja tayi musu yaai jiki, ta mikawa Yaya
Murja kwandunan da suka zo dasu tayi musu bayani. Suka dan cigaba da hira Yaya
Murja tana tamabayarta mutanen gidansu.
Bayan ya gama tambayar Zahra jikin nata ya juya yayi wa Yaya Murja sallama ya dubi
Aisha yace
Ya mika mata hannu kamar mai karbar wani abu, ta zura hannu a jakarta ta dauko
mukullin motar ta saka masa a hannunsa ya juya ya fice bayan yayi wa su Yaya Murja
sallama.
Bayan ya fita Aisha ta mike ta matsa kusa da gadon suka gaisa da Zahran sannan ta
yi mata jaje tare da ya jiki. Da kyar take amsa mata tana ta faman harararta don
haka itama ba tare da bata lokaci ba ta koma ta zauna.
Suna hira jefi-jefi da su Rahma tana kula da agogon wayarta, minti goma sha biyar
suna cika ta yiwa Yaya Murja sallama ta dubi yaran tace
‘Rukayya ku zo muje 15 minutes din yayi kada mu bar Abba yana jira’
Ta fice.
Jimawa kadan yaran suka fice bayan Yaya Murja ta tasa keyarsu.
Su Zahra basu dade da fita ba Amina ta shigo, bayan sun gaisa Yaya Murja tayi musu
sallama ta tashi yayinda Rahma ta bita don tayi mata rakiya.
‘Na ga mutuniyarki sai wani sheki takeyi tana ta yiwa miji iyayi, na ga ma itace
take tuka motar saboda kauna.’
Ta ja tsaki
‘Hmm! Haka Yusra take gaya min ana ta soyayya a hanya. Ki barni kawai Amina!
Yarinyar nan ta raina ni wallahi. Na tabbatar da hannunta a wannan haihuwar da nayi
babu rai shine ta zo ta nuna min ta kwaci mijinta. Wallahi Amina sai nayi maganin
yarinyar nan.’
‘Hmmm! Kinga dai yanzu ki kwantar da hankalinki ki sami lafiya, sai ki san yanda
zakiyi ki tattaro kan kudi don kinga akwai wani malami da za a hadani da shi kwanan
nan kuma an ce aikinsa babu wasa. Kin san ina ta fama da Abban Asiya ina so na
dauki hutun aiki na bishi Abuja yana ta faman gocewa, zargin da nakeyi wata ya
ajiye a can shi yasa ko da tsiya-tsiya sai na je.’
Suka cigaba da hirarrakinsu suna shawarar yanda za a yi a sami kudi aje wajen
Malami, daga baya Rahma ta dawo don haka suka canza hirar.
___
Kwana daya Zahra ta kara a asibiti aka sallameta, suna dawowa gida Rahma tayi musu
sallama ta koma gidansu.
Duk wani ban baki da ban hakuri likitocin sun yiwa Zahra shi domin likita ya
tabbatar mata idan ta cigaba da zama da damuwa zata haifarwa kanta da hawan jini na
din-din-din, sai dai ita bata ga yanda za ayi ta kwantar da hankalinta ba. Duk wata
kulawa Abba yana bata sai dai har yanzu tana ji a jikinta cewa ya san abubuwan da
ta shirya kallonta kawai yakeyi.
A hankali tana kara samun lafiya tana cigaba da tunanin hanyar da zata bi ta sami
kudi. Bata son ta siyar da babbar saitin gwal dinta amma dai ta fara tunanin sayar
da na yaran. Bata son ta tambayi Abba kudi domin bata ga fuska ba duk da komai yana
yi mata kamar yanda ya saba sai dai kawai ita din ta kasa sakewa.
Kwanci tashi har an kai wajen wata uku da haihuwar da Zahra tayi babu rai, basu
samu sun je wajen boka ba saboda har yanzu mahaifiyar Amina a kwance take; domin
kusan za a iya cewa ta zama sai dai a kwantar a tayar. Don haka babu halin Amina
tayi nisa musamman da yake tana matukar kaunar mahaifiyar tata. Haka ta hakura tana
kallo mijin nata yana can Abuja ga shi Asiya tana kawo mata rahotannin cewa yana
tare da matan banza a can din amma babu yanda zata yi don ya ma hanata zuwa Abujan
gaba daya.
Hankalin Abba ya dawo jikinsa don haka ya nemi kudi ya sake fara business din sa;
sai dai wannan karon duk wani abu da zai yi na harkar business din sai idan yana
gidan Aisha ne yake yi domin ko wayar abokan kasuwancin nasa baya amsawa idan yana
gidan Zahra.
Tun tuni aka samarwa Saddiku da Yusra admission a jami’ar Maryam Abacha American
University wato MAAUN; Yusra tana karantar Business Administration yayinda Saddiku
yake karantar Accounting. Da yake kwanci tashi babu wahala gashi a halin yanzu har
suna zana jarrabawar zango na farko wato zasu gama level 1 su shiga level 2.
Tunda suka fara jarrabawa Saddiku yake gayawa Mommy ta karbar masa kudi a wajen
Abba naira dubu hamsin zasu hada suyi end of session party. Sai kaucewa zancen
takeyi saboda ta san yanzu bata da dama a wajen Abban yayin da shi kuma Saddikun
yake sake dagewa da yi mata naci. Haka dole ya sakata tayi masa alkawarin ko da
Abban bai bashi ba ita zata bashi ko da bai kai dubu hamsin din ba.
Kudaden da take hadawa domin suje wajen boka su kadai ne a account dinta domin ta
hada kusan dubu dari biyu; garwar motarta da akayi accident wadda take ajiye a
tsakar gida ita take jira ta sami mai siya ta hada kudin sai suje.
Wanna magiyar da Saddiku yake mata a kan kudin party ma ya kara mata kaimi wajen
ganin ta dawo da hankalin Abban kansu, bata son ganin yaranta a cikin damuwa
musamman Saddikun.
---------
A dakinta ya sameta tana zaune a kan dadduma ta idar da sallar isha’i, bayan ta
amsa sallamarsa ya wuce ya zauna a gabanta kamar mai daukar karatu. Ta dan kare
masa kallo; zuciyarta tana so ta yarda lallai Saddiku yana shaye shaye; to amma
bata ga lebensa da hannayensa suna yin baki ba irin na 'yan wiwi. Abinda bata gane
ba shine shi din ba hayaki yake sha ba kwayoyi yake sha masu tsada da kuma dauke
hankali nan take. Ya kwantar da kai yace
‘Mommy baki turo min 50k din ba, gobe fa zamuyi final paper kuma ranar Saturday
zamuyi party din.’
Tunda ya zauna dama ta san abinda zai tambaya kenan, ta jijjiga kai tana murmushi
‘Ku yanzu ba za ma ku iya tsayawa ku ga result ba kafin kuyi party din idan fa ba
ku ci jarrabawar ba.’
‘Haba Mommy, ai duk mun ci. Kin san a ajin wasu foreigners ne don haka ana gama
exam kowa zai tafi gida shi yasa zamuyi party din. Kusan kowa ma ya biya mu uku ake
jira. Don Allah Mommy ki karba min kudin nan kinga ina cikin organizers fa.’
Suka yi shiru na dan lokaci, jimawa kadan tace
‘Abbanku yace bashi da kudi kuma ka san idan nace masa party zakuyi ma ba zai bari
kaje ba, amma idan kana son 30k ni zan turo maka zuwa gobe idan kuma tayi kadan to
sai dai kai kaje ka tambayi Abban.’
Da sauri yace
Yana fatan idan ta bashi dubu talatin din daga baya sai ya san yanda zai yi ya
takureta ta kara masa ashirin din.
Party suka shirya su uku shi da abokansa, ‘yan ajinsu na Jami’a ma basu san da
wannan party din ba. Ya riga yayi alkawarin dubu dari biyu zai bayar gudummuwar
party din. Ya riga ya yagi mafi yawan kudin a wajen Abban ta hanyar karyar abubuwan
da aka ce su saya a makarantar, a halin yanzu dubu hamsin din kawai yake bukata ya
gama hada kudin su je suyi party dinsu.
………..
Babu yanda ta iya haka ta turawa Saddiku dubu talatin daga kudin da take ta faman
tarawa, sai dai duk nacinsa ta ki ta kara masa wasu kudin; ta dai gaya masa ya samo
makanike ya sayi gawar motarta da yayi accident idan an biyata sai ta kara masa.
Haka ya samo har mutum biyu, sai dai babu wanda ya taya motar a kan dubu dari ma.
Domin duk cewa sukeyi ba zata moru ba don har injinta ma ya tashi daga aiki. Haka
ta hakura ta sayarwa da na karshen a kan naira dubu sittin da biyar. Wanda a hakan
ma yace sai dai su bashi sati biyu zai kawo kudin sai ya dauki motar.
Sai bayan ya tafi Saddiku ya bishi ba da sanin Mommy ba ya karbe naira dubu goma
sha biyar a kan ya kai cikon ya dauko motar.
…………..
Tun bayan la’asar ya shirya yayiwa Mommy sallama. Ya dauki motarta ya tafi party;
motar da tana kallo yanzu ta zama ta Saddiku tunda da tana kokarin ta sa Abba ya
saya masa tashi motar amma yanzu ta san bata da wannan damar.
Kamar yanda Abba ya saba bayan magriba ya dawo gidan. A gidan Aisha zai kwana don
haka gidan Zahra ya sauka; bayan ya huta suka dan taba hira ita da shi da yaran.
Sai da ya dawo daga sallar isha’i sannan yayi mata sallama ya tafi. Kafin ya fita
kuma ya sanar da ita idan goman dare tayi Saddiku bai dawo ba tayi masa waya.
Ta san yace mata sun tafi party don haka bata sa rai zai dawo kafin karfe goma na
dare ba, don haka wajen tara da rabi ta kulle gidan ta turawa Saddiku message cewa
idan ya dawo yayi mata waya tunda ba ciki zai shigo ba a boys quarters dakinsa
yake.
Tunda ta kintsa ta kwanta bata farka ba sai karfe biyu na dare; agogonta ta fara
dubawa a wayarta taga lokaci.
Nan take ta dannawa Saddiku kira, har wayar ta tsinke bai dauka ba sai kawai tayi
zaton ya dawo bacci ne ya kwasheshi tunda ya kwaso gajiya don haka itama sai ta
gyara kwanciyarta ta cigaba da bacci.
__
Tana idar da sallar asuba ta sauko ta bude kofa ta leko tsakar gidan, so takeyi ta
tabbatar Saddiku ya dawo gidan jiya. Ga mamakinta babu motarta a tsakar gidan wanda
hakan yake nufin Saddiku bai kwana a gidan ba. Ta fito ta tsaya a kan baranda ta
kwalawa Malam Sado kira, da gudu ya taho yana rike da carbinsa da yake wiridi.
Bayan ya gaisheta ta amsa tace masa
A kan dining table din kasan ta zauna ta lalubo lambarsa a waya ta sake kira,
ringing kawai wayar take yi Amma ba a dauka ba. Hankalinta ya kai kololuwar tashi
da ta tuno haka yayi mata wancan lokacin da yayi accident. Nan da nan idanuwanta
suka cicciko da kwalla; da sauri ta fara laluben lambar wayar Abbansa. Sai da ta zo
kan lambar tasa sai kuma ta tsaya ta kasa kiransa; to yanzu idan ta kirawo shi me
zata ce masa? Ce mata yayi idan goma tayi Saddiku bai dawo ba ta kirawoshi amma
bata yi hakan ba sai yanzu da safe ta kirawoshi tace masa me? To idan fa accident
Saddikun ya sake yi
‘Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun.’
Ta fada a fili yayinda idonta ya cicciko da kwalla. Gashi bata san abokansa ba don
haka ma bata da lambar ko daya daga cikinsu. Ta tashi jikinta babu kwari ta koma
saman, ta zo daidai kofar dakin su Yusra taji motsinsu. Nan dabara ta fado mata; ta
karasa ta tura kofar ta kirawo Yusra. A dakin Yusran ta sameta, bayan ta amsa
gaisuwar ta tace
‘Yusra yayanki bai dawo gidan nan ba jiya gashi kuma ina ta kiran wayarsa bai dauka
ba, ko kina da lambar abokansa da suke party din tare na kirawosu muji?’
‘To gaskiya Mommy ni ban sani ba, kuma a abokansa mutum daya nake da lambarsa. Bari
na kirawo shi muji.’
Nan ta koma daki ta dauko wayarta ta dawo wajen Mommy din. Ta lalubo lambar Babs
wanda dan ajin su Saddiku ne, shima ta sami lambarsa ne saboda yana sonta duk da
ita din bata sauraronsa.
‘Today is going to be a good day tunda ke kika fara kirana Babe, to ya kike?’
Tace
‘Uhm! Lafiya. Ka san wani abu? Ya Sadik nake nema ka san tun jiya da daddare bai
dawo gida ba yace wai ‘yan class dinku suna end of year party shine nake son naji
me ya hanashi dawowa gashi Mommy tana nemansa.’
‘Party? Gaskiya ba dai ‘yan class din mu ba sai dai ko wasu friends din nasa, don
gaskiya duk mun koma gida ko nima kin ganni a KD.’
‘Amma bari na tambayar miki su Bigi duk da dai na san ba da su bane amma dai idan
har guys din mu ne suka shirya party din to lallai Bigi zai sani.’
Sukayi sallama bayan ya sanar da ita idan ya ji wani abu zai kirawota.
‘Kin ji Mommy!’
‘Hmm! Na ji Yusra. Ni haka yace min da 'yan class dinsu don sai da na bashi 20k
sannan kuma ya zagaya ya karbe kudin da aka sayar da garwar tsohuwar motata ba tare
da ya gaya min ba kuma cewa yayi duk a kan party din ne. To ina ya tafi?’
Jimawa kadan ta sallami Yusran don taje ta shirya mata yara su tafi tahfiz.
Haka tayi ta faman jan kafa cikin matsananciyar damuwa har wajen karfe goma saura.
Wajen karfe goma Abban ya shigo don ya dubasu ita da Yaran. Bayan ya amsa gaisuwar
Yusra a falon kasa ya haye saman. A dakinta ya sameta tana kashingide a gefen gado,
bayan sun gaisa ya zauna a gefen gadon kusa da kafafunta yace
‘Uhm, babu ko daya. Hutawa dai nake yi kafin ‘yan gidan su dawo.’
‘Saddiku har ya fice ko? Ai sun gama exam tunda ke bakya hawa motar yau in ya dawo
ya bani mukullin motar ya huta yawon ya isa haka, da anyi magana yace zasu je
lecture ko kuma zasu hadu suyi karatu.’
Ta dan muskuta
‘Um nima haka na gani, bari ya dawo sai na karbi mukullin motar na boye saboda in
zan fita.’
Suka dan taba hira daga baya yayi mata sallama ya fita; yana mamakin Zahra! Tun
tuni yake so ya karbe mukullin mota daga hannun Saddiku amma ta hanashi sai tace
ita zata kwace kuma bata iyawa. Lokuta da dama yana mamakita, yanda har yanzu ta
kasa gane cewa bata tarbiyyar Saddiku takeyi. Shi yasa har yanzu bai gayamata cewa
ba zai biyawa Saddiku kudin registration ba sai ya je makarantar da kansa ya ga
result dinsu.
Ta kasa gayawa Abba cewa bata ga Saddiku ba kuma ta rasa wanda zata gayawa gashi
har sha biyu saura, ta dai yanke shawarar idan aka yi kiran azahar bata sameshi ba
zata gayawa Abbansa.
Karfe Sha biyu da kwata wayarta tayi kara, ta dauki wayar kamar wadda aka yiwa dole
sai kuma ta ga sunan Saddiku, sai da zuciyarta ta nemi tsayawa lokacin da ta kara
wayar a kunnenta. Kafin tayi magana aka ce
‘Hello.’
Ba Saddiku bane yake magana, haka dai ta daure ta amsa. Bayan mai maganar ya
gaisheta yace
‘Um gamu nan da su a asibitin Malam Aminu Kano emergency shi da abokansa, suma
sukayi tun jiya a wajen party da suka sha kwaya, har yanzu basu farfado ba.’
Ta saki wayar a kan cinyarta daidai lokacin da hawaye ya wanke mata fuska.
Saddiku ya sha kwaya tun jiya ya suma? Yanzu me zata cewa Abbansu, bayan ta gama
gaya masa da safen nan Saddiku ya fita.
Ta mike tsaye, wayar da take ajiye a cinyarta ta subuce ta fadi kasa ta dauke wayar
ta ajiye a kan gadon. Ta karasa gaban wardrobe tana share hawaye ta dauko hijabi ta
saka sanna ta dauko jakarta a kan mudubi ta dawo ta dauki wayar ta jefa a ciki ta
nufi ficewa daga dakin.
Har ta kama hannun kofar sai kuma ta tsaya ta kasa murdawa; to ina zata? Babu mota
a gidan kuma Malam Ali baya nan, shi kuma Abban da yake ba a nan ya kwana ba bata
ma san ko yana gida ko baya nan ba. Ta juyo cikin sanyin jiki ta koma kan gadon ta
zauna ta zuba fuskarta a tafukan hannunta ta sake fashewa da kuka. Bata da wata
mafita illa ta kirawo Abban Saddiku ta sanar da shi domin idan ma taje asibitin ita
kadai a halin yanzu komai zai iya faruwa.
Ta kama gefen hijabin da yake jikinta ta goge hawayenta, tayi ajiyar zuciya ta
laluba jakarta ta dauko wayarta. Ta lalubo lambar Abban Saddiku ta danna kira ta
kara a kunnenta zuciyarta na dakan uku-uku.
…………
Fitowarsu kenan daga gidan Hajiya shi da Yaya Bello, suka shiga motar Abban suka
kama hanyar gidan Yaya Bello inda a can zasu ci abincin rana. Yana zura mukullin
motar kira ya shigo wayarsa wadda ajiyeta kenan a kusa da giyar motar; ya fasa
tayar da motar ya amsa wayar ya kara a kunnensa. Ba tare da ta amsa sallamarsa tace
‘Abba Saddiku bashi da lafiya yana asibitin Malam a emergency, yanzu Yayan abokinsa
da suke tare ya kirawoni ya sanar da ni.’
‘Nima dai ban gane bayanin ba amma dai ba accident bane, nima yanzu zan sami motar
haya na wuce asibitin idan kuma kana unguwar sai na shirya mu tafi.’
Ita kuwa Zahra yana ajiye wayar ta dora hannu aka ta sake rushewa da kuka; shikenan
a gaban Yaya Bello za a yi mata wannan tonon asirin, ya sami dalilin da zai shiga
rayuwarsu ita da yaranta ya hanasu jin dadi.
Sai da tayi mai isarta sannan ta dauki wayarta ta kirawo Yaya Murja ta sanar da ita
halin da ake ciki, duk da bata gaya mata cewa kwaya Saddikun ya sha ba.
Sukayi sallama a kan idan taji abinda ake ciki ta sanar da ita.
…………
Har suka isa asibitin Malam Aminu Kano babu wanda yace wa dan uwansa wani abu; shi
Abba yana ta mamakin to Saddikun da aka ce masa dazu ya fita meye zai sameshi har a
kaishi emergency kuma ace ba accident ba yayinda shi kuma Yaya Bello yake kallon
hanya yana nashi nazarin.
A kusa da emergency din yayi parking suka fito suka shiga, sai dai suna shiga kuma
ya rasa wanda zai kama. Don haka ya janyo Yaya Bello suka dawo waje ya kirawo Zahra
ya tambayeta wanda zasu nema; bayan ta sanar da shi ya ajiye wayar ya kirawo lambar
Saddikun sanna suka nufi komawa cikin emergency din.
Yana shiga ya hango wanda yake waya da shi; yaro ne matashi wanda ba zai wuce
shekaru ashirin da biyar ba zuwa da shida. Da hanzari ya karaso wajen su
Abban,bayan sun gaisa ya mikawa Abban wayar Saddiku yana fadin
‘To ni dai abokinsu ne ya kirawoni kuma a hotel na samesu wai party sukeyi shine
suke competition aka wanda yafi shan kwaya da yawa zasu bashi kudi 250k. Su ukun da
suke kwance a nan su suke shan kwayar shine da sauran suka ga sun sume duk suka
gudu sai abokinsu daya ya kirawo ni ya gaya min don harda kanina a cikinsu. Shima
yana gaya min ya gudu, don yanzu ma likitocin tambayar da suke shine a gaya musu
sunan kwayar da suka sha don su san irin abun da ya dace suyi musu amma ni ban sani
ba; abokan nasu kuma duk sun kashe waya. Gasu can dai su uku a kwance a sume an dai
musu allura.’
‘Subhanallah!’
‘Likitan da yake duba su yana wancan office din, ku zo mu karasa sai kuji daga
bakinsa.’
Yaya Bello yaja hannun Abban Saddiku wanda ya kasa wani katabus suka bi bayan
yaron.
Bayan ya gabatar da su a wajen likitan shima likitan irin bayanan da yayi musu ya
sake basu, ya dora da
‘Matsalar itace bamu san irin kwayar da suka sha ba. Shi daya yaron da ya farfado
yace sunan kwayar flash dayar kuma rod, a lussafinsa shi kwaya uku ya sha yayinda
su kuma suka sha biyar ko shida. Muna bincike kuma muna jira su farfado mu sami
ainahin sunan kwayar domin shine zamu san irin abinda ya dace muyi musu.’
Suka yiwa likitan sallama bayan ya sanar dasu idan sun farka za a mayar da su
sashen kula da kwakwalwa.
Bayan sun fito daga ofishin suka karasa inda Saddikun yake; yana nan a kwance babu
alamar wani motsi a tare da shi idan banda numfashi da yake futarwa a hankali. Suka
kare masa kallo Yaya Bello yace
‘Allah ya kyauta.’
Ya janyo hannun Abban Sadik wanda yake binsa kamar mutum-mutumi suka fito bayan sun
yiwa yaron godiya sun sanar dashi cewa suna nan a farfajiyar asibitin idan an
bukaci wani abu.
Akwai dan waje daga gefen emergency din da kujerun siminti na zama, nan suka je
suka zauna. Suna zama Abban ya zuba fuskarsa a tafukan hannunsa yayinda shi kuma
Yaya Bellon ya zauna kusa da shi yana nashi nazarin ba tare da yace komai ba.
Sun dauki kusan minti goma haka kafin Abban Sadik ya sauke hannuwansa ya dubi Yaya
nasa cike tsananin damuwa yace
‘Allah ya sauwake.’
‘Amin ya Allah.’
‘Wallahi Yaya ban san yanda aka yi Saddiku ya zama haka ba. Kusan mutum uku ne suka
yi min magana a kan na binciki yaron nan, don malaminsu na secondary school ma kai
tsaye ya gaya min cewa yana shaye-shaye. Amma duk yanda naso na dauki mataki a kai
uwarsa ba zata bari ba domin wasu lokutan ko bari na ganshi ma bata yi. Gashi ko an
kama shi da laifi ta iya kare shi, wasu lokutan ma kamar shashantar dani take ta
mantar dani al’amarinsa. Yanzu ka ga abinda ya faru ko Yaya? Da anyi mata magana
sai tace wai ana so a hadani da shi.’
‘Sha’anin mata ne sai hakuri. Yanzu jira zamuyi ya farfado muji daga bakin
likitocin yanda za ayi a taimaka masa don ba zamu barshi haka ba.’
Cikin kunan rai ya cigaba
‘Ka ga tunda har ya kai ya shiga gasar shan kwaya kenan ya dade yana yi har ta bi
jikinsa, kuma ma kudi har naira dubu dari biyu ina suka samo su? Ni dai ban taba
bawa Saddiku naira dubu goma ba ma ba balle dubu dari biyu ko fiye. Ina ya sami
wadannan abokanma?’
Suka cigaba da tattaunawa Yaya Bello yana kwantarwa da Abban hankali yana gaya masa
za a samu ya bari in Sha Allahu.
Wajen karfe biyu suka jiyo kiran Sallah daga nesa, Yaya Bello ya dafa Abban yace
‘Ba muyi Sallah ba ai gara mu lekashi sai mu nemi masallaci muyi Sallah ko.’
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
38
A nan asibitin suka zauna, sai waya Yaya Bello yayi gida ya sanar da su Asma’u taje
ta bawa Hajiya abinci.
Tun shigowarsu abokin Sadik din ya bawa Abban mukullin motar Sadik din ya sanar da
shi hotel din da sukayi party din inda a nan motar take. Don haka suna nan zaune ya
kirawo wani yaronsa Shamsu yace ya zo ya sameshi a asibitin. Da yake lokacin da
suke wayar Shamsun yana court road ba tare da bata lokaci ba ya hawo Babur ya
karaso ya samesu. Mukullin motar Mommy din ya bashi ya sanar da shi inda motar
take, yace yaje ya dauki motar ya ajiye masa ita a wajensa zai nemeshi. Sukayi
sallama ya hau babur dinsa ya kama hanya.
Bayan an idar da sallar la’asar su Abba suka koma inda Saddiku yake kwance. Zuwa
lokacin daya yaron wanda ya rigasu farfadowa har an canza masa daki yana tare da
iyayensa. Shi kuma daya yaron kanin saurayin da su Abban suka tarar mahaifiyarsu ta
riga ta zo inda ta yiwa likitan bayanin tana so su sallameshi zuwa gobe don ita da
yaran zasu bi jirgi zuwa Lagos daga can zasu wuce Dubai hutu; tana so likitan ya
rubuta mata medical report idan sun je can likitocin zasu sake duba yaronta.
Bayan ta gama bayanin suka gaisa da Abba suka jajantawa juna, likitan yayiwa su
Abban bayanin cewa su Saddikun ma yanzu sun farka don haka ana bukatar a samo
madara su sha sannan za a canza musu daki inda za a cigaba da kula da lafiyarsu.
Zuwa karfe biyar da rabi sun dan kara farfadowa domin shi Saddiku har yana kiran
Mommy yana wasu zantuka da ba a gane me yake fada. Nan aka turashi a gadon jinya
aka mayar dashi wani dakin a sashen kula da kwakwalwa. Aka saka mishi drip kuma aka
sake yi masa allurai.
Bayan likitan ya fita Abba ya zauna a kujerar dake ajiye a dakin yayinda Yaya Bello
ya tsaya a daidai kan Saddikun yana tofa masa addu’oi.
A hankali yayi shiru ya daina surutun, Yaya Bello ya dawo ya zauna a kujerar dake
kusa da wadda Abban yake kai. Ya dubi Abban yace
‘Ko Zahran za a sanarwa saboda a sami wanda zai zo ya kwana da shi mu samu muje
gida zuwa safiya ko?’
‘Eh ba zan ma kirawota ba don bana jin zan iya saurarenta yanzu. Namiji dai ya
kamata a samu ko kuma ni din in an jima sai na dawo zuwa safiyar mu gani.’
‘Ba za ayi haka ba, gamu da samari a dangi. Ko wajen su Jamilun Inna ai za a sami
mai kwana da shi ko kwana nawa za ayi. Kuma ma yanzu ina ga Muhammadu zan kirawo ya
taho musu da kayan bukata ya zo su kwana da shi tunda ba abu ne da ake so ya baza
dangi ba ayi ta faman cewa yana shaye-shaye.’
Kafin Abban ya bashi amsa ya kirawo Karima ya sanar da ita halin da ake ciki, yace
ta bawa Muhammadu kudin mota kuma ta zubo musu abincin dare ta bashi abun shimfida
suna jiransa idan ya zo sai su tafi.
Muhammadu shine yaron Yaya Bello na farko wanda zai bawa Saddiku kamar shekaru
hudu, don a halin yanzu shi yana ajin karshe a Jami’a inda yake karantar aikin
jarida.
Nan suka zauna har zuwa lokacin da Muhammadu ya iso sannan sukayi masa sallama suka
tafi.
-----------
Tunda Abban Saddiku ya fita ya sanar da ita gasu a asibiti kuma shima bai san me ya
sami Saddikun ba don baya cikin hayyacinsa take cikin matsananciyar damuwa. Gashi
Abban ya ce kada ta sake ta zo asibitin sannan kuma ya ce ta daina damunsa da waya
idan ana bukatar wani abu a wajenta zai nemeta. Haka ta kasa sukuni kuma ta rasa me
zata cewa yaran da suke ta faman tamabayarta ko bata da lafiya; don haka kawai sai
ta biye musu a kan bata da lafiya sannan kuma Yaya Sadik ma bashi da lafiya yana
asibiti Abba ya kai shi.
Har la’asar tana rike da waya tana jiran shigowar kiran Abba ko kuma ta ji
shigowarsa gidan amma shiru. Hankalinta ya kara tashi don haka ta sake kiran Yaya
Murja ta rushe da kuka. Cikin firgici Yaya Murja tace
‘Subhanallahi! Zahra Saddikun mutuwa yayi ne kike kuka haka? Ki gaya min me ya
faru.’
‘Yaya nima ban sani ba Abbanshi yana can tare da shi kuma yaki yayi min bayani har
yanzu shiru, cewa ma yayi kada na sake yi masa waya sai ya dawo.’
‘Ikon Allah! To kiyi hakuri mana, na san tabbas da mutuwa Saddiku yayi da yanzu kin
ji labari ai lafiya ce take buya akasinta baya buya. Kiyi hakuri zuwa lokacin da
zai dawo gidan sai mu ji.’
Jimawa kadan kuma Yaya Murja itama ta kasa nutsuwa saboda yanda Zahran take kuka,
don haka nan da nan ta barwa abokiyar zamanta girkin da yake nata ta kama haryar
gidan Zahra.
A dakin ta sami Zahran suka zauna tana ta bata baki; sai dai har zuwa lokacin
Zahran bata gaya mata gaskiyar abinda ya samu Saddikun ba. Ta dai sanar da ita cewa
lafiya kalau ya fita abokinsa ya kirawota yace bashi da lafiya har sun kai shi
emergency. Don haka suka zauna suna jiran Abban ya dawo ko ya bugo waya.
Har Magriba ta kawo jiki bai dawo ba don haka Yaya Murja tayi mata sallama ta tafi
nata gidan a kan duk abinda taji ta sanar da ita, sannan kuma idan dare ya kara yi
Abban bai dawo ma ta sanar da ita sai ta gayawa Yaya Muhammad ya nemeshi.
Suna fita daga asibitin suka sami masallaci sukayi Sallar Magriba sannan suka wuce
ya sauke Yaya Bello a gidansa.
Ya ji dadi matuka da Allah ya sa ba a gidan Zahra zai kwana ba don yanda zuciyarsa
take tafasa baya jin zai iya saurara mata; domin duk halin da Saddiku ya shiga
laifinta ne.
Ba zai kirawo wannan abun da jarrabawa ba domin sakaci ne kuma ya san da laifinsa a
ciki; to amma me yasa Zahra take katangeshi daga yiwa dansa tarbiyya? Shi din me ya
rufe masa ido yaki ya jajirce? Tabbas Zahra itace ta san kulle-kullen da ta dade
tana yi a kansa kuma baya jin zai iya yafe mata idan ta lalata masa yara.
Kai tsaye gidan Aisha ya wuce; ta gama abincin dare ta jera a table gidan yana ta
kamshin turare.
Kallo daya tayi masa ta san cewa akwai damuwa a tare da shi. Bayan ya amsa sannu da
zuwanta ya dubi dining table yace
Yana fitowa daga wankan ta zuba masa abincin wanda tuwo ta dafa da miyar agushi, ya
ci ya koshi ba tare da yace mata komai ba. Bayan ya gama ya taso daga table ya dawo
gaban TV, ta kwashe kwanukan sanna ta hado shayi ta ajiye masa. Ya dauki remote ya
kunna TV a daidai lokacin da ta zauna a kusa da shi tana kallonsa.
