Iran tazama Jamhuriyar Musulumci acikin shekara ta 1979, bayan khomeini ya ƙwace mulki daga Mohammad Reza Pahlavi. shi'a ne mafi yawan aƙidun mutanan ƙasar. Sedai akwai mabiya sunnah da wasu addinan kaman Kiristanci da zardtosht.
74,000,000 mabiya aƙidar shi'a sune mafiya yawa aƙasar. Ahlus Sunna kuwa yawansu bai wuce adadin mutane 20,000,000 ko 25,000,000 daga ƙabiloli daban daban kamar turkumawa, kablwshawa, da kurdawa. yawan kurdawa zasu kai 10,000,000 zuwa 12,000,000 dukkanin su ƴan ahlus-sunnah ne.
Ranakin hutu:
Sallar cikar shekaran farisawa da ta kurdawa ranar 21, ga watan Maris wannan sallah ce mai muhimmanci garesu.
Tarihi ya nuna cewa kafin shekara ta 1000, makiyayan Farisa da ƙabilar Kurdawa sune mutanen farko waƴanda suka zauna a Iran, tun a shekara ta 500, kafin haifuwar Annabi Isah, Farisa ta kamu da yaƙin basasa da juyin juya hali na mulki a wannan shekara inda turawa suka mamaye ƙasar, suka sa hukunci me tsanani tun daga wannan lokacin ƙasar ta samu kanta a babbar matsala , a shekara ta 612, kafin haihuwar Annabi Isah, Ashurawa suka ƙwace mulkin kasar bayan sun ƙwace mulkin ƙasar.
Tsarin gwamnati da dokokin Iran tsarin musulunci ne na shi'a kuma suna bin dimokaraɗiyya suna zaɓin shugaba a kowace zagayowar shekaru hudu (4) shugaban Iran yana iya ya shiga zaɓe sau biyu kaɗai tsarin siyasar Iran tana kama da tsarin Amurka, Iran tana adawa da Amurka da Isra'ila sosai.
↑A. Fishman, Joshua (2010). Handbook of Language and Ethnic Identity: Disciplinary and Regional Perspectives (Volume 1). Oxford University Press. p. 266. ISBN978-0-19-537492-6. " "Iran" and "Persia" are synonymous" The former has always been used by the Iranian speaking peoples themselves, while the latter has served as the international name of the country in various languages