‘Na ga kamar ka shigo da damuwa ne shine tunda ba a gaya min ba nake kokarin
karantawa, tunda ka san an ce labarin zuciya a tambayi fuska.’
Yayi murmushi.
Nan ya bata labarin abinda ake ciki, sosai ta jajanta masa sannan tace
‘Kuma ka ga maganar Yaya gaskiya ne, idan aka samu ya farfado gaba daya akwai
rehabilitation centers inda idan ka biya zasu ajiye shi tsawon wani lokaci a
dorashi a kan magunguna da therapy har a samu ya rabu da shan kwayar. Sai dai fa su
yawanci gaskiya a can ake kwana kamar boarding school.’
‘Amma fa babu uwar da zata so ace danta yana shaye-shaye, ita din ma na san idan
kayi mata bayani zata gane kuma zata so a rabashi da mugun abu. Ka dai yi mata
bayanin tunda ko babu komai yana bukatar addu’arta.’
‘Hmmm!’
Bayan ya kurbe shayin ya ajiye kofin, ya dauki kafafunsa ya dora a kan cinyar
Aishan tare da gyara zama. Ta muskuta ta fara matsa masa kafafunsa tana yi masa
tausa domin ta san idan yayi mata haka abinda yake bukata kenan.
Sai wajen karfe tara da rabi sannan ya tashi yayi sallar isha’i wadda bai samu yayi
a masallaci ba saboda gajiya. Bayan ya idar ya dauki mukullansa yayi mata sallama a
kan zai je gidan Zahra ya dawo.
Tana kwance a dakinta ta jiyo shigowarsa gidan, nan da nan ta taso ta fito falon
sama don ta tareshi.
Yaran duka sun yi bacci sai Rukayya da Yusra wadanda suke zaune a falon kasa suna
jiran suji halin da Yayansu yake ciki kafin su kwanta. Bayan ya amsa sannu da
zuwansu ya nufi saman.
Yace
Yusra tace
Baya son ya amsa wanna tambayar don yana ganin bai dace ya ce musu dan uwansa
shaye-shaye yayi ba. Ya kada kai yace
‘Zuwa yayi gidansu abokinsa suka sha lemo wanda yayi expiring ba tare da sun sani
ba shine suka sami food poisoning shi da abokansa biyu.’
Yana cikin bayanin suka shiga falon saman don haka Mommy taji lokacin da yake
maganar food poisoning, sai da tayi ajiyar zuciya saboda yanda ta dan sami nutsuwa;
to da me yasa bai yi mata bayani ba ya barta cikin damuwa?
Suka yi masa sai da safe itama Mommy din suka yi mata sai da safe suka shige
dakinsu na na saman domin kwanciya bacci.
Suna shigewa ta mike ta bi bayan Abban wanda ya nufi dakinsa tana yi masa sannu da
zuwa. Bata sani ba ko ya amsa ko bai amsa ba, ta dai san bata ji yayi magana ba sai
dai da yake bata ganin fuskarsa bata san yanayin da yake ciki ba.
A tare suka shiga dakin, ya wuce ya ajiye mukullan hannunsa a kan mudubi sannan ya
janyo ‘yar kujerar da take gaban mudubi ya zauna yayinda ita kuma ta zauna a gefen
gado suna fuskantar juna. Tace
‘Ya jikin Saddikun? Naji kanacewa yara food poisoning ne, wanne irin abinci suka
ci?’
Kallonta kawai yake a fusace wanda ita kuma take mamakin dalilin da yasa yake
kallonta kamar itace tayi poisoning Saddikun. Ta dan bata rai ta kawar da kai ,
yace
‘Ai nima nan zuwa nayi na tambayeki abinda Saddiku yaci ya sami poisoning din?’
Mamakinta ya karu yayinda ta kara shan kunu saboda yanda ta kula yana so ne kawai
ya raina mata hankali. Tace
‘Ce maka nayi ya fita, kuma ai a lokacin ya fita din ko ka ganshi ne a gidan bayan
nan?’
Ya jijjiga kai saboda yanda take bashi mamaki, ya rasa yaushe Zahra ta kware a
karya haka. Yace
‘Ban gashi ba, amma bari na sake tambayar watakila zaki fi ganewa. Jiya a ina
Saddiku ya kwana?’
Gabanta ya fadi yayinda tayi sauri ta waske; sai a lokacin ta gane inda ya dosa. To
ana maganar yau ya za ayi ya dinga tamabayarta jiya. Tana jin motsin kwayar idonsa
a kan fuskarta domin ya ki ya daina kallonta wanda hakan ya saka ta kasa sukuni.
Bata da wata mafita domin ta tsani yanda yake warware duk wata karya da ta yi masa
ba tare da bata lokaci ba. Ta saci kallon fuskarsa suka hada ido, ta sake shan kunu
sannan tace
‘Yace min zasu yi party na end of session, kuma na ga tun a secondary suke irin
wannan party din shi yasa ban zata da wani abu ba. Shine yayi dare ni kuma bacci ya
kwashe ni ban sanar da kai ba.’
‘Shine kika nuna min ya dawo kuma a gidan ya kwana? Ba ma wannan ba; kin zama kece
uwarsa kece ubansa shi yasa kika bashi kudi kuma kika bashi izinin ya tafi party
kika bashi mota yaje yayi abinda ya ga dama ba tare da ke da shi kun nemi izini na
ba tunda dama kin nuna masa ni din bana son shi?’
Bata da bakin magana don haka ta sunkuyar da kai tayi shiru, so take kawai ya gama
wannan hayaniyar tasa ya gaya mata abinda ya samu Saddikun da kuma halin da yake
ciki.
Ya fuskanci ba zata yi magana ba. Yayi murmushin takaici yace
‘To ina yi miki murna Zahra, saura kadan ki hallaka Saddiku domin jiya da kika
boyemin kika bashi kudi da mota ya tafi party zuwa sukayi suka sha miyagun kwayoyi
wadanda jikinsu ba zai iya daukan wannan yawan ba. Wannan shine ya janyo su ukun
suka sume aka samu aka kaisu asibiti. Tun jiya basu farfado ba har zuwa lokacin da
na barosu a asibitin, sai dai mu cigaba da addu’ar Allah ya tasheshi lafiya tunda
likitocin sun tabbatar ya dade yana shaye-shayen kwayoyi.’
A firgice take kallonsa da baki bude, kafin ta sami kalaman da zata gaya masa ya
mike ya dauki mukullin da ya ajiye ya nufi kofar. Sai da ya kama hannun kofar ya
juya ya dubeta yace
‘Kuma ban baki izinin zuwa asibitin ba, idan kuma kin ki ji to zaki sha mamaki.’
Tana nufin ya gaya mata domin ta samu tayi waya taji halin da yake ciki tunda ta
kula shi din ba zai yi mata bayani ba.
Cikin halin ko in kula yace
Wannan wacce irin musiba ce ? Yanzu dama da gaske ne ake gaya mata Saddiku yana
shaye-shaye amma yaron nan yana musa mata? Yanzu ya zata yi? Gashi Abban ta kula
wulakanci kawai yake yi mata domin yaki yayi mata cikakken bayani. Gashi bata ji ya
shigo da mota ba, to ina motar tata da Saddikun ya fita da ita?
Ta fada a fili lokacin da tambayoyin suka fara yi mata yawa a ka. Anya kuwa wannan
abubuwan da suke faruwa babu sa hannu a ciki? A ce Saddiku yana shaye-shaye sannan
kuma gashi Abbansa ya juya mata baya yanata faman yi mata wulakanci?
Ta share hawayenta yayinda ta mike ta fice daga dakin, wayarta zata dauko ta kirawo
Yaya Murja ta sanar da ita. A falo ta zauna a kan kujera ta dauki wayar tata, har
ta budo lambar Yaya Murja sai kuma ta tuna cewa bata shirya sanar da Yaya Murja
cewa Saddiku shaye-shaye yakeyi ba. Musamman da yake taba yiwa Yaya Murja korafin
yanda mutane suke faman gaya mata cewa Saddiku yana shaye-shaye. Tun a lokacin Yaya
Murja tace mata ta bincika sosai kuma ta sanar da Abbansa, har ma ta ce ta tura
mata shi domin idan ta gan shi ko zata iya fuskantar wani abu a tattare dashi. Ko
maganar bata yi masa ba balle ta bincikeshi don a lokacin gani take kawai kiyayya
ce da hassada tasa ake mata haka. Sai daga baya ta samu ta tsara Yaya Murja.
To yanzu idan ta kirawota me zata ce mata? Nan ta ajiye wayar ta kifa kanta a kan
kujerar ta sake fashewa da sabon kuka.
Haka ta kwana cikin matsananciyar damuwa; tunaninta daya hannu aka saka mata a
al’amuranta take ta shiga matsala kuma ko wanene sai ta rama.
Mutum biyu take zargi; Aisha wadda dama duk itace silar rikita mata gidan aurenta
wanda a baya yake cike da kwanciyar hankali da kauna, sai kuma Yaya Bello wanda
sosai take zarginsa a kan al’amarin Saddiku tunda ta kula yana bakin cikin yanda
yaransa basu da gata kamar yanda Abban yake kulawa da yaranta, tunda shi baya iya
bawa nasa yaran gata kamar yanda Abban yake bawa nasa.
Tabbas sai ta rama; tunda daman yanzu account dinta ya fara nauyi. Sarkar Rukayya
ta gwal kawai zata bayar aje a sayar shikenan da zarar Amina ta sami dama sai suje
wajen malamin da ta samo musu tunda itama a halin yanzun tana da tata matsalar.
…………
Ko da gari ya waye ranar aiki ce don haka Abba ya shirya daga gidan Aisha suka fice
gaba daya ba tare da ya je gidan Zahra ba. Ya riga ya san babu abinda suke bukata
kuma ya yi waya da Malam Ali ya riga ya kai masa yara makaranta.
Babu yanda Aisha bata yi ba ya barta ta rakashi asibitin itama ya hanata, sai dai
ta hada breakfast inda ta soya dankalin bature da sauce din kaza sannan ta zuba
musu ruwan zafi a flask ta bashi ya kai musu. Yana fitowa ya sayi kayan shayi ya
wuce asibitin.
Da sallama ya tura kofar dakin ya shiga.
Muhammadu yana zaune a kan tabarmar da ya shimfida yana kokarin hada musu shayi da
ragowar ruwan da ya zo da shi jiya. Ya ajiye kofunan da suke hannunsa ya tari Abban
ya karbi kayan hannunsa ya ajiye. Bayan Abban ya amsa gaisuwar sa yace
‘Likitan ya zo ne Muhammadu?’
Yace
‘Bai zo ba, nurse din ce ta shigo tace yaci abinci zata dawo ta bashi magani.’
‘To ga abinci nan ka zuba muku ku ci, bari naje na sami nurse din.’
Yana fita ya sami waje ya zauna, basu dama yayi suci abinci sannan ya samu yayi
magana da Saddikun kafin likitan ya shigo.
Sai da ya basu kusan awa guda sannan ya dawo dakin, lokacin sun gama cin abincin
har nurse din ta bawa Sadik maganinsa. Sun gama cin abincin, Saddiku yana zaune a
kan gadon yayinda Muhammadu yake zaune a kan tabarmar yana karatu. Bayan Abban ya
amsa sannu da zuwansu yace
Yace
‘A’a, sai gobe ne zamu yi test shi yasa nake karatu. Yau ba zan shiga makaranta
ba.’
‘Abba bari na zauna a nan waje na cigaba da karatun, idan ana nemena Ina nan.’
Ya ji dadin hakan don dama so yake yayi magana da Saddikun, wanda tun bayan da ya
cewa Abban Ina kwana ya sunkuyar da kai bai sake dagowa ba.
Sukayi shiru na dan lokaci babu mai magana, shi Abban yana kallon Saddikun yayinda
shi kuma ya sunkuyar da kai ya kasa hada ido da Abban nasa. Jimawa kadan Abban yayi
gyaran murya yace
Ya dago kai idonsa cike da kwalla, suna hada ido da Abban yace
‘Likitane ya duba ka Saddiku, nurse din da ta shigo ta baka magani bata wuce
sa’arka ba sai dai ko ta baka shekaru biyu zuwa uku, kalli yayanka Muhammadu yana
karatu don ya zama dan jarida, ni da na haifeka public administration na karanta
shi yasa kaga na kai matsayin da na kai. Amma kai Saddiku ka zabi zama dan kwaya,
ka tara kayan maye ka sha ka fita daga hayyacinka shi kenan abinda kake so
Saddiku.’
‘Ka daina bani hakuri Saddiku, baka yi min laifi ba. Kanka ka yiwa laifi kuma
kayiwa Allah laifi. Ya baka rayuwa kuma ya baka dama ka zama abun alfahari ga
al’umma amma ka zabi shaye-shaye.’
‘Mommy.’
‘Ka san yanzu jikinka ya saba ba zaka iya rayuwa babu kwayoyin da kake sha ba
saboda ka zama addicted ko?'
Bai iya amsawa ba kai kawai ya daga don ya san hakan ne.
‘Ina son ka Saddiku, ina son kayi rayuwa a hayyacinka kaima wataran ka zama wani ka
tara naka family din cikin nutsuwa. Akwai makarantar da zasu taimaka maka ka daina
shan kwaya amma fa makarantar kwana ce, idan likita ya sallameka daga nan can zamu
wuce. Idan Allah ya sa ka rabu da addiction din a wata shida sai ka fito ka cigaba
da karatunka.’
Jimawa kadan Abban yayi masa sallama ya fito ya tura masa Muhammadu sanna ya wuce
office zuciyarsa cike da damuwa.
Yana tausayin Saddikun sanna kuma yana ganin laifinsa ne da yayi sakaci a kan
Saddikun, yana fatan Allah ya bashi ikon ceto Saddikun.
Kafin ya isa office din yayiwa Aisha waya ya sanar da ita ta dafawa Sadik abincin
rana idan ta dawo daga aiki idan ta gama ta yiwa Malam Ali waya ya zo ya karba ya
kai.
…………
Tun safe take jiran shigowar Abban don ta gama shirin zuwa asibiti wajen Saddiku
amma har wajen karfe tara bai shigo ba. Wajen karfe tara da rabi ta sa Yusra taje
ta dubo gidan Aisha ta kirawo Abban, sai dai bata dade da fita ba ta dawo ta sanar
da ita babu kowa a gidan.
Zuciyarta ta kara tafasa saboda ta gaji da abinda Abban yake mata, ita da danta a
hanata zuwa ta dubo shi.
Ta dauki wayarta ta shiga daki sannan ta danna masa kira, sai dai har ta gaji da
kira bai amsa wayar ba. Ji take kamar ta rusa ihu saboda takaici, ta rasa ma wanda
zata gayawa taji dadi. Ta zauna a gefen gadonta ta lalubo lambar Yaya Murja wadda
tun jiya take kiran Zahran ita kuma ta ki dauka saboda tana kunyar abinda zata fada
mata.
‘Zahra ina kika shiga ne ? Tun dare nake faman kiranki. Yusra dai ta ce min kina
nan amma me yasa ba kya daukan waya. Kin gan ni a tsaye gidan naki zan taho ko kina
asibitin?’
‘Ina gida. Abbansu ya hanani zuwa asibitin kuma ya ki ya gaya min me ake ciki.’
Wajen sha daya saura Yaya Murja ta shiga gidan, a daki ta sami Zahran ta ci kuka ta
koshi. Nan ta bata labarin irin wulakancin da Abban yakeyi mata tun lokacin da aka
kwantar da Saddikun a asibiti, gashi ya ma ki ya barta koda ta ji muryar Saddikun.
Sai dai duk cikin bayanan da take yi bata gaya mata ainahin abinda ya sa Abban ya
ke mata hakan ba.
A iya sanin Murja ta san akwai fahimtar juna tsakanin Zahra da Abban Sadik; duk da
a baya bayan nan Zahran tana kokarin ta fahimtar da yayar tata cewa tunda Abban
Sadik din ya auri Aisha ya canza mata.
Gaba daya dai ta kasa gane bayanin da Zahran take yi mata a halin yanzu; amma ko ma
menene ya za ayi ace mace ta haifi danta kuma ace mata bashi da lafiya amma an
hanata ta ganshi kuma an ki ayi mata bayanin halin da yake ciki.
Sai da ta samu Zahran ta tsagaita da kukan sannan ta zaro wayarta daga jaka ta
lalubi lambar Abban Sadik din ta kirawoshi.
Cikin girmamawa da mutuntawa suka gaisa ta tambayeshi jikin Saddiku sannan ta sanar
da shi tana gidansa, ta nemi yayi mata kwatancen inda Saddikun yake a asibitin tana
son zuwa ta duba shi. Bai yi mata wani musu ba domin ya san dama za ayi hakan; sai
dai ko da ta nemin izini zasu taho da Zahran ya sanar da ita kada su taho da ita
idan ya zo zai kaita da kanshi.
Don haka nan take ta tashi kai tsaye ta fito daga gidan ta hau motar haya ta nufi
asibitin Malam. Kafin ta isa asibitin Abban ya isa don haka a farfajiyar wajen ta
sameshi bayan yayi mata kwatancen wajen.
A zaune yake a kan irin kujerar nan ta dutse don haka itama Yaya Murja sai ta
zauna, bayan sun sake gaisawa sukayi shiru tana jiran yace su tashi ya kaita dakin
da Saddikun yake. Madadin hakan sai yace
‘To duka bayanan nata wallahi ba ganewa nayi ba saboda tana cikin damuwa, kamar dai
tace jiya da safe ya fita shine aka kirawo ta akace kamar sun ci wani abu suna
asibiti. To tace kai kadai ka zo ka ganshi kuma baka bata wani bayani ba, shi yasa
ma take cikin damuwa.’
Ya jijjaga kai.
‘Saboda bata son bacin ran shi tana kallo tun yana SS 2 yake shaye-shaye gashi
yanzu har ya zama addicted, jiyan da ba dan Allah ya sa da kwanansu a gaba ba da
sai dai mu dauki gawarsu. Yau da na fita daga nan kuma makarantarsu naje ashe ma
shi ba karatun yake yi ba, tunda jarrabawar da yace mata sun gama ta bashi kudin
party harda mota ya tafi an ce guda biyu kawai ya rubuta a cikin paper goma sha
daya; kin ga babu maganar karatu ko.’
‘Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun! Ita kuwa Zahra garin yaya tayi haka?’
Nan ta gaya masa yanda suka yi da Zahran a kan maganar zargin da takeyi, sannan ta
sake bashi hakuri.
Nan ya tashi yayi mata jagora har dakin Saddikun, ta dai samu natsuwa yanda taga
Saddikun tunda a hayyacinsa yake har hira ma suka yi kuma ya gaya mata babu inda
yake masa ciwo don likitan ma yace da safe zasu sallameshi.
Bayan sun fito ne Abban yake gaya mata ya riga ya sami rehabilitation center da zai
kai Saddikun, wanda a yanda ya tsara daga nan asibitin kai tsaye center din zasu
wuce.
Tace hakan yayi domin itama tana so taga Saddikun ya zama mutum, sai dai ta roki
Abban a kan ya taimaka ya bari Zahra ta ga Saddikun kafin a tafi da shi
rehabilitation center din tunda ya ce da ita wata shida zai yi a can kuma shi kadai
zai dinga zuwa yana ganinsa. Yayi mata alkawarin gobe da safe zai kawo Zahran ta
ganshi inda daga nan zai daukeshi su wuce.
Kai tsaye daga asibiti gidan Zahra ta koma saboda yanda take cike da takaicin abun
da Zahran tayi. Bayan ta sanar da ita Saddikun yana nan kamar ma lafiyarsa kalau
sai kuma ta hau ta da fada.
‘Shima kansa Abban haushin ki yake ji saboda yanda kika tsaya kika bari Saddiku ya
lalace kuma kika dinga hanashi yayi masa fada, shi ya sa kika ga yayi banza dake.
Don haka idan ya dawo ki lallaba ki bashi hakuri tunda gaskiya dai da laifinki don
shi da kansa yace ke kika bashi kudin party din. Ki samu ki bashi hakuri don
gaskiya yayi fushi sosai, kuma idan an kai Saddikun rehabilitation center ki kawar
da idonki a samu ya sami lafiya tunda dai kin tabbatar ubansa ba zai cutar da shi
ba.’
‘Wallahi Yaya wannan wulakancin da yake yawan yi min tunzura shi matarsa take
tunda da ai ba haka yake ba.’
‘Ba zamu iya gane hakan ba sai lokacin da yayi fushi da ke ba tare da wani dalili
ba don yanzu kam kin yi abun fushi. Kawai ki gyara kuma ki bashi hakuri.'
Ta riga ta san daman haka Yaya zata ce don haka tayi shiru.
Duk yanda yake jin haushin Zahra ya san dole yau ya ganta tunda kwananta ne. Sai da
ya gama duk abinda zai yi ya ci abincin dare a gidan Aisha sannan wajen tara da
rabi ya shiga gidan Zahra.
Duk yanda ya so ya kyaleta bata bashi dama ba saboda yanda ta sameshi a daki ta
saka shi a gaba da kuka tana bashi hakuri. Ta bashi tausayi sannan kuma baya son
ganinta a damuwa don haka da wuri ya nuna mata ya hakura. Ya dan ci abincin daren
da ta dafa duk da a koshe yake. Haka suka kwana babu yabo babu fallasa.
Gari yana wayewa bayan sun gama cin abinci yara sun tafi makaranta ya daukesu ita
da Yusra suka wuce asibitin.
Sai a lokacin Zahra ta sami natlsuwa da taga Saddikun, suka dan taba hira har ta
tambayeshi ina motarta. Sai a lokacin ya tuna da motar inda yace mata bai sani ba
sai dai ko ta tambayi Abba don wayarsa ma Abban aka bawa kuma har yanzu Abban bai
bashi wayar ba. A halin da ake ciki ba zata iya maganar motar ba don lallabawa
takeyi ta kankarowa kanta mutunci don haka tayi shiru.
Basu dade ba Yaya Bello ya iso ya samesu, suka gaisa da Zahran sannan ya jajanta
mata jikin Saddikun. Shi da Abba suka shiga ofishin likitan, sai da suka fi minti
talatin suna tattaunawa sannan suka fito; domin likitan ne ya hadasu da masu
rehabilitation center din. Suna fitowa aka rubutawa Saddiku sallama.
Yusra ta taya Muhammadu suka kwaso kwanukan abinci wadanda duk na Aisha ne suka
zuba a motar Malam Ali da yake jiransu, Abba ya bawa Muhammadu kudin mota yace ya
wuce gida. Har ya kama hanya Yusra tace masa
Yace
‘Na Antinki ne idan kun je gida Malam Ali zai kai mata.’
Sai da Zahra tayi da gaske sannan ta danne damuwarta kada Abban ya ga sauyi a
fuskarta; wato mutan gidan Bello da Aisha sun fita mahimmanci a rayuwar yaranta shi
yasa ya danka musu Saddikun ya hanata ganinsa bayan babu wanda ya haifar mata
yaron. Lallai!
Daga gefe guda likitan ne tsaye da Yaya Bello da Abban suna magana, bayan Saddikun
ya zuba kayan hannunsa a motar Malam Ali ya karasa ya cewa Abban ya fito.
Abban ya dubeshi yace
‘Kaje ka yiwa Mommynka Sallama daga nan zamu wuce da kai makaranta ni da Yaya zamu
kai ka.’
Ya amsa ya wuce wajen su Mommy din.
Tayi zaton da ita za aje taga makarantar amma Abban yace ba haka za ayi ba su wuce
ita da Yusra Malam Ali ya mayar da su gida, shi da Yaya Bello zasu kai Saddikun.
Shi kanshi Abban sai da ya kula da yanda ta fusata, ta shige motar ta rufe domin
Yaya Bello ma da ya taho yayi musu sallama sai hakura yayi ya tsaya wajen Abban
yayinda Malam Ali yaja motar.
Abba yaja motar shi da Yaya Bellon suka nufi kan titin gwarzo road inda daga nan
ne zasu kara neman kwatancen makarantar.
Har suka isa gida Zahra ba tayi magana ba saboda yanda zuciyarta take tafasa; wato
yanzu kenan Bello shine zai dinga tsarawa yaranta rayuwa saboda sun mayar da ita
‘yar iska shi da dan uwansa. Za a kai mata yaro makaranta amma bata ma isa a kaita
ta ga wajen ba kenan idan wani abu ya sami Abban Bello ne kawai ya san inda Saddiku
yake.
Gaskiya ba zata jure ba, wulakancin ya isa. Bata san me ta tsarewa Aisha da Bello
ba suka janye mata hankalin miji, amman dole ta dauki mataki.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
39
Sai da aka bawa su Abban Sadik takardu suka cike sannan aka nuna musu dakin
Saddiku, bayan nan kuma aka yi musu bayani cewa ba zasu ziyarceshi ba sai bayan
sati biyu. Babu waya a hannunsa don haka aka basu lambar wayar da za a iya kira ayi
magana da shi. Mutum biyu kawai ake so wadanda sune zasu dinga ziyartar sa don haka
Abba ya sa sunanshi da na Yaya Bello a kan su kadai ne za a dinga bari suna
ganinsa. Sukayi masa sallama suka taho zuciyar Abban cike da damuwa yana fatan
Allah ya sa kafin ya dawo Saddikun ya fara samun natsuwa.
Haka suka fito suka bar Saddikun shima yana matse hawaye yayinda kwakwalwarsa take
kokarin gamsar da shi cewa iyayen nasa basu daina son sa ba.
__
Tunda aka kai Saddiku makarantar nan Zahra ta kasa nutsuwa. A da idan tana cikin
damuwa Abban ne yake kwantar mata da hankali, yanzu kuma da take cikin tsananin
bukatar hakan yayi burus da ita. Bai taba hanata kwananta ba amma dai babu wata
hira da take shiga tsakaninsu; ita tana jin haushinsa kuma tana fushi yayinda shi
yake ganin shine ya kamata yayi fushi ba ita ba. A halin yanzu ma kwata-kwata baya
jin Zahra a ransa kamar yanda yake jinta a da.
Kusan kwana goma kenan da kai Saddikun amma duk ta rame tana neman fita hayyacinta
saboda damuwa da rashin bacci, gashi kullum ta dan sami baccin sai ta yi mafarkin
Saddikun a wani yanayi mara dadi.
Ranar asabar ce don haka yara sun tafi tahfiz, don haka ta koma dakinta ta kwanta
tunda maigidan ba awajenta yake ba. Tana kwanciya bacci ya kwasheta.
Yana zaune a wani waje mai kyau da haske, shimfidun wajen farare ne tas haka ma
kujerun. Yana zaune a kan kujera cikin shigar fararen kaya, sai dai abinda ya
firgita ta shine yanda duk kyan wajen da kuma kyan shigar Saddikun kuka kawai yake
faman yi yana matse hawaye. Magana take yi masa iya karfinta amma ko jinta bayayi,
kuka yake mai ban tausayi harda shessheka.
Irin wadannan mafarkan da takeyi su suke daga mata hankali; ta san dai kuka ba
alkhairi bane to me yasa take ganin Saddiku yana kuka?
A hankali ta sauko daga kan gadon, har zata tashi sai kuma ta koma ta zauna. Ta
mika hannu ta dauko wayarta a kan durowar gefen gado ta lalubo lambar Abban Saddiku
ta buga masa; bayan ya dauka ta sanar da shi tana so taje gidan Yaya Murja. Ba tare
da bata lokaci ba ya bata dama tunda Malam Ali yana nan.
Hijab kawai ta saka saboda bata ma da kuzarin canza kaya, ba tare da bata lokaci ba
Malam Ali ya dauketa suka fice.
Ba karamin dadi taji ba lokacin da ta shiga gidan Yaya Murja ta tarar babu kowa a
falon kasa; wanda falon amaryar Yaya Murja din ne. Kai tsaye ta haye sama, inda ta
tarar da Yaya Murja zaune da yaranta suna hirarrakinsu. Cike da farin ciki yaran
suka yi mata oyoyo, ta karasa ta zauna a kusa da yayarta. Gaba daya yaran suka
matso suna gaisheta yayinda Yaya Murja ta umarci Hibba; yarinyarta ta uku wadda
Yusra ta girmeta da shekara daya; ta debo ruwa ta kawowa antinta.
Bayan yaran sun gama gaisheta sannan ta fara gaisawa da Yaya Murja, a nan ta
fahimci kanwar tata tana cikin damuwa don haka ta jata suka shige daki.
Suna zama a gefen gadon ta kifa kanta a kan cinyar Yaya Murja ta fashe da kuka.
Bata hanata ba sai da tayi mai isarta tayi shiru don kanta, ta janyo tissue a kan
durowar gefen gadon ta goge hawayen sannan Yaya Murja wadda take kallonta da mamaki
tace
Ta karasa face majinar da ta taru a hancinta ta ajiye tissue din a kasa sannan tace
'Yaya na rasa yanda zan yi da Abban Sadik, wallahi ji nake kamar an canza min shi.’
'Hmn! Yaya kin san har yanzu bai gaya min inda ya kai Saddiku ba? Gaba daya ma ko
kula ni baya yi a cikin gidan harkar gabansa yake yi. Idan a kan abinda ya faru da
Saddikun ne ai na bashi hakuri amma sai ya dinga faman share ni kuma ba zai gaya
min inda ya kai min yaro ba, kashe ni yake so yayi tunda idan na mutu bashi da
asara ya auri wata matar?’
Yaya Murja tayi murmushi ta kamo hannun Zahra ta rike a nata hannun tana kallon
fuskarta a nutse, sai da suka dauki kusan minti daya a haka sannan tace
'Abinda nake so dake shine, kwata-kwata ki cire tunanin kishiyarki a ranki idan
kikayi haka shine zaki iya fuskantar rayuwarki kiyi gyara a inda kike bukatar
hakan. Kin ji ko?’
'Abban Sadik mijinki ne kuma a halin yanzu laifi kika yi masa, ki sake kwantar da
kai ki bashi hakuri. Ki sake janyo shi a jiki kamar yanda kuke da. Kuma ina son ki
kwantar da hankalinki, Saddiku dansa ba zai taba cutar da shi ba don haka ki barshi
ya nemawa yaronsa lafiya. Kada ki sake yi masa maganar Saddiku. Ki nuna masa duk
yanda yayi da yaransa dai-dai ne, ke dai so kawai kike ku koma kamar yanda kuke a
da. Ki kuma nuna masa duk wani laifi da kika yi masa da wanda kika sani da wanda
baki sani ba ba zaki sake ba; domin kin san wani lokacin maza saboda mulki ba zasu
gaya mana laifin ba sai dai muga sauyi a halayyarsu. Kuma kullum dare ki dinga
tashi musamman ranakun da ba kwananki ba kina yin sallar dare kina addu'a, wallahi
a hankali zaki ga komai ya dawo dai-dai.’
Ta gyada kai; ta sami natsuwa da wadannan kalaman duk da dai babu yanda za ayi ta
cire kishiya daga lissafinta tunda ta san duk abubuwan da suke faruwa da ita sa
hannu ne na kishiya. Amma dai tayi alkawarin zata gwada shawarwarin Yaya Murja.
'Shi Kuma Saddiku ki cigaba da yi masa addu'a amma don Allah ki bari a gina
rayuwarsa. Kinga yaranki kamar mu suke, dukkansu mata sai shi kadai namiji. Idan ya
bi hanyar lalacewa zasu taso basu da wani uba bayan ranmu. Kina kallo mu iyayenmu
duka sun rasu yanzu Yaya Muhammad muke takama da shi; to da ya zama dan shaye-shaye
ai da kinga bamu da sauran gata a duniya.’
'Hakane.'
'Yauwa.'
Saida suka dauki lokaci Yaya Murja tana kwantar mata da hankali sannan da magriba
ta fara kawo jiki tayi mata sallama ta kama hanya.
Duk yanda lokaci ya kure sai da ta tsaya a gidan Amina domin tana so ta samu
tabbacin maganarsu tana nan ta zuwa wajen malamai.
Bayan a sun gaisa da Aminan ta rakata daki ta duba Ummansu wadda take kwance sannan
suka dawo falon Aminan suka zauna.
A nan suka cigaba da kulla yanda da zarar Umma ta dan ji sauki zasu kai ziyara
wajen malamansu don samarwa kansu mafita a aurarrakinsu wanda a halin yanzu suke
cikin wani hali.
Sai bayan sun yi sallar Magriba sannan Zahra ta fito suka kama hanyar gida da Malam
Ali.
—----
A ‘yan kwanakin nan jikin Hajiya kara rikicewa kawai yakeyi, duka da cewa Yaya
Bello a tsaye yake a kanta. Kusan shekaru biyar kenan tana fama da hawan jini wanda
daga baya ya hade mata da diabetes. Shi yasa ma kullum Yaya Bello yake zuwa yana
bata abincin da kansa don ya tabbatar ta ci abinda ya dace. Sai dai duk da haka
‘yan kwanakin nan da an samu jininta ya sauka sai kuma diabetes din ya tashi, idan
kuma ya yi sauki sai jinin ya sake hawa. Haka dai suke lallabawa.
Ranar Juma'a ce don haka da wuri Abban Sadik ya tashi daga aiki. Ya je ya gaida
Hajiya da safe amma duk da haka yaji yana so ya sake komawa, don haka ba tare da
bata lokaci ba ya juya kan motarsa ya nufi gidan Hajiyan.
A masallacin suka hadu da Yaya Bello wanda shi kuma ya zo ne don ya duba Hajiyan ya
bata abincin dare.
Tuwon alkama da miyar zogale Yaya Bello ya kawo mata; wanda shine abincin da ta fi
so tun da aka hanata cin shinkafa. Anisa ce ta dauko musu plate ta kai musu daki
don yau Hajiyan gaba daya ta ki fitowa falo. Haka suka saka ta a gaba ta dan ci
tuwon kadan tace ta koshi, sai shayin goruba da aka hada mata ta shanye kofi guda.
Ta koma kan gadon ta kashingida ta barsu zaune suna ‘yan hirarrakinsu a tsakaninsu.
Sai da akayi sallar isha'i sannan suka yi mata sallama suka tafi suka barta da
Anisa da mai aikinta kamar yanda suka saba.
………
Tun ranar da Zahra taje gidan Yaya Murja ta dawo ta aikata duk abinda yayan ta bata
shawara; tunda ta fuskanci a halin yanzu bata da wata mafita da ta wuce hakan. Don
haka babu laifi Abban Sadik din yana dan sauraronta duk da dai har yanzu bai ce
mata komai a kan Saddiku ba.
Kwananta ne yau don haka yana dawowa daga gidan Hajiya ya tsaya a gidan Aisha yayi
mata sallama sannan ya wuce gidan Zahra.
Kamar yanda suka saba karfe goma sun gama komai ya rufe gida, shi da ita ma sun yi
shirin bacci.
Tana kwance idonta a rufe domin bacci ya fara daukanta yayinda shi kuma yake zaune
a gefenta da computer dinsa a kan cinyarsa yana aiki. Karar wayarsa ce ta farkar da
ita, ta gyara kwanciya yayinda ya kai hannu kan durowar gefen gadon ya dauki wayar.
Lokaci ya fara dubawa ya ga karfe sha biyun dare har da minti goma; sai da gabansa
ya fadi domin ya san ba lafiya ba tunda yaga Yaya Bello ya kirawoshi a wannan
lokacin.
Yana kara wayar a kunnensa kafin yayi wata magana Yaya Bello wanda kana jin
muryarsa zaka san kuka yake yace
Katse wayar kawai yayi ya ajiye computer dinsa ya mike a dai dai lokacin da itama
Zahran ta tashi zaune tana tambayar abinda ya faru. Ya dubeta yana fitar da kwalla
yace
Sukayi shiru na dan lokaci yayinda ya cigaba da kokarin saka kayansa. Ya dauki
mukullin motarsa ya nufi kofa, ta mike tana fadin
'Amin.'
'Ku bari sai mun yi waya tukunna, zan turo Ali ya kai ku.’
……..
Kafin gari ya waye labarin rasuwar Hajiya ya zagaya gari. Karfe tara na safe aka
gama hadata aka kaita makwanci. Sai da aka dawo daga makabarta sannan Abba ya sanar
da iyalansa su taho, don haka gaba dayansu suka taho. Itama Aisha saida ta biya ta
dauko Amira sannan suka wuce saboda ko ba komai ta samu wadda zata debe mata kewa a
gidan.
Kafin yamma gida ya cika da dangi da abokan arziki, domin Hajiya Balaraba mace ce
mai mutane sosai. Allah bai bata haihuwa da yawa ba domin yara hudu kawai ta haifa,
kuma da yake ita kadai ce matar mahaifinsu sai suka zama basu da ’yan uwa. Duk da
haka tana da dangi da yawa, domin mahaifinta yayi aure-aure kuma ya tara yara su
goma sha takwas. Lokacin da tana da jajayen sawunta yanuwanta da suke mafi yawansu
mazauna Sumaila ne suna zumunci da ita sosai, sai dai daga baya bayan rasuwar
mahaifinsu Yusuf din da dukiyar ta kare a hankali kowa ya janye jikinsa. Yanzu kuma
da aka sami labarin rasuwarta kowa ya zo ana ta kuka ana tuna alkhairinta lokacin
da tana da hali.
Duk yaranta suma sun hallara da ‘yayansu, Ummulkhairi ce kawai bata iso ba wadda a
Lagos take zaune inda aure ya kaita. An riga an sanar da mijinta rasuwar wanda yayi
alkawarin shi da ita zasu biyu jirgi kafin magriba zasu iso.
……..
Tun Hajiya tana da lafiyarta ta bar wasiyyaa cewa idan ta rasu kada ayi mata zaman
makoki, amma saboda ‘yan uwanta wadanda suka taho daga Sumaila da kuma Ummulkhairi
da yaranta su biyar wadanda sai sunyi sati biyu sannan zasu koma Lagos haka aka
hakura aka yi zaman na kwana uku. Duk wanda ya tambayi Saddiku haka Yaya Bello yake
cewa yana makaranta suna jarrabawa shi yasa ba a gaya masa rasuwa ba.
Ranar da aka kwana uku da safe Yaya Bello da kansa ya shiga har cikin gidan ya
sanar da mata cewa bayan azahar zai sa a kawo mota za a mayar da su Sumaila. Duk
yanda Yaya Saratu ta so ya bari a kai bakwai bai ma saurareta ba. Itama Ummulkhairi
da taji wannan sanarwar take ta sanar da shi tana so ita da yaranta su wuce gidan
Yusuf su karasa kwanakin nasu a can. Don haka ta karfin tsiya Yaya Bello ya sallami
kowa aka share makoki.
Azahar nayi shima Yaya Bello ya tattara iyalansa a gaba suka koma gida tare da
Najma ‘yar wajen Ummulkhairi. Iyalan Abba suka shiga mota Malam Ali ya ja suka
tafi, shi kuma Abban ya dauko Ummulkhairi da yaranta wadanda zasu karasa hutunsu a
gidansa. Yaya Saratu kawai suka bari a kan ita sai da yamma zata tafi sai a bar mai
aikin Hajiya da kuma Innani kanwar Hajiya tare da Anisa wadanda sai daga baya zasu
tafi.
……….
Lokacin da su Zahra suka bar gidan makokin Ummulkhairi ta sanar da ita suna nan
zuwa ita da yara, don haka suna shiga gidan ta sa aka fara gyara musu dakin baki na
falon kasa. Sai dai suna shiga unguwar Abba ya ajiyesu a gidan Aisha yace su sauka
a nan tunda kusa ne sa dinga shiga wajen Zahra da yaran.
Yana shiga gidan Zahra tana zaune a falon kasa yayinda Jummai take goge dakin.
Bayan ya amsa sannu da zuwanta ta ce
'Eh tare muka taho suna gidan Aisha na san nan din ma da anjima zaki gansu.’
Bai saurari abinda zata ce ba ya haye saman; ba zai iya sauraron komai ba saboda
yanda ya gaji kuma ga damuwa.
Ta kawar dakai tana mamaki; yanzu kenan ba zai ma bari ta sauki bakinsa ba! Ta
tashi itama ta haye saman.
Haka aka gama jimamin rabuwa da Hajiya kowa ya koma harkokinsa, mutanen Lagos ma
suka gama hutunsu suka koma gida.
—-----
Dole ta saka Zahra tana yin amfani da shawarwarin Yaya Murja tunda ko babu komai ta
san sai ta kwantar da kai a wajen Abba sannan zata sami kudin zuwa wajen Malami.
Tunda dama da business dinta take samun kudi kuma a halin yanzu babu zancen wani
business domin duk ta cinye kudin.
Yanda take ganin walwalar Abban ta san cewa Saddiku yana lafiya tunda ya gaya mata
yana zuwa duboshi kuma yana yi masa waya. Shima Abban ya sami natsuwa ne saboda
yanda yake ganin cigaba a wajen Saddiku; rehabilitation center din sun bashi rahota
a yanzu da Saddiku ya kai wata biyu a hannunsu an samu an raba shi da miyagun
kwayoyin; yanzu aikin gyaran dabi'unsa ake yi da kuma karatun islamiyya da ake biya
musu. Wannan ya sa Abban ya kara sakewa da Zahran duk da bai sanar da ita inda
Saddikun yake ba.
……
Mahaifiyar Amina ta fara samun lafiya sannan kuma a halin yanzu akwai kanwar Aminan
wadda take karatu a Sudan ta zo hutu, don haka tana gidan Aminan kuma tana kula da
Umman nasu. Don haka suke cigaba da shirye-shiryen zuwa wajen boka; domin Amina ta
samo musu sabon boka.
Yau ranar asabar ce kuma da yake ana cikin hutun makaranta kullum yara suna gida,
don haka ta gaji da hayaniyarsu tana so ta dan fita. Gidan Amina take son zuwa don
ta san a nan ne zata samu a saurareta kuma a bata irin shawarwarin da take so. Ba a
gidanta Abban Sadik ya kwana ba don haka sai wajen karfe goma na safe ya shigo
gidan. Bayan ya gama abinda zai yi da zai fita ta tambayeshi izinin fita wanda ba
tare da wani bata lokaci ba ya bata dama.
Nan da nan ta shirya, ta sallami yaran sannan ta barwa Jummai abincin rana da
abincin dare don batayi niyyar dawowa da wuri ba. Ta fito Malam Ali ya ajiyeta, ta
sallameshi domin Aminan zata mayar da ita gida idan sun gama.
Sai da ta fara gaisawa da Umman su Aminan ta yi mata ya jiki sannan suka zauna a
falo suna gaisawa da Aminan. Basu jima a falon ba suka koma dakin Aminan. Nan suka
baje a kan kafet din da yake tsakar daki, Raihana kanwar Aminan ta zo ta kawowa
Zahra ruwa da lemon roba suka gaisa sannan ta fice ta ja musu kofa.
'Aminoni ina cikin damuwa wallahi ba zaki gane ba, yanda kika ganni nan daurewa
kawai nakeyi amma komai ya tsaya min.’
'Baki kai ni damuwa ba Uwar Saddiku! Idan banda Daddy ya raina ni ya za ayi ace ina
zaune nan a Kano yana Abuja yana bin matan banza; harda wadda aka ce shi ya ajiyeta
kamar matarsa yake mata komai. Kuma duk abun nan ya hana ni zuwa Abujan kuma sai
yayi wata biyu bai zo ba, da ya zo kuma dama kwana biyu ne zai ce yana da aiki don
haka nan da nan zai koma. Ni zai yiwa tozarci!’
'To ai haka zamu je don kin ga ni ma na kusa hada 300k, ina ga ko bata isa an gama
aikin ba zata isa a fara. In ya so idan ana bukatar ciko sai na bada dakunnen
Rukayya a sayar.’
'Nima kusan na hada kudin, kin san akwai aikin da za a yiwa Ummanmu a asibitin
koyarwa na A B U. To Raihana ce zata zauna da ita, so nake sai sun tafi asibitin
kafin a sallameta sai muje mu gama duk abinda zamu yi. Saura sati shida, kada ki
damu kawata kafin azumin bana komai ya dawo dai-dai.’
'Ina ga ma mu dan kara don ni so nake sai ya dawo min da Saddiku tukunna, ina jin
shi kuma saura sati biyu ya dawo. In ya dawo na ganshi sai na fi samu nutsuwa, kai
da danka saboda zalunci a hanaka ganinsa!’
Sai da akayi sallar la'asar sannan Zahra ta shirya Aminan ta mayar da ita gida.
__
Kwanci tashi Saddiku yayi wata shida a rehabilitation center, kuma yau Alhamis yau
ce ranar da za a daukoshi a dawo da shi gida. Cikin walwala Abba ya shirya tunda ya
riga ya dauki hutu ba zai je office ba a ranar, bai gayawa kowa cewa yau zai dawo
da Saddiku ba ya fice ya nufi gidan Yaya Bello.
Sai da suka kama hanya sannan Yaya Bello ya sanar da shi cewa idan sun dauko
Saddikun shi ya saukeshi a kasuwa, suka kama hanya cikin walwala.
Suna isa suka sami Saddikun a shirye da kayansa tsaf a reception yana jiransu, suna
shiga aka yi musu iso wajen shugaban center din wanda shine zai basu takardar
sallama.
Bayan sun gama gaisawa ya mikawa Abba takardu ya sa hannu ya tura masa; yayi gyaran
murya yace
'To Alhamdulillah, Sadik Yusuf ya fita daga harkar shaye-shaye da izinin Allah. Sai
dai akwai bukatar a tabbatar bai koma harka da abokansa na baya ba domin ‘yan
shaye-shaye suna da zumunci. Zasu iya sake janshi cikin harkar ba tare da bata
lokaci ba. Ba wai hanashi harka da abokai za ayi ba, no, kawai a canza masa
environment ko makaranta yanda da kanshi zai sake zabar abokai. Alhamdulillah ma
yaron yana da saukin kai domin ya koyi abubuwa da yawa kuma ya haddace wajen izu
sha biyar a nan din.’
Sukayi sallama suka dauko Sadiku suka kamo hanyar gida; sai da suka sauke Yaya
Bello a kasuwa sannan suka wuce gidan.
Babu kowa a farfajiyar gidan, duka suna cikin falon kasa suna kallon TV saboda
ranar children day ce don haka babu makaranta. Ita kuma Mommy tana falon sama.
Da sallama Saddiku ya shiga falon yana dauke da karamar jakarsa wadda kayansa suke
ciki, gaba daya daskarewa suka yi na dan lokaci suka kasa magana. Rukayya ce ta
fara mikewa ta sa ihu
'Yaya Sadik!’
Kafin ayi wani abu ta mike ta daka tsalle ta fada jikinsa ta rungumeshi tana
dariya. Gaba daya su suka taso suka fada jikinsa da gudu banda Yusra wadda ta fito
daga dakinsu ta tsaya tana kallonsu tana dariya.
A nan Abban ya shigo dauke da sauran kayan Saddikun yana dariya yace
Suka karasa ciki gaba daya bayan Abba ya amsa sannu da zuwan da suke masa. Yusra
wadda ta zauna a hannun kujera tace
'Yaya Sadik bamu san fa zaka dawo ba don ko dakinka ba a gyara ba, gashi yau Jummai
bata nan.’
'Ke Rukayya sai kije ki share masa dakin in ya so idan Jummai tazo gobe sai ta kara
gyarawa.’
Rukayya ta dan bata fuska saboda haka suka saba duk lokacin da ake bukatar wanda
zai yi wani aiki to nan da nan Yusra zata ce Rukayyan tayi don ita kusan bata
moruwa.
‘Bari ka gani Yaya Sadik in ba haka ba Ya Yusra bata ki ka kwana a kan kurar ba.’
Da sauri ta shiga kicin ta kwaso tsintsiyoyi ta fito ta nufi kofar waje da niyyar
ta gyara masa dakinsa na boys quarters. Abba ya mike yana fadin
'Rukayya dakinsa na cikin gida zaki gyara masa nan zai dawo, boys quarters din ma a
rufe yake.’
Tun da taji ana ihun dawowar Saddiku ta leko ta kafar bene ta hangosu ta koma ta
zauna a falon saman tana jiran shigowarsu. Bata hango Saddiku sosai ba amma dai ta
ganshi a tsaye don haka ta tabbatar Saddiku ta ya dawo lafiya, yanzu jiran
shigowarsa kawai takeyi.
Abba ne ya fara shigowa falon; cike da walwala ta mike ta tareshi. Shi kansa ya
dade bai sami irin wannan tarbar daga daga gareta ba, bayan ya amsa sannu da
zuwanta ya dubeta yace
'Ga danki nan na dawo miki dashi babu abinda ya gutsurar miki shi ko?’
Ya shige daki yana dariya yayinda ita kuma ta nufi kicin, kafin ta karasa kofar
kicin din saman Saddiku ya shigo da sallama don haka ta juyo tana kallonsa tana
amsa sallamar cike da farin ciki. Matsowa take tana kare masa kallo yayinda shi
kuma yake ta murmushi; ya canza gaba daya. Ya kara girma da kwarjini gashi yayi
haske da kiba, harda wani dan gemu wanda da ta tabbatar babu shi. Murmushi kawai
take tana kallonsa yayinda ta karasa ta zauna a kujera, ya kula ta rasa abinda zata
ce masa don haka yace
'Mommy na dawo.’
Suka dan taba hira sannan Saddikun ya tashi ya sauko inda ya shiga dakinsa ya taya
Rukayya suka gyara.
……..
Dawowar Saddiku ta yiwa Zahra dadi sosai, domin ita kanta ta kula da canjin da aka
samu a tare da Saddikun wanda haka yake kara burgeta; ta tabbatar yanzu Saddikunta
ya zama mutum sannan kuma yanzu Saddikun ya zama na hannun daman Abban. Domin kusan
kullum idan dai Abban yana gida to suna tare, koda kuwa yana gidan Aisha, kuma suna
yawan fita tare duk da basa gaya mata inda suke zuwa. Abu daya ne bai yi mata dadi
ba yanda Abban ya sanar da ita Saddiku zai sake JAMB kuma BUK zai koma a daidai
lokacin da zai zama Yusra kanwarsa tana shirin shiga level 2 ko ma gama level 2
din. Duk da yanda ta kula shi Saddiku wannan bai dameshi ba. Ita a tsarinta ta fi
so a mayar da shi Maryam Abacha American University ko kuma a kalla a samar masa
wata jami'ar ta kudi amma ba BUK ba; ta san wannan shawarar Bello ce kuma a halin
yanzu ba zata iya ja da maganar ba don bata so ta bata wannan walwalar da suke ciki
ita da Abban. Don haka zata bari tunda tana sa rai nan da sati biyu zasu je wajen
malaminsu ita da Amina ta san da an musu aiki zata samu ta canza komai. A yanzu ma
maganar da akeyi ta riga tayi magana da Yaron Malam yayi mata aiki na kwarjini irin
wanda yayi mata wancan karon don tana so Abban ya dan fara sauraronta kafin wancan
aikin ya fara.
Kwanan Saddiku biyu da dawowa Yaron Malam ya bayar da aikinta aka kawo mata. Ta
Whatsapp ya turo mata da sakon yanda zata yi amfani da abun wanda ba tare da bata
lokaci ba ta aikata kuma ta bawa Abban ya cinye.
………
Tunda lokacin da Saddiku yana asibiti ta tambayi abba motarta yace ta tambayi
Saddiku bata sake tayar da maganar ba. Sai yanzu da taga Saddikun ya dawo sannan ta
sameshi ta tambayeshi inda ya bar mota. Ya sanar da ita da motar yaje hotel din da
sukayi party din amma daga nan bai san yanda akayi da motar ba. Ta so ya tambayi
Abban amma ya sanar da ita shi ba zai iya tambaya ba sai dai ita ta tambaya. Tana
son motar musamman yanzu da take ganin Saddikun yayi hankalin da zai bar mata
motarta, don haka ta shirya zata tambayi Abban inda motar take ko kuma a kalla ya
bata wata. Tabbatarwa da tayi cewa tayi amfani da kwarjinin da Yaron malam ya bata
sannan kuma ga kayan mata da ta siya a wajen Hajja shi ya kara mata kwarin gwiwar
tambayarsa.
………
Daga sallar asuba ya dawo, ya riga ya saba baya son komawa bacci bayan sallar
asuba. Don haka kawai sai ya zauna a falo ya kunna TV tunda bashi da wani aiki da
zai yi. Nan ta fito falon har yanzu tana sanye da rigar baccinta wadda ta dora
babbar rigar a kai. Bayan ta gaisheshi ta shige kicin ta hado masa shayi, bayan ta
ajiye masa shayin ta zauna a kusa dashi suka cigaba da kallon tashar BBC din da ya
kunna.
'Na'am.'
'Ni kuwa wai ina motata? Ka san tun Saddiku yana asibiti baka gaya min inda motar
take ba.’
Ya kurbi shayinsa, ya rike kofin a hannunsa ya dubeta ya kau da kai sannan yace
'Daga baya an sameta a hannun wasu yara, sai dai an sakata a kasuwa an sayar tun
tuni.’
'To yanzu ya za ayi da ni? Ai ko wata sai a dan bani ko na sami ta fita unguwa.’
Ya sake kurban shayin sannan ya ajiye kofin a kan teburin da yake gabansa, ya
kalleta suka hada ido na dan lokaci yayi murmushi sannan ya dauke kai yace
'Zahra! Kin san daman ba wai ina sha'awar baki mota bane, kin dade da sanin cewa
wannan ba ra'ayina bane. Sau biyu ina baki mota ba da son raina ba, kuma duka
lokutan biyun saida nayi nadamar baki. Waccan motar ma da Saddiku yayi accident ina
cikin gidan nan kika san yanda kikayi da ita ba tare da kin yi shawara da ni ba.
Ita kuma ta biyun kinga yanda aka kare. So ni dai ba zan sake saya miki mota ba.’
Ta sunkuyar da kai yayinda shi kuma ya mayar da hankalinsa kan TV din da take
gabansa.
'Hakane. Sai dai ina ga ai yanzu na koyi hankali, kuma in sha Allah abinda ya faru
a baya ba zai sake faruwa ba.’
Suka sake yin shiru na dan lokaci, shi yana shan shayinsa ita kuma tana tunanin ta
inda zata fara; domin ba zata hakura da mota ba musamman da yake Aisha tana jan
mota. Abu daya ne take jin zai sa ta hakura da mota shine idan ya hana Aisha ma
hawa mota. Ta dan yi gyaran murya tace
'Hm! Ina ganin tunda ita Aisha tana da tata motar ai nima zai fi zama dai-dai ka
bani wata motar tunda yanzu nace duk abinda ya faru na kiyaye; in ya so sai a
sallami Malam Ali. Yaran ma ni sai na dinga kaisu makaranta ina daukosu kamar yanda
itama Aisha take kai kanta duk inda zata.’
Ya kurbe dan ragowar shayinsa ya ajiye kofin, ya fuskanceta gaba daya yace
'Zahra. Kece kika yiwa Aisha dalilin da ta sa kudinta ta sayi mota saboda kin hana
direban da na ajiye muku yayi mata hidima, yanzu kuma bata yi min wani laifi da
motarta ba balle nace ta daina hawa mota. Ke da kanki ki janyo dalilin da ya rabaki
da mota; tare da cewa sau biyu ina saya miki mota ba tare da na sayawa Aisha ko
taya ba. Ba zan sake saya miki mota ba, duk inda zaki je direba ya kaiki ko kuma ni
na kai ki. Alfarma daya zan iya yi miki shine idan kin sami kudi kema zaki iya
sayawa kanki mota sai dai ko kin saya idan motar ta fara barazana ga tarbiyya da
lafiyar yarana to za a fitar min da ita daga gida. Mun gama maganar mota ni dake.'
Ta bi kofar da kallo tana murmushin yake; wato duk wannan ban hakurin da tayi ba za
a yafe mata ba kenan? Saboda tsabar wulakanci wai ita yake gayawa ta tara kudi ta
sayi mota saboda yana takama ya auro ma'aikaciya mai kudi.
'Hmmm!’
Tayi gajeriyar dariya ta mike domin ta san yanda ya saya mata waccan motar ba tare
da yayi niyya ba yanzun ma hakan za a sake yi, domin sun gama magana da Amina saura
kwana goma sha biyu Ummansu ta tafi Zariya wanda washegarin ranar da ta tafi su
kuma zasu je wajen malamansu.
Tana shiga daki ta tuna ya kamata ta turawa Amina kudin da ta hada a account dinta
tunda zuwa yanzu ta tabbatar ba zata sake samun wasu kudi kafin nan da lokacin ba.
Don haka ta dauki wayarta ta tura naira dubu dari biyu da saba'in zuwa account din
Amina. Tana ganin sun shiga ta kirawo lambar Aminan, bayan sun gaisa tace
'Kawata na turo miki 270k gara ki rike a wajenki don wallahi bana jin zan sami
cikawa su kai 300k kafin upper week din nan. Wadannan din ma da kyar suka hadu da
fizga-fizga sai dai ko bayan an yi aikin lokacin an bude min bakin aljihu.’
'To babu komai, nima nan da kyar na hada 200k amma na san zuwa next week zai turo
min kudin cefane na next month don haka da su zan yi amfani ya sake bayarwa idan
aiki yayi.’
Suka yi dariyar mugunta sannan sukayi sallama suka ajiye waya kowacce cike da
yakinin burinta ya kusan cika.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
40
Tunda sukayi maganar mota Abba ya zata zai ga Zahran ta canza masa, amma sai ya ga
ta cigaba da lallabarsa don haka shima bai nuna mata wani canji ba.
Yau din ranar talata ce kuma ba a gidanta Abban yake ba. Haka ta tashi sallar asuba
jikinta babu dadi, ba zata iya cewa ga inda yake mata ciwo ba amma dai ta san bata
jin dadi. Kafin ta idar da sallar asuba ta fara jiyo hayaniyar yara suna shirin
makaranta. Ta gama azkar dinta ta mike, ta cire hijabin ta ajiya sannan ta fito
daga dakin.
‘Ina Rukayya?’
'To. Ku gama shiryasu su tafi makarantar zan dan kwanta don bana jin dadi.’
'Yauwa, to ga gidan nan idan Jummai ta zo sai kiyi mata bayani. Idan rana tayi a
dafa shinkafa da miya.’
'To Mommy.'
Can wajen karfe tara da rabi Abban ya shigo da shirinsa na tafiya office, bayan
Yusra ta gama yi masa bayanin Mommy bata jin dadi ya wuce saman don ya dubota.
'Ni kaina bana ce ba wallahi, ba dai na jin dadi ne amma dai kaina yana dan ciwo
don haka na sha Panadol na kwanta.’
'Ok. To idan dai kin ji babu hali kiyi min waya sai na zo muje asibiti, kada ki
zauna da ciwo haka.’
'Ok. Tare da Saddiku zamu fita, zan ajiyeshi gidan Yaya Bello akwai wajen da zai
kaishi don ya fara koyon gyaran computer kafin admission dinsa ya fito.’
……….
Har karfe daya ta wuce Mommy bata sauko ba. Lokacin Jummai ta gama abinci ta gyara
gidan, itama Yusra tayi sallah har yara sun kusa dawowa daga makaranta. Ta dai san
yanzu haka bacci ne ya kwashe Mommy din amma dai ta dade, don haka ta hau saman da
nufin ta tashi Mommy din ko don ma tayi sallar azahar.
Sanyin da ta ji a jikinta ya bata tsoro don haka ta mike a firgice ta rarumi wayar
Mommy din ta shiga neman lambar Abba. Bata taba ganin mutuwa ba amma tabbas wannan
yayi mata kama da mutuwa, bata son wannan tunanin da kwakwalwarta take biya mata
nan take jikinta ya fara rawa. Da kyar ta lalubo lambar Abban nata ta buga, ta ci
sa a kuwa wayar tana shiga ya dauka. Kafin ya gama yi mata sallama a gigice tace
'Abba Mommy ce ka zo bata da lafiya.’
Kafin yace wani abu ta jefa wayar kan gadon ta fice daga dakin da sauri jikinta
yana rawa. A guje ta sauka daga been tana yi tana tsallake wasu, ba tare da ta
tantance inda zata tafi ba ta nufi fita daga falon kasa.
Har ta fita sai kuma ta tuna Jummai tana kicin don haka ta dawo da gudu ta shiga
kicin din tana haki tana fadin
'Kin gani fa Jummai, Kinga Mommy kamar fa bata motsi kinga yanda na fita dazu har
yanzu bata motsa ba ko suma tayi?’
Jummai ta tsuguna a gaban gadon ta dubi fuskar Mommy din; tabbas mutuwa Zahra tayi.
So take ta fasa ihu amma bata so tayi hakan gidan daga ita sai Yusra, don haka ta
mike tana fadin
'Bari naje gidan commissioner da gudu na kirawo Mama, Allah ya sa bata tafi asibiti
ba. Idan tazo na san zata san abun yi ko kuma su tafi asibiti tunda Abban baya
nan.’
Nan ta fito ta bar Yusran tana tsaye ta rasa abinda zata yi kuma ta kasa sake taba
Mommy. Jummai bata dade da fita ba itama Yusran ta fito daga dakin ta zauna a falon
sama tana share hawaye tana fatan Allah ya sa Mommy suma tayi.
Jummai tana fita ta tsallaka da gudu ta shiga gidan commissioner, tayi sa'a Mama
bata fita ba tana tsaye a tsakar gida tana bayarda kayanta da za a wanke mata.
Cikin gaggawa ba tare da ko sun gaisa ba Jummai tace
'Subhanallahi!’
Ta juya ta shiga falonta, ba tare da bata lokaci ba ta fito sanye da hijabi tace
Jummai da Mama suna shiga farfajiyar gidan Abban shima ya tura gate din ya shiga,
yana shiga suka juyo yayinda Abban yace
Suka shige gidan gaba daya kai tsaye suka haye saman Abban yana biye da su. Suna
shiga Jummai ta ja hannun Mama suka wuce yayinda Abban ya tsaya a kan Yusra yana
tambayarta
'Yusra me ya sami Mommy din? Kukan me kikeyi?’
Bata bashi amsa ba sai hawayenta da yake karuwa. Zuwa yanzu shima hankalinsa ya Kai
koluwar tashi duk da bai fahimci abinda yake faruwa ba to amma me zai sami Zahran?
Muryar Jummai ce ta katse shi yayinda cikin daga murya take fadin
Cikin hanzari ya rabu da Yusran ya nufi dakin, yayinda itama Yusran ta dafa masa
baya kamar zata ture shi. Kusan tare suka shiga dakin suka tsaya a gefen gadon inda
Mama take kokarin gyarawa Zahran kwanciya. Jummai ya fara kalla wadda take durkushe
a gaban gadon da hannuwanta a kanta hawaye yana gudu a kan fuskarta da bakinta a
bude. A firgice yace
Ta jijjiga kai
'Ai sai dai muyi hakuri, Mommy Allah yayi mata rasuwa few hours ago don gashi har
ta fara sandarewa.’
Zubewar Yusra suka ji wadda tana jin ance Mommy ta rasu ta sume.
Take gaba dayansu sukayi kanta, Mama ta dan tabata sannan ta tallafo kanta ta dubi
Abban tace
Sai da yayi da gaske ya iya daukar Yusran saboda yanda jikinsa yake karkarwa, gashi
idanuwansa basa gani sosai saboda yanda hawaye suke fita babu kakkautawa. Kansa
yana juyawa kafafuwansa suna neman su kasa daukansa haka ya karasa falo da kyar ya
kwantar da Yusra a kan kafet din tsakar falon. Yana ajiyeta ya juyo ya nufi komawa
dakin yayi da Mama ta tsuguna a gefenta tana kwalawa Jummai kira
Cikin sanyin jiki ta fito daga dakin tana share hawaye; fitowar tata tayi dai-dai
da shigowar sauran yaran gidan daga makaranta, Rukayya ce kawai bata tashi ba
saboda ta tsaya lesson. Turus suka tsaya ganin Yusra a kwance ga Mama a kanta. Ummi
ce ta fara magana tana fadin
Sumayya tace
Cikin sanyin jiki suna karewa kowa kallo suka wuce suka zauna a kan kujerar zaman
mutum uku suka jeru kamar masu jiran wani abu.
A hankali Mama ta dinga shafawa Yusra ruwan har aka samu ta farfado, tana bude ido
tayi yunkurin tashi Mama ta dafe ta tana fadin
'Yi hakuri Yusra kin ji, kada ki jiwa kanki ciwo kiyi hakuri kiyi tayi mata addu'a
kawai.’
'Mutuwa tayi Mama! Wayyo Mommy Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un!’
Daidai nan Abba ya fito daga dakin yana share hawaye. Da gudu Ummi ta tashi ta fada
jikinsa tana fadin
Sauran yaran da suke biye da ita suka tashi da gudu suka shige dakin yayinda Jummai
ta bisu da gudu. Itama Ummin sai ta saki Abban ta bi bayansu. Kukansa ya kara
tsananta yayinda yake ta maimaita
Ya nufi dakinsa ya shige ya turo kofar. Yana shiga ya kirawo Yaya Bello ya sanar da
shi sannan ya kirawo Malam Liman ya sanar da shi. Bashi da kuzarin da zai sake
kiran wani don haka ya jefa wayar kan gado ya sa tafukan hannunsa ya rufe fuskarsa
ya saki hawayen da yake ta faman makalewa.
Yanzu shikenan Zahra ta rasu? Wannan din wacce irin mutuwa ce haka ba tare da wani
notice ba. Ya dafe kirjinsa wanda yake kara kuntata yace
'Astagfirullah.'
Daga nan falon inda su Jummai suke zaune da yaran suka jiyo sallamar namiji daga
falon kasa. Jummai ta mike ta ajiye Sumayya tana share hawaye ta fice daga falon.
Jimawa kadan ta dawo saman, ta karewa yaran kallo; yanda suke a gigice gaba daya
bata ga alamar akwai wanda zai iya kirawo mata Abban ba don haka ta wuce ta
kwankwasa kofar dakin nasa.
Ya bude yana share ruwan alwalar da yake fuskarsa, yana budewa tace
Yana shiga ya dauki wayarsa ya kirawo Aisha ya sanar da ita halin da ake ciki, Bai
saurari tambayoyin da take yi masa ba ya ajiye wayar ya fito ya nufi falon kasa. A
nan falon Abban ya zauna shi da su Malam Liman suna jajantawa suna jiran isowar
Yaya Muhammadu da Yaya Bello.
Basu dade da zama ba Rukayya ta shigo, wadda Malam Ali ne ya koma makaranta ya
daukota da ya fahimci abinda yake faruwa. Bai gaya mata abinda ya faru ba don haka
da ta hango Abba a falo sai ta dafe kirji tayi dan gajeran murmushi, ta kasa magana
domin ta kula zaman nasu ba na lafiya bane don haka da gudu ta haye sama.
Yanda ta ga Yusra a kashingide kanta babu dankwalu da Mama zaune a kusa da ita ya
sa ta karasa falon da gudu. Ta zube a gaban Yusra ta dafa ta tana haki tace
Da karfi Rukayyan ta banbare Yusra daga jikinta ta tureta, ta fara bin fuskokin
‘yan uwanta da kallo. Ta kama hannun Mama wanda yake dafe da cinyar Yusra yayinda
ta sa hannunta na hagu ta dafe kirjinta tana fitar da hawaye tana fadin
Kafin a bata amsa numfashinta ya fara yin sama don haka Mama ta saki Yusra ta dafe
Rukayya tana umartar Jummai ta debo ruwa.
A daidai nan Saddiku ya shigo falon; wanda tare da Yaya Bello suka zo gidan. Ya
kare musu kallo na dan lokaci da jajayen idanunsa. Kai tsaye ya shige dakin Mommy.
Kallo daya yayi mata ya tabbatar ta mutu, nan ya tsuguna a gaban gadon yana kallon
gawar yana fitar da hawaye.
Daidai lokacin da aka fara samo kan Rukayya a lokacin Aisha ta shigo falon saman.
Kusa da Jummai ta karasa tana fadin
'Wallahi Anti ni yau ko haduwa bamuyi da Mommy ba, Yusra tace min bata jin dadi ta
kwanta. Muna kasa ni da Yusra muna hidimar mu Yusran ta shigo ta koma tana ihu
Mommy babu.’
Ta tashi ta karasa kusa da Rukayya wadda Mama take kokarin samo kanta, tana
tsugunawa a wajen Rukayyan ta fado jikinta ta rushe da kuka tana fadin
Rungumeta tayi itama ta fashe da kuka tana bin yaran da kallo na tausayi yayinda
rasuwar mahaifinta ta dawo mata sabuwa, don a lokacin bata fi shekarun Rukayyan ba.
Jimawa kadan ‘yan uwan Zahran suka shigo, su Yaya Murja suka zauna nan wajen yaran
yayinda su Yaya Muhammad suka shigo suka duba gawar.
Nan da nan aka sauka da ita falon kasa inda a nan ne su Yaya Murja zasu yi mata
wanka da sutura da taimakon malamai mata guda biyu da Malam Liman ya kirawo domin
wankan.
………
Kafin wani lokaci gida ya dinke da mutane. Nan da nan aka yi mata sutura maza suka
dauka aka nufi masallaci domin yin Sallah saboda can ya dan fi sarari domin babu
laifi ta sami mutane.
Nan da nan aka dafeshi, aka karasa sakata. Shima Abban da kyar ya jure tsayuwar
saboda yanda kansa yake sarawa. Aka sakata aka rufe mutane suka tattaro suka dawo
gida.
Haka aka cigaba da karbar gaisuwa. Itama Aisha hutun aiki ta dauka don a gidan
makokin take wuni sai dare take komawa gidanta.
A hankali har aka kwana uku. Ranar kwana uku bayan sallar isha'i ana zaune a falon
kasa Suwaiba kanwar Zahran ta dubi Yaya Murja tace
'Yaya ba zaki tafi da Sumayya ba kuwa? Ni nayi nayi da ita tace ba zata bini ba
kuma wallahi tunda akayi rasuwarnan fa bana jin ta ci abincin kirki.’
Ta daga kai alamar eh. Aishan ta dubi Yaya Murja tace, bari a jima kadan idan muka
je can sai taci abincin.
Wajen karfe tara Aisha ta mike ta ja hannun Sumayya da Ummi ta yiwa su Yaya Murja
sallama ta fice.
Cikin hanzari Yusra tabi bayansu. Motsin da Aishan taji ya sa ta juya, ganin Yusra
ya sa ta tsaya don ta zata wani abun zata fada ko ta bawa ‘yan uwanta.
Ta matso dab da Aishan ta sha gabanta a lokacin da Ummi da Sumayya har sun kusa isa
gate don haka suka tsaya daga nan.
Da mamaki Aishan ta bude baki zatayi magana Yusran ta daga mata hannu ta cigaba
'Ki bar ganin Mommy ta rasu ki zata zaki maye gurbinta, baki isa ba kuma ba zaki
taba isa ba. Nan ba gidanki bane kada ma ki taba tunanin zan barki ki shiga dakin
uwata wallahi kin yi kadan, kuma idan wani abu ya sami su Ummi wallahi sai kin
gwammace zama da Mommy da zama da ni. Eye service kawai.’
Kafin Aishan tace wani abu Yusran ta wuce ta koma ciki ta barta da baki a bude tana
mamaki. Sai da Ummi ta gaji ta dawo ta taba Aishan sannan ta tuna ya kamata su tafi
ne.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
41
Ranar da Zahra ta kwana hudu da rasuwa bayan azahar Abba ya sallami mutane, ya
sanar da su Yaya Muhammad an tashi daga makoki. A cikin gida ma an sanar da mata
don haka nan take aka fara watsewa, itama Amina wadda da ita aka yi zaman kwanaki
ukun tayi musu sallama ta tafi. Zuwa la'asar ya zama gidan babu kowa sai Yaya
Jummai da Rahma wadanda suka ce sai washegari zasu tafi inda zasu bar yaran da
Goggo Binta wadda goggon su Zahran ce; idan an yi kwana bakwai ita kuma zata tafi.
—----
Ranar kwana biyar gidan ya dan sami natsuwa domin mutane sun yi saukin zama, sai
dai da an zo babu dadewa ayi musu gaisuwa a tafi. Yaran gaba dayansu suna cikin
tsananin damuwa, musamman masu wayon daga kan Saddiku zuwa Nana. Ummi da Sumayya
dai suna dan sakewa sai dai tun ranar da aka kwana hudu Yusra ta hansu bin Aisha
idan ta shigo don haka suka rage samun wanda zai saka su a gaba su ci abinci.
Abba yana kokarin kulawa da su don bai koma aiki ba, sai dai shima a cikin damuwar
yake wuni. Ya kasa gane abinda yafi yi masa zafi a ransa; mutuwar Zahra ko kuma
halin maraicin da yaransa suka shiga. Yana iya kokarinsa wajen basu hakuri sannan
kuma ga Goggo Binta ma tana kokari amma duk da haka da damuwa yake ganinsu.
Bayan an idar da sallar isha'i sai da ya siyowa Ummi yoghurt sannan ya shiga gidan.
Rukayya ya samu a falo tana kwance kamar mai bacci, sai dai yana shiga falon ta
tashi zaune. Bayan ta amsa sallamarsa tayi masa sannu da zuwa. Ya mika mata ledar
yoghurt din yace ta kaiwa Goggo nata sannan ta raba sauran ita da ‘yanuwanta.
Tana karba ya wuce sama, kai tsaye dakinsa ya shige ya turo kofa ya zauna a gefen
gado yana tunani. Bai dade da zama ba ya dauki mukullinsa ya fito ya rufe dakin;
sai da ya leka dakin Sadik ya sanar da shi kada ya rufe gidan don yanzu zai dawo
sannan ya fita.
Gidan Aisha ya nufa; tun ranar da akayi rasuwar rabon da ya shiga gidan nata; sai
dai kawai yana ganinta a gidan Zahra. Yau ne kawai zai ce bai ganta a gidan ba.
Da sallama ya shiga falon, tana zauna a kan kujerar zaman mutum uku da waya a
hannunta yayinda TV take kunne. Bayan tayi masa sannu da zuwa ya zauna, ta wuce
kicin ta dauko masa ruwan sanyi. Ta zuba masa ruwan a kofi sannan ta zauna a
gefensa.
'Ya yaran?’
‘Kaina ne yake ta ciwo tun asuba, shi yasa tun safe da na shiga na ga basa bukatar
komai na dawo na dan kwanta.’
Tayi ‘yar dariya ta matsa jikinsa ta zauna, ta kwantar da kanta a kan kafadarsa.
Suka sake yin shiru na dan lokaci, basu jima ba Abban ya kirawo sunanta. Ta daga
fuskarta daga kafadarsa ta kalleshi tana murmushi, da ya tabbatar ya sami
hankalinta sai ya cigaba
'Jibi in Allah ya kai mu za ayi kwana bakwai, kuma a ranar zan koma aiki. Zan sa a
gyara miki daki a can gidan zuwa next week sai ki koma. Kin ga daman saura wata uku
kudin hayar gidan nan ya kare sai na basu gidansu.’
Duk da ta san zai yi wannan maganar amma sai da maganar ta shammaceta. Ta dan
jijjiga kai domin ta kore damuwar da ta lullubeta, ta lalubo muryarta ta hanyar yin
gyaran murya sannan ta muskuta kadan da fuskanceshi tace
'A dai dan kara lokacin ba nextweek ba don na dan kara shiryawa.’
'Babu damuwa take your time. Ai ba lallai sai kin kwashe kayanki gaba daya ba a
lokaci guda. Idan aka gyara dakin; wanda shima temporary ne kinga sai ki kwashi iya
kayan bukatarki a hankali a kwashe sauran. Kafin nan ma kin ga an gama gyara miki
daki a saman.’
'Yauwa. Ki dai shirya da wuri don kin ga Goggo Binta jibi zata tafi, ba zai yiwu a
bar yaran su kadai babu Babba a gida ba tunda nima ranar zan koma aiki.’
Suka dan taba hira wadda duk yawanci shi kadai yake zancensa, daga baya yayi mata
sallama ya koma wajen yaran.
Yana fita ta bi bayansa ta rufe gidan ta dawo ta kintsa tayi shaf'i da witri, ta
gyara zama a kan daddumar. Ta daga hannunta ta karanto ayatul kursiyyu da sauran
azkar, ta bude baki zata roki Allah amman ta rasa yanda zata jera kalmominta. Sai
da ta gaji da rike hannunta a sama ba tare da ta samo kalmomin ba don haka cikin
damuwa ta karanto ‘Rabbi inni lima anzaltu ilaiya min khairin fakeer'.
Ta sauke hannuwanta cike da damuwa da kuma saka rai cewa Allah ba zai jarrabeta da
abinda ba zata iya ba. Ya za ayi ta koma wannan gidan? Ba gidan take tsoro ba amma
ba zata iya zama da Yusra ba. A zamanta da Uwar Yusra; duk da sai su kusan shekara
basu hadu ba; amma sharrin uwarta bai barta tayi zaman aure cikin nutsuwa ba to
yanzu me zai faru idan ta fara zama da Yusra? Yarinyar da ta tare ta ido na ganin
ido ta gaya mata ba zata barta ta zauna lafiya ba. Gaskiya ba zata iya zama da
Yusra ba. Bata san da yaren da zata gayawa Abba cewa ba zata koma gidan ba domin
abu ne da aka saba, sannan kuma bata san dalilin da zata bashi na kin komawar ba.
Tabbas da ace babu Yusra da Nana to zata koma ta rike masa ragowar yaran; duk da
cewa tana sane da halin ko in kula din da shi yake da nata yaran wadanda ubansu ya
mutu tun kafin uwar yaransa ta mutu.
Ta san ba zai taba iya yi mata adalci ba tsakaninta da yaransa domin ta gani a
gidaje da dama, duk wanda ya tashi cewa zai yi tana cutar marayu. Bata so ta zama
silar raba da da uba don haka tana ganin idan aka takura ita kam sai dai ta hakura
da wannan auren; tunda ma zuwa yanzu babu wata riba da zata iya nunawa tace ta ci
da wannan auren. Haka ta kwanta cikin damuwa saboda abu daya ta sani ba zata iya
zama da Yusra a sami zaman lafiya ba.
—-----
Washegari ranar Lahadi haka ta wuni zuciyarta babu sukuni saboda waccan maganar da
take mata yawo a rai. Ta so ace ta je islamiyya da ta tambayi malamarasu ko akwai
wani hadisi ko aya da zasu sa dole ta rike masa yaran da ba ita ta haifa ba, amma
saboda rasuwar ta bari sai wani satin zata koma islamiyya.
Tuk kafin azahar Abban ya kirawota ya sanar da ita ta ajiye masa abincin rana don
haka nan da nan ta dafa taliya da miyar kifi ta jera a table, sannan ta hada zobo
ta saka a fridge.
Sai wajen karfe uku ya shigo, yana shigowa ta sa masa abincin. Sai da yaci ya koshi
don kusan tunda akayi rasuwar nan bai zauna ya ci abinci ya koshi ba sai yanzu. Da
aka kirawo sallar la'asar ya fita masallaci, bayan ya dawo yace mata zai yi bacci
ne kada a tasheshi. Yana shirin shigewa dakin tayi gyaran murya tace
‘'Nima ina son zuwa gidan Hajiya, ko naje in ya so sai na dawo kafin magriba?’
'Lafiya kalau, na ga su Yaya Zainab ne kawai suka zo gaisuwa babu ita duk da na san
gwiwarta tana ciwo amma dai munyi waya da ita. Ina so dai naje na gani.’
Ya shige dakin yayinda ita kuma ta mike ta shige nata dakin domin ta shirya.
……..
Tana shiga gidan Hajiya ta tarar da Anti Uwani da Zahida suna zaune a falo suna
hira. Bayan sun gaisa ta dubi Zahida tace
Tayi dariya
'Hajiya tana daki, inaga bata idar da azkar ba shi yasa bata fito ba. Yaran kuma
Abban Afra ne ya fita dasu wai zasu je sayen kaya za ayi kaltaran menene a
makaranta.’
A zaune ta sameta a kan dadduma da kafafunta a mike, bayan sun gaisa tayi mata ya
jiki suka dan taba hira sannan ta taso ta dawo falon. Bata dade da zama ba Anti
Uwani ta tashi ta shige dakin da Hajiya take.
Anti Uwani tana shigewa Zahida ta taso ta dawo kusa da Aisha, tana zama Aishan ta
dubeta tace
Sukayi shiru na dan lokaci, jimawa kadan Aishan cikin murya me dauke da damuwa tace
'Me yace?’
'Wai na tashi daga gidan da nake na koma gidan Zahra saboda yara.’
'To da me kike tunani? Ai ko wanene ma haka zai yi tunda kinga wancan nasa ne kuma
yanzu bashi da wata mata a ciki.’
'Hmm! Baki gane ba Zahida. Nifa ba zan iya zama da yaransa ba gaskiya, ba wai ina
nufin dukansu ba a'a. Idan aka dauke Yusra da Nana to bani da matsala da sauran
yaran. Amma ba zan iya zama da Yusra ba, ke ko gwadawa ma ba zan yi ba sai dai ayi
min duk abinda za ayi Amma ba zan zauna da Yusra ba.’
'Yusran wai zata kai shekara nawa ne da kike tsoronta har haka?’
‘Sha takwas ne idan tayi yawa sha tara. Ba wai tsoronta nake ji ba amma Zahida
yarinyar nan tabbas idan ta sami dama zata iya poisoning dina na mutu. Ko bata
kashe ni ba kuma ba zata taba bari mu zauna lafiya da ubanta ba, nutsuwar da yake
son samu ba zai samu ba. Kinga kuma duk abinda ya faru da shi da duk masu kallo
cewa za ayi ina musgunawa marayu.’
'Zahida kin san dai tunda na auri mutumin nan uwar Yusra bata barni na yi rayuwar
aure ta shekara daya ba tare da wata matsala ba ko, to wallahi wannan yarinyar ta
fi uwarta sharri. Kuma da bakinta ta tare ni ta gaya min ba zata taba bari na zauna
lafiya ba muddin na tare a gidansu. To ba wai ina jin tsoron abinda zata yi bane
ina jin tsoron kada ta kureni na ce zan rama don ramuwar tawa ba zatayi kyau ba,
gara kawai kar a fara.’
'To yanzu ya zaki yi? Tunda dai shi ga abinda yace.’
'Ban sani ba Zahida, don ban ma gaya masa ba zan koma ba. Ce masa kawai nayi sai ma
gama shiryawa, amma tabbas ba zan zauna da Yusra ba.’
'Ai kuwa akwai rigima tunda dai kin san ko sakin uwarsu yayi kece zaki rike yaran
nan balle mutuwa tayi.’
'To wa ya dora min? Ai babu inda Allah yace dole sai na rike masa yaran da bani na
haifa masa ba don kawai Ina aurensa. Don haka sai dai ayi duk wacce za ayi.’
A dai-dai nan Abdul da Farha suka shigo tare da Abban Afra suna rike da ledodi. Nan
suka zube kayan suna nunawa mamansu yayinda shi kuma Abban Afra ya sanar da Zahida
ta gayawa Hajiya zasu tafi.
Ba tare da bata lokaci ba Hajiyan ta fito tare da Anti Uwani suka yi musu sallama
suka tafi. Suna fita itama Aisha ta mike tana shirin tafiya, Hajiya tace
'Wallahi Hajiya gani nayi baki sami zuwa gaisuwa ba shine nace bari na zo na duba
kafar, ko abincin dare ma ban yi ba.’
‘Ga kafa nan dai yanda kika barta. Gara kam ki tafi tunda yanzu gida ya zama ke da
yara kar ki dinga lattin abinci.’
Tayi musu sallama ta fice, tana tunanin maganar Hajiya. Wato su sun ma zata ta tare
da yaran ne ko me, don taga kowa maganar yaran kawai yake mata kamar yanzu itace
uwarsu.
Tana shiga gidan aka fara kiran Magriba, ta leka dakin Abban ta hangoshi yana nan
yana bacci. Don haka ta karasa ta tasheshi saboda magriba. Tana yin Sallah ta fada
kicin, nan da nan ta tuka tuwon semovita miyar kuka wadda ta sha busasshen kifi da
nama. Ta hada ta ajiye a kan table sannan ta shiga wanka.
Bayan ta gama abinda takeyi ta dawo falo ta zauna tana jiransa. Karfe tara saura ta
kalli agogon, har yanzu bai shigo ba? To ko ba zai ci abincin bane? Ta sake kallon
wayarta sannan ta mayar da ita ta ajiye. Bata son ta kirawoshi domin bai saba ce
mata zai dawo ya saba ba, ta san ba lallai ya kwana a wajenta ba domin tunda akayi
rasuwar a can yake kwana kuma bata da matsala da hakan amma dai ta kasa gane
dalilin da zai sakata ta dafa abinci kuma yaki zuwa. Har ta gaji da karatun wasikar
jaki bai shigo ba don haka ta zuba abincinta ta fara ci.
Ta yi gajeran murmushi
Ta cigaba da cin abincinta yayinda shima ya zubo abincin a faranti ya dawo inda
take ya zauna suna ci suna hira. Bayan sun gama cin abincin ta hada kwanukan ta
kwashe sannan ta kawo masa shayi, ta zauna suka cigaba da hira.
'Ni kam bari naje na kwanta idan zaka fita kayi min magana wallahi bacci nake ji.’
Da mamaki tace
'Yaran fa?’
'Ai Goggo Binta tana nan, sai jibi ne zata tafi. Ina tunanin ma na lallabata ta
kara mana ko sati ne kafin nan kin gama shiryawa tunda kin ga idan tace dole jibi
zata tafi to fa ko baki shirya ba dole ki koma can din in ya so a dinga kwashe
kayan a hankali.’
Tace
Haka ta karasa shiryawa cikin sanyin jiki domin idan aka ce jibi zata koma gidan
Zahra to tabbas akwai rigima don ba zata koma ba. Gashi ta rasa da kalaman da zata
yi masa bayanin cewa ba zata koma ba don ta san ba zai fahimceta ba; a halin yanzu
ma bata jin akwai wanda zai fahimceta. A iya shekarun da tayi a rayuwa ta ga matan
aure da dama wadanda yaran miji ke hanasu zaman aure wadanda ba a taba yi musu
adalci, bata jin nata labarin zai babanta. Wani lokacin sai taji kamar ta koma ta
fara zama da su ta gani ko zaman zai yiwu, amma zuciyarta tana tuna mata idan ta
fara sai ta fi shan wahalar bari don haka gara ma kawai kada ta fara.
Tana nan kwance tana karanta wasikar jaki ya shiga dakin ya sameta. Ba tare da wani
bata lokaci ba ya shirya ya cimmata a kan gadon, lokacin har ta fara gyangyadi. Sai
dai da yake ta san bukatar da ta kawoshi kuma ita din ma tayi kewarsa haka ta biye
masa suna raba dare suna biyan bashi.
Tun kafin Abban ya sanar da Aisha zata koma gidan Zahra ya sanar da Jummai. Ya bata
umarni a fitar da duk wasu kayan da suke dakin Saddiku ya kwashe ya kai gareji a
gyara dakin don nan Aisha zata zauna kafin a gyara mata daki a sama. Nan da nan ba
tare da bata lokaci da ta shiga aiki.
Tunda Rukayya taji wannan labarin ta kasa boye murnar ta, do da kanta ta dinga taya
Jummai fitar da kayan dakin nan har aka gama. Yusra tana kallonsu tana kwafa
musamman ya da taga Rukayyan tana ta rawar jiki.
Ranar litinin wadda tayi dai-dai da kwana shida da mutuwa ranar Abba ya umarci yara
da suyi hakuri su koma makaranta. Musamman Aisha ta tashi da safe ta dafa musu
abincin makaranta sannan tayiwa Abban waya ya turo Rukayya ta daukar musu. Haka ta
zuzzuba musu kowa ya dauki nasa in banda Nana wadda tace ita indomie zata dafa.
Tun wuri Yusra ta dawo daga tata makarantar don haka ko da sauran yaran suka dawo
wajen karfe biyu da rabi a gidan suka sameta. Bayan sun ci abinci Jummai ta
taimakawa Nana, Ummi da Sumayya suka shirya suka wuce islamiyya. Basu dade da fita
ba Rukayya ta shiga dakinsu na kasa inda ta sami Yusra a kashingide a kan gadonsu
tana chatting a waya. Kai tsaye ta nufi wajen da ta ajiye jakar makarantar ta ta
bude ta fara zaro littafanta. Yusra ta dubeta tace
Yusran ta tashi zaune a kan gadon a dai-dai lokacin da Rukayyan ta mayar da jakar
ta rufe ta mike da litattafai a hannunta tana shirin ficewa daga dakin.
Yusran tace
'Kuma karatun ne ba zaki iya yi a nan ba duk fadin gidan nan dole sai kin je gidan
da aka hanaki zuwa.’
'Lallai! Wato ke tun kafin ma Mommy ta kwana bakwai da barin duniya har kin fara
karya dokokin da ta kafa miki ko, kamar daman jira kikeyi ta mutu ki koma inda ta
hanaki zuwa.’
Cak ta tsaya a inda take ta juyo ta kalli Yusran yayinda idanuwanta suka cicciko da
kwalla; kalaman yayar tata sun yi matukar yi mata ciwo a zuciya sai dai bata da
wata amsa da zata iya bata. Ta ja hijabin jikinta ta goge kwallar da ta fado
fuskarta ta juya ba tare da ta ce komai ba ta fice daga dakin. Tana fita ta tsaya a
bayan kofar ta rasa me zata yi; tafiya zata yi kamar yanda tayi niyya ko kuwa ta
hakura ta zauna a nan tayi karatun? Sai dai ta san idan ta zauna a gidan to da
zarar Sumayya ta dawo daga islamiyya karatun ya kare. Domin a wajenta take zama
kuma ko me take bukata haka Yusra zata ce taje Rukayya tayi mata.
Ta share hawayenta ta wuce tsakar gida inda ta jiyo motsin Goggo Binta da Jummai,
ta sanar da su ta tafi gidan Anti Aisha sannan ta wuce cike da damuwa.
………
Yanda Aishan ta ganta cikin damuwa ya sa ta zata damuwar rasuwar ce don haka ta
saka ta a gaba ta dinga bata baki tana yi mata nasiha har ta samu ta sami natsuwa.
Ta sakata a gaba ta fara karatun wanda kusan tare suka yi shi.
Sai da akayi kiran Magriba tayi sallah taci abinci sannan ta koma gidan. Bata kula
Yusra ba har dare yayi suka kwanta.
……….
Ranar Talata da safe kamar yanda Abba ya saba bayan ya shirya zai fita aiki ya
tsaya a falo wajen Goggo Binta domin ya gaisheta. Bayan sun gaisa ta sanar da shi
cewa gobe zata tafi, ba zata sami damar kara kwana ba. Sai dai tayi masa alkawarin
idan an kwana biyu zata dawo. Nan ya nuna mata babu damuwa goben idan ta shirya
Malam Ali zai kaita har can Sumaila shi da Saddiku, ya tabbatar mata da cewa kafin
ma ta tafi Aishan zata dawo gidan.
Yayi mata sallama ya fice aiki.
Ya san Asiha ta riga tafi aiki don haka sai bayan da ya zauna a office sannan ya
dauki waya ya kirawota, ya sanar da ita ya kamata da ta koma gida ta hada kayanta
don daga yau zuwa gobe da safe yake so ta koma gidan Zahra saboda Goggo Binta zata
tafi.
Bata iya ce masa komai ba sai dai tace masa idan ya dawo sayi maganar.
Haka ta karasa wunin ta a makaranta tana tunani rigimar da za ayi domin ita abu
daya ta sani; ba zata zauna da Yusra da Nana ba domin Nana duk abinda Yusra ta
sakata shi take yi.
__
Tun bayan rasuwar Zahra da Yaya Murja ta koma gida take tunanin makomar yaran. Ta
yi tunanin Abba zai sa Aisha ta dawo gidan domin kula da su to amma hakan bai
kwanta mata a rai ba. Bata san Aisha sosai ba sai ta hannun Zahra, a iya wannan
sanin kuma bata taba jin wani alkhairi a kan Aishan ba. Hasali ma Zahran ta nuna
musu cewa Aisha tana da sharri sannan kuma tana bin malamai sosai don ta mallake
gidan. Don haka take jin bai kamata a bar ta da yaran ba sai dai idan hakan shi
kadai ne zabinsu. Tana da labarai da yawa na irin haka yanda matar uba take mayar
da yara kalar tausayi saboda rashin uwa kuma zata yi iya yinta ta tabbatar hakan
bai faru da yaran Zahra ba; duk da ta san abu ne maii tsananin wahala.
Sun yi waya ta san gobe Goggo Binta zata tafi don haka yau ta tashi da niyyar zuwa
gidan suyi sallama. Gidan Suwaiba ta fara zuwa don su tafi tare.
A dakin Suwaiban suka zauna ita Suwaiban tana canza kaya suna hira. Cikin damuwa
Yaya Murja tacewa Suwaiban
‘Jiya da mukayi waya da Yusra tace Abbansu yace Aisha zata koma gidan amma dakin
kasa ya sa a gyara mata.’
Suwaiba tace
'To Yaya ai idan ma dakin Ya Zahran yace ta shiga ba wani abu bane, na san ma hakan
za ayi. Watakila dai yana jira ne ya sami lokaci a kwashe kayan a raba tun da ko
ana so ko ba a so kayan da suke nata ne sun zama na magada.’
'Hakane. To ni zaman nake ji; kin san fa duk labaran da muke ji a kanta ba masu
dadi bane, kamar dai daga abubuwan da Zahran take fada matar tana da fitna ga
sharri.’
'To Yaya mu ya zamuyi? 'Yaya dai nashi ne don haka yanda yake so haka zai yi da su.
Don kuwa kin san babu makawa ita zai bawa rikon yaran nan wanda hakan shine
daidai.’
'Hakane. Ni da tunanina ko ayi masa magana idan ba damuwa ya auri Rahama, kinga
dama ta saba zama da yaran shi kuma ya saba zama da mata biyu shikenan sai ta rike
yaran ‘yar uwarta.’
'Ai ba mu zamu yi masa magana ba, idan muka kaiwa Baffa shawara su sai su
shawarceshi. Ita kuma Rahma ni bana ma jinta; ya za ayi taki yarda ma? Kalli fa
shekarun da ta dauka babu aure, ai ina ga ko musu ba zata yi ba tunda ko babu komai
ta san ba zata je gidan Zahra ta sha wahala ba.’
'Mu tafi Yaya don ina son na dawo kafin ‘yan makaranta su dawo.’
Lokacin da suka je gidan yaran duka suna makaranta sai Goggo da Jummai, suna nan
zaune a falon kasa suna gaisawa Saddiku ya fito a shirye. Bayan sun gaisa suka dan
taba hira sannan yayi musu sallama ya wuce wajen da yake koyon computer.
Duk yanda Yaya Murja ta so taji yanda zamantakewa take tsakanin Aisha da yaran nan
bata sami wani abun aibi ba. Duk da Jummai bata san wani abu game da Aisha ba
saboda kwata-kwata Zahra bata bada damar hakan ba, amma dai abubuwan da ta sani
game da ita duk alkhairi ne. Don haka basu sami wani abu da zasu iya kamawa ba.
Suna Shirin tafiya Yusra ta dawo, bayan ta ajiye kayanta ta zauna a wajensu suka
cigaba da hira.
Daga bakin Yusran ne Yaya Murja ta dan ji wasu bayanai na karya wadanda suka kara
tabbatar mata da cewa Aisha zata iya cutar da yaran nan idan an barta da su. Kafin
azahar suka yi musu sallama suka tafi; Yaya Murja tana kara tabbatarwa da Suwaiba
cewa gara idan an kwana biyu suje su sami Baffa a yiwa Abban magana ya auri Rahma.
__
Sai da aka yi sallar la'asar sannan Abban ya samu ya baro office, aiyuka sunyi masa
yawa musamman da yake ya dauki tsawon sati bai je aikin ba. Yana shiga unguwar ya
wuce wajen yaran, bayan ya dubasu ya tabbatar sun tafi islamiyya ya wuce gidan
Aisha.
Sai da yaci abinci ya huta sannan ya sameta a falo tana kallo, bayan ya zauna yace
'Wai ya naga baki fara hada kayan bane, kin san fa ya kamata a ce yau kin koma
saboda Goggo ma ta san ba su kadai za a barsu na.’
Ta kalleshi suka hada ido, tayi murmushin yake. Ta hada tafukan hannunta ta ta rufe
tsakiyar fuskarta da su tana kallonsa ta gefen idonta.
Binta kawai yakeyi da ido yana mamakin kalaman da take son fada da suka yi mata
nauyi haka, a lokaci guda kuma yana mamakin abinda ya hanata ta fara kokarin bin
umarnin da ya bata.
Sai da tattaro duk wani karfin hali da take dashi ta bude baki a hankali tace
Kallon da yake binta da shi ya sa ta dakata da maganar ba don iya abinda ta so fada
kenan ba.
'Ban gane ba. To ya za ayi da yaran? Kin san dai idan sun dawo nan dakunan ba zasu
ishemu ba sannan kuma nan din gidan haya ne wancan shine nawa. Don haka kinga dole
haka zaki koma can din. Idan ma akwai wani abu da kike so a gyara a gidan a hankali
za a mayar miki da shi yanda kike so ai ko?’
Ta sake saita fuskarta ta dan jijjiga kai tana dubansa, suka dan yi jim suna kallon
juna sannan tace
'Gaskiya ba wai gidan ne ba zan koma ba. Ka san dai raino abu ne mai wahala kuma
mai nauyi, duk kwatancen da zan yi maka ba zaka gane ba. Gaskiya ba zan iya rike
yaran bane ba wai gidan ne bai yi min ba.’
Ji yayi kamar ta buga masa guduma a ka, ya kalleta cike da tsananin mamaki wanda a
hankali ya fara komawa fusata. Nan take itama ta bata rai ta kawar da kanta. Bayan
ya gama kare mata kallo yace
'Ban fahimcekiba, kina nufin kice ba zaki zauna ki kular min da yara ba kenan? To
ya kike so nayi da su? Haka za a barsu su cigaba da zaman kansu ke kuma gaki a nan
a matsayin matata ko kuwa hakura zanyi da aikin na zauna na dinga kula da su?’
'Ban sani ba, amma dai na san abinda ba zan iya ba. Kayi hakuri ka fahimce ni.’’
'Ya za ayi na fahimceki Aisha, kina gaya min ba zaki iya zama da ‘yayana ba? Me
suka yi Miki? Ko kuma kishin mahaifiyarsu ne zaki koma yi da su da har kike
kyamatarsu haka?’
Wata zazzafar kwallace ta fado kan fuskarta; dama ta san babu wanda zai fahimceta
musamman shi da yake so a yita kula da shi da ‘yayansa. Batayi magana ba don haka
ya cigaba.
'Daman shi yasa tun farko kika ki zama a cikin iyalina? Kina nufin ni kadai kike so
ba kya son zuri'ata Aisha? Wannan ai ba so bane. A kan idonki yaran suka zama
marayu amma kice ba zaki iya kula da su ba ke ko ladan rikon maraya ba kya so? To
ya kike so nayi da su?’
Tayi murmushi tare da share kwallar idonta, ta mika hannu ta dafa hannunsa dake
ajiye a kan kujera. Ya kalli hannun nata sannan ya zare hannunsa tare da jifa da
nata hannun. Gaba daya tsoron da yake zuciyarta ya fice don ta kula so yake yayi
mata wata fassara da ban. Ta gaji da share kwalla don haka ta bari hawaye ya fara
bin fuskarta, ta bude baki a hankali tace
'Tun kafin su zama maraya nake rikon marayu don idan ba na manta karatun islamiyya
ba to wanda ubansa ya mutu shine maraya amma wanda uwarsa ta mutu musulunci baya
kiranshi maraya don uba shine karshen gata. Ban san yanda zakayi da su ba amma dai
na san kana da zabi kamar yanda musulunci ya tanada idan an sami irin wannan dangin
uwa zasu iya rike yara, idan kuma lallai matarka kake so ta rike su to ai kana da
damar da zaka kara aure ka sa matar a gidan. Ni bani da matsala da hakan. K..’
'Ke yanzu a kan ki zauna da yaran kin gwammace na kara aure? To naji kema kina da
marayu, ai wannan ba zai zama matsala ba sai ki dauko su su dawo nan mu zauna tare.
Wannan ma da kin yi magana ai da tuni suna nan.’
Tayi yake tace
'To don Allah su su Yusran me yasa ba Zaki iya rike su ba, yaran ma da kusan kowa
ya iya kula da kansa? Me suka yi miki ko me uwarsu tayi miki da ya shafe su kika
tsane su haka?’
Ta kula bata da wata mafita idan bata gaya masa gaskiyar abinda yake ranta ba. Ta
muskuta kadan tace
‘Ba wai ba zan iya rike maka yara bane, hasali ma ko dan shege ka kawo zan iya rike
maka shi har bayan ranka. Amma gaskiya ba zan iya zama da Yusra da Nana ba, idan ka
cire su biyu zan iya rike sauran yaran.’
Kan sa ya kara kullewa, binta kawai yake da kallo. Ya gyara zama cike da bacin ran
wannan rainin hankalin da Aisha take masa yayi ‘yar dariyar takaici yace
'Ah! Aisha kina bani mamaki. Yusra da Nana su kadai kika tsana? To me sukayi miki
da ba zaki iya zama da su ba?’
'Allah ya sani ban tsane su ba amma cutarwar da mahaifiyarsu tayi min tana da
matukar yawa duk da kai ma ka san wasu sai dai ka ki gayawa kanka gaskiya.’
'Duk wata cutarwar da Zahra tayi min da Yusra take amfani, ban iya kai kara ba shi
yasa ban taba gaya maka ba musamman bayan ka nuna mini yaranka masu tarbiyya ne ba
zaka dauki laifinsu ba. Idan baka manta ba akwai lokacin da ka dinga kasa cin
abinci na saboda yanda dandanon yake canzawa, to a wannan lokacin Yusra ake aikowa
ta zo ta saka min sabulu a abinci wanda sai da Allah ya toni asirin ta na gane.
Yanzu ma kuma ranar da aka kwana uku da rasuwar mahaifiyarta tayi min alkawarin ba
zata taba bari na maye gurbin uwarta ba kuma na tabbatar da gaske take.’
Ya nuna ta a raine
‘Ban iya rigima da tashin hankali ba kuma na tabbatar in dai da Yusra zan zauna to
a cikin haka zan rayu. Ba zan iya ba, amma sauran yaranka gaskiya bani da matsala
da su zan iya rike su kamar ni na haifesu.’
'Wannan duk maganar banza kikeyi! Idan dai zamana kike a wannan gidan to na baki
umarni gobe ki koma wancan gidan an gyara miki daki, idan kuma zaman kanki kikeyi
to sai ki yi yanda kike so.’
Sai da ta gaji da share hawaye sannan ta tashi ta rufe gidan ta wuce daki inda tayi
alwala ta kabbara Sallah domin ta san Allah ne kawai ya san halin da zuciyarta take
ciki a yanzun.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
42
Tana sane da cewa Goggo Binta zata tafi don haka gari yana wayewa bayan ta gama
shirin tafiya aiki ta zubo sandwich din da ta yiwa yara a roba ta dauko abinda zata
bawa Goggo ta nufi gidan.
A falon kasa ta samesu duka suna karyawa. Da gudu Sumayya tayi mata oyoyo ta fara
surutu, Saddiku da yake zaune a dining table ya juyo ya gaisheta. Ta karasa ta
zauna a kusa da Goggo a dai-dai lokacin da Yusra ta mike ta shige kichin. Cikin
girmamawa suka gaisa da Goggo da sauran yaran, ta mikawa Rukayya robar sandwich din
tana fadin
Ta mikawa Goggo daya robar. Rukayya ta dauki robar ta shige kicin. A daidai lokacin
Goggo ta dubeta tace
'To nifa yau bako zai yi halinsa, sai dai nace Allah yaji kan wannan yarinyar.
Wadannan yaran kuma dama tare na ganku sai dai nace Allah ya zaunar daku lafiya.’
Tace
'To a dawo lafiya. Ni dai nan da awa daya ma na tafi in sha Allah.'
Nan da nan Goggo ta fara godiya tana saka mata albarka. Ta mike ta nufi kofa bayan
tayiwa yaran sallama tana tuna musu gara su fito kada su makara.
Ta kofar kicin Yusra ta fita tsakar gida don haka babu wanda ya san tana waje. Dai-
dai lokacin da Aishan ta kusa karasawa bakin kofar dai-dai lokacin Yusra ta shigo
falon. Iya karfinta ta bangaji Aisha da kafada har saida Aishan ta danyi baya. Ta
kalleta sama da kasa ta wuce. Cikin sanyin jiki itama ta fice daga falon, ta tsaya
a bakin gata ta hadiye malolon bakin cikin da ya tokare mata makogoro ta share
kwallar takaicin da ta gangaro daga idonta; ya ma za ayi ta zauna da Yusra?
Babu wanda ya ga abinda ya faru sai Saddiku wanda yake kan dining table. Ya jijjiga
kai ya cigaba da cin abincinsa, yana mamakin yanda Yusra ta zama marar kunya domin
shi kansa ba kyale shi tayi ba tun lokacin da ya dawo daga makaranta.
Kafin Aishan ta fice daga gate din Abba ya sauko daga sama ya yiwa yaran magana su
fita a kai su makaranta. Bayan sun fice ya gaisa da Goggo yana tambayarta ita da wa
ya jiyo hirarsu. Tace
'Tace idan ta dawo daga aiki ai zata dawo dakinta. Sai ayi ta hakuri, Allah ya ji
kan mahaifiyarsu kuma Allah ya baku hakurin rashi gaba daya.’
Wannan maganar da Goggo ta sanar da shi ta kara masa nutsuwa, duk da daman ya san
Aisha ba zata ki bin umarninsa ba. Sai da ya jira Goggo ta shiga mota Malam Ali ya
ja su ita da Saddiku sannan shima yayiwa Jummai sallama bayan ya sanar da ita ta
sake share dakin da aka gyarawa Aisha sannan ya fice.
—------
Haka Aisha ta wuni a wajen aiki zuciyarta babu dadi, duk wanda ya kalleta sai ya
tambaya ko bata da lafiya. Abu daya take jaddadawa kanta shine ba zata zauna da
Yusra ba, idan Abba ya matsa mata tabbas zata iya hakura da aurensa.
Ana tashi daga aikin ta kama hanya ta koma gidanta, bata da niyyar barin gidan don
haka ta cigaba da harkokinta kamar yanda ta saba.
Wajen karfe uku lokacin da su Rukayya zasu tafi islamiyya ta ja Ummi da Sumayya
suka shiga gidan Aishan. A take Nana ta koma gida ta gayawa Yusra wadda tayi
alkawarin idan suka dawo sai ta koyawa Rukayya hankali don ba zata barta ta dinga
karya dokar Mommy ba ko da bayan ran Mommy din ne.
Ta kalleta tana murmushi, bata san amsar da zata bata ba don haka tace
'Ba'a fasa ba amma zan dan fita tukunna sai dai kafin ku dawo na dawo.’
'To Anti.'
Ta aika Rukayya kicin ta dauko musu biskit ta bawa Ummi da Sumayya suka yi mata
sallama a kan idan sun dawo zasu sameta a gidansu suka fice.
Ta bi bayansu da kallo cike tsananin damuwa; da ace su ukun nan ne kadai yaran Abba
tabbas da tuni wani zancen ake ba wannan ba musamman yanda ta kula shima Saddiku
tunda ya dawo daga makaranta cikin girmamawa yake mu'amala da ita.
Suna fita ta kirawo Zahida ta sanar da ita yanda sukayi da Abban. Zahida tace
‘'To yanzu ya za ayi? Kinga fa ko Hajiya ba a gayawa halin da ake ciki ba.’
'Hmn! Da na gaya mata da yanzu ta tursasa ni na koma gidan ni kuma wallahi ba zan
yi wannan rayuwar ba. In ya dawo kawai ya daga min hankalin gidan zan tafi sai ayi
ta ta kare don ba zan zauna da wannan yarinyar ba. Ko yau ma baki ga wulakancin da
tayi min ba da na shiga gidan, Ina kuma ga a ce kullum ina tare da ita.’
Cikin damuwa Zahidan tace
……….
Wajen karfe biyar Abba ya dawo daga aiki, gaba daya ya sakankance cewa zai tarar da
Aisha a gidan. Yana shiga falon bayan ya amsa sannu da zuwan Yusra wadda ya tarar a
falon kasan tana kallon TV ya karasa ya bude kofar dakin da aka gyarawa Aishan. Ga
mamakinsa babu komai a dakin, ya janyo kofar ya juyo ya cewa Yusra
Bai amsa ba ya haye saman zuciyarsa tana dugunzuma. Me yasa Aisha take son ta saba
umarninsa? Me take nufi da hakan? Idan bata rike masa yaran ba meye amfanin ta a
rayuwarsa a daidai wannan lokacin? Bai taba zaton zai dawo ya tarar bata gidan ba
amma gashi saboda raini bata dawo ba.
Tana zaune a falo a kan kujerar zaman mutum daya tana ta faman dube-dube a waya.
Bata ji alamar ya yi sallama ba don haka bata amsa ba, ta mike tsaye ta ajiye wayar
ta nufo shi tana yi masa sannu da zuwa.
Bai amsa ba ya tsaya daga bayan kujerar yana mata wani kallo na takaici, ta karasa
ta tsaya daga kusa da shi tana fadin
'Ga ab…’
Muryarshi ce ta katseta
'Aisha me nace miki? Me kike a gidan nan bayan ga inda nace ki koma kafin na dawo
zaki bar min yara su kadai, zaman kansu zasu yi kenan saboda mahaifiyarsu ta rasu
ko me?’
A fusace ya nuna ta
'Idan dai zamana kike to yanzu ba tare da bata lokaci ba ki fito ki koma can gidan
idan ba haka ba kuma to zaman kanki kike yi. Mun gama magana da maigidan nan next
week zasu karbi mukullinsu idan kuma zaki kama hayar sai kiyi magana da su ki kama
hayar tunda kin fi karfina.’
Ta bude baki zatayi magana ya dakatar da ita yana mata kallo mai cike da takaici,
ya fice ya mako mata kofar.
Yana fita ta zagaya ta zauna a kan kujerar ta sa kuka. Ita kanta bata san kukan me
takeyi ba tunda dama ta sa ran hakan zata faru. Sai da tayi mai isarta sannan ta
share hawayenta, ta dubi agogon bangon da yake dakin taga karfe shida saura minti
biyar. To zaman me takeyi a gidan mutane tunda ya gaya mata gida ya fita daga
hannunsa kuma idan ta zauna zaman kanta takeyi. Ta mike a hankali ta shige dakinta.
Kafin magriba ta tattara kayanta na bukata da kuma duk wasu kaya masu mahimmanci
wadanda motarta zata iya dauka. Ta fito ta zuba a motarta, ana kiran Magriba ta
rufe gidan ta ja motarta ta nufi gidan Hajiya.
—-------
Abba yana fitowa daga gidan Aisha ya koma gida, kai tsaye dakinsa ya shige ya rufo
kofa. Ya zauna a gefen gadonsa kamar wanda aka tunkuda, ya hada tafukan hannunsa
guda biyun ya zuba fuskarsa a ciki yana fitar da wani huci na takaici; bai taba
tsammanin taurin kan Aisha ya kai haka ba. To me Yusra tayi mata da zata ce ba zata
zauna da ita ba? Ita Yusran ya zai yi da ita kenan? Babu yanda za ayi ace a
rayuwarsa yanzu ya kara aure don wannan ba zai ma yiwu ba. Iya tsawon rayuwarsa
abinda ya sani shine idan aka saki mace ko ta rasu to idan dai tana da abokiyar
zama yaran wajen abokiyar zaman suke komawa ba tare ma da anyi wata magana ba.
Ita Aishan me yasa take jin cewa tana da zabi? Me Yusra tayi mata da har take jin a
cikin yaran zata rike wasu wasu kuma ba zata zauna da su ba? Tabbas ya san da sa
hannun Zahra a lokacin da ya manta da Aisha na wani lokaci to amma menene laifin
Yusra a ciki?
Ya daga fuskarsa ya gyara zamansa; in dai Aisha tana son zama dashi dole ta zauna
da yaransa gaba dayansu, kuma zai yi iya yinsa wajen ganin hakan ya faru. Ko babu
komai yana son ta sosai kuma a iya tunaninsa ita kadai ce macen da zata zauna masa
da yaran tsakanin da Allah babu cutarwar. Ya tabbatar bata da mugunta kuma bata da
sharri, hasali ma zai iya cewa idan dai magana ake ta tarbiyyar yara ta fi Zahra
iyawa saboda yanda yaga mu'amalarta da yaranta da kuma yanda take kula da Rukayya.
Ba zai taba rabuwa da Aisha ba kuma ba zai kara aure ba, itace dai zata hakura ta
zauna masa da yaran.
Yana nan zaune ya jiyo motsin su Sumayya suna shigowa sun dawo daga islamiyya. Yana
matukar tausayin yaran kuma tabbas ya san suna bukatar uwa kamar Aisha, yana fatan
kafin gari ya waye ta farka daga mafarkin da takeyi ta tattaro kayanta ta dawo
gidan.
……..
A guje su Sumayya suka shiga gidan suna murna saboda sun zata zasu sami Aisha a
gidan. Yusra ce kawai a falon, ba tare da ko sallama ba Sumayya ta dubeta tace
A gajarce ta amsa
'Bata nan.’
A dai-dai nan Rukayya ta shigo falon bayan ta yiwa Yusra sallama ta sanar da ita
sun dawo kai tsaye ta wuce dakin da aka gyarawa Aisha ta tura kofar. Babu komai a
dakin don haka ta mayar da kofar ta rufe sannan ta wuce dakinsu na kasa. Yusra da
take zaune a kan dining table ta bi bayanta da harara sannan tayi tsaki; wanda
Rukayyan ta ji amma sai ta kawar da kanta.
Tana shiga dakin ta ajiye jakarta ta canza hijabinta, Ummi da take zaune a gefen
gado bayan ta ajiye tata jakar tace
'Yaya Rukayya Antin bata dawo nan ba, gidanta zaki je?’
Dogon tsakin da Yusran ta ja shi ya sa Rukayyan ta dubeta, ita kuwa Ummi a take ta
fara kokarin cire hijabinta don tana shakkar Yusran. Cikin izgilanci Yusran ta
matsa gaba Rukayyan tace
'Babu inda zaku je wallahi. Ke wai wace irin marar tunani ce Rukayya, uwarki ta
mutu amma ko sati biyu ba ayi ba kin fara karya dokokin da ta shinfida miki lokacin
tana raye. Iya biyayyarki da Mommy kenan? dama jira kike ta mutu ki koma wajen
makiyiyarta? To wallahi baki isa kije wajen wannan ma-sharranciyar matar ba yau. Ke
kenan saboda tsabar ba kya kishin Mommy kullum ki kwashe mata yara ki kai su inda
ta hanaki zuwa sai kace mai kwakwalwar kifi. To yau babu inda zaku tunda uwar taku
nan zata dawo sai…’’
Cikin takaici idonta yana fitar da kwalla ta matsa kadan zata shige ta gefen Yusran
amma Yusran ta tareta, ta sake matsawa Yusran ta sake tareta tana fadin
'Malama ki cire wannan hijabin ki zauna babu inda zaki je. Lallai yau da Mommy zata
dawo duniya da tayi mamakin yanda kika manta da ita kike kokarin sake uwa….’
Kafin ta gama fadin abinda tayi niyya Rukayya ta dage iya karfinta ta tunkudata. Ta
tafi taga-taga, saura kadan ta kai kasa ta dafe kofar dakin ta tsaya tana kallon
Rukayyan da mamaki. Cikin kunan rai tace
‘Kan bala'i, wato saboda matar nan ta gama dake ni kike turewa saboda baki da kunya
kuma kinga babu idon Mommy ko?’
A fusace ta nufo ta yayinda ita kuma Rukayya take tsaye ta nade hannuwanta a
kirjinta tana fadin
'Babu ruwanki da ni Yusra, fita a harkata! Zan je na tambayi Abban idan yace kada
naje sai na fasa amma ke baki is…’
Kafin ta rufe bakinta Yusran ta dauke ta da mari. A take ta dafe kumatunta tana
huci, kafin tayi wani tunani ta zare hannu itama ta gaurawa Yusran mari.
Da gudu Ummi ta fice tana kuka ta haye sama don ta kirawo Abba.
Yusran ta cakumo wuyan hijabin Rukayya, cikin zafin nama Rukayyan ta fisge ta
tunkede Yusran wadda ta fadi kasa, ba tare da bata lokaci ba Rukayyan ta bita kasa
ta haye kan ruwan cikinta tana ta kai mata duka ko ta ina; duk wani bacin rai da
Yusran ta dade tana cuzguna mata da shi tun kafin rasuwar Mommy ya dinga dawo mata
don haka ta rufe ido tana ta faman kai mata duka. Ganin abun yayi yawa yasa Yusran
ta fara ihu tana kokarin ture Rukayyan daga kan cikinta wanda ya gagara, kamar ma
karawa Rukayyan karfi takeyi. A dai-dai nan Abba ya banko kofar ya shigo Ummi da
Sumayya suna biye da shi. Da karfi ya fincike Rukayya daga kan Yusra wadda idonta
ya rufe, ta fizge daga rikon da Abban yayi mata tana huci. Ba tare da bata lokaci
ba ya gaura mata mari wanda ya dawo da ita hayyacinta ta dafe kumatun tana kallonsu
shi da Yusran tana fitar da hawaye masu zafi.
Da gudu Sumayya ta fice ta nufi bayan gida inda Jummai da Nana suke wanki don ta
kirawosu.
Abban ya tsuguna a kan Yusran ya kamata ta mike tsaye yana nuna Rukayya yana fadin
‘Wannan wane irin rashin hankali ne Rukayya, yayarki kikewa wannan dukan kamar kin
sami wata jaka?’
Ta sunkuyar da kai hawayenta yana diga yayinda Abban ya tallafi kafadar Yusran yana
kokarin zaunar da ita a kan gado yana duba fuskarta inda bakinta ya fashe yake
fitar da jini.
'Baki da hankali Rukayya? Kalli yanda kika ji mata ciwo. Fice kije dakina ki jirani
kuma ki daina wannan kukan don sai jikinki ya gaya miki.’
Ya zaunar da Yusran a gefen gado yana share mata hawaye yayinda Rukayya ta ja kafa
ta fito daga dakin. Tana fitowa taci karo da Saddiku yana shirin shiga dakin wanda
shigowarsa gidan kenan yana dauke da jakar computer dinsa. Ya sha gabanta ya dafa
kafadarta da mamaki a fuskarsa yana tambaya
'Rukayya me ya sameki?’
A nan Jummai ta shigo da gudu Nana da Sumayya suna biye da da ita, suka tsaya a
inda suka ga Saddikun yana tambaya. Sumayya ce ta bashi amsa tace
'Fada sukeyi ita da Yaya Yusra shine Yaya Rukayyan ta zane Yaya Yusran.’
A nan Rukayya ta fada jikin Saddikun ta fashe da kuka, ya dafa bayanta yana bata
hakuri.
Jummai ta wuce shi ta shige dakin, ta tsuguna a gaban Abban tana fadin
'Subhanallahi. Muna can ni da Nana muna wankin uniform ashe fada suke yi haka. Yaya
me kika gayawa kanwarki ya fusata ta haka? bari na samo ruwa a wanke bakin.’
Abban yace
Yana fitowa yaci karo da Saddiku yana bawa Rukayya hakuri, ya dubesu yace
'Ba ce miki nayi kije dakina ki jirani ba, mara kunya fitsararriya?!
'Ka kyaleni da ita ka shiga kaga yanda ta kama ‘yar uwarta da duka sai kace mara
hankali.’
Ta ja kafa ta wuce saman tana shesshekar kuka, shi kuma Saddiku ya wuce dakinsa.
A hankali Abban ya ja kafa ya karasa kan dining a table din kasan ya zauna ya dafe
kai, wannan wacce irin musiba ce? Yaran da basu taba yin wani fada irin wannan ba?
Me yasa Aisha tayi masa haka? Da tana gidan nan ai da hakan ba zata faru ba. Jummai
ta fito daga dakin ta sameshi a zaune, ta rage tsawo tace
'An wanke fuskar Alhaji, ciwon ma ai baiyi tsananin ba. Yarinta ce take damunsu,
gashi Yaya ta iya tsokana. A yi hakuri a yiwa Rukayyan a hankali.’
Kai kawai ya daga mata ta tashi ta wuce kicin tana rike da hannun Sumayya. Jimawa
kadan shima ya tashi ya haye saman zuciyarsa a jagule.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
43
Ba a jima da idar da sallar Magriba ba ta tsaya a bakin gate din gidan, ta matsa
horn don ta san Abdallah yana nan. Kafin ta danna na biyun ya leko, yana ganinta ya
koma da murna ya bude gate din. Ba tare da bata lokaci ba ta tura motar cikin
farfajiyar gida, ta sami guri a cikin garejin gidan ta ajiye motar ta yanda duk
wanda ya kalla ya san motar a nan zata kwana.
Tana fitowa daga motar ta mikawa Abdallah mukullin motar ta nuna masa akwati a
bayan motar tace shi kadai zai dauko ya bar sauran kayan sai daga baya.
Kamar mara gaskiya ta shiga gidan da sallama, Hajiya, Anti Uwani da Farha suna
zaune a falon. Da gudu Farha ta mike daga kusa da Anti Uwani ta rungume Mamanta
tana mata sannu da zuwa. Kafin ta gama amsawa Abdallah ya shigo da akwatin ya nufi
dakin Anti Uwani da shi. Itama Farha ta dubi Aishan tana murmushi tace
Ta karasa cikin falon ta zauna a kan kafet daga gefen Hajiya wadda take zaune
kafafunta a mike. Ta gaida Hajiya sannan ta juya ta gaida Anti Uwani. Hajiya ta
dubeta fuskarta da alamar tambaya tace
'Lafiya dai da magribar nan kuma naga ana kwana zaki yi kina daga kai?’
Ta danyi murmushin yake ta kawar da kai saboda yanda kallon da su biyun suke binta
da shi yake saka ta jin kamar wata mai laifi. Tace
'Bari naje nayi sallah, ko magriba ban yi ba ga shi nan har an fara kiran isha'i.’
Ba tare da ta saurari abinda zasu fada ba ta bar wajen da sauri ta shige dakin da
yaran suka shiga da kayanta.
Hajiya ta dubi Anti Uwani tace
'Kin ga yarinya don Allah, guduwa fa ta yi. Tabbas wannan zuwan nata akwai dalili.’
Har aka ci abinci akayi sallar isha'i tana daki, babu wanda ya nemeta. Sai dai Anti
Uwani ta zuba abinci ta bawa Farha ta kai mata daki. Da yake tana tattare da yunwa
ta dan taba tuwo, ta mayar ta rufe kwanukan ta wanke hannunta a bandakin da yake
cikin dakin sannan ta dawo ta kashingide a gafen gadon Anti Uwani.
Bata dade da zama ba Anti Uwani ta turo kofa ta shigo dakin, bayan Aishan ta amsa
sallamarta ta wuce ta zauna a gefen gadon yayinda Aishan ta gyara zama ta janye
kafafunta. Bayan Anti Uwanin ta zauna ta dubi Aishan, suna hada ido ta sunkuyar da
kanta yayinda Anti Uwani tayi murmushi. Tace
‘Kya ji kunya mana Shatu! To ya aka yi? Don dai wannan zuwan na san ba na lafiya
bane.’
Sukayi shiru na dan lokaci, Anti Uwani tana sauraronta ita kuma tana kallon
hannunta tana tunanin ta inda zata fara. Jimawa kadan ta gaji da yanda Anti Uwanin
ke kallo da sauraronta ta bude baki da kyar tace
'Cewa yayi idan na zauna a gidan zaman kaina nakeyi, shine na taho.’
'Ban fahimceki ba fa, Yusufan ne yace zaman kan ki kikeyi ko kuwa? Kiyi min bayani
yanda zan gane.’
Ta dan muskuta ta fara yiwa Anti bayanin abinda ya faru a kan umarnin da ya bata ta
koma gidan yaransa har zuwa inda yace idan bata koma ba zaman kanta takeyi ba
zamansa ba. Ta kara da
'Shine na taho.’
Mamakin Anti Uwani ya sake karuwa, domin duk wannan bayanin da Aishan ta dauki
lokaci tana yi kara kulle mata kai kawai tayi; ta kasa gane dalilin da ya sa ita
Aishan ba zata koma wajen yaran nasa ba. Tace
‘A’a! To ai dole yace zaman kanki kikeyi Aisha, matar nan ta mutu fa me ya sa ba
zaki bi umarninsa ki koma gidan ki kular masa da yaran ba? Wannan ai kowa ma ya san
haka ce zata kasance.’
Nan ta fayyacewa Anti Uwani dalilan da suka saka ba zata rike masa Yusra da Nana
ba, ta bata misalan wasu daga cikin abubuwan da Yusran ta yi mata.
'To ai shine. Kuma ni Allah bai dora min zama da yaransa ba, ya kai su dangi uwarsu
ko kuma ya auro wata ta rike masa su amma ba ni ba. Kinga ni uwarsu musamman take
koya musu tsanata don haka zai yi wahala a sami wanda zai saukesu daga kan koyarwar
uwarsu, amma kinga idan wata ya aura watakila su bata dama ta zauna da su.’
‘Hakane Shatu. Amma fa gaskiya duk bayanin nan naki babu wanda zai fahimceki fa don
ina jin ko Hajiya ba zata saurareki ba. Ina ga gara kiyi hakuri ki koma in ya so a
zauna da Yusufan ya tsawatarwa yarinyar watakila ki ga abun ya zo da sauki.’
'Wallahi Anti Uwani ba zai tsawatar mata ba, kuma ko ya tsawatar mata babu abinda
zata fasa tunda yaran sun saba ba sa jin magabarsa. Ba zan iya rayuwa da wannan
yarinyar ba wallahi don idan ta kasheni nawa marayun yaran ta cuta shi ubanta wata
zai auro su cigaba da rayuwarsu. Idan kuma bata kasheni ba to in ta kureni nace zan
dauki mataki a kanta wallahi kowa ba zai ji dadi ba tunda ai duk muguntarsu nima na
iya Allah ne yake katangeni.’
Sukayi shiru na dan lokaci. Abun ya sha kan Anti Uwani sai dai ta san babu wanda
zai fahimcesu. Ita ta san irin wadannan yaran don ta zauna da su, don daya har
bayan an yi mata aure ma haka ta dinga zuwa cikin gidan tana haddasa fitna a karshe
sai da ubanta ya saki Anti Uwani a kan laifin da ba nata ba. Ta muskuta tace
'Su Baffa suyi masa magana, idan ya dauke Yusra da Nana bani da matsala da sauran
yaransa, ko dan shege ya bani kuma zan rike masa da amana. Amma idan dai aka ce sai
na zauna da Yusra to gaskiya na hakura da aurensa.’
'A'a abun ma ba zai kai haka ba in sha Allah. Amma dai ina kokonton yiwuwar abinda
kike so domin su fa maza gani suke kamar tunda suka aureki to ko me suka rakito
dole ki zauna da shi. Iyayenku ma kuma goya masa baya zasuyi. Kuma daga baya idan
ta kashe miki auren a cigaba da zaginki.’
'Duk ma abinda zasuyi sai dai suyi don wallahi Anti Uwani idan aka ce sai na zauna
da yarinyar nan zaku nemeni ku rasa ba zaku sake gani na ba.’
'Bana son rashin hankali, kada na sake jin wannan zancen kin ji na gaya miki. Ki ci
gaba da addu'a in sha Allah za a sami maslaha.'
Sukayi shiru na dan lokaci kowa da abinda yake tunani, jimawa kadan Anti Uwani ta
tashi ta fice ta koma dakin Hajiya; inda ta tarar Farha har tayi bacci yayinda
Hajiyan take zaune a kan dadduma inda ta idar da shafa'i da witri.
Nan ta zauna ta bawa Hajiya labarin abinda Aishan ta gaya mata. Cike ta mamaki da
takaici Hajiya tace
'Kin ji ko Uwani, na gaya miki yarinyar nan fa bata da hankali har yanzu. Ya za ayi
kina matsayin matar mutum kuma kice yaransa marayu sai kin zabi wadanda zaki rike
masa?’
'To Yaya ai tayi mutunci ma tunda ita nata marayun ko daya bai zaba ba balle ya
taya ta rikonsu.’
Ta harareta
'Kinga Uwani ki daina tunzura yarinyar nan fa. Ke da baki taba haihuwar nan ba ba
kin zauna da ‘yayan kishiyoyin ba kala-kala, me ya kasheki? Duk sharrinsu ba haka
suka hakura suka barki ba?’
Ta kawar da kai
'Na hakura na barsu dai Yaya bayan sun sa ubansu ya kore ni. Kuma zama da su din ai
rayuwa ce wadda na cikin gidan yari ya fi ka ‘yanci kuma ko makiyi na bana yiwa
fatan irin wannan rayuwar Yaya.'
Suka yi shiru na dan lokaci. Hajiya bata so ta tunawa Anti Uwani tata rayuwar ba
don ta san tabbasa ta sha wahala a hannun yaran kishiyoyi domin ita din Allah bai
taba bata haihuwa ba. Kuma haka Allah ya hada ta da mijin da ya dinga auren mata
suna haifa masa yara yana sakinsu, kusan duka yaran ita ta rikesu. Duk wata
fitnarsu haka zai muttsike ido yace itace bata san ciwon yara ba don bata haifa ba,
haka tayi wannan rayuwar kuma daga karshe ya saketa a kan laifin da ba nata ba.
Sai daga baya kafin rasuwarsa ya dinga kokarin mayar da aurenta ita kuma a lokacin
ko sauraronsa bata yi ba.
'Idan gari ya waye zan gayawa Abubakar ya sanar da Baffansu; ai tayi mutunci ma
tunda ba duka yaran tace ba zata rike ba. Tunda na bude ido nake zuwa islamiyya har
yau ban daina zuwa ba kuma ban taba ji a cikin karatu an karanta aya ko hadisin da
yace dole idan kina auren mutum ki rike masa yaran da baki haifa ba, hasali ma har
aka gama bayanin masu riko babu matar uba a ciki to na me za ace sai ta yi? Idan
yana so ta rike masa su kuma ai matarsa ce sai yayi amfani da dabara ya lallabata
ba wai ya nuna mata isa ba. Kuma idan sun sabauta Aishan ai yaranta suka cuta da mu
da muka haifeta, tunda shi ubansu aure zai kara ya cigaba da rayuwarsa.’
'Hakane. Bari dai gari ya waye Baffa yazo, idan aka bi abun a hankali za a sami
mafita in sha Allah.'
Jimawa kadan Anti Uwani tayi mata sai da safe ta tashi ta koma daki; dukansu
zuciyoyinsu babu dadi. Ita Hajiya ba da son ranta ta tunawa Anti Uwani tata rayuwar
auren ba wadda take cike da jarrabawa kala-kala ga rashin haihuwa, ita kuma Anti
Uwani abubuwan da suka faru da ita suna dawo mata tana tunani babu yanda za ayi ta
bari Aisha ta shiga irin rayuwar da ita tayi.
Rayuwar auren Anti Uwani ce gaba daya ta dinga dawo mata; abubuwan da tace ba zata
sake tunawa da su ba balle su sa mata damuwa amma yau sun hanata bacci.
Shekaru kusan talatin tayi a gidan miji amma iya shekarar farko ne kawai zata ce
tayi a nutse. Tunda ta shekara bata haihu ba dangin miji suka fara takura mata, tun
baya biye musu har shima ya fara damuwa. Kuma babu wanda ya taba cewa taje asibiti
sai dai ayi ta bata tsimi tana shanyewa, haka tayi ta shan rubutu da tsimi wani
daga gidansu wani kuma daga wajen dangin mijin. Ga kuruciya a tare da ita don bata
fi shekaru Sha biyar ba a lokacin. Shekara uku a gidansa ya kara aure; yarinyar
kuwa tana tarewa ta sami ciki. Haka aka mayar da Anti Uwani kamar mai aiki a gidan;
kwashe amai, wanki, girki duk itace idan kuma dare yayi maigidan yace wajen amarya
zai kwana kada wani abu ya sameta. A haka cikin damuwa da hantara suka cigaba da
zama da matar nan har ta haifa masa yara biyar duka mata, daga baya ya saketa ya
kwace yaransa tunda dama ko da uwarsu tana nan ma duk wata hidimarsu da ta gida
Anti Uwani ce take yi. Bayan ita ya auro wata wadda ita kuma tana shigowacta haifa
masa yara biyu maza. Haka Anti Uwani ta cigaba da bauta mata saboda da zarar ta ki
yin wani abu sai maigidan yace tana bakin ciki don Allah bai bata haihuwa ba. Daga
karshe tana zaune a tsakar gidan tana hura wuta zata dora abinci yayinda amaryar
gidan take janyowa maigidan ruwan wanka a rijiyar tsakar gidan karamin yaron gidan
mai shekaru kamar bakwai yayiwo tsokana ya shigo gidan da gudu basuyi aune ba sai
ji sukayi ya fada rijiyar nan. Nan take uwarsa tace Uwani tana kallonsa ya fada
rijiyar bata rikeshi ba. Shi kuma maigidan yace idan dai yaron ya mutu to ya saki
Uwani saki uku. Da kyar aka dauko gawar yaron daga rijiyar inda a nan take maigidan
ya kora Uwani gida.
Bayan wanna kuma ta auri wani mutum wanda shi kuma lafiya suka zauna don shi bai
hadata da iyalansa ba ma suna gari da ban da ban, shekara tara da aurensu Allah ya
karbi rayuwarsa. A nan wancan ya dawo cikin zawarawa ita kuma tace gaba daya ma ta
gama aure a duniya tunda ko babu komai a lokacin ta tsufa.
Da kyar bacci ya kwasheta tana tuna rayuwarta ta baya kamar mai kallon fim.
—----
Bai san tsawon lokacin da ya dauka a zaune a kan dining table din ba, gajiya kawai
yayi da zaman ya tashi jikinsa babu kwari ya hau saman. Kai tsaye dakinsa ya wuce,
yana shiga ya zauna a gefen gadon ya dafe kansa da hannuwansa. Motsin da ya jiyo
daga daya gefen gadan shine ya janyo hankalinsa, ya sauke hannuwansa ya kalli
bangaren da ya jiyo motsin. Rukayya ce a takure a kasa daga gefen gadon ta hada kai
da gwiwa; sai a lokacin ya tuna shi ya ce tazo ta jirashi a daki.
'Rukayya.'
Ya kirawo sunanta.
'Um.'
'Taso ki zo nan.’
Ta taso tana goge fuskarta wadda tayi ja gaba daya saboda kuka; duk da zuwa yanzu
babu hawaye a fuskarta. Ta zagayo ta dawo gabansa ta tsuguna tana kallon kasa. Ya
kare mata kallo na dan lokaci cikin damuwa, ya mika hannuwansa ya kamo nata
hannuwan wadanda suke ajiye a kan gwiwarta ya rike tafukan hannunta a cikin nasa ya
sake kiran sunanta. Ta amsa a gajarce tare da daga Ido ta kalleshi ta mayar da
idonta kasa. Yace
'Kin san bana son karya don haka gaskiya zaki gaya min.’
Cikin sanyin murya tana kokarin danne hawayen da yake shirin kwace mata tace
'Ban gane ba Rukayya, kiyi min bayani sosai. Me ya hadaku fada? Me yasa don zaki je
gidan Anti Aisha za a ce ba kya son Mommynki?’
Sukayi shiru na dan lokaci, shi yana sauraronta yayinda ita kuma take tunanin yanda
zata yi masa bayani ba tare da ta fadi laifin Mommy ba. Shirun ya dan tsawaita kuma
ta san ita yake jira tace wani abu, ta share kwalla daga idonta sannan ta fara yi
masa bayanin abinda ya faru har ya sa suka fara fadan. Bayan ya gama sauraronta
yace
'To zuwa gidan Antin ne ya zama yiwa Mommy rashin biyayya ko kuwa wa yace mata zaki
sake uwa ne?’
Bata son yanda yake turata kan bayanan da zasu shigo da Mommy cikin maganar amma ta
san dole ta bashi amsa. Ta kosa da tsugunon sannan kuma bata son maganar, haka ta
sake share kwalla ta cigaba da bayani.
Tayi masa bayanin yanda Mommy ta hanata zuwa gidan tunda ya auro Aishan sannan tace
'Kuma yanzun ma ba zama zanyi ba, zuwa zanyi na gani ko akwai kayan da zan tayata
kwasowa tunda ka ce mana zata dawo shine ita kuma ta fara gaya min maganganu.’
Yayi shiru na dan lokaci yana so ya hada zantukan gaba daya ya basu ma'ana, sai dai
kansa gaba daya ya cushe sai sara masa yake. Da kyar ya daga kwayar idonsa ya kalli
Rukayyan saboda yanda duk wani motsi na kwayar idon nasa yake kara masa ciwon kai.
Yace
'To kiyi hakuri, idan kin je gidan Aisha ba yana nufin zaki sake uwa bane don babu
wanda yake iya sake uwa, sai dai Aishan itama uwarku ce gaba daya tunda kinga yanzu
nan zata dawo ta dinga kula da ku. Amma bana son ki sake yiwa wani irin dukan da
kika yiwa yayarki, rashin hankali ne zaki iya jiwa mutum ciwo.’
'To Abba.'
'Tashi kije, kada ki sake kulata kuyi wani fadan idan ta yi miki wani abu ki zo ki
gaya min ko ki gayawa yayanku.’
'To.'
Har ta kama hannun kofar zata bude ya sake kiran sunanta, don haka ta dawo ta
tsuguna daga gefe. Yace
‘Akwai wani abu da Anti Aishan takeyi ne wanda yasa Mommy din bata son kuje
wajenta?’
'Wallahi Abba babu wani abu, haka kawai ne sai Mommy din taga kamar Antin zata
cutar damu kuma wallahi ba haka bane. Ita kuma Yaya Yusra sai ta dinga zugata ba
zata bata hakuri ba.’
Ya jijjiga kai ya sallami Rukayya wadda ta fito daga dakin ta rufe masa kofa.
Gaba daya kansa ya kulle; tabbas ya san Zahra bata son Aisha kuma ya san akwai
lokutan da take hana Rukayya zuwa gidan amma bai san abun ya kai haka ba. To ko shi
yasa Aishan tace ba zata zauna da Yusra ba? Watakila wani abune na kiyayya da
Yusran take bayyanawa Aishan yasa take jin ba zata iya zama da ita ba. To amma ai
babu inda zai kai Yusra don haka dole Aishan tayi hakuri ta zauna da yaran gaba
daya. Zai yi magana da Yusran zuwa da safe kuma zai sakata a gaba suje ta bawa
Aishan hakuri in yaso ma sai ta tayata kwaso kayanta kafin su Rukayyan su dawo
makaranta ta dawo gidan.
Sarawar da kansa yakeyi tayi yawa don haka ya mike ya matsa gaban karamin fridge
din da yake dakin ya bude ya dauki ruwa sannan ya koma gaban mudubi ya dauki
Panadol ya hadiya. Ya shiga bandaki ya yiwo alwala da nufin yayi sallar Magriba
wadda bai yi ba ya tsaya rabon fada gashi har ana kiran isha'i; sai dai yanda yaji
da ya fito ya tabbatar ba zai iya yin sallar a lokacin ba.
Don haka ya kwanta a gefen gadon ya dafe kai tare da rufe idanuwansa.
…….
Washegari da wuri ya tashi duk da kasancewar ranar asabar ce. Karfe bakwai na safe
ya sauko daga saman, yaran gaba daya suna kan dining table suna cin abinci domin
akwai tahafiz wadda karfe takwas saura kwata ake shiga. Yusra ce kawai wadda bata
tashi daga bacci ba bata wajen amma har Saddiku ma yana zaune. Bayan ya amsa
gaisuwar su ya tambayesu Yusra inda suka tabbatar masa bata tashi daga bacci ba.
Surutunsu ya sa Jummai ta fito daga kicin inda take aiki, ta tsuguna ta gaisheshi.
Bayan ya amsa ya koma ya haye saman inda Rukayya ta bi bayansa da abincin safen sa
ta ajiye masa a table din saman ta sauko.
Ya shige dakinsa ya kashingide a kan gado ya fada tunani; tabbas yana bukatar mace
a gidan don da ace da mace a gidan wadda ba ‘yar aikin gidan ba da ya san yanzu
yana bacci amma dole ta sa kullum sai ya tashi ya tabbatar yaran sun shirya sannan
idan sun tafi makaranta shima ya shirya ya fita nasa aikin. Ya san Aisha karfe
takwas take tafiya islamiyya don haka bari zai yi sai bayan azahar lokacin ta dawo
yaje suyita ta kare. Domin shi yau din nan yake son ta dawo gidan.
Har bayan azahar yana gidan yana sauraro ko zai ji shigowar Aisha amma bai ji
motsinta ba. Don haka wajen karfe uku bayan yara sun tafi islamiyya ya shirya ya
nufi gidan Aishan da shirin zai je yaji abinda ya hanata dawowa, da shirinsa na
wucewa gidan Yaya Bello bayan ya gama da Aishan.
Da mukullinsa ya bude gate din ya shiga, yana zuwa kofar shiga falon yaganta a
garkame da kwado. Mamaki ya rufe shi; tunda yake da Aisha bata taba fita ba tare da
ta tambayeshi ba. To daga islamiyya ne bata dawo ba ko Kuma wani wajen ta wuce bata
gaya masa ba?
Har ya saka mukulli zai bude kofar sai yaga idan ya shiga ma babu abinda zai yi don
haka ya juya ya fice daga gidan ya nufi gidan Yaya Bello yana san ra duk ma inda
taje kafin ya dawo ta dawo in ya so sai yaji.
A farfajiyar gidan ya sami Yaya Bellon yana zaune yana shan fura da ‘yar autarsa
Minal wadda zazzabi ya hanata zuwa islamiyya. Bayan Minal ta gaisheshi ta shiga
gidan ta karbo masa kofi don ya sha furar, tana ajiyewa ta koma cikin gidan.
Bayan Abban sun gaisa da Yaya Bello suka cigaba da hirarrakinsu. Yaya Bello ya
dubeshi yace
'Wallahi Yaya bata koma ba, sai wasu dokoki da ta kafa na shirme. Ni gaba daya ma
na kasa fahimtar ta. Wai ita bazata rike yaran duka ba sai dai dole na cire Yusra
da Nana su bazata iya zama da su ba.’
'Ah, kamar Yaya? Wannan ai zancen banza ne ma. To su Yusran da Nana gidan marayu
zaka kai su kenan ko ya take so kayi dasu?’
'To basa dai jituwa da Yusra, ita kuma Nana zaka iya cewa ko uwarsu bata kai Yusran
iko da ita ba. Kuma da Zahran ma ai basu sami wata jituwa ba tunda ka ga abinda ya
faru har na shekara ban shiga gidan Aishan ba ko ba a fada mata ba Zahran take
zargi kamar yanda kowa ma ita yake zargi. Da wasu abubuwa dai na cutarwar da rashin
kunya da tace ana aika Yusran tana yi mata. Don haka tace ma wai Yusran ta tareta
bayan rasuwar Zahran ta gaya mata ba zata barta ta maye gurbin uwarta ba.’
'Ai ka ji! Duk shirme ne nasu na mata. Nawa Yusran take da Aishan zata ce ta rasa
yanda zata yi da ita? Wanna ma ai ba wani abu bane, idan ka koma sai ka hadasu ka
jawa yaran kunne a gabanta. Kuma in ta dawo nan din ma ai ba kyalewa zaka yi ba,
duk wanda yayi ba dai-dai ba sai ka dau mataki kuma gidan ma sai ka sa ido tunda
yanzu babu irin muguntar fa da mata basa yiwa dan kishiya.’
'Hakane. Sai na koma gidan yanzu zan saka ta a gaba mu koma can din.’
'Gara haka, Kai ma ka huta da biyan kudin hayar. Amma idan kace zaka biye ta tata
sai ta tarwatsa maka iyalin don haka ma kada ka saurara mata. Idan ba zata zauna
maka da wadannan marayun yaran ba yanzu kam bata da wani amfani a wajenka.’
Suka cigaba da hirarrakinsu Yayan yana kara karfafa masa gwiwa lallai kada ya kyale
Aishan dole ta koma ta kula masa da yaran.
Sai wajen karfe biyar na yamma sannan Abba yayi masa sallama ya kama hanyar gidan.
Yana shiga unguwar ana kiran sallar Magriba don haka kai tsaye masallaci ya wuce.
Sai da aka idar da sallar Magriba sannan ya wuce gidan Aishan. Kamar dazu haka ya
tarar da gidan a rufe, cikin tsananin mamakin inda Aishan ta tafi ya sa mukullinsa
ya bude kwadon ya shiga falon. Dakinta ya fara shiga inda ya hangi akwatunanta na
saman wardrobe babu guda uku a cikinsu, ya karasa ya bude wardrobe din ya tarar ta
kwashe mafi yawancin kayan sawarta. Yayi murmushi yana tunani yanzu haka ta riga
shi dawowa ta hada kayanta ta koma can gidan, don haka cikin kwarin gwiwa ya fito
ya nufi gidan.
Duka yaran suna zaune a falon kasa; kafin ya karasa shiga ciki Sumayya ta taso da
gudu tayi masa oyoyo. Bayan ya shiga ya zauna sannan ya dubi Jummai wadda take
tsaye da leda a hannunta tana jira ya dawo ta tafi gida yace
'Eh Alhaji dama jira nake ka shigo sai na tafi tunda Yayansu ma bai dawo ba
tukunna.’
Mamakinsa ya bayyana, yayi sauri ya wayance ya sallami Jummai ta fice bayan ta yiwa
yaran sallama shi kuma ya haye sama yana ta mamakin inda Aisha zata tafi harda
kwashe kaya haka ba tare da ta sanar da shi ba.
Ya zauna a gefen gado ya zaro wayarsa daga aljihunsa, ba tare da bata lokaci ba ya
lalubo lambar Aishan ya danna mata kira. Har aka fara kiran sallar isha'i yana nan
zaune yana faman kiran wayar amma ba a dagawa, haka wayar zata kari ringing har ta
katse. Cikin kosawa da damuwa ya mike ya shiga bandaki yayi alwala ya fito ya nufi
masallaci yana ta tunani kala-kala; to ina Aishan ta tafi? Me ya hanata daukan
wayars?
Yana daf da shiga masallacin dabara ta fado masa, don haka ya tsaya ya lalubo
lambar Zahida ya kirawota. Bayan sun gaisa ya tambayeta yayarta. Nan take ta sanar
da shi Aisha tana gidan Hajiya, yayi mata sallama ya ajiye wayar.
Ya mayar da wayar aljihunsa yana murmushin yake; wato Aisha gidansu ta tafi kenan
saboda ba zata rike masa yara ba? To wannan wacce kalar fitna ce? Wai dama haka
Aishan take ko kuwa wani ne yake zugata? To idan ma don yaranta ne ai yace ta
kwasosu su dawo gidan tare? Shi dai bai taba ganin inda mutum yana da mata taki
rike masa yara ba, ko da kuwa shegu ne balle yaran da aka san uwarsu. Yana nan
tsaye yana mamaki ba tare da ya sami amsar tambayoyinsa ba aka tayar da Sallah, don
haka ya mayar da wayar aljihunsa ya karasa masallacin ya shiga sahu cike da damuwa.
Ana idar da sallah ya koma gidan, a nan ya tarar Saddiku ya dawo don haka yayi musu
sallama ya shiga mota ya nufi gidan su Aishan. Duk da bai san me zai je yayi ba
amma dai yana jin gara yayiwa iyayenta bayani don yana kyauta zaton zasu goya masa
baya.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
44
Tun a wannan daren Hajiya ta kirawo Abubakar ta sanar da shi ga Aisha a gida don
haka gobe yazo da safe don a sami mafita. Suna ajiye waya ta kirawo Baffa, bayan
tayi masa bayani yace to shima da safen zai zo don bai kamata a bari ta sake kwana
ba ba tare an bi diddigin abun ba.
Ko da gari ya waye da yake Baffa ya saba sammako tun kafin su gama karin kumallo ya
iso gidan, Anti Uwani ta zubo masa dafadukan taliya da kunun tsamiya. Ya sanar da
ita ya riga ya ci abinci kafin ya fito sai kunun kawai ya debi rabin kofin ya zauna
a falon yana sha yana jiran isowar Abubakar don yace ya fi so ayi a gabansa.
Wajen karfe takwas da kwata shima Abubakar din ya iso. Nan suka hadu a falon Hajiya
da ita Hajiyan, Anti Uwani, Baffa da kuma Yaya Abubakar. Har Hajiya ta fara yiwo
bayanin abinda ya kawo Aishan gidan Baffa yace
'Ai bari zakiyi Hajiya ta fito Aishatun muji daga bakinta, ta hakane idan ma bata
da gaskiya da izinin Allah zan ganeta.’
Ko Hajiya bata fito ta yiwa ina kwana ba saboda tsoron abinda zata cewa Hajiyan sai
a lokacin ne ta gaisheta ta gaida su Baffa ma. Bayan ya amsa gaisuwarta yace
'Shatu ba fa na son rigima da rashin gaskiya. Me ya hadaku da mijinki har kika taho
gida tun jiya, gashi ko sawunki bai biyo ba kinga da alama kenan akwai abinda kika
yi masa?’
'Babu abinda nayi masa Baffa, shi yace idan na cigaba da zama zaman kaina nakeyi
shine na taho.’
'Assha! Akwai abinda kika yi din kenan in ba haka ba me ya kawo wannan maganar?’
Tayi shiru tana tunanin ta inda zara fara. Jimawa kadan Yaya Abubakar yace
Baffa ya daga masa hannu alamar yayi shiru, sannan ya dubi Aishan yace
'Ina sauraronki Aishatu, me ya kawo har yace miki zaman kanki kikeyi? Kuma me yasa
baki bashi hakuri ba kika taho?’
Ta kasa bude bakinta don haka Anti Uwani ta karanto masa bayanin abinda Aishan ta
gaya mata da ta zo. Kafin Baffan yace wani Abu Yaya Abubakar yace
'Ahaf! Ai wallahi na san akwai abinda tayi masa. Wannan shegen taurin kan nata ne
ya tashi shi yasa take so ta kashe aurenta.’
'Aure kam ba zai mutu ba da izinin Allah, Aishatu me yasa ba zaki zauna masa da
duka yaran ba? Wannan ai abu ne ma wanda ba sai kin jira ya nema ba. Haka aka saba
ko rabuwar aure aka samu matar da take gidan ita take hada kan yaran ta rike, balle
wadannan marayun. Kinga lada biyu zaki samu,ga ladan kula da marayu ga ladan
biyayyar miji.’
Tayi gyaran murya ta korowa Baffa bayanin irin abubuwan da Yusran take yi mata tun
daga farkon zamanta har zuwa maganganun data gaya mata ranar sadakar uku da kuma
bangazarta da tayi a falon gidan. Tace
'Wallahi Baffa ba zata bari mu zauna lafiya da shi ba, duk wani abu da uwarta ta
dinga yi min na cutarwa cigaba kawai zatayi kuma gashi nan ta fara. Shekararta
kusan ashirin Baffa, ko ni na haifeta ta kai yanzu ba lallai tayi yanda nake so ba
balle ta riga ta shirya cewa ni makiyarta ce. Ba wai ina tsoron abinda zata yi min
bane amma ina tsoron kada ta kureni nima nace zan rama tunda yara da yawa da matan
uba suke cutarwa wasu ai da akwai irin hakan a ciki don dai kawai ba za a sauraresu
bane.’
Sukayi shiru gaba daya kowa da abinda yake tunani. Har Baffa ya bude baki zai yi
magana Hajiya ta riga shi
'Eh da wannan. To amma fa kin ji bayaninta, kuma duk muna nan yarinyar nan ta
kwashe fiye da shekara tana zaman kan nata babu miji wanda kowa ya san sihiri ne
shiru kawai mukayi don a zauna lafiya. Sanna kuma ga furucin yarinyar nan wanda ana
halin zaman makokin uwarta tayi. Kuma tabbas yaron da aka bawa sabulu ya dinga zuba
maka a abinci don kaci idan ka bata masa rai wataran zai saka maka guba kaci ka
mutu don ya huta.
‘Kin gani ko Anti Uwani! Babu wanda ya damu da rayuwata kowa kawai na yiwa miji
biyayya na rike masa yara. Yarinyar nan ba zata canza ba wallahi saboda kamar
karatu uwarta ta dinga biya mata kiyayyata, duk wata tsawatarwa ba zata yi mata
amfani ba. A karshe kuma duk abinda ya faru da ubanta da duk masu kallo cewa za ayi
nice da laifi in cutar marayu. Ba zan iya rayuwa cikin kunci ba.’
Haka Anti Uwani ta dauki lokaci tana bata hakuri tana jaddada mata ta cigaba da
addu'a komai zai tafi dai-dai.
Gaba daya wunin ranar Hajiya da Anti Uwani basu kula juna ba saboda sun kasa
fahimtar juna; ita Anti Uwani tana goyon bayan lallai tunda Aisha tace ba zata
zauna da Yusra ba ya kamata a kyaleta tunda har ta fadi wannan matsalar don ita ta
san irin wadannan mutanen basa canzawa. Yayinda ita kuma Hajiya take ganin haka
akeyi don haka itama Aishan hakuri zatayi taje ta zauna.
….
Hajiya da su Farha suna zaune a falo lokacin wajen karfe tara saura aka kwankwasa
kofar. Abdallah ne ya fita don ya duba, nan da nan ya dawo ya sanar da Hajiya Abban
su Yusra ne. Ta bashi umarni yaje ya bude kofa ya shigo da shi falon. Kafin su
shigo ita da Farha sun tattara kwanukansu Hajiya ta yafa mayafinta. Cikin girmamawa
suka gaisa da Hajiya inda ta sanar dashi sakon Baffa, ya tabbatar mata da cewa da
ya fita zai kirawo Abubakar ya sanar da shi gobe da safe sai su hadu a gidan
Baffan. Tayi masa sallama ta shige daki bayan ta sanar da Aishan ta fito yana
jiranta a falo.
Sai da ta gama gunguninta sannan Anti Uwani ta korota daga dakin ta fito. Nesa da
shi ta zauna akan kujerar zaman mutum daya ba tare da ta ce masa komai ba kuma ba
tare da ta kalleshi ba. Shine ya gaji da shirun yace
‘Saboda na san bai kamata nayi zaman kaina ba shi yasa na taho don su shiga
maganar.’
'To ai idan dai Yusra ce kin san ba zan barta ta raina ki ba, kuma Yusra ma ai
macece kamar ke ko yanzu Allah ya fito mata da miji aure za ayi mata itama ta tafi
gidanta. Kinga ai an rabu lafiya ko?’
'Uhm! Ai zan koma, idan kuka gama magana da Baffa in sha Allah zan koma.’
Bai san me zai ce mata ba gashi dare yana kara yi, amma dai tunda tace zata koma
idan sun gama magana da Baffa kuma baya jin zasu kasa fahimtar juna da Baffa, don
haka yayi mata sallama ya tafi. Tun kafin ya isa gida ya kirawo Yaya Abubakar ya
sanar da shi gobe zaizo, suka tsayar da lokaci a kan karfe sha daya da rabi su hadu
a gidan Baffan. Sai da ya sanar da Yaya Bello domin tare zasu je gidan Baffan
sannan ya karasa gidan.
__
Kamar kullum haka ya tashi ya tsaya a kan yaran har suka tafi tahfiz, ya zama gidan
daga Saddiku sai Yusra da Jummai wanda take aiyukanta. Da yake lokacin karfe takwas
ne da safe sai kawai ya koma daki ya dauki computer dinsa ya fara aiki.
Wajen karfe tara saura yana nan yana aikinsa Saddiku ya shigo da sallama, bayan ya
amsa sallamarsa ya nuna masa gefen gadon ya zauna. Ya mika masa kudi yace
'Abba ga wannan, dubu goma sha biyu ne yanzu Anti Jamila kawar Mommy ta kawo. Tace
wai cikon kudin Mommy ne na leshi.’
'Leshi? Tun yaushe sukayi cinikin don na ga Mommyn ta dade fa bata sayar da kaya
ba?’
'Ai inaga Abba kudin nan fa ya fi shekara don Mommy din da kanta ta dade tana mitar
bata cika mata kudinta ba.’
Ya tabe baki
'Abba ina ga fa a duba wayarta musamman ta Whatsapp za a sami ragowar wadanda take
bi bashi, kuma ita din ma babu mamaki wasu kawayena nata suna binta bashi.’
'Hakane. Ka san tun ranar da ta rasu da na karbi wayar na ajiye gaba daya na manta
ma ban sake bi ta kanta ba. Bari yanzu ma sai na fara dubawa in sha Allah zuwa
yamma sai a tattara wadanda take bi da wadanda suke binta. Akwai ma kawarta Amina
ina jin itama za a samu wasu bayanan a wajenta.’
Ya mike ya matsa gaban durowarsa wadda yake ajiye litattafai a kai yayinda Saddiku
ya fice daga dakin don dama wanka zai shiga a lokacin da Jamilan ta shigo kawo
kudin.
Ya san inda ya ajiye wayar don haka ba tare da bata lokaci ba ya dauko ya kunna
sannan ya dawo ya zauna a gefen gadon.
Chajin wayar bashi da yawa sosai amma dai yana ganin zai isheshi ya duba abinda
yake son dubawa. Ya kunna data dinta ya ajiye wayar don sabbin sakonninta su gama
shigowa. Bayan kamar minti biyar ya dauki wayar ya budo Whatsapp ya fara bin
sakonnin da bata buda ba wadanda yawancinsu ma bayan ta rasu aka turo su. Duk
sakonnin sunayen mata ne don haka duk wanda ya bude ya duba sakonnin karshe yaga
hirarrakinsu ne sai ya mayar ya rufe. Wasu sakonnin kuma na groups ne don haka su
tsallakesu ma ya dinga yi.
Aminoni aka saka a kan sunanta kuma yana gani ya san Amina ce don ya san Zahra tana
kiranta da hakan. Ya bude sakon; maganarsu ta karshe hoton rasit me wanda Zahran ta
turawa account din Amina kudi kusan dubu dari uku da sako a kasan hoton an rubuta
‘na turo kawata'.
Mamaki ya kama shi; to kudin menene wannan da Zahran ta turawa Amina har dubu dari
biyu da saba'in? Ya duba sakon da yake samanshi wanda voice note ne da Zahran ta
turawa Amina, ya bude ya fara sauraro kamar haka:
'Kawata na kasa hada 300k din nan amma gaskiya gara muje haka, zan turo miki abinda
na hada. Na gaji da yarinyar nan wallahi, so nake duk ma yanda za ayi a datse
wannan auren. Shi kanshi Abban na su so nake ya dawo hannuna kamar da don yanzu
baki ga wulakancin da yake min ba.’
Ya sake shiga mamaki da damuwa a lokaci guda, ya cigaba da bin sakonnin yana budewa
har dai ya fahimci cewa magana sukeyi a kan Zahra tana so a kashe aurensa da Aisha.
Tafiya kawai yake yana bude sakonnin yana saurara yana yin sama. Har ya zo kan wani
sakon yana budewa ya fara saurara kamar haka:
‘Kawata sai kiranki nake baki daga ba, wallahi aiki ya karye don yau ya tuna da
matarsa, kin ganshi can yana ta rawar jiki ya tafi wai a can zai kwana. Ki kirani
don Allah mu san abun yi.’
Kwanan watan ranar da ta tura wannan sakon ya kalla ya tabbatar lallai ranar da ya
koma gidan Aisha ne bayan ya dauki dogon lokaci bai je ba. Duk wani haufi da yake
dashi a kan cewa Zahra tsafi tayi masa ya manta da Aisha yanzu ya kau, kuma ya
tabbatar warin da ya dinga ji a gidan Aishan ma itace.
Ya fada a fili yayinda ya share gumin da ya karyo masa; yana da wannan zargin a kan
Zahra amma ya so ace abun ya tsaya a zargi sai dai ya makara. To me yayiwa Zahra
haka har ta dinga kokarin cutar da shi da matarsa, ta sayar da imanin ta. Gashi
sakonnin sun nuna har ta mutu tana da niyyar ta je ta sake yi masa wani tsafin. Ya
fita daga sakon Aminan ya sake biyowa sakonnin da bai bude ba wadanda yawanci na
group ne.
'Yaron Malam.'
Ya fada a fili a daidai lokacin da yazo kan sakonnin. To wanene kuma Yaron Mallam?
Bai taba jin sunan ba balle yace ko a dangin Zahran ne, to wanene shi? Ya bude
sakonnin wadanda sun kai kamar guda goma, na karshensu bayan kwana biyu da
rasuwarta ne aka turo. Duka voice note ne don haka ya bude na karshen ya saurara
kamar haka
“Hajiya Zara ina ta kiranki kwana biyu shiru. Na dawo daga tafiyar da nayi kuma na
sami sa a. Don yanzu haka na shirya wani aiki da zan yi miki wannan abokiyar zaman
naki sai ta bar miki gidan nan idan ba haka ba kuma zata hadu da jinya wadda ba
zata warkeba; kin san kuwa namiji baya son doguwar jinya dole ya mayar da ita
gidansu. Kuma shi din ma za a saka miki shi a kwalba. Sai dai kawai nace ki taho da
kudi don gaskiya aikin mai tsada ne.”
Ya fada a fili yayinda ya mike kamar wanda aka tsikara; lallai Zahra ta tabbata
azzaluma! To kashe Aishan take son yi kenan!
'Shigo.'
Saddiku ne ya bude ya shigo ya dubi Abban da alamar tambaya a fuskarsa sai kuma
yace
'Subhanallah! Ka ga na manta tun last week suka sanar min zasu zo yau din. Gani nan
zuwa.’
Ya koma ya zauna a gefen gadon ya dafe kai; gaba daya ya manta tun wancan satin
Murja ta kirawoshi ta sanara da shi zasu zo ranar Lahadi su bude dakin Zahra su
kwashe kayanta na sawa. Ya amsa musu don shima yana so su kwashe kayan, don shi ya
ce har gadon Yaya Murja ta kwashe su sa a kasuwa sai su kawo kudin a rabawa yara
shi ya yafe; fenti yake son yiwa gidan gaba daya kafin Aisha ta shiga dakin.
Ya kashe wayar cike da damuwa ya ajiyeta a kan durowar gefen gado ya matsa gaban
wardrobe ya goge fuskarsa da tawul ya fice daga dakin. A falon kasa ya samesu inda
ya zauna suka gaisa, Yusra da Saddiku wadanda basu je makaranta ba suna zaune suma.
Bayan sun gaisa ya dubi Saddiku yace
'Ka bude mana dakin Mommynka Saddiku, za a duba kayan ne a kwashe masu amfani a
sayar a raba gado kamar yanda Allah ya ce.’
Ba tare da ya amsa ba ya mike ya haye sama tunda mukullin dakin nata yana dakin
Abban inda Saddikun ya ajiye. Abban ya mike tsaye yana yiwa su Yaya Murja iso zuwa
saman. Suna mikewa wayarsa da take aljihunsa ta fara kara, ya ja baya yayi musu iso
su wuce saman inda suka wuce Yusra tana biye da su. Ya lalubo wayar ya amsa da
saurin tana daf da tsinkewa ganin cewa Yaya Bello ne.
'Ina ka tsaya ne? Kace zamu je wajen iyayen Aisha sha daya da rabi gashi sha daya
da rabin har ta yi baka zo ba balle mu tafi.’
'Wallahi Yaya, idan na zo dai zaka ji. Bari na kirawo Abubakar din.’
Yana ajiye wayar ya kirawo Abubakar ya sanar dashi suyi masa uzuri zasu zo da
Magriba, nan ya sanar dashi dama an yi rasuwa Baffa yana son yaje jana'iza don haka
suka bari sa hadu da magriba.
Yana ajiye wayar ya mayar da ita aljihunsa ya haye saman, yana isa falon saman kuma
ya tsaya ya jona wayar tasa a chaji sanna ya shige dakin Zahran.
Yana shiga ya tarar da su sun fito da kayanta na sawa suna ta lodawa a akwati, ga
wasu kuma a gefe wadanda sababbi ne sai kuma manyan leshinanta wadanda Yaya Murja
take ganin a bawa yara su dinka. Nan da nan Yusra da Saddiku suka taya su suka lode
kayan a akwatuna, wadanda akwatunan basu dauka ba aka waresu gefe zuwa lokacin da
za a sami mazubi a san yanda za ayi da su.
Dan akwatin sarkokinta an dauko shi inda Yaya Murja ta ware na good ta mikawa Abban
tace
Ba tare da ya duba ba ya karbi dan akwatin ya bawa Saddiku ya kai masa daki.
Wani akwatin ya hango a saman wardrobe na agogo, ya mika hannu ya dauko. Yana
daukowa yaji wani abu ya fada bayan wardrobe din. Ya zauna a gefen gadon ya bude
akwatin; agogunata ne a ciki da sarkokinta na fashion. Ya mayar ya rufe ya mikawa
Suwaiba yana fadin
A nan Yaya Murja ta sanar da shi ta sami mai sayen gadon amma nan zai zo ya gani
ayi ciniki idan ya biya sai ya dauka. Ya dubi Saddiku wanda yake kwashe tarkacen
kayan shafawa da kwalliyarta a kwali yace
'Bar wannan in suka duba sa kwashe zo ka kama min wardrobe din nan mu matsar a
dauko abinda ya fada tunda an kwashe kayan ciki gaba daya. Idan muka dauko sai mu
kwance gadon don mai sayen ko bana nan idan suka zo sai kawai ya duba suyi magana
da Antinka.
Suka kama wardrobe din da kyar suka dan matsar da shi gaba, Abban yace Saddiku ya
shiga bayan ya dauko duk abubuwan da suka fada. Nan ya shige ya dinga kwaso
tarkacen; wasu warin dankunnaye, agogo guda daya wanda shine ya fada lokacin da
Abban ya dauko akwatin da irin lallen nan rani wanda ya ma riga ya bushe. Ya zo
fitowa daga bayan ya taka kwalbar fiya-fiya, ya tsuguna ya dauka yana gogewa. Abban
ya mika hannu ya karba yana cewa
Saddikun ya amsa
Ya karasa goge kwalbar yana dubawa; wani dan abu ne a ciki kamar busasshiyar fata
da allurai guda biyu a jiki sai kuma wani guntun farin tsumma ko takarda bai gane
ba. Abun yayi masa kama da tsafi sannan kuma ya tuna masa abun da aka cire a gidan
Aisha lokacin da ana shuka bishiya, don shima allurai ne a jikin abun. Ya tuna
wancan warin don haka yaji tsoron bude kwalbar fiya-fiyan ya jefe a aljihunsa da
niyyar sai ya kaiwa liman ko Malam Sama'ila sai a bude.
Yaya Murja tana kallonshi ta dauke kai, duk da bata fahimci menene abun ba amma dai
ta ga kamar abun ya karawa Abban damuwa. Suka cigaba da tattara kayan suna
duddubawa.
Abba da Saddiku suka kama katifar suka jingine bayan Yusra ta cire zanin gadon. Nan
da nan suka kama kwance gadon. Katako ne mai nauyin gaske don haka da kyar suke
kamawa suna jinginewa. Kan gadon yafi komai nauyi don haka sai da Suwaiba ta sa
hannu ta bangaren Saddiku sannan suka cicciba suka jingine. Ta juyo ta dauki wata
bakar robar da ta gani a bayan gadon, kafin ace wani abu ta bude tana mamaki don
babu ko rubutuba jiki balle tace mai ne.
Tana budewa wani farin hayaki ya fito daga cikin robar ya kanannade yayi sama;
Saddiku, Abba da Murja da Yusra duk suna tsaye suna kallo. Suka zaro ido kowa ya ja
baya yayinda Suwaiban itama ta saki robara kasa ta ja baya tana fadin
'Wayyo Allah!’
Haka hayakin da ya fita daga robar ya nannade yayi sama suna kallo ya bace, suka yi
cirko-cirko. Abban ya karasa ya daga robar a kasan ba tare da ya dauka ba. Wani abu
ne a ciki kamar kwan agwagwa sai dai shi akwai rubutu a jiki. Suka dan matso suka
zubawa abun ido. Abban ya fara karanto ayatul kursiyyu a fili ya tofawa wannan
robar sannan ya ci gaba da jan ‘la haula wa la kuwwata illa billah’; yasa hannu ya
zaro kwan a hankali. Babu nauyi kwata kwata, yana dubawa ya ga kwan ya tsage kuma
babu komai a ciki; kamar bawon kwan ne kawai. Ya juya yana karanta rubutun da yake
jikin bawon kwan; sunansa ne da sunan mahaifinsa da na mahaifiyarsu aka rubuta da
jan rubutu. Sai kuma aka rubuta sunan Aisha da na iyayenta da bakin rubutu kuma aka
sokeshi da jan rubutu.
Cikin sanyin murya Saddiku yayi tambayar da kowa yake son yi ya kasa
Su Murja da Zahra duk sun kasa magana sai kallon-kallo kawai sukeyi suna zare
idanu. Ba jimawa Saddiku ya dawo ya mikawa Abban wayar yana cewa
Yana karbar wayar ya kawar da missed calls din Yaya Bello ya lalubo lambar Malam
Liman ya kirawo. Aka yi sa'a yana kusa don haka ba tare da bata lokaci ba ya ce
gashi nan zuwa.
Daga su Murja har su Zahra duk jikinsu yayi sanyi don haka gaba daya suka hakura da
aikin suka fara diban kayan da zasu fito da su suna fitowa dasu falon.
Kafin su gama Malam Liman ya bugo wayar Abba ya sanar dashi yana kasa, ya umarci
Saddiku da ya shigo da shi. Ya sauko daga saman da sauri.
Yana zuwa bakin kofar falon kasan ya ci karo da Yaya Bello yana sallama a bakin
kofar. Bayan ya amsa gaisuwarta yace
'Saddiku Ina Abban naka ne? Lafiya dai kuke gaba daya? Ina kannenka? Ina ta kiran
wayar Abban baya dagawa.’
‘Yana nan, aiki mukeyi a dakin Mommy. Malam Liman ne yake jiransa a waje yace na
shigo da shi, bari na kirawoshi sai nazo na kirawo Abban.'
Jummai ta fito daga kicin da taji motsin Yaya Bellon, bayan ta gaisheshi tace
'Suna sama ma shi da su Hajiya Murja ne, bari na kawo maka ruwa.’
Tana shigewa Saddiku suka shigo tare Malam Liman, bayan sun gaisa da Yaya Bellon
Saddiku yace
'To bismillah.'
Ya bi bayansa.
Ya mike gabobinsa babu kwari don ya zata wata lalura ce ta sami Abban wadda tasa ba
zai iya saukowa ba zai ce a zo da mutum.
Cirko-cirko suka tarar da su Abban a daki babu mai magana, yana ganin yayansa yace
Suka karasa ciki suka gaggaisa a tsattsaye. Abban ya nunawa Malam Liman robar wadda
take ajiye a kasa da kuma kwan a kan murfin yayi masa bayani sannan kuma ya mika
masa kwalbar fiya-fiya da ya jefe a aljihu. Suka tsuguna gaba daya Abban yana sake
yi musu bayanin hayakin da ya fita daga cikin robar Liman yana dubawa.
'To ka san idan mutum ya mutu duk wata tashin-tashina barinta ake yi. Yanzu a nan
waye bare wanda ba dan uwan ita marigayiya ba? Don ka ga idan da wanda ba zai rike
mata sirri ba sai ya fita.’
'Wadannan dai yaranta ne ka san su, wannan yayana ne shi kadai gareni dan uwa,
wadannan kuma yayarta ce da kanwarta uwa daya uba daya.’
Liman yace
'Ai ba ma sai ka fita ba ina ga duk nan amintattune, sai dai kawai zan bamu shawara
duk abinda muka ji muka gani mu barshi a nan mu cigaba da yi mata addu'a.’
'Gaskiya wadannan abubuwan guda biyu da ka bani tsafi ne ko sihiri, hayakin da kuka
ga ya fita ba zan yi mamaki ba idan aka ce aljani ne to amma ba zan sani ba tunda
ban gani ba. Ko ma menene ya fitan bana jin zai tsaya nan kusa tunda kamar ya sami
‘yanci ne.’
'Ka ga wannan gutsure na na rigar wanda aka yiwa sihirin gashi nan. Sai a tattara
wadannan tarkacen a kona sannan a binnesu tare da zancen, wadanda suka rigamu gidan
gaskiya Allah ya yafe musu.’
Sukayi dif kamar ruwa ya cinyesu kowa da abinda yake tunani. Sai da Malam Liman ya
gaji da shirun yace
'Kai Saddiku sai ka kwashi wannan ka kona ka binne shike nan a cigaba da addu'a.’
Abba yace
'Babu wata matsala. Ai na riga na tofesu da ayoyin Allah kuma tunda me shi ta rasu
ba zai yi tasiri ba. In ya so dai yara su karanta suratul bakara a gidan don a sami
natsuwa gaba daya.’
Yayi musu sallama Abba da Yaya Bello suka bi bayansa don yi masa rakiya.
'Uhm! Ina ga sai mu tafi, ragowar kayan ma dawo. Ko kuma bari Abban ya dawo sai na
tsaya mu kona wannan tarkace.’
Suwaiba tace
‘Allah ya kyauta.’
Suka fara hada kayansu don tafiya; gaba dayansu kowa zuciyarsa a jagule har Yusra
wadda ta kasa magana. Nan falon saman suka zauna suna jiran Abban. Tunani kala-kala
ne yake yawo a ran Yaya Murja; to yaushe Zahra ta fara tsafi? Ga shi ta mutu? Kuma
ga dukkan alamu Abban take yiwa wanda gashi yanzu ya gani.
Haka suka zauna har Abban ya dawo saman suka yi masa sallama cike da jin nauyin
abinda ‘yar uwarsu ta aikata suka fice cike da tsananin damuwa da mamaki. Godiya
daya suke yiwa Allah da Liman yace kada a fita da zancen don haka ma suka fice ba
tare da sun cewa Abban komai ba a kan zance.
Suna tafiya Abban ya koma dakin ya rufo kofa yayin da Yusra da Saddiku suka shige
dakinsu.
UWAR SADDIKU
Written by
Sakina Yazid
(Innar su Amal)
45
Su Yaya Murja suna fita daga gidan suka wuce gidanta don dama a nan zasu ajiye
kayan da suka kwaso kafin su san abinda zasuyi da su. A dakinta suka zube a gajiye
cike da damuwa. Kowa ya kasa magana saboda damuwa.
Jimawa kadan Suwaiba ta dubi Murja ta kirawo sunanta, sai dai kafin ta fadi abinda
take son fada hawayen da take tarewa ya kwace. Itama Murjan ta kama share kwalla,
sai da sukayi mai isarsu sannan Suwaiban ta goge fuska tace
'Yaya kin ga yanzu dole mu bar maganar Abban Saddiku ya auri Rahma, tunda na san mu
kanmu kallonmu kawai yake yi. Wannan abun da Yaya Zahra tayi ai dole ya zata duka
haka danginmu suke. Aishan kuma da muke kokarin mu kare yara daga fitnarta kinga
ashe ba itace mai fitnar ba.’
'Hmm! Suwaiba ai dole a bar wannan maganar tunda jiyan nan dama na yiwa Rahman
maganar itama ta sakawa idonta toka tace ba zata aureshi ba kada ma mu soma
maganar. Watakila ko ita ta san da wadannan abubuwan da Zahran take yi shi yasa
taki shiga gidan.’
'Babu mamaki, amma dai ina mamakin yanda akayi Zahra ta zama haka. Kullum fa nusar
da ita nakeyi yanzu dubi abubuwan da muka gani, da wanne ido zaka fuskanci ubangiji
ka yi wannan aika-aikar?’
Nan suka dauki lokaci suna jimami da jajantawa, sai da aka fara kiran azahar sannan
Suwaiba tayiwa Murja sallama ta tafi.
……..
Tunda Abba ya shiga dakin ya rufo kofa ya zauna a gefen gado ya zuba fuskarsa a
tafukan hannunsa cikin damuwa. Tunani sun yiwa kwakwalwarsa yawa don haka bai ma
san me yake tunani ba.
'Zahra.'
To shi kuwa me yayi wa Zahra zata cutar da shi da Aisha? Me yayi zafi har ta barar
da imaninta? To tun yaushe take wadannan abubuwan?
Ya fada a fili yana goge fuska. So yake ma ya fitar da hawaye ko zai ji sanyi a
ransa amma ko digon hawaye idonsa ya kasa fitarwa.
Lallai wadannan sune abubuwan da Aisha ta san ana yi mata har take jin ba zata
zauna da Yusra ba. Yanzu haka Yusran ake turawa tana binne mata irin wadannan
abubuwan shi ya sa tace ba zata zauna da ita ba; kuma bai ga laifinta ba a yanzu.
Domin ko shine ya san halin Zahra to da tuni ya dade da rabuwa da ita.
'Allah ka hana yarana bin wannan hanyar da uwarsu ta bi, Allah ka shiryesu ka hana
su shirka.’
Yanzu wannan dabi'ar Zahra ta dora Yusra a kai? Lallai yana da aiki.
Zahra bata yi masa adalci ba, ta cutar da shi.
A take nadama ta rufe shi, bai taba nadamar auren Zahra ba kamar yanda yakeyi
yanzu.
Haka ya wuni a dakin yana ta tufka da warwara shi kadai, don ko masallaci bai fito
ya je ba balle ya nemi abinci.
Itama Yusra haka ta wuni, sai dai ita damuwarta ba me yawa bace. A iya tsawon
rayuwarta ta san kullum Mommy tana tsaye a kan nema musu kariya, wannan abubuwan da
aka samu a dakin Mommy din ta san suna cikin wannan kariyar wanda Mommy din ta
sanar da ita duk addu'oi ne don haka ita bata ma ga wani abun tashin hankali a ciki
ba. Fatan ta daya Allah ya sa kada wata cutarwar ta samesu saboda wadannan abubuwan
da aka kona.
—-----
Yana dakin har bayan karfe uku, sai wajen la'asar yunwa ta dameshi. Yana fitowa ya
hango abincinsa a kan dining table don haka ya zauna ya ci. Yanda yaji gidan shiru
ya san yaran sun tafi makaranta don haka yana gamawa ya sauko ya sami Jummai a
tsakar gida ya tambayeta in Saddiku, ta sanar da shi Saddikun yace mata ya fita
amma kafin magriba zai dawo. Yayi mata sallama ya fice ya nufi gidan Yaya Bello.
Ya san sai dare ya kamata suje gidan su Aisha, to amma zaman dakin ya isheshi. Gara
ya bi Yayan gidan su tattauna ko ya samu zuciyarsa tayi sanyi.
Tun a farkon layin ya hangi Yaya Bello yana tsaye da ‘yan unguwa, yana wucewa shima
Yayan yayi musu sallama yabi bayansa.
Yana yin parking Yayan ya karaso suka hadu, bayan sun gaisa suka wuce cikin gidan.
Yaran da Ummansu duka basa nan sun tafi biki sai Muhammad kadai, bayan ya kawowa
Abban ruwa ya koma dakinsa.
Sukayi shiru na dan lokaci, jimawa kadan Abban ya ajiye kofin ruwan da yake
hannunsa yace
'Na kasa nutsuwa Yaya, ace ina zaune da mace shekaru masu yawa kowa yana kyautata
mata zato ashe matsafiya ce ban sani ba?’
'Gaskiya dai nima har yanzu ina mamaki; don ka ga da ace a lokacin tana raye an ce
ka zabi daya ko ita ko Aisha to tabbas na san da mu da duk wani danginka zamu ce ka
rabu da Aisha ka dauki Zahra, ashe itace bara-gurbin.’
Ya jijjiga kai
'Yanzu Yaya ya zan yi da Aisha? Wallahi ina sonta kuma bana jin a yanzu a shekaru
na zan iya wani kara aure. Kuma a halin yanzu Aishan ita kadai ce na yarda zata
rike min yaran nan amana. Kuma…’
'Uhm! Abinda ka gani game da Zahra ai ya isa ya tabbatar maka dan Adam bashi da
tabbas ko?’
'Da wannan Yaya, amma ka san dan Adam kowanne da dabi'arsa fa. Wallahi a zaman da
nayi da su da ace Aisha ce ta rasu ta bar min yara ba zan iya bawa Zahra rikonsu ba
don na san ba zata rike min amanarsu ba. Amma ka ga Aisha, bata da matsala. In dai
ta amsa tace zata yi abu to tabbas zata yi kuma cikin aminci. Matsalarta daya
kafiya da taurin kai, gashi ita ko dan wayon nan da ake yiwa mata a lallabasu idan
dai bata son abu to baka isa kayi mata wayo a kansa ba idan kuma tana son abu to
tana da kafiya a kansa.’
'Wallahi Yaya ban sani ba, da ma za su dan kara mana lokaci na samu nayi tunani
sosai. Ka ga fa ga dukkan alamu irin kulle-kullen da muka samu a dakin Zahra irinsu
ake aika Yusran tana binnewa Aisha, kuma ai ka ga da cutarwa sosai.’
Nan ya bashi labarin yanda ya kusan shekara baya iya shiga gidan Aishan saboda wari
da yanda aka hako abun warin a gidan Aishan, har ya gangaro kan sakonnin da yaji a
wayar Zahran wadanda suke nuna cewa tana da hannu wajen barin cikin da Aishan ta yi
har sau biyu. Cikin mamaki Yaya Bellon yace
'Ikon Allah! Lallai matar nan ta dade tana cutar da kanta, don tabbas wannan kanta
ta cutar.’
'To idan muka je wajen Baffan nata kawai ka amince musu a kan za ka dauke Yusra da
Nana. In ya so ko nan wajena sai ka dawo min dasu daga baya sai ka sa Yusran a gaba
ta bata hakuri. Kuma ko ma bata karbe su ba nan din sai muyi zamanmu in ya so ka
barta da wadanda ta zaba.’
'Yaya ni bani da damuwa idan yarana suna wajenka na san lafiya za a rike min su,
amma zan so ace suna cikin gidan a tare gaba daya.’
'To ya za ayi, kaga dai yanzu wadannan abubuwan da muka gani ya tabbatar maka da
abinda Aishan take tsoro. Kaga ita kanta Yusran tana bukatar a tsawatar mata a
sauketa daga kan waccan tarbiyyar da uwarta ta dorata a kai. Ka bari ayi hakan,
idan aka kwana biyu sai a lallabi Aishan mu ga abinda hali zai yi.’
Kai kawai ya dagawa Yayan don shima bai hango wata mafita ba bayan wannan.
'Kuma idan ka koma gidan ka tara yaran gaba daya ka sanar da su cewa Aishan zata
dawo gidan, ita kuma Yusra ka sanar da ita zata dawo nan saboda tana yiwa Aishan
rashin kunya. Amma idan ta fi son zama a can din to ta nemi Aishan ko a wayane ta
bata hakuri.’
Nan suka zauna suka cigaba da hirarrakinsu, sai gefin magriba ya yiwa Yayan sallama
ya nufi gidan don ya shirya ya dawo su tafi wajen Baffan Aisha.
__
Lokacin da Yaya Abubakar ya sanar da su an fasa haduwa da su Abban Sadik sai da
magriba Aishan da Anti Uwani har sun shirya don tafiya gidan Baffan. Da suka ji
haka sai suka fasa shirin suka bari sai bayan la'asar sa je.
Can wajen azahar Zahida ta shigo gidan da yaranta. Bayan sun gaisa da Hajiya ta
dawo falo inda ta zauna wajen Aisha. Kafin su gaisa ta zaro sabuwar waya a kwalinta
ta mika mata tana fadin
'Ga wayarki inji Abban Afra, yace rasit din yana ciki kuma kina da canjin dubu daya
da dari biyar don an dan sami ragi.’
'Kai shima don Allah harda wani canji. Wallahi kamar kin san jiya saura kadan na
fasa wayar nan don takaici, ko awa nawa zata yi tana caji da ka cire daga socket
zata dawo babu caji, lallabata kawai nakeyi.’
Nan suka bude wayar suka kunna da yake ya riga yayi mata caji suka cigaba da
dubawa. Jimawa kadan suka koma kusa da socket Aishan ta saka tsohuwar wayar tata
tana duba abubuwan da suke ciki don Zahidan zata bawa ta kaiwa Abban Afra a sayar
mata da ita. Ta tura hotunanta da videos wadanda take so zuwa sabuwar wayar, tana
ta dube-dube tazo kan recording wanda wayar takeyi idan tana waya. Ta dubi Zahida
tace
'Kinga yau naga inda wayar nan take tara min hira. Kin san nace miki kullum na gama
waya sai naga an saka min recording saved amma ban san a ina ake saving ba.’
Suka fara budewa suna sauraro, wasu suna dariya don yawanci hirarrakinsu ne su
biyun.
Recordings din suna da yawa sosai don haka suka dinga tsallake wasu suna bude wanda
suke son ji. A hankali ta zo kan wani recording guda daya da lambar Zahra, tayi
murmushi yake tace
'Ga na mutuniyarki.’
Tayi mamakin ganin recording din don a zamansu bata jin sun yi waya da Zahra ya kai
sau biyar. Ta danna ta kunna suka fara sauraro kamar haka:
“‘Dama Abban Sadik ne bai shigo ba kuma na kirawo wayarsa bata shiga shine nace ko
lafiya.’
‘Lafiya kalau, yayi bacci.’
‘Um, t….’
‘Kema ina baki shawara kije kiyi baccinki, idan dai mijinane Yusuf uban Sadiku to
bazaki sake jin duriyarsa ba. Ya manta dake ya goge babinki a rayuwarsa, ko da me
kike takama kuma ya fi karfinki, duk lokacin da kika gaji sai ki tattara kayanaki
ki koma gidanku. Kuma don Allah kada ki sake kirana a irin wannan daren muna kwance
da mijina.’”
Zahida tace
Aishan tace
'Uhm.'
'Kada ki goge tura a sabuwar wayar, kin san fa in an jima muka je su Baffa kokari
zasuyi ki koma ki zauna da wannan muguwar yarinyar tata. Wannan zai iya zame miki
hujja tunda duk abubuwan da tayi miki abubuwa ne da babu wanda ya gani.’
'Hakane.'
Sai can wajen karfe shida saura suka shirya ita da Zahida da Anti Uwani suka nufi
gidan Baffan.
__
Dawowar su Rukayya kenan daga islamiyya don ko uniform basu gama cirewa ba.
Bayan ya amsa sannu da zuwan su ya nufi saman, har ya kusa shigewa sai kuma ya ga
gara yayi magana da yaran ko zai fuskanci wani abu kafin suje wajen Baffan Aishan.
Ya juyo ya dawo falon kasan, ya kwalawa Yusra kira, bayan ta fito daga dakin yace
Ba tare da bata lokaci ba suka fito gaba dayansu suka sameshi a falon ya a zaune.
Kowa ya nemi waje ya zauna yayinda Sumayya ta wuce ta zauna a jikin Abban. Ya kare
musu kallo sannan yayi gyaran murya yace
'Allah shine me rayuwa, dukanmu muna cikin bukatar Mommy Allah ya dauki ranta.
Hakuri kawai zamu yi sannan kuma mu cigaba da yi mata addu'a. Zuwa next week in sha
Allah za a fara aiki a gyara gidan gaba daya, idan aka gama Antinku zata dawo nan
mu zauna gaba daya.’
Idonsa yana kan Yusra yana lura da yanda take ta faman murgude baki tana kau da
kai. Ya dubeta yace
'Zata zauna ne ba don a sake muku uwa ba sai dai ita din ma uwarku ce don haka
akwai bukatar kuyi mata biyayya kuma ku bata hadin kai mu zauna lafiya. Sai dai ke
Yusra tace ke da Nana kuna yi mata rashin kunya sosai, me yasa.’
'Wallahi Abba tana yi mata rashin kunya sosai, ranar sadakar uku Mommy ma baka ga
yanda ta bangajeta ba kuma Anti Aishan bata ce mata komai ba.’
Idon Abban yana kanta tana hararar Saddikun. Yayi gyaran murya yace
'To ka ga kenan ba za a sami zaman lafiya a gidan ba tunda abun ya kai da bangaza
wataran za ta kamata da kokawa.’
Tace
'Itama da kanta ta gaya min abubuwan da kike yi mata kuma kin san dai ba zata yi
miki karya ba. Yanzu kina da kwana uku ki kirawota a waya ki bata hakuri ki sanar
da ita kin daina yi mata duk wani abu na raini, idan kin kirawota zata gaya min.
Kin ga shikenan sai muyi zamanmu lafiya babu wanda ya raina wani. Amma idan baki
kirawota ba to Babanki Bello yace sai dai ki koma gidansa don wajensa ne ta kai
kararki. Ki kirawota ki bata hakuri zata sanar da shi in ba haka ba gidansa zaki
koma komai za ayi miki kamar a nan. Tunda kinga ni ba zan iya saba maganar Yayana
ba don ban raina shi ba kamar yanda ke kika raina naki Yayan har kike murguda masa
baki a gabana.’
Ya tsallake su ya nufi daki yayinda su kuma suka nufi benen da nufin saukowa.
Har ya murda kofar dakin zai shiga sai kuma ya fasa ya dawo ya samesu a kafar bene
don haka duk abinda Yusra ta fada ya ji. Bai kula da ita ba yace
Bai taba sanin lalacewar Yusra ta kai haka ba, tun kafin ma aje ko ina ta sanar ba
zata bi umarninsa ba. Lallai gara ya barta taje gidan Yaya Bello don ya san ba zai
yi mata a hankali ba. Watakila idan ya cigaba da addu'a Allah ya sa ta canza hali.
Nan da nan ya shirya suka tafi masallaci tare da Saddikun, suna dawowa ya shirya ya
wuce gidan Yaya Bello.
……….
Tun a hanya ya sanar da Yaya Bellon yanda suka yi da Yusra, nan suka yanke maganar
cewa kawai Yusra da Nana su dawo gidan Yayan.
A falon Baffa suka zauna gaba daya; Aisha, Anti Uwani da Zahida suna gefe yayinda
Baffa da Ya Abubakar suke gefe sai Abban da Yaya Bello da suma suke gefe.
Tunda ya zauna yake kallon Aishan; tayi kyau tayi fes kamar bata da wata damuwa.
Yanda yaki ya dauke idonsa daga kallonta ya sa ta sunkuyar da kai. Yaya Bello ne ya
kula da halin da ake ciki ya tabo Abban.
'Yusufa me ya hadakane da amaryar taka har ta taho gida, duk da tace ba kaine kace
ta taho ba?’
'To tazo da wasu dalilai wadanda suka sa take jin ba zata iya zama da yarinyar ba,
amma gata nan sai tayi bayani a gabanka kaji.’
A nan Baffa ya bawa Aishan umarni tayi bayanin abubuwan da Yusran takeyi mata da ma
wasu abubuwan na cutarwa da Zahran ta dinga yi mata. Ta dora da
'Duk abinda za ayi kuma ita ake turowa ta shigo min da shi gida. Sannan kuma kullum
muka hadu da ita sai ta gaya min bakar magana don kawai ina kawar da kai ne.’
Baffa yace
'Wannan maganar zargi a barta tunda kinga malamai ma sun ce wasu abubuwan aljanu ke
son cutar da kai sai su nuna maka cewa wani ne daka sani.’
Tace
'Baffa wasu abubuwan idan tayi min da kanta take gaya min ko ta aiko Yusran ta gaya
min.’
Kafin suce wani abu ta zaro waya ta kunna recording din da suka tsinta dazu na
muryar Zahra. Kowa yayi kasake yana sauraro. Abba ya sunkuyar da kai zuciyarsa tana
kara kuntata, muguntar Zahra da jahilcinta har ya kai haka?
'To Alhamdulillah, hakan yayi. Allah ya shirya mana zuri'a da mu gaba daya.’
'Shatu ki dinga hakuri kin ji, yaro ko naka ne wanda ka haifa wani sai dai kayi
hakuri da shi a lallaba. Bana jin ki da yara sai dai mu raka ku da addu'a, tunda
gashi ita da take baki matsala bata nan don Allah sauran kuyi zamanku lafiya. Kuma
ku sani mutum yana barin mugun hali ya shiryu musamman wanda ake tsaye ana masa
addu'a don haka idan ta canza hali ita din ma duk ki hadasu ki rungume.’
Tace
'To Baffa.'
‘Akwai kuma yaran wajen Aishan su biyu idan babu damuwa sai ta taho da su duk su
hadu a nan suyi zamansu gaba daya.’
'Wadannan ma ba za ayi haka ba. 'yan uwan mahaifinsu suna so su karbesu tunda Farha
da take karama yanzu shekarunta sha biyu, suna ganin ya kamata a basu yaransu. Kuma
yaran sunyi na'ama don haka nan da wani dan lokaci zasu koma wajen kanin
mahaifinsu.’
'Tunda ya auri yarinyar yana kallon yaran bai taba cewa su zo su koma wajenta ba
sai yanzu da yake so ya bata rikon nashi yaran, ko kunya babu wai su koma can.
Hmmm!’
'Hajiya Uwani ayi mana afuwa dai, kin san wani lokacin son kan mu yana rufe mana
ido da yawa.’
………..
Tun da suka fito Aisha ta kasa walwala sosai. Bata ji dadin yanda taga Abban ba;
yayi wata rama gashi kamar ma bashi da lafiya. Ta ji haushin kanta da ta ki daukar
wayarsa har ya gaji ya daina kiranta. A take tausayinsa ya kamata duk da bata san
me yake damunsa ba. Bata da wata matsala da shi kuma zata koma kamar yanda ya fada,
musamman da yake ya amince zai dauke Yusra.
Haka suka koma gida tana cike da damuwar halin da ta ga Abban. Tana son ta
kirawoshi a waya to amma bata san me zata ce masa ba, don haka ta hakura ta kwanta
bacci.
Wajen karfe sha daya da rabi wayarta tayi kara, lokacin bacci ya fara daukanta.
Tayi firgigit ta farka ta dauki wayar tana dubawa, Abban Sadik ne yake kiranta don
haka ta tashi a hankali ta fice daga dakin saboda kada ta tashi Anti Uwani da Farha
daga bacci.
Ta amsa wayar ta kara a kunnenta dai-dai lokacin da ta karasa falon ta zauna a kan
kujera.
Yanayin yanda ya kirawo sunanta sai da tsigar jikinta ta tashi. Ta gaisheshi sannan
ta tambayeshi yaran, bayan ya gama amsa gaisuwar yace
Bata da amsar da zata bashi don haka tayi shiru. Sai da ya gaji da shirun sannan ya
cigaba
Sukayi shiru na dan lokaci jimawa kadan ya sake kiran sunanta, ta amsa murya kasa-
kasa. Yace
'Ba a gida ba gaskiya, please idan kin tashi daga makaranta ki zo office mana.’
Sukayi shiru na dan lokaci bata amsa ba, ya gaji da shirun ya sake maimaita mata
'Ki zo office kin ji Aisha.’
Tace
'Ok.'
Yace
'Tsabar damuwa ce kawai, mutum yana da mata biyu a wayi gari daya ta mutu dayar
kuma ta gudu ai kin ga dole na shiga damuwa ko?’
'Ni fa ba guduwa nayu ba.’
Yayi dariya. Suka dan taba hira sannan sukayi sallama ta koma ta kwanta.
—----
Washegari ranar litinin tun kafin yara su tafi makaranta ya sanar da su idan sun
dawo daga makaranta su hada kayansu zasu tafi gidan Yaya Bello sai an gama aiki a
nan sannan zasu dawo. Itama Jummai ya sanar da ita an bata Hutu, idan yaran sun
tafi gidan Yaya zata iya tafiya ta barwa Saddiku mukullin gidan idan an gama aiki
zai kirawota. Ya kawo kudi naira dubu ashirin ya bata yace ta yi wata hidimar, ya
fice ya barta tana godiya.
Tun kafin ya karasa office din ya kirawo Aisha don ya tabbatar bata fasa alkawarin
da ta yi masa ba akan zasu hadu a office, inda ta tabbatar masa zata zo da karfe
sha biyu da rabi.
………
A zaune yake a office din yana faman duba lokaci saboda yanda ya kagu yaga Aishan.
Sha biyu daidai ya ajiye aikin da yakeyi ya dan kifa kansa a kan tebur, ba tare da
bata lokaci ba bacci ya kwasheshi saboda yanda ya tara bacci da gajiya kwana biyu.
A haka ta shiga ta sameshi a office din, sai motsin shigarta ne ya tasheshi daga
baccin. Ya muttsike idonsa tare da mikewa tsaye yana murmushi, ya zagayo gaban
tebur din ya tsaya a gabanta yana dan tokarewa da tebur din. Ya kama hannuwanta
duka biyun yana murmushi, ta mayar masa da murmushin sannan tace
'Ni da wa?’
Ya saki hannunta ya mika hannu ya dauko mukullin motarsa da waya yana fadin
'Ban yarda ba. Kizo muje idan muka dawo sai ki wuce gidan.’
Ba ta son rakiyar sai dai taga kamar ko ma ina zai je ba dadewa zai yi ba, sannan
kuma ba zata iya yi masa musu ba saboda yanda tayi kewarsa kuma bata son ta bata
masa rai don ta kula yana tare da damuwa. Don haka ta amsa ya sakata a gaba suka
fito.
Suna fitowa daga office din yace ta bar motarta a nan idan sun dawo sai ta dauka,
don haka suka shiga motarsa suka wuce.
Yana tuki suna hira, nan da nan suka iso BON hotels, Kano. Ya shiga ciki yayi
parking yayinda take binsa da kallo mai cike da tambayoyi. Yayi murmushi yace
Ya fito yayinda itama ta fito ya rufe motar suka shiga hotel din.
Daga baya-baya ta tsaya don haka bata ji abinda yake fada ba a reception, ya gama
aka bashi wani kati ya juyo ya ja hannunta suka shige ciki.
Binsa kawai takeyi tana mamaki; to wanda zai gani kuma a daki zasu hadu?
Kafin ta gama tunanin sun tsaya a bakin kofar wani daki, nan da nan yayi amfani da
katin da ya karba a reception ya bude kofar dakin. Ya shige ciki yayinda ita kuma
ta dan noke, ya juyo ya jata ciki ya rufe kofar. Ta zazzare ido tana fadin
Yayi dariya
Ta marairaice tace
Ya dan kara matsawa daf da ita yanda yana jin dumin numfashinta, ya saki hannunta
daya ya dago habarta suka hada ido. Ta sunkuyar da idonta. Ya sumbaci lebenta
sannan ya kai bakinsa daidai kunnenta yace
Ta dan ji kunya don bata zata tsoron da take ji ya bayyana a fuskarta ba, yayi
murmushi yace
'Aisha na gaji ne da yawa kuma da zan iya samun hutu ni kadai da ba zaki ganni haka
ba har ki dinga tambayata ko bani da lafiya. 2 hours kawai zaki bani zaki ga na
warke. Ai zaki iya ko?’
Ba zata iya ce masa a'a ba saboda yanda yake mata maganar da salo na magiya da
lallashi, sannan kuma ita kanta tayi kewarsa kuma ga hakkinsa na aure a kanta wanda
ta san dole ta saukeshi. Don haka tayi murmushi ta daga masa kai alamar eh.
Ta gama kallon dakin sannan ta zauna a gefen gadon, ta zaro waya ta kirawo Anti
Uwani ta sanar da ita kada suga ta dade bata dawo ba sun fita da Abban Sadik. Kafin
ta ajiye wayar aka buga dakin aka ce room service ne. Ta mike ta bude kofar a
hankali, ma’aikatan hotel din su biyu suka turo dan teburin nan mai taya da abinci
kala-kala a kai suka ajiye mata suka fice. Abban yana fitowa itama ta shiga tayo
alwala. Sai da suka idar da sallah sanna suka zauna suka ci abincin suna ci suna
hira cike da walwala. Yanda yake cin abincin yasa ta dube shi da tausayi tace
Ya dubeta yace
'Hmm! Nayi breakfast. Kawai dai na dade rabon da na ci abinci a nutse kuma naci na
koshi shi yasa yunwa tayi min yawa. Yanzu kuwa inaa ci kina min hira ai dole na ci
na koshi.’
Tayi dariya.
Bayan sun gama cin abincin ta tashi ta wuce bandaki ta wanko hannu, tana tashi
shima ya bita. Suka wanko hannu a tare suka fito.
Suna fitowa ta nufi gefen gadon zata zauna, ya karaso kafin ta zauna ya sha
gabanta. Ya kama gefen laffayar da take jikinta wadda ta ki cirewa tunda suka shigo
yana fadin
'Ai sai ki cire wannan nadin ki huta tunda ba yanzu zamu tafi ba ko, nifa bacci ma
zan yi kuma dai ai kya tayani ko?’
Tana ji tana gani ya warware laffayar, yana ajiyeta a gefen gadon ya kare mata
kallo daga ita sai straight skirt na atamfa da kuma bakar riga irin fitted dinnan
mai kamar roba ta bi jikinta duk ta kwanta. Kamar a can kasan makoshinsa yace
'Nace ki daina fita da wannan fitnanniyar rigar fa, ai gara ma da hijab kika sa.’
Haka ta biye masa yayi yanda yake so, sai da ya dauki lokaci ya gamsu sannan ya
gyara kwanciya ya jata jikinsa ya rungumeta. Kafin tayi wani yunkuri bacci ya
kwasheshi, ta duba agogon wayarta sannan ta dan gyara kwanciya ta lumshe ido itama
bacci yayi gaba da ita.
Itace ta fara farkawa wajen karfe uku da da rabi, ta yunkura zata zare jikinta ya
riketa yana dariya
'Um.'
Ya rufe bakinta da nashi bakin yayinda ta fara kokarin ture shi, sai dai kafin ta
samu ta kwace ya ci karfinta haka ta sake biye masa.
Sai da hudu ta gota sannan suka tashi suka kintsa sukayi Sallah suka kamo hanya.
Suka koma office din sa don ta dauki motarta. Ya karbi mukullin motar ya bawa Malam
Sule yace ya kai mata gidansu suma zasu hadu a can, ita kuma yace ta zauna shi zai
kaita ya gaida Hajiya.
…………
Yana ajiye Aisha a gida magriba ta kusa don haka kai tsaye ya wuce gidan Yaya
Bello. A can ya tarar da su Yusra gaba dayansu don tun tuni Malam Ali ya kawosu.
'Ai kuwa ko ka ki ko ka so hakane. Inaga dai nima auren nan zan kara ko na danyi
kyan gani.’
Umman Muhammad da take jiyosu daga kitchen ta yiwo gyaran murya. Suka tuntsire da
dariya. Abba yace
'Ai ki barshi Umma babu wadda zata aureshi sai ke, daga ke sai shi har Aljanna.’
Ana yin kiran Magriba Abban yayi musu sallama suka wuce masallaci da Yayan inda
daga can yayi masa sallama ya koma gida.
Ranar Talata da safe ma'aikata suka zo, nan aka fito da kayan cikin gidan gaba daya
har kujerun Abba yace a fito da su a hada da gadon dakin Zahra a sayar a rabawa
magada kudin. Duk wasu gyare-gyare da zasu yi masa ya nuna musu, har kofa yasa ayi
masa daga dakinsa wadda kai tsaye zata kaishi dakin Aishan.
A gyara bandakuna da kitchen din gidan duka biyun sannan a sakewa gidan gaba daya
fenti. Nan da nan aka fara kwaso kayan ana fitowa da su tsakar gidan.
………
A zaune yake a office yana aikinsa, sai ya tuna ya kamata ya kirawo Amina don ya
tambayeta ko akwai wadanda suke bin Zahra bashi kuma yayi mata maganar kudin da
yaga Zahran ta tura mata.
Nan take ya ajiye biron da yake hannunsa ya janyo waya, ya lalubo lambar Aminan
wadda ya kwafa a wayar Zahra. Bugu daya ta dauki wayar tare da yin sallama; bayan
sun gaisa yayi mata bayanin kansa. Ta sake yi masa gaisuwa sannan ta tambayi yaran.
Ya tambayeta ko akwai wadanda suke bin Zahra bashi a kawayensu, ta tabbatar masa
babu wanda yake binta bashi. Sannan ya tambayeta bayanin kudin da Zahran ta tura
mata har naira dubu dari biyu da saba'in. Ta dan diririce sannan a hankali ta janyo
nutsuwarta tace
'A'a daman wasu kayane fa da ta siya, kuma ta riga ta karbi kayan tun kafin ta rasu
don tana turo min kudin ma na turawa mai kayan.’
Daga jin bayanin da tayi ya san karya takeyi sai dai kawai ya kyaleta saboda baya
sha'awar ya daga zancen balle wani yaji kudin na menene aka tura.
—-----
Duk yanda ya so a gama aikin gidan nan a sati biyu abun bai yiwu ba, domin ko fitar
da kayan ma sai da aka dauki kusan sati ana yi.
Don haka lokacin da sati biyu ya cika da kansa yaje har gidan Baffa ya sanar da shi
ba'a gama aiki ba sannan ya je ya sanarwa Hajiya ma.
Sai da aka dauki sati hudu ana aikin gidan nan sannan aka kammala. Don haka a
farkon sati na hudun ranar asabar da safe Abba yaje gidansu Aisha don ya dauketa su
je su yi sayayyar furniture.
Tun kafin ya karasa kofar gidan yayi mata waya don haka kafin ma ya gama tsayar da
motar ta fito. Ta bude kofa ta zauna a gaban motar, tana rufe kofar motar kuma ta
fara gatsina fuska yayinda yake kokarin jan motar. Da hannu ta fara yi masa alamar
ya tsaya ta bude kofar motar ta zuro kanta sai amai. Ya dafe bayanta yana yi mata
sannu, ya dauki ruwan roba a gefensa ya mika mata. Bayan ta dauraye bakin ta
dubeshi tace
'Malaria ne. Na ma fara shan maganinsa tun jiya da daddare, to kasan maganin ma ba
dadi gareshi ba.’
Ya mika hannu ya rufo kofar tata ya karya kan mota yana fadin
'A duba me kuma? Ai da ka bari idan na shanye maganin ban warke ba sai naje.’
Ta kwantar da kanta a jikin kujerar motar tayi masa shiru suka nufi asibiti.
Suna zuwa bayan likita yayi mata tambayoyi ya rubuta mata gwaje-gwaje yace taje
tayi ta kawo sakamakon yanzu. Suka wuce suka nufi dakin gwajin da yake cikin
asibitin.
Ba tare da bata lokaci ba aka dauki jinita aka yi gwajin aka miko musu takardun,
ana mikowa ta karbe. Ta bude; guda daya gwajin malaria ne kuma binciken ya nuna
akwai malaria din dayar kuma gwajin cikin kuma shima ya nuna akwai ciki. Dama tayi
tunanin hakan sai dai ta riga ta cire rai da haihuwa musamman yanda taga shekarun
Abban sun ja kuma itama yanzu tana jin kamar ta wuce haihuwa, shi yasa ma tafi
karkata ga malaria din.
Yanayin yanda ta ninke takardun yasa Abban ya zare takardun daga hannunta ya bude
ya karanta. Ya leka fuskarta yana dariya yace
Ta jijjiga kai kawai suka shige office din likitan yana mata dariya.
Likitan ya kara yi musu bayani sannan ya canza mata magani ya sallamesu suka kama
hanya.
'Yanzu don Allah yaushe za a gama aikin gidan nan na koma, ka ga ba sai Hajiya da
Anti Uwani sun gane nayi ciki tun ban koma ba.’
Yanayin yanda take magana ya bashi dariya, ya kuwa kyalkyale da dariya yayinda ita
kuma ta bishi da harara. Yace
'Yanzu zamu je don ko ka je gidan ma ba zan fita daga motar nan ba, muje kawai muyi
sayayyara.’
Ya sake gintse dariya ya kalli gefen tagarsa, ya karya kan mota suka nufi kasuwa.
Ya fahimci so take suje suyi sayayyar don ta koma da wuri kafin a gane tana da
ciki, shi kuwa yanda yaji dadin cikin nan bai ki aje gidan radio ma a fada ba. Haka
suka karasa shagon kayan dakin inda ta nuna duk wadanda take so ya biya kudin
sannan suka tafi bayan ya bada adireshin gidan da lambar Saddikun don idan sun gama
loda kayan su kai.
Har ya fara dariya ya gintse saboda yanda ta bata rai tana shirin fashewa da kuka,
ta kama hannun motar zata fita yayi sauri ya riketa. Yace
'Kinga gobe ma ya isa su gama daurawa in ya so jibi sai nazo mu tafi ko?’
Kai kawai ta daga masa. Sukayi sallama a kan ta shirya kayanta zai zo jibin ya juya
ya nufi gidan.
………
Kamar yanda yayi mata alkawari haka aka yi. Ya zo da kansa ya dauketa suka koma
gidan. Cikin walwala tayi sallama da su Hajiya da su Abdallah; wadanda suma nan da
sati biyu zasu koma gidan kanin babansu wato Baba Abba. Ta shiga mota suka kama
hanya.
Tayi zaton zata tarar da su Rukayya a gidan sai dai ga mamakinta babu kowa daga ita
sai shi. Haka suka zagaya ya nuna mata dakinta da nashi sannan ya nuna mata sauran
sassan gidan. Bayan sun koma saman ne ta tambayeshi ina yaran, ya bata amsa
'Saddiku yana nan fita yayi, amma kafin magriba zaki ga ya dawo. Su Rukayya kuma
sai next week Yaya zai dawo dasu kafin nan kin shirya gidan yanda kike so.’
'Kayanki na can gidan ma sai muje gobe ki kwaso wadanda kike bukata sauran kuma ki
fadi yanda za ayi miki dasu ko?’
Ta ji dadin yanda yayi mata kofar shiga dakinsa ta cikin dakinta, yanda zata iya
shiga dakinsa ba tare da yaransa sun san ina take ba; musamman matan da dakinsu
yake saman a kusa da nata.
……….
Bayan sati daya da tarewarsu Yaya Bello ya kawo su Rukayya. Ya sake yiwa Aishan
nasiha da kuma bata hakuri sannan yayi musu sallama ya tafi.
Rukayya ta fito da keken dinkinta ta cewa Abban ya kamata ayi masa table, nan take
kuwa ya amsa da alkawari zuwa wani satin za a yi mata table tunda ta kusa candy
kafin admission ya fito sai ta samu ta koyi dinkin.
Tunda suka je gidan Yaya Bello yake faman yiwa Yusra nasiha a kan ta samu ta bawa
Aisha hakuri amma sam ta ki. Idan akayi magana sai tace wai ai ta kirawota itace
taki saurararta.
Kafin ya mayar da su Rukayya ma sai da ya sa Umman Muhammad tayi mata magana amma
da aka tambayeta sai tace ta yiwa Aishan waya wai Aishan ce ba zata fadi gaskiya ba
saboda bata son Yusran. Haka suka kyaleta saboda Umman su Muhammad din ta gane
karya takeyi kuma tana jinta a lokuta daban-daban tana gayawa yaran cewa idan dai
sai ta bawa Aisha hakuri zata zauna a gidan to sai dai ta hakura da zaman gidan ta
san Abbanta ya zabi matarsa a kanta. Don haka Yaya Bello yace a barta a nan din
kawai don ya kula idan ma ta koma can din ba zata yiwa Aishan biyayya ba.
___
Satinsu uku da tarewa a gidan aka fara azumin Ramadan. Cikin walwala suka gabatar
da azuminsu, inda kullum Jummai da yaran suke taya Aisha hada abincin shan ruwa.
Ranar Juma'a ya kama ranar Sallah, don haka washegarin Sallah ranar asabar Yaya
Bello da kansa ya kawo su Yusra da Nana tare da nasa yaran, yayi musu sallama a kan
zai dawo ya daukesu da magriba.
Cikin walwala Aishan ta karbesu don dama bata da niyyar yanke musu zumuncinsu, sai
dai ko gaisuwa Yusra tayi mata ne albarkar idon Yaya Bello. Yana fita ta ja su
Sumayya suka shige dakinsu na kasa.
Ita kuwa Aisha sai ta hau saman ta sa mukulli ta kulle duk dakunan da suke saman ta
sauko da mukullin. Ya zama dakin su Rukayya na sama ne kawai yake a bude. Ta dawo
ta zauna a falon kasa cikin yaran suna ta raha ana ciye-ciye. Suna nan zaune Yusra
ta fito daga dakinsu rike da hannun Sumayya suka haye saman, a hankali ta dinga
hawa benen ko Aishan zata ce wani abu sai dai har ta haye bata ko kalli wajen ba.
Bayan ta gama ganin dakin kannenta ta fito a gadarance ta nufi dakin Aisha, sai dai
tana kama hannun kofar dakin taji a rufe. Haka ta bi duk dakunan har kicin ta jisu
a rufe don haka tayi kwafa suka sauko, ta koma dakinsu na kasan ba tare da ta cewa
kowa komai ba yayinda ita kuma Sumayya ta kwace ta koma cikin ‘yan uwanta suka
cigaba da wasansu da Hanan ‘yar wajen Yaya Bello.
Sai bayan da suka idar da sallar la'asar sannan Nana ta samu taja Rukayya suka fito
tsakar gidan, ta dubeta idonta ya ciko da kwalla tace
'Yaya Rukayya ni na fi so na zauna a gidan nan don Allah ki cewa Abba ko Anti nima
a dawo dani.'
Rukayyan tace
'To kije ki cewa Anti Aisha kina so ki zauna, da kanta zata gayawa Abban sai kawai
a barki a kawo miki kayan.’
Ta sunkuyar da kai tayi shiru na dan lokaci, ta dago ta share kwalla tace
'Yaya Yusra tace kada mu bata hakuri zata raina mu kuma cutar damu zatayi, amma ni
dai ina son zama a nan.’
'To ki biyewa Yaya Yusra kiyi ta shan wahala a banza, baki gaji da wahala bane.’
Nan Yaya; Yar wajen Yaya Bello yayar Hanan ta fito ta samesu don itama duk da sa'ar
Yusra ce amma ta fi kusanci da Rukayya saboda ta fi saukin mu'amala. Rukayya ta
dafa Nana tace
Ta shigo falon jikinta a sanyaye. Babu kowa a falon sai Saddiku da yake zaune a kan
dining table yana karatu a computer dinsa don yanzu ya sami gurbin karatu a BUK
inda yake karantar Computer Engineering. Ya kalli Nanan tana tafiya kamar wadda
kwai ya fashe mata a ciki, yace
'Ke, zo nan.’
'Yaya so nake na zauna a nan shine Yaya Rukayya tace naje na gayawa Anti.'
Ya harareta
'Kina so ki zauna saboda Yusra ta dinga aikoki kina mata rashin kunya ko?’
'Wallahi Yaya ba haka bane, ita Yaya Yusra ma bata san zan zauna ba don tace kada
na kuskura na bata hakuri na bari ita zata sa a koreta a dawo damu.’
Ya yi mata fada sosai tare da gargadin kada ta kuskura ta sake sauraren Yusra in ba
haka ba da kanshi zai mayar da ita gidan Baban, sannan yace
Ta juya ta wuce kicin din inda Aisha da Jummai suke kokarin dora tuwon dare.
Har ta shiga kicin din Aishan bata ce mata komai ba don ta zata wajen Jummai ta
shigo, sai da ta tsaya a gefenta ta kirawota cikin sanyin murya
'Anti.'
Ta juyo tace
'Anti don Allah ki cewa Abba a barni a nan gidan ni gaskiya na fi so na yi zamana a
nan.’
Da mamaki ta dago idonta kalleta don bata zata zata amsa da sauri haka ba, tace
Nana take ta dauko mata wayar ta kirawo Abban a gabanta ta sanar da shi idan Yaya
Bello ya zo ya sanar dashi ya bar mata Nana.
Dadin da yaji ba zai misaltu ba, ya so yayi mata maganar Yusra sai dai baya son ya
taso fitna don shi a yanzu bai ma san da Aishan da Yusran wacece tafi taurin kai
ba. Don haka yayi mata sallama ya kirawo Yaya Bellon ya sanar da shi.
Da gudu Nana ta fito daga kicin din ta karasa ta dafa kafadar Saddiku tace
'Yaya har ta gayawa Abba yace idan Baba ya zo ya barni a nan zai je ya taho min da
kayana.’
Sai bayan magriba sun gama cin abincin dare sannan Yaya Bello yazo daukansu.
Tabbas Yusra ta shaki haushi amma tana kan bakanta na Aisha bata isa ta bata hakuri
ba. Shi ma Abban nata haushinsa take ji saboda tana tunanin ya zabi Aisha a kanta.
Da ba don Yaya Bello ne yazo daukansu ba da wallahi babu wanda ya isa ya fitar da
ita daga gidan; to amma Yaya Bello yana mata kwarjini ba kadan ba, kuma ta san shi
baya daukan taurin kai kamar Abbansu. Yanzun nan zai bata kashi ko ya gaya mata
maganganu masu ciwo. Don haka ta wuce suka shiga bayan motar ita da Yaya yayin da
Hanan ta dane gaban motar.
__
Haka rayuwar gidan Abba ta cigaba. Gaba daya yaran Aisha ta hada tana kula da su,
su kuwa su Farha sai dai idan su zo wuni. Ita kuma Yusra ta ki ta bawa Aishan
hakuri shi kuma Yaya Bello yace kada wanda ma ya sake yi mata maganar gidan nasu,
gara a bar masa ita a nan don yana ganin kamar idan ta koma can ma lalacewa zata
yi. Shi kuwa Abbanta gaisuwa ce kawai take hadata da shi don ta sawa ranta ya daina
sonta don ya fi son Aisha. Sai dai kawai idan ta tuna da Mommy tayi ta kuka tana
fadin Mommy itace uwarta itace ubanta don a yanzu ita bata da Uba. Wajen su Yaya
Murja kawai take zuwa taji sanyi a ranta, tunda suma suna jin haushi yanda a
zatonsu Aisha ta sa Abba ya rabu da ita. Ga kuma labarai na karya da gaskiya da
take yawan kai musu, tunda in ta ga dama ko daga makaranta sai ta hau motar haya ta
wuce gidan Suwaiba ko Murjan.
Shima Abban rashin dawowar Yusra gidan yana ci masa tuwo a kwarya sai dai babu
yanda zai yi. Bai ga alamar Aisha zata saurareshi a kan maganar Yusra ba kuma baya
son rabuwa da ita musamman ma da yake yana jin dadin kulawar da take bawa yaran,
sannan kuma gashi Yaya Bello ya ma ce ba zai bashi Yusran ba shi zai yi mata aure.
Don haka ya tattara ya hakura.
Baya son ya tuna Zahra saboda yanda tunaninta yake bata masa rai, gashi in ya
tunata ma sai ya kasa nema mata gafarar Allah sai dai kawai cutarwarta a gareshi da
yake tunawa.
Idan ya kalli Aisha da cikin da yake jikinta sai ya kara jin haushi Zahran; domin
yanzu ya tabbatar itace ta san kulle-kullen da tayi ta hana Aishan haihuwa.
Idan ya kalli Yusra kuma sai ya kara jin haushin Zahran saboda yanda yake ganin ita
ce ta turawa Yusran wasu akidu masu muni wadanda suka sa ya rasa yanda zai yi da
Yusran.
………
Babbar Sallah ta wuce da wata hudu Aisha ta haifi yaronta lafiyayye, aka saka masa
suna Muhammad Bello. Yayyensa suka yi masa lakani da Baba karami.
KARSHE.